Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a waya amman ba'a sameshi ba, shine sai shi wannan bawan ALLAHn ya karb'i tayin aurenta ga waliyyanshi anan su ne suka karb'i aurenta wajen Baba Buba"

Cewa da D'an uwan Baffah'n Wanda shine ya bada auren Dijen ga Safwan, cike da tsananin firgici Baffah'n ya koma ya zauna dab'as yanata jero salati, tare da godewa ALLAH da har hakan bata kasance ba.

Cikin zubowar wasu hawayen takaici ya kalli SAFWAN yace,. "A matsayina na Mahaifin Dije na rok'i alfarmar ka sauwake mata, don ko auren da Balan yanzu na janyeshi ba za'a sake zancenshi ba har duniya ta nad'e, ina yi maka godiya sosai na gode da taimakonka amman don girman ka taimaki rayuwata da ta 'yata ka sauwak'e mata yanzu ba sai anjima ba"

SAFWAN cikin sauri ya duk'e kanshi tare da yin nazari na d'an lokaci, sannan ya d'ago da jajayen idanuwanshi da a take suka sauya zuwa tashin hankali, ya shafo dan k'aramin gemunshi sannan yace

"Ka yi hak'uri Baba wasiyyar da Mahaifina ya bar man kenan lokacin da zai rasuwa, akan cewa duk runtsi kada in zamo mutum mai auri saki, ballantana irin wannan auren da ko ina ba'a je ba ya haneni da yin irinshi tun lokacin da yana ray...."

Zancenshi ya katse ne saboda ji yo sautin Dije da aka yi tana fad'in,. "Ai billahillazi daga kai har Balan sai kun san da ni kuke zancen, Ni za ku ci wa amana ku yi man k'azafi da raina ban mutu ba??????"

SAFWAN da Balan suka yi saurin kai kallonsu gareta, cikin sabon b'acin rai Safwan ya mik'e ya kalleta ido cikin ido yace

"Ni zan yi maki k'arya?? Yanzu kina nufin kin manta lokacin da kika zo kina fad'a man maganar?"

Dije ta fashe da kuka tace,. "Ai WALLAHI sai dai in aljanuna ne amman Ni kam bansan ma na yi ba"

Safwan ya kalli Maigarin yace,. "Baba ai kasan lokacin da kuka je ganin ya nake bayan ta fita wurina aguje ko?"

Maigarin yace,. "Tabbas hak'ik'atul amri ba ma Ni kad'ai ba har ma da su Malam Tsalha duk mun ganta da idanuwanmu lokacin da ta zo"

Safwan ya ce "to ai a ranar ne take sanar dani wannan magana, har ma ta rok'eni ta ce da Ni don ALLAH ka da in fad'a har sai bayan sun mutun ita da Angonta, Ni kuma ganin zata je ta yi aika aika yasa lokacin da shi Balan ya zo neman Abokina ban ja da tsauri ba na amince a d'aura da Ni, saboda haka ina b'ukatar a bani Matata yanzu mu kama hanyar garinmu saboda mu yi saurin isa gida tare da Iyayena da suka yo tattaki tun daga Yola har wannan Gari domin kawai su karb'a mani aurenta"

Baffah ya mike cikin wata sabuwar rud'ewa yace,. "Ni fa kam ba fa zan lamunta da aje man da 'ya ko'ina ba, shiyasa tun farko naki amincewa da auren Abokinka, ashe ban tsira ba na yi gudun gara ne na fad'awa zago"

Ya k'are maganar cikin share wasu hawayen tashin hankalin rabuwa Dijenshi, cikin sanyin jiki Safwan ya kalli Dije da ke tsaye gaba d'aya ta rasa ma abun cewa saboda tsabar gaskiyar da ta yi mata yawa, sai canke canke ta ke yi wai ko dai da gaske tana da aljanun bata sani ba??don ita daga Balan har Safwan d'in bata san ta yi makamanciyar magana irin haka da su ba.

Cikin d'aga murya Safwan yace,. ,"Ke!!"

