Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sauke ajiyar zuciya.

"wannan wane irin masifa ce take tunkaro shi, ƴar shi ta cikin shi ke son ɗan shi na cikin shi?, taya zai fito ya shaidawa duniya cewa Abdus-samad ɗin ɗan shi ne na cikin shi?, akwai babban al'amarin da ko tunawa baya son yi".

Wayar shi ya zaro ya fara kiran Alhaji Sa'eed, sai dai kash ana amfani da layin, miƙewa yayi cikin sauri kana ya fara zagaye ɗakin.

Daidai lokacin kuwa Hajiya Salma ce da Alhaji Sa'eed suke waya, "Alhaji wallahi ban san yadda zan yi da yarinyar nan ta fahimci halin da ake ciki ba, bana ƙaunar ganin yaron nan a raye gashi na rasa yaya zan yi".

Alhaji Sa'eed yace; "kada ki damu Hajiya Salma, zamu iya amfani da ita wajen tunowar asirin mijin ki, na san cewa idan har abinda yake ɓoyewa ya fito fili to tabbas yaran nashi zasu tsane shi tsana me tsanani, sannan shi kan shi Abdus-samad ɗin zai tsane shi tsana mafi muni sannan kinsan Nagimi's Family dole zasu ɗauki mataki, zasu maka shi kotu kuma kin san hukuncin da za'a yanke mishi ɗaurin rai da rai ne".

Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya tace; "Alhaji Sa'eed har yanzu baka san waye abokin ka ba, ko tafiyar nan da yayi hannun jari yaje ya zuba a wani company dake Hong Kong ƙimanin dala billion sha biyar, sannan yana ɗaukar kaso mafi tsoka a babban companyn dake ƙera gwalagwalai a Dubai, dan haka bana jin kuɗin Familyn nan zai iya da nashi, ba zasu taɓa iyawa ba ka chanza shawara".

Jim yayi yana tunani, yayin da Hajiya Salma take tunanin mafita yake nemo musu, shi kuma a nashi ɓangaren kuɗaɗen ne suka fara girgiza shi, lallai wato Alhaji Mustaphan ashe yana ɓoye mishi wasu abubuwan, shi dai kawai ya san cewa yana da Companyn ƙera motoci a Dubai da kuma lagos, sai Company biyu da yake da hannun jari a India da kuma Bangkok ashe likafa ta cigaba kuɗin nashi ya fara wuce tunanin shi kenan?.

"Me zai hana kawai idan Khausar ta gayyace shi gidan nan mu saka mishi guba a abinci sai ya mutu, idan yaso Baban shima daga baya sai muji dashi?".

Abinda ta faɗa ya katsewa Alhaji Sa'eed duniyar tunanin daya fara kenan, ya girgiza kai kamar tana gaban shi yace; "hakan bame yiwuwa bane Brr Farida a sanin da nayi mata ba zata taɓa ƙyale abin a haka ba, bana so muyi abinda zamu shiga ciki".

Hajiya Salma taja tsaki tace; "yanzu meye abin yi?", Alhaji Sa'eed yace; "watan gobe Brr Farida zata tafi Korea yin wani case ina ganin zamu yi amfani da wannan damar ne kawai".

Hajiya Salma tayi murmushi tace; "shikenan Allah ya kaimu da rai da lafiya, amma wallahi na ƙosa komai ya dawo hannu na, nima na zama ɗaya daga cikin matan da ake lissafawa masu kuɗi a duniya".

Alhaji Sa'eed yayi wani munafikin murmushi sannan yace; "nima na ƙosa wannan lokacin yazo ke dai kome ke akwai ki dinga sanar dani", ta amsa da to.

A haka suka rabu, Alhaji Sa'eed na katse wayar ya miƙe tsaye cikin sauri, Brr Hauwa dake kwance jikin shi tayi saurin miƙewa tana tambayar shi lafiya.

"babu komai, dan Allah ina buƙatar yin tunani yanzu bana son damuwa ko zaki tafi ne?", Brr Hauwa ta ɗaga gira ɗaya tace; "kuɗin da Hajiya Salma ta faɗa maka Alhaji Mustafa na dashi shine ya tsorata ka ko me".

Jin abinda ta faɗa yasa ya ɗan saki rai yace; "ba haka bane, mafita nake nema dole Abdus-samad da Alhaji Mustapha su mutu, kuɗi Hauwa dole ya dawo gare mu, ni dake".

Brr Hauwa tayi murmushi tace; "ka kwantar da hankalin ka, har yanzu fa Brr Farida bata faɗawa Abdus-samad komai ba, suna ganin sannan sirrine tsakanin ta da Alhaji Mustafa banda su biyu babu wanda ya sani".

Alhaji Sa'eed yace; "amma shi Alhaji Mustaphan ai ya san na sani ko", ta shafa fuskar shi tace; "amma kuma ai ya yarda da kai sosai ko".

Ya koma ya zauna kana ya girgiza kai yace; "bana tunanin hakan Brr a da Alhaji Mustapha baya yin komai sai da sani na amma a yanzu ya canza sosai", miƙewa yayi ya ɗauki wayar shi kana yace; "bari naje wajen Oregbu zamu haɗu gobe kawai dan yau till down zamu yi".

Brr Hauwa ta figi jakar ta sannan tace; "muje ka ajiye ni a gida ko?", daga haka suka fice daga gidan.


#LIKE
#COMMENT
#SHARE

*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*.




♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*


*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

📖📖55-56📖📖


Alhaji Mustafa ke tsugunne jikin shi sanye da jan ƙyalle iya gwiwa, tsaye a saman shi Appu ne shima sanye da jan ƙyalle a kwankwason shi sai dai shi ya yafa wani saman kafaɗar shi.

Wani abu dogo ne riƙe a hannun shi, wani ƙaton mutum me ƙaton tumbi ke gefe tsaye da ƙwarya ƙatuwa a hannun shi, Appu ke saka wannan abin cikin ƙwaryar yana yayyafawa Alhaji Mustapha yana zagaye shi yana wasu irin surutai.

Sauran kuwa kansu na ƙasa duka a tsaye suke sanye da jan kaya riga da wando, wajen yayi tsit sai tashin muryar Appu dake wannan surutan.

Sun jima a haka kafin wani hayaƙi ya fara cika wajen, basu motsa ba kai daga gani kasan sun saba da yanayin, sai dai wasu ƙalilan da suke zubar da hawaye kasancewar hayaƙin akwai zafi sosai amma babu halin rufe idanu.

Sun jima a haka wajen awa ɗaya kafin komai na wajen ya ɗauki rawa, wutar dake kunne koda yaushe wacce take saman wata ƴar ƙaramar ƙwarya ta ɗauke, nana fa ko'ina a wajen ya ɗauki duhu.

Minti talatin da faruwar hakan sannan hasken ya dawo, Alhaji Mustafa ya kalli inda yake tsugunne jini ne a gaban shi malala wanda har ya gangaro ya tarar dashi, sai yara guda biyu da suke kwance a wajen cikin su a fafe wanda yake nuna alamun tana nan ne aka sha jinin nasu.

Appu ya fashe da dariya kafin ya matsa, wajen wata giggimemiyar kujera yaja ya tsaya sannan ya nuno Alhaji Mustapha yace; "haƙurin Oregbu ya kusa ƙarewa Tuge, dole ka kawo jinin ɗanka na cikin ka idan ba haka ba fushin sa zai sauka a kanka, shekara talatin kenan da yi mishi alƙawari amma har yau ka gaza cikawa, tun ana rarrashin shi yana amsar jinin wasu wata rana fa ba zai aminta ba", ya juya ga sauran mutanen ya nuna mutum biyu a cikin su yace; "Oregbu yace a gaya muku ya ji daɗin sadaukarwa da kuka yi mishi, dan haka yayi matuƙar murna shi kuma zai canza muku da abinda kuke so".

Ya nuna wani dogo fari a cikin su yace; "yadda ka bashi ɗan ka yace a gaya maka kaine zaka dinga juya shugaban ƙasa wanda za'a rantsar hasalima ma ƴan majalisu kai zaka yi list ɗin su ka bayar mulkin nijeriya naka ne".

Cikin murna yayi sujjada yana godiya, ya nuna ɗayan da hannun shi yace; "kai kuma ka bashi jini me daɗi sosai na ƴar ɗan uwanka dan haka sai ka zama babu babban ɗan kasuwa a ƙasar Ghana wanda yake sama da kai", shima cikin murna ya durƙusa ya hau murna.

