Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cewa mafarki take yi.

Tayi murmushi tace: "kaga ashe mafarki ma nake yi, ja ɗauka gaske ne ina Abdul ɗin?", Dr Abubakar yace; "calm down My Brr ɗanki yana lafiya", jin hakan ya tuno mata da mafarkin ta.

Sai tayi murmushi tace; "ina yake My Dr ina son ganin shi, na san duk inda nake zai kasance a wajen?", Sumayya ta ƙaraso kusa da ita tace; "Mummy Abdul barci yake yi yanzu ko kina so a tashe shi ne?".

Ta girgiza kai da sauri tana lumshe idanu sai dai cikin sauri ta buɗe su sannan ta sauke kan Fadila wacce kanta ke manne da plaster, a hankali kuma komai ya fara dawo mata cikin kai.

Cikin sauri Brr Farida ta fara yunƙurin miƙewa amma Dr Abubakar ya hanata, gaba ɗaya ta ruɗe tana faɗin; "shikenan sun kashe mishi shi".

"yanzu meya faru dashi ya mutu ko?, na dena ganin shi?", magan-ganu dai kala-kala, ganin bata hayyacin ta yasa Dr Abubakar riƙo ta jikin shi ya rungume ta saki kuka me ƙarfi.

Kowa yana tausaya mata, Abban Fadil sai da jikin shi yayi sanyi sanin irin ƙaunar da take yiwa ɗan nata, ya kalli gadon da Abdul ɗin ke kwance kamar gawa.

Malama da Saleema kuwa duk idanu ya kumbura tsabar kuka, Hajja ce ma dai ta dai yi hawayen amma ba kamar su ba dan itama yadda tazo ta same su abin ya bata mamaki.


#LIKE
#SHARE
#COMMENT


*babyn abdul maman meenal elham da farouk*



*ƳAR MUTAN ZAZZAU*




♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

*Ga masu cewa ina jan littafin ne dan na samu kuɗi, Wallahi ba haka bane domin kuwa da ina son siyar da littafi da tuni nayi sai dai ina so ku sani kuɗin ku bashi ne a gaba na, duk wanda ya ɗauki wani abu ya bani ya bani dan raɗin kanshi ne ba wai dan na tambaye shi ba, hasalima kyautatawa ce tsakani na dasu, rubutun novel buri na ne dan haka bana fatan ko gaba nayi novel ɗin siyarwa, na gode sosai to ai hikenan😉*.

*Godiya ta musamman ga Zuciya ta, da kuma Matar so ina miki son so sannan ina jin daɗin sharhin ki sosai Shabihaty fans club kuna ƙarƙashin zuciyar One Love*



*Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai*




📖📖31-32📖📖

*UNGUWAR SARKI,KADUNA*

Cikin sauri ya buɗe idanun shi yana faɗin; "innalillahi wa'inna ilaihir-raji'uun", ƙoƙarin miƙewa yake yi Brr Farida ta riƙo shi cikin sauri.

ya rungumeta yana sakin ajiyar zuciya, Brr Farida kuwa harda ƙara ƙaƙumeshi hawaye yana saukowa daga idanun ta.

Tameer ya shigo tare da likitan da yaje kira, sai a lokacin suka saki juna allurar barci ya kuma yi mishi babu ɓata lokaci barcin ya kuma kwashe shi.

Hajja tace; "tunda yayi barci bari muzo mu tafi Allah ya ƙara sauƙi, Mus'ab(Abban Fadil) ka tashi muje ka sauke mu a gida".

Haka ba dan sun so ba suka miƙe dukkan su, bayan sun tafi Brr Farida ta kalli Surayya tace; "kuma ku wuce gida, na san zuwa anjima zasu sallame mu", haka suma suka tafi cikin jimami Sameer ya tafi kai su.

Ya rage saura Tameer da Brr Farida da Dr Abubakar, hakan yasa wajen yayi shiru, ita dai Brr Farida tana riƙe da hannun Abdul ƙam-ƙam kamar za'a ƙwace mata shi.

Lokaci zuwa lokaci take sauke ajiyar zuciya, kallon shi take cikin tausayawa tabbas da saka hannun wani a wannan lamarin to waye kenan?.

Amsar da ta kasa samu kenan, bata da tabbacin wanda take zargi domin kuwa bata da wata hujja.

Kamar ance ta ɗaga ido ta kalli saitin window idanun ta ya hasko mata dattijon dake tsaye jikin window.

Ƙara zaro idanu tayi gabanta yana dukan uku-uku, shima kuwa ganin ta hango shi yasa yayi saurin barin wajen.

Brr Farida ta miƙe a kiɗime, Dr Abubakar da be san meke faruwa ba yace; "My Brr ina zuwa kuma?", ta bashi amsa yayin da take ficewa daga ɗakin; "ina zuwa".

Sauri take yi kamar ƙafarta zata tsinke ta fice ta zagaya bayan window ɗin, sai dai kash baya wajen nan ta hau jefa idanu tana neman ina zata ganshi.

Har bakin get taje neman shi sai dai Allah be bata sa'ar ganin wanda taje nema ba haka ta gama zagayen asibitin ta dawo.

Tana daf da shiga ɗakin idanun ta ya sauka a kanshi, da sauri ta ƙarasa kusa dashi, shima kuma ita yake kallo fuska gwanin tausayi.

*MUSTAPHA ABUBAKAR TUGE* sunan data ambata kenan a bayan ta iso kusa dashi, ya kalli mutanen wajen sannan ya maida idanun shi kanta itama ta kalle shi ta ɗaga gira ɗaya.

"ko nace Mustapha Sulaiman harɗo, wanne yafi dai-dai? Yadda kake da fuska biyu hakama sunan ka yake".

Alhaji Mustapha ya kalli kanshi ya ƙara kallon jama'ar wajen yana da tabbacin dan basu gane ko waye shi bane da yanzu sun cika wajen dan kowa ya san shi a faɗin garin kaduna kai kaf Nigeria yana ɗaya daga cikin masu kuɗi na farko-farko, gashi kuma da taimakon jama'a sosai wannan ya ƙara mishi farin jini.

Cikin kwantar da murya yace; "Brr dan Allah kizo muje garden ina so muyi magana dake".

Brr Farida tace; "babu magana tsakani na da kai domin babu abinda ya haɗa ni da kai", ta ƙarasa cikin ɓacin rai.

Ya sauke ajiyar zuciya sannan yace; "naji ance Murad yayi hatsari ne shine nazo duba shi, naga jikin nashi ma da sauƙi hankali na ya tashi sosai ina ƙasar Mali labarin yazo mini", ya ƙarasa fuskar shi ɗauke da damuwa.

Brr Farida ta taɓe baki sannan tace; "kamar da gaske yadda ka maida fuskarka sai kace na Allah, to bari kaji kana ɗaya daga cikin prime suspect ɗina kuma zan yi bincike matuƙar da saka hannun ka akan abinda ya sami Abdul bar ganin kana da kuɗi zan tarwatsa farin cikin ka ne".

"haba Farida ya kike magana haka, kada ki manta nine mahaifin Murad ba zan taɓa iya cutar dashi ba, waccen ma baki fahimta bane kuma Fiddausi ma..........".

"dakata ya ishe ni haka! Ka tabbatar ka bar wajen nan domin dai ka sani koda wasa ba zan taɓa bari kaje kusa da ɗana ba ko?, Sannan nayi maka gargaɗi ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba akan ka fita harkata nida ɗana kaƙi ji ko? To wallahi zan ɗauki babban mataki akan ka", tana gama faɗar haka ta shige ta barshi a tsaye.

Alhaji Mustapha ya tsaya cike da takaici gashi yana so ya ga lafiyar ɗan shi amma babu dama, ya kalli kayan dake jikin shi riga daban wando daban sai hula irin taɓani kaji hadisin nan, wannan duk yayi ne dan yazo yaga lafiyar yaron nashi amma abu be yiwu ba haka ya tafi.

Brr Farida kuwa tana shiga ta sauke ajiyar zuciya sannan ta dai-daita natsuwar ta kafin ta ƙarasa inda yake.

Abdul daya farka yana tambayar ina Mummyn shi ganin ta yasa ya danyi murmushi amma be samu martani ba zama kawai tayi gefen gadon.

Ya ɗora kanshi saman kafaɗar ta, ita kuma ta lumshe idanu har yanzu ƙirjin ta be bar bugawa ba, Dr Abubakar ya zuba mata idanu kawai ganin yadda fuskar ta tayi ya san akwai abinda yake damun ta.

Sun jima a haka sannan likitan ya shigo, yayi murmushi yace; "da alamu dai wannan jinyar ta ƙare ganin yadda majinyacin ya zama ɗan lele", duka suka yi murmushi banda Brr Farida.

Nan ya bashi magunguna sannan ya fice, da ƙyar aka samu ya sha maganin sai shagwaɓe fuska yake yiwa Mummyn nashi ganin yadda fuskar Brr Faridan yake yasa ya koma serious.

Sai da ta gama bashi sannan yace; "First love lafiya? Meke damun ki?", ta riƙo hannun shi sannan tayi yaƙe tace; "kada ka damu babu komai me zai dame ni bayan ɗana ya buɗe idanun shi bayan doguwar sumar da yayi".

Yinin ranar haka Brr Farida tayi shi sukuku domin kuwa motsi kaɗan sai taga kamar Alhaji Mustaphan zai dawo inda suke yazo ya cutar mata da ɗa.

******** ***********

*HAYIN RIGASA, KADUNA*


Kwanci tashi babu wuya gashi Allah ya nuna mana lokaci domin kuwa yau saura sati ɗaya bikin su Nusreen, duk ɓangaren uku shirye-shirye suke babu kama hannun yaro.

Nusreen a lokacin idan ka ganta kamar ka sace ta ka gudu tsabar kyawun da tayi saboda ta tsaya sosai Aunty ta gyara ta kuma yadda ya kamata jikin ta har wani sulbi yake yi ga wani yelo-yelo da tayi tsabar haske da dilka data sha.

Saɓanin Nusram da tayi baƙi ta rame sai idanu zuru-zuru, irin farin cikin nan da amarya take yi kam to banda Nusram domin kuwa tunda satin bikin ya kama ta tabbatar da cewa auren za'a yi mata da Alhaji Baballe ta kwanta zazzaɓi ya rufe ta.

Yanzun ma tana kwance jikin ta yayi zafi rau, sai rawar sanyi take yi Nusreen ta shigo ita da Yasmin ƙawarta, sun dawo daga rabon kati duk wani wanda ya kamata su kaiwa to suna ta ƙoƙarin kai mishi.

Gaba ɗaya hidimar daya kamata ayi ta da Nusram sai Yasmin ce ta wakilce ta, Halima ma tazo duk da ba sa'ar su bace amma takan taimaka musu wajen yin hidimar bikin.

"wallahi na gaji sosai gashi gobe ma sai mun sake fita", Nusreen ta faɗa tana ƙoƙarin zama gefen katifar da Nusram ke kwance.

Yasmin tace; "ai gobe kinga Hayin banki zamu shiga sai kuma Shaheeda da take Unguwar Sarki shikenan sai mu dawo".

Nusreen ta yamutsa fuska tana faɗin; "nifa dan dai kin matsa ne amma da bazan wani kaiwa Shaheeda ba", Yasmin tace; "aikuwa ya kamata, dan Shaheeda tana da ƙoƙari kuma ta gayyace ki bikin yayan ta, dan dai kin ƙi zuwa ne".

Nusreen bata ce komai ba sai hannu data kai kan jikin Nusram; "kai Ram jikin ki zafi fa baki da lafiya ne?".

Nusram ta ɗaga kai kawai hawaye na zubo mata, Nusreen tace; "to kin sha magani", nan ma Nusram ta ɗaga mata kai kawai, "Allah ya baki lafiya to", Yasmin tace; "ameen dai".

Nusreen ta miƙe taje ta zubo musu abinci ta kawo nan suka fara ci, ita dai Nusram zazzaɓin banda ƙara rufe ta da yayi ga wahala, shaƙar ƙamshin abincin da taji amai ya taso mata.

Tayi ƙoƙarin miƙewa ta fice daga ɗakin tana ƙarasawa bakin famfo ta fara sheƙa amai me wahala domin kuwa babu komai a cikin ta wanda zata fitar dan rabon data kai abinci bakin ta tun jiya da rana shima sai da Nusreen tayi kuka a gabanta sannan ta yarda ta ci da dare kuwa tun kan Nusreen ɗin ta fara kuka ita ta fara domin bata son cin komai dan ɗaci yake yi mata sosai.

Aunty dake tsaye a ƙofar ɗaki suna lissafin kuɗi da alama matar da zata yi musu dubulan da cin-cin ne tayi saurin ƙarasowa kusa da Nusram ɗin tana yi mata sannu.

Ita ta taimaka mata har ta gyara jikin ta sannan ta wanke wajen tas, ta ƙwalawa Nusreen kira babu ɓata lokaci ta fito.

"kamata kuje ɗaki", Nusreen tace; "to Aunty aman tayi ne?", Aunty tace; "eh wallahi ai inajin Yayan ku yana zuwa zasu tafi asibiti tare".

Mama Jummai dake kusa da murhu kamar koda yaushe tayi shewa tace; "ai amai yanzu ta fara shi kuma muddin ina raye bata ba aure", babu wanda yabi ta kanta.

Da yamma Yaya Sulaiman ya tasa Nusram a gaba suka je wani ƙaramin asibiti nan aka dubata aka bata magun-guna suka dawo gida.

********* ***********

*MAƘARFI ROAD, KADUNA*.

ya zauna yana me ajiyar zuciya, meke faruwa ne, shi kanshi baya da tabbas ɗin abinda yake faruwa yanxu".

Ɗayan mutumin dake zaune kusa dashi yace; "ka kira ni tun ɗazu amma baka ce mini komai ba, meke damun ka ne Tuge?".

Alhaji Mustapha ya sauke tagumin da yayi sannan yace; "Brr Jibril ina cikin tashin hankali, ɗana baya da lafiya yana asibiti".

Saura kaɗan tray ɗin da matar ta shigo dashi a hannu ya faɗi, yar kyakkyawa da ita baƙa mara tsayi, kana ganin ta zaka tabbatar da cewa itace matar gidan.

Sai da ta dai-dai ta natsuwar ta sannan tayi sallama ta shiga, kusa da Brr Jibril taje ta ajiye tray ɗin sannan ta matsa kusa da mijin nata tana miƙa mishi hannu, yayi kissing hannun.

"Abban Khausar zan koma wajen aiki domin yanzu muka yi waya da Md yace nazo da sauri", matar ta faɗa.

Alhaji Mustapha yace; "a dawo lafiya", daga haka ta fice cikin sauri.

Brr Jibril yace; "ya jikin nashi fatan da sauƙi dai ko?", Alhaji Mustapha ya ɗaga kai yace; "da sauki sosai sai dai Brr Farida bata barni na ganshi sosai ba".

Brr Jibril yace; "kada ka damu Alhaji wata rana komai zai zamo me sauƙi insha Allahu ka dage da addu'a kawai".

"Brr Jibril tana zargina da yunƙurin kashe ɗan dana haifa", Alhaji Mustafa ya faɗa cike da damuwa, Brr Jibril yace; "kada ka damu just pray", yayi mishi sallama sannan ya fice.

Cikin tashin hankali take tuƙi, bata ma jira masu tsaron lafiyar nata ba, sai da ta gangara can wajen Kaduna by pass sannan ta gangara zuwa wani gidan gona.

Tayi horn me gadi yazo ya buɗe mata sannan ta shiga, tana yin parking sannan ta fito daga motar kamar zata tashi sama tana shiga ciki ta sami kujera irin ta shaƙatawa ta zauna.

Mutumin dake cikin ruwan tare da wata mace suka fito a tare, duka kallon ta suke yi cikin alamun tambaya.

"Abdus-samad be mutu ba", ta faɗa cikin takaici, ɗayar tayi murmushi tace; "na san da hakan ai tun jiya dan har su Malama da Hajja sun je dubo shi".

Mutumin yayi dariyar mugunta sannan yace; "aikin Razor beyi ba, dan haka na tura Scorpion da saƙo zuwa gare shi".

Dukkan su sun san saƙon kona meye dan haka suka yi murmushi, Mutumin yaja kujera kusa da Matar ya zauna sannan ya riƙo hannun ta yace; "Salma kada wannan abin ya ɗaga miki hankali, Abdus-samad zai mutu dole ne wannan koya so ko be so ba domin babu wanda ya isa ya hanani kauda shi daga bayan ƙasa".

A'a bawan Allah akwai Allah fa, kuma dama idan kwanan mutum ya ƙare ai dole ya mutu😏.

Hajiya Salma ta saki ajiyar zuciya sannan tace; "tabbas hakane amma Alhaji Sa'eed ina tsoron abinda zai biyo baya, bana so mustafa ya mutu ace bani zan gaji dukiyar shi ba ni da yarana kawai nake so su gaji ɗumbin dukiyar shi".

Alhaji Sa'eed yayi murmushi yace; "kada ki damu ke da ƴaƴan ki kawai zasu gaji dukiyar Tuge sai dai zaki san mana nida Baby na", ya ƙarasa yana kanne ido ɗaya.

Salma ta kalli Brr Hauwa suka yi murmushi tare, Alhaji Mustafa yace; "yanzu zan sami biyan buƙata ko?".

Salma tace; "me zai hana sai dai kayi da sauri dan bana so Alhaji ya fahimci daɗewar da nayi gashi ban fito da Securities ba".

"ba matsala just one hour ma yayi", ya faɗa yana riƙo ta daga nan suka shige ciki inda suka bar Brr Hauwa zaune a wajen tana shan iska.

Alhaji Mustafa kuwa ya jima kafin ya tashi ya fito, a falo ya sami yaran nashi guda biyu da Khausar babbar kenan wacce a satin nan ta dawo daga ƙasar Singapore inda take karatun likitan mata, sai mai bi mata Khaleesat wacce take NIGERIAN TURKISH INT ABUJA, tana secondry.

"Yauwa Daddy dama maganar shopping ɗin da muka yi", Khaleesat ta faɗa cikin shagwaɓar yaran masu kuɗi.

"yanzu duk kuɗin dake account ɗin ki Khaleesat sai kin tambaye ni?, kije wajen Habu ya kaiki zan miki tranfer yanzu".

"yauwa amm.......", yayi saurin dakatar da Khausar dake ƙoƙarin yin magana yace; "ina buƙatar hutu", daga haka ya wuce kawai.

Khausar ta taɓe baki, Khaleesat kuwa murna sosai tayi sannan ta haye sama inda ta hau shiryawa domin tafiya siyayya ɗin.

Sai bayan magrib sannan Hajiya Salma ta dawo, sai da ta shiga nata ɗakin tayi wanka ta sake shiryawa cikin riga da skirt ɗin material me kyau da tsada sannan ta fito.

Kitchen ta shiga ta haɗa Coffee sannan ta nufi sama inda ɗakin me gidan nata yake.

Ta shiga da sallama, yana yin waya ne dan haka koda ta ajiye sai ta nemi waje ta zauna, Alhaji Mustafa ya kalle ta sannan ya miƙe ya fice daga ɗakin, Hajiya Salma ta taɓe baki.

"Alhaji Mustafa ka bani mamaki yanzu har kaine zaka iya zuwa dubo ɗan ka ba tare da sani na ba".

Alhaji Mustafa yayi jim sannan yace; "amma dai Alhaji Sa'eed ka san da cewa yaron nan shi kaɗai ne ɗana namiji ko, sannan kuma dole sai na shiga jikin su sosai kafin na iya aiwatar da umarni Oregbu a kanshi".

Alhaji Sa'eed yayi murmushi sannan yace; "hakane kuma tabbas, yanzu ya jikin nashi", Alhaji mustafa ya sauke ajiyar zuciya yace; "Brr Farida bata barni na shiga ba".

"toh! amma dai ina so na ƙara tuna maka da cewa saɓawa umarnin Oregbu dai-dai yake da ɗaukewar numfashin ka dan haka kada son ɗanka ya saka ka saɓa mishi".

Alhaji Mustafa kamar zai zubar da hawaye yace; "na sani kuma zan aikata hakan insha Allah", daga haka ya katse wayar.

Ya jingina da jikin steps ɗin yana sauke ajiyar zuciya, ya zai yi ne?, ɗan shi ƙwara ɗaya tal wanda yake tsananin ƙauna shi zai bawa Dodo ya sha jinin shi, meya saka tun farko ma.yayi wannan alƙawarin".

Oho maka dai kai ka sani😏 Me kan gwanda.

Aishatu Babayo ta ranƙwashe ni tace; "idan kika kushe shi ai kamar kin kushe Abdul ne baki ganin kamar su ɗaya".

Na taɓe baki ina me ƙare mishi kallo, tabbas abinda Zuciya ta(Aishatu Babayo) ta faɗa gaskiya ne kamar su ɗaya da Abdul bambamcin su kawai girman jiki dan Alhaji Mustafa ya ɗan manyan ta.


*Na san wasu zasu ce yau kuma ina One love ta tafi, naji sabbabin suna to ai dama sabbabin suna ba xasu ƙare a buk ɗin nan ba har sai mun kai tsakiya ko ince kusa da ƙarshe sannan ba lallai ku fahimci littafin ba sai munje ƙarshe shima ko.ince tsakiya, fatana dai kuyi haƙuri ku cigaba da bina duk da dai na san ina muku ƴar zilliya amma kamawa tayi ina kuma ƙara baku haƙuri domin kuwa na san cewa kuna haƙuri sosai*.


#LIKE
#SHARE
#COMMENTS

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*

♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*


📖📖33-34📖📖


*UNGUWAR SARKI, KADUNA*.

Sai da Abdul ya ƙara kwana biyar a asibiti sannan aka sallame shi, kuma Alhamdulillahi jikin shi yayi sauƙi sosai da sosai.

Sameer ya kaisu har gida inda ya tarar da su Suraiya suna mishi barka da dawowa, yaji daɗi sosai hakama Brr Farida ita da Dr Abubakar duka sun ji daɗi.

Ɗakin shi ya wuce yayi wanka sannan ya kwanta domin ya huta, sai dai kanshi da yaji yana sara mishi wanda hakan yasa barcin yaƙi zuwa.

Ya jima a kwance kafin wayar shi ta hau ƙara, ya ɗauko ya kara a kunne, "yallaɓai y gida ya aiki?", dama cewa nayi bari na tuna maka ɗaurin aure na 28th Feb 2020, nan da jibi kenan".


*************************⬇**********************
************* Top Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.thn.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > [email protected]

******* FOLLOW US ******

Facebook: Top Hausa Novels

Twitter: Top Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/tophausanovels

Telegram Group: https://t.me/tophausa


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na TOP HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Top Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************



Abdus-samad yace; "insha Allahu ba zan manta ba zan zo kuma", Shureim yace; "yauwa nagode sosai na bawa Fahad IV zai baka".

Yace; "shikenan, sai anjima", daga haka suka yi sallama, be jima ba barci ya kwashe shi.

Sai wajen la'asar ya farka, yayi alwala ya rama sallar dake kanshi sannan yayi wanka ya fito, a falo ya sami Fadila da Surayya suna fira.

Duka suka yi mishi sannu da jiki ya amsa shima, waje ya fita kawai inda ya tarar da Sumayya

Please Login or Register in order to submit comment