Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

TA KOWACE SIGA*
*TARTSATSI.*
*RUWA DA KANKARA.*
*DIJE K'ARANGIYA*
*NI HADIZA D/AUTA BAN LAMUNTA BA AKAN KOWA YA SARRAFA MANI LITTAFAINA BA BA TARE DA IZININA BA AKASIN HAKA KUWA WALLAHIL'AZIM ZAMU GAURAYA DA KOMA WACE DON SAI NA JA HAKKINA AKAN KOMA WA YE A BI DOKA A ZAUNA LAFIYA🤝🏻*


*Lamba ta 26*


Hak'ik'a ba k'aramin k'auyanci Dije da Baffah'nta da 'yan rakiyarta suka yi a Hotel d'in ba, sai dai kasancewar su Safwan d'in sun san daga ina suka fito shiyasa ba su yi mamakin hakan ba, don Dije A.c'n da ta zuk'a ya sata bajewa tana bacci har da su minshari, daga ita har abokan tafiyarta don dak'yar aka tashesu suka yi wanka mai cike da k'auyanci shi ma, sannan suka yi breakfast suka shirya suna jiran Safwan ya dawo daga fitar da yayi cikin gari su tafi.

Aikuwa Safwan fitarshi ke da wuya bai zame ko'ina ba kai tsaye sai Gidansu Lawi, inda ya taradda shi kwance yana bacci kasancewar d'akinshi lik'e yake da gidansu k'ofarshi tana kallon hanya.

Ba k'aramin mamaki Lawi ya yi ba da ya ganshi, cike da d'okin son jin wani labari daga Dijenshi ya yi saurin wartsakewa yace

"Abokina wannan tafiya babu sanarwa fa? Ko dai bazata ka zo ka yi man akan ka sanar dani cewa an amince in zo in auri Dijena? WALLAHI yanzu haka da ka ganni mafalkinta nake yi"

Safwan ya b'ata fuska tare da mik'ewa tsaye ya fito da kud'inshi da Dije ta bada a bashi ya ajiye masa a gefen katifarshi, sannan ya soka hannunshi duka a aljihu yace

"Ga kud'inka nan inji Khadija ta ce in kawo maka, saboda gidansu ance bazata karb'a ba don Ni ma ban so na rabata da kud'in ba shine ta wurgosu d'akinmu ban sani ba ta tsere abinta".

Lawi cikin tsananin firgici tare da fad'uwar da gabanshi yake ta yi da sauri da sauri yace

"Yanzu shi kenan ana nufin an rabani da ita da gaske an aurawa wani ita wanda bai san darajarta ba?, D'ankauye irinta wanda ba zai taimaketa ta cika gurinta a rayuwa ba?"

Ya k'are maganar tare da zubowar wasu hawaye masu zafi akan fuskarshi, Safwan ya yi taku d'aya biyu tare da juyawa Lawi baya sannan ya furzar da iska mai k'arfi a bakinshi yace

"Gurinta zai cika Insha ALLAHu kamar yanda kake yi mata fata don ni zan rik'eta da zuciya d'aya har sai na tabbatar da ta cika gurinta na zama likitar kamar yanda take gurin zama"

Lawi cikin k'ullewar kai da maganganun Abokin nashi ya yi saurin mik'ewa tsaye ya fuskanceshi idonshi fes akan fuskarshi zuciyarshi cike da wasi wasi yace

"Fashe man bak'i akan abunda kake nufi Abokina, don zuciyata ta fara hasasoman abunda nake hangowa kamar ba gaskiya bane"

SAFWAN ya saka hannu ya dafa kafad'ar Lawi yace,. "Ka d'auka cewa komi rubuce yake a Littafin kundin k'addararmu mai kyau ko akasin hakan, kuma ka d'auka cewa matar mutum kabarinshi wani ba zai tab'a auren matar da ba tashi ba"

Lawi cikin matsananciyar damuwa yace,. "A tak'aice kana son ka sanar dani cewa anyiwa Dije aure kuma ba da d'ankauyensu ba to da wa aka d'aura da har zaka d'auki nauyin cikar burinta??"

