Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Safwan ɗin ya shigo da ƙatuwar leda ya ajiye yana faɗin

"Sannu ya jikin?"

Dije ta yi banza da shi matar ta karɓi ledar ta fito mata da doguwar riga ta saka sannan ta bata hijabi, a zaune Dije ta yi SALLAH duk da ko a hakan ba ƙaramar azaba take ji ba, tana ƙarewa matar ta bata tea mai zafi ta sha tare da magunguna ta taimaka mata ta kwanta sai bacci.

Matar ta kalli Safwan ɗin tace, "A gaskiya Oga ka ɗagawa yarinyar nan ƙafa WALLAHi ta ji rauni sosai"

Safwan ya shafa kanshi yace, "ba komi za'a kiyaye yanzu dai ba wata matsala ko?"

Ta kalli Dijen cike da tausayi tace, "Eh Babu amman tana buƙatar kulawa sosai"

Yace "wannan ba damuwa bane insha ALLAHu na gode sosai da taimakonki"

Suka fita tare ya biyata kuɗinta ya dawo zuciyarshi fes cike da wani masifar sonta da yake ji yana ƙara nutso ta ko'ina cikin jikinshi da zuciyarshi, uwa uba ganimar da ya kwasa a jikinta ya janyo mata wani girma da ƙima a idonshi, cike da ɗokinta ya zauna kusa da ita yana shafo gashinta da fuskarta yace

"can't wait loving you fruits loops forever and ever, you are key to my lyf my popster "

Ya kaiwa bakinta wani ƙaramin kiss ya sake cewa, "sugar lipsy, I love you so much sweet bab life partner, your star shine in my heart chocolatynah, you are my final choice Khadija, saboda bazan taɓa iya haɗa soyayyarki da kowace mace a zuciyata ba, kece farin cikina sanyin idaniyata mai sakani natsuwar da a tara mata dubu ba zasu kama ƙafarki wajen tarin ni'imomin da ALLAH ya tattara ya baki ke kaɗai ba"

Haka ya susuce yana ta suburbudo zantukka, Dije kam sai sauke ajiyar zuciya take yi saboda kukan da tasha, cikin jin daɗi ya raɓa gefenta ya rungumota a hankali shima sai baccin.

Ƙarar wayarshi ce da ta fara ɓurari ta janyo suka farka dukansu, cikin sauri ya sauko ya ɗauki wayar jin muryar Lawi yasa ya fara faɗin

"Abokina ya dai?"

Lawin ya ce, "zaka shigo in jiraka mu je Asibitin dubo Zee ko ko? Don fita nike son yi""

Safwan ya zaro ido waje yace, "me ya sameta?"

Lawi yace "kana nufin ba ka san an yi admitting ɗinta Asibiti ba?"

Safwan ya dafe kai ya ce "subhanllah yaushe?"

Lawi yace "Oho ni ma Kamal ne ya sanar dani"

Safwan ya yi shiru sannan yace, "ALLAH dai yasa ba nine sila ba? don ta sanar dani idan naji mutuwarta to son da take yi man ne ya janyo ajalinta, kuma Ni a yanzu hankalina yafi natsuwa da matata, ka gayar da ita kawai Abokina gaskiya ba zan je ba ALLAH dai ya bata lafiya"

Lawi ya ce "ina alƙawarin auren har ya watse kenan?"

Safwan ya kalli Dije da ta yi kamar bacci take yi yace, "matata ta isheni Abokina itama ta yiwa iyayenta biyayya kawai, na so in zo in kawo Khadijah wurinsu Mama to bata da lafiya ne, amman insha ALLAHu kafin in koma school zan kawota su gaisa"

Yana ƙare maganar ne ya kashe wayar zuciyarshi cike da tunanin halin da Zee take ciki, wani sashe na zuciyarshi yana Ƙawata masa son zuwa ya dubota, wani sashen kuma yana nusar da shi ya barta kawai ta yiwa iyayenta biyayya, don ko da ya aurota ba wani kulawarshi zata samu ba matuƙar Dijen Baffah tana kusa da shi.

