Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"ke ina Idris ɗin?", Sahura tayi dariya tace; "yana nan mana amma mun canza shawara sai gobe zai zo domin yace yana so na ɗan gyara kafin na koma".

Nusram tayi dariya tace; "ah lallai kace sababbin ango da amarya kuke kenan?", duka suka kuma yin dariya.

Sahura tace; "dan Allah gobe idan baki da ayyuka masu yawa sai ki yi mini ƙunshi da kitson ko?", Nusram tace; "shikenan Allah ya kaimu amma kuɗin dubu biyar", Sahura ta riƙe haɓa tace; "ai wannan tsakanin ke da ƙanin ki", Nusram ta harare ta tace; "kinji wani daɗin baki".

Nusram ta kuma cewa; "amma ya kamata a yau ki faɗawa Baba da Mama kada su ga kawai kin bi mijin ki gobe", Sahura tace; "shikenan sai yadda kika ce haka za'a yi", daga haka Sahurar ta bar wajen.

Nusram tana idar da sallah kiran mahaifin nasu ya iso kunnen su, Nusreen ta taɓe baki tana faɗin; "wallahi matsalar gidan nan yawa yake dashi".

Duka suka miƙe suka fice, ɗakin Mama Jummai zasu je kuma harda Ummi, tun daga ƙofar ɗaki suke jiyo bambamin Maman.

Haka suka yi sallama suka shiga, Mama tace; "yauwa ku shigo ina kinibabbiyar take har ta san ta sasanta tsakanin miji da mata".

Gaban Nusram ya yanke ya faɗi, ko daga ji ta san da ita take, suna zama Baba yace; "Ina Nusram?", Nusram tace; "gani Baba".

Baban yace; me yasa kika haɗu da Idris har kike neman juyar mishi da tunani?", Sahura ta yi tsagal tace; "Baba wallahi ba haka aka yi ba nina same ta nace ina son na koma gidan miji na shine taje ta bashi haƙuri ni kuma tayi mini faɗa".

Baba yace; "oh har kin kai girman da zaki sasanta aure kenan?", Nusram ta girgiza kai tana faɗin; "kayi haƙuri Baba ita ta same ni da maganar".

Baba yace; "shikenan kin hutar dani ne kuma dama zaman nata ya ishe ni, magana ta gaba da nake so muyi shine akan ku", ya faɗa yana nuna Nusram da Nusreen.

"ɗazu kun wuce ni da Alhaji Baballe, kun dai san shine manager a inda nake aiki to ya nuna yana son na bashi ɗaya daga cikin ku, na dai faɗa mishi Nusreen akwai wanda na bawa ita to ke Nusram tunda baki da kowa ke na bashi dan haka sai ki shirya ina ganin gobe ko jibi zai zo sai ku ƙara fahimtar juna, kuma na faɗa musu duka su biyun bana so bikin naku ya wuce wata ɗaya to amma dalilin shi Shureim wato manemin Nusreen ya bada uzurin mahaifiyar shi da bata ƙasar to hakan yasa na ɗaga ƙafa amma duk da haka bana so ya ɗara wata biyu nan gaba".

Mama Jummai tace; taɓɗijam yanzu Abdullahi auren su Nusreen ɗin za'a yi lallai da sake", Baba yace; "me za'a sake ɗin, ai.magana ta ƙare nine mahaifin su kuma na tsayar musu da miji dan haka nan da ɗan lokaci kaɗan wallahi zasu bar gaba na haba na gaji kullum ni kenan ana zagi na babu dama na saka sabon kaya sai kaji ana cewa dama na bar yara a gaba na sunki aure ai dole na dinga shiga ina fita to wallahi ya isa haka dan haka aurar dasu babu fashi kai koda da almajirai ne sai na aurar dasu".

#LIKE
#SHARE
#COMMENT


*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.




♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

🎶🎶🎶
*Idanu na tsimin su ganka, Abdul kana ina*🎶🎶🎶

🎶🎶🎶
*Baki ya yawaita ambatan ka, hannu ya jinjina*🎶🎶🎶

🎶🎶🎶
*sanya mini shinfiɗa ta fuska, bango na jingina*🎶🎶🎶

🎶🎶🎶
*Abdul in zaka zo ka wulga, nima ba zan ƙi waiwaye ba*🎶🎶🎶






📖📖23-24📖📖


Nusreen ta zunɓuro baki sannan tace; "haba Baba muna ƴaƴan ka amma ka gaji damu, ai wannan babu adalci a ciki, gaskiya ni wallahi ba zan yarda ba aure kamar wasu kaji......", Baba ya kai mata duka cikin sauri ta kauche.

Yace; "wallahi Nusreen tsakanin ni da ke zanga wanda ya isa da wani", bayan Ummi ta shige tana ƙunƙunai.

Mama Jummai ta taɓe baki tana faɗin; "zan san abin yi don ba zai yiwu ba", babu wanda yabi ta kanta, Baba ya miƙe yana faɗin; "na riga da na gama magana".

Ummi ta miƙe haka Nusreen, Nusram kuwa ta daɗe zaune ko kanta bata ɗago ba tana tunano halin da zata shiga, cikin dabara ta goge hawayen idanun ta domin bata so Aziza da Ameera su gani.

A bakin ƙofa taci karo da Mama Jummai ta kalle ta tace; "ai wallahi da sake, zaman gida be ƙare muku ba tukunna dai", Nusram cikin jin haushi tace; "ai bake bace Allah" faɗar haka ta wuce ta bar Mama Jummai a tsaye.

Mama Jummai kuwa bata kuma cewa komai ba domin Allah ya sani tana tsoron Nusram idan har tayi zuciya dan bata da sauƙi.

Tana shiga ɗaki ta tarar da kowa na harkar shi dan haka itama zama kawai tayi, Nusreen ta dawo kusa da ita tace; "Ramluv ki kwantar da hankalin ki babu wanda zaki aura sai wanda kike so kinji".

Nusram ta kalleta tace; "to yanzu waye yace miki bana son shi?", wani kallo Nusreen ɗin ta yiwa Nusram sannan tace; "Ramluv kada ki cuci kanki, na san cew......" da sauri Nusram ta ɗagawa Nusreen hannu sannan tace;

"Rim dan Allah ki rabu dani barci nake ji haka", sanin halin Nusram ɗin yasa Nusreen miƙewa ta koma kusa da Ummi ta zauna.

Nusram kuwa ganin haka yasa ta miƙe ta shige uwar ɗaka, kan katifar su ta faɗa sannan ta saki ajiyar zuciya, ita bata taɓa ganin rashin adalci irin wannan ba taya za'ace anyi aure kalar wannan?, hawaye suka gangaro daga idanun ta.

Tana ji lokacin da Nusreen ɗin ke waya da Shureim baya ta shigo ɗakin ta kwanta, har suka gama Nusram bata bar zubar da hawaye ba domin kuwa abin yayi mata yawa, ji take kamar ta gudu ta bar gidan.

Nusreen tana gama wayar ta juyo tana me haska bayan Nusram ɗin sannan a hankali tace; "Ram!", haka ta kuma kiran sunan amma shiru Nusram bata amsa ba, ganin haka yasa ta ja bakin ta tayi shiru domin ta sani yanzu tana misbehave sai ta daku a hannun ƴar uwar tata.

Nusram kuwa tana jin Nusreen ɗin amma tayi banza da ita domin bata so Nusreen ɗin.ta gane halin da take ciki wannan zata barwa cikin ta ne don wata dama ce da Allah ya bata domin ƙubucewa daga hannun Isa sannan kuma domin bawa Nusreen ɗin damar yin aure.

Duk yadda barci ya iya sata a daren nan sai da ya bar Nusram ta kuma sha kuka har ta ƙoshi sannan ta kaiwa ubangiji kukan ta domin shi kaɗai zai iya share mata hawaye.

Ummi kuwa duk abinda Nusram keyi tana sane dashi, wannan yasa ta ƙudurce a ranta idan har Nusram ɗin bata son wannnan Alhajin to dole ne tayi fito na fito da Baban nasu akan wannan hukuncin domin ba zata so ƴaƴan ta su fuskanci irin abinda take fuskanta ba a gidan auren ta barin ma Nusram wacce take da zurfin ciki da kuma haƙuri.

Nusram koda tayi sallar asuba komawa tayi ta kwanta domin kuwa barcin dama ba'a cin bashin shi a zauna lafiya.

Nusreen shigowar ta uku kenan domin ta tashi Nusram ɗin ta karya amma abu ya gagara, zama tayi gefen katifar tasu sannan tace; "Ram dan Alƙah ki tashi", kamar ma bada ita take ba.

Nusreen ta bubbuga filon da Nusreen ɗin ta ɗora kanta a kai, a matuƙar kasala Nusram ɗin ta buɗe idanu sannan tace; "Pls ki ƙyale ni haka ma Nusreen", Nusreen ta cuno baki tace; "Ummi tace ki tashi fa, ga abin karin ki har yayi sanyi".

Nusram ta kuma maida idanun ta ta rufe kawai ta cigaba da kwasar barcin ta, ganin hakan yasa Nusreen miƙewa.

Nusreen ɗin na cikin shiryawa Sahura tayi sallama ta shigo, Nusreen ta amsa tana me cigaba da abinda take yi, Sahura tace; "Nusreen ko Nusram", Nusreen taja tsaki hakan ya alamtawa Sahurar ko wacece.

"Ina Nusram take?", cikin masifa Nusreen tace; "kin bani ajiyar tane?", Sahura ta ja tsaki ta juya wajen Ummi tace; "Ummi Nusram fa?", Ummi tace; "tana ciki tana barci ko tashi bata yi ba har yanzu".

Sahura tayi hanyar uwar ɗakin, tana shiga ta fara tashin Nusram ɗin, haka dole tasa ta miƙe sannan ta kalli Sahura tace; "me kuma ya faru", Sahura ta washe baki tace; "lallai da kitso mana".

Nusram ta dafe kai tace; "wallahi na manta gashi barci nake ji sosai", Sahura tace; "dan Allah kizo kiyi mini", Nusram tace; "to bari na karya", haka Sahura ta miƙe ta baro ɗakin.

Babu jimawa itama Nusram ɗin ta fito tana zabga hamma, nan ta gaishe da Ummin sannan ta fita tayo brush ta dawo, Nusreen tace; "to ni dai na tafi".

Nusram dake ƙoƙarin kai kunun bakin ta tace; "ina zaki je?", Nusreen tace; "zanje Tudun Nufawa Yaya Sulaiman yana nema na", Nusram ta sauke kofin daga bakin ta tace; "a dawo lafiya", Nusreen ɗin ta amsa da ameen tana me ficewa daga ɗakin.

Sai da Nusram ta gama karyawa sannan ta miƙe ta cewa Ummi; "bari naje na siyo Lallen da zan yiwa Sahura", Ummi tace; "a dawo lafiya", doguwar riga ce a jikin ta kalar ruwan ƙasa ta ɗora hijab ruwan madara a sama ta fice.

******** *********

Kamar yadda suka saba a saman dinning suka tarar da ƴan gidan, haka suka bi su ɗai-ɗai suka gaishe dasu, kowa ya amsa musu amma banda Brr Hauwa.

"lallai Farida ta samu sake idan banda haka mu data guje mu meye na turo mana yaran ta suzo su zauna damu?".

Fatima tace; "wai meye haka ne Brr abinda kuke yi sam be dace ba", da sauri Hajja ta katse ta sannan tace; "faɗa mini abinda be dace ɗin ba?", Fatima ta juyar da kai sannan tace; "ni na tafi", Hajja taja dogon tsaki.

Babu wanda ya kuma magana tsakanin su banda cin abinci da suke yi, Abdul kuwa wayar shi ce a hannun shi yake dannawa.

Hajja ta kalle shi tace; "kai kuma ba zaka ci abincin bane", ya miƙe cikin sauri domin abinda Brr Hauwa ta faɗa ya bashi haushi yace; "Idan zan ci zanje gidan Abban Fadil naci".

Ai kamar ya ƙara zuga ta ne nan ta hau sababi, "tunda shi Jabeer ɗin uban ka ne ai dole kaje gidan shi", Abdul kam hannun Sumayya ya riƙe ya fincike ta dole ta tashi ko gama cin abincin bata yi ba.

"to sake ta ta dawo taci abinci", abinda Brr Hauwa ta faɗa kenan, kamar be ji ta ba haka ya cigaba da tafiya, taɓ ai ji tayi ya gama raina mata hankali tana magana yayi banza da ita a gaban yara ƙanana kan ta buɗe baki ta kuma magana ya fice hakan yasa itama ta miƙe cikin fushi ta kwashi kayan ta.

Suna tafe yana tunanin halin gidan su ya rasa meke tsanin su da Mom ne haka da yayi zafi har haka?.

Koda suka shiga gidan kusan kamar ko wane lokaci babu kowa ya zaunar da Sumayya saman kujera sannan ya nufi sama.

Yana ƙoƙarin shiga tana ƙoƙarin fita, da sauri suka ja suka tsaya, a tare suka saki murmushi me ƙayatarwa, Abdul ya bita da kallo tun daga sama har ƙasa.

Tana sanye da doguwar riga, Dubai abaya kalar ruwan kasa me haske, kanta kuwa blue ɗin mayafi ne wanda tayi rolling dashi, ƙaramin gilashi ne maƙale a idanun ta wanda yawancin likitoci suke sakawa.

Hannun daman ta saƙale da riga ta aikin su, sai kuma hagun ta inda take riƙe da ƙaramar jakar ta da kuma wayar ta babu abinda ke tashi a jikin ta banda ƙamshi.

Ya langaɓar da kai, Saleema ta zuba mishi idanu fuskar ta cike da annuri na ganin ƙanin nata kuma masoyin ta abin ƙaunar ta.

"yau kam zan iya cewa nafi kowa sa'a", ta faɗa cikin sanyin murya wanda kusan halin ta kenan, ya saki ƙayataccen murmushi kan yace; "ni kuma gashi yunwa nake ji balle ma na tantace na tashi a sa'a ko akasin hakan".

Ta ɗan zaro idanun ta sannan tace; "me yasa baka kira ni ba da yanzu na haɗa maka ai", ya kauda kai sannan yace; "gashi kuma naga kin gama shiri da alama direct sai wajen aiki, bari kawai insa Hanne ko Muhibba su dafa mini", ya ƙarasa yana ƙoƙarin juyawa.

Cikin sauri ta riƙo hannun shi tana faɗin; "ayya ba za'a yi haka ba gaskiya bari na shiga kitchen ɗin na sama maka abinda zaka ci", tana gama faɗar haka ta nufi downstairs da sauri, Abdul yabi bayan ta yana me jinjina irin soyayyar da take yi mishi.

Saleema ta ƙara washe baki ganin Sumayya a zaune, Sumayyar ma cikin farin ciki ta gaishe da yayar tata, nan Saleemar ta barsu ta wuce kitchen domin sama musu abinci.

Sumayya ta matso kusa da ɗan uwan nata sannan ta miƙa mishi wayar tana faɗin; "Ya Abdul kalli motar da Daddy ya siya muku".

Amsa yayi yana kallo, motoci ne guda uku masu kyau sosai, ɗaya baƙa ɗaya ruwan ƙasa ɗaya ja, ya miƙa mata yana faɗin; "na san dai baƙar suka bar mini ko?".

Sumayya cikin alhini tace; "babu yadda Mummy bata ba akan Ya Tameer ya bar maka wannan amma ƙememe yaƙi bar maka wai ita yake amma naji Mummy tace zata maka order ɗin wasu guda biyu", ya jinjina mata kai kawai ba tare da yace komai ba.

Wato ya san da biyu Ya Tameer ya zaɓi baƙar ya bar mishi ja domin ya san yadda ya tsani mota ja, haka kuma kowa a gidan ya san Tameer ɗin ke son mota ja har ma su kan tsokane shi da kalar mata ce, amma shine ya zaɓi baƙa kawai dan ganin ya ɓata mishi rai.

"Ya amma gobe ba da wuri zamu tafi ba ko?", Sumayya ta katse mishi tunanin da ya tafi, ya ɗaga kai kawai, sun cigaba da fira inda yawanci kawai ɗaga mata kai Abdul ɗin yake yi domin tunanin shi baya kanta yana kan wannan yarinyar ta jiya.

Saleema ta fito hannun ta ɗauke da tray, da sauri Sumayya ta tashi ta amso ta, Sumayya tace; "sannu Aunty Saleema da aiki ai da kin saka Hanne".

Saleema tace; "kada ki damu ƴar ƙanwata kun wuce kuci abincin Hanne a waje na bayan ina gidan", ta ƙarasa tana kallon Abdul ɗin wanda shima idanun shi yana kanta domin ya san akan shi take maganar ba wai dan Sumayya ba.

Yayi murmushi sannan yace; "aikuwa mun gode da wannan karramawar, kuma munji daɗi sosai, abinda zamu ce kuma shine adawo lafiya", ta saki murmushi tana ɗaga musu hannu ta fice.

Tare suka ci abincin kamar suna gida suna yi suna fira wacce bata da hayaniya sosai, a haka Mummyn ta fito ta tarar dasu nan suka gaishe ta, da yake itama da shirin office ta fito hakan yasa ta wuce su kawai.

Ya miƙe tsaye itama Sumayya haka ya kalle ta yace; "ni zan fita kije wajen Nihal na san tana nan", daga haka ya juya ya fice.

Motar Fadil yaje ya ɗauka sannan ya fice daga Estate ɗin gaba ɗaya, wajen Akram yake so yaje wanda zasu haɗu a jiya amma saboda Nusram basu samu damar haɗuwa ba.

Har ya gifta ya hango kamar ita a tsaye a bakin titi, sai fama duba waya take wanda alamu ya nuna sauri take kuma bata samu mota ba, a hankali ya fara dawowa da baya da baya har yazo kusa da inda take.

Yana sauke glass ɗin suka haɗa idanu, Nusreen ta ja ƙaramin tsaki tana me kauda kai, Abdul kuwa abin ya bashi mamaki, a jiya tsoron shi yake gani a idanun ta amma a yau kuma yaga masifa da tsiwa kawai ke cin ta.

Ya jima a haka ita bata waigo ba shi kuma be wuce ba, Abdul ya kuma juyawa ya kalle ta, Atamfa ta saka me ruwan ganye da ratsin ja da fari haka Hijab ɗin jikin ta fari ne, tayi kyau sosai domin kuwa fuskar nan ta ɗauki kwalliya.

Abdul ya taɓe baki domin ganin shi jiya tafi kyau don jiya babu kwalliya a fuskar ta, ya duba agogon hannun shi sannan ya buɗe motar ya fito.

Gaban ta ya je ya tsaya, Nusreen kuwa kamar bata san dashi a wajen ba duk da yadda gaban ta ke faɗuwa dan yana yi mata kwarjini sosai.

Abdul kuwa cikin bada umarni yace; "shiga muje", wani shegen kallo Nusreen ta wulla mishi kan tace; "sannu Malam Abdullahi🙊".

Abdul ya kafe ta da ido yayin da Nusreen ɗin taƙi yarda su haɗa idanu, hannu ya kai zai riƙo nata da sauri taja baya sannan tace; "wallahi ka sake ka ɗora hannun ka saman jiki na sai nayi maka ihun kwarto", sosai hakan ya bashi mamaki kan yace wani abu motar Shureim ta tsaya kusa dasu.

Shureim ya fito cikin sauri yace; "afuwan Sarauniyar mata wallahi na ɗan tsaya amsar saƙo ne", Nusreen ta cilla mishi harara sannan tace; "ka kyauta daka shanye ni a nan har wasu marasa ilimi da hankali suke tunanin ko ni ɗin ina da araha har haka", ta ƙarasa tana kallon inda Abdul ke tsaye wanda tun lokacin da Shureim ya ambaci Sarautar mata yaji wani abu ya daki zuciyar shi.

Shureim ya kai kallon shi inda Abdul yake, cikin sauri ya ƙarasa yana miƙa mishi hannu; "barka da hutawa yallaɓai", Abdul yayi murmushi yace; "Shureim dama kana nan shine ko ziyara babu".

Shureim ya shafa kai yace; "kayi haƙuri yallaɓai wallahi abubuwa ne sun yi yawa sannan ban jima da dawowa najeriyar ba don ina Egypt karatu".

"ina Ammie? Fatan tana lafiya", Abdul ɗin ya tambaya, Shureim yace; "Ammie tana Syria wallahi ciwon ƙafa ne ya matsa mata".

"ayya amma ya ƙafar yanzu", Abdul ɗin ya tambaya, Shureim yace; "eh to wai likitan da ake saka ran zaiyi mata aiki ne sai nan da kwana uku zai dawo Dr John Burlin".

"John Burlin ai na san shi ka bari zan kira shi sai a san yadda za'a yi aikin", nan fa Shureim ya fara godiya.

Nusreen ta baje hanci da baki tana kallon su bata yi tunanin sun san juna ba, ganin abin bana ƙare bane yasa tace; "wai Habibi a waje zaka barni ne ko kuwa zaka wuce muje?", da sauri Shureim yace; "Afuwan Sahiba shiga muje", ya faɗa yana me buɗe mata ƙofa sai da ta harari Abdul ta ƙasan ido sannan ta shige.

Shureim ya kalli Abdul yace; "yallaɓai mun gode sosai Allah ya saka da alkhairi", babu abinda Abdul ya iya samun dama banda ɗaga mishi kai da yayi, yana kallo Shureim yaja motar ya tafi.

Abdul ya buɗe motar shi ya shiga sannan ya kifa kanshi saman sitiyarin motar, babu abinda ke mishi yawo a idanu banda meye haɗin Shureim da wannan yarinyar?.

"ai amsar a fili take saurayinta ne", zuciyar shi ta bashi amsa, da sauri ya furta; "Impossible!", sai kuma wata zuciyar tace; ina ruwan ka ne?", ya ɗaga kafaɗa alamun babu haka yaja motar shi ya bar wajen.

Nusreen bayan sunyi nisa ta kalli Shureim tace; "meye haɗin ka da wancan?", Shureim yace; "lokacin da mahaifina yake da rai a ƙarƙashin mahaifin shi yake aiki, ke kuma meye haɗin ki dashi", ya dawo mata da tambaya.

Nusreen ta taɓe fuska tace; "babu komai ni ban ma taɓa ganin shi ba sai yau", Shureim yayi murmushi kawai domin sanin halin Nusreen ɗin.

Abdul kuwa koda ya ƙarasa wajen abokin shi Akram ɗin kasa zama yayi dan haka ya miƙe yana faɗin; "ina ji gida zan koma kawai".

Akram ɗin ya miƙe yana faɗin; "haba Abdul yaushe kazo da har zaka koma?, gashi ko maganar da zamu yi ma bamu gama ba", Abdul ya ɗan ja tsaki sannan yace; "kada ka damu idan na dawo next time zamu yi maganar".

Dole haka Akram din ya rako shi har wajen masana'antar, tuƙi kawai yake yi amma hankalin shi naga Shureim da kuma wannan yarinyar ya rasa me yasa abin ya tsaya mishi a rai.

Yana zuwa dai dai layin kamar ance ya kalli hanyar ya hango ta sanye da doguwar riga me ruwan ƙasa da kuma hijab kalar ruwan madara.

Cike da mamaki yake binta da kallo to ko dai aljana ce amma abin da mamaki a yadda yaga tafiyar su ya tabbatar inda zasu je ma da wuya idan sun kai balle har su dawo.

A hankali ya fara bin bayan ta har zuwa ƙofar gidan nasu wato lungun da zaka iya hango gidan su, Nusram da bata san ana bin ta ba ta shige gidan hannun ta riƙe da ledar data siyo kayan lalle wanda ta san zata buƙata wajen yiwa Sahura.


#LIKE
#SHARE
#COMMENT

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*



♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*



📖📖25-26📖📖

Abdul na ganin ta shige

Please Login or Register in order to submit comment