Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ku", abinda take faɗa kenan a cikin ranta.

Sun ɗan taɓa fira a tsakanin su kafin su kwanta barci, sai lokacin Nusram ta ɗan sami sauƙin abinda yake ranta don ko babu komai firar da suka ɗan yi ta rage mata damuwa ba kaɗan ba.


******** **********


Jikin shi sanye da Wando jeans fari da kuma rigar polo t shirt kalar blue da ratsin fari, ƴar ƙaramar jakar shi ce riƙe a hannun shi, Fadil kuma yana bayan shi haka suka shigo da sallama.

Kamar koda yaushe suna saman dinning table inda zasu yi breakfast, Sumayya dake cin abinci ta gaishe dashi, ya amsa fuska a sake sannan ya gaishe dasu, kowa ya amsa kamar kowanne lokaci amma banda Brr Hauwa.

"idan kin gama tashi mu tafi", Sumayya tace; "to Yaya", sannan ta miƙe, cikin rawar jiki Husna tace; "Ya Abdul kai ba zaka ci abincin bane?", be kalle ta ba balle ta saka ran samun amsa daga gare shi.

Hajja tace; "baka ji ana yi maka magana bane?, ni ina mamakin halin ka domin iya sani na uban ka ba halin shi ba kenan, anya kuwa kai ɗan shi ne?".

Wata irin ɗagowa Abdul yayi sannan ya kalli Hajja, itama Malama kamar zata zubar da hawaye take bin Hajjan da kallo.

Ganin yadda ranshi ya ɓace yasa Hauwa cewa; "waye ya sani ko a yawon neman shaidu aka samo shi aka zo aka ƙaƙabawa ɗan uwa na, ni dama na jima ina tunanin haka dan ko kama baya yi da ƴaƴan Doctor".

Hajja ta girgiza kai tace; "tabbas hakan zata iya kasancewa bari Abubakar ɗin ya dawo dole azo ayi bincike kada a lalata mana zuria da bara gurbi".

Wannan karan kam da Sumayya da Malama kasa daurewa suka yi dan haka Sumayya ta saki kuka, Malama kuwa hawaye ta hau sharewa, Fadil kan shi na ƙasa sai dai yadda ya tsuke baki zai tabbatar maka da cewa yaji haushin abin.

Fadila kuwa kasa bari tayi dan haka ta miƙe tace; "yo Hajja dan Abdul yayi nurƙufanci ai ba abin mamaki bane idan aka yi duba da halin Brr Hauwa shima haka yake kinga kenan ita ya ɗauko, taƙama da ƙasaita kuwa kowa ya san halin ki ne ko ince a jinin ki yake, dan wani dalili naku kuke son haramta ɗan sunnah anya abinda kuke yi kuwa dai-dai ne, in dai a neman yawon shari'ah ake samo ɗa ai ya kamata kema Brr a bincike ki gudun ɓata zuria nan gaba", sanin halin Brr Hauwa yasa tana gama faɗar haka taja ƙafar ta, ta bar wajen ɗakin Malama ta shige ta dannan key.

Brr Hauwa kuwa kan ta gama haɗa magan-ganun Fadila, Fadila ta ɓace a wajen, Fadil kuwa jin ɓaranɓaramar da Fadila tayi yasa ya kama hannun Sumayya suka fice daga gidan.

Hajja cikin masifa tace; "ai wallahi zaki zo ki same ni yaushe yaran gidan nan suka ɓace har haka, bari Abban Nihal ya dawo ni Fadila take zagi kuma Malama kina kallon ta?".

Malama har lokacin hawaye take zubar wa, Hajja ta fashe da kukan munafirci tana faɗin; "Brr kaini wajen Ahmad", jin hakan yasa Brr Hauwa miƙewa ta ja hannun Hajja domin tafiya.

Malama na ganin sun fita ta miƙe da sauri taje ƙofar ɗakin ta, sai da ta ƙwanƙwasa tana ƙwalawa Fadila kira sannan ta buɗe, cikin sauri Malama ta janyo hannun ta sannan tace; "zo ki bi su Abdul Hajja ta yafi wajen Ahmad kuma kin san sauran idan har labarin yaje kunnen shi, babu inda kike da mafaka sai wajen Farida dan haka fito maza".

Ita kanta Farida jin sunan wanda aka ambata yasa jikin ta ya hau rawa, Ahmad shine babban ɗan Hajja tsohon sojane, yana ji da Hajja kuma duk abinda ta faɗa dai-dai ne yana taka duk wanda ya taka ta.

