Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

yana ƙofar gidan Maigari yanzu a je a kirashi ai tunda......"

Maganar ta maƙale ne saboda ganin yara sunata shigowa da buhuhunan shinkafa tare da sauran kwalaye, Inna ta bi yaran da kallo riƙe da baki zuciyarta cike da tsantsar farin ciki, sai ga sallamar su Hajiya Mama da su surry, da sauri Inna ta juya tare da washe baki cikin rawar jiki ta nufi ɗaki ta ɗauko sabuwar tabarmar ta shimfiɗa masu a kofar ɗakinta da yake share fess! Da shi, tana tambayarsu ya hanya tare da yi masu barka da zuwa, cikin sauri ta je ta ɗebo masu ruwa ga tulunta mai shegen sanyi cikin babban kwanon sha sabo dal, tayi masu farau faraun fura ta miƙa masu sannan ta dinga taimakawa yaran da har lokacin basu daina shigowa da kayan tsarabarba.

Dije kam tana samu ta fice ta nufi ƙofar gidan Maigarin ƙawayenta su Lanti da Hansai da Mune suka biyota kowa yana ƙoƙarin ya dai samu ya riƙa hannunta, ita ko sai wasar baki takeyi tana faɗin

"Hansai da Lanti kuna nan ku har yanzu baku yi auren ba ashe? Ina Jummala ko anyi mata auren?"

Mune tayi caraf tace,

"Ko sati biyu ba'ayi ba da aurenta ai, sai dai kam ko jiya da naje na isketa sai kuka take yi, ke baki ma sani ba tun ranar da aka kaita ta gudo cikin dare ta dawo gida, wai ita bazata kwana da Garbati ba tunda ɗan'iska ne"

Dije ta yi saurin faɗin

"To faɗi ba'a tambayeki ba, wai ke Mune har yanzu baki daina gulmar taki ba?, To ke yaushe za'ayi maki auren ne?, Amman dai Ni dai WALLAHI ina baki shawara ki daina yawan gulma nan kada watarana ki janyowa kanki a lakaɗa maki shegen dukan tsiya"

Mune ta yi shiru zuciyarta a cunkushe tace, "Ai gaskiya ce na faɗa WALLAHI ki ma tambayi su Hansai ki ji in nayi ƙarya"

Dije tace "Ni dai fa bance kinyi ƙarya ba amman na ce ki rage yawan surutunki na tsiya da baƙar gulmarki da kika saba, don Ni dai WALLAHI banga laifin Jummala ba haka kawai a kaika wajen Namiji ace ku kwana ɗaki ɗaya, don kawai salon ya lalataka azo daga baya ana faɗin ka zama ɗan'iska"

Hansai ta ƙyalƙyale da dariya tace,. "Cafɗi Ni ma fa wai an kusa aurena da Usmanu, amman Ni dai yasin har na matsu ayi a ƙare saboda nasan shi Usmanu ba ɗan'iska bane, Jummala dai kam sai haƙuri tunda Garbatin ya riga da ya tanbaɗe sai neman shiriya"

Lanti kam da tunda ake ta surutun bata ce komi ba, cikin sanyin jiki ta sauke ajiyar zuciya tace

"Ni WALLAHI har ma tsoro auren yake bani musamman yanda Jummala take ta kuka duk dare sai ta gudo Gidansu ana maidata, ni na rasa me ma Garbatin yake yi mata da har take jin tsoronshi"

Cikin tsananin tsusayin Jummalar Dije tace
"wai ina Ladiyo ita dai ai suna zaman lafiyarsu ko?"

Mune ta yi saurin faɗin "cabɗi ai billahillazi ko jiya sai da na taraddasu suna ta kokawa Duduwa tana rabasu suka ƙi bari, Bala sai zagin Ladiyo yake yi wai sai ta biyashi kuɗinshi da ta sata"

Dije da suke tafiyar a hankali suna firar ba shiri ta ja ta tsaya, cikin sabon ɓacin rai ta ce

"Wai kunsan wani abu kuwa??"

