Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta.

*********⬇️⬇️⬇️********

*UNGUWAR SARKI, KADUNA*.

Ya ƙara kallon agogon dake hannun shi sannan yayi tsaki, suna tsaye suna magana, ya kalli Sumayya sannan yace; "ba zaki wuce ki shiga ba", Sumayya ta zunɓuri baki kafin ta buɗe motar ta shiga.

Ya ƙara kai kallon shi gare su sannan ya taɓe fuska kamar yana gaban first love ɗin shi, ya shiga motar sannan ya danna musu horn.

Brr Farida ta kalli Fadila tayi murmushi tace; "kije idan ba haka ba wancan ɗan ujilar zai.iya tafiya ya barki, ku tabbatar kun zaɓo kayan daya dace ki kuma saki jiki ki zaɓi abinda kike so kinji, dalilin na san zaki fi sakewa yasa nace kuje tare da Baby dan na san sai kunfi jin daɗin siyayyar jeki ƴata Allah yayi muku albarka".

Fadila ta juya cike da kunya, Brr Farida ta bita da kallo tana murmushi a baya bata wani son auren amma yadda yarinyar ta natsu yasa taji auren ya kwanta mata a rai.

Koda ta shiga motar sai da Abdus-samad ya harare ta sannan yaja motar suka fice yayin da masu tsaron lafiya suka biyo bayan su.

Suna tafiya kowa ya natsu babu wanda yayi magana, Fadila tace; "wai yaushe zaka je wajen Malama ne?", yace; "kina son komawa gidane", ta ɗaga kai.

Suka kalli juna shida Sumayya sannan suka yi murmushi, yace; "yarinya ai kinzo kenan", Fadila ta ɓata fuska, su kuwa suka sami damar tsokanarta har suka ƙarasa Mall ɗin.

Yana gaba suna binshi a baya har ciki, kowacce taja kwando yace; "Sumayya an sami abinda ake so ko?", tace; "Yaya Abdul ai dai ba'a kuɗin ka bane".

"duk Daddy ne ya ja mini da ya barni na fara aiki na ai da babu yarinyar da zata raina ni", suka tafi suna mishi dariya.

Kiran wayar shi yasa ya ɗan matsa baya domin amsa kiran, "Aunty na barka da warhaka", ta ɗan ja numfashi kan tace; "idan kace mini Aunty sai naji wani iri".

Yayi murmushi yace; "dole na baki girmanki Saleema", ta ɗanyi jim kan tace; "kai baka iya kiran mutum ba sai dai a kira ka ko?", ya ɗan shafa gashin kanshi yace; "afuwan zan dage na koya yanzu lafiya kuwa".

"ina zaune naji ba zan iya haƙuri ba sai na kira ka, zuciya ta ke bani kamar wani abu ya same ka shine na kira naji ko lafiya?", Abdul yabi inda yake da kallo yace; "lafiya ta lau yanzu ma ina Kareem Shopping Mall na kawo Sumayya da Fadila siyayya".

Tayi murmushi tace; "hmm da ace ban gaji ba da nazo sai na taya ka fira, sannan ka faɗa musu kada su sake su wahalar mini da kai, ka kula da kanka".

"an gama ranki shi daɗe, na kuma gode da kulawar ki, kema ki kula", daga haka ya kashe wayar.

Idanun shi ya sauka a kan ribbom ɗin da suke jere a saman canter, yabi su ɗaya bayan ɗaya da kallo har yazo kan wani ya tsayar da idanun shi a kai, ya jima yana kallon shi sak kalar na Nusram wanda ya amsa a wajen ta kalar golden.

Hairat ta kalli Khausar tace; "kinga me na gani kuwa?", Khausar tace; "na gani mana", Hairat ta runtse idanu tace; "damn Sexy, gaskiya gayen ya haɗu dole na shawo kanshi" ta faɗa tana ƙoƙarin zuwa gare shi.

Khausar tayi saurin janyo ta baya tace; "wannan ai yafi ƙarfin ki Baby sai dai ni, amma abinda yake bani mamaki yana kama da Daddy na", Hiarat ta ƙaro zaro idanu tace; "tabbas hakane".

