Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fatan anyi aikin cikin nasara?".

Shureim yace; "kinga ni ba wannan na tambaye ki ba waye wancan daya tafi yanzu?", Nusram ta koma yin dariya sannan tace; "baka gane ni ba ko? To ni ba Nusreen bace ƴar uwar Nusreen ɗin ce dai Nusram".

Wayyo! Ji yayi kamar ƙasa ta tsage ya shige, shifa tsabar kishi ya manta cewa su ƴan biyu ne, ya shafa kai yace; "ayya! Wallahi na ɗauka itace, aikin kam anyi shi sai dai mu jira sakamako kawai".

Tace; "to Allah yasa muji alkhairi bari na kira maka Nusreen ɗin", tana faɗin haka ta juya ta tafi.

Naufal ya kalli Shureim yace; "wallahi yau Allah ya taimake ka amma daba haka ba yau da babu me kwatar ka sai Allah kai da ba'a gama amicewa da kai ba amma har ka sami bakin tuhuma Allah ya soka".

Shureim yayi murmushi yace; "Allah sarki baiwar Allah, me kyawun hali ga hankali", cikin tsokana Naufal yace; "to kodai ita zaka komawa ne?", Shureim ya harare shi.

Nusram kuwa ganin saurayin ƴar uwar nata ya ɗan rage mata damuwa kaɗan don haka da ƴar ƙarfin gwiwar ta ta shiga gidan.

Nusreen na zaune Kubra na saman ƙafar ta yayin da take shafa mata magani Ummi kuma na gefe suna fira.

Da sallama ta shiga kafin ta zauna kusa da ƴar uwar tata cikin farin ciki ta kalle ta tace; "yauwa Rim kawo Kubrar na ƙarasa shafa mata maganin kije waje kina da baƙo".

Nusreen ta washe baki domin kuwa ta san Alƙah ne ya taimake ta har Nusram ɗin ta sauko ta san zuwan mutum ɗaya ne zai dawo da walwalar ƴar uwar tata amma duk da haka cikin salon tsokana tace; "waye kuma?".

Nusram tace; "waye kuwa banda Shureim yana nan a waje dan Allah tashi kije kada ya gaji da jira", Nusreen ta taɓe baki ita ta rasa me yasa ƴar uwar tata ke sonta da Shureim ɗin.

Nusram ta miƙo mata hijab wanda yake a linke tace; "amsa ki saka tashi maza kije", to ya zata yi da naciyar Nusram ɗin gashi tunda ta lura Nusram ɗin na son ta dashi take ganin zata iya amsa mishi.

Amsa tayi ta saka sannan ta yiwa Ummi sallama ta fita, Nusram tace; "yauwa Rim a dawo lafiya", Nusreen ta girgiza kai tana dariya kawai.

Tana fita ta hango su yanzu sun dawo inda su Nusram suka zauna ɗazu domin nan babu hasken wata sai dai ta san su biyu ne kamar koda yaushe dan haka ta hade fuska domin janyowa kanta girma ta fara takawa zuwa inda suke.

Tunda ta fito Shureim ya zuba mata idanu kamar ya maida ta ciki haka yake ji, da sallama ta ƙaraso suka amsa mata sai da suka gaisa sannan Naufal yace; "munzo jin amsar mu ne me aka yanke?".

Nusreen ta dan yi jim sannan tace; "akwai alƙawari da na yiwa ƴar uwata zan jira ta har zuwa ta sami mijin aure dan haka idan kaima zaka iya haƙura zuwa lokacin shikenan".

Naufal yayi murmushi yace; "kafin ayi maganar aure ai za'a yi ta soyayya ko yanzu ita ta kawo mu", Nusreen tace; "tunda ƴar uwata tana sona dashi nima na amince ko dan farin cikin ta".

Naufal yace; "ah lallai mun gode sosai sai ki miƙa mana gaisuwa gare ta, lallai na jinjina mata kuma tayi mana ƙokari", Shureim yayi ajiyar zuciya yace; "Alhamdulillahi na gode sosai".

Naufal yace; "yanzu shikenan zamu sami Baba mu nemi izinin shi dan ya san da zaman mu", Nusreen tace; "shikenan", nan dai suka ɗan taɓa fira.