Ya k'are maganar cikin yi masa kallon tuhuma, cikin sanyin jiki tare da daburcewa Safwan yace,. "A lokacin da ka baro k'auyen KHADIJA ta tub'ure akan ba zata auri wanda aka zab'a mata ba, ganin hakan Mahaifinta ya ce ta je ta auri wanda take so amman a rana da lokacin da aka saka da wancen d'in, idan ba haka ba shi ba zai fasa auradda ita ba kuma ba zai d'aga lokaci ba, shine da ta zo ta sanar dani na yi ta neman layinka ban sameka ba gashi lokacin ana saura kwana biyu, hankalina ya tashi sosai ga Yarinyar ta d'aga hankalinta akan rashin samunka da ba'ayi ba, shine ta rok'eni akan don ALLAH ni in amince in aureta"

Rassssss! Gaban Lawi ya buga ba shiri hawayen da yake mak'alewa suka gangaro masa cikin muryar kuka yace,. "Ba sai ka k'arasa dogon labarinka na k'arya da ka shiryo man ba wanda ko kad'an k'arya bata kamaceka ba don ba halinka ba ce, na fahimci inda duk ka dosa don daman cen na dad'e da gano kana sonta, na kyaleka ne don kawai inga iya gudun ruwanka ka je kawai ALLAH ya baku zaman lafiya, kuma Ni na yafe maka duk abunda ka yi mani saboda kawai nasan cewa kula mata ba d'abi'arka bane, Kuma na godewa ALLAH da ya jarrabeka da son abunda ka rena ko don ka fahimci cewa wulak'ancin da ka ke yiwa Mutane ALLAH ya nuna maka cewa su d'in ba abun reni ba ne, ka je kawai ALLAH ya baku zaman lafiya amman ka sani naji haushin da tun farko ka b'oye mani cewa kana sonta, ka barni sai da na zurma da yawa sannan ka dawo ka kwaye mani baya ka sani amincinmu bai ci haka ba"

Yana k'are maganar ya fice d'akin cikin sauri, Safwan ya bishi da kallo zuciyarshi cike da takaicin abunda ya aikatawa abokinshi, jiki a sanyaye ya janyo k'afafuwanshi ya shiga gidansu Lawin, kasancewar sun sanshi sosai Shiyasa suna jin sallamarshi k'anwar Lawi ta lek'o tana ganinshi ta koma da sauri ta yi cikin Gidan, sai gata ta dawo tace da shi ya shigo

Safwan ya shiga zuciyarshi cike da jin kunyar abunda ya yiwa Lawi, ya isa wurin Mahaifinshi da ke zaune yana fama da jiki ya gayar da shi, sannan Mahaifiyar Lawin ta zo itama suka gaisa, suna yi masa ya Hanya.

Banyan sun gama gaosuwar ne Mamar Lawin tace,. "Aiko ina jin yana d'akinshi ko kun had'u?"

Safwan ya duk'e kanshi yace,. "Eh mun had'u daman wucewa zan yi nace bari in zo in ga jikin Baba, ALHAMDULILLAH ma naga lafiya ta samu"

Mamar tace,. "Eh ai kwanan nan Masha ALLAH jikin sauk'i sai samuwa yake yi"

Safwan ya zura hannu aljihu ya fiddo kud'i masu d'an kauri ya ajiye a saman shimfid'ar Baban yace,

"Ga shi Baba ni zan wuce ALLAH ya bida lafiya"

Mahaifin Lawin yace

"Masha ALLAH Safwanu ALLAH ya tsare ya kaika lafiya ka gayar da mutanen gidan duka"

Haka suka yi sallama ya fito sai dai kam ba Lawi ba samatarshi, haka aka yi ta bulayin nemanshi akan su yi sallama da Safwan amman ba'a ganshi ba, dole ya lallab'o ya baro unguwar cikin jin haushin kanshi akan me yasa bai hak'ura ya barwa Abokin nashi ba, wata zuciyar tace da shi

_"To Kai fa ko ka manta halin da ka shiga ne akan ganin zata sub'uce maka?Shareshi kawai zai hak'ura ne daga baya"_

Haka ya nufo Hotel d'in suka d'uru motocinsu suka kama hanyarsu ta zuwa Yola, har suka isa zuciyarshi bata daina yi masa canki in canka ba, a k'arshe dai ya tsayu akan magana d'aya wadda yake ganin itace mafitar da zai wanke laifin da ya yiwa Abokinshi.

