Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai Kuma aka ce maka itace mai yin abun? WALLAHI Usman ahir dinka ka kiyayi janyowa kanka abunda zai hanaka bacci mai dad'i"

Usman ya nufi hanyar fita yana fad'in,. "Duk buge bugen iskancin da tayi ta hana mutane bacci baka gani ba sai ma Ni laifina aka gani"

Cikin d'aga murya Baffah yace,. "Tunda ifrituwa ce ai dole ta fito cikin dare tana Wasa, WALLAHI in banda muke dare da yanzu sai na rama mata dukan da ka yi mata na d'aukar alhaki"

Ya dubi Dije cikin d'aure fuska yace,. "Me ya kaiki fitowa cikin daren nan kina buge buge?"

Dije ta fara matsar kwallah tace,. "Ba fa inda naje ina tsaka da baccina mai dad'i na ji saukar duka"

Baffah ya janyo hannunta ya zaunar da ita akan Gadon Innar yace,. "Kwanta kiyi baccinki ki barni dashi da safe zamu gauraya"

Dije ta share hawayenta da gefen dankwalinta ta lallaba ta kwanta, sai ajiyar zuciyar take yi cikin tausayinta Baffah yace

"Barni da shi da safe sai ya yi man bayanin dalilin da yasashi dukanki cikin dare, amman ke tsakaninki da ALLAH Dije ba ke bace? har da muryarki fa na jiyo kina rangad'a waka mai dad'i"

Dije ta Sha jinin jikinta tace,. "Nima na jiyo ana wakar Baffah amman wata murya daban ce na jiyo Ni, sai dai ban gano me ake cewa cikin wakar ba"

Baffah ya kalli k'ofar d'akin ya hadiyi miyon tsoron da ya sake diro masa yace,. "To dai yanzu ki yi addu'a ki koma kiyi baccinki kinji?"

Dije ta d'aga masa Kai ya fara tofeta da addu'o'i sannan ya zo zai fita ya juyo yace,. "Tashi ki rufe d'akin kada ya zo ya sake dukanki a banza"

Dije ta tashi zauna tana sharar kwallah tace,. "WALLAHI Baffah tsoro nike ji in kwana ni kad'ai sai inji anata kiran sunana wai in zo mu tafi bakin teku muyi wasa"

Baffah ya dawo da sauri jikinshi ya d'auki rawa yace,. "Ku tafi Ina?"

Ta turo baki tace,. "Wai bakin teku"

Baffah ya fara fad'in,

"K'alu Innalilahi wa'Inna ilairraji'una teku? Lalle akwai gurmi a gaba muddin ba'a daina jangwalo fushin dan Sarkin ba, jirani bari in zo yanzun nan"

Ya fice da sauri har yana tuntube ya nufi dakinshi Inna da ta ji fad'an Baffan da muryar Usman ta lallaba ta fito karkashin gadon, tana so ta fita tana jin tsoro sai ko gashi Baffahn ya shigo d'akin ranshi a b'ace yace,. "To tashi kije cen ki kwanta tun kafin safiya ta waye ki shafa kiga an d'auketa an tafi da ita, tunda ke Kika janyo komi to ki san hanyar da zaki gyara"

INNA ta zaro Ido tace,. "A d'auketa kamar ya?"

Kai tsaye Baffah yace,. "Kamar yanda kika saki kwanji kika lakad'a mata duka, haka su ma za suyi wuf da ita sama su je wasa da ita bakin teku, watak'ila ma shikenan ba zaki sake ganinta ba kinga sai ki sake haifo wata tunda ita kin janyo munyi asararta"

INNA ta mike jikinta yana rawa tace,. "Muje ka rakani in ganota Don Allah"

Baffah yayi kwanciyarshi yace,. "Ni da na je ke kika rakani ki je cen ku kwana da ita sai da safe ALLAH ya tashemu lafiya"

INNA ta dad'e tana kallonshi gano da gaske yake yi yasa ta ja kafafuwanta ta fice, tafe take tana addu'a har ta isa d'akin, sai dai ganin Dije da tayi a zaune tana sharar hawaye yasa ta k'arasa wurinta da sauri tace,. "Ke lafiya kike kuka?"