Suna daf da yin sallama Baban ya iso, da torch light ya haska su, ganin Nusreen yasa yace; "to ƴar banza yau kuma iskancin har ƙofar gida na?", Nusreen ta zumɓuro baki cike da jin haushi.

Su Shureim suka gaishe da Baban ya amsa sannan ya maida kallon shi kan Nusreen yace; "kin wuce kin bani waje ko kuwa?", ba dan ranta yaso ba tayi cikin gida.

Baba ya kalli Shureim yace; "ku kuke lalata mini yara ko?", Shureim ya girgiza kai yace; "a'a Baba", Naufal ya ɗora da cewa; "dama munzo neman amincewar tane kafin muzo neman izini wajen ka".

Baba yace; "su har wani neman izinin ta kuke yi?, waye yake sonta a cikin ku?", Naufal ya nuna Shureim.

Baba ya kalli shureim yace; "yaro ya sunan ka? Kuma wacce kake so a cikin su?", Shureim ya shafa kai yace; "Nusreen nake so kuma sunana Shureim".

Baba yayi murmushi yace; "Shureim in dai Nusreen ce na baka ita kaje ka turo magabanta ka kawai a tsaida rana bana so ta kai wata me zuwa a gida na".

Shureim da Naufal suka kalli juna, su dai tunda suke basu taɓa jin anyi aure haka ba, Naufal yace; "to shikenan Baba mun gode sai dai wani hanzari ba gudu ba, Mahaifin shi ya rasu sai Mahaifiyar shi, Mahaifiyar shi kuma bata ƙasar tana can ƙasar Syria za'a mata aikin ƙafa to muna neman alfarma a bamu dama har zuwa lokacin da zata dawo".

Baba yayi jim sannan yace; "shikenan Allah ya kaimu, kai fa idan har kana so zan iya baka ƴar uwar ta", Naufal ya girgiza kai yana faɗin; "a'a Baba ina da mata".

Baba yace; "to shikenan amma ƙofa a buɗe take idan har da wanda kake ganin zai iya auren ta to kawai ka turo mini shi koda babu akwati sadaki kawai ya isa kaima kuma kada ka takurawa kanka", Shureim ya amsa da to.

Naufal ne ya matsa kusa da motar shi ya ɗauko rafas ɗin ƴan ɗari biyar-biyar ya haɗo da ƴar takarda, biron dake jikin aljihun rigar Shureim ya zara sannan yayi rubutu ya haɗa ya miƙawa Baba yace; "Baba ga wannan a saka mana albarka wannan kuma Number ɗin abokina ne dan Allah a bawa Nusreen ɗin ace ta kira shi dan Allah".

Baba ya washe baki yana faɗin; "ah lallai za'a je daku na gode sosai Allah yayi albarka insha Allahu ina shiga zan bata", ya amshe yana saka musu albarka, nan suka yi sallama ya shige gida su kuma suka tafi.

Ɓangaren Nusram kuwa tana gama shafawa Kubra magani ta ɗauketa ta kaita kan shinfiɗar ta, sannan itama taje tayo alwala tazo ta kwanta.

Abubuwan da suka faru yau su suka dawo mata cikin kai, haka harta gangaro kan zuwan ta kasuwa da bigeta da wannan bawan Allah yayi, dawowar ta gida zuwa ga matsalar Sahura, dukan da Baba yayi mata da magan-ganun da suka yi da Isa.

Tasa hannu ta share hawayen daya zubo mata, yanzu ina zata saka kanta?, gaskiya ko aure zata yi ba zata auri Isa ba sanin cewa ba wai zai iya riƙeta bane.

Ta miƙe ta zauna taja ajiyar zuciya tana ganin kawai gobe zata kai tallan kanta ne masallaci wanda ta yiwa sai yazo ya rufa mata asiri, to kina da tabbacin shi yana da hali me kyau?, abinda zuciyarta ta faɗa nata kenan.

Sai dai duk halin da take ciki bata so Nusreen ta rasa wannan saurayin domin tana ji a jikinta zai zamewa ƴar uwarta alkhairi.

Faɗuwar ƴar uwarta jikin ta ya katse mata tunani, Nusreen ta rungume ta tana dariya, Nusram ma cikin dabara ta goge hawayen fuskar ta.

Ta ɗago Nusreen tace; "Rimluv ban labari na sha meya faru", Nusreen tayi dariya tace; "Ram na amince da Shureim domin shima ya amince da sharadi na".

