Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ƙarasa tana ɗaukar Kubra kasancewar bata tafiya har lokacin.

Ummi na gaba Nusram tana bayan ta suka fito, zuwa wannan lokacin Mama Jummai da Amira harda Isa duk suna tsaye a waje.

Baba yace; "wai keda waye zaki tafi?", Ummi tace; "bangane ba, nida yarana mana", duka wajen suka kwashe da dariya, banda Nusram dake sharar hawaye.

Baba ya harare ta yace; "to ai dana auro ki ba tare dasu aka kawo ki ba", Ummi ta haɗe rai tace; "kamar yadda banzo na tarar dasu a nan gidan ba", daga haka ta nufo hanyar fita.

Baba ya saka hannu ya finciko Nusram yace; "wannan dai me kama da aljanun zaki iya tafiya da ita amma wannan kam babu inda zata je, ba zata gama ɓata yaran birni ba ta koma ƙauye ta ɓata na can, idan naje ana mini kallo arziƙi ta zubar mini da mutuncina ba".

Dan haushi Ummi bata ko juyo ba, jakar dake hannun Nusram ta fincike ta fice kawai, Nusram ta fashe da kuka tana kiran Ummin, amma bata juyo ba.

Baba ya rufe Nusram ɗin da duka yana faɗin; "shegiya ƴar iska, yanzu ke har kina da bakin ihu, ne baƙin jini kawai, ko karya takan sami karen da zai bita amma banda ke".

Nusram kuwa banda sunan Ummi babu abinda take ambata, babu wanda ya bawa Baba haƙuri har sai da ya gaji dan kanshi ya ƙyale ta.

bayan tafiyar shi Mama Jummai ta kwashe da dariya tace; "ai duk wanda yaja dani dole ya yi nadama, wato tunanin ki zaki je Dabai ki huta ko, to babu inda zaki je kina nan tare dani, aure kuma sai dai kiga anayi".

Isa ya ɓata rai yace; "kin manta Jummai nine fa zan aure ta", Mama Jummai tace; "ai auren ku da rashin shi duk ɗaya ne domin na rantse ba zata taɓa jin daɗin auren ta ba".

Suka kuma fashewa da dariya, Nusram kuwa hawaye kawai take yi har lokacin, ga ƙafarta dake zafi.

har wajen sha biyu tana tsugune a wajen, babu wanda ya tanka mata, sallamar Nusreen itace ta dawo da ita hayyacin ta.

Cikin sauri ta miƙe, Nusreen kuwa ganin halin da ƴar uwarta take yasa ta taho da sauri, Nusram ta ƙarasa kusa da ita suka rungume juna.

"Rim Ummi ta tafi ta barmu", jikin Nusreen a sanyaye ta janye Nusram ɗin daga jikinta tace; "me kike cewa ne?".

Nusram taja hannun Nusreen ɗin suka nufi ɗakin nasu, kan kujera ta zaunar da ita sannan ta bata labarin abinda ya faru.

Nusreen ta fashe da kuka, Nusram ma tana sharar hawaye tana rarrashin ƴar uwar tata.

"Ram haƙiƙa kina ganin rayuwa, kowa yana da tashi ƙaddarar ke kuma taki kenan, Nusram waye zai tunanin mahaifin daya haife mu shike bin mu da mugun baki", ta ƙarasa tana kuma fashewa da kuka.

Nusram tace; "kiyi haƙuri Rim kowa da yadda rayuwa take zuwar mishi, Nusreen Ummi bata a cikin gidan nan ya zanyi da rayuwa ta".

Nusreen ta share hawayen fuskarta kafin tace; "zan yiwa Hubby magana sai mu tafi tare dake idan yaso sai ki zauna a wajen Hajiya, kin san dama tana sonki sosai".

Nusram ta girgiza kai tace; "ba za'ayi haka ba, nifa jiya na sami wanda zai aure ni", cikin sauri Nusreen tace; "waye kenan?".

Nusram ta janyo wayar dake jakar ta sannan ta miƙawa Nusreen tace; "kalli kiga hoton shi", Nusreen ta zuba mishi idanu kafin tayi murmushi tace; "wannan ai Abdus-samad Abubakar Nagimi, ɗan attajirin me kuɗi ne ina kuka haɗu dashi".

nan Nusram ta kwashe duka labarin komai ta bawa Nusreen ɗin, Nusreen baɓu abinda take banda murmushi.

"baban shi shine ogan Hubby kafin ya rasu, mutumin kirki ne Nusram ba wai ɗan yankan kai bane, har bikin mu yazo fa", ta ƙarasa tana kwashewa da dariya tunawa da tayi da yadda Nusram ɗin ta dinga shirme, Nusram tayi murmushi kawai.

Sai lokacin ta lura da yadda Nusreen ɗin tayi ƴar ƙiba ga haske data ƙara, Nusram ta girgiza kai tace; "kinga yadda kika koma kuwa?", Nusreen tayi dariya.

Suna zaune wayar Nusreen ɗin tayi ƙara, ganin Aunty ke kira yasa ta ɗaga, nan ta bata labarin abinda ya faru.

"kada ki damu Maman ku ta kira ni ta faɗa mini komai gobe zan zo na tafi da Nusram ɗin", Abinda Aunty ta faɗa kenan.

Nusreen tace; "Allah ya kaimu shikenan Aunty sai anjima", daga haka suka katse wayar, nan ta bawa Nusram labarin abinda Aunty ta faɗa.

Nusram kuwa tagumi kawai tayi, tunani kala-kala shine cikin ranta, shin zai zo, ko kuwa zata cigaba da zama da Mama Jummai ne ko kuwa Aunty zata sami nasarar rabata da gidan?, wa'innan sune abinda ke kai kawo cikin ranta.

Abdus-samad dake zaune cikin office ɗin shi, ya dafe kai, ba zai ce ga dalilin daya saka lokaci zuwa lokaci abin yake faɗo mishi a rai ba.

Iska ya furzar daga bakin shi, be san yadda abubuwa zasu tafiyar mishi ba, amma dai tabbas yana ji a jikin shi wani abu zai faru dashi jin yadda gaban shi ke faɗuwa akai-akai.

Biyar ya bar company ɗin ya ɗauki hanyar hayin rigasa, be shiga cikin gidan ba, ɗakin Fadil kawai ya wuce.

Wanka yayi ya canza kaya kafin ya shiga ciki, babu kowa a falo hakan yasa ya wuce ɗakin Malama kawai.

Tana zaune da alƙur'ani a gabanta, ya saki murmushi matar tana birge shi saboda yawan bautar da take dashi.

Malama ta miƙo mishi hannu alamun ya taho, Abdul kuwa kamar dama abinda yake jira kenan dan haka cikin sauri ya nufi inda take.

Kan ƙafar ta ta kwantar da kanshi sannan ta saka hannu tana shafa gashin kanshi, dama ga damuwa tayi mishi yawa ga gajiya kuma dan haka babu jimawa barci ya ɗauke shi.

Malama ta tsurawa fuskar shi idanu, hawaye ya taru a idanun ta, ta fara karanto addu'a tana tofa mishi.

Cikin barci yaji ana jijjiga shi, ya buɗe idanu ganin Fadil yasa yaja tsaki, Fadil yayi dariya yace; "ka tashi malam shida tayi fa", jin abinda Fadil ya faɗa yasa yayi saurin miƙewa zaune.

"please taso muje ka rakani", abinda Abdus-samad ɗin ya faɗa kenan yana miƙewa, Fadil yace; "ina zaka je?", Abdul yace; "kai dai muje kawai".

A motar Fadil ɗin suka fice, suna tafe duk yadda Fadil ke tambayar shi inda zasu je be bashi amsa ba har suka ƙaraso ƙofar gidan.

Fadil ya kalli ƙofar gidan sannan ya juyo ya kalle shi yace; "har yanzu baka bani amsata ba", Abdul ya buɗe motar kawai ya fito.

Baba da Isa dake zaune saman dakalin ƙofar gidan suka bi su da idanu, Abdus-samad suka yi musu sallama suka amsa.

"amm dan Allah me gidan nan nake nema", Baba yace; "gani nan yaro ya akayi", Abdus-samad yace; "dama nazo ne muyi magana dan Allah idan babu damuwa".

Baba ya tashi ya bi shi suka dan matsa gaba, Baba ya kalle shi yace; "kai nake sauraro", Abdus-samad yace; "dama nazo akan maganar ƴar ka Nusram ne abinda ya far.......".

Yayi saurin dakatar dashi yace; "ba dai akan maganar Nusram kazo ba?", Abdus-samad ya jinjina kai, Baba ya kamo hannun shi yace; "muje".

Abdus-samad cike da mamaki yake bin shi, Baba ya kalli Isa yace; "tashi mu ƙarasa masallaci", Isa ya miƙe, haka Fadil ma ya biyo bayan su.

Masallacin dake kusa dasu suka ƙarasa, kasancewar lokacin sallah ya matso hakan yasa mutane keta alwala, dan haka Baba ma ya ɗauki buta.

Ya kalli Abdus-samad da Fadil dake tsaye yace; "bismillah mana kuyi alwala", cikin sauri duka suka ɗauki buta domin alwala, shi dai Abdul gaba ɗaya jikin shi a sanyaye yake.

Be gama girgiza ba sai da aka idar da sallah yaji Baba yana sanar da akwai ɗaurin aure dan Allah, ya matsa kusa da Liman suka ɗan tattauna sannan ya kalli Abdus-samad yace; "matso mana ɗan nan".

Abdul ya matso kusa da Baban, Liman yace; "menene sunan ka?", Abdul yace; "Abdus-samad Abubakar", gana nan yaga Baba ya ciro kuɗi daga aljihun shi ga miƙawa liman yace; "sadakin ma ni na biya dan Allah ɗaura kawai".


Kafin Abdul yayi dogon tunani yaji kawai Liman yana sanar da ɗaurin aure, ya kalli Baba ya kalli Liman ɗin da kuma maƙwabcin Baban wanda shine yake wakili ga ango, shi dai su suke kiɗan su suke rawar su.

*AN ƊAURA AUREN ABDUS-SAMAD ABUBAKAR TARE DA NUSRAM ABDULLAHI DABAI, AKAN SADAKI NERA DUBU GOMA SHA BIYAR LAKADAN BA AJALAN BA!!!* dogon bayanin dake yawo cikin ƙwaƙwalwar Abdus-samad kenan.

Cikin firgici da kuma razana ya ɗago yana kallon Baban yana girgiza kai, maida kallon shi yayi kan Fadil ɗin wanda yake zaune kamar gunki dan idan banda numfashi dake sauka babu yadda zaka fahimci akwai rai a jikin shi.


*To masu karatu, zan dakata anan saboda isowar Azumi idan Allah ya kaimu gobe da rai da lafiya dan haka ina taya kanmu murnar zuwan wannan wata me albarka Allah ya magance mana wannan babbar annoba da take damun mu wato Covid19, Allah yasa muga ƙarshen watan lafiya, idan Allah ya kaimu bayan sallah da rai da lafiya zamu ɗora daga inda muka tsaya*.

*godiya ta musamman gare ku, mabiya wannan littafin, irin su, Abdul Ƙiru, Ibnatu Baballe Barau, Maman Abdul, Aishatu Babayo, Faɗimatu, Khadija Zakariyya da duk sauran wa'inda ban.amabata ba na gode sosai Allah ya haɗa mu da rai da lafiya*.


*HAPPY RAMADAN IN ADVANCE*



#LIKE
#SHARE
#COMMENTS

*babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖51-52📖📖

Abdus-samad be dena zare idanu ba har aka watse daga masallacin, Liman ya ɗan taɓo shi sannan yayi firgigit ya miƙe tsaye.

"ku taimake ni kada ku ɗaura auren nan nifa ba soyayya muke da ita ba", abinda yake faɗa kenan.

Baba cikin fusata yace; "bangane abinda kake nufi ba ina dama kai kace maganar ta kazo mini, ni kuwa na san idan banda maganar auren ta babu abinda zai kawo saurayi waje na, ko kana cikin kwartayen ta ne?", Abdus-samad ya girgiza.

"amma baka fahimce ni ba, nifa maganar da nazo muyi daban taya zaku ɗaura mana aure babu sanin iyaye na?", Abdus-samad ya faɗa cikin damuwa.

Abba ya ɗaga kafaɗa yace; "wannan kuma matsalar kuce ni dai yanzu zata bar gidana idan yaso tunda baka sonta kaje ka kashe ta", wani abu Abdus-samad ya haɗiye jin abinda Mahaifin nata ya faɗa.

Liman yace; "ya isa haka, ku zauna ayi maganar data dace", duka suka sami waje suka zauna kamar yadda yace.

"kai menene ainihin abinda ya kawo ka wajen Malam Abdullahi?k, tambayar da liman ya jefowa Abdus-samad ɗin kenan.

Labarin komai ya kwashe ya faɗa mishi na yadda ya ganta zata gudu da yadda yayi mata magana akan gobe zai zo ya ɗora da cewa; "gani na mahaifin ta ne shi ba zai so ƴar shi ta bar gidan shi ba dole zai janye maganar aurar da ita kota yaya ne".

Liman ya jinjina kai yace; "tabbas yaro kana da gaskiya, Malam Abdullahi wato duk wani abu dake faruwa akan yaranka babu wanda bamu sani ba, shiru kawai muke yi saboda gudun katsalandan domin kuwa iyayen yanzu basu so ana musu irin wannan shisshigin Malam Abdullahi matsi da takura akan yaran yanzu daman irin abinda yake haifarwa kenan, yanzu baka gudun ace lokacin data tafi taje ta faɗawa abinda be kamata, gaskiya wannan abin sam be dace ba ka gyara ƴaƴa amanace Allah ya bamu kuma idan bamu riƙe su da kyau ba zamu fuskanci fushin shi dan haka ya kamata mu gyara tarbiyar yaran mu".

Sannan kai, ya faɗa yana juyowa ya kalli Abdus-samad; "sai dai kayi haƙuri aure dai ya riga da ya ɗauru amma tunda iyayen ka na nan zamu je sai ayi musu bayani".

Cikin sauri Abdus-samad yace; "a'a nima zan iya yi musu bayani da kaina, amma dan Allah ku raba auren nan".

Baba yace; "aifa sai dai duk abinda zai faru ya faru amma wallahi yau ta bar gidan nan, bari ma ku gani", ya miƙe tsaye sannan ya fice daga masallacin.

Duka suka bi shi da idanu kafin Liman ɗin ya kalli Abdus-samad yace; "haƙuri ya kamata kayi Abdus-samad kaga yarinyar nan tana ganin rayuwa a cikin gidan mahaifin ta, dan a dalilin rashin auren nata yau sai da mahaifiyar ta, ta bar gidan......" nan Liman ya bashi kaɗan daga cikin abinda ya sani wanda yarinyar take fuskanta.

Ya nuna kanshi yace; "ni nan da kaina ta kawo mini cigiyar miji kwana uku da suka wuce tana kuka tana roƙona to abinda yasa ma dan bana da ɗa namiji ne kuma matana huɗu amma da na tsame ta daga damuwar da take ciki, sai dai hakan be samu ba domin kuwa babu wanda ya amince saboda waccen abinda ya faru ranar auren ta, kayi haƙuri ka amshi auren nan domin kuwa wataƙila kai ne Allah ya turo domin ka taimake ta ka fitar da ita daga cikin ƙangin da take ciki shekara da shekaru, yarinya ce me haƙuri da sanyi zaka ji dadin zama da ita, dan Allah kada ka juya mata baya, laifi dai mun riga da munyi domin ya kamata ace mun tambaye ka kafin mu ɗaura auren sai dai ance kaddara ta riga fata, dan haka kayi haƙuri ka amshi auren nan hannu bibbiyu ina fata da kuma buri akan ba zaka yi dana sani ba.

Shi kanshi Abdus-samad zuwa yanzu jikin shi yayi sanyi a hankali ya kai kallon shi kan Fadil, Fadil ya jinjina mishi kai, Abdus-samad ya maida kallon shi kan Liman yace; "shikenan Baba Allah yasa hakan shi yafi alkhairi, zan yiwa iyaye na magana na san zasu fahimta".

Liman ya washe baki yace; "yauwa ɗana idan suka ƙi yarda ma kazo ka ɗauke ni ka kaini ni nan da kaina zan musu bayanin komai", Abdus-samad yace; "insha Allahu".

"Allah yayi muku albarka dai yanzu tashi muje ya fito muku da matar taka sai ku tafi ko?", duka suka miƙe suka bishi.

Yana gaba suna baya har ƙofar gidan Malam Abdullahi, Abdus-samad dai gaban shi banda faɗuwa babu abinda yake yi, sai saƙe-saƙe yake yi.

Cikin gidan kuwa Nusram da Nusreen ke fira duk da ba wata me yawa bace yawanci labarin abinda ya shafi rayuwar su suke yi, sai kuma jimamin abinda ya faru.

Ganin duhu ya fara yi yasa Nusram ta kalli Nusreen tace; "wai ba zaki tafi gida bane?", Nusreen tayi murmushi tace; "ai jira nake Hubby yazo sai mu tafi".

Nusram ta buɗe baki zata yi magana taji sallamar Baba, jin yana ƙwala mata kira yasa gabanta faɗuwa.

Ta kalli Nusreen tace; "Allah yasa lafiya", kafin Nusreen tace wani abu ya ɗago labulen ɗakin ya shigo".

"kaga mini ƴar banza ashe kinajina kika yi shiru, to maza tashi ki shirya mijin ki na waje yana jiran ki".

Mama Jummai dake bayan shi jin abinda ya faɗa yasa tayi shewa tare da yin guɗa, "Lallai ma, amma dai Abdullahi wasa kake yi ko?".

"wasa! An taɓa wasa da aure ne?, kinga kada ki ɓatawa mutane rai ki shirya maza ki fito", daga haka ya juya ya fita.

Mama Jummai ta ja tsaki tace; "wallahi da sake matuƙar angon be gamshe ni ba dole a canza wannan abin", ta fice fuuuu.

Su dai cikin.su babu wanda yayi magana, Nusram ta fashe da kuka, Nusreen tayi saurin riƙota tace; "dan Allah kiyi haƙuri ki dena zubar da hawayen ki haka, ina ji a jikina wannan auren naki alkhairi ne".

Nusram ta girgiza kai hawaye yana zubo mata tace; "Nusreen komai na rayuwata ya canza, babu farinciki babu karatun da nake matuƙar ƙauna babu mahaifiya wacce take kula dani".

Nusreen ta dafata tace; "ki kwantar da hankalin ki ƴar uwata, kowa da yadda rayuwa take zuwar mishi, sannan idan kuma yayi haƙuri sai ki gani wata rana kamar ba'a yi ba".

Nusram dai tayi shiru kawai, Nusreen ta riƙo hannun ta tace; "tashi ki shirya, ki dinga addu'a Allah yasa ƙarshen wahalar ki kenan", ba dan taso ba ta miƙe.

Ruwan da Nusram ɗin ta ɗora bayan ta gama yi musu abinci shi ta juyewa mata, sannan ta koma ta faɗa mata.

Babu yadda ta iya haka ta nufi hanyar bayi, ita kuma Nusreen ta fara shirya mata kayanta, ita harga Allah tana jin matsalar ƴar uwarta yazo ƙarshe kenan insha Allahu.

Tana gamawa Shureim ya kirata a waya kan gashinan zuwa ɗaukar ta, ta amsa da to, koda Nusram ta fito a wajen ta sami Mama Jummai da Isa harda Ameera duk sunyi cirko-cirko.

"ni wallahi Jummai banso wannan auren ba, hakan nan sai naga samu naga rashi", faɗar Isa kenan.

Mama Jummai tace; "kada ka damu nan babu jimawa zaka ƙara gani ta dawo gidan nan wannan karan bama ita kaɗai ba har waccen da take firirita kamar kazar mayu".

Ameera taja tsaki tace; "ni duk haushi ya ishe ni wallahi, amma komai zai zo ƙarshe ne", Mama Jummai tace; "insha Allahu".

Ba tare da Nusram ta kula su ba ta ajiye bokitin ta shige ɗaki inda ta tarar da Nusreen na zaman jiranta.

Doguwar riga ta shadda ta saka kalar ruwan bula me haske, sai farin hijab, duk yadda Nusreen tayi da ita akan ta tsaya tayi kwalliya ƙi tayi dan haka dole ta ƙyale ta, hoda da man baki kawai ta goga kaɗan.

Ƴan kunne da sarƙa ta maƙala kafin ta juyo ta kalli Nusreen tace; "Rim gabana sai faɗuwa yake yi", Nusreen ta riƙo hannunta tace; "ni kuwa zan so ace kin daure kodan maƙiya da suke so suga ya zaki yi".

Ta miƙa mata ƴar ƙaramar jaka kalar kayan jikinta, ta ɗauko turare ta feshe ta dashi sannan tayi murmushi tace; "muje Amarya", kamar me tsoron tafiyar haka ta fara takawa.

Sai da suka fito falo kafin Nusreen ta ajiye mata takalmi me tudu ta saka, Nusreen ta ɗaukar mata duk wani abu da ta san zata buƙata ta saka cikin ƙatuwar Trolley bag ta ɗauka.

Suna fitowa tsakar gida Nusreen ta rangaɗa buɗa, Mama Jummai taja dogon tsaki, Nusreen kuwa ƙara sakin wata buɗar tayi ta ciri turare tana kuma fesa mata.

Har zasu fice Baba yace; "to sarakan zumuɗi an kwana biyu ba'a sami namijin da za'a ɓata ba shine yanzu har sauri kuke yi ko to ai sai ki dawo".

Nusreen ta juya tana zumɓurar baki, Nusram kuwa wajen Baban ta nufa, yace; "wajen Mamanki zaki je gata can a tsaye".

Nusreen data kusa ficewa daga gidan ta juyo tace; "a'a Baba ba sai taje wajen ta ba, ai na riga nayi mata faɗan da Uwa ke yiwa ƴarta".

Baɓa ya ɗauki takalmin dake kusa dashi ya jefa mata, da sauri tayi waje tana janye da jakar Nusram ɗin.

Koda ta fita sai da gaban Abdus-samad ya faɗi, Shureim yayi saurin taro ta ya amshi jakar.

ta juyo sannan tace; "ina angon yazo ya buɗe mana booth", Fadil dake tsaye yayi saurin zuwa ya buɗe mata Booth ɗin ta saka.

"yanzu ina zaki je?", Shureim ya faɗa ganin zata koma gida, ta kalle shi tace; "Hubby zan shiga ne ciki zan fito babu jimawa", daga haka ta shige.

"to kina dai gani da ƙyar kika samu wanda ya aure ki, shima ana bashi yana ƙin amsa da ƙyar aka shawo kanshi dan haka kada naji kada na gani, idan kika sake kika kashe wannan auren sai dai ki nemi wani uban ba dai ni ba", abinda Baba ya faɗa kenan kafin ya miƙe.

Nusram kuwa hawaye kawai take yi, wai shima ana bashi yana ƙin amsa, ita kuma haka take da baƙin jini🙆.

"tashi mana muje suna jiran ki", jin hakan yasa ta miƙe, suna zuwa zasu fita Nusreen na shigowa, ta riƙo hannun ƴar uwar tata kafin suka fice, Mama Jummai da Ameera da Isa suna bin su a baya.

Fadil na cikin mota a zaune, Shureim kuma yana jingine da motar yayinda nesa kaɗan Abdus-samad ke tsaye tare da Liman suna magana.

Suna fitowa waje, Nusreen ta rangaɗa buɗa Mama Jummai ta wulla mata harara, ta turo baki tace; "tunda ke ba zaki yi mana kara ba ai sai.muyi da kanmu", ta sake rangaɗa wata guɗar, hakan shine ya janyo hankalin Maƙwabtan nasu.

Fadil kam ji yake kamar wasa wai Abdul da mata, gashi har yanzu basu samu damar yin magana ba balle yaji taya akayi hakan ta kasance.

shi ya buɗe motar Nusreen ta riƙe hannun ƴar uwarta, sai lokacin Nusram ta samu hawaye suka zubo mata, rungume ƴar uwarta tayi suka fashe da kuka.

Baba dake tsaye bayan su ya ja tsaki yace; "wannan kuma wane sabon iskanci ne, dallah saketa su tafi kuna ta faman ɓata musu lokaci".

Nusreen ta saki Nusram tayi murmushi tace; "kada ki damu ƴar uwata ina ji a jikina ƙarshen wahalarki kenan?", Nusram ta jinjina kai.

Abdus-samad ya dafe kai, wannan wane irin ƙaddara ce, ya kuma kallon su ya ɗan taɓe baki sai faman ƙanƙame juna suke yi.

Baba yazo ya fincike hannun Nusram sannan ya sakata a mota, Nusreen ta zumɓuro baki, Baba ya harare ta yace; "kema wuce ki tafi gidan mijin ki".

Daga haka Baba ya kaɗa kai yayi gida, Liman ne ma ya ɗan ƙara yiwa Abdus-samad ɗin nasiha kafin su tafi.

Nan suka yi sallama da Shureim

Please Login or Register in order to submit comment