Kasancewar an san da zuwansu shiyasa kai tsaye aka wuce da su ainahin gidansu Safwan d'in, aikuwa sai ga Mahaifiyarshi da k'annenshi biyu sun fito tarbarsu cike da d'okin ganinshi, Mama Hajiya waton Mahaifyar Safwan kai tsaye wajen Dije ta nufa inda zuciyarta ta tabbatar mata da itace Matar Safwan d'in, duk da zuciyarta ba k'aramin bugawa ta yi ba lokacin da ta yi arba da Dijen ba, sai dai ta mazge ta rik'o hannunta tace

"Oyoyo 'yata sannu da zuwa"

Dije ta bita da kallo Baki washe tace,. "Laaah! Ashe kin sanni??"

Safwan ya yi saurin fad'in "to maganatu ke bakinki ba zai yi shiru ba? Ko gaisawa ba'a yi ba sai surutu"

Dije ta sunne kai tare da maka masa hararar gefen ido ta kalli Mama Hajiyar ta rusuna k'asa tace,. "Barka da yini Inna"

Mama Hajiyar ta d'agota tana dariyar yak'e tace,. "Barka dai 'yata sannunki da zuwa to mu shiga daga ciki"

Ta janyo hannunta tare da yiwa 'yan rakiyar Dije maraba da Baffah'nta da yake ta kallon k'aton gidan yana jinjina girmamshi a ranshi, har suka shiga ciki inda su Baffanta da sauran mutum biyu da suka rakoshi aka kaisu babban sit room d'in Gidan tare da Iyayen Safwan d'in biyu da suke tare.

Dije kam cikin Gidan Hajiya Mama ta ja ta K'annen Safwan biyu suna biye da su suna k'umshe dariya, musamman dai d'aya k'anwar tashi da har dafe ciki take yi saboda waige waigen da Dijen da 'yan rakiyarta suke ta yi, don suna ta kalle kallensu har suka shiga ciki, in da aka yiwa matan biyu masauki a wani d'aki Dije kam kai tsaye ta nufi d'akinta da ita ta zaunar da ita falonta, su Sury da ke biye da su suna shigowa ta korasu suka fita saboda ganin yanda su ke ta faman yi wa Dijen dariya.

Sannan ta kira wata 'yar aikinsu ta kawowa Dijen Abinci da wad'ancen matan sannan ta yi k'uryar d'akinta zuciyarta cike da tunane tunane, Dije kam ba wani jin nauyi ko jin kunya ta saki jiki ta kwashi abincinta tana santi har da su lashe filet d'in tas da halshenta, sannan da ta k'oshi ma ta saka hannunta cikin miyar ta dinga tsamo tsokokin naman tana cinyewa tana fad'in

"Wannan Abinci sai kace a aljannah?? Cabd'i jam, ai Ni kam gaba ta yi da ni wai zak'wai yasin ai Ni kam ba mai fiddani cikin gidan nan"

Surayya da fiddo kam da suke lab'e jikin k'ofar d'akin sunata turereniyar lek'enta, sai uwar dariya suke ci har sai da Hajiya Mama ta fito ta gansu suka yi saurin barin wajen tare da k'umshe dariyar da take son kashesu, saboda ganin duk felek'en Yaya Safwan d'in ace wai wannan Bagidajiyar ce Matarshi.

Hajiya Mama ta yi zaune tana kallon Dijen yanda bakinta ya nashe da maik'o gashi sai faman lashe hannunta take yi tana fad'in,. "Hannuna Kai ma yau ka san ka shigo gidan Yan gayu munci dad'i abunmu ALLAH yasa in mutu a gidan nan Ni kam, dole in koma in zo da Innata da Gambo su ma su sha dad'insu, ta sake d'auko wani k'aton k'ashi tace wohoho ina ma Gambo ta sami wannan k'ashin nasan da hak'oranta da suka zube duka sai sun dawo"

A cen gefen su Baffah kuwa an tarbesu da manyan kulolin abinci na alfarma, sannan aka nuna masu toilet da komi suka fara gabatar da sallolinsu sannan suka ci abinci suka yi k'at! Sannan aka had'u duka akan a tattauna muhimmiyar maganar da ta had'asu dukansu..