Dije wasu hawaye Suka zubo mata tace, "ba Yaya Usman ba ne ya zo yayi ta dukana bayan ban yi mashi komi ba"

Inna ta yi saurin zaunawa tace, "au! Shine yake dukanki kike ihu?"

Dije ta saka bayan hannu ta share hawayen da suke sauko mata tace,

"Shine"

Inna ta yi saurin fad'in "to me kika yi masa cikin daren nan?"

Dije ta zumburo Baki tace,. "Wai cewa yayi na fita inata buge buge bayan Ni tuwo kawai naci na dawo d'aki ina cikin Bacci naji yana dukana"

INNA ta zaro mata Ido tace

"Kin dai fitan ko?"

Dije ta gyad'a Kai, Inna ta maka mata wata jar harara tace,. "Aiko naji dad'in da ya jibgeki don dama ace bai dake kin ba to da Ni yanzu sai na yi maki nawa dukan, don ina da tabbacin kece kike ta daka kina dukan rufin madafinmu kina waka"

Dije ta yi saurin ja da baya tace,. "Nasha aradu ba Ni bace nima Ina Bacci naji ana ta yi"

INNA ta saka hannu ta dungure mata Kai tace,. "Zaki yi man shiru ko sai na kasheki da mari yanzu?, Ai WALLAHI ba wasu aljanu kece kuma na sake jin kin sake kwata irin wannan rashin mutuncin cikin dare WALLAHI sai jikinki ya gaya maki, ki godewa ALLAH da har aljanun gasken basu kawo maki farmaki ba, don muddin Baki daina kokwayonsu ba WALLAHI wani ya shige jikinki kin boni don ko sai dai ki wayi safiya watarana aga kin mutu, saboda ganinsu za ki yi a gabanki sun fito da siffarsu, kuma kinji ana cewa duk wanda yaga aljanu Ido da Ido da siffarshi ta gaskiya to mutuwa zai yi, amman in har ke kin shirya zuwa Lahira yanzu to kici gaba da koyonsu in kin aza wasa ake"

Dije jikinta ya d'auki rawar tsoro ta makure gefe ta dunkule waje d'aya tana addua, Inna ta maka mata wata hararar ta rab'a gefenta ta yi kwanciyarta hankalinta a kwance don ta gano cewa duk iya shegen Dije ne ba wasu aljanu.



Akafta🤾🏻‍♂️






D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*BAK'ON YANAYI BOOK NE MAI ZAFI HAR KUNA YAKE YI A HANNU SABODA TSABAR TSANANIN ZAK'INSHI BOOK D'IN BAK'ON YANAYI SALONSHI DABAN NE DA KOWANE BOOK DA KA TAB'A KARANTAWA A DUNIYAR LITTAFAI, ZAKU SAMESHI A ARHA DA FARASHIN NERA D'ARI UKU KACAL KUMA ZAKU SAMESHI A COMPLETE DINSHI CIKAKKE MAI B'UKATA TA NEMENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 SAYEN NA GARI MAYAR DA KUD'I GIDA SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI👍🏻 DOMIN KUWA BAK'ON YANAYI DAUKE YAKE DA NASHI KALAR SALO KALA KALA KUMA MABANBANTA MASU BURGE MAI KARATU DA SAKASHI SHIGA CIKIN SHAUKI YAYIN KARANTAWA💃🏻*


*Lamba ta 7*



Aiko Dije har safe ko motsin kirki bata sake yi ba saboda ta tsorata da jan kunnen da Inna ta yi mata, don hasali ma har mafalki ta yi wai gasunan sun bayyana da siffarsu sun zo wurinta zasu kasheta, cikin firgici ta falka a zabure tana fad'in

"Don ALLAH kuyi hakuri bazan sake ba na tuba nabi ALLAH da manzonshi, amman in har kunga na sake to ku d'auki mataki"

Inna da ke shigowa d'akin ta d'auro arwallar sallahr Asuba da nufin ta tada ita sai gashi ta taradda ita zaune tsakiyar gado tana sambatu, Inna ta kalleta da kyau tace

"Lafiyarki tun da safe kike yiwa mutane soki burutsun zance?"

