Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

domin zuwa ta shirya.

Ita kuma Nusram ɗin ta cire hijab sannan ta kwaso kayan da zata fara nata aikin, nan ta shiga haɗawa, su kuwa amaren babu abinda suke sai mamakin yadda wannan matashiyar zata musu gyara.

Haka dai suka fara gyaran inda nan suka cika da mamaki ganin yadda take gyara su cike da bai, Nusreen kuma tana gefe tana haɗa jakun-kuna dama su kan taya ta hakan yasa suka iya domin duk wanda zai zauna da ita tofa ba zai yi zaman banza ba.

Kan wani lokaci ta gama gyaran sannan ta koma kusa da Nusreen ɗin tana taya ta haɗa jakun kunan, suna fira tsakanin su sama sama.

Yayin da suma amaren suke nasu firar lokaci zuwa lokaci, haka har magriba ta kusanto, tashi Nusram tayi ta sirka musu ruwan da zasu yi wanka wanda ruwan ma da wasu itatuwa da sinadarai masu ƙamshi.

Sai da suka fito sannan ta ɗauko wani ƙaramin roba me cike da wani mai me shegen ƙamshi ta basu suka bi jikin su suka shafa.

Ɗayar ta kalli Nusram tace; "gaskiya kin huta da kika koyi sana'a ba ruwanki da zama haka bayan kin yi aure", Nusram tayi murmushi kawai, haka suka yi sallama cike da birgewa da mutuntawa.

Nusreen ta ajiye ta hannun ta tace; "gashi Aunty har yanzu shiru ko lafiya?", kan suce wani abu tayi sallama ta shigo.

"kuyi haƙuri na jima sosai ban dawo ba", ta faɗa tana ajiye uban kayan dake hannun ta, Nusram tace; "babu komai, na manta ince miki Ummi tace ki bata wasu cittan da curry da thyme na hannun ta sun ƙare".

Auntyn tace; "bari na haɗo muku", ta faɗa tana ƙarasa miƙewa domin haɗo musu yayinda su kuma suka hau zaɓar kayan domin tafiya da nasu.

Sai da suka haɗa komai sannan suka yi mata sallama, ta ciro ɗari biyar da ta basu haka suka yi mata godiya suka fice daga gidan cikin sauri akan zuwa jibi zasu dawo domin amsar ragowar kayan.

Haka suka fice daga gidan da kaya niƙi-niƙi Allah yasa babu nisa ma zuwa bakin titi,sun ɗan jima kafin su samu abin hawa kasancewar magriba ta gabato.

Ana kaisu suka sauka, haka Nusreen ta bashi kuɗin shi sannan ta ɗauki nata kayan itama Nusram haka, da ƙyar suke tafiya da kayan dan suna da yawa sosai.

Nusreen wacce ke gaba da kaya a hannun ta, su biyu suka taho a jere Fadil na riƙe da kwallo yayin da Abdul ke gefen shi a iya saurin su shine kada magriba ta iske su akan hanya.

Ɗan bangajar hannun Nusreen yayi wanda yasa kayan dake hannun ta faɗuwa, ita kanta sai da ta kusa faduwa saboda gajiyar da tayi sosai Allah ya taimake ta Nusram ta riƙo ta da sauri.

Abdul kuwa cikin sauri ya tsuguna ya ɗago jakar dake cike da kayan, Nusreen kuwa wani irin haushi yazo mata wuya.

Da sauri ta tsuguna ta fizge jakar tana faɗin; "Malam dallah bani jaka ta mutum yana tafiya kamar wani makaho ai ba kowa kafi sauri ba kuma yadda kake da uzuri haka kowa ma yake da uzuri na rasa me yasa irin ku basu san darajar mata b..........".

Kasa ƙarasa tayi saboda ɗagowar da yayi domin ganin wacece wannan, ita kuwa Nusreen maganar taji ta tsaya mata a maƙogoro saboda wani kwarjini da yayi mata ga idanun shi masu kama dana mage daya kafe ta dasu wanda ya haddasa mata daburcewa.

Ba ita ba ita kanta Nusram babu abinda ƙirjin ta yake sai dukan uku-uku, tunda take bata taɓa haɗuwa da mutumin daya firgitata kalar wannan ba a zahirin gaskiya ba uta yake kallo ba amma ji take kamar a gaban kotu take, jikin ta har rawa yake yi tsabar ruɗewa.