Malama ta kamo hannun ta sannan ta haɗa dana Abdul tace; "maza ku tafi tare idan lokaci yayi da zata dawo zan kira ka sai ta dawo kaji", Abdul da har lokacin damuwar fuskar shi bata kauce ba ya ɗaga kai kawai yana me jan hannun Fadilar.

A waje suka sami Fadil da kuma Sumayya, inda kana gani ka san haƙuri yake bata Abdul yayi murmushi yace; "kuzo mu tafi ko?", ba tare da sun ce komai ba suka bishi a baya.

Fadil ke tuƙa su yayin da Sumayya ke gefe, baya kuma Abdul ne da Fadila, babu wanda yayi magana tsayin lokaci kafin Fadil yace; "Sumayya kuyi haƙuri kun riga da kun san halin Hajja tun ba yanzu ba be kamata hakan ya dame ku ba".

Sumayya ta share hawayen ta tace; "Yaya Fadil da na san abinda zan zo naji kenan a bakin Aunty Hauwa da Hajja da ban matsa sai nazo ba".

Fadila ta saka hannu ta dafa Sumayya tace; "kada ki damu kanki Sumayya baku kaɗai take wa haka ba har mu duk tabi ta dame mu".

Fadil yace; "hali ne kowa da kalar nashi gashi ban san me yasa duk tabi ta tsani Abdus-samad ba, kamar ba jinin ta ba".

Sumayya tace; "amma abinda take yi be dace ba kuma ni ba zan kuma zuwa gidan nan ba", Fadila tace; "aikuwa dole kizo domin kuwa nan shine asalin ki".

Sumayya ta taɓe baki tace; "asali na kuma? Bayan basa kauna ta", Fadil yace; "amma ai muna sanki mu ko?".

Abdul kuwa yana jin su amma be ce komai ba domin kuwa kwata kwata baya son hayaniyar ta dinga damun shi sanin cewa sai dai yayi ta jin ƙunar abin kuma haka shine su Hajjan suke so.

Ya fahimci abu ɗaya shine Brr Hauwa shine tafi tsana yayinda Hajja kuma jinin First love ne bata so.

Yana buɗe idanu yabi kwanar hanyar da kallo, ba zai ce ga abinda yake tunani akan yarinyar ba amma tabbas ya san akwai wani al'amari a rayuwar ta, ya sauke ajiyar zuciya yana me maida kanshi ya kwantar saman kujera.

Sun jima suna tafiya kafin suka iso unguwar tasu, wato *Unguwar Sarki* unguwar da kowa ke rayuwar shi ba ruwan wani da wani, wannan yana ɗaya daga cikin abinda yasa yake son unguwar tasu.

A bakin get aka tsayar dasu, ganin sun tsaya yasa Abdul ɗago kai yana kallon wanda ya tsayar dasu ɗin, mutumin kuwa sai faman washe baki yake yi.

Sumayya ta juyo tace; "Yaya kai fa Bala yake yiwa magana", Abdul ya sauke glass ɗin ɓangaren shi sannan suka gaisa.

Bala cikin durƙusar da kai yace; "dama ƙaramin oga wallahi tun wancan satin nake zuwa neman ka amma aka ce mini kana Rigasa".

Abdul yace; "ya akayi ne Bala?", Bala ya shafa kai sannan yace; "alfarma nake nema a wajen ka da kayi haƙuri na dawo bakin aiki na, Hajiya ta sallame ni akan kuskuren dana aikata kuma gashi yanzu gari babu aiki na nema wani ban samu ba, ga yarinyata da aka kwantar a asibiti shine da naji cewa ka dawo nace bari nazo to.kuma sai na taki rashin sa'a bakanan shine da nazo jiya ake ce mini yau zaka dawo to Allah da ikon shi tun safe nake zaman jiran ka".

Abdul ya dafe kai, wannan wane kalar dogon bayani ne haka, ya ilahi! Sai kuma ya ɗago yace; "ka shiga ciki bari mu shigo mu ma", da sauri Bala ya shige har yana ɗan haɗawa da gudu.

Fadil ya kwashe da dariya domin ya san dogon bayanin Bala ya ɓatawa Abdul ran shi, Abdus-samad kuwa kauda kai gefe yayi.