Ta yi saurin dawowa daga tunanin da ta lula tare da Kai kallonta gareshi, ba kunya Safwan ya rik'o hannunta suka yi nesa kad'an da mutane, sannan ya ja ya tsaya yana k'are mata kallo cikin mere yace

"To bari kiji ni taimakonki zan yi idan munje in sakaki Makarantar secondary har ki zama babbar Likita, idan kuma ba zaki so ba ki fad'a yanzu sai in barki tare da Mahaifinki ya aura maki duk wanda yake so, tunda ke kin kasa hango irin taimakon da zan yi maki bale har ki shawo Kan Mahaifinki ya aminta da auren, bale har ki nuna masa ke zaki aureni kuma za ki bini garinmu duk in da nake ko don cikar burinki na zama babbar Likita"

Dije ta washe baki tace,. "Da gaske Kai ma zaka sakani Makarantar likitocin???"

Safwan ya ce "Eh amman idan har kin amince da aljanunki sun fad'i cewa sai sun kasheki sai sun kashe Bala, sannan kuma idan kin amince za ki bini garinmu"

Dije ta yi saurin kallon hannunta da ya rik'a tace,. "Zan bika amman ya Zan yi da cikin da ka yi mani yanzun nan?"




🤣🤣🤣sai kunzo suna Dije ta samu ciki🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️





Akafta😝







D/AUTA CE🤝🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻*


*Lamba ta 24*



Safwan ya zaro ido waje yace,. "Ci me...??"

Dije ta bata fuska ta bar wajen tana ta yarfa hannun alamun k'yama ta nufi wurin Baffanta tace,. "Ka kwantar da hankalinka Baffah duk bayan kwana biyu Ni zan dinga zuwa ina dubaku kaji?"

Ta k'are maganar tare da langab'e kai, Baffahn ya yi mata wani kallo sannan yace,. "Za ki yi man shiru ko sai na mazgeki?? k'iri k'iri kin sa komi ya lalace muna saboda bak'in sakarcinki, to ni Kinga tafiyata idan kin tashi ki bisu ku je bangon duniya ma in kina so"

Yana kare fad'ar maganar ya mike fuuu! Yana kakkab'e riga ya nufi hanyar Gida, Maigarin ya kalli Dijen yace

"Kin amince zaki bi Mijinki?"

Dije ta d'aga kai tana yarfa hannunta da Safwan ya rik'e fuskarta a yamutse hawaye suna sauka tana saka d'ayan hannu tana sharewa, Maigarin yace

"Alhmdllh"

Sannan ya kalli IYAYEN Safwan yace,.

"Ku yi hakuri bayin ALLAH daga yanzu zuwa gobe za mu shawo kan matsalar, insha ALLAHu tun da sassafe sai ku kama hanya,saboda haka na wakilici MALAM Sanda na amice idan kun tashi ku je da Dije amman da rakiyar mutum Uku zuwa hudu ta gefenmu, saboda mu ga muhallinku kuma mu san inda za'a kai 'yarmu Dije"


Gaba d'aya suka amince da hakan, Maigarin ya kalli Bala ya ce, "Kai kuma sai ka nemi matar da duk kake so a garin nan ka aura tunda har hakan ta riga da ta kasance"

K'anen Mahaifin Bala ya fito da kud'i ya nufi wurin Baban Ladiyo ya ajiye kud'i tare da rusunawa yace,. "A matsayina na k'anen Mahaifin Bala ina nemarwa Bala auren yarka Ladiyo, idan ka amince yanzun nan sai a shafa fatiha kowa ya shaida"

Baban Ladiyo ya daburce ya kalli sauran d'inbin jama'ar da ke wajen yace,

"Ni Malam Shehu na amince da na baiwa Bala auren 'yata Ladiyo jama'a ku
sheda"

Ladiyo ta zaro ido tare da barin wajen aguje ta nufi gida Mutane sai dariya suke yi mata, daga nan ba b'ata lokaci aka rarraba goro cikin dan kankanin lokaci aka d'aura auren Ladiyo da Bala, Baffah Kuma aka kai k'arshe akan za'a kwaso masa kayan d'akin Dije da aka jera gidan Bala a dawo masa da abunshi.

