Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta juyesu duka sannan ta fito da kwalinta ta janyo k'ofar ta rufe ruf da kwadon da ke makale jikin k'ofar, sannan ta tafi da key din ta cillashi cikin ciyayi cikin sauri ta tafiyarta zuwa Makaranta zuciyarta cike da tsantsar farin cikin rama abunda ya yi mata .




Ku taimaka kar ta yi kisan Kai😳🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️






Akafta🤣





D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*BAKINA YA YI KAD'AN YA NUNA DINBIN GODIYATA ZUWA GAREKU BA MASOYA BOOK D'IN DIJE K'ARANGIYA, AMMAN KU SANI INA YINKU SOSAI INA MAKU GASKIYAR SO FISABILILLAH💃🏻*


*Lamba ta 13*


SAFWAN kam cikin Bacci ya fara jin abu yana hawa jikinshi, wani jarumin beran ma cikin k'warewa da mugunta ya cafko masa farcen k'afa da k'arfi sai ga Malam Safwan a zabure tare da kwallah k'ara, idonshi suna kaiwa kan berayen ya fasa wata arniyar k'ara ya nufi k'ofar fita, sai dai mamakinshi rufe take gam gam ba alamun zata iya budewa, SAFWAN kam ya fara tsalle yana ihu Berayen suka firgice suma su ka dinga gudu suna neman maboya, wurin gudun ne wasu Suka yo kanshi aka yi sa'a wani zai hau sama ya kuskure sai gashi ya fado jikinshi, cikin firgici ya fasa wata arniyar k'ara tare da yin tsalle sai ga bera ya shige cikin rigarshi, Safwan ya ci gaba da ihu yanata tsalle har ya samu ya fito rigar da k'yar, amman duk da hakan bai daina zuba ihun ba don kafin kace me k'ofar d'akin nasu ta cika fam da dan Adam, don kuwwar da yake yi iya karfinshi ta janyo hankulan Mutane da yawa ciki kuwa har da Lawi da ke dawowa daga wajen kiran wayar da yayi da mutanen gidansu, kai tsaye aka fara k'ok'arin buge kwadon don a samu k'ofar d'akin ta bud'e, sai dai kafin ma a sami sa'ar budewa tuni Malam Safwan ya some saboda tsabar tashin hankali da firgici da tsoron da ya kamashi, don daman cen shi babu abunda yake tsoro a duniya face b'eraye, akan bera guda d'aya sai ya hargitsa d'aki kaf wajen nemanshi don kuwa muddin akwai bera a d'aki to kam sam shi bashi ba bacci a ranar har sai ya kasheshi sannan ne hankalinshi ke kwanci, to gashi yanzu ya janyo Dije ta yi masa gudunmuwa da manyan zaratan lukutayen kosashin Berayen kauyensu.

Aikuwa ko da aka samu sa'ar bud'e d'akin kwance yake a sheme tsakiyar d'akin tsilla tsillan berayen sai hawa suke yi kanshi suna ta wasa, ganin Berayen yasa Lawi firgicewa saboda yasan yanda Abokinshi yake tsananin tsoronsu, cikin zafin nama ya dauko ruwa ya kandama masa, sai gashi da sauke k'atuwar ajiyar zuciya ya mike a zabure ya fito d'akin yana ihun kiran wayyo a taimakeshi beraye zasu kasheshi.

Mutane kam sai kumshe dariyarsu suke yi ganin wai shi duk akan bera ne yake wannan firgici da tashin hankali har da su suma, Lawi kam sanin wanene abokin nashi da beran ya nufi wajenshi yana ta bashi Baki, sai dai ganin babban farcenshi na k'afa yana zubar jini yasa ya gano ba k'aramar barna Berayen suka yi masa ba, uwa uba fuskarshi da wuyanshi da ya yi jawur ga sawun yagar beran nan ya fito a jikinshi kasancewarshi farin mutum wurin yayi jawur, da kyar ya ciyo kanshi ya daina haukar da yake yi ya samu natsuwa ta ziyartoshi, ya jashi ya kaishi gindin iccen da ke k'ofar gidan Maigarin ya zaunar dashi, maigarin da sauran mutanen kowa sai yi masa sannu suke yi.