Akafta





D/AUTA CE😅

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*






*BAN LAMUNTA BA AKAN KOWA YA SARRAFA MANI LITTAFAINA BA BA TARE DA IZININA BA AKASIN HAKA KUWA WALLAHIL'AZIM ZAMU GAURAYA DA KOMA WACE DON SAI NA JA HAKKINA AKAN KOMA WA YE A BI DOKA A ZAUNA LAFIYA🤝🏻*

*Kukan Kurciya......😉*


*Lamba ta 27*



Safwan kam ko da ya je sanarwa da Hajiya Mama ya taradda ita zaune falonta ta yi tagumi tana nazarin abunda ya ja Safwan ga Dije har ya zab'eta a matsayin matar aurenshi, saboda saninshi da ta yi ciki da bayanshi akan mugun k'yank'yami tare da wofintar da sha'anin Mata, cikin sanyin jiki ya isa wurinta saboda yanayinta ya nuna k'arara damuwar da take ciki, ya sami d'aya daga cikin kujerun ya zauna sannan yace

"Maaah!"

Ta d'ago kanta da sauri tana murmushin yak'e tace,. "Ya dai? Sun kammala cin abincin ne?"

Ya sosa kanshi ya ce "Eh ina ita yarinyar?"

Hajiya Mama ta yi masa nuni da k'uryar d'akinta tace,. "Tana ciki tana SALLAH"

Sannan ya ce "Ok to ki je su Baba Ali suna so su tafi gida shine aka ce ki zo ku yi sallama"

Hajiya Mama ta mike ta janyo hijabinta ta saka tace,. "Ok to mu je"

Ya sosa kanshi yace,. "Itama ta zo ai zaman har da ita ne"

Hajiya Mama tace,. "Ok to ku sameni a cen d'in"

Ta fice zuciyarta bata daina mamakin Safwan ba, Safwan kam kai tsaye d'akin ya nufa in da ya taradda ita tsaye a gaban standing mirror tana kallon kanta tana wasar Baki, tana yi tana rufe fuskarta cen ta bud'e tana dariya saboda ganin kanta jikin k'aton madubin yasata jinta cikin wani nishad'i.

A hankali ya ja ya tsaya bayanta tare da rungume hannu a K'irji yana kallonta, cikin Madubin Dije ta hangoshi tsaye ta yi saurin waigawa sai ko gashi yana yi mata wani kallon reni yace

"Ke Wai shikenan ba zaki yi hankali ba?"

Dije ta sha jinin jikinta tace,. "Ai kasan cewa Ni ba mahaukaciya ba ce ba ko?"

Ta k'are maganar tare da murgud'a masa Baki, ya tako a hankali ya tsaya gaf da ita tare da rik'e mata kunne ya jawo cikin sigar k'eta Dije ta yage baki tace

"Wayyo! Baffahna"

Safwan ya yi saurin sakinta ya ce " ke fa wata b'aro ce to ki zo muje ana nemanki kuma saura idan kika je don ALLAH ki zuba shirmenki da kika saba, WALLAHI in saki jiki in jibegeki a banza kin ga nan ba k'auyenku bane bale har ki sami damar yi man turaren mayu ko ki saka man b'eraye"

Yana k'are maganar ya nufi k'ofar fita yace,. "Ki zo mu je na ce"

Dije ta sha jinin jikinta sosai saboda tuno abunda ta yi masa sannan ta bishi a baya tana fad'in

"Don Allah Ni dai ai ba wani laifi nayi ba kuma yanzu ko? Don Ni dai WALLAHI ALLAH bana son a ce in bar gidan nan, ashe haka kuke cin dad'inku ku kam? Cab! Gaskiya Wallahi kun zo duniyar a sa'a ashe ku ma kuna cikin mutanen da na ji Malaminmu ya fad'a muna ana baiwa Aljannah tun nan duniya ku canye mu Kuma sai a bamu ta Lahira"