Sannan cikin mutuntawa Maigarin ya sa aka shigar da Iyayen Safwan d'akinsu Safwaan d'in, tare da yi masu tarba da abinci mai rai da lafiya wanda Safwan ya sa aka tanadar masu tun kafin su shigo garin.

Bayan sun kimtsa ne Safwan ya yi masu jagora har babban birnin garin ya sama masu masauki sannan ya juyo ya dawo k'auyen.

Dije kam cikin firgici ta koma gida tana yarfa hannu saboda ganin take yi ta hakan ne macizan zasu zube ba za su yi nasarar shiga jikinta su taru ba balle cikinta ya yi k'ato, su Jummala suka biyota d'ii! a baya sunata jin ina ma su ne suka sami irin wannan damar, ta auren mutum d'anboko irin Safwan ga shi fari mai kyau da shi.

Shigarta Gidan ke da wuya ta fara jiyo sautin Baffanta da ya ke ta zuba fad'a cikin d'aga murya, jiki a sanyaye ta isa d'akin nashi tare da rakubewa gefe tace

"Baffahna don ALLAH ka yi hak'uri ka barni in je birnin nan, ka ga idan na yi kud'i na zama likita shikenan zan zo in ta fi da kai mu zauna da ku kai da Inna inda nake"

Baffah ya maka mata wata Uwar harara da jajayen idanuwanshi yace,. "Ke dad'ina da ke sakarci shikenan tunda ya jaki gefe ya karanta Maki k'arya tare da yi maki wayon ya cusa maki ra'ayin biyarshi Ni ma hakan za ki yi man kenan ko?, To bari kiji aure dai an riga da d'aura ba kuma yanda Zan yi in kwanceshi da hannuna amman ki sani ba zaki tab'a biyarshi ba, na fi son abarman ke da igiyar auren saman kanki a gabana har k'arshe duniya aga in.........."

"Da ko baka ji dad'i ba WALLAHI don wannan abin kunya ne ka ke so ka janyowa zuri'armu, saboda haka matuk'ar ina raye Ni ba za'a yi haka ina kallo ba"

Maganar tsohuwa Inna Gambo ce ta katsewa Baffah zancen da yake yi, ta k'araso cikin d'akin tare da dogara sandarta Inna ta yi saurin shimfida mata tabarma ta zauna, Dije ta ja jiki ta isa wurinta ta fad'a jikinta ta fashe da kuka wiwi, Inna Gambo ta shafo kanta tace

"Daina kuka ke ma zaki je ki yi aurenki kamar yanda kowace mace take yi a gidan Mijinta"

Sannan ta d'ago da kanta ta kalli Inna da ke ajiye mata ruwa a sabon kwanon sha tace,. "Ku bar ruwanku bana sha tunda har kuke so ku hana abunda ALLAH ya k'addara, idan ba shirme ba wa ya isa ya ja da hukuncin ALLAH?? Yanzu ku ba ku gano cewa shi ALLAH ba'a yi masa dabara ba?? Kun hanata auren wancen sai gashi ba zato Wannan d'in kuma ya zama ashe shine Mijin, to gargadi na k'arshe gareka Sanda ka kiyayi yin ganganci da abunda ALLAH ya riga da ya tsara a rayuwar 'yarku, don daga Kai har ita Hasiya babu wanda yasan hikimar abunda ALLAH yake nufi da hakan, saboda haka ka bar Dije ta bi Mijinta ku bita da addu'ar fatan zaman lafiya, don sau da yawa abunda baka so shine alkhairinka abunda Kuma kake so sai ka ga ba'a cen alkhairin yake ba, don ba zaka gano hakan ba har sai ka bi diddigi ka sami abun ta k'arfin tsiya sannan ne daga baya zaka gano kuskuren da ka tafka, yo in banda rashin hankali irin naka Sanda ka dubi fad'in garin nan kaf! amman ace 'yarka d'aya ta tab'a samun wannan nasarar auren mutanen birni, ba ka ganin hakan ma wata baiwa ce???, To ka ajiye komi ka fuskanci gaskiya ka gano alkhairin da ke gabanka da sannu a hankali zaka gano manufar yin hakan"

