Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"akwai abinda kike buƙata ne", Nusreen tace; "dama ɗazu ne naje gaishe da Mamanshi, shine wasu a wajen suke ta mini habaici naga ba zan jure ba na rama shine fa Maman shi ta kira shi ta dinga mishi faɗa wai ita bani take so ba Nusram take so", ta ƙarasa kamar zata zubar da hawaye.

Aunty taja hannun Nusreen suka zauna bakin gado sannan tace; "Nusreen haƙuri akeyi a komai yanzu sannan kada ki sake ki kuma faɗawa kowa abinda ke tsakanin ki da dangin mijinki, domin idan kika faɗa mana zamu riƙe su a ranmu ki koyi riƙe sirrinki sannan ki sani nan da gidanku da bamabanci dole ki koyi haƙuri kinji", Nusreen ta ɗaga kai, Aunty tace; "yauwa Allah ya miki albarka", Nusreen tace; "ameen, kunje gidan Nusram ne Aunty".

"eh ya akayi?, daga can muke muka yo nan", Nusreen ta kuma cewa; "na kira wayar ta ba'a ɗaga ba", Aunty ta miƙe sannan tace; "idan kika cigaba da gwadawa zata shiga ne, sai anjima", ta fice kafin Nusreen ta kuma cewa komai.

Ba tare da Aunty ta koma gidan ba, haka suma yaranta kowa gidanshi ya wuce, Yaya Sulaiman ya dawo wajen goma amma babu sa'a domin dai kwalliya bata biya kuɗin sabulu ba.

Nusram na can a kulle a cell banda kuka babu abinda take yi, ga tunanin halin da ƴan uwan ta suke ciki.

Amarya kuwa bayan tafiyar su Aunty Baba yasa su Hansai suka ɗauke ta sai gidan Alhaji Baballe, buri ya cika domin dai babu abinda aka taɓa na Nusram sai washe baki take yi don ta san ta mori gida sama dana duk ƴan uwanta.

********* ***********

*UNGUWAR SARKI, KADUNA*.

Koda ya shigo gidan washe gari a falo ya sami Sumayya da Fadila suna fira, ganin shi yasa suka yi shiru, yace; "ina First Love?".

Sumayya tace; "tana sama bata sauko ba", ba tare da ya kuma cewa komai ba ya nufi saman, Fadila ta bishi da kallo.

Shigar ƙananan kaya ce kamar koda yaushe a jikin shi, blue ɗin riga anyi rubutu da farin kala a gaba sai wando jeans fari hasken fatar shi ya fito sosai.

Da sallama ya shiga ɗakin, Brr Farida dake duba takardu wanda alamu ke nuna na aikinta ne, ta ɗago ta kalle shi sau ɗaya ta komar da kanta ta cigaba da aikin da take yi.

Ya ƙaraso kusa da ita, kan carpet ɗin yaja filo ya kwanta a gabanta, bata ce komai ba har lokacin, hannu yasa ya ɗauki takarda guda ɗaya amma be gane komai a ciki ba.

Ya taɓe baki sannan ya ajiye, yana kallonta tana aikinta shi kuma ya maida kai kawai ya lumshe idanu.

Har lokaci me tsayi sannan ta gama ta hau tattara takardun nata, ya buɗe idanu yana kallon ta, cikin sauri ya riƙo hannun ta sannan yace; "am sorry", ta balla mishi harara.

Ya cuno baki cikin shagwaɓa yace; "ai na baki haƙuri", Brr Farida tace; "kai baka ji ko? Waye yace kaje kayi magana akan wannan matsalar? Ni bance kada suyi aure ba amma su nemo ƴar babban gida".

"inda First love kike da naƙasu kenan", ya faɗa a cikin zuciyar shi, amma a fili yace; "nima First love ai na kusa auren nan na huta", Brr Farida tayi mishi wani kallo ba tace komai ba ta miƙe.

" matar ka Baby har yanzu ma ba'a ƙerata ba tukunna, ni zan nemo maka matar da zaka aura ƴar babban gida me asali da ji da kuɗi ba wai ƴar talaka ba matsiyaci", jan bakin shi yayi shiru dan ya san idan maganar ta cigaba da tsayi to abin ba zai yi kyau ba.

