Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gamsu da hakan dan ya san wacece Mama Jummai.

"to yanzu me za'a kawo muku?", Nusram ta girgiza kai tace; "Alhamdulillahi a ƙoshe nake sai dai ko matar taka".

Sahura ta riƙe haɓa tace; "ni ba zan iya cin wani abu a nan ba kawai dai na gode", duka sai da suka yiwa maganar ta dariya, Nusram kam murmushi ɗauke a fuskar ta, koda ta ɗago caraf idanun ta a cikin nashi.

Gabanta ne ya faɗi cikin sauri ta kauda kanta ƙirjinta na cigaba da dukan uku-uku, ta kalli Sahura da suke faman fira tace; "to ni dai zan wuce idan kun gama ki wuce gida kawai".

Sahura tace; "ina zaki je?", Nusram da duk ta gama tsorata da yanayin kallon da yake mata tace; "zanje shagon Yaya Sulaiman ne ba zan jima ba zan dawo,sai anjiman ku", tana faɗin haka ta bar wajen cikin sauri.

Abdul na ganin ta fita ya kalli Muhibba yace; "ina zuwa?", da sauri ta miƙe tana faɗin; "ina kuma zaka je wanda muke jiran fa br ƙaraso ba", be kalle ta ba sai ma key ɗin dake ajiye saman table ɗin ya ɗauka cikin sauri ya fice.

Koda ya fito nan ya fara dube-duben inda zai hango ta, can ya hange ta harta tare abin hawa, dan haka cikin sauri ya nufi tashi motar.

Ganin hakan yasa Nusram ɗin tace da Me Keke Napep ɗin su tafi kawai ko gama dai-daitawa basu yi ba.

"shi kuma wannan me tayi mishi da zai dami rayuwar ta haka?, oh na shiga uku ni Nusram ko dai Aljani ne?", ita kaɗai take maganar ta.

Leƙowa tayi aikuwa ita yake bi domin motar shi na bayan tasu, kaɗan ya rage bata yi suman zaune ba "idan kuma ɗan garkuwa da mutane ne fa?, to me nake dashi da har zan damu kaina", haka dai take da wasi-wasi a ranta har suka ƙaraso inda zata sauka.

Ji take kamar kada ta sauka, "Hajiya.mun ƙaraso fa", me Keken ya sake maimaitawa, bata da yadda zata yi haka tayi shahada ta sauko daga ciki.

Ta miƙa mishi ɗari biyar ta ƙara gaba cikin sauri kamar wacce ake hankaɗawa, Me keken na ta tsaya ta amshi canji amma ita bata wannan take ba.

Abdul dake hangen duk abinda yake faruwa dan haka ya fito ya jingina da jikin motar yana kallon ƙofar shagon data shiga.

Me keke kuwa ganin bata kulashi ba yasa yaja keken shi yayi gaba abin shi.

Tana shiga tayi ajiyar zuciya tana me neman waje ta zauna tana maida numfashi, kamar wacce tayi gudun fanfalaƙi haka take jin ta.

Sulaiman dake cikin ɗan ɗakin dake shagon yana hango ta dan haka yayi murmushi a ranshi yana faɗin; "Nusram kenan sarkin tsoro", ganin ba zata ƙaraso bane yasa ya miƙe ya nufo inda take.

"kamo ta nan", abinda ya faɗa kenan wanda yasa Nusram ɗin zabura tana neman ficewa, Sulaiman ya kasa riƙe dariyar shi aikuwa ya dara.

Nusram ta sauke ajiyar zuciya ganin wanda ya tsorata ta sannan tace; "Kai Ya Sulaiman dan Allah", shima cikin kwaikwaiyar yadda tayi yace; "Kai Nusram dan Allah".

Ta shagwaɓe fuska kamar me shirin yin kuka, ya kauda kai yana dafe baki yace; "Lalala babu ruwa na", yadda yayi ba ƙaramin dariya ya bata ba, tana dariya tana tafiya zuwa inda table ɗin shi yake.

Har ta wani manta da ɗan garkuwar ta, wanda ya kusa sace ta🤣, Ya Sulaiman kuwa cikin shagon ya shiga ya fara haɗo mata kayan da zata tafi dashi.

