Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bada akawo mashi tare da turaruka masu kyau.

Shiyasa mai motar bai bar garin ba har sai da aka ciyar da shi da abinci yaci ya ƙoshi sannan ya kama hanyar komawa gida, Baffah da sauran waɗanda suka tafi kowa ya nufi gida zuciyarshi cike da farin cikin wannan tafiyar arziƙi da suka yi.

Inna Hasiya zaune ta yi ta tasa saƙon da Hajiya Mama ta bada akawo mata a gaba tana kallo, zuciyarta cike fal! da farin cikin ganin Dijenta ta yi sa'ar aure har ma da dace da suruka tagari da tayi, ba tare da ta tantance ba sai jin ta yi hawayen farin ciki suna sauka a kan fuskarta, cikin farin ciki Baffah ya ce

"Ba kuka zaki yi ba godiya ya kamata ki yi don kam tabbas Dije ta yi sa'ar aure, don ina tabbatar maki da cewa kaf faɗin garin nan namu ba wanda ya isa ya nunawa Dijeta Miji ke har ma da mutanen birnin duka, saboda ALLAH cikin hikimar ya jefo muna yaran nan don kawai su haska rayuwar Dijenmu, na yarda da maganar Inna Gambo da tace shi bawa bai san ta inda alkhairinshi yake ba, fatanmu kawai yanzu ALLAH Ubangiji ya basu zaman lafiya kuma ya ƙara masu haƙurin zama da Dijen"

Inna ta saka gefen zane ta share hawayenta cikin sanyin jiki tace,. ,"Ameen Malam amman ina jin tsoron Dije ta je ta yi abunda zai janyo girmanmu ya zube a idanunsu ka fa san halinta sarai, ko mu ya muka ƙare da ita balai Mutanen da basu san halinta ba?"

Baffah ya maka mata wata ƙatuwar harara ya ce,. "Idan kin san bakinki ba zai faɗi alkhairi akanta ba to ki yi haƙuri bana son maganar don ALLAH"

Inna ta miƙe tsaye tana ƙoƙarin kwashe kayan tace

"ALLAH ya baka haƙuri ita kuma ya sa ta canza ta zama dai dai da yanda ake son kowace macen kirki ta kasance gidan Mijinta"

Ya yi saurin sakin fuskarshi yace, "Ameen ko ke fa? Haka ya dace ki ce tun farko, ba ki wai ki zauna kina ta janyo maganganun da idan aka aunasu dai dai suke da muguwar fata ba"

Inna za ta yi magana kenan sai ga Usmanu ya shigo bakinshi har kunne ya ƙaraso wurinsu yana faɗin , "Sannu da zuwa Baffah ya hanya?"

Baffah ya washe baki yace, "Alhamdulillahi Usmanu ALLAH ya nufa mun dawo lafiya tare da abun alkhairin da aka cikomu da su"

Inna ta ajiye ledar da ke hannunta tana murmushin jin daɗi, Usman sai duba kayan yake yi yana faɗin

"Kai! Kai! Kai! Lalle Baffah Dijenka ta zama hamshaƙiya waɗannan kaya haka?"

Baffah ya janyo wata ledar ya fiddo shadda da turare yace,. "Kai ma ga naka sai ka ji daɗin yi wa ƴar uwarka addu'ar zaman lafiya gidan aurenta"

Usmanu cike da jin daɗi ya karɓa tare da rufe Bakinshi ya ce, "cabɗi ashe muma za mu shana? to ALLAH ya ba su zaman lafiya Baffah, kuma ya sa ta rage rashin jin nata don kar ta je ta janyo muna abun magana"

Baffah ya tsuke fuska yace,. "Alkhairi zaku gani daga kai har Uwarka, tunda ta bar maku filin gidan ai sai ku wataya yanzu"

Yana ƙare faɗar maganar ya miƙe ya nufi waje saboda sallamar da ya jiyo ana yi masa a ƙofar gida.