Khausar taja hannun Hairat tace; "zo muje dole na shawo kan wannan gayen", suna isa kusa dashi Khausar ta kai hannu ta kwaso Ribboms guda biyu ta ƙaraso gaban shi hannunta janye dana Hairat.

"amm pls dan Allah duba mana wanne kala yafi kyau", ya juyo ya kalle su, nan fa ƙafar Khausar ta fara rawa ji tayi kamar shi kaɗai ne a cikin Mall ɗin gaba ɗaya ya cika wajen.

Abdul ya kalle su sama da ƙasa, Khausar riga da wando ne a jikin ta daga ƙugunta belt ta saka ta ɗaure shi, sai Hairat data saka pencil skirt baki da kuma riga fara, babu ko mayafi a jikin su.

"kina da magana ne?", ya faɗa yana ƙara buɗe idanun shi a kansu, Khausar tace; "am dama......dama........dam......dama.......nac......nace......ko zaka duba.........ko zaka duba mana wanne yafi kyau".

Ya ɗan taɓe baki sannan yace; "banda sani akan kayan mata", da sauri Khausar taja hannun Hairat tace; "shikenan muje na gode", sai lokacin Hairat ta sami damar haɗiye miyau ɗin dake bakin ta.

Har suna harɗewa wajen fita, basu ɗauki komai ba dan haka basu tsaya wajen cashier ba.

Abdul ya bisu da harara, kamar ance ya kalli ƙasa yaga ƴar ƙaramar purse ɗin Khausar a ƙasa wato tsabar ruɗewa harta yarda abinda ke hannun ta.

Yana tsugunawa ya ɗauka Fadila da Sumayya suka ƙaraso, dan haka hanyar waje kawai ya nufa, babu bata lokaci aka lissafa kayan ya miƙa Atm ɗin shi aka cira sannan suka fice inda kuma za'a saka a kai musu kayan su mota.

Koda suka fito ya bi wajen da kallo, can ya hango su, da alamu jakar suke nema dan buɗe motar su, ya kalli Sumayya yace; "amshi makullin nan, ki buɗe ku shiga ku zauna ina zuwa" ya ƙarasa yana juyawa ya tafi.

Hajiya Salma ta kalli Alhaji Sa'eed suka yi murmushi, wato tun zuwan Abdul suke wajen kuma duk suna kallon shigar shi da fitosar shi.

"yanzu ne lokacin daya kamata mu aiwatar da nufin mu", faɗar Alhaji Sa'eed kenan yayin da yake danna wayar shi, motar yaran shi dake gaba.

Yana ɗagawa yace; "Scorpion ka aikashi lahira kawai", Scorpion yace; "an gama ranka shi daɗe yanzu lahira zata yi baƙo", ya ajiye wayar sannan ya zaro pistol daka aljihun motar shi ya saita ƙirjin Abdul wande ke nufar motar su Khausar ɗin dan bata jakar ta, kasancewar motar su Khausar ɗin tana gaban ta scorpion ɗin, babu ɓata lokaci ya harbi Abdus-samad ɗin.



#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.


♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

*brr zahra Allah ya ji kanshi yasa Aljanna ce makoma ubangiji ya yafe mishi kurakuren shi*.

Godiya ga ƙungiya ta guda ɗaya tamkar da dubu ko ince miliyan, *GOLDEN PEN WRITTERS ASSOCIATION*, musamman jajurtattun cikin ta *UMAR ƊALHAT da kuma *SHAMSIYYA IBRAHEEM ƊAN MUSA*.

*JINJINA GARE KU*

*Auntyna Amina Alhassan (Oum deedat)*
*Auntyna Ummee Yusuf(oum yusuf)*
*Sumayya Abdullahi Babayo(Sumiee B)*.
*Faridaty(Ƙafar yawo)*
*Harira Aliyu(ƴar fillo)*
*Ummeeteey Yusuf*
*Fatima Batula(Bloody)*
*Maryam Shahada*
*Maryam ankudi*
*Shatu*

Da duk sauran da ban ambata ba, Allah ya ƙara haɗa kanmu ya tsare mu daga sharrin mahassada.