Nusram tace; "bangane ba? Wane sharaɗi?", Nusreen tayi fari tace; "sharaɗina mana na ba zai nemi aure na ba sai kin sami naki mijin".

Shiru Nusram tayi na ɗan lokaci kafin tace; " haba Rimluv wannan wane irin sharaɗi ne?, gaskiya ki janye", Nusreen ta miƙe tana taɓe baki tace; "babu abinda zan canza".

Har suka kwanta kowa da tunanin da yake yi, ita Nusram tunanin ta shine yadda zata nemo mafita akan abu biyu na farko shine matsalar ta da Isa na biyu kuma matsalar ta da Nusreen.

🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

Haka suka isa Mall ɗin cike da nishaɗi domin kuwa Abdul tunda suka rabu be kuma tuna abin ba, hakan yasa ya washe suka cigaba da farin cikin su.

Sai da suka yi siyayya sosai duk inda suka gifta kallon su ake cike da sha'awa, Saleema kuwa yau ji take komai ya warware mata kamar damuwarta ta ƙare gata ga abinda zuciyar ta ke muradi.

Shi yaja mata weelbasket ɗin ita kuma tana zaɓar abinda take so a haka har suka gama siyayyar sannan suka wuce park.

Ƙayataccen waje suka samu suka zauna inda masoya kan zauna domin fira da kuma jin daɗin soyayyar tasu.

Saleema tace; "Abdul ban san dalili ba amma yau naji kamar nafi kowa sa'a", yayi murmushi yana kashe ido ɗaya yace; "da gaske ko?".

Ta ɗaga kai tana ƙara jin son shi har cikin ranta, wayar shi ya zaro sannan ya danna kiran mahaifiyar tashi.

"Baby sai yau ka tuna dani ko?", ta faɗa tana dariya, Abdul ya shafa kai yace; "First love da safe ma munyi waya fa".

"baka san yadda nake ji bane da ko awa ɗaya ba zaka yi ba sai munyi waya, ina kewar ka sosai", ta ƙarasa da alamar damuwa.

Abdul yace; "nima nayi kewar ki Mom jibi zan dawo", Brr Farida tace; "taɓ ai kuwa gobe zan wuce Dubai", ya ƙwalalo idanu yace; "da gaske to gaskiya sai kin dawo zan dawo nima".

Brr Farida ta kalli Sumayya dake gefen ta tace; "to ai ga ƙanwar ka nan duk ta damu ka dawo", cikin sauri Sumayya ta amshi wayar daga hannun mahaifiyar ta.

"Yaya Abdul dan Allah ka dawo", ta faɗa cike da shagwaɓa, Abdul yayi murmushi yace; "sai idan Mum ta dawo kinji zan dawo kada ki damu nima nayi kewar ku sosai".

Sumayya ta noƙe kafaɗa tace; "ni dai ka yiwa Mummy magana gobe ta barni nazo wajen ka".

"shikenan zanyi mata magana nasan zata barki", Sumayya tayi ihun murna tace; "that's my lovely bro, bari na bata", ta faɗa tana miƙawa Brr Farida wacce ke faman hararar ta tunda taji ta ambaci zuwa wajen shi ta haɗe rai.

Tana amsa tace; "kada ma ka fara dan ba zan bari ba", Abdul ya shafa kai yana murmushi wanda Saleema ke ƙara ɗimaucewa duk da waya yake yi yayinda ita kuma ta zuba mishi idanu.

"Kai First love please ki barta dan Allah wallahi zan kula da ita", Brr Farida tace; "kaima ka san son da nake maka ba zaka taɓa neman abu na hanaka ba".

Yayi murmushi yace; "nagode my Mum", Brr Farida tace; "babu komai gobe driver zai kawota and please ka kula da ita soaai dan bana so wani abu ya sameta dan zaman ta kusa da Brr Hauwa barazana ne gare ni".

Abdul yace; "insha Allahu babu abinda zai same ta", nan suka yi sallama cike da ƙaunar juna.

Ya kalli Saleema yace; "Aunty muje gida ko?", tayi murmushi tace; "yadda kace Abdul", yace; "to taso muje", babu musu ta tashi suka tafi.

Abdul ya dubi Fadil da Fadila yace; "to ku kuma idan kun gama sai kuzo mu wuce", Fadil yayi dariya sannan suka miƙe.