Be san dalilin da ya saka Mahaifiyar tashi ke tsananta ƙiyayya ga talaka ba, ita dai me kuɗi in dai aka zo batun aure amma kuma sauran mu'amala zata yi da talaka.

wai matar shi ko ƙerata ba'a yi ba?, me hakan ke nufi zai sami jinkiri kenan kamar sauran ƴan gidan kenan?, ya saki murmushi yana shafa sumar kanshi.

Tsakanin kwana biyu da maganarsu Tameer Dr Abubakar ya gama komai daya dace sai dai kuma matsalar shine ta ɓangaren Sameer dake son Fadila.

Dr Abubakar yace a bari sai sun je Family meeting wanda zasu yi ƙarshen wata me zuwa sai a daddale duk da yana cike da tsoron mahaifiyar tashi wato Hajja be san yadda zata dauki maganar ba.

Brr Farida kuwa bata cewa komai game da auren nasu da anyi magana sai dai tace Allah ya kaimu kawai kowa ya fahimci bikin be wani ɗaɗata da ƙasa ba.



#LIKE
#SHARE
#COMMENT



*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.



*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.


♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖39-40📖📖


"ina ganin Mijin Nusreen zai iya taimakawa tunda Mahaifin shi kan ya rasu babban mutum ne shima ta yiwu ya san wasu manya", cewar Aunty.

Yaya Sulaiman ya ɗan yi shiru kafin yace; "shikenan zan mishi magana sai muji yadda za'a yi", yana faɗan haka ya fice daga gidan.

Aunty da Ummi suka bishi da kallo kawai, a ƙa'ida bayan bikin su Nusram da sati biyu za'a yi nashi amma har yanzu basu sami kwanciyar hankali ba, Aunty ma tana maganar a ɗaga ne amma Ummi tace a'a.

Malam Isma'il Mahaifin Sulaiman shima dai duk iya ƙoƙarin shi a yanzu shine Nusram ɗin ta baro hannun Police.

Da ƙyar ya samu yaga Dpo sai da ya bayar da cin hanci ma tukunna sannan ya sami ganin shi, Nan ya bashi bayanin abinda ya kawo shi.

Sosai ran Dpo ya ɓaci, yayi faɗa sosai taya za'a bar mace a cell tsayin wannan lokacin?, nan ya kira wani Sergent akan ya binciko mishi inda aka kai Nusram ɗin.

Ya amsa da to ya fita, Dpo yace; "kuyi haƙuri manyan ƙasan nan ke amfani da wawayen cikin mu ana ɓatawa Police suna, yanzu zanje a fitar da ita insha Allah, kuma duk lokacin da abu makamancin haka ya faru ga number na ka kira ni kawai".

Abba ya amsa yayi godiya sosai, babu jimawa ɗan sandan ya dawo nan ya shaida mishi tana headquarter dake Barnawa.

Dpo ya kalli Abba yace; "tashi muje Alhaji da kaina ma zani domin a fitar da ita", Alhaji Isma'il yace; "to".

Motar Abban suka shiga, nan Abba ya fara neman wayar Sulaiman ɗin domin ya faɗa mishi yadda akayi.

Sulaiman kuwa sai da ya kira wayar Shureim yaji cewa yana gida sannan ya ƙarasa, a harabar gidan ya tsaya nan Shureim ɗin yazo ya same shi, bayan sun gaisa yace; "ba zaka shiga ba, na faɗawa ƙanwar ka cewa kana hanya".

Sulaiman yayi murmushi yace; "sai dai nace ka gaishe ta amma ni ba zan shiga ba don akwai abinda ya kawo ni", Shureim yace; "meya faru?", Yaya Sulaiman ya bashi labarin komai.

Hankalin Shureim ya tashi sosai, ya fara salati yana jimamin abinda ya faru, yace; "bari na shirya sai muje gidan Kwamishinan ƴan sandan kawai".

Yaya Sulaiman yace to, Shureim ɗin ya tafi kenan wayar Sulaiman tayi ƙara, ganin kiran mahaifinshi yasa ya ɗaga da sauri nan ya faɗa mishi yadda suka yi da Dpo ya kuma ce mishi ya biyo su Barnawa, Sulaiman cikin farin ciki yace; "to Abba gani nan".