Yana cikin nazarin ne Hajiya ta kirashi,ganin sunanta yasa gabanshi ya faɗi ba shiri, ya gayyato natsuwar dole sannan ya ɗaga wayar cikin ɗar ɗar sai ko ya ji tana cewa

"Kuna ina ne yanzu?"

Safwan ya yi saurin kallon Dije yace, "muna Gombe Hajiya mun kusa ƙarasowa"

Tace "to ka yi gaggawar kawo man yarinya tun kafin ka sake ɓat man rai, umurni nike baka ka kawota da sauri ita ake jira"

Tana ƙare Maganar cikin kausasa murya sannan ta kashe wayar, kafin ya tantance abin yi ya ji muryar Dije tana faɗin, "don ALLAH ka kaini gida na fasa zuwa Yolar ni dai"

Safwan ya yi saurin kallonta ya ce

"Ita Yolar me ta yi maki?"

Ta maka masa harara tace, "Ni dai gidanmu nike son komawa kawai, na amince ka je ka auri budurwarka WALLAHi ba zan zauna ka kasheni ba"







😍😍😍








Akafta😅





D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Naga comments ɗinku all kuma na gode🙏🏻*


*Lamba ta 54*


Safwan ya zaro ido waje yace, "kashewa??, To in na kasheki ni in shiga ina?"

Dije ta murguɗa masa baki tace, ,"so kake yi in zauna ka kassarani kenan? ai WALLAHi ni kam bana iya biyayya a wannan baƙin lalacin da ka iya, ƙatoto da kai ko kunya baka ji ka rufe ido ka yi wannan muguwar ta'asa dani, WALLAHi itama innarmu don bata san halinka bane shiyasa ta matsa mani akan in yi maka biyayya"

Safwan ya yana dariya ya dawo kan gadon ya kwanta suna facing ɗin juna tare da ƙura mata idanuwa yana murmushi, Dije kam sai harararshi take yi sama da ƙasa tana murguɗar baki, hakan da take yi ba ƙaramar dariya ta ba shi ba, cikin ƙumshe dariyar yace

"Wai duk wannan hararar ni ake yiwa ita?"

Dije ta ce "to da dawa nake halan?"

Ya ɓata fuska tare da cewa, "kenan har yanzu da sauran renin tsakaninmu kenan? Bayan kuma Baffah da kanshi kinji yana faɗin ki yi man biyayya"

Ta zumɓuro baki tace "to ai kai ka janyo renin? Tunda har baka ji kunyar yi man abunda ka yi man ba "

Yace "ok haka ne ko? To bari in cire tausayinki da nake ji tun da bakin tsiwar taki har yanzu bai mutu ba"

Ya janyota jikinshi ta fasa ƙara saboda zafin da take ji, amman duk da hakan bai hana ya fara yamutsata ba cikin wani sabon salo, Dije tana tureshi tare da kai masa duka amman bai hanashi komawa cikin jikinta ba, tana ihu tana kururuwar neman agaji saboda uwar azabar da take ji tana ratsa ko'ina na jikinta, shi kam ya riga da ya lula cikin hazon gajimare ko gabanshi baya gani bale bayanshi, banda ihun daɗin da yake yi da surutai ba abunda yake fitowa bakinshi sai saka mata albarka kala kala da yake yi, tare da zuba mata ruwan kalaman da ko da wasa bata taɓa tsammanin za su iya fitowa a bakinshi ba.

Sai da ya tabbatar da gamsuwarshi tare da samun nutsuwa a jikinta sannan ya koma lallashinta tare da kalamai masu daɗi na ban haƙuri, Dije kam banda kuka ba abunda take yi cikin kukan ta yunƙura ta miƙe da ƙyar tana faɗin

"WALLAHi ba zan ƙara minti goma cikin garin nan ba sai ka mayar da ni gidanmu ko kuma ni inje da kaina, tunda har kai baka da ɗigon imani a zuciyarka, daman ai son ƙarya ne kake yi man ba wani sona da kake yi sai baƙar yaudarar kalaman da ka saba yi man kullum"