Dukansu suka ce "A'a"

Ta dafa kafaɗar mune tace,. "Na dafeki da alkhairi yau halinki zai yi man rana ko da ko ban biya kwandala ba, karkaɗe kunnenki da kyau kiji Mune Bala dai ashe kuɗi Malaminmu ya bashi shiyasa ya janye zancen aurenmu da shi aka ɗaura da Malam Safwan, ashe daman cen ba son ALLAh da Manzonsa ya ke yi man ba, don haka ki je ki yi ta yamaɗiɗi da wannan zance Mune na baki kyauta, kar ki yi sanya ina son kafatanin wannan garin kowa ma ya san da wannan sirrin da Balan Duduwa ya rufe lokacin aurena dashi, ki bankaɗe komi ƙawata kinji? Tunda har shi ya zama baƙin zalamammen banza kwaɗayayye"

Ba Mune da Dijen ta ke baiwa labarin ba har su Lanti sai da suka jinjina irin abunda Bala ya aikata, Dije zata sake yin magana kenan ta hango Baffah'nta da yake ta sauri tun daga nesa Bakinshi a washe, wanda ko tantama babu akan cewa labarin zuwan Dijen ne ya kai gareshi, aiko aguje ta zanƙara da gudu ta nufeshi tana faɗin

"Wayyo Baffahna Oyoyo Oyoyo wallahi nayi missing ɗinka"

Tana zuwa ta faɗa jikinshi, shi ma cike da tsananin jin daɗin ganinta yace

"Baƙin birni sannunku da zuwa yanzu nake ji ashe ko da gaske Dijengalata ce ta zo ganina"

Ya riƙo hannunta suka nufi gidan sai tsalle take yi tana wasar baki tana murna, su Lanti suka bi su a baya Hansai kam ta doje ta yi gida saboda kunyar surukuta da take yi da Inna Hasiya.

Ko da suka shiga sun taradda Hajiya Mama da su Surry cikin ɗakin Inna sun gama SALLAH, Inna ko sai haɗa wuta take yi tana jefa masu ɗanwaken da ta gama kwaɓashi a gaggauce, don kawai ta sami abun tarbar baƙinsu da shi saboda ita dambun gero ne ta yi tana ganin idan ta basu ƙila ba za su iya ci ba.

Baffah ya isa ƙofar ɗakin cikin farin ciki yayi masu sallama, sai da suka amsa sannan ya shiga yana yi masu sannu da zuwa tare da tambayarsu ya hanya?.

Cikin mutunta juna suka gaggaisa sannan ya fito Dije ta biyoshi a baya tana faɗin

"Baffah banga yaya Usmanu ba"

Ya waigo zuciyarshi fess yace

"Tun da safe ya je birni cin kasuwa kinsan yanzu a cen yake kasa kayan koli yana sai dawa tun lokacin da muka dawo garin Mijinki"

Dije ta washe baki tace,. "ALLAH sarki yaya Usman ashe an kara sanin ciyon kai"

Inna da take dakan toshshi ta goge fuskarta da jiɓin da feso mata tace,.

"Saura k'iris ma ya rage ayi aurenshi kinga shikenan kun zama ɗaya ba zancen wani gori bale har nan gaba ki ɗauka cewa ke ce yayarshi tunda kina ganin kin rigashi aure"

Baffah ya maka mata harara yace, "ko yau aka yi auren ai dai na Dije ne aka fara yi, don haka a daina yi muna wani feleƙe tunda har mu mun riga da mun yi ɗin ai kuma mun wuce wurin"

Dije ta washe baki tace,. "Shiyasa kullum sai nayi mafalkinka Baffahna saboda duk garin nan kafi kowa sona"

Mama Hajiya da ke ɗaki tana ji yo su ta yi murmushinsu na manya zuciyarta cike da sha'awar ahalin sabida barkwancinsu da kusan rabi duk Dijen garesu ta gado, uwa uba ma sun burgeta saboda ganin yanda suke nagartattun ma'aurata masu son farantawa junansu cikin barkwanci.