Ko kan su ƙarasa parking space ɗin har Balan yaje can yana jira, Abdus-samad yace da Sumayya; "menene aikin shi", Sumayya ta bashi amsa da; "wankin motoci yake yi".

Suna gama parking ɗin da kanshi yazo ya buɗewa Abdus-samad ɗin ƙofa, Abdul kuwa ya haɗe rai yaƙi fitowa, Fadil da ya san hali ya dubi Bala yace; "ka maida ƙofar ka rufe baya so ana buɗe mishi", cikin sauri Bala ya maida ƙofar ya rufe.

Abdul yayi murmushi sannan ya buɗe ya fito, masu aikin ya kira sannan yace; "waye ke aikin Bala a gidan nan", Idris yace; "nine nan".

"a da meye aikin ka?", Abdul ya kuma jefa mishi tambaya, Idris yace; "gyaran fulawa", Abdul ya kalli Bala yace; "ka koma bakin aikin ka kawai", yana faɗar haka yayi hanyar part ɗin shi.

Su Fadil kuwa mamaki ne ya cika su, na ganin direct ya bada umarni, Sumayya kuwa murmushi tayi kawai sannan tace: "kuzo muje, idan har kuna gidan nan sai kun dena mamakin ikon da Ya Abdul yake dashi".

Haka suka bi bayan Sumayya, duk ƴan gidan suna falo dan haka Adnan ya nufo su da gudu yana murna, Fadil ne ya ɗaga shi sama yana faɗin; "Oyoyo autan gidan".

Fadil ya ƙarasa kusa da Sameer da Tameer ya basu hannu suka gaisa, Fadila kuma ta gaishe dasu daga inda take.

Surayya tace; "yau kunzo mana gidan kenan? Ko kuwa dai kuma ɗan lelen kuka rako?", Fadil yace; "bangane ɗan lele ba?", ta miƙe tsaye tana me kwashe littattafan ta sannan ta juyo tace; "waye ɗan lele banda Ya Abdul", tana faɗar hakan ta nufi hanyar ɗakin ta.

Fadil da Fadila suka kalli juna cike da mamaki, sun san akwai ƙiyayya tsakanin ƴan gidan da Abdus-samad amma basu ɗauka tayi zafi haka ba.

Sumayya ta fara ƙwalawa Aziza kira, jima kaɗan ta ƙaraso Sumayya tace; "ki kawo wa baƙi ruwa mana", Aziza ta amsa da to sannan ta miƙe ta tafi.

Sameer yace; "ina Abdul ɗin yake?", Sumayya tace; "yana part ɗin shi", Sameer yace; "be san cewa munyi kewar shi bane shine zai wani tafi nashi wajen", ya ƙarasa yana miƙewa domin tafiya, Tameer yaja tsaki yana gyara kwanciyar shi.

"ya Allah! Wannan wane kalar gida ne babu daɗi", abinda Fadil ya faɗa kenan a ranshi, Sumayya ta.miƙe sannan tace; "Aunty Fadila zo muje ɗaki na", Fadila ta miƙe tabi bayan Sumayyar.

Fadil shima ganin yadda gidan yake yasa ya miƙe ya fice kawai, Part ɗin Abdul ɗin ya nufa, ƙofar a buɗe take dan haka ya shiga kawai.

Baya bedroom ɗin amma yana jiyo ƙarar ruwa hakan ya tabbatar mishi da wanka yake yi kenan?, Fadil ya zauna saman bed ɗin yana me bin ɗakin da kallo, kai kace ɗakin wani hamshaƙin me kuɗi ne komai kuma yana inda ya dace.

Abdul ɗin ya fito ɗaure da towel sai ƙarami kuma da yake goge kanshi dashi, ba tare da ya cewa Fadil ɗin komai ba, Fadil kuwa ya bishi da idanu.

Gaban dressing mirror yaje ya tsaya yana shafa mai, har ya gama yayi combing kanshi Fadil kallon shi yake yi, Wardrobe ya bude ya ɗauko kayan da zai saka.

Riga ƙarama baƙa da wando fari jeans three quarter ya saka sannan ya fito daga wajen canza kayan, tuararruka ya hau fesawa nan fa ɗakin ya buɗe da ƙamshi, ya ɗauki zoben shi ya maida yatsan shi yana cikin ɗaura agogo ya ɗago ya kalli Fadil ɗin ta madubi, ganin yadda yake binshi da kallo yasa ya ɗaga mishi gira ɗaya alamar lafiya.