Ya yi banza da ita yana gaba tana biyarshi tana zuba masa surutu har suka kai Babban falon Gidan, in da su Fiddo su ke zaune suna kallo suna labarin shirmen Dije suna dariya, suna hangoshi suka yi muk'us dukansu saboda bala'in tsoronshi da suke ji kamar me, ya wuce abinshi ba tare da ko kallonsu ya yi ba, Dije kam tana k'arasowa tana kalle kallenta ta hango t.v ana wani wrestling, dai dai in da wani k'aton mutum ya d'aga wani sama ya jefoshi k'asa ya bishi ya danne ana kidanyar d'aya biyu uku, Dije ta yi wani tsalle tace

"Tashi ka rama WALLAHI kada ka yarda cabd'i jam haka kawai ka zuba masa Ido ya jibgi banza?"

Sai Kuma gashi Kuma wanda ya danne d'in ya hanashi ci ta hanyar yin wani zillo cikin jin haushin hakan mai son ya ci d'in ya saki kwanji ya yi ta kaiwa na k'asan naushi, Dije ta zabura ta gyara tsayuwar dambe ta sha fili tace

"Ai billahillazi kar ka yarda tashi ka rama nace ko baka jini ba? kutuma lalle Kai yanzu zaune zaka yi yanata jibgarka a banza lalle ma kai wawan banza ne kai cabd'i!"

Surry da Fiddo ko me za su yi ba dariya ba don kuwa daina kallon suka yi suka koma kallonta suna cin uban dariya, Safwan kam jin kamar bata biyarshi yasa ya waiga ganin bai ganta ba ya dawo sai dai tsayin da ya ga ta yi ne shi ma kanshi ya so ya bashi dariya, amman ya mazge ya katsa mata wata uwar tsawa yace

"Ke Uban mi kike yi a wurin ba za ki zo mu tafi ba??"

Dije ta yi saurin waigawa sannan ta b'ata fuska tace, "wani abun takaici na gani yanzu wai wani k'atoton banza ne ya yi kwance anata jibgarshi a wofi WALLAHI ya ji haushi shi kam"

Safwan hararar da ya danna mata ce tasa ta yi muk'us ba shiri ta nufo wajen tare da rab'awa ta gefenshi ta wuce, su Surry kansu tuni suka yi gum! har sai da suka ga ya wuce sannan suka sake fashewa da wata sabuwar dariya saboda abinda Dijen ta yi ba k'aramin dariya ya basu ba.

Bayan sun bar wajen ne Safwan d'in ya fisgota da k'arfi ya had'ata da gini tare da d'aga hannu kamar zai daketa cikin b'acin rai ya nunata da yatsa yace

"WALLAHI kada ki kuskura ki janyo in karairayaki cikin Gidan nan, ke shikenan ba zaki natsu ba sai abu kike yi tamkar wata mahaukaciya to bari kiji na sake ganin kin sake irin wannan shirmen jikinki ne zai gaya maki wawuyar banza,, matsa daga nan kina wani kallona da wasu idanuwanki guru guru tamkar idanuwan mota"

Dije ta zunb'uro baki Kai tsaye ya fisgo hannunta cike da jin haushin kwafsawar da take yi masa suka nufi d'akin, sannan ya saketa da sauri suka shiga tare da sallama a bakunansu.

Dije kam sage da hannu ta shiga ta Sami gefe ta rakub'e tana yarfa hannunta,a zuciyarta tana fad'in

_"Shi Kam wannan mugun mutumen har ciki nawa ya ke so ya yi man ne? "_

Tunaninta ya katse ne saboda jin muryar wani d'aya daga cikin Iyayen Safwan d'in da ta jii yana cewa,. "Matso daga ciki ki zauna kinji 'yata"

Dije ta mik'e ta dawo ciki kad'an ta zauna k'asan carpet kamar yanda taga Safwan d'in ya yi, duk da wata zuciyar ta so ace ta hau Kan kujerar ko don ta ji ya laushinta ya ke, don tunda ta k'yalla Ido ta hangosu tasan ba k'aramin dad'in zama za su yi ba, amman firgicin cikin da Safwan ya sake yi mata yasa ta ji duniyar gaba d'aya ma ta fice mata a Rai.