Fiddo kam sai yatsine yatsine take yi tana ƙarewa ɗakin Inna kallo, Hajiya Mama tana yi tana yi mata kashedi da ido amman duk da haka sai ta fakaici idonta ta yi guntun tsaki.

Baffah ya koma waje inda aka shimfiɗawa Direban tabarma gindin wani iccen dake ƙofar gidan, yana shan iska, ya zauna suka sake gaisawa a tsanake.

Dije ta nufi wurin Inna ta karɓi taɓaryar tana daka toshshin su Lanti suka karɓe suna daka mata, suna ci gaba firarsu ta yaushe gamo.

Bayan Inna ta kammala ɗan'waken ta zubawa Hajiya Mama ga sabon kwanon Samira, su Surry ma kowace da sabon kwanonta haka ma Direban da suka zo da shi, Dije kam dambun geron ta ɗauko ta fara ci Surry ta ce ta zo su ci ta ji don k'amshin dambun sai kai mata yakeyi a hanci, duk da ko shi kanshi ɗan'waken ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba, aiko tana guma lomar dambun ta yi saurin faɗin


"Uh! uh! uhm!"

Sai data haɗye sannan ta ce "cabɗi ashe Khadijah da wayo kika so ki yi man wannan abu da daɗin gaske yake yasin"

Sai ci take yi abunta babu ƙyama cikinsu Dijen da Lanti da Mune da suka fara ci tare, Inna da su ko sai faman dariya suke yi mata da ma suka cenye Inna ta ƙaro masu sannan Baffah ya shigo da ledar ruwan sanyi har suraci suke yi, tare da lemuka irin na ƴan'birni da ya bada aka siyo masu babban garin da ke kusa da su.

Fiddo kam zurum ta yi tana kallon kwanon abincin ta kasa ci, Hajiya Mama da ke ɗakin Inna tana cin abincinta hankalin kwance, ta kalleta tace

"Ke ba zaki ci abincin ba ne??

Fiddo ta turo baki ta ce

"Gaskiya Ni bazan iya cinshi ba ku dai ku ci idan mun fita wannan ƙauyen sai a siyo man wani abu sai in ci"

Hajiya Mama ta wulla mata wata ƙatuwar harara ta ce

"WALLAHI muddin baki ci ba to har mu koma gida bazaki ci komi ba"

Fiddo cikin tsananin ɓacin rai ta ɗauki cokali ta ɗauko ɗan'waken cikin ƙyama ta kai bakinta, sai gashi yayi mata bazata don kuwa wani daɗi ne ya ziyarci halshenta, ta haɗiye ta ƙara kai wata loma Hajiya Mama tana kallonta ta gefen ido, aiko kafin ka ce me har ta kusa tayar da kwanon ɗan'waken, don kuwa har da su cire ɗankwali tana ƴar waƙa tana rawa da kai.





Ni dai kar ki cenye ki raga man fiddo☹️



Kuyi hkr dani kwana biyu na shiga rububi ne😆





Akafta🧐






D/AUTA CE✍🏻


*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Soyayya da tasiri in har an saka tarbiyya,idan zaka yo komi farko ka fara yin niyya, duk mai ƙinka in ya biyo hanyarka za ya sha kunya, fasahar gwani matsayi nai ya fi inda zai zauna, hanci kan ji ƙamshi baki sa ƙashi ka ɗan tauna, ido kan ga haske linzami kace da ni suna ahaaa😉*



*Lamba ta 37*


Kafin ka ce me sai ga fiddo ta tada kwanon ɗan'waken tare da ɓalle murfin lemun da Baffah ya siyo masu, ta kafa kai ta kwankwaɗe tass ta jefar da gorar ta buga wata uwar gyatsa tare da shafa cikinta ta kalli Hajiya Mama da itama ɗin ita take kallo tana yi mata dariya, Fiddo ta wayancewa da faɗin

"WALLAHI ashe dai naji yunwa sosai Hajiyarmu"

Hajiya ta yi mata wani mere tace, "Naga alama kam tunda gashi har kin tada kwanon ɗan'waken duka, bayan ko daɗinshi ma baki ji ba"

Fiddo ta yi saurin ƙyalƙyalewa da dariya tace,. "yunwa ce naji ai"