Nusreen dake zaune tana jiran shigowar tasu jin an buɗe ƙofa yasa ta miƙe da sauri sai dai ganin mijin nata shi kaɗai yasa tace; "ina Yaya Sulaiman ɗin fa".

Ya dafe goshi yace; "Sorry Nurulƙalbiy, ashe bashi bane ya iso wani abokina ne Yaya Sulaiman ɗin ya kirani akan wai ba zai samu zuwa ba", ya ƙarasa yana wucewa bedroom.

Babu jimawa ya fito da shirin fita, cikin sauri tace; "Hayateey ina kuma zaka je, kayi mini alƙawarin yau babu inda zaka je fa".

Ya riƙo hannunta cikin sigar lallashi yace; "Nurulƙalbeey kiyi haƙuri ki bari na fita wani abokina ne Custom suka riƙe mishi kaya shine yazo akan yana so na raka shi kinji ba daɗewa zan yi ba", tace; "shikenan amma idan ka dawo zaka kaini gidan Ramluv ko?", ya ɗan yi jimm sannan yace; "to shikenan sai na dawo ko", ta ɗaga kai, har bakin ƙofa ta rako shi sannan ya tafi.

Ita kuma ta juya ta koma wajen Mama kawai ta wuce don bata son zama ita kaɗai, da sallama ta shiga Mama dake yanke farce ta amsa sallamar da murmushi a fuskarta, tun tana adawa da auren har ta haƙura yanzu.

Nusreen ta ƙarasa ta amshi Nail Cutter ɗin tana cigaba da yanke mata, suna fira jefi-jefi har ta gama.

Yaya Sulaiman yace; "munyi waya da Abba yanzu yace mu wuce Badarawa", Shureim yace; "to muje can ɗin", suka shiga motar Yaya Sulaiman ɗin suka tafi.

Suna zuwa ana fito da Nusram, Yaya Sulaiman sai da hawaye ya zubo mishi ganin yadda ta koma, fuskarta tayi baƙi sosai kamar almajirar data shekara bata ga ruwa ba, tana tafiya tana ɗingishi ga rama da tayi sai idanu Zuru-Zuru kamar ba Nusram ɗin daya sani ba tsayin lokaci, ya tabbatar da ace a hanya suka haɗu tabbas ba zai ganeta ba.

Shureim da Abba suma duka jikin su yayi sanyi sosai, Dpo kuwa ranshi ya ɓace sosai ya rufe su da faɗa suna ta bashi haƙuri sai da yayi warning ɗin su sosai sannan aka cike takardu na beli kan a basu Nusram ɗin.

Nusram da duk jikinta take ji kamar an ɗaure shi tamau ga wani irin ciwon kai dake damunta, ƙafar ta kuwa tsabar zama waje ɗaya ne gashi dandamaryar siminti take wuni ta kwana har kwana uku wannan shine dalilin riƙewar ƙafar.

Sulaiman ya buɗe mata ƙofa ta shiga da ƙyar sannan shida Shureim suka shiga gaba, Nusram ta jingina kanta da kujera tana cigaba da share hawayen fuskarta.

Ita yanzu rayuwar gaba ɗaya ta sire mata, ji take dama ta mutu ta huta kawai, wannan wane irin tozarci ne.

Tana jin lokacin da Yaya Sulaiman ya kira Aunty yake faɗa nata gasu nan sun taho amma sun bar Abba a can.

Suna isa gida Nusram ta yunƙura ta fito, bata tsaya ba dan bata so mutane su ganta sai dai ina ta makaro domin kuwa mutane sun riga sun san meya faru dan haka wa'inda ke waje nan suka tsaya kallon ta.

Tana ɗingisa ƙafa ta shiga gidan, Shureim ya kira likitan su akan yazo ya duba ta koda wata matsala, babu jimawa ya iso.

Nusram kuwa tana shiga gidan Mama Jummai ta rangaɗa guɗa, Amira kuwa ta hau dariya, Aunty ta fito da sauri ta taho wajen ta suka rungume juna suna kuka.

Ummi tace; "ai da sai ku ƙaraso ba wai ku tsaya a nan ba", Aunty ta taimakawa Nusram ɗin ta ƙarasa ɗaki.

Ummi da kanta ta juyewa Nusram ruwa me zafi ta kai mata bayi, Aunty ta taimakawa Nusram ɗin ta shiga wanka tayi saɓi sama da sau biyar sannan taji iska me daɗi ta shigar ta wannan ya tabbatar mata da ta fita kenan.

