Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙasa cikin kiɗimewa yana ta sambatun kiran sunan Dijen, tare da faɗin

"Ina kika shiga ne don ALLAH ki dawo wallahi ina sonki ke ma kinsani ai"

Har dare ya raba yana ta abu ɗaya zuwa lokacin mutane sun fara taruwa kanshi ana tambayarshi mafari, da dai ya fahimci ya tarawa kanshi ƴan kallo ne ya tashi ya faɗa Motarshi ya nufi gidansu wani ɗan uwansu kuma abokinshi, cike da tsantsar tashin hankali yake yi masa bayanin duk abunda yake faruwa, Abokin nashi ya jinjina abun a ranshi sannan ya ce

"A gaskiya Abokina ka yi kuskure babba yanzu mafita ɗaya ce ka je ka baiwa Hajiyar Haƙuri kafin ka kama hanyar zuwa garinsu yarinyar, saboda jikina yana bani ta yi gida don ta gaji da abunda kake yi mata ne shiyasa ta gudu"

Sannan Safwan ya tuno da wayarshi ya ɗaukota da nufin kiran Hajiyar sai ga kiran Lawi da Kamal ya fi ashirin a wayar, cikin sauri ya kira Lawin da rawar baki yake faɗin

"An ganta?"

Lawi murya mai cike da damuwa yace "WALLAHi ba'a ganta ba ni na fara zargin ko ta yi garinsu"

Safwan ya dafe kanshi cikin wani sabon firgici yace,. "Don Allah Abokina ka roƙar mani Hajiya in dawo gidan in bata haƙuri WALLAHi gobe tun da sassafe zan kama hanyar garinsu Khadija in dawo da ita"

Lawi yace "kayi haƙuri Abokina WALLAHi Hajiya ta shiga damuwa sosai akan ɓatan khadija yanzu haka ma da ƙyar na lallasheta ta daina kuka, ga gidan gaba ɗaya hankalinsu ya tashi madadin farin ciki gida ya koma na jimami"

Safwan a kiɗime ya kashe wayar tare da furta "Innalilahi wa'Inna ilairraji'un Allahumma la sahla illa maja'altahu sahla, ALLAH ka tsare yarinyar nan a duk inda take, Ubangiji ka bani ƙarfin gwiwar tunkarar wannan mummunar ƙaddara da ta faɗowa rayuwata"

Ya kalli Abokin nashi da jajayen idanuwanshi yace, "bari inje Mubarak banga ta zama ba tunda har nine na janyo komi"

Mubarak cike da tausayinshi yace, "ba dai yanzu kake nufin zaka bi bayanta ba?"

A zafafe ya faɗa motarshi yana faɗin "banga ta zama ba ai kuma matuƙar ba ganin yarinyar nan nayi ba....."

Kiran wayarshi ne ya katse maganar da yake yi cikin sauri ya ɗaga saboda ganin numbar Hajiyarshi ce, kafin ma yayi magana yaji muryarta cikin muryar kuka tace

"WALLAHi matuƙar baka dawo man da yarinyata ba to kada ka kuskura ka tako ƙafarka cikin gidan nan"

Cikin rawar murya yace, "ki bini da addu'ar tsari kawai Hajiyata, nayi maki alkƙawali bazaki ganni ba sai tare da Khadija insha ALLAHu"

Kittt! Hajiyar ta kashe wayar saboda wani kukan tausayin kansu da ya kamata, Surayya dake ta bata haƙuri ta yi saurin faɗin

"Don girman ALLAH Hajiyarmu ki yi haƙuri Insha ALLAHu ba abunda zai sami Khadijah ALLAH zai kareta a duk inda take"

Hajiya ta miƙe ta nufi toilet Surayya da Fiddo da yayyensu biyu mata da wasu ƴanuwasu da ke ɗakin suka bita da kallon tausayi, saboda yanda ta ɗaga hankalinta sosai akan rashin ganin Dijen, kowa sai faɗin albarkacin bakinshi yake yi akan lamarin.