Inna da Usmanu suka bishi da kallo cikin sanyin jiki Inna tace, "Ni na rasa gano inda Malam ya nufa da mu da kullum yake ganin kamar mu bama son Dijen"

Usmanu ya yi saurin faɗin , "ya san sarai duk muna sonta Inna kawai dai don tana ƴar gaban goshinshi ne yake ƙin son a faɗi aibinta, bayan kuma mu gaskiya ce muke kai kuma ita muke faɗa, saboda gudun a barta ba kwaɓa ba hantara ta ƙara sangarcewa aje a shiga uku, yanzu dai tunda komi ya wuce fatan da za mu yi mata shine ALLAH yasa wannan auren ya zamo silar shiryuwarta, don kin ga mu fa in mun juri halinta WALLAHI su cen ba jura za su yi ba"

Inna ta sauke ajiyar zuciya tace, "ALLAH dai ya sa ta gyara mu ma ai farin cikinmu ne Usmanu"

Muryar Baffah da suka ji yo a bayansu yana faɗin "Ameen" shi yasa duk suka miƙe kowa ya nufi sabgoginshi, Baffah ya yi guntun murmushi yace

"Kuna nan zaune kuna gulmar Dije zaku ganinta ta zamo Babbar Hajiya ba tare da kun tantance ba"

Usman ya ƙumshe dariyarshi ya shige ɗakinshi zuciyarshi wasai saboda ganin bakinsu zai huta da bari barin Dije.

Kafin ka ce me gari ya ɗauka Dije ta auri ɗan gidan masu kuɗi a birni mutane sai shigowa yiwa Inna da Baffah sam barka ake yi,su Jummala da Lanti sun ji ina ma ace su ne suka sami wannan damar, don ko Balan Duduwa ma da ya ji labarin abun alkhairin da aka yi wasu Baffah kai tsaye ya nufi ɗakin Duduwa Bakinshi a washe yana faɗin

"Kin gani ko Duduwa ke da ke yi man faɗa kan abunda na yi yanzu ga shi ko Mahaifinta ya ji daɗin abun har wasu ma sun sheda"

Inna Duduwa ta maka masa wata ƙatuwar harara ta ce

"Kai tafi cen sakaran banza ashe daman cen son da kace kana yiwa Dijen na ƙarya ne tunda har ka karɓi kuɗi a matsayin fansar son da kake yi mata"

Balan ya turo baki irin na sangarta yace,. Haba Duduwa yanzu don ALLAH duk wannan tsiren da nake siyo maki kullum baki gode ba?, Yanzu ga shi naci riba biyu ga Matata kuma ga kuɗina ina mora, Ni dai WALLAHI kam banyi nadama ba don ni da ma zai sake ganin Ladiyo ya ce in bar masa ita ya biyani wasu kuɗin tsaf zan bar masa ita, ai da arziƙi gidan wasu gara gidanmu WALLAHI cab! Ai ni....."

Sai jin ya yi muryar Ladiyo a bayanshi da ke ƙoƙarin shigowa tana faɗin, "ai ni ma WALLAHI da ashe zai ganni ya ce yana so da sai nafi kowa murna, ko da zan huta da tusoshin da kake buga mani duk daren ALLAH kafin safiya ta waye ka yi ashirin"

Bala ya zabura ya ce,

"Don Ubanki ba tare da ke muke cin ƙuli ƙulin tsiren ba? Ko ba ke ma kina tusar ba? Shikenan ni na haƙura banyi ƙorafi ba ke zaki zo kina tona man asiri gaban Duduwa, to ba zaki sake cin tsiren da ƙulin ba baƙar munafuka"

Ladiyo ta riƙe ƙugu tana maka masa harara sama da ƙasa tana murguɗar masa baki, Duduwa ta yi sakato tana kallonsu cike da takaici tace,. "Kun dai ji haushi ku kam! Amman ko da yake kai ne babban mai laifin ba ita ba, ALLAH ya shiryeka da baƙin halin da ka tsirowa kanka daga jin ɗimin kuɗi a hannunka ka rikice saboda zalama, to tsiren ma idan ka sake kawo man sai na ci mutuncinka sakaran banza"

Tana ƙare faɗar maganar ta ɗauki zanenta ta yafa ta bar masu gidan tana tafe tana faɗa har gidan Inna Gambo, kasancewar ƙawarta ce ta ƙud da ƙud tun ƙurciya har yanzu da suka manyanta.