Ta ɗan ji ƙarfi a jikin ta domin kuwa da kanta ta fito har zuwa ɗaki, cikin kayan ta wanda Ummi bata riga ta kyautar ba Aunty ta ɗauko mata doguwar riga Buba ta saka.

Tana zama likitan da Yaya Sulaiman da kuma Shureim suka shigo, bayan sun jajanta abinda ya faru sannan likitan ya shiga aikin shi.

Ya duba ta sosai sannan yace; "akwai allura yanzu zanyi mata guda biyu sai kuma magunguna wanda zan rubuta muku suma guda biyu sai a siyo ta shanye insha Allahu zata sami sauƙi stress ne kawai sai rashin barci da kuma sanyi daya shige ta.

Aunty tace; "to Allah ya kyauta gaba", duka suka amsa da ameen, Shureim da Yaya Sulaiman suka fice daga ɗakin sannan likitan yayi mata allura daga nan ya fice shima.

Ummi ta miƙowa Nusram ɗin liptin me zafi wanda aka sawa citta da kanunfari tace; "ki shanye yanzu", ta amsa ta shanye tas.

Aunty ta ciko cokali da man tafarnuwa ta miƙo mata tace; "ki dinga sha kullum cokali ɗaya da safe ɗaya da yamma", Nusram ta ɗaga kai kawai.

Ruwan zafi da ƙyalle me kyau Ummi ta miƙowa Aunty inda ita kuma ta amsa, ƙafafun Nusram ɗin ta saka a ciki ɗaya bayan ɗaya tana gasawa har zuwa cinya.

Har lokacin Nusram ɗin bata ce komai ba, sai dai kallon su kawai da take yi, tun tana ɗan janye ƙafar har ruwan ya fara yi mata daɗi hakan yasa ta lumshe idanu kawai.

Aunty bayan ta gama ta kuma shafe mata ƙafafun da man tafarnuwar sannan tace; "to kwanta", Nusram ta kwanta yayin da Aunty ta ɗauki ruwan ta fita dashi.

Aunty na bakin famfo wata mata ta shigo ɗaya daga cikin maƙwabta, suka gaisa da Aunty sannan ta wuce, da sallama ta shigo, Nusram na jinta amma ta ƙara lumshe idanu.

"oh ashe haka kuma abu ya faru Allah ya kyauta gaba", sai da Ummi tayi jimm sannan tace; "ameen", hakan be ishe ta ba sai da ta kuma cewa; "ina zaune sai ga Hassan da gudu yana faɗin Mama fito kiga Nusram ko Nusreen ɗin gidan Jummai me abinci an dawo da ita, yana faɗin hakan nace Nusram ce domin kuwa itace take folistashon saboda mijinta ya kamata da ƙato cikin daren da aka kai.........".

Bata ƙarasa ba Aunty dake tsaye a bakin ƙofa ta shigo tana huci a katse ta; "ya isa haka munafikai masu zuwa lahira da ƙoƙon masaki, masu barci da ido ɗaya, wato abinda kuke so kenan kuji inda wani abun ashsha ya faru ku yaɗa to ki sani wannan ƙaddarace ta hau kanta kuma bata wuce kan kowa ba".

Matar ta riƙe haɓa tace; "ke baiwar Allah kada ki ɗorawa ƙaddara yaran da suke sakaka babu mafaɗi waye be san yadda motoci ke ɗaukar su yana ajiyewa ba, ai itama waccen aiki ne yaci mijin wannan kam daga gani ya riƙe Allah da ƙarfi ne", Aunty ta ɗaga hannu domin kwashe ta da mari Ummi tayi saurin riƙewa tace; "a'a Maman Adam kada ki aikata wannan kuskuren", Aunty ta fuzge hannun ta.

Matar taja tsaki ta miƙe tana faɗin; "dama ai tabarmar kunya da bori ake naɗeta yara sun zama annoba a gari mu dai idan abin ya fara ƙarfi zamu kai ƙara ne kawai wajen me unguwa", tana faɗin hakan ta fice.

