Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yi mata kalamai masu sanyi tare da kiran sunayen da suke faɗawa junansu cikin wata murya mai tsada, cikin nasara Zee ta dawo hayyacinta tare da fara zubar da hawaye gefe da gefen fuskarta, sannan ta ƙura masa ido ko ƙiftawa bata yi saboda ganin take yi abun kamar almara ko a mafalki, Safwan ɗin da ko hannunta bai son taɓawa ko acen ƙasar Turai wai shine yau da tsotsar bakinta, cikin mayen sonshi da ke fisgarta ta riƙe hannunshi gam ta ce

"My man me yasa ka yaudareni?"

Ya yi saurin ɗora hannunshi akan lebenta yace, "ki bar zancen plss a shirye nike da aurenki a duk lokacin da kika tashi"

Zee ta washe baki cikin farin furucinshi ta ce, "duk da ka yaudareni amman still har yanzu ban daina sonka ba, me yasa so yake makaho ne? me yasa zuciyata ta ƙi karɓar ƙiyayyarka da na yi ta cusa mata?, Haƙiƙa ka yi nasarar samun sarautar zuciyata You are my prince chrmn and my everything shonah"

Safwan cike da tausayinta yace "na yi kuskure ki yafe mani albarkacin son da kike mani ko don ceto lafiyarki, saboda ko da ina son a yi muna auren yanzu kin ga sai an jira kinji sauƙi tukunna, don kin san ba za'a yi aure kina cikin ciwo ba"

Zee ta yi saurin share hawayenta ta yunƙura da nufin ta shi zaune amman ta kasa, dole ya riƙata ta tashi zaunen tare da taimaka mata ta jingina jikinta da filo tana binshi da kallon ƙauna, cike da jin daɗin ganin nasarar da aka samu ne Safwan ɗin ya leƙa ya kira likitocin, abun mamaki sai ga Zee sun taradda ita zaune tana share hawayenta jefi jefi.

Cikin sauri wani likita ya kira Iyayenta suka shigo cike da jin daɗin albishirin ɗin da ya yi masu, mamaki fal zuciyoyinsu saboda ganin yanda ta ke zaune har da su dariyar ƙarfin hali, dukansu har likitocin sun gasgata ba ƙaramin so Zee take yi wa Safwan ba, Aminu kanshi da ya dawo ya taradda ita zaune ana bata tea tana sha ya jinjina lamarin, take yanke ya sallamawa kanshi barin Zee ko don ta samu abinda take so, saboda a yanzu ya tabbatar da cewa babu wanda ya isa ya yi abunda ALLAH bai tsara a cikin rayuwarshi ba, haka wani bai isa ya auri matar da ba ta shi ba, don da tuni ya aureta saboda dakon sonta da ya yi ta yi a zuciyarshi tun tana ƙarama.

Kowa sai murna yake yi kan haka ne ma mahaifin Zee ya ja hannun Safwan ɗin suka fita, cike da jin daɗin ganin ƴarshi ta fara dawowa hayyacinshi yace

"Duk da bansan me ya haɗaka da Zainab ba amman jikina ya bani cewa kai ka janyo mata shiga halin da take ciki, a matsayina na Mahaifinta ina roƙonka da ka taimaki rayuwar ƴata ka aureta, tunda har kai take so ni ba zan takura rayuwarta ba saboda haka ba zan taɓa aura mata wanda bata yi na'am da shi ba, idan ka shirya ka turo iyayenka ni zan aura maka ita da hannuna ko da kowa baya so, tunda tana sonka ni ma kai nake so na aurawa ƴata"

Safwan ya yi shiru yana nazarin mafita saboda ya rasa ta wace hanya zai nunawa Baban Zee shi ba zai aureta ba, amman cikin zuwan wata dubara ya buɗa baki zai yi magana Baban Zee ya dafa kafaɗarshi ya ce

"Kada ka ji komi ni zan baka ita da hannuna fatana kawai ALLAH ya sa ka riƙe mani ita Amana kuma ka dubi son da take yi maka ka riƙeta tsakani da ALLAH"