Maigarin yasa aka fito da Berayen d'aya bayan d'aya anata kashesu, amman duk da hakan Safwan kafewa yayi akan shi ba zai sake shiga d'akin ba, don ko wunin ranar ma duk a waje yayi komi saboda tsoron shiga d'akin da yake yi, lokacin da dare yayi ma Dole sai d'akin wasu samarin yaran Maigarin aka kai shi ya yi bacci, amman duk da hakan motsi kad'an zai sa ya zabura haka ya kwana zuciya ba natsuwa.

Ko da safiya ta waye tun da sassafe ya nufi Makarantarsu Dije don ko karyawa bai jira ya yi ba saboda gaba d'aya zama gidan ya gundureshi, aka yi dace itama Dijen ta yi sammakon fitowa don kusan ma itace ta biyu ko uku da zuwa Makarantar duka, tana hangoshi saman baranda kanshi duke yanata tunani ta fara kumshe dariyarta, ta yi k'ok'arin saita kanta ta isa wurinshi ta tsaya gabanshi cikin jarumta tace

"Toch me toch fire live me live dengerous your cross the bala'i kaddara your business for nown you tunani in kwakwalwarka"

Tana kare maganar ta gyara zaman Jakar fatar da ke rataye a kafad'arta ta yi masa wani kallo ta wuce fuuu abinta zuwa class dinsu, don tsoron ya sake yi mata irin dukan da yayi mata ranar, Safwan kam binta yayi da wani kallon tafi cen sakarai yana wani mere sai cen Kuma ya tuntsure da wata arniyar dariya, don a iya zamanshi garin ko Murmushi bai tab'a yi ba amman sai gashi yau da kyakyatawa kuma duk a sanadin abokiyar fadan nashi Dije, yarinyar da yake jin tsanarta har cikin zuciyarshi tsana irin wadda bai tab'a yiwa kowa irinta ba.

Yabi bayanta da kallo yana dariyar takaici yace, "crazy girl"

Dije kam murna kawai take yi shima yau ta wankeshi da turanci don ya gano cewa ita d'in ba jahila bace kamar yanda yake kallonta, taji matuk'ar dad'in samun aron littafin da Lawi ya bata don kuwa dashi ta ke kwana a saman kanta tana hardar kalamai tana had'a wannan da wancen ta yi magana cikin turancin duk da ba dai dai take yi ba amman ba laifi tana kamo hanya.

Har aka tashi school Safwan bai da wata natsuwa Dije kam sai jinta take yi cikin nishadi, don tasa a ranta duk ya kuskura ya sake yi mata wani abun abunda zata yi masa a gaba sai yafi wanda ta yi masa a yanzu.

Safwan kam kalamanta sun saka ya zargi cewa ko itace ta yi masa wannan horon da Berayen?, Sai dai ya sa a ranshi zai binciki kawarta d'aya idan har da gaske ita din ce to shi ko sai ta yabawa aya zakinta, aiko safiya tana wayewa ya yi sammako kamar yanda ya yi jiyan sai gashi ko Mune da su jummalo sun zo zasu wuce ya kira mune ta k'araso wurinshi cikin ladabi ta gayar dashi, sannan ya yi mata tambayar cewa

"Kawarki ta gaya maku cewa ta saka man beraye a d'aki ko?"

Mune ta fara waige waige tace, "A'a ba Ni ta fad'awa ba su Jummala ne ta fad'awa"

Safwan ya had'e fuska yace,. "Au da gaske kenan itace ta saka man?"

Mune ta rufe bakinta da sauri tace,. "Ni ma ban sani ba na dai ji tana fad'awa su jummalar don ni yanzu ko magana na yi mata bata amsa man gaba take yi dani"

Ta k'are maganar cikin taruwar kwallah a idonta, Safwan ya bita da kallon mamakin ashe zarginshi ya zama gaskiya ita din ce amman Lawi ya tsaya Kai da fata yanata kareta tare da wanketa tas da soso da sabulu, cikin k'ara tsuke fuska yace

"Me ya had'aku da har take gaba da ke?"