Ta nufi ƙofar fita ya yi saurin biyota yana faɗin "haba khadija wai tona man asiri kike son yi wurin mutane?,kada fa ki sa jama'a su zargi cewa ba muharramata ba ce ke"

Dije ta fashe da kuka cikin takaicinshi da ya cika mata ciki tare da faɗin, "Ni kam WALLAHi babu wanda ya janyo man wannan abun face su Inna"

Safwan yana dariya ya lallaɓata suka yi wanka a gurguje duk da ita ko kaɗan ba da son ranta ba, sannan suka haɗa ƴan komatsansu suka fito, ganin yanayin yanda take tafiya ne yasa gabanshi ƙirewa ya faɗi, saboda tsoron Hajiya Mama ta gano abunda ya faru bayan ya gama cika bakin cewa me zai yi da ita.

Cikin rashin kuzari ya riƙeta gam a jikinshi tana cije leɓe suka shiga motar, sai da ya biya ya sissiyo mata abubuwan maƙulashe da nufin toshiyar baki sannan suka bar Gombe suka kama hanyarsu ta zuwa Yola.

Kasancewar da yunwa a cikinta ta saki jiki ta ci abubuwan da ya siyo mata sannan ta langaɓe sai bacci, ko da suka isa garin ma baccinta take sha ƙa har sai da suka kusa kaiwa unguwarsu sannan ta falka tana ƙarewa gidajen unguwar kallo tace

"Don Allah ka kaini wani wuri inda bazan ga Hajiyarmu ba"

Cikin ranshi yace

_"Ni ma da zan sami hakan da nafi kowa murna"_

Amman a fili ya ce, "kin san kina jin kunyar haɗuwa da ita kika tafi ba da saninta ba?"

Dije ta matso ƙwallar da ta maƙale a idonta tace, "Ni ba ma wannan ba da wane idon zan kalleta idan ta gano abunda ka yi mani?"

Ya sosa kanshi yace

"To ni me ma na yi maki? Salon ki je ki haɗani da ita ko?"

Ta yi saurin kallonshi tace "au kana nufin ka manta abunda ka yi kenan lalle, to ko WALLAHi in baka bini a hankali ba tsaf zan fayyace mata komi"

Ba shiri ya fashe da dariya yace "to na biki a hankalin don ALLAH kar ki fallasani don nasan ƙaramin aikinki ne, idan kuma ke baki san yanda ake rufe sirrin miji ba to ki tona ɗin sai inga da ni da ke waye zai jiyo kunya?"

Wasu hawaye suka zubo mata akan fuska tace, "WALLAHi ALLAH baka kyauta man ba, yanzu shikenan zata gano na iskance"

Ya yi shiru yana saurarenta tana kuka tana soki burutsun zantukkanta, har suka je bakin gate ɗin gidan sannan ta sake fashewa da wani sabon kukan, cike da mamakinta da fargabar da ta cika masa zuciya ya yi parking ya fito suna gaisawa da ma'aikatan gidan, Dije kam kasa motsi ta yi har sai da ta ji yo muryar Fiddo tana yi wa Safwan Oyoyo.

Sannan ta muskuta da ƙyar ta fito tana goge hawayen da suka ɓata mata fuska, ganin yaran wata yayarsu Safwan ɗin sun nufota suna faɗin

"Oyoyo sannu da zuwa" yasa ta washe ta taryesu da murnarta ta ɗauki ƙaramin yaron, ko kallon Fiddo da shi bata yi ba ta fara taku a hankali cikin ƙarfin hali ta shiga cikin gidan, Safwan ya bi bayanta da kallo cikin tausayawa halin da take ciki a zuciyarshi, Fiddo ma shi ta bi da kallo tana faɗin

"Ai WALLAHi yayanmu duk abunda Hajiya ta yi maka ka fanshe akanta, kana ga fa tunda ta bar gidan nan bamu sake ganin fuskar Hajiya ba, kullum zancenta ɗaya ne ALLAH ya dawo da wannan ƴar ƙauyen lafiya, ita bata ko ta jin taka sai ta ɗiyar wasu haka kawai ta zo ta ƙwace muna fada a wurin Hajiya, yawwa ina zancen da ta ji muna yi da kai....? shikenan fa ta hau akan cewa wai ni da kai ne muka haɗa kai muka sa ƴar ƙauyen ta bar gidan, duk rantsuwar da nasha yi mata fa bata yarda da ba hannunmu ba"

Safwan ya bita da kallo mai cike da harara yace, "to wai ke wa ma ya tambayeki wannan uban surutun da kike yi? Yarinya dai gata na dawo da ita to kuma yanzu me yayi saura?"