Ya miƙe tsaye sosai sannan ya matso kusa da Nusreen yace; "ina gain tunda har na baki haƙuri ai ya kama ta ki haƙura ko, *MENE NE RIBA TA??* (littafin zaratan marubutan Golden pen, wanda mutum biyar ke aikin rubuta shi domin kawowa masoyan su) dan naci zarafin mace wacce bata da ƙarfi kuma take da rauni, ya kamata ace kin kula da martabar ki da darajarki ki dena ɗaga murya a titi duk kuwa da irin abinda aka yi miki", daga haka ya juya ya tafi Fadil yabi bayan shi.

A tare suka sauke ajiyar zuciya kafin Nusreen taja tsaki jiki a sanyaye ta ɗauki kayan nata suka wuce gida.

Koda suka isa gidan sun tarar da mutanen gidan na cikin ɗaki domin yin sallah hakan yasa kayan kawai suka ajiye suma suka fara ƙoƙarin yin sallah.

Har lokacin jikin Nusram a sanyaye yake domin har zuwa yanzu sautin muryar shi be bar kunnuwan ta ba, haka tayi sallah sannan suka zauna lissafi.

Sai da suka fitar da komai sannan wani yaro ya shigo yana faɗin ana sallama da ƴan biyu, Nusram tace; "Rim tashi kije kina jin abinda yaron nan ya faɗa".

Dole tasa Nusreen wacce har yanzu bakin ta ya gagara buɗewa kamar da ta miƙe tana jan tsaki ta ɗauki hijab tayi waje.

Kamar yadda ta zata kuwa sune dai a tsaye cike da jin haushi ta ƙarasa wajen su, Shureim kuwa babu abinda yake yi banda kallon ta yana jin wani farin ciki a cikin zuciyar shi.

Naufal kuwa dama drama ɗin su yasa ya biyo abokin nashi dan haka tun fitowar ta ya fara kunshe dariya dan yadda ta fito kawai zai tabbatar maka da babu wasa.

Ɓangaren Abdul kuwa yarinyar ta bashi mamaki sosai ga wanu haushin ta da yake ji a rayuwar shi ya tsani mace me tsiwa da hayaniya ko rawar kai, dalilin da yasa kenan yaji abin ya ɓata mishi rai sosai.

Fadil yace; "kai amma gaskiya sun haɗu wallahi daga gani ƴan biyu ne", Abdul yace; "suwa kenan?.

Fadil cikin mamaki yace; "kai wai baka lura dasu biyu bane?", Abdul cikin jin haushi dan yanzu ya fahimci dawa yake ko ince wacce yake nufi dan haka yaja bakin shi yayi shiru.

Haka Fadil ya cigaba da wani zuzuta kyawun su yayin da Abdul yake ji kamar ya kwashe shi da mari.

"wai kai me yasa kake mini hakane yarinyar da babu abinda ta iya sai tsiwa shine zaka wani dame mu da maganar ta idan son ta kake ai sai kaje ka aure ta, mtseww yarinyar ƙarama sai rainin wayo".

Fadil yace; "ai kai kayi mata laifi ya kamata ace ka ɗauki duk wani abu da yazo daga gare ta wai kai baka lura da tsananin kyawun da take dashi ba, ai wallahi da ace zan sami kalar ta na auro ta a nan familyn to da sai na ɗinga ɗaga kai domin kuwa na san na sami mace me kyau".

Abdul yaja wani tsakin sannan yace; da alamu ka samu taɓin hankali, ai wannan ba wata me kyau bace abu mummuna da ita ka wani dage sai koɗata kake yi ai wallahi ka cuci familyn mu daka haɗa su da ita".

Fadil yace; "ai kuwa kaf familyn mu babu me nuna mata kyau bayan kai dan dai baka tsaya ka kalle ta da kyau bane".

Cikin sauri Abdul yace: "dan Allah na gaji da jin wa'innan shirmen kazo muje muyi alwala mu wuce muyi sallah", haka dole Fadil yaja bakin shi ya tsuke.