Dije ta waiga gefe da gefenta sannan ta fara saukowa gadon tace,. 'ba komi"

INNA ta bita da kallo har ta fice d'akin ta girgiza kai sannan ta shimfida wata sabuwar tabarmar kaba da suke sallah akai ta tada sallahrta.

Dije kam har ta k'are arwallar ta dawo d'akin tunanin mafalkin take yi, jikinta a sanyaye ta yi sallah ta gayar da Inna sannan ta fara bitar karatunta na allo, Inna cikin jin dad'in ganin sauyin Dije ta bita da addu'ar ALLAH yasa abun ya dore a haka, don dai ita jikinta yana bata ko dai da gaske Dijen akwai wasu k'wank'wammai akanta masu sakata jidali da yawan fad'ace fad'ace kullum?, Ta fice zuciyarta cike da jin dad'i ta yi madafi domin ta d'ind'ima masu tuwon da zasu karyawa dashi.

Dije Kam tana k'are bitar karatunta ta jingine allonta ta nufi d'akin Baffah domin ta yi mashi Ina kwana, aiko sai gashi sunyi kicib'is da Usman ta ja baya ya shige d'akin sannan ta bi bayanshi da harara ta shige d'akin itama, Baffah yana kishingide da carbi a hannunshi yana ja yana gyangyadi, jin sallamar Usman yasa ya yi saurin tashi zaune yana amsa masa sallamar fuska a d'aure, ganin Dije a bayanshi yasa ya saki fuskarshi da fara'a tana shirin zama nesa dashi yayi saurin fad'in,. "Matso nan kusa da ni Dijengalata ya jikin naki?"

Dije ta zunburo Baki tace,. "Naji sauk'i sai dai dukan da Yaya Usman yayi mani ashe duk ya farfasa man jikina kallo ka gani Baffah"

Ta k'are maganar tare da zubowar wasu kwallah tana nuna masa tsintsiyar hannunta inda shatin bulalar ya fito rad'am.

Baffah ranshi ya K'ara b'aci cikin d'aure fuska yace da Usman da ke k'ok'arin gayar dashi yace,. "Ajiye gaisuwarka bana so tunda har baka ji kunyar saka bulala ka yiwa Dije irin wannan dukan ba, don tsabar rashin imani Innarku ta daketa da dare ace wai kaima ka bita tsakar dare da dukan kawo wuk'a, to bari kaji muddin ka sake yi mata irin wannan dukan WALLAHI sai na sab'a maka, don nafi son Ni in illataka da hannuna da dai ace Yariman Aljanu ya kawo maka farmaki, don ko Hasiya ALLAH ne ya tsareta da yau bata tashi da idanuwanta ba, duk kuma akan dukan da tayiwa Dijen, Kai ma ka kiyayi kanka da tsokano fushin d'an Gidan mai martaba"

Usman yayi saurin toshe dariyarshi yace,. "WALLAHI Baffah k'arya take yi ba wasu aljanu don da idona na ganta jiya tana rera waka tana dukan rufin madafinmu"

Baffah ya galla masa wata jar harara yace,. "To ka godewa ALLAH da har siffarta ka gani a jiki ba siffarsu ba, to bari kaji Kai kanka zasu iya yin siffarka suje inda suke so bale ta Dijen"

Usman ya yunkura zai tashi yace,. "Ni zan tafi gona Baffah kafin ka shigo" Saboda ganin da yayi idan ya tsaya musu ne zasu ci gaba da yi da shi don gano da Baffah Kam yayi amanna da karyar aljanun Dije.

Baffah ya ce "ba zaka bari ka ci tuwo ba?"