Mune tana shirin bashi amsa ne ta hango Dije tafe tana tsallen jin dad'i tana yan wakokinta, ta yi saurin dafe k'irjinta tace

"Na shiga Uku don ALLAH kar kace Ni na fad'a maka WALLAHI dukana zata yi in taji"

Cikin rawar jiki Mune ta bar wajen da sauri har da su gudunta ta shige ajinsu, Dije Kam duk da ta hangosu amman ko kallo bai isheta ba ta dage kanta sama ta shige aji, sai ko gashi ya shigo class d'in yayi masu karatu saboda takaicin Dijen ko tambaya d'aya bai tambayeta ba, don ko ta d'aga hannu da nufin bada wata amsar sai ya basar da ita ya zab'i wata, haka yayi ta yi tun Dije bata damu ba har ta zo wuya itama ta daina d'aga hannun.

Ko da aka tashi ya sakata kamun kunne cikin rana tsoron ya daketa yasa ta kama kunnen, tun tana juriya har ta kai ta fara kuka tana fad'in jininta zai dawo ta kai zubowa zai yi k'asa idan taci gaba, ya ce ta koma yin kneel down ta d'aga kanta sama ta kalli rana hannuwanta duka biyu ya d'ora mata duwatsu masu dan girma yace kuma ta yarda suka fad'i jikinta ya gaya mata.

Dije tsawon minti sha biyar tana kallon ranar da taji azaba ta Kai mata karo ta fad'i sheme alamun aljanun sun zo, Safwan ya dauko bulala zai daketa ta yi saurin tashi tana fad'in

"Don girman ALLAH Malam ka yi hakuri yunwa nike ji ka bari in je gida"

Yace da ita suna nan har marece sai ta fad'i uban da yasa ta saka masa beraye a d'aki, Dije ta fara rantsuwar ba ita bace Mune ce amman duk da hakan sai da yayi mata bulala goma tare da gargadin ko kallonshi ta sake yi sai ya nakasata bale har ta sake shirya masa wata mugunta.

Dije ta dawo gida sai kumbure kumburen fuska take yi sai dai taki fad'in abunda yayi mata don kada Baffah yace bazata sake zuwa Makarantar ba.

Marece sakaliya ta tanadi kuka da toshshi ta k'ulle a leda, tana ta harkokinta har zuwa dare sannan ta sassada ta debi garwashin wuta cikin wani mataccen kwano ta rufe ta fita, Kai tsaye Gidan Maigarin ta nufa tamkar wacce aka aika tana shiga sashen d'akinsu Safwan d'in, ta ajiye kwanon ta fiddo tosshi da kukar da ta makale jikinta ta leka d'akin ta hangoshi yanata danne dannen wayarshi, ta dawo ta watsa tosshin da kukar ta yi saurin zuwa ta ajiye masa a bakin k'ofar ta janyo d'akin da sauri ta sake rufewa da wani k'aton iccen katako ta dantseshi ta tafiyarta"

Safwan kam ko da ya ji sautin rufe d'akin yayi saurin Kai kallonshi ga k'ofar, abun mamaki sai ga hayaki ya hango yana fitowa cikin kwanon mikewar da zai yi bala'in azabar da ke cikin hayakin ta fara kaiwa idonshi da hancinshi ziyara, aiko nan take ya fara atishaya ya yi ta dukan k'ofar akan a bud'e masa ba kowa wajen don Lawi ma yana wurin Maigarin sunata firarsu, aiko tun yana iya gane gabanshi har hayakin ya turnuke d'akin ko hannunshi baya gani ga kuma tsananin azabar da ke cikin hayakin, ko da Lawi da sauran Yan Gidan suka zo kawo masa agaji tuni Safwan ya galabaita sai sauke numfashin yake yi a wahalce yana nishi sama sama.