Fiddo cikin tsoron yanayinshi da taga ya canza a lokaci ɗaya yasa ta sha jinin jikinta ta ce "ka yi haƙuri big bros Bari in shiga ciki kafin ka ƙaraso"

Da sauri ta shige ta barshi yana tunanin ya shiga ko ya bari sai dare ya sulalo ya shige ɗakinshi?, Wata zuciya tace da shi ya shiga kawai ya roƙeta yafiya ya sauke nauyin, ya mazge ya ja ƙafafuwanshi ya shiga gidan cikin fargaba, yana ta rokon ALLAH a zuciyarshi akan kada yasa Hajiya ta ja abun da tsauri.

Sai dai yanayin da yaga ta tarbeshi ne yasashi shan jinin jikinshi amman a hakan ya ƙoƙarta yace,

"Don Allah Hajiyarmu ki yi haƙuri WALLAHi......."

Ta yi saurin ɗaga masa hannu tace, "ajiye ban haƙurinka ni ba shi nake buƙata ba, yarinya dai gata ta dawo hannuna to kaji da kanka kawai don ALLAH"

Safwan zai fara yi mata magiya ta katsa masa tsawa tare da bashi umurnin fita ɗakin, ya miƙe ba shiri ya fice cikin ƙunar zuciya, Hajiyar ta bugawa Fiddo da ke tsaye wata uwar harara itama ta fice sum sum, ta kalli Dije da ke zaune tana sharar ƙwallah ta ce

"Ke kuma jeki ɗaki ki jirani kafin in zo"

Dije ta miƙe a hankali ta fara ɗingisa ƙafa Hajiya ta bi ta da kallo har ta shige, cikin tausayawa ta dawo da kallonta ga Yayarsu Safwan ɗin tace

"Ummi ki kirashi kawai yanzu tunda har mun samu ta dawo lafiya, gobe idan ALLAH ya kaimu tun da sassafe sai ku kama hanya, saboda bana son ma yasan ke ce kika tafi da ita, don nasan halinshi bana don ya dameki akan sai an bashi ita"

Aunty Ummi ta yi shiru sannan tace, "Hajiyarmu naga kamar yanzu yana son Matarshi fa ki yi haƙuri ki yafe mashi don ALLAH Hajiyarmu"

Cikin tsananin ɓacin rai tace "eh nasani Kuma a sanadiyar hakan ma ne nike son nuna masa cewa ko shege yana da ranar shi, saboda haka ki yi abunda nace da ke kawai umurni na baki ba shawararki na nema ba"

Cikin sanyin jiki Ummi ta ɗaga waya ta kira wani mai suna Garba, bayan ya ɗauka tace da shi gobe tun da sassafe ya zo ya ɗaukesu ya yi driving ɗinsu ita da yaranta zuwa Abuja.

SAFWAN kam yana fitowa kiran Ruma yana shigowa wayarshi, ganin mai kiran har yaso kar ya ɗauka ganin ta dameshi da kiran ne yasa ya ɗaga, cikin Muryar kuka Ruma tace

"Don Allah ka zo Zee tana cikin mawuyacin hali kuma ba wanda take kira sai sunanka, plss ka zo WALLAHI tana unconscious we need your help seriously kuma urgent plss and plss"



Wata sabuwa🤦🏻‍♀️






Akafta😉









D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Ku yi haƙuri ku yi haƙuri ni ma ba haka na so ba😢*



*Lamba ta 55*


Cikin wani sabon tashin hankali tare da kiɗimewa ya koma wurin Hajiyar, yana sanar da ita halin da Zee take ciki tare neman izininta akan komawar da yake son yi Gomben, ba tare da wata damuwa ba ta ce da shi ALLAH ya tsare, har ya fito ya dawo yana sosa kai yace