Baffah ya yi saurin share guntayen hawayenshi da suka cika masa ido yace,. "Ki yi hak'uri Inna na amince ALLAH yasa shine alkhairin kamar yanda kika fad'a, amman kam Dole ne in je inga inda za'a kaiman 'yata ko a ina ne ko"

Dije ta mik'e daga jikin Inna Gambo tace,. "WALLAHI Baffah shi ma ya ce zai sakani Makaranta a cen birnin har in zama likitar"

Baffah ya mike tsaye zuciyarshi cike da k'una ya fice don baya son ya furta wani abun da yayar Mahaifiyarshi da ta rage kaf cikin dangin iyayenshi taga ya yi mata rashin kunya, Dije ta bishi da kallo ta sake komawa jikin Gambo tace

"Ni dai Gambo na fasa zuwa birnin tunda Baffahna baya so"

Gambon tace,. "Ko shi ba so ne ba ya yi ba rabuwa da ke ne baya so, musamman da aka ce garin Mijin naki nesa ne sosai"

Dije ta yi saurin fad'in cewa,. "To ai duk bayan sati biyu Sai in dinga zuwa ganinKu ke Gambo"

Inna Gambon ta yi dariya tace,. "Ai ko shekara shekara kike zuwa kin yi sauri ballantana sati biyu"

Dije ta yi saurin mik'ewa tace,. "Ai Ni kam ko wata bazan bari ayi ba Gambo, kuka zan ta yi masu sai an kawoni na ganku WALLAHI "

Gambo ta yi mere tace, "yaro man kaza ke dai ki rik'e abunda na yi ta fad'a maki saboda aure yana da dad'i amman Kuma yana da wahala, don haka ba za'a ci ribarshi ba har sai an had'a da hak'uri, kiji ki ki sauraro ki gani ki yi Kamar baki gani ba, ki rufe kunnuwanki ruf ki raba idanuwanki da ganin abunda bai shafeki ba"

Haka Inna Gambo ta dauki lokacin tana ta baiwa Dije shawarwarin da ita sam bata san ma'anarsu ba.

Ko da dare ya yi Maigarin ya zo da kanshi ya yiwa Baffah bayanin abunda ake ciki, ba jayayya ya amince amman yace k'afarshi kafarsu sai yaga inda za'a kai masa Dijenshi.

Inna da Baffah'n kwana suka yi sunata ja mata kunne tare da nasihohin da Suka sakata jin bata son tafiya ta barsu, Baffah ya k'arfafa mata gwiwa akan cewa ai tare za su, sannan hankalinta ya kwanta.

Aiko Asubar farin ta nufi gidan Gambo ta d'auko ajiyarta tare da yi mata sallama, haka ta bi gidan kawayenta duk tana yi masu bankwana kamar ba Amarya ba, alhali cen gidan sai nemanta ake yi akan ta shirya kar su makara a tafiyar tasu kasancewar tafiya ce sosai a gabansu.

Tare da rakiyarsu Hansai da su Jummala da Lanti har da Mune ta dawo gidan zuciyarta cike da tunanin jin wai Bala ya auri Ladiyo kawarta.

Bayan sun shirya ne Safwan da Iyayenshi suka zo sake gaisawa da Baffah, ba k'aramin dad'i Suka ji ba da ganin sauyin da aka samu, don har cikin Gidan Baffah ya yi masu jagora Safwan ya gayar da Inna bayan sun gaisa da Iyayen nashi, sannan suka yi masu alkhairi mai tsoka don har gidan Gambo aka kaisu suka gaisa itama suka yi mata alkhairin.

Inna Kam cikin sanyin jiki ta jinjina maganganun da Inna Gambo tayi, saboda ganin Safwan da Iyayenshi yasa ta gano ba k'aramar baiwace Allah ya yiwa Dijensu ba, mutanen unguwa da abokan arzik'i suka cika k'ofar gidan dank'am ana yi masu sallama, bayan duk wad'anda aka zab'a za'a je da su kowa ya shiga motane amman ba'a ga Dije ta fito gidan ba, ana k'ok'arin a shiga a fito da ita ne sai gata ta fito janye da akuyarta tana fad'in

"Zo muje ke ma ba zan ci amanarki ba don zan zama Likita, don haka dole ne kema in kin fara zawo in yi maki allura"

Cike da mamaki kowa ya saki baki yana kallonta, Safwan kam mere ya yi ya d'auke Kai yana k'umshe dariyarshi, Inna ce ta karb'e akuyar tana cewa da ita ta bari idan ta sake dawowa ta tafi da ita, Dije Kam ta fashe da kuka cikin fushi Usman ya fisgo hannunta ya sakata motar Safwan a seat d'in gaba ya zaunar da ita sannan ya rufe k'ofar.

Haka Suka bar k'ofar gidan sai bye bye ake yi masu tare da yi masu addu'ar ALLAH ya tsare hanya.




Maza bisa Kan Yan birni😝





Akafta🤣





D/AUTA CE🤝🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*GA KIRA DA BABBAR MURYA BAN YARDA BA KUMA BAN AMINCE BA BAN LAMUNTA BA DA A SAKE CANZA KO A SAKE SARRAFA MANI LITTAFAINA BA TA KOWACE SIGA*
*TARTSATSI.*
*RUWA DA. KANKARA.*
*DIJE K'ARANGIYA*

*NI HADIZA D/AUTA BAN LAMUNTA BA AKAN KOWA DA YA SAKE SARRAFA MANI LITTAFAINA BA TA KO WACE HANYA DA KO WANE YANAYI BA TARE DA IZININA BA AKASIN HAKAN KUWA WALLAHIL'AZIM ZAMU GAURAYA DA KOMA WACEE DON SAI NA JA HAKKINA AKAN KOMA WA YE A BI DOKA A ZAUNA LAFIYA🤝🏻*
BAN AMINTA BA!
BAN AMINTA BA!
KAR A SAKE!
KAR A SAKE!


*Lamba ta 25*



DIJE kam duk Wanda ta sani sai ta tashi tsaye ta fito da kanta tana d'agawa mutane hannu, tun Safwan yana jin takaicin abun a ranshi har sai da ya kai ya katsa mata wata arniyar tsawa yace

"Wai ke wace irin bak'auya ce ke? Wannan abu da kike yi tamkar wata zararra fa?"

Dije kam bata daina gaisawa da mutanen k'auyensu ba, cike da jin haushin abin ya ciyo kugunta ya janyo zanenta da k'arfi ta dawo dab'as ta zauna, kanta ya bugu da bayan seat d'in tace

"Wash! ALLAH kaina"

Cikin masifa yace,. ,"Ya dad'e bai cire ba shi kan naki tunda ke ba kya ji WALLAHI ba zan lamunci hakan ba"

Dije ta makure ta sha jinin jikinta tana yi masa hararar gefe tana mui mui, mata biyu yan rakiyar Dijen da suke tare da su cikin motar suka had'a baki wajen fad'in cewa

"Don ALLAH ka yi hak'uri k'urciya ce"

Safwan ya yi banza da su tamkar ma bai ji su ba, ba shiri su ma suka yi gum motar ta yi shiru na d'an lokaci aikuwa cen Dije ta hango wata 'yar Makarantarsu ta Allo ta yi saurin yin wani zillo tamkar biranya ta dale saman seat d'in da kafafunta ta tashi tsaye ta fito da jikinta suka tana fad'in

"Ladidi kin ganni nan cikin mota anyi mani aure birni zan je, me kike so idan zan dawo in kawo maki?"

Ladidin ta washe Baki tace,. "Burodi nike so Dije don ALLAH fa kar ki mance kinji??"