Ganin halin da yake ciki ne yasa Maigarin yaji tsoro yasa Lawi ya d'auki motarsu aka saka Safwan da wasu mutum biyu suka nufi Asibitin babban garin da suke karkashinshi, cikin gaggawa aka shiga dashi emergency room, Lawi da sauran mutanen duka sun yi jugum jugum saboda sun ji tsoron halin da Suka ga Safwan d'in ya shiga cikin kankanin lokaci.





Team Safwan ku garzayo ni kam nayi nan🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️





Akafta🤾🏻‍♂️







D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*ALHMDLLH Lalle dole ne in godewa ALLAH saboda Littafin Dije k'arangiya ya Kai in da Ni din ban isa in je ba, Na gode sosai mutanen Dije Ina yinku all dinku wallah💃🏻💃🏻💃🏻*

*Jinjinar ban girma gareki Kanwata ta gefen awazar damata waton HAJIYA DUDUWA Ina godiya da soyayyarki ga Littafin K'arangiya ALLAH ya bar zumunci tawan🥰🤝🏻*


*Lamba ta 14*


An d'auki lokaci kafin ayi nasarar dawo da numfashin Safwan dai dai, sannan aka kaishi d'akin hutu tare da makala masa ruwa in da shi yake ta barcinshi sharkaf yana ta sauke numfashi a hankali.

Daga Lawi har mutanen da suka zo da su sai a lokaciin hankalinsu ya kwanta, ganin ya dawo cikin natsuwarshi duk da har lokacin bai farfado ba, amman alamun nasarar da suka bayyana ne yasa suka ji natsuwa ta zo masu, a k'arshe dai Lawi ne ya kwana da shi su kuma suka juya suka koma kauyensu domin su sanarwa da Maigarin halin da ake ciki.

***

Dije kam ko da ta saka turaren ba gida ta yi ba lab'ewa tayi tana jiran taga ta ya abun zai kasance, aiko sai gashi tana jikin gini mak'e ta sha jinin jikinta ta fara jin yana ta dukan k'ofa, ta rufe bakinta saboda dariyar da ta sub'uce mata cike da jin dad'i ta k'ara bud'e kunnuwa domin ta ji me yake fad'a, jin yanata atishaya yasa ta fara tsallen jin dad'i ta nufi k'ofar da nufin ta bud'e katakon da ta rufe d'akin dashi ne ta jiyo takun talkami za'a zo, cikin firgici ta koma maboyarta cikin duhu ta lafe luf jikin ginin, sai dai abunda ya firgitata shine ganin an fito da Safwan rangai rangai yana wani numfashi sama sama, nan take jikinta ya d'auki rawa tare da gwalalo ido cikin tsananin tsoro ta biyo bayansu Lawi da sauran mutanen, ganin an sakashi a mota ana shawarar a kaishi Asibiti yasa ta zunduma aguje cikin tashin hankali ta nufi gidansu.

Aiko shigarta ke da wuya Inna ta fara balbaleta da fad'a akan ina ta fito cikin daren? kuma me ya fitar da ita?.

Dije ta yi tsuru tsuru tana warar idanuwa cikin tsoron abunda zai je ya dawo in har wani abin ya sami Safwan d'in, aiko ba shiri ta fashe da wani irin kukan tausayin su Innar, don tasan muddin ya mutu to daga ita har su sun shiga Uku don zaman duniyar ma sai ya gagaresu bale garin nadu, cikin Kuka ta fara fad'in

"WALLAHI Ni ban yi komi ba Inna don ALLAH ki yafe mani"

INNA Hasiya ta bita da kallo cikin duhun daren ta cafko hannunta cike da rud'ewa da jin tsoron in ba wani abu miyagun garin suka yi wa Dijenta ba, sai da ta d'auki wuk'a a kitchen sannan ta jata har kuryar d'akinta ta jefar da ita a tsakiyar d'akin, fuskarta a had'e ta nuna mata wuk'ar tace

"Zaki fad'a man abunda ya fitar da ke gidan nan ko ba zaki fad'a ba sai na kasheki an huta?"