Sai dai faɗanta ya tsaya ne saboda ganin Gambo rungume da atamfofi biyu tana murna bakinta yaƙi rufuwa sai zubawa Dije ruwan addu'a take yi, Duduwa ta janyo kujera ƴar zuƙunno ta zauna tana faɗin

"Gambo wannan farin cikin daga ina haka?"

Gambo ta ɗaga Atamfofin sama tana kallonsu ido cikin ido tace,. "Daga hannun Jikata Dijen Sanda saƙo ne tun daga gidan mijinta ta çe akawo mani in saka in ji daɗin yi mata addu'ar nasarar zaman lafiya da Mijinta"

Gambo ta yi shiru sannan ta ce "Ah lalle dole ki yi farin ciki sosai to ALLAH ya haɗa hankulansu kafin nan da shekaru mu ga ƴan dugadugai suna yawo a tsakiyar gidan nan naki"

Gambo ta yi saurin faɗin, "Allahumma Ameen Duduwa karɓi goro ki tamna don mu ji daɗin yin firar"

Duwawa ta karɓi goron ta kai bakinta ta ramtsa tace, "Lalle wani hani ga ALLAH baiwa ne ya hanata Bala ya baiwa ɗanbirni, to ALLAH ya basu zaman lafiya daga ita har Balan tare da Matarshi Ladiyo"

Inna Gambo tace "Ameen ya rabbil'alamina Aminiyata"



Dije kam............😛


Ku yi manage insha ALLAHu maybe anjima ku jini matuƙar na samu yanda nike so😁





Akafta🤗






D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*BAƘON YANAYI ne sunan Book ɗin don haka idan kin san baki karantashi ba to ki garzayo da gudunki don kar ayi babu ke, da 300 kacal zaki sameshi a complete ɗinshi ki yi yanda kike so, don ke da kanki zaki banbance tsakanin tea da shayi kada ki bari a yi babu ke salonshi daban ya ke da saura don tun daga sunan zaku gane cewa fa shi ɗin na daban ne, ga mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09032685442 sai na ji ku👍🏻😅*



*Lamba ta 32*



Dije kam kwana biyu da zuwanta Yola Hajiya Mama ta sa Safwan ya fara yi mata lesson, saboda a cewarta don ta sami ƙarfin gwiwar tunkarar makarantar da za'a sakata da kyau, aiko sai ga shi duk da kyarar da yake yi mata hakan bai hanata fahimtar karatun da yake koya mata ba, don wannan karon ma ta ci Sa'a da Hausa ya ke fahimtar da ita duk wani abund bata gane ba, don wani zubin ma Hajiya Mama a gabanta ake karatun saboda cin zalin Dije da yake yi, duk da aranta wani lokaci sai ta ƙudurta ramawa sau kuma ta tuno huɗubar da Baffah'nta ya yi mata sai ta fasa, sai dai ta yi ta binshi da harara tana cizon yatsa saboda kullum cikin dare sai ta yi kukan rashin ganinsu.

Sai dai ta samu Surry da Hajiya Mama suna ina ka aza da ita komi take buƙata ko da bata faɗa ba yi mata ake yi, abinci ma kala kala ake baje mata ta ci wanda take so, Fiddo kam yanzu tsakaninta da Dije sai harara da murguɗar baki saboda faɗan da Hajiya Mama ta yi mata sosai akan Dijen, tare da gargaɗi mai tsanani akan duk ta sake yi wa Dije gori ko ta ci zarafinta sai ta saɓa mata.

A yau ma sati ɗaya da zuwan Dije gidan Garin suna babban falon gidan ne suna karatun kamar kullum, Safwan yana koya mata karatun tana gyangyaɗin Bacci don daman cen Dije ba gwanar firar dare ba ce, jin haushin baccin da take so ta yi bayan Hajiyar ta hana shi fita zuwa inda ya so ya je yasa ya fakaici idon Hajiya Mamar, ya janyo mata dogon tsoronta da ya fito cikin hular da ke saman kanta, cikin ƙeta ya janyo tsoron da ƙarfi ba shiri Dije ta ƙwallah ƙara tare da dunƙulewa tana kuka mai cike da takaicin hanata baccin da yake yi da muguntarshi kala kala.

Hajiya Mama ta yi saurin faɗin,. "Ka kiyayeni Sawan me ta yi maka yanzu kuma?"

Safwan ya sosa kanshi cikin sauri yace,. "Bacci fa take yi Hajiya Mama don ta renani ga shi ƙiri ƙiri ta sa an hanani fita kuma ta zo tana yi wa mutane baccin renin wayo"

Hajiya Mama ta tashi cikin sauri ta riƙo hannunta tace,. "Tashi mu je ki yi baccinki tunda karatun na mugunta ne ake yi"

Dije ta miƙe tsaye sai ga zobenta da Lawi ya bata ya faɗo ƙasa don ana karatun ta cire shi tana wasa da shi, bayan wucewarsu ne ya miƙe da nufin barin wajen sai ga shi ya hango Zoben, cikin ko in kula ya duƙa ya ɗauki Zoben ya saka aljihunshi ya nufi ɗakinshi, zuciyarshi cike da tunanin ina ta samo zobe mai kyau haka? Wata zuciyar tace da shi maybe Hajiya Mama ce ta bata shi, sai kuma cen ya tuno da zasu zo garin ya hango Zoben a hannunta, to wa ya bata? Haka ya yi ta yiwa kanshi tambayar da babu mai amsa masa, amman ya ci alwashin sai ya tambayeta ya ji ina ta samo zoben don yasan da sanin cewa kaf garinsu babu mai wayewar da zai iya bata kyautar Zoben.

Haka kawai ya ji zuciyarshi ta kasa natsuwa don wata zuciyar tana sanar da shi cewa ƙila Lawi ne ya bata shi, haka ya kwana cike da takaicin da shi kanshi baisan mafarinshi ba.

Shiyasa ko da safiya ma ta waye ƙin fitowa ya yi ayi break da shi kamar yanda aka saba kullum, sau biyu ana turo kiranshi yana faɗin zai zo amman yaƙi fitowa, dole Hajiya Mama bayan sun ƙare ta ce da Dije ta ɗauki nashi ta je ta kai masa,amman idan ta ga zai daketa ta dawo abunta kar ta zure ya yi mata dukan banza.

Aiko cike da Sa'a tana ƙwanƙwasa ɗakin ya ce a shigo, ta tura ƙofar ta shiga tana ƙoƙarin ajiye wa ne ya galla mata harara ta ja baya kaɗan cikin tsoro ta ajiye zata fita ya yi saurin fisgota da ƙarfi sai gata ko ta faɗo jikinshi saboda kasancewarta lange lange ba wani kumarin kirki, cikin masifa ya yi saurin tureta ta faɗi ƙasa sai ga ta da saurin faɗin

"Wayyo hannuna"

Ya wurga mata harara sannan ya fito da zoben yace,. "Uban wa ya baki wannan Zoben???"

Dije ta yi saurin kai kallonta ga zoben ta washe baki ta ce

"Laaa ina ka ganshi?? Tun dazu nike ta nemanshi WALLAHI"

Cike da takaicin rashin amsa masa tambayar da bata yi ba yace,. "Ina kika samo shi ko sata kika fara yi a gidan namu bamu sani ba??"

Dije ta zaro Ido tare da rufe bakinta alamun firgici ta ce,. "Sata????"

Ya ɗaga mata kai ya ce "Eh sata saboda wannan Zoben kaf ƙauyenku babu wanda ya isa ya yi maki kyautarshi"

Dije ta miƙe tsaye cikin fushi ta riƙe ƙugu tace,. "Kam balasi me kake nufi da hakan? Ai billahillazi Ni ba ɓarauniya ba ce ka je ka tambayi Hajiyar taka idan na taɓa ɗaukar maku wani abu ka ji, kuma WALLAHI idan har ta rufeni kace da ita ban yafe ba......."

Karaf ta ji saukar mari akan fuskarta ta yi saurin dafe kumatu cike da mamaki tace,. "Laaa! Laaa! Laaa! Ni ka mara? Me na yi maka da zaka mareni?"

Safwan yana wani muzurai ya taso mata a harzuƙe yace,. "An mareki ke ɗin ɗiyar waye da ba za'a mareki ba WALLAHI idan baki faɗa man inda kika samo zoben nan ba dukan tsiya ne zan yi maki, ƙaramar mara kunya ko an faɗa maki ke wata tsiya ce da har za'a ji shayin sakin ƙwanji a jibgi abun banza?, Kwaɗayayyun banza kawai don masifa irinta baƙin ƙauyen naku ace wai mijin da zai aureki a siyeshi da kuɗi don bala'i kuma ya amince, to ki sani ni ba wai don ina sonki na auroki ba kar ki zargi hakan ki zo wa mutane da renin hankali, zaki faɗa ko ba zaki faɗa ba sai na kakkaryaki a gun yanzun nan?"

Dije ta kawo iya wuya saboda baƙaƙen maganganun da yake ta jifarta da su, cikin fushi ta nunashi da yatsa tace

"Ka daina gangancin sukar garinmu don Ni ma ba sonka nake yi ba tun farko da Malam Lawi ka nemo ya aureni da nafi farin ciki sau dubu da wannan cin zarafin da kake yi mani a cikin gidanku, Zobe kuma mai sona tsakani da ALLAH ya bani wanda nake hango da ace shine tsaye a gabana yanzu ba zai taɓa yi man gori ba, kai ma ɗin ka je kai da ALLAH don ba yafe maka ƙazafin satar da ka yi man na yi ba"

Tana ƙare maganar ta zo zata fita saboda kukan da ya zo mata, Safwan ya riƙo hannunta da sauri ya dawo da ita gabanshi ido cikin ido suke kallon juna ya zare mata idanuwa tare faɗar

"Uban wa ya baki Zoben na ce ko ba zaki faɗa ba??"

Dije ta fisge hannunta cikin fushi da hayagaga tace,. "Masoyi na na gaskiya Abokinka Malam Lawi shine ya bani, idan kuma kana tamtama ka je ka tambayeshi ka ji kuma WALLAHI idan har baka bani abuna ba akan shi zaka janyo in in yi maka abunda kaf garin nan sai an tsine mani"

Tana ƙare maganar ta fice tana wani irin kuka gwanin ban tausayi, saboda ba ƙaramin zafi ta ji ba akan ƙazafin satar da ya yi mata, uwa uba da cin zarafin mutanen ƙauyensu da ya yi.

Safwan kam ba shiri ya dafe kai saboda abunda ya ji ta faɗa akan Zoben da wanda ya bata shi ya sa ya ji duniyar tana juyawa da shi, ya yi shiru na ɗan lokaci sannan ya furzar da iska a bakinshi yace

"Lawi hmmmmm!"

Yana cikin nazarin abun yi ne sai ga Hajiya Mama ta zo tana rufeshi da faɗa kamar zata dakeshi ba tare da ma ta jira taji ba'asin maganar daga Bakinshi ba, ta ce ya bata Zoben dole ba yanda ya iya ya fiddoshi aljihu ya miƙa mata, sai dai kam damuwar da yake ciki ta janyo ƙanzil ya kasa cewa bale har ya yi yunƙurin kare kanshi, har ta yi faɗanta ta gama ta fita bai ce da ita komi ba, cikin tsananin fushi yace

"Dole ma ne in tattara inawa inawa in bar mata gidan don WALLAHI ba zan zauna takaicin Black Cat ya janyo in mussure ba, ina ba zai yiwu ba WALLAHI zan bar maki ita Hajiya tunda kinfi sonta da ni"

A gurguje ya shirya ya fice gidan yanata cuku cukun barin garin zuwa makarantar da yake son yin applying zuwa U.S sai ko ga shi cikin nasara ya harhaɗa komi da ya dace sati biyu a tsakani ya ɗage ya bar ƙasar gaba ɗaya.

Daga Dijen har su Surry sun ji daɗin tafiyar tashi saboda takurasun da yake yi kullum, amman yanzu ko za su sakata su wala yanda suke so, Dijen ma itama Hajiya Mama da kanta ta ɗauketa ta kaita wata bording school ta kuɗi da ke cikin babban garin Yolar, cikin nasara ana yi mata interview aka yi nasarar samun abunda ake so ba laifi aka ajiye ta J.a.s.s 1 da nufin idan ta shiga 2 idan an auna ƙwaƙwalwarta sai ayi mata jumping zuwa 3 ta zana J.l.c, Dije ta sha kukan rabuwa da Hajiya Mama saboda a ɗan zaman da suka yi ta gano cewa ba ƙaramin kirki take da shi ba, kuma tana sonta sosai don komi da ake buƙata na ɗan makaranta sai da ta siya mata har ma da kayan da ba wani muhimmanci ne da su, da waɗanda ita kanta Dijen bata sansu ba bale amfaninsu.

Sannan Hajiya Mama da kanta ta sanarwa da principal d'in Makarantar cewa Dije matar aure ce kada a daketa kamar yanda ake yiwa sauran ɗalibai, duk da Dijen ta ji haushin kiranta da matar auren da ta yi saboda gargaɗin da Safwan ya yi mata kafin ya tafi akan cewa ko da wasa ta faɗawa wani cewa shine Mijinta sai ya fasa mata baki.

*****

Cikin sati ɗaya Dije ta fahimci kan makarantar saboda wata yarinya da wata prefet ta haɗata da ita mai suna Hannatu.

Hannatu ɗiyar masu kuɗin gaske ce ga ta da son mutane sosai kowa faram faram take da shi tun gida babu ruwanta da ƙyama irinta ɗiyan masu kuɗi, haɗuwarta da Dijen yasa ta ji daɗi sosai shiyasa ta dinga fahimtar da ita duk wani abu da bata sani ba, cikin ƙanƙanin lokaci shaƙuwa ta shiga tsakaninsu saboda bala'in kirkin da Hannatun take da shi.





ALLAH ya yi taimako Dijen Baffah, Safwanunmu kuma a dawo lafiya da guzurin baturiya💃🏻😛🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️




Akafta😁







D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*BAƘON YANAYI ne sunan Book ɗin don haka idan kin san baki karantashi ba to ki garzayo da gudunki don kar ayi babu ke, da 300 kacal zaki sameshi a complete ɗinshi ki yi yanda kike so, don ke da kanki zaki banbance tsakanin tea da shayi kada ki bari a yi babu ke salonshi daban ya ke da saura don tun daga sunan zaku gane cewa fa shi ɗin na daban ne, ga mai buƙata ta nemeni ta wannan number 09032685442 sai na ji ku👍🏻😅*



*Lamba ta 33*


Cikin wata ɗaya da zuwan Dije makarantar da yawa mutane sun fara saninta, saboda halin nata da a ko'ina baya b'oyuwa don kuwa watarana tana zaune kan barandar da hostel ɗinsu, taga wata house captain ɗinsu ta saka wata yarinya kneel down tanata dukanta, kuma ga shi ita yarinyar har ta fi Captain ɗin tsawo da girma saboda jin haushin zaunen da ta yi anata dukanta tana ihu yasa Dijen ta nufi wurunsu ta tsaya, cike da fushi ta fisge bulalar hannun Captain ɗin ta zubawa yarinyar bulala ɗaya iya k'arfinta tace

"Kinga yanda na yi maki ko to haka nike so ki karɓi bulalar ke ma ki rama ko in haɗa maki jini da majina yanzu"

Ba Captain ɗin ba harta ita kanta yarinyar da sauran mutanen da ke wajen sai da suka zaro ido, saboda mamakin ƙarfin halin Dije a matsayinta na junio a house ɗin, ganin yarinyar ta ƙi karɓa cike da tashin hankali da tausayin Dijen yasa ta rufe bakinta alamun firgici.

Captain ɗin ta riƙe ƙugu tana ƙarewa Dije kallo sama da ƙasa tace,. "Ashe ko yau zan ci Uban Matar aure a makarantar nan sai naga uban da ya ɗauke maki gindin da zaki tunkarata da wannan baƙin gangancin"

Ta yi wata arniyar dariya ta fisge bulalar a hannun Dijen ta yi ta zabga mata bulolin ta duk inda ta samu, Dije kam jin zafin dukan yana ratsata yasa ta yi wani ihu ta yi tsalle ya haye kan Captain, kafin kace me wurin ya cika maƙil da yan makaranta, tsakanin prefet da senios har ma da juneos ɗin ba'a bari ba, don kuwa Dije ta zage damtse sai artabun doke doke take yi tsakaninta da Hause Captain ɗin, in da da ƙyar aka ɓanɓari Captain ɗin a hannun Dijen, don kowa ƙasa ta murƙusheta tanata kai mata naushi aiko gaba ɗaya prefet suka taru kan Dijen sunata jibga saboda takaicin abunda ta yiwa ƴar uwarsu a gaban junios ɗinsu masu ganin girmansu da kuma jin tsoronsu.

Hannatu a gefe sai uban kuka take ci saboda ganin dukan da ake yiwa Dijen, ganin za su kassarata ne yasa ta bazama aguje sai gidan principal ɗinsu tana sanar da ita, aiko a firgice principal ɗin ta nufo Hostel ɗin don zuwa lokacin makarantar gaba ɗaya ta taru wajen ɗauki ba daɗin dukan da prefet ɗin suke yiwa Dijen, don kowa ya kasa karɓarta a hannasu hasali ma wata ɗaya daga cikinsu da ta so a ƙyaleta itama aka hayayyaƙo mata dole ta yi shiru.

Ko da principal ɗin ta zo tuni sun jigatar da Dijen Baffah don kuwa gaba ɗaya sun ji mata raunuka don ko motsin kirki bata iya yi, cike da tashin hankali principal ɗin ta sa aka ɗauketa aka nufi clinic da ita cikin sauri aka fara treatment ɗinta, sannan ta sa aka haɗa assembly na gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba kowa ya hallara prefets ɗin da suka yi aikin kam gaba ɗaya cikinsu ya ɗuri ruwa, don kuwa sai a lokacin ne wasu da yawa suka ji labarin cewa wai matar aure ce, duk da cewa wasu sam basu yarda da cewa matar auren ba ce duba da yanayin karancin shekarunta, don kwata kwata a lokacin Dijen shekararta goma sha huɗu.

Cikin tsananin ɓacin rai principal ɗin ta yi ta faɗa cikin firgici da jin tsoron abunda zai biyo baya, saboda jan kunnen Da Hajiya Mama ta yi tun farkon kawo Dijen akan kada a daketa ko a sakata wani aikin wahala saboda matar aure ce, sannan ta yi hani ga kowace prefet da ta sake dukan juneos ba tare da ƙwƙƙwaran dalili ba, sannan ta tsawatar sosai akan kada a sake yiwa kowa irin wannan dukan da ake yiwa yaran mutane.

Bayan an sallami sauran ɗaliban ne aka bar prefets ɗin inda aka yi bincike aka fitar da waɗanda suka daki Dijen aka yi masu horo mai tsanani sannan aka karɓe ɗankwalayensu sannan aka basu suspension na kwana uku zuwa gidajensu.

Sannan sauran ta tsoratar da su sosai akan kada su sake dukan ƴar kowa

Please Login or Register in order to submit comment