📖📖43-44📖📖






Cikin tashin hankali da kiɗima Sumayya da Fadila suka yi ƙasa da kai jin karar harbi, Abdul kuwa hannu yasa ya taro Khausar dake ƙoƙarin zubewa bayan ta ƙwala wani irin ihu na azaba da raɗaɗi.

Hajiya Salma ta zaro idanu ganin wacce aka samu, cikin sauri ta buɗe motar ta fito ta nufi inda suke, kan wani lokaci wajen ya hargitse, ganin hakan yasa su Scorpion jan motar su suka gudu.

Da taimakon Securities na wajen aka saka Khausar cikin mota, sannan suka rankaya asibiti, wayar Saleema ya kira yana tambayar ta tana asibiti.

"meya faru ne? Wani abu ne ya same ku?, bana asibitin amma bari na taho yanzu", ta faɗa duk ta gama rikicewa, Abdul kuwa ajiye wayar yayi ya dafe kanshi.

Suna isa asibitin aka amshe ta, sai da suka yi rubuce-rubuce kafin aka fara dubata, ta zubar da jini da yawa dan ma bullet ɗin a kafaɗa ya same ta.

Hajiya Salma zuwa lokacin hawaye kawai take yi tana ihu ganin zata rasa ƴar ta, Alhaji Sa'eed ke lallashin ta, Sumayya da Fadila ma kuka suke yi dan basu taɓa ganin tashin hankali irin wannan ba.

Kasancewar da sanayya sai a lokacin Police suka iso, Abdul ko magana ya kasa yi ranshi a ɓace yake ya rasa menene dalilin da yasa ake kai ƙoƙarin kashe shi.

Sun ɗauki report sannan suka ce zasu dawo zuwa lokacin da Khausar ɗin ta farka, Dr Saleema ta fito daga ɗakin ta dube su tace; "ta rasa jini da yawa dan haka dole sai an ƙara mata leda biyu".

Hajiya Salma ta ɗora hannu akai tace; "na shiga uku ƴata zata mutu ta barni garin son zuciy.....", Alhaji Sa'eed be bari ta ƙarasa ba yayi saurin cewa; "haba Hajiya Salma kada kije kiyi saɓo mana".

Abdul dai kallon su kawai yake yi amma a yadda alama ta nuna wannan ce mahaifiyar yarinyar, yace; "kiyi haƙuri insha Allahu komai zai koma dai-dai, yanzu zan je sai a ɗebi nawa a sa mata", Dr Saleema tace; "Abdul........".

Ya riƙe hannun ta yace; " muje kawai Aunty", bata da yadda zata yi dole suka tafi Lab ɗin tare, ita dai Salma ba'a son ranta ya bada jinin shi ba.

"yanzu Abdul sai ka bawa stranger jinin ka wacce ma baka santa ba?", Abdul yayi murmushi yace; "kada ki ce mini imanin ki ya gaza a nan mana, haba ina kallon ki a matsayin me tausayi, muje a saka mata", Saleema tayi ajiyar zuciya tace; "ka koma ka kwanta bari naje a saka mata".

tana fita ya lumshe idanu yana tunani, su waye wai ke son ganin bayan shi ne?, ya san Mahaifiyar shi ta san wani abu daya danganci hakan amma kuma ba zata faɗa mishi ba.

Dr Saleema tana zuwa ta same su a tsaye harda Brr Hauwa, Brr Hauwa kuwa ganin ta sai da ta ɗan tsorata ita kuwa Dr Saleema duk da yadda zuciyar ta ke mata kokwanto amma sai ta kauda kai kawai ta shige.

Shi kanshi Abdul lokacin da ya fito sai da abin ya bashi mamaki, amma bece mata komai ba, ita kuwa Brr Hauwa nunawa take ai Alhaji Sa'eed ɗin ita ce lauyar shi.

Sai da komai ya dai-daita sannan Abdul yace da Fadila da Sumayya su tashi su tafi, har wajen Hajiya Salma yaje yace; "kiyi haƙuri insha Allahu zata sami sauƙi".

Cikin ƙufula tace; "wallahi idan yarinya ta, ta mutu sai nayi shari'a da kai, an kawo maka hari amma yanzu ƴata ce a cikin wahala", har ya fara tafiya yaja ya tsaya ya juyo yana kallonta.