Nusreen kuwa sai da ta bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya tana yatsina fuska, dama ga haushin waccen daya gama raina mata wayo ya kuma hana ta fitar da abinda ke ranta ga kuma wannan ɗan anacen da yake neman takurawa rayuwar ta.


#LIKE
#SHARE
#COMMENT
#VOTE

@ wattpad_ 13 deeja.


*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.



♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖15-16📖📖



shureim yace; "barka da wannan lokacin gimbiyar mata", Nusreen tayi mishi wani kallo sannan tace; "wai kai meye matsalar ka ne dani?".

Yayi murmushi sannan yace; "ni kuwa nake da matsala dake, tun daga lokacin da muka yi wannan haɗuwar har yanzu ban kuma samin kwanciyar hankali ba kullum da tunanin ki nake kwana nake tashi ki taimaki bawan Allah ki amshe shi hannu biyu dan Allah".

Mamaki ya hana Nusreen magana, lallai ma wannan ya raina ta cab, cikin masifa tace; "au sakar maka fuskar da nake yi har yasa ka fara tunanin tara ta da wannan maganar lallai ma dole na ɗauki mataki akan ka".

Shureim ya kalli Naufal dake faman ƙunshe dariya yace; "Naufal ka dena irin haka ma ya ana maganar rayuwa ta kai kuma kana faman dariya".

Naufal yace; "yi haƙuri, amm ƴan mata ki daure ki bashi dama akan laifin da yayi miki ya samu damar gyarawa, dan Allah ki amsa mishi kada hakan ya zama matsala a rayuwar shi".

Nusreen tace; "ai rayuwar shi ba'a hannu na take ba dan da a hannu na take da sai na bashi idan yaso ya dauwama a duniyar".

Naufal yace; "yanzu dai ba wannan maganar ba yayi miki laifi kiyi haƙuri kinji, ki amshi ƙoƙon barar shi ko ya samu sauƙi na abinda yake damun shi".

Nusreen ta yamutsa fuska tace; "sai nayi tunani akai", sosai Shureim yaji daɗin hakan.

"to yanzu ya sunan ƙanwar tawa?", Naufal ya tambaya, sai da Nusreen ta harare shi ta ƙasan ido sannan tace; "Nusreen".

Cike da shauƙi Shureim ya sake maimaita sunan; "Nusreen! Nice name", Nusreen tace; "bari na tafi kawai gida kada Baba na yazo ya same ni a nan".

Tana faɗin haka tayi shigewar ta gida, Shureim kuwa kamar ya ɗaga Naufal sama haka ya dinga ji.

Naufal yace; "ka bari mana har sai ta amsa", Shureim yace; "wallahi naji daɗi sosai", haka suka tafi cike da farin ciki.

Tana shiga ta tarar da Nusram na harhaɗa kayan da suka amso daga Tudun Nufawar, Nusram tace; "har kin dawo kenan?".

Nusreen ta bata amsa tana me zama gefen katifar su tace; "eh har na dawo ban daɗe ba ko".

Bata bata amsa ba sai da mai da komai inda yake sannan tazo ta zauna kusa da ita tace; "Rim faɗa mini gaskiya waye yazo".

Nusreen tace; "ina wannan wanda ya taɓa watsa mini ruwa har yace maman shi zai kai Airport", Nusram ta ɗaga kai alamar ta gane.

Nusreen ta cigaba da cewa; "to shine yazo wai yana so na", Nusram farin ciki ya lulluɓe ta tace; "Alhamdulillahi ashe dai kema kina da rabon yin aure, Rim dan Allah kada ki dakatar da wannan domin kuwa tun lokacin da muka haɗu na lura yana da tarbiya sosai".

Nusreen tayi murmushi sannan tace; "amma kin san duk son da nakewa ɗa namiji ba zan taɓa aminta dashi ba har sai kema kin samu naki ko?".

Jikin Nusram a sanyaye tace; "Rim kada muyi haka dake idan kuma Alƙah ya ƙaddara ba zan taɓa yin aure ba fa?".

Nusreen tace; "nima shikenan ba zan yi ba", Nusram ta riƙo hannun ta cikin alamar lallashi tace; "dan Allah ki daure ki janye wannan maganar taki domin kuwa zaki ɗaura mini laifin da bazan iya kare kaina ba a wajen Allah, kiyi haƙuri ki tsaida miji kiyi aure".