"Khadija fa? Don Allah zan bata saƙo kafin in tafi"

Hajiyar tace da shi tana ciki ya yi saurin shigewa ɗakin zuciyarshi cike da tunanin abubuwa da yawa a ranshi, sai dai yanayin da ya taradda ita ne yasa gwiwowinsa suka yi sanyi, cikin mutuwar jiki ya ja ƙafafuwanshi ya isa wurin da take kwance tana ta cisgar kuka, ya yi saurin duƙawa gaban gadon tare da ƙoƙarin ɗago fuskarta amman ta ƙi ba shi damar hakan, cikin damuwa ya ce

"Haba khadija yanzu kuma me aka yi maki?don ALLAH ki yi haƙuri ki yafe mani abunda na yi maki, Ni ma ba da son raina ba na kasa controlling kaina ne shiyasa, ban san me yasa na sake aikata maki abunda na yi ba duk da nasan zan cutar da ke, plss ki yafe mani don ALLAH, plss ki ɗago fuskarki ki ce dani kin yafe mani don ALLAH"

Dije taƙi ɗago fuskar haka ma ta ƙi daina kukanta, yana cikin magiyar ne kira ya sake shigowa wayarshi, cikin sauri ya fiddo wayar ya duba ganin Daddyn Zee ne da kanshi yasa ya yi saurin ɗagawa, cikin muryar kuka mai haɗe da tashin hankali Daddyn Zee ya ce da shi

"Don Allah ka zo ƴata zata rasa ranta a sanadinka, plss ka bi yo jirgi urgently ake buƙatar ganinka, don ALLAH ka taimaki rayuwar ƴata ka zo"

Ya ce "insha ALLAHu zan zo soon" sannan ya kashe wayar ya miƙe jkinshi yana rawa ya kalli Dije da ke ta kukanta, cikin damuwa ya ce

"Ni zan je Gombe yanzu Khadija ki yi man addu'ar dawo wa lafiya kinji?"

Yana ƙare maganar ya duƙo da kanshi saitin fuskarta ya sakar mata da wani kiss a kumata sannan ya fice da saurinshi, daga nan inda take tana ji yo shi yana yin sallama da su Hajiyar, haka kawai ta ji kamar ta tashi ta bishi ta sanar da shi ta yafe masa, amman wata zuciyar ta gargaɗeta akan kada ta yi hakan saboda kunyar idonsu Hajiya da Aunty Ummin da ke falon, sai dai a zuciyarta ta yi masa fatar ALLAH ya dawo da shi lafiya, saboda bata fahimci ko wanene ya yi kiran nashi ba, ammsn taji rashin son tafiyar har cikin ranta.

Tana kwance ɗakin ne Hajiyar ta shigo ta yi toilet minti biyar a tsakani sai gata ta fito ta ce da ita ta biyota toilet ɗin, cikin fargaba Dije ta miƙe ta tako a hankali saboda zafin da take ji yana ratsata, sai dai ganin fuskar Hajiyar a haɗe ya sa ta yi saurin gyara tafiyar cikin ƙarfin hali, Hajiyar ta maka mata wata uwar harara ta ce

"Ki cire komi naki ki shiga cikin ruwan nan ki buɗa ƙafafuwanki da kyau su ratsa jikinki, ki yi haka har sau uku duk kika tara ruwan kinga wannan maganin ki zuba a cikin sannan ki sake shiga, idan kuma baki yi yanda na ce da ke ba to ni zan zo da kaina in yi maki, tunda ke Kika janyo wa kanki duk abunda ya yi maki, to ai ga shi nan ya barki da jinyar jiki shi ko a jikinshi"