Dije tace, "bazan mance ba Ladidi Sha kuruminki kinji ai kud'i zan yi idan naje, ke karatun Likitancin fa zan yo a cen fa ki ce da Malam Mainasara ya ci gaba da yi man addu'a sai na dawo"

Haka Dije ta yi ta zuba shirmenta da Ladidi har suka daina ganin juna, sannan ta dawo ta zauna tana washe Baki tace

"ALLAH sarki garinmu shikenan zan barka kar ka yi kuka ka ji sai na dawo"

Safwan dai zuciyarshi ta kai wuya ya k'ufula sosai Shiyasa bai biyeta ba don matuk'ar ya kulata ba k'aramar jibga zai yi mata ba, gashi tare yake da Baffah'nta da yan uwanta yasan dole ne sai sunji ba dad'i, shiyasa ya yi kwafa kawai ya yi sannan ya ci gaba da tuk'inshi sannu a hankali har suka shiga babban birnin k'auyen su Dijen, aiko tana hango wani mai shayi da biredi motar tana gudu ta fara yunkurin tsallakewa ta tagar da nufin ta fita, Safwan ya yi nisa da tunani sai gashi ya dawo hankalinshi ba shiri saboda fahimtar abunda take so ta yi, aiko ba shiri ya fisgota ta dawo ciki tare da yin sauri ya zuge glass d'in ya rufe ruf, ta yi saurin kallonshi tace

"Don girman ALLAH ka barni in sha shayi da burodin cen WALLAHI raina ya biya sosai, ka ga yawuna ma har sun tsinke gaba d'aya WALLAHI"

Ta k'are maganar tare da had'iye wasu yawun suka wuce a makoshinta kutt! Safwan ya yi banza da ita, Dije ta tashi ta fara dukan gilas d'in tana fad'in

"Wayyo ALLAH ga wani kifi cen za'a gasa daga ganinshi zai yi dad'i WALLAHI"

Cen kuma ta sake cewa "ji matar cen tana soya kosai gaskiya daga ji zai yi dad'i WALLAHI, har da wani Abu gashi cen ina ma zan samu in ci shi inji?"

Ta k'are maganar cikin marairecewa Safwan ya yi k'ok'arin yin parking a gefen titin ya fito ranshi a b'ace ya nufi wurin mai suyar k'osan, mintuna a tsakani sai gashi ya dawo da ledodi himili guda sai ga motar bayansu ta Iyayen Safwan, wadda Baffahn Dije yake ciki suma sun tsaya suka ce da shi lafiya?, Kai tsaye ya sanar da su cewa Dije ya yiwa siyayyar abun kari tace bata karya ba, cike da jin dad'in hakan Baffahn ya washe Baki ganin himilin ledodin, sannan ya ce da su su tafi abunsu kawai shi zai biyosu daga baya, Baffahn ganin Dijen da Mata biyu yan garinsu yasa bai ji komi ba ya koma motar suka tafi, shi ko ya bud'e murfin gefen Dijen ya zuba mata ledodin a cinya duka ya karb'i wata da wani yaro ya rik'o masa itama duk ya tula mata a jiki sannan ya rufe k'ofar garam! Da k'arfi ya zagaya ya shiga ya tada motar suka bar wajen.

Sai ga Dije da kwallah k'ara tana fad'in wayyo ALLAH zafi kunama tana cizona a cinya WALLAHI"

Ya yi banza da ita cikin sauri ta ture ledodin da ke saman cinyarta sai ga Ledar ruwan zafin shayin da yasa aka k'ullo mata ta fado k'afarta har sun zuba kad'an ta yi saurin d'age k'afar tana fad'in

"Wayyo ALLAH zafi"

Ta saka hannu ta shafo k'afar ganin abu fari yasa ta lasa aikuwa ta yi saurin dukawa ta d'auko ledar tana wash! zafi tana lasar bayan ledar inda shayin ya zubo ya b'ata bayan ledar.

Sannan ta ajiye ledar gefen sitarin motar ta duka ta d'auko wata ledar sai ga kosai yana tiririn zafi, ta yi saurin budewa ta d'auko guda ta kai baki sai gata da yin saurin fad'in

"Wayyo!"