Usman zai yi magana Inna ta shigo da kwanon abincin Baffah ta ajiye, ta kalli Dije dake rakub'e kusa da Baffah'n tace,. "Tashi ki d'auki abincin yayanki ki kai masa dakinshi, kema ki d'auki naki kici ki tafi Makaranta"

Dije ta yunkura ta tashi ranta a bace tana fitowa ta bi hanyar d'akin Usman da kallo ta yi kwafa, saboda d'akin ya nufa ya shige abunshi ko waigota bai yi ba, ta nufi madafin ta bud'a kwanon abincinshi da kullum dashi ake zuba masa abinci ciki, ta bud'a langar ta damko gishiri cike da hannunta ta nutse dashi cikin miyar, ta maida murfin ta rufe ta d'auko tana tafe tana had'e fuska har ta kai dakinshi ta yi sallama ciki ciki ta ajiye kwanon bakin k'ofar shiga d'akin zata wuce, ya yi saurin fad'in

"Ki kawoshi nan a gabana ki ajiye"

Ta fisgi kwanon ta je gabanshi ta ajiye tana wani cin magani har ta zo fita yace,. "Ki kawo man ruwan sha to"

Dije ta fice ko waigoshi bata yi ba sai ko gata da ruwa cike da kofi kamar arzik'i ta ajiye cikin ladabi sannan ta fita da sauri jikinta yana rawa ta nufi wurin Baffah da ke cin tuwonshi har lokacin, ta wani marairecewa tace

"Don Allah Baffah ka rantsewa Yaya Usman akan kada ya sake dukana, don yanzu haka hararata kawai yake yi nasan k'iris yake jira ya kamani yayi ta jibga kamar jaka"

"Baffah yace kyaleshi je kici abincinki ki tafi Makaranta kar kiyi latti yaran da kike karantarwa su yi ta jira"

Dije tuno irin cin zalin d'in da take yiwa yaran makatantar yasa ta kyalkyale da dariya tace,. "Bari in d'auko tuwon nan inci Baffah a gabanka"

Ta nufi madafin da saurinta don tsoron Usman ya cafketa aiko fitowarta ke da wuya taji ya shako wuyanta, Aiko ta fasa k'ara tare da kiran sunan Baffah akan ya kawo mata agaji, sai ko gashi ya fito Usman yana d'aga hannu da nufin ya saukeshi a fuskarta Baffah ya rik'e hannunshi cikin fushi Yace

"Wai kai shikenan ita bazaka barta ta sakata ta wala ba cikin gidan nan? To WALLAHI wannan karon ko kallon banza naga ka sake yi mata sai na rama mata"

Ya fisge hannun Dije daga rikon da Usman yayi mata suka shige dakinshi, Usman ranshi a b'ace ya kalli Inna yace

"Gishiri fa ta saka man a tuwon da kikace ta kai mani, ruwa ma da nace ta debo man duk sai da ta zuba gishirin ciki ina kurbawa ba shiri na furzar saboda bala'in zartsinsu, amman Kinga Baffah laifina ya gani to WALLAHI idan ta cikani sai na karyata cikin Gidan nan"

Baffah ya lek'o kanshi Usman yana gaf da fita yace, "Wanda ya fasa karyata ban gode masa ba, Kai ko ka zuba ido ka ga irin kalar hukuncin da zan dauka kanka"

INNA dai ranta a b'ace tace ,. "Haba Malam ka dubi abun nan fa da idon basira, gishiri fa ta zabga masa a abinci da ruwan sha ina ko Dije taga gaskiya anan?"

Baffah ya yi mata wani kallo yace,. "Anji bata da gaskiyar ku had'u ke da shi ku kasheta"

INNA tace,. "ALLAH ya baka hak'uri ni dai fadar gaskiya ce tawa"

Baffah cikin d'aga murya yace,. "To ba'a so ki rik'e gaskiyarki ku bar Yarinya ta sarara"

Dije dai sai guma lomomin tuwonta take yi tana kammalawa ta wanke hannunta ta ja allonta ta fice, tana tafe tana wakarta har ta kusa kaiwa Makarantar ta hango Hansai da itama tun daga nesa da ta hangota tafe ta k'ara d'aga kafafuwanta da sauri don bata son Dije ta cimmata, aiko Dijen tana hangota ta kwalla mata kira ganin taki tsayawa yasa ta d'aga murya tace,. "WALLAHI in baki tsaya ba na kamaki sai na canza maki kamannu"

Hansai ta tsaya jikinta yana rawa tace,. "Aikena aka yi akace in yi sauri in dawo"

Dije ta k'araso hannunta rik'e da k'ugu tana yiwa Hansai wani kallo tace, "Aikenki aka yi Kuma na ganki da Allo?"