Baba Ali ya sake cewa

"Masha ALLAHU kamar yanda kowa ya sani ne wannan zama mun yishi ne saboda Safwan da Khadija, saboda auren da Ubangiji ya nufa aka yi a tsakaninsu, to Masha ALLAH yanzu Malam Sanda ga gidansu Mijin 'yarka yanda idan ka tashi nemanta kasan ta inda zaka nemeta, Hajiya Balkisu kinga Mahaifin Khadija Malam Sanda wad'annan kuma abokan tafiyarshi ne, Khadija kin ga Mahaifiyar Mijinki Safwan Mahaifinshi kuma tuni ALLAH ya yi masa rasuwa,m sai dai Ni yayanshi tare da wannan k'anenshi tare da sauran 'yan uwanmu Mata da maza da suka rage, shi kam sai dai mu bishi da addu'ar ALLAH Ubangiji ya dad'a masa Rahama a cikin k'abarinshi tare da musulmin duniya gaba d'aya, mu ma idan ta mu ta zo yasa mu cika da imani"

Dukansu suka ce "Ameen Ameen" sannan d'aya bayan d'aya kowa ya yi jawabi tare da neman ma zaman auren nasu albarka, sannan aka ja hankalinsu duka daga shi har ita akan zaman auren tare da nuna masu muhimmancin auren tare da hak'uri a zamantakewar auren duka.

ALHMDLLH shi kanshi Baffahn na Dije yanzu hankalinshi ya kwanta sosai saboda ganin yanda suke Mutane masu karamci, daga nan shi ma ya damk'awa Safwan da Mahaifiyarshi har ma da Iyayen Maza amanar Dijenshi, tare da rok'onsu akan duk abunda ta yi wanda bai dace ba don ALLAH ayi hak'uri da ita da sannu zata dawo dai dai da yanda ake son kowace d'iyar ta kasance, don a fakaice ya yi masu nuni da su yi hak'uri da halayenta don ba ya son ya bayyana k'arara cewa ga laifin 'yarshi, ya fi son idan sun gani a matsayinsu na masu ilimi su fahimtar da ita abunda ya dace su d'orata kan hanya har ta fahimci rayuwar da yanda ake zama cikinta.

Taro ya watse akan cewa gobe tun da sassafe su Baffah'n za su kama hanyarsu ta komawa gida, sannan su Iyaye mazan suka yi sallama da su akan sai goben za su zo su yi sallama da su Baffah'n, Safwan da Hajiyarshi har gindin mota suka rakasu suna yi masu godiya har suka bar Gidan.

Dije kam suna fita ta tashi ta nufi Baffah'nta tana washe baki tace,. "Baffah Kai ma ka ci naman mai yawa ko? WALLAHI baka ga Wanda na ci ba ga abincinsu mai shegen dad'in tsiya"

Baffah ya washe Bakinshi ya ce, "kin samu gidan Aure Dije don ALLAH ki yi biyayya kinji?"

Dije ta d'aga Kai, tana matsa 'yan yatsunta tace,. "Ai ni duk ma aikin da suke so in yi masu zan yi WALLAHI ko don su dinga bani abincina mai dad'i ina ci"

Baffah ya ce,. "Duk abunda Mijinki ya sakaki ki yi masa kinji? haka ma Mahaifiyarshi kin ga dai suna da kirki don ALLAH kada ki yi abunda zai janyo har ace baki kyauta ba"

Dije tace,. ,"Insha ALLAHu Baffah ba Zan yi rashin ji ba ko cen garinmu ai ka ga su ke ja na ai"

Baffah ya ce "Nan ma ai dole su ja ki amman don ALLAH kar ki biyesu ki ce ke dole sai kin rama ki kyalesu da halinsu da sannu zaki ci ribar hak'urinki"

Dije tace "to Baffah amman don ALLAH ka ce da shi ya daina rik'e man hannu WALLAHI Ni bana son inyi ciki gashi yanzu har ciki biyu ya yi mani d'aya nan d'aya a k'auyenmu"

Ta k'are maganar cikin zubowar wasu 'yanmatan hawaye, Baffah zai yi magana kenan sai ga su Safwan d'in sun shigo, dole ya wayance yana fad'in