Wannan shine abunda ya faru kafin Hajiya ta kira garinsu Dijen ta ji labarin cewa tana cen, don ko shi Safwan ɗin yana kan hanyarshi ne ya sami labarin cewa tana garinsu a bakin Surayya, saboda ƙoƙarinta na son rage masa damuwar da yake ciki.

Ranar yinin bikin Surayyar ma bikin ba wani armashi saboda damuwar da uwar bikin take ciki, haka aka tattara aka kai Surayya ɗakin Mijinta ita kanta zuciyarta ba daɗi saboda halin damuwar da ta baro Hajiyarsu a ciki.

Safwan kam sai da ya ganshi a babban birnin su Dijen sannan hankalinshi ya fara daidaito, ya yi masauki anan sannan ya kimtsa sosai cikin shiga ta alfarma ya buga Motarshi ya nufi ƙauyensu Dijen, zuciyarshi cike da jin daɗin matsalarshi ta zo ƙarshe, saboda fushin da Hajiyar take yi da shi ya fi komi ɗaga masa hankali fiye da duk wani hali da yake ciki.

Dije kam kasancewar daga ita sai kayan jikinta ta shigo garin, Inna ta ɗauki turminta biyu ta baiwa Usmanu tace ya kai babban birninsu inda aka yi wa Hansai ɗinkinta na aure ayowa Dijen ɗinkin Express saboda mijinta yana kan hanya, ya karɓa ya tafi yana dariyar yanda Inna take son farantawa surukinta.

Da marece sakaliya Usmanu ya dawo da ɗinkunan Inna ta karɓa tana ta murna Dije kam iyakacinta ido, don gaba ɗaya jin take yi zama gidan ya gundureta saboda jin da ta yi ance Safwan yana kan hanyar zuwa garin.

Kasancewar shagar dare ya yiwa garinsu Dijen shiyasa da yawa mutane basu san da zuwan nashi ba, cike da jin daɗi ya yi parking ƙofar gidan ya fito yana baza babbar riga sai tashin ƙamshi yake yi.

Jin ƙarar ajiye motar yasa Usmanu saurin fitowa saboda daman cen kowa da tsumayin zuwan nashi yake a gidan, bayan sun yi musabaha ne Usmanu ya ce da shi ya shigo, Safwan ya biyo bayanshi zuciyarshi sai dakan lugude take yi saboda tsoron kada Dijen ta bashi kunya a gaban surukan nashi, da sallamarshi a baki ya shiga Baffah da Inna baki har kunne suke amsa masa sallamar, Dije da ke ɗaki tana gunguni tun daga cen ta ji yo ƙamshin turarenshi, ta yi saurin duƙunkunewa kan gadon har da su lulluɓewa duk da gayun da Inna tasata ta yi na tarbon Safwan ɗin.

Safwan cikin ladabi da jin nauyinsu ya rusuna yana gayar dasu, inda suma ɗin suke amsawa cikin mutunta juna da karamci irin na surukantaka, bayan an ƙare gaishe gaishen ne Safwan ya ɗan muskuta tare da ƙara sunne kanshi yace

"Don ALLAH ayi haƙuri da zuwan da Khadija ta yi WALLAHi bansan da zuwan na ta ba a yafe mani don ALLAH"

Dije daga cen ɗaki jin abinda ya faɗa yasa ta yi zumbur ta fito tana huci tace

"Ba kai kace......."

"Kul!" Katon kashedin da Inna ta yi mata kenan wanda ya sata yin shiru ba shiri, ta yi saurin komawa ɗakin tare da fashewa da kuka tana faɗin

"Shikenan Ni komi na yi bani da gaskiya ai"

Baffah ya kalli Safwan da kyau yace, "ka yi haƙuri da halinta don ALLAH don alamu duk sun nuna ba ƙaramin surutu take sakaku ba, don ko wannan zuwan da ta yi hakan ya tabbatar mani da cewa har yanzu bata san minene auren ba, ina mai ƙara baka haƙuri akan shirmen da take yi maku don ALLAH ku ƙara haƙuri da ita, insha ALLAHu da sannu komi zai daidaita har ma ku yi alfahari da zamanta cikinku"

Safwan ya duƙe kai yana murmushi yace, "ba komi Baffah insha ALLAHU ma komi ya wuce daga yanzu, saboda gobe idan ALLAH ya kaimu lafiya nike son mu koma tare da ita"

Baffah ya yi shiru sannan ya ce, "ina neman alfarmarka Muhammadu akan ka yi haƙuri ka bar muna ita anan zuwa wani ɗan lokaci, Insha ALLAHu zamu fahimtar da ita komi saboda gudun irin wannan matsalar da ta faru ta sake faruwa"

Kirjin Safwan ya buga dirim! dim! Cikin firgici yace, "don ALLAH ka yi haƙuri in tafi da ita Baffah, saboda WALLAHi idan ban koma da ita ba akwai matsala, saboda yanzu haka Hajiya fushi take yi da ni sosai akan zuwan da Khadija ta yi, kuma ta sanar da ni cewa muddin ban dawo ƙafata ƙafarta ba to kada ma in koma gidan, gashi ina son in koma makaranta saboda saura shekara ɗaya in kammala karatuna"

Baffah ya yiwa Inna wani kallon neman shawara ta ɗaga masa kai a fakaice, cikin sauki ya ɗauko hannu sannan ya ce

"To ya yi ai ba komi ALLAH ya nuna muna goben lafiya kuma ya tsare hanya ku je lafiya"

Cike da jin daɗi Safwan ya washe baki ya ce, "Ameen Baffah" Inna ta ce da shi 'ka yi haƙuri ko ruwa bamu baka ba"

"Dije!!" Inna ta ƙwallawa Dijen kira tace ta je ta kaishi ɗakin samartakar Usmanu ya ci abinci, Dije ta fito tana tunzure tunzure ta nufi ɗakin da ke cikin zauren gidan, wanda tun da safe Inna ta gyarashi tsaf aka malala ƙatuwar tabarma sabuwa dal, tare da wata babbar carpet a samanta, ga wani turaren wuta da aka ƙamsasa ɗakin da shi, kasancewar Abincin da komi da aka tanadar masa yana ɗakin an ajiye, Dije tana shiga ɗakin ta ja ta tsaya tana wani cin magani tana gunguni, Safwan cike tsantsar farin ciki ya nufi inda take tsaye ya tsaya tare da rungume hannuwa a ƙirji yana ƙare mata kallo cikin hasken ƙatuwar fitilar cajin da ke haskaka ɗakin, wadda takanas Usmanu ya siyowa su Inna ita har da Baffah da tashi ta zama torch light a babban birnin garinsu, idan zai je da safe ya fita da su a cikosu da caji ya kawo masu, shiyasa basu rabo da caji kullum gasu da ɗan karen haske tamkar nefa.

Kallon da Safwan ɗin yake yi mata ne yasa ta ɗago fuskarta tana yi masa hararar sama da ƙasa, sannan tace

"Ka daina murna don kaji ance zan koma WALLAHi muddin ka sake taɓani idan na baro garin to ko gidan nan bazan dawo ba, tunda na gano suma ɗin ba sona suke yi ba komi nayi sai anga laifina"

Safwan ya sauke wata ajiyar zuciya tare da ƙara matsowa daf da ita ya dafa bango da hannunshi ɗaya yayi mata rumfa, cikin tsoro ta yi saurin kallonshi tace

"A gidan namu ma bazaka barni ba kenan?"

Yayi wani murmushin gefen baki yace, "Ni ba a namu gidan kika so ki kasheni da soyayyarki ba? Ko kin manta abunda kika yi mani a gaban kowa wanda har yanzu gashi kin janyo budurwata ta gujeni?"

Dije ta yi saurin rufe fuska tace, "Surayya ce tace dani inyi hakan idan naganka tare da budurwar, to ma ni ina ruwana da ita da har zansa ta gujeka?, Ka je cen ku sasanta abunku don ni yanzu gaba ɗaya ma daga kai har ita baku gabana"

Ba shiri ya ɗora hannunshi saman leɓunan bakinta, cikin wata siririyar murya yace, "shiiiiiii! Bana son doguwar magana anan gidan, ki zo kawai ki bani abincin da aka ce ki bani yunwa nake ji"

Ya ƙare maganar tare da langaɓe mata kai kamar wani yaro, Dije ta kalleshi cike da mamakinshi ta ce

"Ka je gashi cen ka ci ni bana son salon yaudara don an ganni cikin gidanmu"

Safwan ya yi saurin haɗe fuska ya ce

"To shikenan bari inje in sanarwa da Inna kince in zuba da kaina"

Yana gama faɗar maganar ya nufi ƙofa da nufin fita ta yi saurin shan gabanshi tace, "To Ni dai ka tsaya ai ba cewa na yi bazan zuba ba ko?"

Ya yi saurin bushewa da dariya yace, "to muje ki bani kuma ga baki nake so idan ba haka ba yanzu inje in sanarwa da su Baffah"

Dije ta yi saurin zuwa wajen kayan abincin tana zuba masa ta ce

"shi dai mutum duk muguntarshi to ya kiyayi haɗa ɗiya da Uwayenta"

Cikin dariya ya ce

"Wannan kuma ai sai ki yiwa kanki wa'azi don ke kullum aikinki kenan haɗa ɗa da Uwatai, yanzu haka akanki ance kada ya kuskura ya sake taka gidan Ubanshi matuƙar ba tare da ke ya dawo ba, sai ki auna da tawa muguntar da taki wacece ta fi muni???"





To reader's ku bashi amsa in Dijen taku ta kasa🤪





Akafta🤣







D/AUTA Ce✍🏻
*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Ina baku haƙuri akan rashin mayar da reply ɗin da banyi ba na comments ɗinku😍amman ku sani na gani all kuma ngd gaba ɗayanku🙏🏻*



*Lamba ta 51*



Dije tace "taka muguntar ce mana, saboda miye ma Ni baka yi man ba?, Ai WALLAHi ka ci sa'ar Inna ta ce kada in koma yi maka wani abun da bai dace ba, da bazaka bar garin nan ba har sai na bar maka shaidar da zaka nuna a matsayin tarbar da nayi maka, wadda a kullum ka kalleta sai ka tuno da ni don kuwa tambon ba zai taɓa goguwa a jikinka ba"

Safwan ya tako a hankali ya ƙaraso inda take zuƙunne tana zuba abincin, shima ya yi durƙuso ido cikin ido yake kallonta na tsawon mintuna, sannan cikin wata murya mai kama da raɗa ya ce

"Ko yanzu mi ye marabar dambe da faɗa?, Ai tuni kin barni da taɓon da ya fi wanda kike da gurin yi mani a yanzu, tambon da nike da tabbacin har abada ba zai taɓa goguwa a cikin zuciyata ba, kin riga da kin sakar mani dafin da ya bi jikina ya mamaye ko'ina lungu da sak'o, a ganinki wannan tambon bai fi wanda kike ikirarin ki yi man ba a yanzu?"

Dije ta turo baki ta ce,

"Ai fa yanzu kam tunda an ganni gidanmu komi ma cewa za'a yi, amma da na yi sakacin da na bika kuma sai ka nunawa duniya cewa ni ɗin ba kowa ba ce bayan ƙaskantacciyar ƴar ƙauye, ka sani a shekarun baya ka yi nasara akaina wajen biyarka da na yi saboda daɗin bakin da ka yi mani, amman ka sani wannan karon daban da wancen cen, saboda cikin alƙawullan da ka ɗaukar mani ko ɗaya baka cika mani ba"

Cike da mutuwar jikin da kalaman nata suka haifar masa ya yi jarumtar faɗin

"Kamar wane da wane fa don ina son yanzu in tabbatar maki da gaskiyar duk abunda kika ji ya fito bakina"

Dije ta jawo abincin gabanshi ta ce

"Ka zauna da kyau ka ci abincin ni dai kada ƙafafuwanka su yi sanyi ace garinmu aka samu ciyon"

Tana ƙare faɗar maganar ta miƙe ya yi saurin riƙo hannunta yace, "ina zaki je kuma muna firarmu mai daɗi?"

Dije ta wurga masa wata harara tace, "abinci aka ce in baka Kuma gashi na baka to kuma ni yanzu zaman me kake so in yi anan?"

Safwan yana rike da hannunta ya yunƙura ya miƙe tsaye, cikin mayen sonta da ke fisgarshi ya saka hannu biyu ya rungumota duka jikinshi, ta yi saurin zillewa amman sai da ya sake rungumotan har ƙamshin turarenshi mai daɗi ya daki hancinta, cikin wata murya da ita kanta batasan ya aka yi ta canza ba tace

"Haba Malam ka daina abunda kake yi ba kyau fa, saboda akan wannan halin naka na dawo gida amman kuma gashi anan ɗin ma ban tsira ba, kai wai halan baka jin kunyar wani ya ganmu da wannan zunubin da kake ƙoƙarin aikatawa gareni kullum?"

Safwan ya kai bakinshi saiti da nata ya sakar mata wani guntun kiss, ta yi saurin kaucewa tana goge bakin da hannunta ta ce

"WALLAHi Malam kaji tsoron Allah Ni dai gaskiya nike faɗa maka"

Ya yi saurin damƙe hannunta yace "tsoron ALLAHn kenan tunda ba wani waje naje nayi hakan ba, kuma mallakina ce ke ina da ikon yin duk abunda nake so da ke, saboda Allah ya bani damar in zo maki a duk lokacin da na so kuma inyi abunda naga dama"

Dije ta zaro ido tare da rufe baki alamun firgici tace, "har da irin wannan abun duka?"

Ya ɗaga mata kai tare da lumshe ido sannan ya buɗesu fes akanta yace, "har da shi har da ma kuma abunda yafi hakan ɗin duka"

Dije ta yi saurin ƙwace jikinta ta ce, "Ni dai WALLAHI Allah ban son irin wannan lalacewar, don wannan ma idan wani ya ji ai sai kasa ayi mani kallon ƴar'iska, haka fa wani a tasha ya so ya lalaceni ALLAH ya taimakeni asirinshi ya tonu"

Dirim! dum! dam! Haka ƙirjinshi ya buga ba shiri tare zuwan wani aringizon tashin hankalin da ya ziyartoshi, yanayin da ta ganshi yasa ta yi saurin shan jinin jikinta saboda tsoron kada ya kai mata duka, amman duk da hakan sai da ya damƙo gashinta iya ƙarfinshi yace

"Me kika aikata man bayan idona? Wanene shi? Wa ya baki izinin fitowa gida ba tare da izinana ba? WALLAHi kinji na rantse kika yarda wani abu ya faru WALLAHi dake ki sani bazan taɓa yafe maki ba"

Ya yi wurgi da ita har sai da kanta ya daku da gini ba shiri ta fasa wata uwar ƙara, amman ko takanta bai bi ba ya fice ɗakin fuuu ko da su Baffah suka fito sai jin ƙarar tashin Motarshi suka yi, cike da mamaki suke tambayarta me ya faru

Cikin kuka take sanar da su cewa

"Wai fa daga na faɗa masa abunda wani ɗan iska yaso ya yi mani a cikin tasha shine fa ya jawo mani gashi iya ƙarfinshi har sai da na bugu da gini, ya yi fushi ya tafiyarshi gashi ko abincin ma bai tsaya ya ci ba"

Baffah da Inna da shi kanshi Usmanu suka ƙumshe dariyarsu, saboda kai tsaye sun gano cewa kishinta ne ya janyo yayi abunda yayi, Inna ta fara yi mata faɗan rashin dalili tace

"Ai in dai baki bar baƙin surutunki ba to sai ya janyo maki watarana ya yi maki ɗan karen duka, ai gara da ya yi maki hakan sai gobe ki ƙara tunda ke bakinki sam baya da sirri kwata kwata"

Dije ta yi fuuu ta wuce ɗakin Innar tana kuka saboda takaicin tafiyar da ya yi bai ci abincin ba, Usmanu ya yi sashenshi yana dariya a ranshi yace

"Wannan yarinya ko yaushe zata yi hankali Oho?"

Baffah da Inna Kam tsakar gida suka yada zango suna ta firar Dijen da shi Safwan ɗin, zuciyar inna cike da jin daɗin ganin Safwan ɗin yana mugun son Dijen tasu, saboda abunda ya yi yasa dukansu sun gano cewa ba ƙaramin so yake yi mata ba, haka ma yasan darajarta zai riƙeta amana ya bata kulawar da kowace mace take buƙata a wurin mijinta.

Hankalinsu a kwance suka kwana saɓanin ita Dijen da ta kwana tana juye juye saboda haushinshi da take ji, uwa uba kuma ɓacin ran da ya nuna ba ƙaramin tsaya masa a rai ya yi ba, har sai da Inna ta tashi zaune tare da yadata da fitila ta kira sunanta, Dije ta yi saurin share hawayenta ta amsa tana sharɓar kukanta, cikin tausayinta Inna tace

"Tashi ki zauna magana zamu yi"

Dije ta yunƙura ta tashi tana ci gaba da goge hawayenta da hularta da ke hannunta, Inna tace

"Ki natsu da kyau ki saurareni Dije, saboda ina son ki fahimci halin Mijinki ku daina samun saɓani da shi,Mijinki ba wai sonki ne baya yi ba halinshi ne hakan saboda ALLAH ya yoshi mutum mai zafi,ki yi ƙoƙari ki karanceshi ki kiyayi abunda kika san zai ɓata masa rai, haka ma ki so abunda kika fahimci yana so ko da ko ke bakya son abun a ranki, kuma ki sani Mijinki yana da ikon taɓa ko'ina na jikinki ba tare da ya yi laifi ba, asali ma har lada ALLAH zai bashi idan yayi abunda kike ganin kamar bai dace ba, ki tallafi kanki da Mijinki Dije ko da ko bayan bamu duniya ki yi ƙoƙari ki samarwa kanki wata daraja mau girma a wurinshi, yanda ko da ya auro wata ba zata fiki da komi a wurinshi ba, don WALLAHi wannan mijin naki da kike gani to kowace mace tana fatar ace ta samu irinshi, amman ke gaki ALLAH ya baki kyauta kina so ki yi wasa damarki"

Dije ta share hawayenta tace, "Inna me yasa kullum baki ganin laifinshi sai nawa? Ko don ban sanar da ke cewa yanzu haka aure zai yi ba da wata abokiyar karatunshi"

Inna ta zaro ido waje
Tace. " aure??"

Dije tace "Aure inna kuma har kashedi yayi mani akan idan na sanar da ita cewa Ni Matarshi ce sai ya yi man mugunta, kuma baki ganta ba ƴargayu da ita harda mota take tuƙawa"

Inna ta yi shiru tana nazari sannan ta ce, "to ke ina ruwanki da motarta tunda dai dake da ita duk ɗaya kuke a wurinshi,don har ma kin fita saboda ke yanzu Matarshi ce ita kuwa budurwarshi ai ko a hakan ma ke matsayinki yafi nata nesa ba kusa ba, saboda haka ki yi ƙoƙari ki danƙe Mijinki a hannu ko da zata shigo daga baya to ke kin riga da kin fita matsayi a wurinshi, saboda haka ki ajiye shirme Dije ki kama Mijinki WALLAHi tun kafin wata mace ta yi maki sakiyar da babu ruwa akanshi, don haka ki bi abunki sau da ƙafa duk abunda yace ki yi idan yace ki bari ki bari sai ki ga a hankali ma ya daina wannan zafin kan da yake yi"

Dije ta yi shiru tana nazari sannan tace, "to ai Ni Inna bama zama yake yi ba ai saboda yanzu haka da an ƙare bikin Surayya zai tafiyarshi to wace biyayya zan yi masa bayan bamu ma tare?"

Inna tace "ko bangon duniya ya je ai dai Mijinki ne ko? Kuma kuma zai dawo kuma zaki yi masa biyayya ko bayan idonshi, saboda haka ki yi ƙoƙari kafin ya koma ya ji daɗin ɗan zaman da zai yi da ke, saboda ko da ya tafi ki barshi da kewarki a zuciyarshi yanda kullum zai yi ta fatar yayi sauri ya kammala karatun nashi ya dawo wajenki, amman idan kika yi sake har ya yi auren baki canza wannan halin naki ba to idan ya je mantawa ma zai yi dake ya yi ta Amaryarshi, ya barki sake da baki anan kina lissafin lokacin dawowarshi, wataƙila ma idan ya ji daɗi sai dai kiji ya ƙara wasu shekaru yace ba yanzu zai dawo ba"

Dije ta yi shiru sannan ta ce "to yanzu idan nayi masa duk abunda yake son zai fasa auren ko kuwa??? "

Inna ta yi saurin faɗin

"Ina ruwanki da aurenshi ya auri matan duniya ma idan zai iya kedai ki bi hanyoyin da duk na sanar da ke ki samu ki samo kanshi, da kinyi haka shikenan kin gama da matsalar wasu mata cen, don shi da kanshi zai bayyanawa matan matsayin da kike da shi a wurinshi, kuma dole ma suma su shiga taitayinsu idan har suna son zaman lafiya tare da shi"

Dije tace "aiko inna sai na ba ki mamaki don kuwa bazan taɓa bari wani ya sake jin tsakanina da shi ba, in dai har hakan shi zai kankaro mani darajata a wurin ƴanmatanshi"

Inna tace "yawwa Dijeta ki gwada hakan da na sanar da ke ke da kanki zaki gano irin nasarar da za'a yi"

Haka Inna ta yi ta ɗorata a hanya har taga Dijen ta fara gyangyaɗi sannan tace su kwanta sai da safe a ci gaba, Dije ta baje tana ta sharar baccinta mai cike da mafalkai iri iri na Safwan da budurwarshi Zee.

Ko da safiya ta waye tun asuba Inna ta ci gaba da bata wasu darussan, Dije kam ta naɗe komi cikin ƙwaƙwalwarta har ALLAH Allah take yi ta fara aiwatar da su idan sun koma cen, fatanta kawai Safwan ɗin ya nunawa Zee irin yanda take da matsayi a wurinshi.





Hhhhhh wasar zata fara kenan😅








Akafta🤪






D/AUTA CE

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*ALHMDLLH MUTANEN ƘARANGIYA BA ABUN DA ZAN CE DA KU SAI GODIYA, SABODA KUN NUNAWA LITTAFIN ƘAUNA FIYE DA YANDA NAYI TUNANI, TSAKANINA DA KU SAI SAMBARKA DA SON SO IRIN NA FISABILILLAH😍 ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU*



*Lamba ta 52*


Ko kafin Safwan ɗin ya zo tuni Dije ta yi wankanta tsaf ta shirya, cikin zuciyarta cike take da ɗokin zuwan na shi saboda ta bashi haƙuri akan abunda ta yi masa, duk da kuma wani sashen na zuciyarta cike yake da jin nauyin haɗuwarta da Hajiya Mama, saboda yanda ta kamo hanya abinta ba tare da ta yi sallama da ita ba, bayan ta gama kammala duk abunda zata yi ne tace da Inna tana so ta je ta yi sallama da Inna Gambo, Inna tace ba inda zata je har sai Mijinta ya zo, ta ɓata fuska tace

"Inna fa sauri zan yi inje in dawo don kada ya zo yace sauri yake yi ba zai bari inje ba"

Inna tace "sai ki lallasheshi ai tunda kina son ya barkin"

Suna cikin wannan diramar ne suka jiyo ihun yara da saukar mota a ƙofar gidan, Dije ta diririce tace

"Kinji ko Inna gashi nan ma har ya zo ban tafi ba"

Inna ta maka mata wata uwar harara ta ce, "da kin je ai da zai ɗaukemu mutanen banza in ya zo bai taradda ke ba.."

Sallamar Usmanu da shi Safwan ɗin ne ya katse maganar Inna ta yi saurin faɗawa ɗaki ta sako hijabi ta fito

Please Login or Register in order to submit comment