Nusreen ta taɓe baki tana me miƙewa tace; "ba zan taɓa canzawa ba Ram, kuma ina nan akan baka ta har sai ranar da kika sami miji sannan nima zan tsaida mijin aure na", tana gama faɗin haka ta fice daga ɗakin.

Nusram ta buga uban tagumi tana me tunanin halin ta da halin da ta tsinci kanta, Ummi dake tsaye saman kanta, ta dafa ta tace; "Nusram ki dena damuwa kowa da kika gani da tashi ƙaddarar".

Nusram cikin jimami tace; "Ummi da ace ina da wanda ya taɓa cewa yana sona yau dana fito dashi a matsayin miji ko dan Nusreen, Ummi ko Nusreen bata faɗa mink ba na san cewa ba zata taɓa canzawa ba akan abinda ta faɗa, sannan bana so tayi asarar wannan mutumin domin kuwa daga ganin shi yana da nagarta kuma zai iya jurewa halin ta, sai dai kash babu wanda ya taɓa furta kalmar so a gare ni".

Ummi cikin tausayin ƴar tata tace; "kada ki damu ki miƙawa Allah lamuran ki shine kawai wanda zai iya share miki hawayen ki".

Ranar haka Nusram ta kwana cike da zullumi da tunanin mafita, yayin da Ummi ta kwana tausayin ƴar tata ganin halin da take ciki.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

Yana zaune ya tasa laptop a gaba sai faman shagwaɓa yake zubawa da alamu dai waya yake yi shida Brr Farida domin yadda yake yi kaɗai zai nunar maka da hakan, Fadil kuwa in banda dariya babu abinda yake yi.

Abdul ya ɗago ya dalla mishi harara sannan ya cigaba da amsa wayar shi, "First Love ki bari dan Allah su fara zaɓa idan yaso wacce suka bar mini ina son ta a haka".

Brr Farida tace; "shikenan tunda haka kace amma ka sani ko bata yi maka ba tunda kai kaso haka zaka amsa".

Ya ɗaga kai alamar ya yarda, Brr Farida tace; "nayi kewar ka sosai yaushe zaka dawo ne?", ya shafa sumar kan shi yana murmushi yace; "nan da kwana uku".

Sosai Brr Farida ta ɓata rai sannan tace; "wai kai me kake samu daga wannan gidan ne da ka nace shi kake son zaman cikin shi duk irin yadda ƴan gidan suke nuna maka ƙiyayya".

"yaushe Daddy zai dawo ne, yace mini gobe amma kuma banga alamun hakan ba", ya faɗa cikin son kaudar da waccen maganar.

Sanin halin ɗan nata yasa tace; "eh yace sai nan da sati me zuwa idan Alƙah ya kaimu, nima ina so naje Dubai saboda kayan hannu na ya ƙare".

"kai First Love yanzu sai kiyi tafiya ki barni gaskiya zan biki", ya faɗa cikin shagwaɓe fuska, tayi murmushi tace; "idan ka dawo daga nan ɗin ba idan kuma baka dawo ba yaro sai dai kaji na wuce".

Ya noƙe kafaɗa yace; "idan kika tafi ni kuma sai inyi zama na a nan gidan in ƙi dawowa", Brr Farida tayi dariya tace; "in dai Rigasa ne ai gaka ga ta nan da ƙafar ka zaka gudu domin yanzun ma dan Abban Husna baya ƙasar ne".

Shiru yayi shi yana mamakin yadda Maman shi ke sanin wasu abubuwan da yake faruwa a gidan koda ace bata nan, ya ɗan dafe kan shi yace; "bye Mum zan kwanta".

Tace; "ok shikenan sai da safe kada ka manta kayi addu'a kaji I love you", ya bata amsa da "love you too", ya katse kiran.

Ta baya ya faɗa saman gadon kanshi na kallon sama, tunanin rayuwar su yake yi yana kuma mamakin wasu abubuwan gashi idan zai kwana yana tambayar Maman shi ba zata bashi amsar da yake so ba kuma shi ya san tabbas akwai wani abin.

"Kana tunani akanta kamar yadda nake yi?", muryar Fadil kenan yayinda ya katse mishi tunanin shi.