Alhaji Sa'eed da Brr Hauwa kuwa fuskar su ƙarara ta nuna rashin gaskiya, bece komai ba ya juya ya tafi, ita kanta Dr Saleema tayi mamaki sosai, cikin sauri ta biyo bayan su.

"dama kai aka kawowa harin?", yaji saukar tambayar, ya juyo yace; "eh amma ai babu komai ya riga da ya wuce", dr Saleema tace; "Allah ya kyauta gaba", suka amsa da Ameen.

Ko a mota yana jin Fadila tana tambayar Sumayya wai dama shi aka kawowa hari, itama Sumayyar tace; "wallahi ban sani ba banda yanzu da tayi maganar".

shi dai bece komai ba har suka isa gida, Brr Farida dake zaman jiran su ta taso da sauri, "har kun dawo?".

"eh", abinda ya faɗa kenan ya wuce part ɗin shi, Brr Farida ta bishi da kallo kafin ta juyo ta kalli Sumayya tace; "meya faru", Sumayya ta bata labarin duk abinda ya faru.

Hankalin Brr Farida ya tashi sosai, " ku shiga ciki ina zuwa", nan suka wuce suka shiga falo ita kuma tayi hanyar part ɗin Abdul.

Ya shiga bayi wanka ta fito dan haka ta samu waje ta zauna tana jiran fitowar shi, koda ya fito da sauri ta miƙe taje wajen shi ta riƙo hannun shi tace; "Baby meya faru a wajen siyayyar".

Yace; "babu komai", ya fara goge sumar kanshi, Brr Farida ta kuma cewa; "amma Sumayya tace an kai maka attack", be juyo ba ya cigaba da abinda yake yi.

"Abdul magana nake maka fa", ya juyo hannun shi riƙe da Comb yace; "First Love me kike so kuma nace miki, sun baki labarin abinda ya faru ai".

Brr Farida tace; "shikenan, Allah ya kiyaye gaba", ta fice daga ɗakin, da kallo Abdul ɗin ya bita tana fita yayi wurgi da comb ɗin hannun shi.

Kanshi ya dafe da hannu ɗaya yace; "tabbas akwai abinda kike ɓoye mini, menene wannan?".

Be fita ba har akayi kiran sallar la'asar sannan ne ya yi Alwala ya wuce masallaci, be dawo gidan ba sai dare.

Ganin dare yayi kawai sai ya wuce part ɗin shi, Brr Farida tana hango shigowar shi tayi ajiyar zuciya sannan ta juya ta wuce ɗakin mijin ta.

"yanzu hankalin ki ya kwanta ko, tunda ya dawo", ya faɗa, tayi murmushi tana ɗaga kai, "sai dai ya fara zargi na a al'amuran shi", Dr Abubakar ya riƙo hannun ta yace; "ki kwantar da hankalin ki, na san Abdul ba zai taɓa ganin laifin ki ba koda ace ya san tarihin shi gaba ɗaya dan haka ki kwanta kiyi barci, gobe zan fara shirye-shirye dan ina so ya fara aiki a watan nan", Brr Farida cikin tsoro tace; "kada kayi haka dan Allah ka bari ba yanzu ba".

"dole ne Abdus-samad ya fara aiki, kin san dai ba zai zauna a haka ba ko, Tameer da Sameer duka aiki suke yi, ga Surayya itama sannan rashin fara aikin shi hakan zai janyo cece kuce a cikin family", Brr Farida ta kau da kai kawai.

Bata kuma cewa komai ba ta kwanta, haka shima Dr Abubakar ɗin kowa da abinda yake tunani.

******** ********

"yanzu irin abinda kika fuskanta kenan, Ram amma shine babu wanda ya faɗa mini", Nusreen ta faɗa cikin kuka bayan Nusram ta gama bata labarin abinda ya faru.

Nusram ta dafata tace; "ya isa haka, ki share hawayen ki, dani da Atika duka ɗaya ne, ni yanzu abinda yafi damu na shine yadda zan sami miji cikin sati biyu, Rimluv bana so ta dalilina auren shekara talatin ya warware", Nusram ta ƙarasa cikin damuwa.