Haka suka dawo gida cike farin ciki, sai da suka ajiye Saleema a gidan su sannan suka wuce.

Duka ɗakin Malama suka nufa, tana zaune saman sallaya dattijuwar akwai ibada koda yaushe cikin bautawa ubangiji take.

Fadila taje ta kwanta a jikin ta, Abdul ya kalle ta ya taɓe baki yace; "katuwar banza kawai", Fadil yayi dariya.

Abdul ya shiga bayi yayi Alwala sai da ya fito sannan Fadil shima ya shiga yayo tashi alwalar sannan suka tafi masallaci.

Basu shigo gida ba sai bayan isha'i dan haka direct dinning area suka nufa inda dama duk mutanen ɓangaren na zaune a wajen.

Suna zama Husna ta miƙe ta fara serving ɗinsu bece mata komai sai dai harara daya dalla mata.

Ita kuwa batama san yana yi ba, dan haka abincin kawai ta zuba ta turo mishi gaban shi yaja ya fara ci.

Koda ya gama tashi kawai yayi ya shige ɗakin Malama, Hajja tace; "wallahi ka fito daga ɗakin nan domin ba ita ta haifa mini Abubakar ba" kota kanta bebi ba.

Kan gadon Malama ya faɗa kawai ya gaji sosai hutawa yake buƙata, ya gyara kwanciyar shi yana me jan tsaki, gaskiya idan Daddy ya dawo aiki zai fara ya gaji".

Ya lumshe idanu fuskarta ta dawo mishi da sauri ya buɗe idanu, me kenan? Yarinyar da kwanaki ya ganta harta nemi tayi mishi tsiwa amma yau kuma ta canza hali koda yake dama mata ai canzawa suke kamar hawainiya".

Ƙara gyara kwanciya yayi kawai yana kawar da tunanin ta, a haka barci ya kwashe shi me cike da abubuwan mamaki.


#LIKE
#SHARE




♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖19-20📖📖

*MURAD* shine sunan dake mishi yawo a ƙwaƙwalwa, cikin tsakiyar daji yake masu dogayen bishiyoyo, babu abinda ke tashi a wajen sai wasu irin muryoyi cikin ɓacin rai da hargitsi suke ƙwala wannan kiran.

Yasa hannu biyu ya toshe kunnuwan sa yana me tsugunawa a wajen, jikin shi sharkaf da zufa cikin ƙanƙanin lokaci numfashin shi ya fara sama-sama wanda a dai-dai wannan lokacin Malama ta ɗago shi a tsorace tana kiran sunan shi.

Kamar wanda aka jefa rami ko rijiya me zurfi haka numfashin shi ya dawo, cikin tashin hankali da kiɗima ya buɗe idanun shi, Malama ke zaune tana tofa mishi addu'o'i gefen ta kuwa Fadila ce da Fadil duka idanun su na kanshi.

A hankali numfashin shi ya dai-daita sannan idanun shi suka buɗe gaba ɗaya, kamar wanda aka watsawa ruwa haka jikin shi ya jiƙe sharkaf da zufa.

Ganin ya dawo hayyacin shi yasa Malama cewa; "ka dena wasa da addu'a, ya zaka zo ka kwanta barci ba tare da kayi addu'a ba idan wani abu ya same ka fa ina kake so na saka rayuwa ta".

Duka suka bita da idanu suna mamakin furucin ta, ganin kallon da suke mata ne ya tunatar da ita meta faɗa dan haka cikin sauri ta riƙo hannun Abdul tace; "bana da abinda zan faɗawa Kakarka da mahaifiyar ka don haka ka kiyaye", jinjina kai kawai yayi sannan ya fara ƙoƙarin miƙewa.

Fadil yazo ya taimaka mishi har ya dai-daita a tsaye sannan suka yi musu sai da safe suka fice.

Koda suka koma nasu ɗakin sai da yayi alwala sannan ya kwanta, yana kwanciya wayar shi nayin ƙara.

Ganin wake kiran shi kuma baya son ɗaga mata hankali dan ya san har yanzu ba wai ya gama dawowa dai-dai bane dan haka ya maida wayar silent kawai ya koma barcin shi.

Washe gari, da safe sai da suka shirya tukunna suka fito zuwa falo, akan dinning kamar kowanne lokaci suka same su, sanin halin Hajja yasa bema nufi kan dinning ɗin ba.

Daga saman kujera ya gaishe dasu ɗaya bayan ɗaya suka amsa mishi, Husna da tunda ya fito take kallon shi don yayi mata kyau sosai.

Jikin shi ƙananan kaya ne as usual, wando fari da riga blue gashin kanshi yasha gyara sosai, ƙafar shi sanye da slipper irin na maza shima kalar blue, babu abinda yake tashi a jikin shi banda ƙamshi.

"Ina kwana Yah Abdul", be ɗago ya kalle ta ba yace; "lafiya", sosai amsa gaisuwar ya ƙular da ita amma sai ta share kawai.

Sayyada kam babu ruwan ta hakan yasa gaisuwa sosai ke shiga tsakanin su har ya kan tsokane ta ma.

Bayan sun gama karin nasu kowa ya kama gaban shi, Fadil da Fadila suka wuce wajen aiki, Husna da Sayyada suka wuce makaranta, Hajja da Malama kuma falo suka dawo suka zauna saman kujeru.

Hajja ta saka glass ta ɗauki jarida ta fara karantawa yayinda malama kuma ke riƙe da husnul muslim tana karanta addu'o'i.

Abdul kuwa yana kwance ne idanun shi a lumshe, a haka zaka zata barci yake yi amma kuma idanun shi biyu.

Fuskar yarinyar jiya kawai yake gani, koda yayi ƙoƙarin kauda fuskar sai ya kasa hakan yasa ya ƙara gyara kwanciya kawai.

Babu jimawa sosai Brr Hauwa ta fito cikin riga ja iya gwiwa da wando baƙi jeans, kanta kuwa tayi rolling da ɓaƙin gyale yayinda ta sako ƙaton shade.

Dan kyau tana dashi kuma jikin ta baya nuna tsufanta domin macece me kwalliya, kan kujera ta ajiye jakar sannan ta zauna itama tana gaishe da Iyayen nata.

Wayar Abdul tayi ƙara hakan yasa ya buɗe idanun shi sannan ya buɗe idanu, a hankali ya zaro wayar ganin me kiran ya sashi sakin murmushi kafin ya ɗaga.

"Morning mom", daga can ɓangaren tace; "morning Baby ya ka tashi?", ya ɗan shafa kanshi sannan yace; "yadda kika tashi haka na tashi mama na".

Tayi murmushi tace; "jiya na kira ka but u didn't pick d call hope kana lafiya dai ko?", lafiya ta lau kawai at dat time nayi barci ne kuma ban duba call logs ɗina ba yau da safe sorry".

"Never mind, yanzu zan wuce airport ga Sumayya nan yanzu driver zai kawo ta ita da Adnan sannan idan na fita zan maka transfer na kuɗi domin bana so kan na dawo kuɗin hannun ka su ƙare kazo kana complain".

"ba zan yi complain ba Mom kawai ki bari akwai enough kuɗi a waje na", cikin basarwa tace; "mun canza shawara inaji idan na gama abinda nake yi zan wuce England wajen Daddyn ku kawai sai mu taho tare dashi on monday".

Abdul yace; "hakan ma yayi, zamu baro rigasa ranar lahadi kenan?", Brr Farida tace; "duk yadda kuka yi ma ya rage naku", yayi dariya kawai.

Itama dariyar tayi kafin tace; "bari na wuce sai ka sauka idan na saka sim zan nema ka bye bye I love you".

'Love you too, take care", ta amsa da insha Allah", daga haka suka katse wayar, yana me jin daɗi.

Brr Hauwa taja tsaki, Hajja da Malama dai babu abinda suka ce, Abdul yace; "Ina kwana?", kamar ba zata amsa ba sai kuma tace; "lafiya lau", daga haka ta miƙe ta fice.

Shima Abdul ya taɓe baki kafin ya miƙe ya fice, Gidan su Saleema ya nufa, kamar yadda ya zata duk sun fice daga gidan sai Muhibba itama tana shirin fita.

"ina zaki je?", tace; "zanje gidan su Nihal ne dan kaga nan babu kowa", ya ɗan shafa kanshi sannan yace; "fara taimaka mini da abinci tukunna", babu musu ta ajiye gyalen hannun ta tayi hanyar kitchen shi kuma ya zauna saman Sofa wacce take falon.