Hajiya Mama tana dariya tace "Ga wani ki ƙara ko da ALLAH zai sa ki ji yunwar ta yi nesa da ke"

Fiddo ta yi saurin faɗin,. "A'a naƙoshi fa amman da ace wannan yarinyar zata iya irinshi idan mun koma gida ai da sai ta dinga yi man kawai"

Hajiya Mama ta yi saurin ɓata fuska tace,. "Eh kam tunda zamanki take yi me zai hana ta yi maki WALLAHI ki kiyayeni tun kafin ki janyo in barki garin nan tare da Khadijah har sai kinyi sati biyun da zata yi, kinga shikenan sai ki tayata ganin gidan"

Fiddo ta zaro ido waje tace,. ,"Don ALLAH kiyi haƙuri WALLAHI na daina"

Suna cikin firar ne Surry da Dije da su Lanti suka shigo Dije ta gabatar da su ga Hajiya Mama, cike da jin daɗi take amsa gaisuwarsu saboda ganin yanda suka durƙusa har ƙasa suna gaidata cikin ladabi cikin farin ciki ta yi masu kyautar kuɗi sunata godiya cike da murna.

Bayan komi ya lafa ne aka sake sabuwar gaisawa tsakanin Hajiya Mama da su Inna Hasiya, inda take sanar da su Safwan baya ƙasar ya je ƙaro karatu na tsawon shekara uku, amman ta sanar da su Dijen zata ci gaba da zama a hannunta har ALLAH ya dawo da shi lafiya, sannan ta sanar da su zancen makarantar da Dijen take yi, cikin jin daɗi su Baffahn suka yi masa fatar dawowa lafiya, tare da yiwa Hajiya Mama godiya da irin kayan arzukkan da ta cikasu da su, tsakanin kayan abinci da kayan masarufi, sannan ta kawo jimillar kuɗi har dubu ashirin ta basu tace su yi cefane, Baffah da Inna saboda tsabar jin daɗi har kukan murna suka yi sai zuba godiya suke yi.

Dije ta ja Surry suka yi gidan Inna Gambo domin su gayar da ita, suna cen ne su Hajiya Mama suka taraddasu aka sake aza sabuwar gaisuwa da Inna Gambon inda take ta yi wa Dije sharrin ta je birni tasha jar miya ta fara manyan kumatu, Hajiya Mama ta saki jiki ta dinga kare Dijen cike da barkwancin suka baro gidan bayan ta cikata da kyautar bajinta, sannan suka dawo gidansu Dije inda suka taradda Maigari ya aiko masu da kwano fam da naman kajin hausa da yasa aka yi masu dafuwar ruwa sun dafu lunguɓus sai ƙamshin daddawa da kayan yaji ke tashi, aiko cike da zumuɗi Surry ta fara ɗanɗanawa tana rawar kai ta zuzzuba masu har da Direbansu sannan ta ɗauki sauran ta kaiwa Inna Hasiya tace suma su ci, Inna cike da jin nauyi ta nuna mata ai ba komi su na gida ne su ci abunsu kawai, amman duk da haka atafau ta ce dole suma sai sun ci tunda suma ɗin ai ba baƙi bane.

Haka suka yi ta harƙallarsu cikin mutunta juna har zuwa marece, sannan suka shirya tsaf da nufin tafiya sai ga Usmanu ya dawo kan Babur ɗinshi da Baffah ya siya masa don zirga zirgar kasuwancinshi da ya fara cikin babban birnin, cike da jin daɗin ganinsu ya gayar da su a mutunce Dije sai farin ciki takeyi saboda ganin ɗan'uwanta.

Sun kimtsa tsaf da nufin tafiya saboda akwai inda zasu je su kwana da safe su kama hanyarsu ta zuwa Yola direct, sannan aka yi masu rakiya har gidan Maigarin suka je suka kai masa gaisuwa tare da godiya akan ɗawainiyar da aka yi da su, Mama Hajiya ta yi masa alkhairi tare da matanshi sannan ta fito aka rakosu har bakin motarsu ana yi masu ALLAH ya kiyaye.