Dije ta zaro ido tare da ja da baya tana kumshe kukanta Inna ma tana biyarta da wuk'ar zare da idanuwa kamar da gaske yankatan zata yi, Dije ta kai jikin bango ta fara kyarma tana fad'in

"WALLAHI Inna ban yi komi ba ki yarda dani"

Cikin b'acin rai Inna tace,. "Baki yi komi ba kika fita? Bayan kin San cewa Baffahnki ya hanaki fitar daren?yanzu haka ga Abincin Inna Gambo nan ajiye ina jiran Usman ya dawo ya kai mata, in da ina b'ukatar ki fitan ai sai a baki kije ki kai mata, zaki fad'a ko sai na yankaki d'in?? "

Inna ta nufota da wuk'ar saitin wuyanta Dije ta zaro Ido tare da fasa k'ara tace

"Wayyo Inna ki yi hak'uri wajen Dan birni naje na yi masa
turaren hayakin toshhi da kuka"

INNA ta dafe kirji tace

"La'ilaha illallahu Muhammadur'rasulullahi Dije kashemu zaki sa ayi a garin nan ne?me yayi maki kuma ya zu da zaki yi masa turaren mayu?"

Dije ta Sha jinin jikinta tana ajiyar zuciyar kuka tace,. "To Inna ba shi bane ya dakeni ranar"

Inna cikin fushi ta kai mata wani mangari tare da wata muguwar faka a baya tana fad'in,. "Ba sai da nace ki kyaleshi kar ki yi masa komi ba? Ashe duk nasihar da nayi maki ta bayan kunnuwanki ta bi ta wuce?, To ai kin kyauta kije ki yi abunda duk kika ga yafi maki tunda Ni kin maida maganata ba komi"

Tana k'are maganar ta fice ranta a matuk'ar bace tana fyace majinar kukan da ya zo mata ba shiri, Dije ta dunkule itama sai kukan take yi saboda har ga ALLAH taji tsoron halin da taga Safwan a ciki.

Ko da Baffah da Usman suka dawo Inna bata yi k'asa a gwiwa ba wajen zayyane masu komi, hankalin Baffah a tashe ya garzaya gidan Maigarin, in da ya taradda k'ofar gidan dank'am! Ana ta bi da zancen abunda ya faru, sai dai duk kashe kunnuwan da yayi bai ji ance Dije ce silar abun ba, hakan yasa shi sakin jiki ya baje anata cecekuce akan binciko wanene mai hannu akan faruwar lamarin, don har kwanon da Dije ta debo garwashin da shi sai da ya gani anata tuhumar inda kwanon ya fito, tare da zayyana irin abunda aka yi masa kwana biyu da suka wuce da Beraye, Wanda a iya bincike duk an bincika an tabbatar d'akin babu wani bera ko d'aya kafin faruwar hakan, ALLAH ya taimaka Safwan da Lawi basu fad'i cewa Dije ce ta aikata ba, to sai gashi yanzu ma ta sake kwatawa don kawai k'ok'arinta na rama abunda aka yi mata, don bata yafiya kuma bata manta ranar d'aukar fansa.

Baffah dai haka ya baje k'ofar Gidan Maigarin har wad'anda suka je kai Safwan Asibiti suka dawo, jin ba'asin samun nasara akan matsalar yasa ya yi sallama da su ya mamayi idanuwan Mutane ya dauke kwanon ya nufo gida da shi , Ko da ya shigo ranshi a b'ace ya wurgar da kwanon ya kalli Inna da ke cika tulunta da ruwan da Usman ya debo mata, yayi kwafa sannan yace

"Ki gaggauta jefa kwanon cen masai tun kafin bincike ya sa a gano Dije ce ta aikata wannan bak'in halin, don WALLAHI wannan karon kam ta jangwalo muna k'aton jidali, saboda yanzu haka fa yaron yana Asibiti sai da naji yanayin jikin nashi sannan na baro wajen"

Inna ta daina zuba ruwan ta yi tagumi tace,. "Ni WALLAHI na fara tunanin ko dai ayi wa Dije aure ne a huta?"