Aunty tace cikin ɗaga murya; "ki tafi Zaria ne wajen Sarki, kada ki tsaya wajen me Anguwa, banzaye shashashu", Mama Jummai dake zaune a waje tana ji ta tuntsire da dariya tayi shewa tace; "sai ni Jummai ƴa ga Habu da Lantana ai duk wanda yaja dani sai ya faɗi".

Aunty ta balla mata harara kanta ja tsaki, Mama Jummai tayi shewa tace; "wai ɗan karo ma ya samu sake", cikin jin haushi Aunty tace; "ɗan karo ya wuce agola ya kaiwa ƴar masu gida hari", Mama Jummai bata kuma jan maganar ba sai tayi gum.

Har yamma Nusram na kwance bata tashi ba, Sai wajen biyar sannan ta tashi ta rama sallolin da ake bin ta, zuwa lokacin ta ɗan sami sauƙi.

Yaya Sulaiman da yazo ɗaukar Aunty ya ƙara mata sannu da jiki, murya a dashe tace; "na gode sosai da ɗawainiya", ya ɗan ranƙwashe ta na wasa yace; "ina wasa dake ne".

Su Ummi suka yi dariya, sunyi sallama inda Ummi ke ƙara godiya a gare su, Aunty tace; "kada ki damu ai ɗa na kowa ne kuma Nusram idan kin tuna dama tawa ce".

Haka suka tafi suka bar su, abin mamaki har dare ƴan shigowa ganin ƙwaƙwaf basu dena shigowa ba, Mama Jummai kuwa tafiyar Aunty sai ta bude shafin habaici, babu wanda yace ci kanki.

Koda Isa ya dawo Nusram na jin lokacin da take faɗa mishi, yayi shiru kafin yace; "Allah ya kyauta gaba", Mama Jummai ta balla mishi harara.

Bayan sallar isha'i Nusram na zaune saman abin sallah tana lazimi, Isa yayi sallama ya shigo, a sanyaye ta amsa.

Kusa da ita ya tsuguna sannan yace; " ya jikin?, ta amsa da; "lafiya lau", Allah ya kyauta gaba", tace; "ameen", ya jima tsugunne a wajen Nusram tayi banza dashi.

Da kanshi kuma ya miƙe ya fice daga ɗakin, Nusram ta sauke ajiyar zuciya hawayen baƙin ciki yana zubo mata.

Ta koma ta kwanta tana jiyo muryar mahaifin nata a tsakar gida amma ko leƙowa beyi ba, hasalima sai lissafe-lissafe suke yi shida Mama Jummai da alamu dai bashinta yaci.

Cikin dare Ummi taji saukar numfashi da kuma kakari, da sauri ta miƙe ta ƙarasa wajen Nusram ɗin, tana kwance tana murƙususu gefen ta kuwa Kubra ce ke barcinta.

Ta juyo da ita hankali tashe tace; "Nusram meke damun ki", Nusram ta nuna cikin ta hawaye na zubo mata.

Ummi ta buga uban tagumi, yanzu me take dashi wanda zata nemawa yarinyar ta magani duk wani kuɗi da tayi tanajin sa ta kashe shi wajen bikin nan, ta sauke ajiyar zuciya tace; "Allah ka dube ni".

Hijab ta ɗauko ta saka sannan tazo ta kama Nusram ɗin ta miƙe, sai da ta taimaka mata wajen saka hijab ɗin sannan ta riƙe mata hannu a ɗurkushe Nusram take tafiya har suka fito daga ɗakin.

Ummi ta duba agogon wayar ta Sha biyu harda rabi, ta kalli Nusram tace; "Nusram bari na faɗawa Baban ku, ko zai taimaka mana", Nusram ta ɗaga kai tana durƙusawa a wajen dan wani irin murɗawa da cikin yayi.

Ummi kuwa ƙofar ɗakin Mama Jummai taje tana bubbugawa, sun jima sosai kafin azo a buɗe, Mama Jummai ke baya sai Baba a gaba.

"meye kuma yanzu kika zo zaki dame ni?", Ummi ta haɗiye wani abu me ɗaci tace; "Nusram ce bata da lafiya shine nace ko zaka taimaka a kaita asibiti", Baba yaja tsaki zai koma ciki Ummi tayi saurin ɗurkusawa tace; "dan Allah Baban Nusreen ka duba girman Allah ka zo mu kai yarinyar nan asibiti kada ta mutu".