Dijen ma sai wasar baki take yi tana yi masu bye bye sai dai suna haɗa ido da Fiddo ta galla mata ƙatuwar harara tare da murguɗa mata baki, Fiddo ta taɓe baki tare da yi mata wani mere tana yatsinar fuska, Hajiya Mama kam haka suka rabu cikin aminci tare da kewar juna, zuciyar Hajiyar fes saboda jin daɗin karamcin da aka yi masu, uwa uba sauƙin kan da Baffah'n Dije ya nuna akan rashin zaman Safwan gida tare da 'yarsu.

Bayan sun tafi ne Dije da su Baffah suka koma cikin gidan zuciyarsu cike da girmama irin mutuncinsu Safwan, Baffah sai jinjina lamarin Ubangiji yake yi tare godiya gareshi akan haɗasu da yayi da surkai nagari, waɗanda suka san mutunci tare da girmama ɗan'adam k ko da ko sun san cewa sun fisu nesa ba kusa.




Sauka lafiya su Hajiya Mama😆



Not edited😓




Akafta 😉







D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Alhmdllh Alhmdllh lalle dole ne in fara godiya ga Ubangiji kafin in ce komi, saboda jin daɗin yanda kuka nuna man ƙauna ta zahiri tare da ɗinbin karamcinku gareni ni D/AUTA, ku sani naji matuƙar daɗin ganin irin ruwan addu'o'inku gareni masu ɗauke da fatan alkhairi iri-iri, haƙiƙa duk wanda ALLAH ya baiwa masoya ya ji daɗi a rayuwarshi ta duniya, kamar yanda ni ma a yanzu naji mugun daɗi marar misaltuwa akan zallar ƙaunar da kuka nuna mani tare da littafina na DIJE ƘARANGIYA, naji daɗi na gode sosai wallahi ALLAH ya bar zumuncinmu da ku har aljannah, ni ma ina sonku all my FAN'S son so fisabilillah💋*



*Lamba ta 38*


Baffah saboda tsabar farin ciki nan take ya ce da inna, "idan ALLAH ya kaimu gobe ki ɗibi gero ki yi wainar sadaka a raba ko don mu nunawa Allah jin daɗin baiwar da ya yi muna, don WALLAHI sai yanzu nake jin nauyin abunda na aikata lokacin da na ke son hanawa Dije auren Malaminsu, musamman wancen yaron da shine tun farko ya fara yi wa Dije so na tsakani da ALLAH, ashe alkhairin nata wajensu yake ina ta ƙoƙarin hanata kaiwa wajenshi, Dije ki ci gaba da yi wa mutanen nan biyayya don ALLAH saboda ba ƙaramin mutunci ne da su ba, don ko a cikin masu kuɗin su nasu mutuncin daban ne, yanzu ki duba ki ga yanda suka saki jiki da mu tamkar cewa daman cen mun saba da su, Wallahi Ni dai kai bakina ba zai gaji da zunduma masu addu'ar fatan alkhairi tare da gamawa lafiya ba.

Dije tana wasa da gefen gyalenta tana ta wasar bakin jin daɗin yabonsu da yake yi, sai ko SAFWAN ya faɗo mata a rai ta saurin ɓata fuska tace

"To ai kai Baffah ita da surry ne masu mutuncin amman shi kanshi malamin namu fa ba halin kirki ne da shi ba, tare da wannan ƙanwar ta shi ƙarama WALLAHI in banda na ke tuna cewa kace kada in biyeta da tuni na aikata mata mara daɗi, don fa kusan kullum da sai ta tsokaneni da faɗa"

Baffah ya yi murmushinsu na manya ya ce,. "Ai shiyasa nake ta saka maki albarka saboda kawai biyayyar da kike mani ko da baki ganina kusa da ke, amman kada ki in sake jin kin faɗi cewa Mijinki ba shi da kirki tunda har ya nunawa duniya matsayinki ya aureki ai ya gama maki komi Dije"

Dije ta ɓata fuska tace

"Wallahi fa ba sona yake yi ba Baffah har kuɗi fa ya baiwa Balan Duduwa ya toshe masa baki akan ya bar masa ni, to mai sonka ne zai yi maka irin wannan kutunguilar?"