Safwan ya dafe goshinshi cikin rikicewa yace "na gode Alhaji"

Alhajin ya sake dafa kafaɗarshi cikin murna ya ce"ALLAH ya albarkaci aurenku"

Sannan ya koma cikin ɗakin cike da jin daɗin samarwa ƴarshi abunda take so, Safwan ya riƙe ƙarfen baranda ya yi shiru tare da juya zancen cikin ranshi, ya nutsa sosai cikin zurfin tunani sai jin magana ya yi ana ce wa da shi

"Ko wane Mutum tafe yake da kundin ƙaddararshi na yarda da tawa ƙaddarar na amince na rasa Zainab ALLAH Ubangiji ya baku zaman lafiya"

Zancen Aminu kenan da ke tsaye soke da hannunshi duka biyu a aljihu, yana ƙare faɗar hakan ya juya zai tafi Safwan ya yi saurin dafo kafaɗarshi ta baya Aminu ya tsaya cak! Kamar an masa dole, Safwan ya yi ƙarfin halin faɗin

"Kada ka yi fushi akan abunda kake so ka yi haƙuri ku daidaita da Zee ku yi aurenku kawai, Ni na haƙura na bar maka ita ka je ku yi aurenku plss"

Aminu ya juyo ya sauke hannun Safwan da ke kafaɗarshi ya sake mayar da hannunshi aljihu yace

"Kada ka ji komi ka ji da kanka ni na barwa ALLAH kuma ina da tabbacin zai yi man mafita"

Yana ƙare faɗar maganar ya bar wajen tare da jan Motarshi ya fice asibitin gaba ɗaya, Safwan cikin tashin hankali ya ciro wayarshi ya kira Lawi domin ya ji a ina zai sameshi, Lawi ya yi masa kwatance sannan ya fice Asibitin ko sallama bai yi da su ba ya nufi wurin Lawin.

Cikin guntun bayani mai gamsarwa Safwan ya yi masa bayanin duk halin da ake ciki, Lawi ya yi shiru yana nazari sannan ya ce

"To ka aureta kawai tunda ƙaddarar aurenta ne ya haɗaku tun farko"

Safwan ya goge jiɓin da ya jiƙa masa fuska yace, "Ni ban san da wane idon zan kalli Khadija in ce da ita zan yi aure ba, WALLAHi ni yanzu auren Zee ya fita kaina, na fi son in mayar da hankalina kan matata in gyara abunda na ɓata a baya, in nuna mata irin gatan da kowace mace take nema a wurin Mijinta, ka sanar da ni Abokina ta ya zan saukewa kaina auren Zee??"

Lawi ya ce "ba wata mafita gaskiya saboda kai kasan irin son da take yi maka, kuma nasan kai ma kana sonta to tunda har anyi hakan mafita ɗaya ce ka sami Aminun har gida ka sanar da shi da gaske kake yi ka bar masa Zee, idan ya amince shikenan idan kuma ya ƙi sai ka aureta kawai tunda ALLAH bai haramta maka ita ba"

Safwan ya yi shiru yana nazari sannan ya nemi Lawin ya rakashi su je gidansu Aminun ba musu suka nufi gidan, sai dai iya daɗin bakinsu da nuna masa su ma sun san fiqhu da Tauhidi bai sa Aminu ya karɓi buƙatarsa ba, don ya yi biris akan buƙatarsu sosai ya rufe ido ya nuna baya ra'ayin aurenta, sannan ya nuna masu cewa shi fa ya haƙura ya yi imani akan duk abunda ALLAH ya tsara masa, kuma insha ALLAHu shi ma kwanan nan zai fito da mata ya yi aurenshi, dole ba don sun so ba suka haƙura suka bar gidan cikin sanyin jiki.

Tare suka koma Asibitin da Lawi sun ɗan jima a cen sannan suka yi masu sallama suka dawo gidan Lawin, gidanshi da yake ta gyara saboda lokacin aurenshi da yake ta matsowa.

Da safe ma ko da suka koma sun taradda ita da sauƙi sosai don kuwa sai samuwa yake yi a hankali, ganin hakan yasa ƴan'uwan Zee suka ta yi masa godiya tare da yi masu fatar alkhairi a auren nasu, cike da jin nauyi yake amsa masu ba yabo ba fallasa.

Kasancewar Zee ta ji albishiri ɗin aurenta da Safwan a bakin mahaifinta yasa ta saki jiki sai wasar baki take yi, zuciyarta cike da jin daɗin mallakar mutumen da tafi so fiye da kowa ne ɗa Namiji a duniya.

Bayan kowa ya fice ne aka barta da Safwan ɗin don ko Lawi fitowarshi ya yi ya barosu, cike da jin daɗin ganinshi cikin muryar ciyo ta ce

"My hero ya zaka yi da mata biyu da kake ƙoƙarin haɗawa a zuciyarka?"

Safwan ya yi dariyar yaƙe ya ce

"ALLAH zan roƙa ya bani ikon yin adalci tsakaninku"

Cikin jin kishin matar tashi ta ce, "to yanzu idan mun yi auren da ita zamu koma school ko kuwa?"

Ya yi shiru sannan ya ce, "sai abunda Hajiyata ta ce sannan duk hukuncin da ta yanke muna to ni banda ja akanshi"

Cikin sauri aranta ta ce _"ALLAH yasa ma ta ce a barta anan ɗin mu mu tafiyarmu abunmu"_

Amman a fili tace

"ALLAH ya sa mu dace all, amman plss ka nuna mani wacece Uwargidana ko da a hoto ne, don ina son na nasan wacece ta yi saurin sace zuciyar Realitynah?"

Safwan ya yi ƴar dariya saboda tuno Dijen Baffah sannan ya ce "saurin me kike yi zaki santa soon Insha ALLAH "

Haka Zee ta yi ta shige masa suna ta firarsu cikin natsuwa har Safwan ɗin ya yi sallama da ita akan zai koma Yola ya turo Iyayenshi ayi zancen auren nasu.

Cike da tsantsar farin ciki ta yi ta jera masa kalaman soyayya tare da yi masa fatan ALLAH ya tsare hanya, da ma zai ta fi har son ta yi ta sauko ta rakashi sai da ya hanata sannan ta haƙura, tana yi masa bye bye yana yi mata suka rabu.

Mahaifinta ya karɓi account ɗin Safwan a take yanke ya yi masa transfer ta 2million ya ce da shi ya je ya fara shirye shiryen aurenshi da Zee, saboda komi cikin gaggawa yake son ayi saboda buƙatar su koma makaranta cikin lokaci.

Safwan ya tafi zuciyarshi ba yabo ba fallasa don har cikin ranshi bai yi wata murna akan auren ba bale kuɗin da Daddyn Zee ya ba shi, don a ganinshi tamkar ma ya renashi ne, saboda tambayar kanshi da ya yi akan cewa, shin ya ɗauki kuɗin ya bashi ne don ya siyeshi da kuɗin ya auri ƴarshi? ko ku wa don ya nuna masa cewa su ma masu kuɗi ne fiye da su?.





Oho Safwan🙄 ni dai in baka so ko 5ok ka yi man transfer a nawa bank account na yi maka alƙawari zan tayaka addu'ar neman zaɓin ALLAH😝





Akafta🤣









D/AUTA Ce

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*




*Because of you ƙanwata Leemart pinkey MHiss purple ALLAHU ya bar zumunci ta hannun damata🖐🏻*


*Lamba ta 57*



Jiki ba kuzari yake driving har ya isa Yola cikin amincin ALLAH, sai dai yawan faɗuwar da gabanshi yake yi yasa ya ji baya sha'awar zuwa gida, sai da ya biya wajen Mubarak suka tattauna sosai akan matsalar sannan ya nufo gidan.

Jiki a sanyaye ya yi parking ya daɗe zaune cikin motar yana nazarin ta ina zai fara?, wurin Hajiya Mama ko wurin Khadijarshi?, a ƙarshe dai ya yanke shawarar fara tunkarar Hajiyar saboda ta fi khadija matsala a wurinshi, don ita da ya kanainayeta da daɗin baki zata bi ba tare da yasha wahala ba, cikin ƙarfin gwiwar da zuciyarshi take ba shi ne ya fito ya nufi cikin gidan, sai ko ya taki sa'a ya taradda Hajiyar da Fiddo a babban falo suna kallo, ya shigo da sallamarshi ya ƙaraso ya zauna tare da faɗin

"Wash! ALLAH Hajiyarmu gani na dawo lafiya"

Idonta akan tv tace "masha Allah sannu da dawowa"

Fiddo ta gayar da shi cikin ladabi sannan ta ce, ,"big bros ya jikin Aunty Zee ɗin? da fatar taji sauƙi sosai?"

Ya shafo sumar kanshi da take cike da gashi kwance baƙi ƙirin a saman kan nashi, sannan ya ce

"Ta sami lafiya khadija fa?"

Fiddo ta yi saurin kallon Hajiya Mama sannan ta ce "Tana ɗaki maybe bacci take yi"

Cikin jin nauyin idon Hajiyar ya ce "je ki ce ta kawo man abinci"

Fiddo ta daburce ta miƙe tana sosa kai tace "tun ɗazu fa kamar bata gidan nan don ban ga ko wulgawarta ba"

Cikin faɗuwar gaba ya zaro ido waje "me kike nufin sanar da ni? Ba ta nan to ina ta je ne ba tare da izinina ba??, Hajiyarmu ko ke kika aiketa ne don nasan Khadija ko ƙawa bata da a cikin garin nan bale ace ta je cen, ko dai tana gidan Surayya ne?"

Hajiya Mama cikin ko in kula ta ce, "mi ye damuwarka da ita ne? Ni fa bana son takura, saboda haka ka bar yarinya ta sha iska"

Safwan ya marairece fuska yace , "matata ce fa Hajiya ko ba komi akwai haƙƙin aurena a kanta"

Hajiya ta maka masa harara ta ce "don kana aurenta ai har yanzu bata zama kamar sauran matan aure ba, don cikin haƙƙoƙanta da Allah ya rataya a wuyanka nawa ka sauke faɗa man cinka? ko shanka? Ko kuma suturarka?, To bana son zaƙewa da yawa don ni nake da ikonta tunda kai da kanka ka saka muna ita cikin ƴan aikinmu, to yanzu kuma ka ke son zuwa ka kawo mani wani zancen banza cen"

Safwan ya yi saurin faɗin "to na tuba a gafarceni Hajiya yanzu ina ta je in je in ɗaukota",

Cikin basarwa Hajiyar ta ce "to Khadija dai bata gidan nan na turata aikatau wani gari, saboda naga mu nan ƴan aikin ma sun yi muna yawa, shine na ga da a barta haka kawai zaune ba wani moruwarta da muke yi, shine na ga gara kawai na turata cen ɗin, insha ALLAHu duk kuɗinta na wata wata idan an aiko mani zan je da kaina har ƙauyensu in kai wa iyayenta"

Firgici tashin hankali tare da ruɗewa duka suka ziyarto wa Safwan ba tare da ya shiryawa zuwansu ba, cike da wani tsantsar tsagwaron tashin hankalin da ya bayyana a kan fuskarshi ya ce

"WALLAHI ina sonta Hajiya don ALLAH ki dawo man da matata hannuna, na yi maki alk'awali zan riƙeta in mata gata fiye da kowace mace mai gata a gidan Mijinta"

Ya ƙare maganar cikin muryar kuka tare da zuwa gaban Hajiyar ya durƙusa gwiwa bibbiyu ya haɗa hannu biyu waje ɗaya alamun roƙo ya sake cewa

"Na tuba Hajiyarmu ki yafe mani WALLAHIL'AZIM yanzu da gaske ina sonta, kuma a shirye nike da in zauna da ita a inuwa ɗaya a matsayin matar aurena"

Fiddo ta bi shi cike da kallon mamaki baki a sake tace, "Dijen kake so big Bros??"

Wani hargitsatstsen kallon da ya bi ta da shi da jajayen idanuwanshi yasa ta yi saurin rufe bakinta da hannu ta bar falon, Hajiya Mama ta ƙi kallonshi sai kallon tv'n take yi kamar kallon take yi da gaske, don bata son Kallonshi saboda gudun tausayinshi ya karya mata zuciya, Safwan ya riƙo ƙafarta tare da duƙewa ƙasa cikin wata murya mai cike da ban tausayi ya ce

"Ki gafarceni Hajiyarmu nasan na yi kuskure a baya plss ki dawo man da khadija don ALLAH Hajiyarmu"

Hajiya ta miƙe tsaye ta yi taku ɗaya biyu kamar zata bar falon sannan ta tsaya ta waigo ta ce

"Yanzu ba wurin budurwarka ka fito ba? Kuma ba aurenta ka ke so ka yi ba? To ka je na baka dama tuni ka yi aurenka ai, amman ka sani yanzu na fasa amincewa da tariyar khadija gidanka, zan barta cen wajen aikatau ɗin sai ka rubuta mata takardar sakinta idan ta sami mijinta a cen sai ta yi aurenta"

Tana ƙare faɗar maganar ta wuce abinta ta nufi ɗakinta, cikin sauri ya biyota cike da wani sabon tashin hankali yana faɗin

"Don girman ALLAH Hajiyarmu ki yi haƙuri ki yafe mani laifukana"

Sai dai yana kawowa bakin ƙofar ɗakin ta rufo ƙofar ɗakin da ƙarfi har saura ƙiris ta haɗa da kanshi, Safwan ya dawo baya cikin hanzari sannan ya durƙushe bakin ƙofar yana faɗin

"Zan mutu Hajiya idan har ba'a kawo man matata ba"

Daga cen cikin ɗakin Hajiyar ta ce "ka yi sauri ka mutun don ALLAH, kana da rai ma wani aure zata yi bale ka tafi ka bar duniyar?"

Safwan ya dafe saitin zuciyarshi yace

"Wayyo Hajiyarmu kada ki yi man irin wannan horon wallahil'azim ina sonta ke ma zaki sheda hakan"

Haka ya yi ta surutanshi har ya gaji Hajiyar bata sake tankashi ba, dole ya gaji ya miƙe ya nufi ɗaikinshi ya faɗa gado cikin ƙunar zuciya tare da yin nadama akan abunda ya aikatawa Dijen Baffah a farko, yanzu ga shi Hajiyar tana son horashi da laifin da har ya mance da ya aikata, saboda yanzu giyar sonta da ke walagigi da rayuwarshi yasa ya manta baya, haka ya yi ta kukan zucinshi cikin ɗaki cike baƙin cikin da ya mamaye masa zuciya, saboda Zee sai damunshi da kira take yi wani bayan wani ko gajiya bata yi amman yaƙi ɗaukar ko ɗaya, saboda damuwar da yake ciki a ganinshi ta shi ta shalle tunanin ta ta damuwar.

Haka ya yi ta yiwa Hajiya magiya akan ta dawo masa da Khadijarshi, da ya ga ma ta ƙi saurararsa ne ya kira Fiddo cikin sirri yana tambayarta inda aka kai khadijar, amman itama cike da jin haushinshi ta ce ita bata ma san Dijen bata gidan ba, dole ya koma tambayar ma'aikatan gidan sai dai su ma duka bakinsu ɗaya ne babu wanda yasan inda aka kaita, sai ga Safwan da biyar gidajen ƴan'uwa lungu da saƙo yana binciken ina aka kawo sabuwar ƴar'aiki, amman dai iya bincikenshi babu Dije babu mafarinta, dole ya dawo gida a jigace yana yi wa Hajiya kuka da hawayen da suke ta sauka a kan fuskarshi ba tare da sautin kukan ya fito ba, amman a hakan Hajiyar ta bushe fitilarta ta ce ba zata dawo da ita ba kuma sai ya bata takardar sakin Dijen dolenshi.

Damuwa goma da ashirin suka yi masa yawa a kai saboda izuwa lokacin Mahaifin Zee ma ya shiga cikin jerin sahun masu kiran nashi akan ya turo Iyayenshi, saboda danginsu sun yo masa caa! Akan rashin kyautawar da zai yi wa Aminu, shi
kuma ya kafe akan cewa duk abunda ƴarshi take so shi ma cen yake so, don har meeting aka yi akan matsalar ƙarshe kuma aka watse baram baram, saboda wasu da yawa sun ga laifinshi ya yin da wasu kuma suka goyi bayan Daddyn Zee ɗin saboda illolin auren dolen da ake hangowa, a ƙarshe dai Aminu da kanshi yake baiwa masu goyon bayanshi haƙuri akan lamarin, tare da sare masu gwiwa wajen sanar da su cewa shi fa ya janye, dole kowa ya haƙura aka zubawa Daddyn Zee ido aga iya gudun ruwansu shi da ƴarshi.

Kan haka ne ya yi ta samun Safwan ɗin da kira sai dai zance ɗaya ne yake yi masa na cewa wanda zai zo nema masa auren ya yi tafiya, da ma ya fahimci kamar zillewa yake son yi yasa su ji kunya ga ƴan'uwansu ya ce ya ce da shi

"Ya bashi number'r wakilin nashi shi zai kirashi ya yi masa bayanin abunda ke faruwa"

Dole Safwan ya saka masu ranar da zasu zo shi da Iyayenshi akai ƙarshe akan lamarin, sannan hankalin Daddyn Zee ya kwanta tare da kwantar na ƴarshi da ta ƙi ci ta ƙi sha akan damuwar rashin ɗaukar wayarta da Safwan ɗin baya yi.

Safwan ya je wa da Hajiya Mama da maganar tare da fayyace mata komi akan halin da ake ciki, sai dai duk da ta ji zafin abun aranta amman hakan bai sa ta hanashi auren ba, asali ma ta amince masa kamar farko yanda yasa mutane suka tursasata kan zancen auren, saboda tausayin yanda ya firgice cikin lokaci ɗaya saboda rashin Dijen, ya bi ya rame saboda damuwar da ya sakawa zuciyarshi akan rashin Matarshi, sannan ta san muddin ta hanashi auren bayan ta ɗauke masa Dijen ta cutar da rayuwar ɗanta, sai dai bata amince da auren ba ne sai da ta yi nazarinshi sosai akan damuwar rashin Dijen bazai barshi ya ji daɗin auren da zai yi ba, kuma ta hakan ne zata ƙara samun wata damar da babu wata ƴa mace da zata samu a wurinshi.

Safwan kam cike da tausayin kanshi da ita kan Zee ɗin ya tura Iyayenshi suka neme masa aurenta inda aka saka rana da lokaci sati biyu kacal masu zuwa, saboda su koma school su ci gaba da harƙallar karatunsu.

****

Biki sai ƙaratowa yake yi duk da ango kam ba wani jin daɗin auren ko zumuɗi irin na ango da yake yi, don a kullum dare ya kwanta baya baccin kirki saboda mafalkin Dijen da yake yi cikin yanayi kala kala, ta ɓangaren Zee Kam sai shirye shiryensu suke yi cike da alfahari, saboda su cusawa waɗanda basu son auren haushi, inda su kuma suka koma gefe suna kallon ta yanda za'a yi auren cin amana ya yi daɗi.


*****

Dijen Baffah kam duk da ta ji daɗin garin amman zuciyarta cike take da kewar Mijinta, bata da wani aiki sai na tunaninshi da kalamanshi waɗanda ada take hangosu a matsayin na yaudara, sai ga su a lokacin tana jinsu har cikin ruhinta, saboda ba ƙaramin daɗi suke yi mata a kunnuwa da gangar jikinta ba, waɗanda wani zubin bata san lokacin da wasu hawwyen kuka yake zuwar mata ba, don ita a son samunta a barta ta koma wurin Mijinta ta yi masa biyayyar da Inna take ta yi mata jan kunne akan ta yi masa, yanzu ta amince wa zuciyarta cewa itama fa tana son MALAM Safwan, ga shi ko waya babu a hannunta ba le ta kirashi ta ji daɗi, kuma kunyar idon Auntyn da kashedin Hajiyar yake sa ta ƙi tambayar a wane hali yake.

Ganin halin da take ciki ne yasa Aunty Ummi ta fara shiga damuwa duk da tana iya ƙoƙarinta wajen sakata nishaɗi saboda gurinta na son cire mata damuwa, shiyasa ko auren da ta ji ƙin nuna mata wani abu da zata gano ta yi, saboda jan kunnen da Hajiyar ta yi mata akan kada ta bari ta san da zancen, da ma lokacin auren ya matso ne ta yi mata ƙaryar wani biki ne daban zata je, da ma Dijen ta nuna tana son zuwan itama sai ta ce da ita ta yi haƙuri ba zata daɗe ba, don ma ta kwantar mata da hankali ta bar yaranta mata manya ta tafi da ƙananun saboda Maigidanta daman cen ba mazauni bane ba.

****

Biki bidiri bireɗe amfanin soyayya aure Zee ta angwance da masoyinta Safwan, zuciyarta cike da tsantsar farin ciki saɓaninshi da yake cikin ƙunci don duk wasu events ma ba da shi aka yi ba, an ɗauki Amarya daga Gombe zuwa Yola mahaifar Mijinta, inda aka wuce da ita gidan Hajiya Mama kai tsaye saboda ta kwashi tubarrakin uwar mijinta ta sawa aurensu albarka kafin akaita gidan angonta.



Sorry team Dije 🙇🏻‍♀️ku sani babu ruwana nidai 🙌🏻🏃🏻‍♀️









Akafta🙌🏻






D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Mutanen Dije ina baku haƙuri🙏🏻dangane da auren Zee da Safwan ya yi, amman ina son ku sani ana yin book ne don faɗakarwa tare da wa'azantarwa sannan da kwatanta abunda ke faruwa a cikin al'ummarmu, saboda haka ku natsu tsaf ku bini sannu a hankali zan warware maku komi cikin tsarinshi😉*


*Lamba ta 58*



Har ƙuryar ɗakin Hajiya Mama aka kai Zee da ke ta rufe fuska tana ta wasar baki saboda daɗin da ya kasa ɓoyuwa a kan fuskarta, gaban kowa da mutanen da suka yi mata rakiya Hajiya Mama ta ce da Zee

"ALLAH ya baku haƙurin zama,
kuma albarkaci aurenku tare da zuri'a ɗayyaba gaba ɗaya, sannan da fatar zaman lafiya ke da abokiyar zamanki"

Dirim! dum! Shine bugun da zuciyar da Zee ta yi amman ta wayance tare da noƙe fuskarta tace "Ameen" Hajiya Mama ta ƙara da cewa

"Ki yi haƙuri nasan zaki ga abokiyar zamanki bata sami halarta bikin ba, to hakan ya faru ne a sanadin hidimar karatun da ya sha kanta, amman ina fatar a duk lokacin da zama ya haɗaku ki yi ƙoƙari ki baiwa Mijinki haɗin kai wajen yi maku adalci a tsakaninku, ALLAH ya baku zaman lafiya a tsakaninku duka ya kawar da sheɗan cikin gidanku gaba ɗaya"

Kowa sai "Ameen Ameen" yake faɗa sannan ta kawo dunƙulalliyar kyauta ta bata, aka fito da Zee mutane da yawa sai yaba kirkin Hajiyar yake yi, inda kai tsaye aka wuce da Zee katafaren gidan Safwan wanda ya laƙume maƙudan kuɗi wajen haɗashi ta ko'ina, inda itama kanta Zee iyayenta suka zuba ta su bajintar wajen ƙawatashi da kayan ƙarau lungu da saƙo, abun dai masha ALLAH sai wanda ya gani don tsayawa misalta haɗuwarshi ma ɓata baki ne, saboda haka masu karatu na baku wannan aikin wajen misalta gidan da kanku.

Har ɗakinta aka kaita iyaye da ƴan uwa da ƙawayenta sai addu'ar zaman lafiya su ke yi mata,

Please Login or Register in order to submit comment