Cikin fushi ta fice toilet ɗin tana ta ƙananan faɗa, Dije ta bi ruwan da ke cike da bahon wankan har turirin ɗimi suke yi, amman saboda gudun ta zo ta yi matan kamar yanda ta faɗa ya sa ta yi saurin cire kayanta ta shige ruwan zafin ta zauna, ruwan suna shiga jikinta tana yarfa hannu tare da cije leɓe har suka dallashe, sannan ta fara jin ƙarfi a jikinta ta yi hakan sau uku kamar yanda Hajiya ta ce sannan ta yi wanka ta fito, sai gata tana takawa da kyau duk wani zafi da take ji ya rage sosai, bayan ta shirya ta ci abinci ne Hajiyar ta zaunar da ita ta ce

"Gobe idan ALLAH ya kaimu Ummi zata je da ke Abuja, zaki zauna a cen ki ci gaba da karatunki a cen, insha ALLAHu zata riƙeki kamar yanda na yi maki a nan, fatana kawai ke ma ki ɗauke ta tamkar yanda kika ɗaukeni, don duk da kinsani amman dole in ƙara sanar da ke cewa itace gaba da Safwan shi yake bi mata, ki yi haƙuri da duk abunda ya yi maki da sannu zai hankalta har ya dawo ya baki matsayin da nike ta yi maki fata a wurinshi, sai dai ki iya mu'amala da kowa saboda yanzu da da cen inda aka fito ba ɗaya ba, kina da aure kuma Mijinki yana sonki ko da ko bai faɗa ba, saboda ki riƙe masa amanar kanki kuma ki riƙe mutuncin aurenki, ALLAH ya baku haƙurin zama ki dage ki yi karatunki don shine gatanki ko don ke ma ki tallafi iyayenki da hannunki"

Dije ta yi shiru tana sharar ƙwallah tace "ALLAH ya bamu haƙurin zama"

Ummi da Hajiya ta ce "Ameen"

Tun cikin daren ranar Hajiya ta haɗa mata kayanta tsaf! Asubar farin Garba ya zo ya ɗaukesu suka kama hanya sai fatan sauka lafiya ake ta yi masu, bayan tafiyarsu ne Hajiya Mama ta riƙo kunnen Fiddo ta ce

"Ke kuma WALLAHi ko da wasa na ji kin sanar da shi cewa ga inda Matarshi ta ke, to ki sani daga ranar kin bar gidan nan, don kuwa ƙauyensu Baabah Kulu zan kai ki cen ki zauna har sai an tashi aurenki a dawo da ke nan"

Fiddo ta zaro ido waje tace "Haba Hajiya wannan mugun ƙauyen? Ai WALLAHi ni ko yini ɗaya ba zan iya yi a cen ba bale har in yi rayuwa a cen tab! Mutuwa, Hajiya garin da ko toilet ba bu daji ake kashi kike so in je inyi rayuwa a cen?"

Hajiyar ta sunne dariyarta tace, "to idan ba kya so ki ceci kanki kawai a wuce wurin, amman WALLAHi duk ranar da naji kin faɗa masa inda take to a ranar zaki bar garin nan ki je cen"

Fiddo ta yi saurin shigewa ɗakinsu tana zancen zucinta tana faɗin, "to ni me ma zai sa in faɗi inda take tunda har ma ba wani damuwa ya yi da ita ba, kuma ma ni daga ALLAH ya rabamu da ƙaya ai godiya yakamata inyi wa ALLAH ba wai faɗa masa ba, don ni har kuɗi ma zan iya badawa akan kada ya gano inda take"

Ta faɗa gadonsu cike da jin daɗi tace"ALLAH ya raka taki gona WALLAHi Ummu ta gayar da Aysha"

***

Safwan kam a kiɗime ya isa Gomben kai tsaye Asibitin ya nufa don ko Lawi bai nemi rakiyarshi ba, sai kuwa ga shi zuwan ya yi rana don kuwa ko da ya je numfashinta sama tana kiran sunanshi cikin dusashiyar muryar da ta sha ciyo na faraɗ ɗaya, mahaifiyarta da Daddynta da sauran Yan uwanta da Aminu da ƙawarta Ruma duk kuka suke yi, ganin Safwan ɗin da ta yi ne yasa ta yi saurin kiran sunanshi da ƙarfi ta some, ai kuwa ɗakin ya ɗauki kuka saboda tsammaninsu ko ta rasu, shi kanshi Safwan ɗin kwatanta tashin hankalin da ya shiga abu ne babba, saboda ganin yanda ta rame lokaci ɗaya sai karen hanci da ya fito idanuwanta duk sun zurma, hankalinshi bai kwanta ba har sai da likitoci suka rufu a kanta tare da yin nasarar zuƙo numfashinta, cikin dawowar numfashin ne ta fara nishi sama sama tare da sauke numfashin da sauri da sauri, Mahaifin Zee ya zo gabanshi ya duƙa hawaye suna kwaranya akan fuskarshi ya ce