Babu jimawa ta fito hannun ta ɗauke da tray, yam balls da kunun gyada sai Fried egg da tea da kuma bread.

Sai da yayi bismillah sannan ya fara ci yayinda ita kuma Muhibba ta zauna tana zuba mishi idanu domin yanayin cin abinci ma abin kallo ne cike da natsuwa.

Sai da ya gama ta maida kayan sannan ta fito, yana gaba tana bin shi a baya ganin ya nufi hanyar fita daga Estate ɗin yasa tayi saurin tsayar dashi.

"Ya Abdul ina zaka ne?", sai da ya ɗan ja tsaki sai kuma yace; "akwai inda nake son zuwa ne", ta langaɓar da kai tace; "ko nazo na rakaka ne?".

"jeki inda zaki je kawai", yana faɗin haka ya cigaba da tafiyar shi, ganin hakan yasa Muhibba biyo shi da gudu, koda ta ƙarasa inda yake be kalle ta ba kawai ya cigaba da tafiya a haka har suka fice daga gidan.


🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸🔸

Nusram ta gama shirin ta hankali kwance, ganin tana da sauran lokaci dan yau sai bayan an sakko sallar juma'a zasu shiga makaranta.

Ta kalli Nusreen wacce ke kwance tana malelekuwa saman katifa kunnenta kare da waya tana amsawa cike da farin ciki.

Nusram ta taɓe baki tace; "kinibabbiya ana so ana kaiwa kasuwa", Nusreen tayi dariya tana juya idanu.

Nusram ta ɗora da cewa; "zan je in dawo yanzu ba zama zanyi ba munyi waya da Idris yace mu haɗu a Juny Caft, ko zaki je ne", Nusreen ta girgiza kai kawai.

Nusram ta juya ta fice tana faɗawa Ummi sai ta dawo, Ummi ta bita da adawo lafiya, kamar yadda suka shirya da Sahura akan zata fara yin gaba haka kuwa akayi.

A can saman layin nasu ta iske ta, Sahura ta bita da kallo itace ƙanwar su a ƙalla shekara biyar zuwa huɗu tsakanin su amma ba zata nunawa Nusram ɗin ƙuruciya ba.

Doguwar riga ta saka ta yadin rariya wacce aka yiwa ɗinkin gown ta buɗe sosai fari ne yadin da ɗige-ɗigen ruwan goro,hijab ɗin data saka kalar goro ne hakan ya ƙara haskaka kalar fatar ta.

Fuskar ta babu kwalliya sosai dan haka a washe take, sai lips ɗin ta data sakawa man baki kalar orange me ɗan turuwa sosai tayi kyau.

"muje mana idan kuma kallo na zaki tsaya yi to bismillah", Sahura tayi dariya kawai, me Keke Napep suka tare inda ya ɗauke su har can Sardauna crescent.

Sanda suka shiga caft ɗin yana zaune yana jiran su, koda ya gansu cikin farin ciki ya miƙe tsaye.

Baƙi ne amma kuma babu laifi yana da kyau, idan ka ganshi yaro ne ba wani babba ba, ga tsafta komai tsaf-tsaf hakan yasa Nusreen ke cewa ɗan daudu domin kuwa komai nashi a tsaftace yake harma yaso yafi wata macen ƙyale-ƙyale.

A mutunce suka gaisa, sannan Nusram tace; "Idris kayi haƙuri naji duk abinda ya faru daga bakin ta kuma nayi mata faɗa dan haka insha Allahu ba zata sake ba, kaga zaman a gida bashi da wani amfani ka daure ka maida matarka kawai".

Idris cikin girmamawa yace; "shikenan babu komai Aunty amma idan wani abu ya taso daga baya to gaskiya zan haƙura kawai".

Nusram tace; "insha Allahu babu abinda zai faru, zata kiyaye na gode sosai dan Allah anjima kazo sai ka ɗauke ta".

Idris yace; "shikenan ta shirya ɗin idan na dawo daga kasuwa saina biyo mu tafi amma ta sani wallahi mahaifiyar ta, idan ta faɗa mini mara daɗi tafiya ta zan yi".

Sahura tace; "ai bama sai ka shigo ba kana zuwa ka kira waya ta kawai zan fito", Idris ya

Please Login or Register in order to submit comment