Ta fara hura bakin da hannu tana fad'in,. "Wai wai gaskiya wannan yafi na garinmu dad'i"

Sai da taci sosai sannan ta waigo ta mikowa su Inna Kandala rabi tace

"Ku ci kuma ku ji yafi na garinmu dad'i"

Sai da taci kosan sosai sannan ta bud'a wata ledar sai ga soyayyar doya da kwai ta yi saurin zaro ido tace,. "WALLAHI shine na hango kai honi Dije yau ina ta shan dad'ina WALLAHI cabd'i"

Ta sake rabawa biyu ta mik'awa na baya ta fara cin doyar tana fad'in,. "Shi Kuma wannan abun ko da mi ake had'ashi shi kuma? Kai Yan birni suna jin dad'insu WALLAHi"

Haka ta tasa doyar a gaba ta ci mai isarta sannan ta fara sauke nishi tana fad'in,. "Cikina zai fashe yasin"

Sannan ta ajiye ledar doyar itama ta bud'e wata ledar sai ga waina da miya k'ulle a leda sai kamshin manshanu ke tashi, Dije ta zaro Ido tace

"Kai kai ho! ni Dije ho! Ni Dije gashi na koshi bansan ya zanyi da wainar nan ba?"

Safwan ya yi saurin fad'in,. "Ki zubar kawai a wuce wajen"

Ta k'ara damke ledar tace,. "Cabd'i ai WALLAHI Ni kam sai na cita inji ya take itama, don nasan dole ma ta yi dad'i don ba zata yi kamshin banza ba"

Sannan ta ajiye ledar wainar ta d'auko wata leda sai ga k'aton Biredi ta zaro ido tace,. "Idona idonka WALLAHI wayyo ALLAH dad'i na gode sosai ka ji in akuyata ta haifu na yi maka alk'awali zan baka abunda ta haifa kyauta ai kana so ko?"

Safwan ya shafa gemunshi yace,. "A yi ta kaya Ni kam na yafe"

Dije ta zunburo Baki tace,. "Don ma ka samu zan baka?"

Tana k'are fad'ar maganar ta ciro ledar shayin ta huda ta fara gutsuro biredi katoto guda ta kurbi shayin, tace

"A'a'a'ah haka shima
nasu shayin yake da dad'i haka? Wayyo har wani k'amshin dad'i yake yi yasin, Kai garin dad'i na nesa Kai! Kai! Kai!"

Haka ta dinga sambatu tana Shan shayin da biredin har ta kusa canye rabin ledar biredin sannan ta yi gyatsa tace,. "Alkur'an yau na yi cin haram ALLAH ya jikanki Dije ina Innata tana kusa ta ci itama ta ji"

Ta mik'awa matan biredin da ledar shayin ta shafa cikinta tace,. "Sai ka sacce in sake cin wainar itama inji ya take"

Kafin ka ce me sai ga Dije da langabewa tana bacci sai ajiyar zuciya take saukewa a hankali, Safwan ya kai kallonshi gareta ya girgiza Kai a ranshi yace,.

_"Dole ki yi bacci wannan ci da kika yi kam acicin banza wa'kazuba"_

Sannan ya mayar da hankalinshi akan tuk'inshi yana yi yana murmushin da shi kad'ai yasan ma'anarshi.

Tafiya ta mika Safwan da sauran abokan tafiyar sai shillawa suke yi Kan titi suna k'ara nausawa Kan hanyarsu, Dije kam har lokacin baccinta take yi har sai da lokacin sallah yayi Suka tsaya suka yi suka ci abinci Suka k'ara mikar titi tun suna jin dad'in tafiyar har dukansu suka fara jigata musamman su Baffah da Basu tab'a irin tafiyar ba, Dije kam duk sai da ta canye komi sannan ta ji natsuwa ta zo mata, shiyasa ba wuya ta sake komawa bacci har duhun dare ya sauka.

K'arfe d'aya saura Suka isa garin Gombe inda suka yada masauki a wani hotel da nufin tun da sassafe su kama hanyarsu ta zuwa Yola.





Akafta👍🏻






D/AUTA CE🤝🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*GA KIRA DA BABBAR MURYA BAN YARDA BA KUMA BAN AMINCE BA BAN LAMUNTA A CANZA A SARRAFA MANI LITTAFAINA BA

Please Login or Register in order to submit comment