Sai da ya haɗa tas sannan yazo inda take, cike da wasa da dariya suka gaisa yana yi yana tsokanar ta, wani tayi dariya wani kuma ta ƙyale shi.

"wai ina waccen me tsiwar ne?", ta san wacce yake nufi dan haka tace; "me tsiwa yanzu tsuntsun so ke shawagi da ita a sama", ya ɗaga gira ɗaya ta jinjina mishi kai.

Nan take bashi labarin yadda akayi da abinda Baba ya faɗa na ya bashi ita, Sulaiman ya zaro idanu yace; "Babu bincike?".

Nusram cikin jimami tace; "kaima kamar ka manta halin Baba kenan?", Sulaiman yayi ajiyar zuciya sannan yace; "zan so haɗuwa dashi kuwa inajin gobe na shigo layin naku idan yaso duk abinda muka yi zan je na sami Abba shi zai san abin yi akai amma ya za'a yi a ɗauki ƴa kamar wata kaza a bashi haka kawai to ko kaza ce ai a bincika a gani ba ɓarawo bane", Nan dai yayi ta faɗan shi ita dai Nusram bata ce komai ba.

"To ke kuma fa?, har yanzu?", Nusram cikin jimami ta bashi labarin abinda Isa ya faɗa, a zuciye ya miƙe tsaye sannan yace; wallahi yayi ƙarya a ɗauki ƴa me asali a bawa shege".

Nusram dama ta san hali, cikin zuciyar ta tace; "aifa abin nema ya samu", cikin lallashi ta miƙe tace; "Ya Sulaiman nifa abinda nake so shine mu rabu lafiya ka san yadda Baba ke son shi yana faɗa mishi Baba yarda zai yi".

Sulaiman yayi huci yace; "naga uban daya isa ya aura miki wannan ɗan iskan me kama da mata-maza", Nusram kamar tayi dariya amma tana tsoro yanzu abin ya ƙare akanta dan haka taja bakin ta tayi gum.

"to yanzu dai mu ajiye maganar Isa a gefe, ayi ta Shureim tunda zaka shigo gobe zan faɗawa Nusreen ɗin sai tace yazo goben sai ku haɗu, yanzu bani kayan na wuce".

Ya galla mata harara, Nusram tayi murmushi tace; "haba Angon Aisha", shi kanshi sai da ya murmusa sannan ya miƙe ya biyo ta.

Yana gaba riƙe da kayan tana bayan shi haka har suka fito waje, tana ɗaga idanu ta sauke a kanshi aikuwa saura kaɗan ta faɗi saboda tsorata.

Wannan wane irin mutum ne ace duk wannan daɗewar yana tsaye yana jiranta, shi kuwa Sulaiman bema lura dashi ba dan haka nesa dashi kaɗan suka tsaya.

Abin hawa ya fara wuya idan akayi la'akari da lokacin Sallah daya matso, sun jima a tsaye kafin Sulaiman yace; "to kodai zaki koma shago ne ki zauna idan yaso in mun sauko daga masallacin sai na kaiki ko kuma lokacin zaki sami abin hawa?".

Ta girgiza kai tana fadin; "a'a Yah Sulaiman kawai kaje masallacin ni zan tsaya Allaha zai kawo kaga ana saukowa zamu wuce makaranta kuma bana so waccen tayi ta jira na ka santa da ƙorafi".

Ya ajiye kayan sannan ya ciro dubu ɗaya ya miƙo mata yace; "shikenan sai anjima idan kuma har an sauko kina nan to", ta amsa tayi godiya yayin da shikuma ya koma shagon domin shiryawa.

Abdul da duk yana tsaye yana jin me suke cewa domin tazarar dake tsakanin su bata yi nisa sosai ba sannan kuma hankalin shi gaba ɗaya yana kansu.

Nusram kuwa tsaye take amma kaɗan-kaɗan takan ɗago ta kalle shi, sai dai a yadda yake zaka ɗauka wayar dake hannun shi yafi bawa mahimmanci.

Tayi ajiyar zuciya ganin ko kallon ta beyi ba sai dai ta makaro domin kuwa yana kallon yadda duk ta wani tsargi kanta kamar mara gaskiya, minti biyar suna tsaye a haka kafin ya ɗago sosai ya kalle ta shi take kallo amma ganin yana ɗago yasa tayi saurin kauda kanta.

Kamar ta koma haka take ji, tana kallon shi ta gefen ido harya maida wayar shi cikin aljihu sannan ya fara takowa zuwa inda take.

Ta kalle shi ganin ya nufo ta gadan-gadan yasa tayi saurin juyawa amma sai dai kan tayi wani taku ya ƙaraso inda take.

Kayan hannun ta ya riƙo ganin taƙi saki yasa ya kalle ta, cikin sauri kuwa ta saki, yayi murmushi sannan ya fara takawa zuwa wajen motar tashi.

Sai da ya kai kayan ya buɗe booth ya saka sannan ya juyo ya dawo, hannun ta riƙo ta cije ganin hakan yasa ya fizge ta da ƙarfi, ko tayi ihu bashi da amfani domin kuwa babu mutane sosai kasancewar duk sun tafi masallaci.

Shagon Sulaiman ɗin ma ya rufe domin kuwa ta ƙofar baya suke bi su tafi masallacin tana ji tana gani ya buɗe motar ya saka ta sannan ya maida ya rufe ya zagaya ya shiga.

Ita dai sai idanu babu baki ga kuma kirjinta dake dukan tara-tara,😂, haka har ya tada motar bata iya ce mishi komai ba.

Ganin da gaske tafiyar zai yi cikin rawar murya tace; "dan Allah kayi haƙuri mu bamu da wasu kuɗin da zamu baka Baba na talaka ne Mama na itama talaka ce dan Allah ka kayi haƙuri ka sauke ni na tafi gida Mama na hankalin ta zai tashi haka ma ƴar uwa ta, wallahi bamu da wani kuɗi rufin asiri kawai muke dashi".

Magan-ganun ta yake juyawa cikin ranshi, wato ita kallon me garkuwa da mutane take mishi kenan?, be san lokacin da murmushi ya ƙwace mishi ba.

Ita kuwa ganin yayi murmushi yasa idanun ta kawo hawaye cikin sheshsheƙar kuka tace; "idan kuma masu yin fyaɗe ne kayi haƙuri ka maida ni gida Baba na zai iya kashe ni idan hakan ta faru Mama na kuma zata shiga damuwa sannan maganar idan ta fita za'a iya fasa auren ƴar uwata dan Allah kada ka lalata mini rayuwa ka bata sunan gidan mu kasa Mama ta sami abin yiwa Ummi gori",.

Ga abin dariya amma babu halin yi hakan yasa kawai ya maida hankalin shi kan titi, ganin hakan yasa Nusram ta fara addu'a domin ta san yau tata ta ƙare cikin uku za'a yi ɗaya ko dai yayi mata fyaɗe ko kuma ɗan garkuwa da mutane ne ko ɗan yankan kai.

Ta ciro wayar ta a hankali ta kalla, Number din Nusreen ta nemo ta tsurawa number ɗin idanu haka kawai taji wani kukan yazo mata shikenan ita kuma tata ta ƙare.

Nima kaina nace; "Allah sarki Nusram RIP 😭.



#LIKE
#SHARE
#COMMENT
#VOTE
#FOLLOW @13deeja


*Babyn Abdul,Maman meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*


♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖21-22📖📖

Wayar dake gefen shi tayi ƙara ganin Muhibba ce me kiran wannan yasa ya dannan amsawa, "Haba Abdul kana ina ne?", abinda ta faɗa kenan?.

"Abdul!", Nusram ta sake maimaita sunan a cikin ranta, inbox ta shiga ta rubuta summary ɗin abinda ya faru harda sunan data ki wata ta kira shi.

Wayar na hannun ta tana juyawa tana me fatan koda ace ya kashe ta ne to wani ya tsinta domin kuwa bata ga alamun wasa ba a fuskar shi.

"Nifa gani a hanyar gida kawai ki nemi abin hawa ki wuto gida", amsar daya bawa Muhibba kenan.

Cikin jin haushi Muhibba tace; "haba Abdul amma dai ai hakan ba adalci ban.......", kafin ta ƙarasa ya katse wayar.

Nusram data zuba mishi idanu, ta kauda kanta ganin sun ɗau titin da zai kai su Hayin Rigasa yasa ta saki ajiyar zuciya har sai da ya juya ya kalle ta.

Dai-dai kwanar hanyar gidan nasu yaja ya tsaya wato inda ya bige ta, bece mata komai ba itama ganin hakan yasa tayi shiru tana saƙe-saƙe a ranta.

Cikin ɗan ƙarfin hali ta kai hannu ta fara ƙoƙarin buɗe motar sai dai abin ban haushi taƙi buɗewa hakan yasa kawai ta koma yadda take ta zauna.

Ta kalle shi, ba ita yake kallo ba kuma yaƙi ce mata komai, hakan yasa ta fara murza zoben hannun ta.

Abdul dake kallon ta amma idan baka sani ba sai kace idanun nashi a lumshe suke saboda yadda yayi, shi jira yake ta nuna mishi hanyar da zasu bi ita kuma ta kasa fahimta.

Nusram ganin zaman yayi yawa yasa ta kada baki tace; "dan Allah ka buɗe mini na fita", jin yayi shiru yasa ta sake kallon fuskar shi.

"so cute", abinda ta faɗa kenan ganin idanun shi a rufe, sai kuma tace; "very arrogant", be san lokacin da murmushi ya suɓuce mishi ba wanda hakan ba ƙaramin kyau yayi mishi ba.

Nusram kuwa idanu ta zaro tana me dafe ƙirji, ya buɗe idanun shi gaba ɗaya a kanta, sosai ta daburce har jikin ta ya fara rawa.

"wai baki gaji da gani na bane da kika barni a nan?", abinda ya faɗa kenan, yadda yayi maganar idan ba kana kusa ba, ba lallai kaji ba.

Nusram cikin in-ina tace; "to ai......to ai......to....ai kaine baka buɗe mini ba", shima cikin kwaikwayar ta yace; "to ai......to ai.....to....ai kece baki faɗa mini hanyar da zan bi ba".

Hannu ta ɗaga sannan ta nuna mishi hanyar shi kuma ya tada motar ya shiga, haka tayi ta nuna mishi hanya har zuwa ƙofar gidan nasu wato lungu daga shi kana hango gidan su.

Sai da ta fita sannan shima ya buɗe motar ya fito, boot ya buɗe ya ɗauko mata jakar kayan sannan ya ƙaraso inda take tsaye.

Ita kuwa kallon shi kawai take yi tana yaba kyawun da Allah yayi mishi, mutum kamar balarabe, yaran dake wasa a wajen su kansu duk shi suke kallo don ganin balarabe a layin su.

Ya miƙo mata jakar kafin yace; "nifa bana son yawan kallo", cikin sauri ta amsa sannan ta juya ta fara tafiya, Abdul kuwa yabi bayan ta da kallo, har tayi nisa sannan ta tsaya.

Ta juyo ta kalle shi sannan tace; "na gode", ya jinjina kai kawai ita kuma ta juya sai dai idanun ta yayi mata mugun gani domin kuwa Isa ne a tsaye a gaban ta.

Cikin masifa yace; "uban waye wancan daya ajiye ki", Nusram ta kauda kai gefe, cikin takaici yace; "wallahi baki isaba domin baki da mijin da ya wuce ni", ya nuna ta yace; "wato dan iskanci har yanzu baki bar bin maza ba kenan, kuma wai abin ban haushi balarabe kika komawa to wallahi tun kan ki bar mana abin faɗa yau zanje na sami Baba na faɗa mishi meke tsakanin mu".

Nusram cikin sauri tace; "amma Isa ai ban riga na amince ba ko", shima cikin sauri yace; "wannan kuwa ke ta shafa", ya wuce ya barta a tsaye.

Ta juya a hankali ta kalli inda yake tsaye sai dai babu shi, wato ya tafi tun ɗazu kenan?, taja ajiyar zuciya sannan ta shige gida.

Abdul kuwa yana ganin suna magana da wani mutumi yaja motar shi ya tafi, yana tafe yana mamakin yadda har ya taimaki wannan yarinyar.

Koda ya isa gida har an sauko masallaci hakan yasa kawai ya wuce ɗakin Malama, bayin ta ya shiga yayi alwala.

Yana fitowa ta kalle shi tace; "lafiya baka sami sallah ba?", ya ɗan sosa kai sannan yace; "wallahi wani abu ne ya ɗauke mini hankali, kuma kan na iso an sauko".

Cikin haɗa rai tace; "ka maida hankali akan addinin ka, ka dena wasa dashi", yace; "to Malama".

Da kanta ta shinfiɗa mishi abin sallah ya hau ya fara, Malama ta kalle shi tayi murmushi.

Bayan ya idar da sallar ya juyo ya kalli Malamar yace; "Sumayya tazo ko?", tace; "eh kana fita ɗazu ɓaka jima ba ta iso ina jin tana ɗakin Hajja ko kuma tana gidan Mukhtar(Abban Nihal).

Ya jinjina kai kawai ba tare da yace komai ba ya haye saman gadon ta ya kwanta, baya son zuwa gidan Abban Nihal Allah ya sani har cikin ranshi, a haka har barci yayi awon gaba dashi.

Malama ta matsa kusa dashi tayi mishi addu'a, tana kallon shi cike da tsananin ƙauna.

Har su Fadil suka dawo tana zaune kusa dashi ta kasa tashi ta barshi, Fadil da Fadila suka kalli juna suna mamakin abinda Malama take yi akan Abdul kwata-kwata bata son abinda zai taɓa shi tun suna ƙanana haka rayuwar take.

Fadil yayi gyaran murya da sauri Malama ta tashi daga kusa da Abdul, Fadila ta nemi waje ta zauna saman center carpet din dake shinfiɗe tana faɗin; "wash wallahi na gaji".

Fadil ya harare ta sannan yace; "kamar wani aiki tayi a office ɗin ina kallo fa Hafeez ne yayi aikin kina gefe", tayi murmushi tana kauda kai gefe.

Sumayya ta shigo da sallama sannan ta ruga da gudu tana ihu, Fadil ya buɗe hannu ta faɗa jikin shi.

Firgigit Abdul ya farka, cikin sauri ya dafe kai sannan ya kalle su yadda suke ihu yaja tsaki.

Su kam bama su san yana yi ba, Fadil kuwa ya koma kamar wani yaro sai biye mata yake yi, Abdul cikin jin haushin tashin shi da suka yi ya ɗauki filo ya cilla musu.

Sumayya ta kalle shi ta shagwaɓe fuska, ya cilla mata harara kan yaja tsaki ya miƙe, Fadil kuwa dariya kawai yake yi dan ya san sun gama bawa Abdul haushi dan ya tsani yana barci a tashe shi.

Bayin Malama ya shige, su kuwa bama ta shi suke ba dan haka suka cigaba da hayaniya a ɗakin, inda Sumayya ke basu labari su kuma suna dariya.

Fadila tace; "ai ni kam naso zuwan Surayya ko dan na kwashi dariya", Sumayya tace; "taɓ kema kin san Aunty Surayya ba zata zo ba sai dai Daddy idan ya dawo".

Fadila tace; "ai da yake Family meeting ya kusa zuwa nan da two months fa", Sumayya tayi ihu tana faɗin; "yes gaskiya naji daɗi".

Abdul daya fito daga bayi yana nemi waje ya zauna ya dafe kanshi, Malama ta dafa shi tana tambayar lafiya.

Yayi murmushi yace; "kawai hayaniyar wa'innan ne take damuna", Malama ta miƙe tana murmushi kawai.

Sai da suka gama shirmen su sannan suka fice waje, Fadila ta kalli Abdul tace; "wallahi har ɗakin yayi shiru", bece mata komai ba sai wata harara daya jefa mata.

Ya jima a zaune kafin ya miƙe ya fice, ɗakin su yaje yayi wanka sannan ya fito falo inda su Sumayya suke a zaune.

****** ******* ******


Ɓangaren Nusram kuwa tana shiga gida kamar yadda tayi zato, Nusreen keta surfawa Mama Jummai rashin kunya yayin da Mama Jumman take surfa mata zagi.

Nusram tayi ajiyar zuciya kan tayi sallama ta shiga gidan, Nusreen na ganin Nusram tayi shiru sannan ta shige ɗaki.

Mama Jummai kuwa cikin hargagi tace; "shegiya mara kunya ai da kin fito kin cigaba daga inda kika tsaya kuma ni nan na faɗa kuda aure wallahi sai dai kuga ana yi", Nusram dake daf da shiga ɗaki ta juyo ta kalli Maman kan ta juya ta shige ɗakin.

"kya juyo ki kalle ni mana shegu masu yawon ta zubar", Maman Jummai kenan wacce ke sake cigaba da bambami.

Nusram na shiga ɗakin ta sami Ummi na zaune tana ƙulla man ja da man gyaɗa yayin da Kubra ke gefen ta, tana wasa domin kuwa yanzu ta kan zauna har ma ta dinga wasa da abinda aka bata.

Sannu ta yiwa Ummi sannan ta shige uwar ɗaki anan ta tarar da Nusreen tana ƙara gyara fuskar ta, domin su tafi makaranta.

Jakar hannun ta ta ajiye sannan ta juya ta fice, alwala ta ɗoro tazo ta data sallah sai da ta idar sannan ta kwashi litattafan ta sannan suka tafi.

Bata faɗawa Nusreen abinda ya faru tsakanin ta da Isa ba domin sanin hali yafi sanin kama, hakan yasa taja bakin ta tayi shiru.

Basu baro makaranta ba sai yamma, Nusreen na rataye da jaka inda Nusram ke rungume da littattafai haka suka jero.

Suna karyo kwanar lungun su suka hango Mahaifin nasu tare da wani mutumi wanda yake tsaye jikin motar shi.

Nusreen da Nusram haka suka gaishe da baƙon baban nasu, hakan Baban nasu yayi ta washe baki shi kuwa baƙon bin su yayi da idanu kamar wani maye har lashe baki yake yi.

Suna shigewa gidan ya haɗiye yawu sannan ya kalli Baban su Nusreen ɗin, Baban yace; "kayi haƙuri Alhaji Baballe insha Allahu nan da ƙarshen wata zan haɗo maka kuɗin ka".

Alhaji Baballe ya girgiza kai yace; "a'a Malam Abdullahi dan dai dubu ɗari ai ba zai gagara na bar maka ba dan haka ni yanzu wata magana nake so muyi da kai".

Malam Abdullahi yace; "ina jin ka Alhaji", Alhajin yace; "wa'innan ƴan shilan ƴaƴan waye ne?", Baba yace; "wai Nusreen da Nusram ƴaƴa na ne ka gansu nan sai dai garari a gari babu wanda yazo domin auren su na rasa yadda zanyi dasu".

Alhaji Baballe ya washe baki yace; "to ai ni dai in dai ba'a musu miji ba sai ka aura mini ɗaya daga cikin su kawai", Baba ya washe baki yace; "aikuwa na gode da wannan alfarmar da zaka yi mini, sai dai Nusram da ita Nusreen wani yazo kwanaki duk da akwai yarjajeniya a tsakanin mu".

Alhaji Baballe yace; "koma wacece ni dai a cikin su ina son ɗaya", Baba yace; "in dai Nusram ce na baka sai dai mu jira lokaci kawai".

Alhajin yace; "ka tambayi yarinyar kada yazo bata amince ba dan itama tana da haƙƙi a kai", Baba ya ja tsaki yace; "ba dai kana son ta ba ai magana ta ƙare".

Alhaji Baballe yace; "a'a fa kada a takura mata dan ka san yaran yanzu ka dai tambaye ta idan ta amince sai ka sanar mini ina jira".

Baba ba dan son ranshi ba yace; "shikenan zan tuntuɓe ta ɗin", haka suka yi sallama da Alhajin sannan Baban ya wuce masallaci jin an fara kiraye-kirayen sallah.

Cikin gidan kuwa suna shiga Nusreen ta ja tsaki tace; "banza maye kawai", Nusram dai bata ce mata komai ba.

A bakin ƙofa suka sami Ummi tana kwashe abincin data gama nan suka yi mata sannu da zuwa.

Ummi cikin farin ciki tace; "yauwa sannun ku ƴan mata na, yau da alamu anyi ciniki kenan naga babu ko ɗaya da kuka dawo dashi".

Nusreen ta miƙawa Ummi kuɗin tana faɗin; "gashi ki ajiye wallahi kaya yau sunyi kasuwa gaskiya yau Yaya Sulaiman ya bamu kaya designer".

Nusram kuwa tsintsiya ta ɗauka ta hau shara, sai da ta gama sannan ta ɗauki buta domin yin alwala.

A bakin famfo ta sami Sahura, Nusram tace;

Please Login or Register in order to submit comment