Nusreen kuwa cikin fushi tace; "ya lalace mana, me auren ya tsinana mana, ko kuma ita Ummin me Baban yake tsinana mata, nifa dama can na gaji".

"amma ban taɓa sanin baki da hankali ba sai yau, mu kuwa auren yayi mana wani abu domin ya bamu sunan uba, martaba da daraja wacce sai wanda aka haifa ta hanyar aure yake da ita, idan banda abin ki ko Isa ma ai sheda ne a wajen ki, sannan Ummi da kike maganar ita ai ko babu komai tana da daraja da matsayi wacce budurwa ko bazawara bata da shi dan haka ki dawo cikin hayyacin ki bana so na kuma jin kinyi wannan maganar".

Nusreen ta zumɓuro baki tace; "ai ke dama ba'a yi miki abin arziƙi, daga magana sai kiyo kan mutum da wa'azi", Nusram ta ɗauki jakar ta tace; "kinga tafiya ta tunda ba zaki tsaya ki saurare ni ba".

Da sauri Nusreen ta janyo ta tace; "haba rabin jikina, dawo ki zauna wannan shine zuwan ki na farko gidan nan yaushe zaki zo kuma kice zaki tafi haka".

babu yadda ta iya haka ta zauna, sun yi fira sosai duk da rabin firar dai ta ƴan gidan su ce daga nan kuma suka yi kitchen inda suka dora abinci.

"bari dai naga meye a jakar nan da kike ta yawo dashi", Nusreen ta kai hannu ta ɗauke jakar Nusram tana dariya.

Nusram tace; "ban son bincike dan Allah ki bani kayata", tana buɗewa ta zaro wayar cikin mamaki take bin Nusram ɗin da kallo.

Nusram ta kauda kai, ita har ta manta da wayar ma a ciki, "wannan fa daga ina?", Nusreen ta jefo mata tambayar.

Nusram ta taɓe baki tace; "ina tahowa ne wani a bayan me mashin ta faɗo daga jikin shi, nayi mishi magana amma be ji ba shine na ajiye da fatan anjima ya kira".

Nusreen ta girgiza kai tace; "me wannan wayar ya wuce me hawa mashin, ki faɗa mini gaskiya", Nusram tace; "ƙaryata ni zaki yi kenan?".

tayi dariya tace; "ba haka bane, Allah yasa ya kira da wuri", Nusram ta amsa da Ameen, nan suka wuni tare har gaishe da Hajiya tare suka je, nan Nusram taga tsantsar ƙauna.

Data tashi tafiya haka Hajiya ta haɗo mata kayan kwalliya da kuma atamfa Nusram tayi godiya, Haijya cike da sha'awarta tace; "kada ki damu ƴata, ki ɗauke ni kamar mahaifiyar ki", Nusram tayi murmushi tace; "to Hajiya".

Har bakin get Nusreen ta raka Nusram ɗin, "to.ki gaida Ummi da Kubra, wallahi sai nake ji kamar na bi ki mu tafi", Nusram ta dalla mata harara.

"ina ji nan da one week zanje gidan Yaya Sulaiman shima naga wace wainar yake toyawa", Nusreen ta kwashe da dariya.

Haka suka rabu cike da farin ciki, ta jima a bakin titi tana jiran abin hawa sai dai yanayin unguwar da kuma yadda yamma ta fara yi yasa gaba ɗaya hanyar take shiru.

Nusram ta danna wayar dake ƙanƙame a hannun ta, ƙarfe shida da minti ashirin, nan da lokaci kaɗan za'a fara kiraye-kirayen sallar magrib, a hankali ta fara takawa hannun ta riƙe da kayan da Hajiya ta bata ɗayan kuma riƙe da wayar sai ƙara ƙanƙamewa take yi.

Abin haushi har aka kira sallah Nusram bata sami abin hawa ba, gashi gari ya fara duhu nan fa ta ƙara sauri dan bata so wani abu ya same ta kan hanyar.