Cikin fushi Baba yace; "ta mutu mana waye ya damu yarinya taje ta gama iskancin ta, ta nuna mini ban isa ba ta kwaso abin kunyar ta shine zaki zo ki tasa ni a gaba wai sai na kaita asibiti, to wallahi babu inda zanje, ai inda Allah ya taimake ni ba ita kaɗai na haifa ba da sai dai a ɗauki gawata a gidan baƙin cikin ta ya kashe ni".

Ummi cikin kuka tace; "dan Allah ka taimaka kazo a kaita asibiti duk wannan idan ta sami lafiya ayi maganar", Baba yace; "wallahi Maimuna babu inda zanje ina saurayin da yayi cikin yazo ya kaita mana", be bari ta kuma cewa komai ba ya maida ƙofar ya rufe.

Nusram zuwa yanzu jikin ta har rawa yake yi, ga zafin ciwo ga kuma baƙin ciki na magan-ganun da Mahaifinta yake faɗa akanta.

Ummi ta jima a tsaye a wajen tana share hawaye kafin ta koma wajen Nusram ɗin ta taimaka ta ɗago ta suka fara tafiya a hankali har suka fice daga gidan.

Garin yayi tsit ga duhu, haka dai suke tafiya a hankali idan cikin ya murɗa sai dai ta tsugunna a wajen idan yayi sauƙi sai su cigaba da tafiya.

A haka har suka ƙaraso bakin titi, babu mutane sosai sai jefi-jefi kuma yawanci sai dai su kallesu kawai su wuce wasu ma basa ko kallon inda suke.

Duk motar da Ummi tayi ƙoƙarin tarewa bata tsayawa, ita dai Nusram na tsugunne tana riƙe da cikinta duk addu'ar da tazo bakin ta ita take yi.

Zasu kusa rabin awa a wajen sannan wata mota da har ta wuce ta kuma dawo da baya ta tsaya, mutumin ya leƙo da fuskar shi yace; "ina zuwa Hajiya da daddare haka".

Ummi tace; "kaga yarinya tace bata da lafiya shine nace ko zaka taimaka mana ka kaimu asibiti, wand ake kusa duk idan dare yayi rufewa suke yi".

Ba tare da ɓata lokaci ba ya buɗe musu ƙofa suka shiga, sannan yaja suka tafi, sun yi tafiya me ɗan nisa sannan suka iso asibitin.

Sai da ya taimaka ma Ummi suka shiga har cikin asibitin, aka bata gado har aka shiga duba ta domin babban mutum ne, ya duba agogon hannun shi ya kalli Ummi kafin ya ciro kuɗi a aljihun shi ya miƙo mata yace; "gashi ko zaku buƙaci wani abin, yanzu idan zan fita zan muku clearing bill ɗin ku", Ummi tsabar murna kamar ta tsuguna a ƙasa ta mishi godiya.

Yace; "kada ki damu ɗa na kowa ne Allah ya bata lafiya", Ummi ta amsa da ameen, haka ta bishi da kallo har ya fice daga asibitin, ga dai shi babban mutum amma kuma yana da sauƙin kai sosai.

Ta jima zaune a wajen kafin likitan ya fito sannan Nurses suka fito janye da gadon da Nusram ɗin ke kai a kwance, likitan yace; "ki bisu zasu kaita ɗakin da zata huta Alhaji Mustapha ya riga ya biya duk wani kuɗi da za'a yi muku aiki a nan, dan haka zuwa safe zaki je Pharmacy ki amso mata magun-gunan ta, inda ta buge ne ko kuma takata akayi dai ban sani ba to wajen ne ke mata zafi yaso ma ya taɓa mahaifarta amma Allah ya kiyaye be taɓa ba ɗin yanzu munyi mata allura insha Allahu nan da safiya zata sami sauƙi", Ummi tace; "to an gode sosai", tabi Nurses ɗin don kai Nusram ɗin ɗakin hutu.

Ɗaki na musamman aka kai su, su kaɗai ne a ciki ga couch nan sai gado har da tv wato plasma ga sanyi babu wani hayaniya, sai da suka jona mata drip sannan suka fice daga ɗakin.

Ummi ta shiga bayi ta ɗauro alwala sannan tazo ta shinfiɗa ɗan kwalin ta, dan bata ɗauko komai ba ta

Please Login or Register in order to submit comment