Hansai ta Kai kallonta ga allon cikin rawar Baki tace,. "Allon zan ajiye sai in tafi aiken"

Dije ta dungure mata Kai tace,. "Ke dai kinji haushi WALLAHI bak'ar makaryaciya, na ganoki ai don kinsan kin tonani ne shiyasa kike tsoron mu had'u, amman kinsan kina tsorona Ubanwa yace kije ki sanarwa Maigari Wai k'arya nake yi ba wata Kura?"

Hansai ta zaro Ido tace,. "Ni d'in WALLAHI Ni k'arya ake yi man bani na fad'a ba"

Dije ta ajiye allonta ta rik'e k'ugu tace,. "To wa ya fad'a??"

Hansai hawayen da take makalewa suka zubo tace,. "WALLAHI in har nice na fad'a ALLAH kada ya dagar dani anan wurin"

Dije ganin hawaye ga fuskar Hansai yasa ta d'auki allonta ta lakamo kafad'ar Hansai din tace,. "To Zo muje na yafe maki amman don ALLAH ke baki san wacce ta fad'a ba cikinmu?"

Hansai ta share hawayenta cikin jin dad'in yafe matan da Dije tayi tace,. "WALLAHI bansani ba nikam Dije"

Dije tace,. "To yi shiru shikenan zaki zo Wasa Gidanmu ai anjima ko?"

Tace,. "Eh in Innata ta barni"

Dije tace,. "Zata ma barki ki zo nayi maki d'iyar kare mai shegen kyau"

Tace,. "To"

Sannan suka rankaya har cikin Makarantar inda Suka taradda ta cika fam! Sai karatu ake tayi, Dije taje ta bita karatunta ga Babban malaminsu, sannan ta d'auki bulalarta ta fara koyawa yara karatu, aiko suna ganinta kowa yasha jinin jikinshi sai d'aga murya suke yi suna ta karatu da k'arfin gaske, saboda sun san irin bala'in kashin da take basu wanda abu kad'an ne zai janyo yasa ta ci uban yaro, musamman wad'anda basu gane karatun su Kam ba k'aramar azaba take basu ba.

Don wani zubin ma Kan yaro take hayewa ta taushe masa kai tana muntsilarshi, wani zubin ma har cizo take had'awa mutum da shi in ta kama, don Iyayen yara da yawa sun Sha kawo kararta wurin Malamin musamman idan sunga shatin bulalar ko na muntsilar ko cizon da take yiwa 'ya'yansu, Malamin yana toshe kunnuwanshi ne kawai saboda bala'in k'ok'arin da take da shi gashi kuma yaran suna gane karatunta kuma tana natsar da Makaranta su daina rashin ji in tana wurin, sai dai yayi mata fad'a cikin hikima baya ma nuna mata wai k'ararta aka kawo don tsoron kada ta yi abunda zai fi wanda ta aikata .

Saboda ko baffanta ba'a kwana biyu ba'a Kai masa k'ararta ba akan ta daki wani ko taci zalin wani, iyakaci dai ya bada hak'uri idan ya shiga yayi ta nusar da ita akan ta rage tsaurara horon da take yiwa yaran.

Aiko bayan an tashi Makarantar ne suna tafe su biyar dinsu kamar kullum,har sai da suka kai wani lungu sannan Dije tace

"Yawwa daman Ina son in gano a cikinku wacece taje ta fad'i cewa Wai k'arya ce nake yi ba wata Kura??"

Kowa ya fara rantse rantsen ba shi bane Dije ta kalli Mune da kyau tace,. "Ke nasan duk cikinmu kinfi kowa bak'in surutun tsiya da fad'i ba'a tambayeki ba, don haka kece kika fad'a ai na ganoki yarinya"

Mune ta zaro Ido waje tana muzurai tace,. "WALLAHI Nima banso fad'a ba ai Babanmu naga garin gudu yaji ciyo a k'afa shine fa na fad'a masu gaskiya don su kwantar da hankalinsu"

Dije ta yi wani tsalle ta ciyo kwalar Mune tace,. "Yau ko za'a yi watandarki a bakin tekun zurmukus banbaradusa, ai daman nasan kece kika fad'a to kisani sai na yi kuli kulin rakkiya dake a garin nan yau"

Dije ta mik'awa Hansai allonta ta saki Mune tasha d'amara da gyalenta Mune tana ganin haka ta ce k'afa mi naci ban baki ba, aiko ta zunduma da gudunta Dije ta bita itama sauran kawayen nasu da wasu Yan kallo suka bisu a baya, sai ko gashi Mune taci karo da yayanta tayi saurin yin bayanshi ta b'oye, Dije tana kawowa ta yi tsalle ta dako Mune ta bayanshi, cikin fushi ya rik'e hannun Dijen yace

"Me tayi maki da zaki daketa?"

Dije ta fisge hannunta ta murgud'a masa baki tace,. "Ai Kaima kasan idan bata yi man komi ba haka kawai bazan biyota ba"

Yayan Mune ya kalleta cikin fushi yace,. "Waike me yasa kullum baki rabuwa da fad'a da anjaki da ba'a jaki ba ke duk sai kinyi?"

Dije ta hade fuska tana wani girgizar jiki tace,. "Ni dai ka matsa babu ruwanka kada Kuma in zo in yi maka wani abu aga laifina"

Yayan Munen ya rik'e Baki yace,. "Au ko Nima fasa man Kan zaki yi kamar yanda kika fasawa Bintalo goshi, don Kinga Maigari yace ayi maki hakuri a kyaleki shine kike ganin kamar tsoronki ake yi ko??, To bari kiji ni WALLAHI idan kika yarda kika shiga sabgata sai na lakad'a maki shegen duka a garin nan Inga mai d'aure maki gindi"

Dije ta ja baya da k'arfi ta ce. "He! he! he! daman shi abun dai ai shi abun fad'i yin kanshi yake yi don kuwa kanku aka farashi, ko ka manta duk garin nan kowa yasan cewa Iya Zulai barauniya c......."

Kafin ta k'arasa yayan Mune mai suna Tanbari ya Kai mata wani mahaukacin mari, Dije tace la.la.la. Ni ka mara?"

Cikin tsananin fushi yace,. "An mareki ke d'iyar Gidan Uban w.........."

Kafin ya k'arasa Dije ta duka cikin zafin nama ta debo k'asa ta watsa masa a cikin idanuwa, aiko tambari ya yi saurin kai mata wani uban naushi ta kauce da sauri.

Idonshi cike taf da k'asa ya fara Kaiwa iska naushi iya k'arfinshi yana fad'in,

"Yau sai na kassaraki na kamaki sai na kakkaryaki a garin nan"

Dije ma bakinta bai yi shiru ba sai ramawa take yi, Aiko yana fad'a Yana kaiwa iska naushi ta inda yake jiyo muryarta, har ya Kai wurin wani icce ya bugoshi da k'arfi sai gashi da fasa k'ara don kuwa kanshi yaci karo da iccen ya bugu da k'arfi ga hannunshi da ya naushi iccen, zafi biyu da biyu ya durk'ushe a k'asa yana murkususun wayyo hannunshi.





Akafta🤾🏻‍♂️🏃🏻‍♀️







D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻*


*Lamba ta 8*



Mune ganin yayanta yana kuwwa yasa ta sake zundumawa da gudu ta yi gida da nufin taje ta fadowa Innarsu, Dije kam karbar Allonta ta yi ta kalli su Hansai tace

"Ku muje in kuma anan zaku tsaya sai in tafiyata"

Yayan Mune sai tsine mata yake yi Dije ta waigo tace,. "Ni bani da lokacinka tunda ALLAH ya saka man akanka, saura kuma idan ka tashi fad'i kace nice na ji maka ciyon a hannu"

Yanata surfa mata zagi tana masa dariya taja kawayenta suka tafi suka barshi anan, kowa idan aka kai gidansu ya shige masu ratsewa su yi hanyar da zata sadasu gidajensu kuma su ratse su tafi, suka bar Dije ita kad'ai tana tafe tana Yar wakarta zuciyarta cike da jin dad'in abunda ta yiwa Tambari, aiko sai gashi ta had'u da Bala wanda tun daga nesa da ya hangota fuskarshi a washe ya k'araso idonshi akanta yace,.