Fadil ya girgiza kai yana murmushi, shima Abdus-samad ɗin murmushi kawai yayi yana me juya kanshi zuwa gefe.

Wayoyin shi ya kwasa sannan yace da Fadil ɗin; "muje ko?", tare suka fito daga bangaren, a harabar gidan suka tarar da sauran duk sun fito.

Kusa da Tameer da Sameer yaje sannan yace; "barkan ku da hutawa", Sameer yayi murmushi yace; "barka da fitowa ɗan lelen Mommy ai na shiga amma kana bayi lokacin".

Ba tare da Abdul ɗin yace komai ba ya lumshe idanun shi, Tameer yaja tsaki yana kauda kanshi gefe, hannun Abdus-samad Sameer yaja ya kai shi har gaban motar tashi sannan yace; "ga gift ɗin Daddy daya turo.mana da ita", murmushi kawai yayi kafin yace; "thanks" yana faɗar hakan ya juya ya koma inda yake ya zauna.

Shi kanshi Sameer yaji haushin abinda Abdul ɗin yayi.mishi haka ma su Fadil ɗin, Tameer kuwa murmushi yayi yana yin ƙwafa.

Sumayya ta zauna kusa da Abdus-samad ɗin ta riƙo hannun shi, ta buɗe baki zata yi magana ya buɗe idanun shi gaba ɗaya a kanta.

Wani irin abu taji wanda gaba ɗaya kamar ya janye duka miyau na bakin ta, maida bakin tayi ta rufe, a hankali yace; "pls kaina ciwo yake yi i need some space".

Tashi tayi ta bar wajen dan ta san tunda ya faɗi hakan to hakan yake nufi wato baya son damuwa.

Fadil da Fadila kuwa kallon su kawai suke yi, Surayya waya ce a hannun ta take latsawa Tameer ma haka, Sameer kuwa yana zaune ne yana kallon wani wajen.

Fadila cikin raɗa tace; "anya kuwa zan.iya zaman gidan nan?", Fadil yace; "zaki iya mana, meya faru?", tace; "kalli kaga fa basa fira tsakanin su ni da har ina cewa na baro kurkuku na dawo waje me ƴanci ashe gwara can da nan?".

Fadil ya girgiza kai yace; "taɓ gaskiya na tausaya miki to ko zamu tafi tare ne?", Fadila ta ƙwalalo idanu tana faɗin; "Abba Major fa?".

Fadil ya ɗaga kafaɗa, Fadila ta girgiza kai tana faɗin ka barni kawai a nan", Fadil yace; "to shikenan".

Ɓangaren Abdul kuwa wannan mafarkin daya saba shi yayi, sai dai wannan karon fuska ce wacce babu nama ko ɗaya a jiki take tsaye a gaban shi, iya fuskar kawai sannan tana ƙwala wannan kiran na *MURAD* a gigice ya farka duk ya haɗa zufa, duka suka bishi da kallo.

Ya sauke ƙafafun shi daga saman kujerar yana me dafe kanshi, Fadil ya ƙarasa inda yake ya dafa shi, Abdul ya ɗago ya kalle shi.

"lafiya kake kuwa?", abinda Fadil ɗin ya tambaya kenan, Abdul yayi murmushin dole yace; "lafiya ta lau", Fadil yace; "shikenan to bari nazo na tafi gida", Abdus-samad ya miƙe domin rakashi.

Sai da Fadil ɗin yayi musu sallama sannan suka ƙarasa kusa da motar shi, Abdul ya buɗe mishi ya shiga inda shi kuma Abdul ɗin ya juyo ya dawo ciki.

Fadila kam zaman gidan duk babu daɗi take ji amma bata da yadda zata yi dole hakan nan ta zauna a gidan dan shine rufin asirin ta kawai.

Wajen Sumayya ta koma inda nan suka fara fira domin ita kanta ta lura kamar zamar gidan ya ishe Fadilar hakan yasa tayi ƙoƙarin ɗauke mata hankali.

Abdul kuwa yana zaune a wajen ne amma kuma sanyi-sanyi yake ji hakan yasa dole ya miƙe ya koma part ɗin shi ya kwanta sai dai yana kwanciya zazzaɓi ya rufe shi.

Sai wajen Magrib sannan zazzaɓin ya sake shi, bayi ya shiga yayi wanka tare da ɗoro alwala yazo ya tada kabbarar sallar la'asar yana idarwa ya janyo waya domin kiran Fadil yaji ya yaje gida.

Ganin missed calls na Mommyn shi yasa yayi murmushi, tun safe daya kira ta akan zasu taho be sake kiran ta ba, number ɗin Fadil ya kira inda nan ya mishi ya yaje gida.

Fadil yace; "lafiya ƙau, ya jikin?", Abdul ya ɗan basar sannan yace; "na sami sauƙi, ni kuwa in tambaye ka mana?", Fadil yace; "ina ji".

Shiru yayi na ɗan lokaci kafin yace; "barshi ma kawai, sai anjima ka gaishe da Malama", Fadil yayi dariya yace; "shikenan ni.kuma ka gaida mini ƴan biyu ta", daga haka suka rabu.

Number ɗin Mummyn shi ya kira nan ya dasa mata shagwaɓa ita kuma tana ta yi mishi dariya, "Allah Mummy gidan babu daɗi da bakya nan har zazzaɓi sai da nayi baki ga yadda na rame ba".

Brr Farida tayi dariya tana faɗin; "asha yaron nawa rago ne ban sani ba, to idan na mutu fa", ya ƙara turo baki gaba kaman tana kallon shi yace; "nima mutuwa zan yi balle ma sai na riga ki mutuwa", cikin sauri Brr Farida tace; "ya isa haka, ina ƴan uwan ka?".

"nifa ina ɗaki na tun kan la'asar", Brr Farida tace; "kada kace mini a ɗaki kayi sallah", yace; "barci ne fa ya kwashe ni kuma da gaske nayi zazzaɓi yanzu ne na sami sauƙi".

Brr Farida tayi ɗan jimm sannan tace; "shikenan, Allah ya sauƙe, tahowar wuri zamu yi gashi ma ina ta haɗa kayan mu ka san mu yanzu dare yayi sosai".

Ya ɗan shafa kai yace; "hakane fa, bari naje nayi sallah bye", tace; "bye take care", yace; "sure love you", sannan ya katse wayar ya miƙe ya fice domin amsa kiran ubangiji.

Sai bayan isha'i sannan ya shigo gidan, a saman dinning ya tarar dasu, shima nan ya zauna suka ci abincin tare.

Firar dai sama-sama ce dan ji da kansu ba bari yake suyi wata fira ba, sai bayan sun gama ne ma ya ɗan taya su Fadila firar kafin ya nufi part ɗin shi domin kwanciya.

Laptop ɗin shi ya janyo inda ya kira Mummyn shi, bata yi barci ba dan haka kuwa suka shiga fira, duk da su can daren yayi nisa sosai, sun jima suna fira har barci ya ɗauke shi.

Brr Farida tabi ɗan nata da idanu tana murmushi, soyayyar shi daban take a zuciyar ta wacce ta san Allah ne ya saka mata shi, ko yaya zai ji a ranar da duk ya san gaskiyar rayuwar shi.

"kada ki damu zai ɗauki haƙuri", Daddy ya faɗa, ta juyo ta kalli mijin ta cikin karaya tace; "ina tausayawa halin da zai shiga Abban Adnan".

Dr Abubakar ya rungumo matar tashi yace; "kada ki damu komai zai zo da sauƙi, sannan ma bana jin zai san gaskiyar al'amari tunda kin riƙe amana sannan ba duka mutane bane suka san ainihin waye shi ba".

"amma kuma Malama ta sani, sannan shi kanshi ya fara mini tambayoyi akan waye Murad ga Alhaji Mustapha dake raye kuma na san har yanzu yana bibiyar rayuwar Abdus-samad ɗin".

Dr Abubakar yace; "kada ki damu hakan ba zai zama wata barazana ba domin kuwa Allah zai mana tsari dashi", haka ya dinga lallashin ta har ya samu hankalin ta ya kwanta.



#LIKE
#SHARE
#COMMENT


*Babyn Abdul, Maman Meenal, Elham da Farouk*.


*ƳAR MUTAN ZAZZAU*




♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠
*RAYUWAR ABDUS-SAMAD*
♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠♠


https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/


*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*




*~We are bearer's of so golden pen🖊~*

*~we write assidiously perceive no pain~.*

*~So magical,Our creative golden pen✍,behold our words.~*

*~A product of our pen🖊,savour our words, for it will cause you no pain.~*







*_daga alƙalamin ✍_*


*ƴar mutan zazzau*
*(one love)*

*sadaukarwa gare ku*


*Bashier Sufyan(Sardaunan gauraye)*

*Ibraheem Aliyu (Jikan Nufawa)*

*Heart you so much*

*Sannan ga masu son shiga whatsapp group na Rayuwar Abdus-samad kuyi searching Aishatu Babayo sai ku tura mata da number ɗin ku ta pc zata saka ku a ciki amma dan Allah iya mata kawai banda maza, Na gode sosai*

📖📖29-30📖📖


Fadila tana gyara ɗaurin ɗan kwalin ta Abdul ya turo ƙofar ya shigo, koda ta kalle shi sai da numfashin ta ya kusa ɗaukewa ganin irin kyawun da yayi.

Sumayya dake ƙoƙarin ɗaure gashin ta, ta juyo tace; "wow Ya Abdul ka haɗu kamar yau ne ɗaurin auren ka", ya gyara links ɗin shi sannan yace; "ku fito fa, dan bana so First love tayi zaman jiran mu".

Fadila ta ɗaga kai alamun to, tana ƙara kallon ɗan uwan nata, cikin shigar manyan kaya wato shadda kalar sararin samaniya wacce taji aikin hannu.

Kanshi babu hula sai dai kwantacciyar sumar shi wacce ke ƙara mishi kyau, ya juya cikin ƙasaita ya fice daga ɗakin.

Fadila ta saki wata irin ajiyar zuciya har sai da Sumayya ta kalle ta, cikin sauri Fadilar ta basar tana me zama gefen gadon Sumayya.

Yana tsaye ya juya baya yana amsa waya suka fito dukan su, ganin waya yake yi yasa duka suka tsaya Surayya ita ma ta fito sanye da riga da skirt na atamfa.

Abdul tace; " ka bari later kawai yanzu zamu je ɗauko Mummy ne a airport", yana faɗar haka ya katse wayar.

Ya juyo ya kalle su, Surayya ita kanta sai da taga kyawun Yayan nata don haka cikin sauri ta kauda kai, ita fa abinda ke hanata tafiya tare dashi kenan sai tayi wanka na ƙasaita yana yin nashi sai ya shafe nata.

Suna gaba yana baya haka suka fito harabar gidan, anan suka tarar da Tameer da Sameer, kowannen su cikin shirin ɗauko iyayen nasu.

Abdul yayi murmushi yace; "to muje", yana ƙoƙarin buɗe mota, Tameer yace; "amma dai ya kamata ace mun hau motar da Daddy ya siya mana ko?".

Sai da Abdul yayi ɗan jimm sannan yace; "to shikenan", Tameer yace; "idan ma baka son jar ne, ga makullin tawa", Abdul ya kalli yayan nashi da mamaki sai kuma ya kauda kai cikin sauri yace; "nop bari naje a tawa kawai".

Tameer ɗin ya taɓe baki yana me nufar tashi motar, shima Abdul ya nufi tashi, Abdul da Sumayya sai Adnan a baya, sai Sameer da Fadila dan tace ba zata shiga jar mota ba kamar ta ƴan shan jini, Surayya kuwa ta Tameer ta shiga domin tafiyar su zata fi dai-dai.

Haka suka fice daga gidan cikin farin ciki domin zuwa ɗauko iyayen nasu babu ma kamar Abdus-samad wanda yake jin kamar ya shekara ne bega mahaifiyar tashi ba.


********* **********


Nusreen ta kalli Nusram wacce ta zuba ubam tagumi, itama cikin damuwa ta ajiye zanin gadon dake hannun ta, ta zubawa ƴar uwar tata idanu.

Ummi da Auntyn Tudu suka shigo tare wanda hakan shiya dawo da Nusram daga duniyar tunanin data tafi, cikin sauri ita da Nusreen suka amshi kayan dake hannun su.

Sai da suka zauna Aunty tace; "Wash wallahi na gaji, Allah yasa ma wancan yaron ya amso ragowar", Ummi tace; "tunda har kin faɗa mishi zai amso ne kada ki damu".

Kaya ne na kitchen sai kuma sauran kayan da zasu yi amfani dashi na bikin, nan aka baje ana gani, ita dai Nusram nata idanu ne babu abinda take tunani sai auren da zata yi.

Nusreen ta juyo ta kalli ƴar uwar tata sannan tace; "Ram

Please Login or Register in order to submit comment