"Ki yi hak'uri ai ko nan gida ne kamar cen d'in saboda nan da cen duk d'aya ne a wajenki Babu banbanci"




Akafta😛





D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*Masu buk'atar Littafaina ga su kamar haka:*

*TARTSATSI*

*RUWA DA K'ANK'ARA*

*BAKAN GIZO*

*DIJE K'ARANGIYA*

*BAK'ON YANAYI sai dai shi na kud'i ne da d'ari uku kacal zaki sameshi a complete d'inshi😇*


*Lamba ta 28*


Haka Baffah ya shashantar da zancen aka yi ta fira har aka yi magrib suna tare da Safwan sunata fira duk da ba wani sabawa ya yi da su ba amman ba laifi sun d'an tab'a fira, kiran sallah'r yasa Dije ta yi cikin Gidan tare da matan biyu domin su yi SALLAH, su Baffah kuwa suka yi masallacin da ke k'ofar gidan.

Ko da dare ya yi Hajiya Mama ta saka Dije ta yi wanka da kanta ta nuna mata yanda zata yi kwalliya ba irinta haukarta da ta saba ba, ta d'auko wasu sababbin kayan bacci masu shegen kyau tace ta saka, Dije kam saboda hud'ubar da Baffah'nta ya yi mata sannan da kashedin da Safwan d'in ya yi mata shi yasa ta rage shirme in taga wani abu da bata sani ba sai ta yi shiru ba zata yi ta surutu ba, bakinta alekum ta saka kayan tare da fessesa mata turaren da Hajiya Mama ta yi sannan ta kira Surry tace da ita ta je ta Kai Dije d'akin Safwan, Dije ta zaro Ido waje tace

"Hajiya me zanyi wajenshi Sabida ALLAH Ni kam cikin daren nan yanzu??"

Hajiya ta dafe goshinta tace,. "Ki je ki yi kwanciyarki a cen kafin da safe sai a kaiki gidanki in da zaku zauna da Mijin naki"

Dije ta zaro Ido waje tace,. "Kina nufin gidan nan zan bari???, WALLAHI idan na barshi an cuceni wa zai bani irin abincin da na ci d'azu mai d'an karen dad'i?"

Hajiya Mama ta dafa kafad'arta tace,. "Ki kwantar da hankalinki insha ALLAHu abincin da zaki ci a cen har sai ya fi na wannan Gidan dad'i, yanzu dai ki je da safe idan kika zo zan yi maki bayanin komi"

Dije ta marairece cikin kuka tace,. "Yanzu tsakaninki da ALLAH d'akin Namiji zaki kaini inje in kwana???bayan nasan ke ma kanki kinsan cewa hakan bai dace ba amman kike k'ok'arin turani???"

Hajiya Mama ta dafe goshinta ba shiri ta kai zaune tace da Surry da ke sunne kai tana k'umshe dariya da ta je, sannan ta janyo hannun Dijen ta zaunar da ita kan gadon ta yi shiru na d'an lokaci sannan tace

"Ai dai kinsan cewa an yi maki aure da shi ko?"

Dije ta d'aga kanta, Hajiya Mama tace

"Masha ALLAH to ai kinga shi baya cikin jerin mazan da aka haramta ki je d'akinsu ko?"

Dije ta yi shiru na d'an lokaci tana tunani tace,. "To Ni dai tsakani da ALLAH Innata ta hanani ko magana in dinga tsayawa ina yi da maza sosai, kuma yanzu idan Baffahna ya ji ai WALLAHI dole ma ne ya dakeni, Ni dai don hasken da ALLAH ya yi wa Qur'ani kada ki bari ya sake yi man ciki na uku"

Hajiya Mama ta zaro ido waje tace,. "Ciki na Uku?????"

Dije tace, "Eh ya yi man d'aya a k'auyenmu yanzu gashi d'azu lokacin da ya zo kirana muje wurinku sai da ya yi man d'aya yanzu haka Ina jin macizai sun fara taruwa a cikina kin gani WALLAHI cikina ya k'ara yin k'ato"

Hajiya Mama ta yi shiru tana nazarin maganganun Dijen sai cen ta nisa tace,. "To ta yaya yake yi maki

Please Login or Register in order to submit comment