Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fushi dashi da kuma nuna kishin ta ƙarara abin dariyar kuma kowacce akan abu mabambamta, ita kuma wannan me ta jiyo ne?.

Lokacin da yake faɗawa Brr Farida yana wajen budurwar shi ne ai tana wajen a lokacin, wannan shine abinda ya 9 hankalin ta.

Ya saki wani murmushi, shi abin nasu dariya ma yake bashi, lallai me mata uku yana ƙoƙari to ina shi ina wannan aikin ai ko biyu da wuya ya iya haɗawa kodan gudun irin wannan.

Da sallama ya shiga, mutane da yawa ke zaune a falon amma babu Brr Farida, gaishe dasu yayi wasu daga cikin su har suna jan shi da wasa shi dai sai dai kawai yayi murmushi.

Ɗakin Hajja ya nufa a tunanin shi Brr Farida na can, bata ciki don haka ya fito ya nufi ɗakin Malama anan kuwa ya same ta, zaune tare da Ummin Fadila suna fira.

Su kaɗai ne a ɗakin dan haka ya shiga da sallama suka amsa mishi, Brr Farida ta bishi da kallo har ya ƙaraso kusa da ita.

Ganin kallon yaƙi ƙarewa ya saka shi taɓe fuska yace; "First Love wannan kallon fa?", hannu ta saka ta kama kunnen shi tace; "wannan kunnen baya jin magana ko?", ya ɗan saki ƙara yana turo baki.

Malama ta shigo da sallama itama, ganin shi yasa tace; "ashe har ɗan naki ya shigo kenan?", Brr Farida ta saki kunnen shi ta maida kallon ta kan Malama tace; "eh gashi nan ya shigo yanzu".

Gefe ya koma ya zauna yana turo baki gaba, Brr Farida kuwa ta juya suka cigaba da firar su da Ummin Fadila, ganin tayi banza dashi yasa ya matso kusa da ita.

Bata juyo inda yake ba, gaban ta ya dawo ya zauna harda tankwashe ƙafa, Brr Farida ta balla mishi harara tace; "matsa ka bani waje", ya shafa gashin kanshi yace; "First Love yunwa fa nake ji".

"ai na ɗauka ka ƙoshi da soyayya ne, ita budurwar taka bata baka abinci ba?", tuno mishi da hakan yasa ya saki murmushi yana lumshe idanu.

Brr Farida ta saka hannu ta mintsini kumatun shi har sai da yayi ƙara, cikin sauri ya tashi daga kusa da ita ya koma kusa da Ummin Fadila wacce ke dariya, suna birge ta sosai yadda suke ƙaunar junan su.

"dawo nan" ta faɗa tana ƙunshe dariya, ya noƙe kafaɗa yace; "Allah yau First Love mugunta kike jin yi mini da alamu yau kin dena sona", yadda yayi maganar ya saka su dariya.

Malama ce ta dawo hannun ta ɗauke da plate dan tunda taji yace yunwa yake ji ta fita, a gaban shi ta ajiye kafin ta juya ta kuma fita.

Ya buɗe plate ɗin, fried rice taji kayan lambu gefe kuma rabin kaza ce soyayya 😋, ya ɗago ya kalli Brr Farida kafin ya cuno baki.

"meya faru kuma?", bece komai ba sai abincin daya ɗauko ya matso kusa da ita ta gane me yake nufi dan haka ta amshi cokalin ta fara bashi a baki.

Ummin Fadila tayi dariya tace; "har kuma an gama faɗan kenan?", Brr Farida tace; "to dama waye ke shiga tsakanin faɗa na da Baby, aikuwa dai daya sha kunya ko?", ya ɗaga mata kai.

Malama data shigo hannun ta ɗauke da gorar ruwa da kuma exotic ta kalle su ta kauda kai tana sakin murmushi wanda ni dai bangane inda ya dosa ba.

Sai da yaci ya ƙoshi kafin ya janye kanshi ya koma gefen ta, kanshi ya ɗora saman kafaɗar ta ya lumshe idanu.

Yana jin su suka cigaba da firar su har zuwa wani lokaci kafin barci ya fara kwasar shi, Brr Farida ta ɗan taɓa shi ya buɗe idanu wanda suka yi ja.

"au barci ma kake yi kenan?, to ka tashi kaje ka kwanta mana", sumba ya kai mata a goshi kafin ya miƙe yana faɗin; "sai da safe", ya fice.

Ɗakin su Fadil ya wuce dama nan ne inda yake sauka, yana shiga ya same shi tare da ƴan mata gidan, bece musu komai ba ya wuce, kan gado ya faɗa sai barci.

wajen sha ɗaya sannan Fadil ya samu suka rabu dashi, ya kalli Abdul dake sharar barcin shi yayi murmushi kawai, domin kusa abinda ya faru ɗazu duk akan idanun shi ne.

Yana kallon lokacin daya janyo Nusram ɗin jikin shi ya kwance ribbom ɗin, hakan yasa ya bar wajen yana mamakin halin ɗan uwan nashi kuma a ganin shi zuwa yanzu ɗan uwan nashi ya fara jin wani abu a kanta.

Bayi ya wuce, yana shiga Brr Farida ta shigo ɗakin, wajen Abdul ta ƙarasa ganin yadda yake barcin ta tabbatar beyi addu'a ba.

Tana cikin yin addu'ar Fadil ya fito, kallon su yayi kafin ya kauda kai yana murmushi, shi kuwa yana mamaki shekara da shekaru a haka ya san su wai basa gajiya da ƙaunar juna ne?.

Tana gamawa ta shafa mishi a jiki kana ta juya domin tafiya, Fadil yace; "sai da safe Mummy", ta amsa sannan ta fice.



******** ********


Da sallama suka shiga gidan kowa da abinda ke ranshi, Kabeer ya taso da sauri yana faɗin; "yauwa kunga na duk wanda zai fi kyau dan na san nata ne me kyau", ya ƙarasa yana ƙoƙarin riƙo hannun Nusram ɗin.

"Wow!, dama na faɗa kamar a india", ya faɗa yana shafa inda zanen lallen ya bi, cikin sauri Nusram ta ƙwace hannun ta a ɗan hasale tace; "meye haka Kabeer bana so", ta ƙarasa fuskar ta a ɗaure.

Dr Saleema taja tsaki ƙasa-ƙasa kafin ta wuce ɗakin ta, Fadila cikin jin haushi tace; "ai wallahi nima nawa yayi kyau kuma ko ka yaba ko kada ka yaba ni na san dai yayi kyau".

Muhibba tace; "ai kuwa dai wallahi itama wannan ɗin na san me kake yiwa ai", ta ƙarasa tana murguɗa baki gefe, Mummy dai bata ce komai ba.

Nusram ta ƙaraso kusa da Muhibban ta zauna har lokacin ranta a dagule yake, Muhibba ta kalli ribom ɗin hannun ta tace; "lalala garin yaya kika kwance doghnut ɗin kanki, ina ma kika tsaya ne?", itafa wa'innan tambayoyin sun fara isar ta.

Kafin tace wani abu Muhibban ta saka hannu ta cire gyalen dake saman kanta, gashin ta ya bayyana, ba iya Kabeer da Kamal ba har Aunty Maryam da Aunty Muhsina sai da suka sauke numfashi.

Aunty Muhsina tace; "kamar a india, gaskiya yayi kyau", Nusram kuwa ta maida kallon ta kan Ƙabeer da Kamal wa'inda suka kafe ta da idanu kamar su haɗiye.

Ta kalli Muhibba dake ƙoƙarin maida mata da ribbom ɗin kanta amma ta kasa tace; "dan Allah Muhibba ki ƙyale ni haka, in sha Allahu zan maida da kaina", ta ƙarasa kamar zata yi kuka.

Muhibba zata yi magana Abban su dake zaune da jarida a hannu yace; "Hibba bata ribbom ɗinta".

Nusram kuwa gabanta ya faɗi saboda jin muryar Abban nasu, bata taɓa tunanin shima yana falon ba, ta ɗago ta saci kallon shi, shima dai idanun shi yana kan ta, da sauri ta miƙe tsaye.

Ta karɓi ribbom ɗin a hannun Muhibba tayi hanyar ɗakin Dr Saleema da sauri, ko ba'a faɗa mata ba tana ji a jikin ta idanu sunyi yawa a kanta.

Da sallama ta tura ƙofar ta shiga, Dr Saleema ta ɗago ta amsa tana me cigaba da ɗauko kayan da zata saka daga cikin wardrobe.

Bata kuma kulata ba, itama sai kawai ta fara cire kayan ta, towel ta ɗauka ta ɗaura sannan ta nufi bayi, Dr Saleema ta bita da kallo har ta shige kafin taja tsaki, zuciyar ta kawai ke bata wankan tsarki zata yi😂😂.

Nusram kuwa koda ta shiga bayin wanka kawai take yi amma tana mamakin meya canza yanayin Auntyn nata da wuri haka?.

Tana fitowa ta sami Dr Saleemar saman bed ɗinta hannun ta riƙe da waya tana dannawa, wajen dressing mirror ta wuce inda ta fara shiryawa.

Sai da ta gama duk abinda zata yi kana ta wuce wajen kayanta ta ɗauko rigar barci maroon colour me tsantsi ta saka, gashin kanta da taji ya dame ta dalilin da ya saka ta fara ƙoƙarin ɗaure shi kenan amma ta kasa.

Kusa da Dr Saleema ta matso tace; "Aunty dan Allah ɗaure mini gashi na", Dr Saleema ta watsa mata wani kallo sannan tace; "da ni nake ɗaure miki gashin ko kuwa shi wanda ya kwance meyasa baki ce ya ɗaure miki ba".

Shiru Nusram tayi gaban ta yana faɗuwa, Dr Saleema taja tsaki tace; "aikin banza ni bana son iyayi, sai da kuka gama soyayyar ku yanzu zaki zo ki wani isheni, tashi ni ki bani waje".

Cikin sanyin jiki Nusram ɗin ta miƙe, har ta fara tafiya ta dawo ta tsaya gaban Dr Saleemar tace; "Aunty dan Alƙah kiyu haƙuri", ta ƙarasa muryar ta na rawa.

Cikin sauri ta juya tayi hanyar fita tana share hawaye, ita kuma meye laifin ta a nan, ɗakin Muhibba ta buɗe ta shiga, da Fadila da Muhibban suka bita da kallo, bata ce musu komai ba ta faɗa saman gadon tana fashewa da kuka.

Ɓangaren Saleema kuwa jikin ta ne yayi sanyi, amana fa aka bata amma ji yadda ta yiwa yarinyar, gashi yanayin sanyin yarinyar na birge ta, ta sani itama kanta yadda tayi mata bata kyauta ba.

Wayar dake hannun ta, ta ajiye kafin ta miƙe tabi bayanta, ta shiga ta samu su Fadila sun tasa ta a gaba suna tambayar ta lafiya kuwa ita kuma babu abinda take faɗi sai "kiyi haƙuri", Dr Saleema jikin ta ya kuma yin sanyi.

A hankali ta taka har gaban ta, Nusram idanun ta a runtse yake dan haka bata ji zuwan ta ba har sai da ta kira sunan ta, da sauri ta buɗe idanun ta kana tashi ta zauna.

Ɓare baki tayi zata yi kuka, Dr Saleema ta dakatar da ita, "ya isa haka tashi muje", babu musu ta miƙe tabi bayan ta.

Fadila da Muhibba suka kalli juna suka taɓe baki alamar su suka sani, cigaba suka yi da firar su dan sun san wata ƙila wani abu ne ya faru tsakanin su.

Suna shiga ɗaki Dr Saleema taja hannun ta har saman kujera ta zaunar da ita, sai da ta runtse idanu kana ta kama gashin nata.

Abinda ya bata mamaki yadda taji shi a bushe, duk a tunanin ta zata jishi a jiƙe, nan da nan taji wata irin kunya ta kamata, ta ɗan saci kallon Nusram wacce ke faman sauke ajiyar zuciya.

Taci wuya sosai kafin ta iya ɗaure gashin, ta saki ajiyar zuciya sannan tace; "muje mu kwanta ko?", ta kama hannun Nusram ɗin suka ƙarasa saman bed ɗin suka kwanta.

Kallon juna suke yi har na tsayin lokaci kafin Nusram tace; "dan Allah Aunty kiyi haƙuri wallahi babu abinda ya faru tsakani na dash..........".

Da sauri Dr Saleema ta dakatar da ita tace; "ya wuce raina ne a ɓace, amma ai ba laifi kika yi ba tunda dai mijin ki ne kuma ko gaba ya buƙaci wani abu a wajen ki to lallai ki bashi dan sai ya ɗaga kafar shi zaki shiga aljanna kinji", ta ɗaga kai.

"yauwa to yanzu ayi barci ko, sai da safe kuma", tana faɗin haka ta juya baya, duk da barcin take ƙoƙarin tilasta kanta tayi amma abin ya gagara, data rufe idanu sai taga lokacin da Abdus-samad ɗin ke ƙoƙarin kissing Nusram ɗin a gabanta.


#LIKE
#SHARE
#COMMENTS.


*Babyn Abdul, Maman Meenal Elham da Farouk*.



*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.







An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment