Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da Tameer a zaune.

"barka da fitowa Yah Abdul ɗazu ai naje wajen ka amma kana barci sai na ƙyale ka", cewar Sumayya, Abdus-samad yayi murmushi yace; "hakane, Yaya Tameer barka da hutawa".

"barka ya jikin", ya tambaya, sai da ya shafa gashin kanshi sannan yace; "da sauki", daga haka babu wanda ya kuma magana a tsakanin su.

Abdul yana zuba musu idanu da alama fira suke yi akan wani abu me mahimmanci, "Yaya ni ina ganin kawai ka sami Daddy da maganar".

"kin san halin Mummy shiyasa nake so ki fara sanarwa da Daddy ke da kanki idan yaso sai ni nayi mata magana daga baya", Sumayya tayi dariya tace; "to Yaya na".

"tunda kina son a fita dake anjima ba", ta kuma yin dariya tace; "Yaya ai kaima buƙatar kanka ta tashi", yace; "to ya isa haka".

Motoci suka fara shigowa gidan dan haka duka suka maida hankalin su kan motocin, sai da suka gyara parking sannan Brr Farida ta fito ita da mijin ta.

Abdus-samad ya miƙe da farin ciki ya tare ta, ta mishi peck a goshi sannan tace; "ka gama barcin kenan?, na shiga wajen ka ai Daddyn ku na raka wajen wani tsohon abokin shi wanda ya kusa aure".

Duka suka yi dariya, Brr Farida ta harare su duk suka yi shiru banda Abdus-samad, tace; "kai kuma ba zaka dena ba kenan?".

Ya ɗora yatsun shi biyu saman leɓen shi, Tameer yace; "saboda Allah me sa'an Daddy zai yi da mata?", Brr Farida tace; "sai kaje ka tambaye shi".

Abdus-samad ya kauda kai gefe yace; "ni tsorona ma ace tare da Daddy zasu angwance, dan maza ba abin yarda bane".

Brr Farida ta kalli Dr Abubakar da sauri, cikin sauri ya girgiza mata kai yana faɗin; "me zan yi da wata amarya a yanzu ai ke kin ishe ni".

Brr Farida tace; "kai dai ka sani wallahi ka sake ka ƙara aure kai da matar sai na maka ku kotu", suka kwashe da dariya, cikin jin haushi ta shige cikin gidan ta barsu.

Dr Abubakar ya gallawa Abdus-samad harara yace; "kana neman janyo mini tashin hankali ko", ya saukar da kanshi ƙasa yace; "yi haƙuri Daddy", ya rasa me yasa duk soyayyar da mahaifin nashi yake nuna mishi baya iya sakewa dashi kamar yadda yake sakewa da Mahaifiyar shi, sai ya dinga jin nauyin shi sosai.

Nan ya zame yayi part ɗin shi ya barsu suna cigaba da yiwa Daddy dariya dan haƙiƙanin gaskiya ya kasa shiga gidan.

******** *************

Baba ya gyaɗa kai bayan ya gama sauraren bayanan Ummi sannan yace; "Maman Kubra wa'innan yaran ƴaƴa na ne dan haka ki fita daga cikin wannan maganar".

Ummi tace; "ni dama ba wani abu nace ba gani nayi ita waccen ba lafiya ta cika ba.......", be bari ta ƙarasa ba ya katseta.

Cikin tsawa yace; "sai akayi me kuma? Nawa ake kaisu gidan miji basu da lafiya?", Ummi ta girgiza kai sannan tace; "maganar gaskiya fa ba son auren nan take yi ba kawai ina gani a fasa shi, don gaskiya bana so tayi irin wannan auren".

Baba ya ɗauke ta da mari hagu da dama, hakan ya janyo hankalin dangin ta da dangin shi wanda suka zo daga Dabai, sun ɗauka shawara suke yi a tsakaninsu amma zuwa yanzu sun fahimci cewa faɗa ne suke yi.

Inna Gaje( Ƴa ga me gari wacce take kamar ƙanwa a wajen Abdullahi), ta ƙaraso da sauri tana faɗin; "ashsha meya kawo faɗa kuma yanzu".

Baba ya nuna Ummi yace; "wallahi kar ki ɓata mini rai idan ba haka ba zaki sha mamaki na, kuma ki sani aure babu fashi matuƙar baki goyi bayan shi ba to zaki bar garin nan ki koma Dabai kuma ba'a matsayin matata ba a matsayin bazawara dan wallahi duk wanda ke adawa da wannan auren zan iya rabuwa dashi ko waye, kuma itama munafikar ki fada mata matuƙar ba zata mini biyayya ba to ta tattara kayanta ta bar mini gida kuma ta nemi wani uban dan babu ni babu ita".

Nusram ta fashe da kuka bayan sauraren bayanin Baban, Ummi ta share hawayenta tace; "kiyi haƙuri kinji", Nusram ta ɗaga mata kai kawai domin bata da bakin magana a lokacin.

Nusreen kuwa jikin ta yayi sanyi sosai ganin yadda mahaifiyar tasu take zubar da hawaye, wannan wane kalar cin mutunci ne ace a bainar jama'a sai Mahaifin nasu ya nuna basu da galihu.

Aunty ke aikin rarrashin Ummin, tana kuma ƙoƙarin kwantar mata da hankali. Ba jimawa wayar Nusram ta ɗauki ƙara ganin Yaya Sulaiman yasa ta ɗauka.

"fito waje ina jiran ki", abinda ya faɗa kenan ya kashe wayar, Nusram ta miƙe duk da jikin ta babu ƙwari, Nusreen ta miƙe da sauri tana so ta taimaka mata amma Nusram ta dakatar da ita.

"kada ki damu Ya Sulaiman ke nema na a waje", abinda ta bata amsa dashi kenan sannan ta saka hijab ta fita.

A tsakar gida ta sami Mama Jummai da Babbar ƴar ta Habiba sai ƙaramar wacce bata yi aure ba Atika a tsaye suna magana amma suna ganin ta suka dena.

Nusram ta kauda kai domin ita Habiba dai ƙanwar tace amma bata wani birge ta dan yarinyar akwai shige-shigen boka, kwanaki ma garin hakan ne wani ɗan damfara ya damfare ta dubu ɗari uku.

Idan kaje ɗakin ta babu komai ko leda babu amma kuma ta san inda take fito da kuɗin zuwa wajen boka, shi yasa sam basa shiri da Nusram kwata-kwata.

Atika kuwa ta cika girman kai da gani-gani hakan yasa Nusram ko kulata bata yi dama dai waccen ƴar neman rigimar ce amma ita kam ko kallon inda take bata yi.

Dama cikin su masu sauƙin biyu ne Sahura da Ameera sune kuma wa'inda Nusram ke kula su.

Su kuwa duka biyun shakkar Nusram ɗin suke yi hakan yasa basa shiga sha'anin ta, ko kwanaki sai da Nusram ɗin ta kama Atikar ita da wani ɗan iskan yaro suna taɓe-taɓen su, hakan ya tsorata Atikar amma taga koda ta dawo gida Nusram ɗin ko kallon ta bata yi ba haka duk ƴan gidan babu wanda yayi mata magana hakan yasa take ƙara shakkar ta( rashin kula ɗan iska da mara kunya ya kan ƙara maka kwarjini).

Habiba tabi bayan ta da harara tana me jan tsaki, Mama Jummai tace; "barta duk ta gama iyayin ai na yau ne".

Habiba tayi dariya tace; "ina fa wani iyayi mutum ya kuma kamar tsinke", Atika tace; "ina jin iskancin da take yi ne acan ta samu HIV", suka kwashe da dariya.

Habiba ta ciro ƙullin magani guda ɗaya da turare da kuma laya guda ɗai-ɗai, ta ɗaga maganin tace; "wannan yace duk yadda za'ayi a tabbatar Baba yaci a cikin abinci yau da daddare".

Ta miƙawa Atika turaren tace; "wannan kuma ke ce zaki shafa shi yanzu idan Alhaji Baballe yazo kije ki gifta ta gaban shi abinda ake buƙata kawai yaji ƙamshin, sai wannan layar ita kuma ki sami kusa da rijiya anjima bayan kowa yayi barci ki haƙa ki saka ta a wajen shikenan aikin".

"yace da zarar Baba yaci abincin nan to zai ƙara tsanar ta ne sannan duk abinda kika ce zai aikata, shi kuma Alhaji Baballe da zarar yaji ƙamshin wannan turaren to duk abinda Baba yace mishi zai aikata, yadda layar nan take a binne haka bakin shegiyar zai ɗaure ba zata iya ƙaryata komai ba haka kota ga Bangis ba zata mishi ihu ba", suna gama jin bayanan Habibar suka shewa.

"wato na lura Habiba kin fini tsanar wa'innan yaran, shi yasa kika fi waccen soloɓiyon".

"ai dole nayi kishi dasu kinga akwatin ɗazu da ina ganin saura kaɗan jini na ya hau, barin ma na Nusram goma sha biyu fa kai dole ma su koma na Atika".

Mama Jummai ta kuma washe baki tana faɗin; "yauwa ƴar albarka haka nake son ji daga bakin ki", Atika kuwa sai faman murna take yi jin duk wa'innan uba uban kayan zasu koma nata.

A saman sabuwar motar shi ta same shi, shima dai Yaya Sulaiman ɗin saura kwana ashirin da biyar nashi bikin shi, tayi sallama ya amsa mata yana binta da kallon tausayawa.

"Nusram wai me yasa ba zaki rungumi ƙaddarar ki ba kiyi haƙuri ko Allah zai baki lada, haba Nusram kamar ba musulma ba".

Hawaye ya zubo mata, cikin sheshsheƙar kuka tace; "Ya Sulaman nifa na haƙura kuma na yarda da duk abinda ya same ni daga ubangiji ne sannan ina neman lada a wajen shi, sai dai wasu abubuwan ne dole naji takaicin faruwar su".

Yace; "ya isa haka, be kamata ace har yanzu kina zubar da hawayen ki ba, ki zama jaruma mana", ta jinjina kai tana goge hawayen fuskarta.

Yace; "yauwa ko kefa, yanzu amshi wannan ɗinkin ku ne wanda zaku saka gobe akwai shadda a ciki kalar brown ita zaku sa da rana anko ne gaba ɗayan mu", ta amsa da to tana mishi godiya.

Ya ɗan ja ta da fira har ta sake tana maida mishi da fara'ar ta, kan wani lokaci ma har ta soma kwasar dariya, tabbas Sulaiman ya taka muhimmiyar rawa a rayuwar ta Nusram.

Koda su Shureim suka zo Nusreen ta fito wajen su, tayi mamakin hangen ƴar uwar tata tana fira da dariya, tunawa da cewa a gidan su Sulaiman ɗin ta taso kuma tare suka taso yasa ta taɓe baki ta wuce.

Nusram kuwa da yake ƙofar gidan da jama'a hakan yasa bata ma lura dasu Shureim ɗin ba, sun jima suna tsaye sannan motar Alhaji Baballe ta karyo kwanar layin.

Duk ƴan wajen sai da suka bi motar da kallo don ta haɗu sosai daka gani ka san mamallakin ta ya ci ya sha ya tada kai.

Shi kuwa Alhaji Baballe hasko Nusram da yayi tana kwasar dariya ba ƙaramin ɓata mishi rai hakan yayi ba, wato dalilin da ya saka tace mishi ta yafe zuwan da zai dinga yi wajen ta kenan.

Cikin jin haushi ya fito daga motar, Nusram ta kalli Ya Sulaiman tace; "bari naje wajen Alhaji na dawo", yana tsokanar ta tana dariya haka ta bar wajen.

"waye wancan ɗin", ya tambaya cikin fushi da kuma yatsinar fuska, Nusram ta kuma kai kallon ta kan Ya Sulaiman daya ke danna wayar ta da alama wani abu yake kallo ganin yadda ya ɓata fuska kuma ya natsu.

Ta juyo ta kalli Alhaji Baballe rai ɓace bata taɓa jin haushin titsiya ba sai yau bata sani ba dan ko babu ɗigon son Alhajin a ranta bane oho, tace; "Yaya na ne".

Alhaji Baballe yace; "shine kuma sai ku fito titi kuna fira kamar wasu saurayi da budurwa", tsabar haushi da takaici Nusram kasa cewa komai tayi.

Sallamar Atika yasa ta ɗago tana kallon ta, taci kwalliya cikin atamfa doguwar riga da wani siririn mayafi saman kafaɗar ta, fuskar ta kuwa taci kwalliya sosai ga wani uban turare da ta saka wanda saura kaɗan kan Nusram ya juya.

Cikin kissa ta tsugunna tace; "ina wuni Alhaji", ya amsa yana kallon fuskar ta, ta saki murmushi ta maida kallon ta zuwa Nusram tace; "Aunty Nusram waccen ne ya aiko ni".

Nusram tabi inda Atikar ta nuna da kallo wani gajere ta hango sai dai bata gane ko waye ba kasancewar wajen babu haske dan haka bata ganin fuskar shi.

Atikar tayi murmushin mugun ta tace; "gashi yace in baki", ta ƙarasa tana miƙo takardar hannun ta wacce take linke.

Nusram ta saka hannu ta amsa ta dube ta tace; "Atika waye wancan ɗin", cikin salon munfinci tace; "Aunty wannan saurayin naki ne fa wanda kuke yawan fita tare dashi wanda kwanaki Baba ya mishi gargadi akan ya dena zuwa ƙofar gidan nan saboda ya kamaku tare a zaure kuna aikata abinda be kamata ba, bayan anyi haka kika gudu wajen shi har kika kwana biyu har Baba yasa aka je aka kama shi da ƴan sanda to ya ce mini ɗazu aka sako shi shine ya sami labarin za'ayi auren ki, shine yazo".

Kan Nusram ta gama fahimtar me Atika take nufi Atikar tayi gaba da sauri, Alhaji Baballe kuwa jin abinda Atika ta faɗa yasa yayi saurin fizge takardar daga hannun Nusram ɗin.

Cikin fushi ya ɗago bayan ya karanta wasiƙar yace; "lallai kin cika ƴar iska amma duk da haka bari kiji abinda zan faɗa miki auren ki dai ba zan fasa ba kuma ki kuka da kanki idan kika shigo hannu na, kada ma kiyi ƙoƙarin cewa kin fasa domin kuwa kuɗin da mahaifin ki ya ci mini ba zai taɓa iya biya ba har ƙashen rayuwar shi dan haka auren mu babu fashi". Yana faɗar haka ya ciro bandir ɗin ɗari biyar-biyar guda uku ya cilla mata yace; "gashi nan kuɗin da zaki yi amfani dashi ne gobe tunda kince bakya buƙatar komai na biki", yana gama faɗar haka ya wuce ya barta.

Har ya shiga motar shi ya rufe ƙofa sai kuma ya buɗe ya cillo mata takardar sannan ya maida ƙofar ya rufe ya figi motar tashi ya bar wajen.

Nusram ta saki kuka tana tsugunnawa a wajen, ga mutane duk a wajen har sun fara cece kuce, Ya Sulaiman yazo ya ɗagota sannan ya tsugunna ya kwaso mata kuɗin da takardar.

"Nusram kiyi haƙuri, kada wa'innan abubuwan dake faruwa su dame ki, ki sani bayan wuya sai daɗi kuma a dukkan tsanani akwai sauƙi na faɗa miki wata rana sai komai ya wuce kamar ba'a yi ba", Nusram ta gyaɗa kai kawai.

Kuɗin ya zuba a aljihu sannan yace; "zan je na ajiye wa'innan kuɗin ba zaki taɓa ko biyar ba, duk abinda kike buƙata kiyi mini magana zan kawo miki amma bana so kiyi amfani da komai na Alhaji Baballe".

Takardar ya linke bayan ya gama karantawa sannan yace; "zan ajiye takardar itama kada kuma ki faɗawa su Ummi wannan abin kinji", ta ɗaga kai.

Hannu ta kai tace; "dan Allah ka bani na karanta", ya miƙa mata takardar:-

*Assalamu Alaykum, zuwa ga masoyiyata Nusram, ki sani na fito ɗazu daga cell kuma naji yadda tsohon ki yake son rabani dake, dan haka na yanke shawarar gobe zan zo mu gudu da daddare dan haka ki shirya komai naki zan zo sai mu gudu kawai.*

*daga Bangis(ur love)*

Nusram ta miƙawa Yaya Sulaiman takardar kawai domin kuwa ta san ba zata fahimci komai a ciki ba dan bata san inda maganar ta dosa ba.

Shureim kuwa ganin abinda ya faru yasa suka sallami Nusreen da sauri ganin yadda hankalin ta ya koma kan ƴar uwarta.

"Ram meya faru ne tsakanin ki da wancan ƙaton?", Nusreen ta tambaya bayan ta ƙaraso kusa dasu.

Yaya Sulaiman ya galla mata harara sannan yace; "wuce ki bar nan wajen", ta wuce tana ƙunƙunai har ta shige gida.

Yaya Sulaiman ganin ta tafi ya ƙara jawa Nusram kunne akan kada ta sake ta faɗaws ƴan gidan abinda ya faru sannan yace taje ta kwanta domin dare ya fara ja.

Tana shiga zaure taji an fincikota, kanta ya bugu da jikin bango ta saki ihun wahala, sai dai be fita ba domin an toshe mata baki.

Ɗakin Isa dake zaure nan aka hankaɗa ta, ta faɗi ƙasa cikin kiɗima ta juyo tana bin inuwar mutumin da kallo, ɗakin babu haske sosai dan haka bata ganin ko fuskar waye.

Cike da tsoro tace; "waye dan Allah", ba'ayi magana ba sai dai janta da aka yi zuwa ciki kan katifar ɗakin aka cillata sannan mutumin yayo kanta yanzu kam ta gane meke shirin faruwa da ita dan haka suka shiga dambe.

Sun jima a haka yana ƙoƙarin kaita ƙasa amma abu ya faskara, shi kanshi Isan yayi mamakin ƙarfin ta be taɓa tunanin haka take da ƙarfi ba, ƙara ƙaimi yayi inda Allah ya bashi sa'ar cire hijab ɗin dake jikin ta, ya kuma yaga rigar jikin ta.

Ya ɗaga ta ya buga a katifar sannan ya saka ƙafa ya danne ta, haiƙam yake son rabata da kayan jikin ta, Nusram kuwa zuwa yanzu ƙarfin ta yayi ƙasa gashi dama ba wata lafiya ta cika ba wanda dole ta saduda.

Shi kuwa ganin ya sami dama a kanta yasa ya saki jiki sosai yana ƙoƙarin aikata mata abinda zuciyar shi ke raya mishi.

Hannu Nusram ta miƙa Allah ya taimake ta taji ta riƙo wani abu wanda ba zata bambamce kwalbace, ƙarfe ne ko kuma roba bace duk da haka tana fatan ya kasance abinda zai taimake ta ne.

Ragowar ƙarfinta ta tattaro ta hankaɗe shi, ganin hakan ga ƙoshi ga kwanan yunwa ya ƙara harzuƙa Isa dan haka ya ɗauke ta da mari wanda sai da ta kifa, wannan abin ta ɗaga ta kwaɗa mishi a kai iya ƙarfin ta.

Ya saki wata irin ƙara me ƙarfi wacce ta ratsa duka gidan, Nusram kuwa jin hakan yasa tayi saurin dirowa tayi hanyar waje.

Sai dai kanta kai ga fita yasa ƙafa ya taɗiyo ta, ta faɗi a wajen hakan kuma yayi dai-dai da ƙarasowar mutane.

Ɗaki ya gauraye da haske, nan fa Mama Jummai ta saki ihu tayi kan Isa tana riƙo shi tana tambayar shi abinda ya faru.

Babu abinda yake faɗi sai " Nusram zata kashe ni", jin abinda ya faɗa yasa Mama Jummai saka salati.

Tayi kukan kura ta faɗa kan Nusram wacce ke kwance tana sake ƙudundune jikin ta da hijab ɗin ta wanda ta ɗauka bata kai ga sakawa ba.

Aunty taje ta bangaje Mama Jummai sannan ta ɗago Nusram tace; "haba Jummai a sai ki tsaya kiji meya faru".

"wane kalar meya faru? Kina ganin Kaltume zata kashe mini ɗa", Aunty ta taɓe baki tace; "to sai ki bibiyi meya faru tukunna", Mama Jummai zata kuma magana Baba yace; "duka a tafi ɗakin Jummai domin ayi maganar".

"dakata Jummai ba ita bace babba dan haka ɗakin Maimuna za'a je", cewar Baba Sailuba yar Malam Abdullahi.

Haka aka ɗunguma zuwa ɗakin Ummi, aikuwa ɗaki ya cika maƙil dan harda ƴan Dabai wa'inda suka zo biki.

"meya haɗa ka da ƴar uwar ka?", Baba ya tambaya, Baba Sailuba tayi saurin cewa; "a ina ta zama ƴar uwar tashi? Ban sani ba Abdullahi ko kai kayi mata cikin shi a waje?".

Cikin sauri Baba yace; "a'a Yaya wallahi da ɗanta na ganta", Baba Sailuba tace; "yauwa yanzu naji batu ka tambaye shi meye haɗin shi da ƴar sunnah bayan shi shege ne bashi da uba", Mama Jummai ta wulla mata harara.

Isa ya saukar da kai yace; "dama ina kwance ne kawai sai na ga mutum a tsaye a kaina kan nayi wani motsi ta faɗo jiki na tana faɗin wai sai na biya mata buƙata".

Nusram ta girgiza kai hawaye yana zubo mata jin irin sharrin da Isa yake mata, Baba yace; "ni kam na shiga uku yanzu iskancin naki gida ya dawo kenan?, wallahi idan kika cigaba da ɗauko mini magana zan tsine miki kibi duniya".

Nusram hankali tashe ta rarrafo zuwa gaban Mahaifin nata cikin kuka tace; "dan Allah Baba kayi haƙuri wallahi ba haka bane nazo shigowa gida ne shine ya jani ɗakin shi don yayi mini fyaɗe har ya yaga mini riga amma wallahi bani naje ɗakin ba".

Mama Jummai tayi salati tana tafa hannu tace; "yanzu Nusram waye zai miki ƙarya Isa ko waye", Baba yace; "bar shegiya me baƙin hali".

Baba Sailuba tace; "shegantata zaka yi Abdullahi yanzu ɗan shege yafi ɗan sunna a wajenka, lallai ba banza aka barka ba".

Baba yace; "Yaya ki duba wannan lamarin fa", ta ɗaga mishi hannu tace; "ya isa haka Abdullahi maganar yarinyar nan abin dubawa ne be kamata ka goyi bayan ɗaya daga cikin su ba zaka yi dana sani fa".

Nan dai Baba ya tafi yana bambamin shi, Baba Sailuba ta ɗago Nusram tace; "kinji kiyi ta addu'a Allah yana sane da ke", Nusreen ta amshi Nusram ɗin suka shige ɗaki suna kuka.

Ummi kuwa banda hawaye babu abinda takw gogewa Aunty na ƙara kwantar mata da hankali, to dai magana ta shiga unguwa domin kuwa jama'a duka sun ji, wasu sun yarda da abinda Nusram ta faɗa wasu kuma sun ƙarya ta jin abinda ya faru tsakanin ta da Alhaji Baballe ɗazu.

Ranar dai kam gidan ba kowa yayi barci ba wasu hidimar biki wasu kuma ɓacin rai ya hanasu barci ciki kuwa harda Nusram wacce tasha kuka ta godewa Allah.

Washe gari da safe kuwa da ƙyar take buɗe idanun ta saboda kumbura da yayi, Nusreen ma dai idanun ta yayi ja sosai dan itama kwana tayi tana kuka don taya ƴar uwar ta jimami.

Koda Aunty tazo ta same su a kwance nan ta rufe su da faɗa, haka dole Nusreen ta tashi tayi wanka ta shirya don an kusa ɗaurin aure.

Nusram kuwa magani tasha sannan ta koma ta kwanta, ta ɗaga hannu ta kalli lallen dake zane a hannun ta wanda da ƙyar ta bari akayi mata shi sai da Ummi tayi mata kuka sannan ta bari aka yi shi.

A yanzu kam babu abinda ta tsana kalar auren nan nata, ta ɗaga kai ta kalli yadda jama'a ke hada-hada.

Nusreen ake sheƙawa kwalliya me kyau da kuma ɗaukar hankali, Aunty ta shigo ganin Nusram ɗin a kwance yasa tace; "au yanzu baki tashi ba kenan? haba Nusram tashi dan Allah mana", ta ƙarasa tana kamo Nusram ɗin don ta miƙe.

A haka jikin ta babu wani ƙarfi ta miƙe ta ɗauke sosa da sabulu tayi bayi, ta tarar Aunty ta haɗa mata ruwa me kyau da ƙamshi nan tayi wankan sannan ta fito.

A wajen famfo suka haɗu da Atika wani lace ne me tsada ta saka a jikin ta, sosai taci kwalliya zaka iya tunanin ma itace amaryar.

Nusram ta kauda kai gefe batare da tace mata komai ba, Atika kuwa ta saki murmushi na izgilanci tana sakin shewa.

Tana shiga Aunty ta jata zuwa uwar ɗaka nan suka tarar da Safeena tana zaman jiran su dan haka tana shigowa ta fara aikin ta wato kwalliya.

Sadiya ta buɗe ledar kayan da Yaya Sulaiman ɗin ya bata jiya ta ɗauko mata shaddar, doguwar riga ce wacce taji stone work har zuwa ƙasa tayi kyau

Please Login or Register in order to submit comment