Baffah ya yi dariya mai sauti yace,. "Yaro man kaza to ai sonki ne da yake yi ma yasa ya bada kuɗin don kawai ya sami damar aurenki, don idan har da gaske baya sonki ai ba abunda zai sa ya damu don kawai wani zai aureki, amman kin ga yanzu sonki ne ya janyo ya yi amfani da damar da ALLAH ya bashi ya yi nasarar aureki, don haka ko da wani kika ji ya faɗi hakan to kada ki yi shayin ce wa da shi ni Baffahnki Ummaru Sanda nace ƙarya yake yi, ko da ko shi mijin naki ne kika ji ya faɗa to bance ki amince da zancen ba, don kuwa so mai suna so yake yi maki ko da ko bai faɗa ba"

Dije ta share guntayen hawayenta tace,. "To Baffah me yasa kullum yake ta yiman mugunta??, WALLAHI fa Hajiya kamar zata dake shi watarana idan taga yana cin zalina"

Baffah daɗi ya sa bakinshi yaƙi rufuwa yace,. "Ki godewa ALLAH Dijengalata saboda ya yi maki baiwar da ba kowa yake yi wa irinta ba, ki ce Alhmdllh kawai sai ya ƙaro maki wata ɗaukakar"

Dije ta washe baki tace,. "Alhmdllh na godewa ALLAH Baffahna WALLAHI na ji daɗin bokon da Hajiyar ta sakani, saboda na haɗu da mutane masu mutunci Baffah, WALLAHI baka ga yanda suke sona ba don ɗaya ma har karatu take ƙarani duk da su nasu karatun ba irin namu na nan garin bane, amman na fara ganeshi har ma na Kai hizif talatin wurinta Baffah, duk da fa cewa ta yi dole sai na dawo baya tun farko amman na yi nisa wallahi"

Baffah ya faɗaɗa fuskarshi da fara'a yace,. "Ai duk inda kike albarkar da muke saka maki tana tare da ke, ke dai ki ci gaba da haƙuri kawai da sannu zaki zamo abar kwatance a wannan garin namu, tashi ki je ki yi SALLAH idan na dawo masallaci mu ci gaba da firarmu kawai"

Yana ƙare maganar ya miƙe tsaye ya karɓi butar da Inna take miƙo masa ya fice ƙofar gida zuciyarshi cike fal da farin ciki.

Bayan fitarshi ne Inna ta jawo hannunta da sauri suka yi ɗaki, ta maka mata wata uwar harara tace

"Na sake jin kin faɗi sirrin dake tsakaninki da Mijinki ko na gidan aurenki ga kowa sai na saɓa maki, ko da ko Baffah'n ne naji kin sake tona wata magana ba mai daɗi ba to ni kaɗai nasan abunda zan yi maki, tunda har na gano ke har yanzu baki da wayo, in kuma har kina son ya hanaki komawa ki daina makarantar da kike son zama likitan shikenan, kije ki yi ta faɗa har ya ji zafi ya ce ba zaki ci gaba da karatun ba"

Inna tana gama faɗar maganganun cike da jin haushi ta fice, Dije ta biyota tace "na Bari Inna ni yanzu ma ko da wani ya tambayeni cewa zan yi ina jin daɗin zama da shi har ma da ƙanwarshi Fiddausi, ai ya yi haka ko Inna?"

Innar ta juyo tace,. "Da kin taimaki kanki don muddin kika sake faɗar wani aibin da ya shafi aurenki to tsaf zai ce ba zaki koma birnin ba, shikenan sai ki dawo nan ki ci gaba da zaman tunda haka kike so"

Dije ta rufe bakinta tace,. "Laa! Kin ko ga sai yanzu na tuno Inna itama da Hajiyar sai da tace da ni kar in faɗa maku yana cin zalina"

Inna tace ",kinji ba tunda kin janyo ta fahimci baƙin surutunki naki ko?, To yanzu dai ki ko yi ɓoye sirrin Mijinki da na gidan aurenki ga kowa ma, ke har ni kaina nan bance ki faɗa man ba"

Dije ta toshe dariyar da ta zo mata tace,. "Har da ke Inna to ke wani zaki je ki faɗawa ne halan?"