"A'ah su Dije Makaranta aka fito ne??"

Ta Kai kallonta gareshi ta bata fuska tace,. "Eh cen na fito"

Tana maganar tana ci gaba da tafiya abunta, Bala ya biyota a baya yace,. "Dije ki tsaya akwai maganar da nike son muyi Ni da ke"

Dije ta waigo ta rik'e kugunta tana yi masa wani kallon reni tace,. "Magana kuma? Bayan wadda muke yi da Kai yanzu?"

Ya gyara tsayuwarshi yana fesheta da wani arnen murmushi yace,. "Wannan ta musamman ce ai don WALLAHI na dad'e da abun cikin Raina sai dai tsoro yasa na yi ta b'oye abuta a cikin zuciyata"

Dije tana yi masa kallon Ido cikin Ido tace,. "Toh kace abun babba ne Bala? ALLAH yasa dai ba cewa za'a yi nayi wani abun ba kuma?"

Bala ya yi saurin fad'in,. "Ba kiyi komi ba na aibi Dije illah ni da kika sakani shiga damuwa da zullumi kullum safiya"

Dije cikin k'ulle kai da rashin gano inda zantukan Bala Suka nufa tace,. "To ai sai ka fad'a Kai tsaye basai ka tsaya zagaye zagaye ba"

Bala ya kafeta da kallo cikin tsananin kaunarta da ta cika masa zuciya yace,. "WALLAHI Dije sonki dai Nikeyi tun da dad'ewa, ammman na kasa furta maki ina jin tsoro"

Dije ta yi saurin dafe k'irji tace,. "Yanzu Kai Bala duk mutuncin da nake ganinka dashi ashe daman cen dan iska ne Kai ban sani ba??"

Balan ya zaro Ido waje yace,. "Iskanci kamar yaya Dije don nace Ina sonki shine nayi iskancin??"

Dije ta maka masa wata jar harara tace,. "Yo in ba iskanci ba me ya kawo zancen kana Sona? Ko ka d'auka Ni Yar iska ce kamar kai to WALLAHI wurin Duduwa zan kaika in sanar da ita don ta ja maka kunne tun kafin ka janyo Baffahna ya kasheni a garin nan"

Aiko ta juya ta nufi gidansu Bala, Bala ya bita yana magiya akan kar ta Fado ta rufa masa asiri ba zai sake yi mata maganar ba, amman Dije ta Kai wuya shiyasa bata fasa nufar gidan ba cikin fushi kamar wata zakanya, aiko tana shiga ta fara kwallawa Duduwa kira waton Kakar Bala ta wajen Uba da bayan rasuwar Mahaifiyarshi ya dawo hannunta.

Sai ko ga Duduwa ta fito d'aki tana gyara daurin zanenta tace, "lafiya kike kirana? injin dai ba bashinki naci ba?"

Dije ta k'araso ta kantare k'ugu tana wani cije Baki tana murgudashi tace,. "Aiko dole ki ganni tunda har Bala yake so ya maidani Yar iska kamarshi"

Tsohuwa Duduwa ta zaro Ido waje tace, "ke dakata Dije ki fita idona in rufe kada ki kuskura ki yiwa Balana sharri"

Dije ta yi mata wani kallo ta waiga bayanta inda Balan yake shigowa Gidan tace,. "Ai gashinan ki tambayeshi in har zai fadi tsakaninshi da ALLAH me ya fad'a mani yanzu?"

Bala ya k'araso yana dariya yace,. "WALLAHI Duduwa ba fa wani Abu nace da ita mai girma ba, cewa kawai fa nayi da ita Ina sonta shine fa ta ce sai ta kawoni k'ara wurinki"

Duduwa ta kalli Dije ta yi wani mere tace,. "Ke daga ma kin samu yace yana sonki shine zaki biyoshi Gida da kullin sharrinki? To don yace yana sonki miye abun iskanci a ciki?"

Dije ta galla mata harara tace,. "Au yanzu na gano Ashe da had'in bakinki yake so ya lalatani, to WALLAHI sai dai yaje ya bidi Yar iska dai dai shi don ni ba Yar

Please Login or Register in order to submit comment