Ɗaya ya kalli sauran biyun dake zaune yace; "gafa wata kaya nan tana tahowa", ɗayan ya bita da kallo, ya lashe baki yace; "gaskiya Baaba yarinyar ta gama haɗuwa", ɗayan yace; "ai ni nama kasa cewa komai kace yau akwai sharholiya", suka fashe da dariya.

Nusram da taji ƙarshen maganar tasu ta ƙara ƙanƙame kayan hannun ta, tana me ƙara yin sauri, a baya suka biyo ta suna faɗin; "ƴan mata sai ina?", bata kula su ta ƙara sauri.

Ganin sun kusa cin mata yasa ta fara gudu, suma kuwa suka rufa mata baya, gudun su da nata ba ɗaya bane dan haka suka cimmata.

"dan Allah ku ƙyaleni na tafi", suka sheƙe da dariya, daya yace; "bari na tambaye ki, kina jin tsananin yunwa da ƙishirwa sai kawai kiga abinci lafiyayye da ruwa me sanyi zaki ci ko zaki bar shi?", ta girgiza kai hawaye na zubo mata tace; "dan Allah kada ku cutar dani".

Ɗaya ya saka hannu ya finciko ta, ta faɗi ƙasa, Nusram ta saki ihu suka kwashe da dariya, kayan ɗaya ya kalla ya tsuguna ya ɗauka yace; "kai Baaba harda abin arziƙi take tafe dashi, amsa mun sami na zuwa canje wajen sholay gobe ya bamu kaya", ɗayan kuwa ya ɗauki ledar kayan.

Nusram ta miƙe tsaye tace; "dan Allah ku barni na tafi to", Babu fa inda zaki je sai mun kwashi namu rabon malama", ya ƙarasa ya yaga hijab ɗin dake jikinta.

Tasa hannu ta kare ƙirjinta, tana fashewa da kuka, ɗayan ya kalle ta yayi dariya yace; "lallai nifa na lura Abba yawanci masu saka wannan abin sunfi kaya wai ya hakane, kenan rowa kuke yi mana ko", ta girgiza kai.

Wanda aka kira da Abban ya kalli wayar dake hannun ta yace; "kai yasin babbar karuwace kalli wayar dake hannun ta", jin hakan yasa ta ƙara ƙanƙame wayar.

"ke bamu wayar nan", Nusram ta matsa baya tana girgiza kai tace; "dan Allah ku ƙyale ni haka na tafi ba tawa bace", ganin zata ɓata musu lokaci yasa ɗayan yayi kanta dan ƙwatar wayar ita kuma ta hana, yana ƙoƙarin karɓa tana karewa ya saka hannu ya murɗeta.

Be kai ga amsar wayar ba, mota taja ta tsaya, duka suka bi motar da kallo, na ciki be fito ba haka be tafi ba, ganin sun shagala da kallon motar yasa ta hankaɗe wanda ya riƙe ta, ta koma kusa da motar ta tsaya.

Fin minti biyar Abdus-samad ya bin su da kallo, yana kuma kallon yadda suke ƙoƙarin wulaƙanta mace duk da be san wacece ba, ganin yadda yake ƙoƙarin riƙe yarinyar ne yasa ya ƙaraso gaban su.

Sai dai zuwan shi ya fahimci wacece hakan ya kuma fusata shi, a hankali ya ɓalle murfin ƙofar ya fito, kallon kallo suka yi da juna, cikin mamaki da firgici suka juya a guje suka bar wajen.

Ganin hakan yasa ya juyo ba tare da ya bisu ba ya kalle ta, tana tsugune a wajen tana kuka, ya ɗan ja tsaki cike da jin haushi kan yace; "dallah Malama tashi ki shiga mota".

Ta ɗago fuskarta a firgice sai dai ganin ko waye ya ƙara firgitata, jikin ta ya hau rawa, hakan da tayi ya tuna mishi da tsoron shi take ji fa dan haka ya jingina da motar yana kallonta.

Bata bar kukan ba kuma bata tashin ba, "zan fa tafi na barki kuma idan na barki a wajen nan ba mutum uku ba har mutum shida zasu iya kawo miki hari", jin hakan yasa ta miƙe da sauri tana

Please Login or Register in order to submit comment