Abdul yace; "waye kenan?", Fadil yace; "wacce muka haɗu ɗazu mana, gaskiya yarinyar ta haɗu wallahi".

"just shut up", ya faɗa cikin fushi, ina cikin farin ciki zaka lalata mini da wani zancen banza".

Fadil yayi murmushi yace; "Allah ka sake tunani, wallahi yarinyar zaku dace sosai barin ma ɗayar dan naga ita tana da hankali sosai kuma itama wannan ɗin banga wani aibunta ba", jin shiru ya tabbatar masa da idan zai kwana yana magana ba zai amsa mishi ba hakan yasa yaja bakin shi yayi shiru.

Abdul kuwa sai da ya tabbatar da yayi addu'a sosai sannan ya gyara kwanciyar shi domin yin barci wanda kuwa be jima ba barcin ya ɗauke shi.

Washe gari da wuri suka tashi domin zuwa ƙwallo ta ƙaddara, sai dai sauƙin ta a cikin estate ɗin suka buga.

Suna ƙoƙarin shiga Brr Hauwa na ƙoƙarin fitowa, dan haka cikin sauri ya kauce ya bata hanya, ta mishi wani kallo sannan taja tsaki ta wuce.

Hakan be wani dame shi ba domin ya riga ya saba da halin na ƙanwar mahaifin nashi, wacce yake mamakin abinda yasa bata ƙaunar shi.

A kan dinning suka tarar da sauran, dan haka suma zama kawai suka yi, Husna ta jefa mishi wani kallo sannan tace; "Ina kwana".

Ko kallon inda take beyi ba hakan ba ƙaramin bata haushi yayi ba amma haka ta daure ta miƙe a ƙoƙarin ta na haɗa mishi abin kari.

"am ok", abinda ya faɗa kenan yana ƙoƙarin miƙewa, Hajja tace; "kai bana son iskanci koma ka zauna kaci abinci".

"Hajja nifa ba yanzu zanyi break fast ba", ya bata amsa, cikin ƙasaita ta kuma cewa; "ba wannan na tambaye ka ba, umarni na baka".

"haba Hajja tunda yace ba zai ci ba ki ƙyaƙe shi man........", cikin ƙaraji Hajja tace; "ke kuma waye ya saka bakin ki a ciki ƙaramar alhaki, ki sani idan ina sha'anin ƴaƴa na bana buƙatar bare ya saka mini baki".

Fadila ta kalli Malama wacce fuskar ta ke ɗauke da damuwa tace; "kiyi haƙuri bada wata manufa na faɗa ba", tana gama faɗin haka ta miƙe ta bar wajen.

Abdul kuwa dan dole ya koma ya zauna, sai da ya harari Husna sannan yace; "serve me", jikin ta har rawa yake wajen zuba mishi.

Sai da Hajja taga ya fara cin abincin sannan ta bar wajen, yana ganin ta shige ɓangaren ta yaja tsaki yana kauda abincin.

Husna tace; "Yaya ai baka ci komai ba", ya balla mata harara sannan yace; "duk ranar da kika kuma gigin shiga rayuwa ta sai na kusan sumar dake banza mara hankali".

Husna ta cuno baki, Saleema tayi sallama ta shigo, jikin ta sanye da riga da wando pakistan sai hannun dake riƙe da rigar lapcoat ɗayar kuma tana riƙe da kula.

Tayi kyau sosai ga kuma murmushin daya kuma ƙawata fuskar tata, tunda ta shigo idanun ta ke kanshi tana me ƙara washe baki.

Yayi mata kyau sosai dan yana sanye da wando fari ne da riga blue kanshi kuwa yayi combing ɗin shi hakan yasa gashin ya kwanta sosai.

Shima kuwa da murmushin ya bita, har kusa dashi ta ƙaraso, Fadil da Fadila suka gaishe da ita, ita kuma ta gaishe da Malama.

Malama ta amsa tana me tashi ta bar musu wajen, Sayyada ma ta gaishe da ita ita kuwa Husna gefe ta kalla tana me sakin tsaki ƙasa-ƙasa.

Murmushi suka kuma sakarwa juna sannan tace; "ina kwana", ya ɗan sosa kai yace; "lafiya lau, har kin shirya".

Sai da ta juya idanu sannan tace; "eh har na fito na jira kazo breakfast baka zo ba shine na biyo ka dashi".

"am ok na riga naci abinci anan", sai da murmushin dake fuskar ta ya ɗauke cikin damuwa tace; "nifa da kaina na shiga kitchen na haɗa maka amma babu komai nasan maybe dan baka san zan maka bane".

Wani irin murmushi yayi wanda ya tafiyar da imanin su gaba ɗaya, shi kanshi yana jinjinawa haƙurin Auntyn tashi wannan kuma ke janyowa take matuƙar birge shi yana son mace me sanyin hali.

Saleema da take ji kamar ana ƙarawa zuciyar ta wutar son shi ta juya tace; "bari na wuce wajen aiki", tana faɗin haka ta fara tafiya.

Cikin sauri ya miƙe ya biyo bayan ta yana faɗin; "bari na raka ki", ya ƙarasa yana amsar jakar hannun ta.

Sosai Saleema taji daɗin hakan kuma ta san cewa yayi ne dan ya sanyaya mata rai na rashin cin abincin ta da beyi ba.

Husna kuwa kamar ta ɗora hannu a kai tayi ihu haka take ji yayin dasu Fadil suka kasa riƙe dariyar su sai da suka dara sosai.

Husna kuwa abin ya ƙara baƙanta ranta dan haka ta nufi ɗakin Hajja tana kuka, su kuwa suka cigaba da dariyar su.

Suna fita harabar gidan motar Abban su Fadil na shigowa, da sauri Saleema ta buɗe motar ta shiga yayin da shi kuma Abdul ɗin ya mika maya jakar tata.

Abba daya fito daga cikin tashi motar yabi motar ta da kallo yana girgiza kai, Abdul ya shafa kai sannan ya gaishe da Abban.

Cikin fara'a Abban ya amsa, hakan ba karamin daɗi Abdul ɗin yaji ba ganin yadda ɗan uwan mahaifin nashi ya sakar mishi fuska.

Haka ya riƙo hannun Abdul ɗin har cikin gidan, da gudu Fadil da Fadila suka yi wajen mahaifin su nan suka gaishe dashi ya amsa yana tambayar su ina wajen aikin ba, nan suka bashi amsa da yanzu zasu tafi.

"to ayi sauri a tafi bana son wasa da aiki", dole suka ƙarasa shiryawa da wuri suka fice, hannun shi cikin na Abdul suka shiga ɗakin Hajja.

Hajja tace" na rasa me dangin Malama suka baka da kake naniƙe muku kabi duk ka wani manne dasu, to ka sani su ɗin rabin ƴan uwan mahaifin ka ne".

Abdul ya saukar da kai ƙasa cike da kunya ga Abban su Fadil amma bata ji kunyar faɗin haka ba.

Abban Fadil kuwa yayi murmushi kawai idan da sabo yaci su saba da halin Hajjar; "ina kwana Hajja".

"mun tashi lafiya?", amsar data bashi kenan, beyi fushi ba yace; "lafiya lau", daga haka bata kuma cewa komai ba.

"bari na ƙarasa na gaishe da Malama, ga wannan a sa mana albarka", ya ciro ƴan dubu-duɓu ɗauri biyu ya ajiye a gaban ta.

Da ƙyar ta iya cewa; "an gode Allah yayi albarka", Abban Fadil ya amsa da Ameen yana me jinjina mulki irin na Hajja.

Yana miƙewa Abdul shima ya miƙe, Hajja tace; "to ɗan annace ina kuma zaka je?", kamar ba zai amsa ba sai kuma yace; "gidan Abba".

"wane Abban?", ta ƙara jefa mishi tambaya shifa ya fara gajiya dan haka a ɗan ƙarage yace; "Abban Kabeer", wani ɗan murmushi tayi sannan tace; "a dawo lafiya".

Har ya juya sai kuma ta kira shi, ba dan yaso ba ya juyo ya dawo, " yauwa ɗazu meya haɗa ka da ƴar uwar ka Husna".

Sai da yayi jim sannan yace; "meta ce miki?", Hajja cikin hasala tace; "ina tambayar ka kana tambaya ta?".

Yayi shiru be tanka ba, sanin cewa ba zai faɗa mata bane

Please Login or Register in order to submit comment