Appu ya ɗaga mishi hannu kana ya ɗora da cewa; "abu guda zaku yi tare abu guda kuma kowa da nashi wanda zaku yi tare shine ku baiwa almajirai guda uku sadakar dubu goma amma jefa musu zaku yi".

Ya nuna na farkon yace; "ka samu yaro wanda bai gaza shekara goma sha takwas ba kada ya wuce haka kayi luwaɗi dashi a masallacin ƙofar gidan ka sha biyu na daren gobe".

Ya nuna ɗayan yace; "ka sami jariri sabuwar haihuwa ɗa namiji ka ɗauke shi ƙarfe ukun dare kayi jefa dashi a tsakar gidan ka bayan kayi zindir idan be mutu ba ka sake yi mishi haka har sai ya mutu, buƙatar ku ta gama biya", jinjina kai suka yi sannan suka matsa baya.

"Alhaji Sa'eed Yahya Tsillo, da kai da Alhaji Mustafa Abubakar Tuge, Oregbu yace a faɗa muku yana son jini daga gare ku ƙafin nan da sha bakwai ga watan gobe".

Alhaji Sa'eed yace; "ayi mini afuwa ƴaƴa biyu suka rage mini yanzu", cikin daka tsawa Appu yace; "ka kawo ko ka haukace", Alhaji Sa'eed yace; "zan bayar".

"zaka iya bayar da na ƴar ƙanwarka Azeema domin Oregbu yace jinin ta akwai wuyar samu", cikin murna Alhaji Sa'eed yace; "zan kuwa kawo ta".

Appu ya juya ga Alhaji Mustafa yace; "ko dai ka kawo jinin Abdus-samad ko kuma ka kawo jarirai guda goma", Alhaji Mustafa yace; "tunda jinin Abdus-samad yaƙi samuwa kona bayar dana Khaleesat ko Khausar mana".

Appu yayi ihu yayi kirari kafin ya girgiza kai yace; "wa'innan ba jinin ka bane, jinin ka na asali yake so, kada ka kuma kawo zancen su", cikin sauri ya amsa da to.

Nan suka cigaba da kafurcin su da tsibbace tsibbacen su, har zuwa gabatowar asuba kafin suka watse.

Alhaji Mustafa da Alhaji Sa'eed tare suka taho, sun shigo garin Kaduna ana kiraye kirayen sallar asuba dan haka suka sami masallaci suka yi sallah.

Bayan an idar Alhaji Mustafa ya dubi masallacin babu kowa domin kowa ya kama gaban shi ya kai kallon shi ga abokin shi yace; "Alhaji Sa'eed ka taimaka mini mana, ban san ya zanyi ba".

Cikin ɗaure fuska Alhaji Sa'eed yace; "meka maidani Mustapha, nifa lura jinin Murad ɗin ne baka son bayarwa".

Ya girgiza kai yace; "ba haka bane ka duba da kyau ka gani matsaloli sun fara yawa tun da suka haɗu da Khausar ta liƙe shi take so, Brr Farida taƙi ko kusa ta faɗa mishi cewa nine mahaifin shi balle na samu damar raɓar shi, sannan yaron be cika shige-shige ba balantana na sami wata dama akan shi, ga Salma yadda take sona take kula dani ta yarda dani ba zan iya kallon idanun ta ince mata wai ina da wani ɗa ba".

Alhaji Sa'eed yayi murmushi yace; "hakane kuma gaskiya, to amma yanzu abinda za'a yi shine ya kamata ace muna kula da takun Brr Farida domin na san shirun ta ba wai yana nufin shiru ɗin bane dan haka me zai hana mu tura wata matar ta sami aiki a gidan ta idan yaso sai ta dinga kawo mana rahoton abinda yake faruwa".

Alhaji Mustafa yace; "Alhaji Sa'eed duk abinda ya kamata kayi ni dai kayi amma ka tabbatar da cewa asirina dana rufe shekara Ashirin da bakwai be tonu ba".

Alhaji Sa'eed yace; "kada ka damu kai dai ka bar mini komai a hannu na baka faɗa mini meya kaika Dubai ba?".

Alhaji Mustafa yace; "hannun jari na zuba a wani company, so nake gaba kaɗan na siye companyn gaba ɗaya haka ma Brr Jabeer ya bani shawara".

"to amma ya maganar takardun gidan gonarka dake By Pass?", Alhaji Mustafa ya ɗan yi jim kafin yace; "suna nan, akwai matsala ne?", Alhaji Sa'eed ya girgiza kai.

Sai da gari yayi haske sannan suka fito daga masallacin kowa ya shiga motar shi ya nufi hanyar gidan shi.

********* **************
*HAYIN RIGASA, KADUNA*.

Da asuba suka tashi tare kamar haɗin baki, Dr Saleema ta fara alwala kafin Nusram itama ta miƙe ta shiga bayin domin alwala.

Koda Nusram da Dr Saleema suka idar da sallah babu wanda ya tashi daga inda yake, hakan ya tabbatar da cewa dukkan su, suna da kamanceceniya ta wajen halayyar su.

Sai bakwai kafin Dr Saleema ta miƙe ta shiga bayi, wanka tayi bayan ta fito ta dubi Nusram tace; "ki shiga kema kiyi wankan zamu wuce asibiti", Nusram ta jinjina kai sannan ta miƙe ta shige.

Nusram na fitowa ta sami Dr Saleema tana shiryawa itama ta hau nata shirin kafin wani lokaci duka sun gama shiryawa.

A jere suka fito, Muhibba da Kamal ke saman dinning, yayin da Kabeer da Hafeeza ke zaune a saman kujera suna haɗa taƙardu.

Duka idanu suka zubo musu wanda hakan yasa Nusram jin ta fara takura, bayan Dr Saleema ta shige.

Koda suka ƙaraso saman kujera Dr Saleema taja hannun Nusram ta zaunar da ita sannan itama ta zauna.

Kamal da Kabeer suka sauke ajiyar zuciya a tare, shiru ya ɗan biyo baya kafin suka fara gaishe da yayar tasu.

Ta amsa cikin sakin fuska, tana miƙewa Mummy na shigowa, "ina kwana Mummy?", ta amsa da lafiya lau, Nusram itama ta gaishe da ita kafin duka suka nufi dinning.

Muhibba tayi serving ɗin su, ita dai Nusram gabanta banda faɗuwa babu abinda yake yi ga wani irin kallo da mazan ke binta dashi.

Ta kasa cin komai banda juya cokalin da take yi, Kabeer ya kalli ƴar uwar tashi sannan ya kuma kallon Nusram wacce kanta ke sauke a ƙasa.

Tayi kyau sosai sanye take da atamfa me ruwan goro da ɗige-ɗigen kore, hijab ɗin dake jinkin ta shima kore ne wanda ya ƙara haskaka fatar ta.

Hannun ta riƙe gam da wannan wayar dai ta Abdul domin kuwa barci ne kawai ke rabata da wayar amma kusan koda yaushe tana hannun ta.

"Wai Yaya Saleema ina kika samo wannan kyakkyawar ne?", Dr Saleema ta ɗan kalle shi kafin tace; "Ƙawata ce ta fara karatu anan Kaduna shine tazo zama anan".

"oho! Na gane sannu baƙuwa", Kabeer ɗin ya faɗa, Nusram ta ɗanyi murmushi wanda yasa dukan su sakin baki tace; "yauwa sannun".

Zai kuma magana Mummy ta dakatar dashi don haka dole yaja bakin shi ya tsuke, suna gamawa Dr Saleema ta miƙe inda itama Nusram ɗin ta miƙe.

"Yaya Saleema kika ce makaranta take yi da ai sai ki bari mu tafi tare da ita ko?", cewar Muhibba wacce ta miƙe ta roƙo hannun Nusram ɗin.

Hafeeza ma ta miƙe ta kalli Kamal tace; "kai tashi mu tafi, kada mu makara", har ya miƙe Mummy tace; "amma da dai da Kabeer kuka tafi shine fa zai je ɗauko Daddynku a Airport".

Hafeeza ta duba agogon hannun ta kana tace; "ya dai kaini idan yaso ya dawo daga nan ma sai yayi signing kawai", Mummy tace; "shikenan", daga haka suka juya suka fice.

Ɓangaren su Dr Saleema kuwa ta kalli Muhibba tace; "wannan amanace a waje na ki bari idan kuka ɗan saba sai ku cigaba da tafiya tare kinji".

Muhibba ta zumɓuro baki gaba tace; "ni wallahi Yaya Saleema ina sonta da ƙawa", Dr Saleema tayi murmushi kana tace; "kada ki damu, Nusram muje ko".

Da Muhibba da Kabeer suka maimaita sunan cikin birgewa; "Nusram!!", Kabeer yayi murmushi yace; "nice name", Muhibba ta kwashe da dariya.

Ita dai Dr Saleema ganin abin nasu bana ƙare bane yasa taja hannun Nusram ɗin suka fice daga gidan.

Koda suka shiga mota babu wanda yayi magana, gaba ɗaya Dr Saleema ta maida hankalin ta kan tuƙi yayin da Nusram kuma ta kunna wayar tana kallon hoton da ya zamar mata jiki wajen kallon shi domin har yanzu bata san password ɗin wayar ba hakan yasa sai dai ta kalli hoton idan ta gaji da kallo ta kashe ta ajiye.

A ɗan kaikaice Dr Saleema ta kalle ta, ta ɗan yi murmushi ganin hankalin ta ya tafi gaba ɗaya kan wayar, bata ce da ita komai ba har suka iso babban asibitin garin Kaduna inda Saleemar ke aiki.

Suna tafe suna gaisawa da jama'a har zuwa office ɗin Dr Saleemar, ga dai shi asibitin gwamnati ne amma office ɗin babba ne hakan ke nunarwa da Dr Saleemar babbace a asibitin.

Kan kushin ta nunawa Nusram ita kuma ta hau kujerar aiki inda ta fara ganin marasa lafiya, ita dai Nusram na zaune tana kallon su haka har barci ya kwashe ta.

Bata farka ba sai daf da azahar, Dr Saleema data gama ganin marasa lafiya tana shan coffee ta kalle ta tace; "lallai sannu da barci", Nusram ba tare da tace komai ba ta miƙe ta zauna.

Babu jimawa wata Nurse ta shigo kiran Dr Saleemar, dan haka cikin sauri ta miƙe, ta kalli Nusram tace; "Nusram zan shiga Theatre yanzu ga remote nan kiyi kallo idan anyi kiran sallah ga bayi nan sai kiyi alwala kiyi sallah, idan kuma kina jin yunwa ga wannan ki danna za'a zo sai ki faɗi abinda kike son ci, wata ƙila na jima sosai, wata mata ce take naƙuda to kuma abin yazo da gardama bari naje kinji", Nusram tayi mata fatan nasara kafin ta fice tana murmushi cike da yaba hankalin Nusram ɗin.


Ta jima zaune kafin akayi kiran sallah, bayin ta shiga tayo alwala sannan tazo tayi sallarta, koda ta idar a wajen ta zauna tana tunani.

Rayuwa kenan! Ko yaya ƴar uwarta take oho?, wane hali Ummi take shima bata sani ba, ƙaddara duk ta raba su kowa ya kama nashi wajen.

Gashi bata da Number ɗin Nusreen balle ta kirata sai dai tana da number ɗin Ummi da ta Auntyn Tudu dan haka zata roƙi Dr Saleema ta ara mata waya sai ta kira su ko zata sami sauƙi.

To yanzu ma ina mijin da aka ɗaura mata aure dashi, waye ya san inda yake ma?, tun jiya ko wane hali ta kwanta be dame shi ba.

Wata zuciyar ta ce mata; "ke Nusram shiga hankalin ki, kin manta cewa Baba ya ɗauke ki kamar wata sanda ya bashi babu bincike ba komai, waye ya sani ma ko sadaka ya bashi?, bata san lokacin da hawaye suka fara kwaranya a idanun ta ba.

Tun daga farkon tashinta ta fara tunani har kawo i yanzu, Baba be taɓa nuna musu ƙauna ba ita da ƴar uwarta, ka ɗauki mutum sukutum da guda ka bawa wanda baka sani ba.

Shin wai haka duk iyaye maza suke, basu da tausayi, imani da kuma ƙaunar akan yaran su kodai sune basu yi dacen Uba ba?.

Ta girgiza kai, ba haka bane ai tana zuwa gidan su Auntyn Tudu tana ganin yadda Abba ke haba haba da yaran shi har fira suke zama suyi dashi.

Kwatanta halayyar mahaifinta tayi data Abban, kwata-kwata basu da kamanceceniya, tunda ta taso zata iya irga Albarkar da Baba ya taɓa saka musu, haka tunda take dashi be taɓa zama sunyi fira dashi ba kuma be taɓa tambayar me suke so ba ko meye damuwar su ba, shi dai kawai tunda ya haife su gani yake ya gama komai.

hannu taji saman fuskarta wanda hakan shine ya dawo da ita duniyar tunanin data faɗa, ta ɗago idanun ta jajur ta zuba mishi su.

Shima ɗin ita yake kallo, tun jiya daya koma gida ko barci be yi ba saboda tunanin halin da yake ciki.

Ya kasa yanke shawara guda ɗaya shin ya faɗawa Brr Farida ne ko kuwa yaja bakin shi yayi shiru?, ƙarshe dai dole yaja matsaya akan kada ya faɗa mata.

Yarinyar tana bashi tausayi idan yayi duba da irin yadda aka barota daga gida aka ɗauke ta aka damƙawa mutumin da ko sanin shi ba'a yi ba, dan ya tabbatar yanzu da zai koma wajen mahaifinta ba gane shi zai yi ba.

Aiki ya taso dan shi a ƙa'ida huɗu yake tashi ko biyar, kamar ya wuce gida amma sai yaga rashin dacewar hakan, dan haka ya yanke shawarar zuwa ya duba halin data kwana.

sanin cewa Saleema na asibiti yasa ya taho kuma yana da tabbacin Dr Saleema ba zata taɓa barin ta a gida ba.

Ya daɗe tsaye kanta amma bata sani ba saboda dogon tunanin data tafi, ya kauda hannun shi daga fuskarta yace; "meke damun ki?".

Kanta kawai ta saukar ƙasa, ganin bata bashi amsa ba yasa ya taɓe baki sannan ya miƙe ya koma saman kujera ya zauna.

Nusram kuwa a yanzu shi kanshi haushin shi take ji domin kuwa shima yana tuna mata rayuwar ta da kuma zamowar shi silar barowar ta gida, duk da dai ta san cewa taimakon ta yayi.

Jin an zare wayar hannun ta yasa ta kalle shi, wayar ya juya kafin ya kunna, hoton shi ya bayyana yayi murmushi sannan ya maida wayar ya ajiye.

"da alamu dai ita kaɗai ta rage miki kadara ko?", ya faɗa, Nusram kuwa ko arziƙin kallo be samu daga gare ta ba, ya ɗan jingina da kujera yana kallon fuskar ta sosai.

Bata ɗago ta kalle shi ba har yanzu kuma bata ce dashi uffan ba, ya kuma taɓe baki sannan ya kira Brr Farida.

Tana jin shi har ya gama wayar shi, sannan ya kuma maida kallon shi kanta yace; "wai ke kurma ce kome?", nan ma bata yi magana ba.

Ya sunkuyo dai-dai fuskarta a ɗan hasale yace; "haka daman aka koyar dake zaman auren?", har lokacin dai bata ce komai ba.

Zuwa yanzu fa ya fara hasala ya riƙo fuskarta yace; "ni nake miki magana kina banza dani, baki san koni waye ba ko?".

Nusram kuwa ganin ya takura mata ga halin da take ciki na damuwa yasa ta fincike fuskar ta, ta miƙe cikin sauri ƙafin taja tsaki ta juya domin tafiya.

Ko taku biyu bata yi ba ya damƙota, hannunta ya murɗe ta baya ya jingina jikin ta da nashi.

"ni kike yiwa tsaki?", ya faɗa a fusace, Nusram hawayen azaba ya zubo mata, ta runtse idanu tana me sakin kuka wanda hakan yayi dai-dai da shigowar Dr Saleema.

Sai da gabanta ya faɗi wani abu ya taso ya tokare mata maƙogoro, ta juya tana ƙoƙarin ɗaukar laptop ɗin

Please Login or Register in order to submit comment