"Ka taimaki ƴata ta dawo cikin natsuwarta"

Aminu da ke tsaye ranshi a ɓace ya fice ɗakin, Safwan ya ɗago Mahaifin Zee ɗin ya miƙe cikin kwantar da murya yace

"Ka yi haƙuri Alhaji Insha ALLAHu ALLAH zai bata lafiya"

Muryarshi da ta ji yo yasa ta yi saurin faɗin sunanshi, Likitan ya ce ya matso kusa da ita ya bashi wuri ya matsa jikin gadon, Zee ta yi saurin riƙe hannunshi ƙam ƙam tana zubar da wasu hawayen takaicin kanta ta ce

"Me yasa ka yi man ƙarya? Me yasa ka amince da ni bayan kasan kana da matarka wadda ka fi so fiye da ko wace mace?, a hakan ka so in aureka in je inyi auren boranci? Ina sonka my man amman ka sani ko da zan mutu ba zan aureka ba, na yafe maka abunda duk ka yi mani ALLAH ya haɗa fuskokinmu a al..ja..n...n...ah"

Sarƙewar da numfashinta ya yi ne yasa ta sake somewa, Mahaifiyarta ta fashe da wani uban kuka, Ruma da ƙawarta da sauran matan da ke ɗakin suma suka kwantsama kukan, da ƙyar likitoci shawo kansu wajen fitar da su ɗakin suka dawo kan Zee ɗin suna ta aikin neman ceton rayuwarta.







Wayyo Zee Baby😢




Akafta🥰









D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*


*Addu'o'inku da kullum kuke bina da su ba ƙaramin faranta man zuciya suke yi ba🥰, na gode 🙏🏻sosai Mutanena Alkhairin ALLAH ya kai maku a ko ina kuke👍🏻 muna kyawon tare🤝🏻*



*Lamba ta 56*



Likitoci sun yi iya ƙoƙarinsu amman numfashinta sai sama da ƙasa yake yi, wani likita ya ce da Safwan ɗin ya yi mata magana cikin daɗaɗan kalamai, ko da ALLAH zai sa ayi nasarar ceto ranta cikin mawuyacin halin da take ciki, saboda tana sonshi idan ta ji muryarshi kuma ALLAH ya shiga cikin lamarinta aka yi dace za'a yi nasara.

Safwan riƙe da hannun Zee ɗin da har lokacin take riƙe da shi jabau!, yana hawayen tausayinta ya ce

"Plss my precious ki tashi gani a kusa da ke, ke ma kinsan ina sonki kuma bazan iya rayuwa babu ke ba, plss and plss for give me i apologies for you and everything else, ki tashi ki kalleni ido cikin ido in sanar da ke a shirye nike da aurenki a kowane lokaci, kinsan na yi maki alk'awali kuma insha ALLAHu bazan saɓa ba, ki tashi ki kalli Man ɗinki ki ido cikin ido ki ce kin yafe masa plss my dream"

Ya ƙare maganar cikin wata muryar kuka saboda yanda yaga har lokacin numfashinta ya ƙi daidaita, saboda yana jin tsoron ace ƴar mutane ta mutu ta sanadinshi, ganin anƙi samun abinda ake buƙata ne yace da likitocin su bashi minti biyu, saboda sun san kan aikinsu yasa suka bashi haɗin kai wajen ficewa dukansu, Safwan ya miƙe ya yi sunkuyo saiti da fuskarta ya buɗa bakinta ya saka nashi ciki, cikin wani salo ya fara zuƙo numfashinta a hankali tare

Please Login or Register in order to submit comment