Baffah ya maka mata wata harara yace,

"WALLAHI ba wani aure da zan yi wa Dije yanzu tana yar shekara sha Uku, addu'ar nan dai da muke yi mata kullum to ita za mu ci gaba da yi ko yanzu, ina da tabbacin komi yayi tsanani to maganinshi ALLAH sarki, don haka yanzu ki yi gaggawar jefa kwanon cen a Masai mu huta da fad'uwar gaba"

Har ya fara tafiya ya waigo ya kalli Inna da tayi tagumi ta yi shiru tana nazarin mafita, cikin damuwa yace

"Ina ita Dijen?"

Inna ta yi masa nuni da hannunta akan cewa tana d'aki, Baffah ya nufi d'akin, Inna ta ja kafafuwanta ta d'auki kwanon ta nufi bayi ta jefashi sannan ta dawo cikin sanyin jiki ta k'arasa zuba ruwan ta nufo d'akinta, in da ta taradda Baffah ya ke ta balbale Dijen da ruwan fad'a kamar ya daketa, Dije kam sai kukanta take ta sharba tana ajiyar zuciya wata bayan wata.

Ranar dai haka mutanen gidan suka kwana kowane da abunda yake damunshi, Inna kam kwana ta yi tana rokarwa Dije shiriya tare da rokon ALLAH akan ya bata Miji nagari.

***

Malam Safwan kam sai da ya kwashi awanni sannan ya dawo cikin hankalinshi, in da ya kurawa Abokinshi Lawi idanuwa yana son ya gano tantagaryar abunda ya faru dashi, aiko sai gashi take yanke ya dinga kallon abun a cikin idanuwanshi in da Kai tsaye bayan k'are tunanin nashi zuciyarshi ta tabbatar masa da cewa Dije ce ta yi masa wanna aikin, cikin k'unar zuciya ya gyara kwanciyarshi ya kalli Lawi yace

"Yarinyar nan ko kad'an bata da imani kasheni take so ta yi abokina"

Lawi ya gyara zamanshi yace,. "Me yasa kake son d'orawa yarinyar nan laifin da ba ita ce ta aikata ba?"

Safwan ya k'ara b'ata fuskarshi yace,. "Yarinyar nan ko da ace kanwarka ce iya abunda zaka yi akanta kenan, ban san me yasa kake son kare yarinyar cen ba wai ko dai sonta kake yi ne Abokina?"

Lawi ya yi saurin girgiza kai yace,. "Ko d'aya Ni dai bana son ka dinga zarginta akan abunda ba ita ce ta yi ba, don takamar kaji cewa ta saka maka Beraye to ai wannan baka ji ta fad'a a bakin kowa ba, don haka ka daina zarginta kuma ka ajiye zaton cewa ita ce ka bi a hankali in har ita d'in ce zaka gano ai idan mun koma"

Safwan ya zaro Ido waje yace,. "Mu koma ina? Ai ni kam daga nan sai Gida don kam bazan koma bak'in kauyen nan ba, don na tsani ganin fuskar bak'ar shegiyar yarinyar nan, na tsaneta na tsaneta WALLAHI muddin ina ganinta to ko nine Nan zan yi ajalinta"

Lawi ya zaro ida cikin tsoron lafazin Safwan d'in, sannan ya kyalkyale da wata arniyar dariya yace

"Lalle ashe ko gaba da gabanta waton dai da gaske tsoronta kake ji Abokina, tunda har akanta zaka ajiye aikinka mai Muhimmanci"

Safwan yayi masa wani kallo yace,. "Tsoro??? Duk in rasa wa zan yi tsoro sai wannan bak'ar magen? Cabd'i aiko kayi kuskure Abokina amman tunda har kace haka Zan koma Makarantar inci gaba da karantarwar amman anan garin zan sami wurin zama sai in dinga zuwa ina dawowa"

Lawi ya k'umshe dariyarshi yace,. ,"Har yanzu da tsoron dai to ALLAh yasa hakan shine alkhairi amman Ni kam ina cen kauyen don a gaskiya naji dad'inshi"

Safwan ya yi masa wani mere yace,. "Kaji da rashin hankalinka amman Ni kam na k'are kwana garin daga yau"




🤣🤣🤣🤣🤣





Akafta😹







D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*BAK'ON YANAYI LITTAFI NE MAI ZAFI 300 KACAL ZA TA MALLAKA MAKI SHI MAI BUKATA TA TUNTUB'E NI TA WANNAN NUMBER 09032685442*



*Lamba ta 15*


Tun daga Ranar Dije ta yi sukuku da ita don daga Baffah har Inna sun daina sakewa da ita, daman cen shi Usman ba wani shiri suke yi da ita Sosai ba, Dije cikin dabara ta dinga makalewa gidan Inna Gambo, don wani zubin ma dawowarta Makarantar bokon ke da wuya take tafiyarta gidanta ko Makarantar allonsu daga cen ta ke zuwa, INNA kanta ta fi sha'awar zuwanta Gidan da dai ace taje ta yi ta janyo masu abun magana, duk da ko ita Inna Gambon ana nuna mata halin watarana, saboda muddin ta kawo mata Abinci bata bata nera biyar d'in da take bata kullum ta kawo mata tuwon ba, to ko ko da ta ajiye tuwon sai ta dawo tace

"Inna Gambo kinji Innata tace in babu biyar d'in to a bada tuwon"

Wani zubin ta hanata d'aukar tuwon watarana kuma tace da ita,. "D'auki tuwonku ki kaiwa duk wanda kike so tunda daman cen ba don ALLAH kike kawo man ba"

Watarana kuma ta jefa mata nera biyar d'in tace,. " D'auki gata nan amman ki sani gobe kar ma ki kawo man tuwon don bana so "

Dije sai ta d'auke biyar d'in sannan ta dawo tana kalailameta da dad'in baki, Sabida gyaran hanya har shara da wanke wanke sai ta yi mata, sannan ta dinga debo mata ruwa tana cika mata tukanenta da tulunanta na ruwa.

Inna Gambo da Dije in sun had'u wajibi ne ma sai ka yi dariya saboda yanda suke tsarguwar junansu, musamman dai ita Gambo da kullum ta ke yiwa Dije kirari da cewa

"Alhudahuda Sarkin karatu sillen kara ta Ummaru Sanda, sarka mai rikicin gan gan, in kin so ayi ta morarki in kuma kin k'i ki fad'i ki rikice a rasa gano kanki, Dijengala ta megari Dije ba auren talaka ba talaka noma da sassabe, ALLAH ya kai mu inga aurenki ko don in baiwa Mijinki gudunmuwar bulala"

Dije kam in Gambo tana yi mata kirarin har wani tsallen jin dad'i take yi tana rufe ido wai ita kunya, to dai kam wannan karon ko ita Gambon ta gano damuwar da Dijen take ciki, saboda zaunenta ta ke yi ta yi ta karatunta duk wata kiriniya ajiyeta ta yi ta koma sukuku da ita.

Hankalinta bai kwanta ba sai ranar da ta je Makarantar ta hango Malam Safwan, cikin sanyin jiki ta isa wurinshi ta gayar da shi ta wuce ajinsu, duk da bai amsa ba amman ta ji dad'in ganin ya mirmije daga ciyon dolen da ta sakashi.

SAFWAN kam binta yayi da kallon tsana tamkar ya janyota yayi ta jibga yake ji, amman tsoron sharrin da zata sake kulla masa yasashi yin alk'awalin ba zai sake biyeta ba, ballantana har watarana ta janyo masa bala'in da bai san ta inda zai taroshi ba, karatu dai ne ya zama dole to zai yi masu amman kam yasa a ranshi ba zai sake shiga shirginta ba.

Ta bangarenta ne da kawayenta suka yanke shawarar kai kararshi wajen shugaban Makarantar, saboda basu fahimtar karatunshi sabida tsagwaron turancin da yake ta zuba masu, har za su fita Dije wani

Please Login or Register in order to submit comment