Inna ta fice ɗakin tana faɗin "Maba zan baiwa kuɗi ya yi ta sanarwa yana shela ko'ina a garin nan sai kowa ma ya sani"

Dije ta tuntsure da dariya tace,. ,"ALLAH ya bar man ke Innata"

Inna ta ɗauki butarta ta yi bayi tana faɗin "ke kuma ya shirya man ke ba"

Da dare ko da Baffah ya dawo gidan da ledar tsirenshi da ya siyowa Dijen tuni har ta yi bacci, dole ya ajiye mata sai da safe sannan ya bata ta cenye tana yi wa Usmanu dariyar an bashi tsoka biyu.

Bayan ta yi wanka ne tace da Inna zata je gidansu Gambo su ƙara gaisawa, Inna ta ce da ita to ta jira a bata kayan tsarabar da aka kawo masu ta kai mata nata kaso, Baffah ya ce ta raba kayan a kaiwa duk wanda ALLAH yasa da rabonshi a ciki, ta fidda na Gambon Usmanu ya karɓa zai wuce mata da kayan a babur ɗinshi, sannan shi ya wuce birni wajen harkar kasuwancinshi.

Sauran na mutanen garin kuma ya kira yara da kanshi anata lissafa gida gida da wanda za'a kaiwa sabulu da Omon, ita kuma Dijen ya bata na Maigari ya ce ta fara zuwa gidanshi ta kai masa kafin ta je gidan Gambon.

Lanti da Mune sune suka riƙa kayan suka taka mata har gidan Maigarin, cikin natsuwa Dijen ta gayar da shi tare da Matanshi sannan ta karɓi kayan tsarabar ta bashi tare da yi wa uwargidan Maigarin ya jikinta akan kariyar da ta janyo mata lokacin gudun kura, duk da har lokacin bata koma dai-dai ba amman sunji daɗin kular da ta nuna masu, suna saka mata albarka ta fito gidan tare da jinjina yanda Dijen ta fara shiryuwa, saboda ganin yanda ta yi masu komi cikin ladabi ba kamar cen baya ba da ko gidan bata shigowa bale su sami arziƙin ta zo gayar da su.

Suna fitowa Dije tace da su Lanti gidan Gambo nik son in je amman zuciyata tana bani in fara zuwa wurin Jummala in ganota, saboda jiya da tausayinta na kwana Lanti musamman labarin gudowar da kuka ce tana yi, ina son inje inji dalilinta don gaskiya bana son a cutar da rayuwarta WALLAHi"

Mune ta sauke ajiyar zuciya tace,. "Hu'umm to ALLAH yasa Garbatin baya gida"

Suka haɗa baki wajen cewa "Ameen" Dije ta ƙara da cewa "ko ma yana gidan ai sai ya fito ya barmu mun gaisa da ƙawarmu"

Suka rankaya zuwa gidan Jummala sai dai tun kafin su isa suka fara jiyo kururuwar Jummala, cikin sauri suka ƙarasa cikin gidan abun mamaki ɗakin Jummalar a rufe amman sai kuwwa take zubawa tana magiya akan ya yi haƙuri, cikin faɗuwar gaba Dijen ta je bakin ƙofar ɗakin ta fara bubbugawa tana faɗin

"Jummala ki buɗe ɗakin me ya faru da ke ne? Buɗe nice Dije na zo ganinki"

Bubbugar ɗakin da Dijen take yi shi ya dawo da Garbatin daga duniyar ma'aurata da ya lula, cike da tsanani jin haushi ya sauko gadon yana gyara zaman kayanshi ya nufi Kofar ya buɗe, yana ƙarewa Dije kallo da jajayen idanuwanshi da suka so su baiwa Dijen tsoro, cikin dakiya tace

"Matsa daga nan
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment