Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kada ka janyo abunda zai sa Inna ta tsine man in bi duniya don ALLAH"

Cike da jin haushin magiyar da take yi ya mayar da rigarshi ya buɗe ɗakin a fusace ya fice, cikin sauri ta mayar da zif ɗinta ta ɗauki gyalenta ta fice jikinta sai rawa yake yi, sai dai ganinshi duƙe jikin motar ya dafe kai yasa ta ji jikinta ya yi sanyi, amman a hakan ta buɗe seat ɗin gaba ta zauna tana share hawayenta, sai da ya ɗauki lokaci sannan ya shiga ya tada motar suka fice gidan Maigadin yana yi masa ALLAH ya tsare amman ko kallonshi bai yi ba.

Kai tsaye wajen kamun ya nufa da ita yana ajiyeta bakin Gate ɗin ya juya abunshi ko kallonta bai sake yi ba, Dije ta bi motar da kallo cike da mamakin abunda ya sauyashi lokaci ɗaya, cikin sanyin jiki ta ja ƙafafuwanta ta shiga wurin kamun.

Har aka gama kamun bata da wata natsuwa yaƙe kawai take yi saboda abunda Safwan ya yi mata yasa taji zama garin gaba ɗaya ya fita kanta, don ko ƙudin da ta tanada don ta yi liƙi haka ta koma da su gida ko nera bata liƙa ba, asali ma gaba ɗaya komi ta ji ya fita ranta har sai da Surayya ta fahimci halin da take ciki, cikin damuwa ta ke tambayarta me aka yi taganta so silent haka? me Yaya Safwan ɗin ya yi mata? Dije kam iyakaci tace ba komi ƙarshe ma sai kuka ta fashe da shi, Surayya ta yi ta bata haƙuri don jikinta ya bata cewa wataƙila ko dukanta ya yi saboda ta gaya mata cewa Hajiya ta matsa masa dole shiyasa ya kawotan.

Fiddo kam daɗi kawai take ji saboda ganin Safwan ya fara koya mata hankali, don yanayin Dijen ya nuna ƙarara akwai abun takaicin da ya ƙumsa mata, Hajiya ma kanta ganin yanayin Dijen yasa ta jata gefe tana yi mata faɗa akan ta daina yi masa kuka idan ya yi mata wani abu, ta nuna masa bata ji zafi ba ta hakan ne zai gano kuskurenshi har ya fahimci bai kyauta ba, cikin kwantar da murya ta samu ta shawo kan Dijen, duk da Dijen taso ta sanar da ita abunda ya yi mata amman tana jin kunyar ace ta faɗi wannan abun kunyar wani ya ji, sai dai tasha alwashin duk ya sake kwatsnta mata wannan iskancin ita ko sai ta faɗawa Hajiyar komi.


Safwan kam ALLAH ne kawai ya kawoshi gida saboda rikitaccen yanayin da ya faɗa, wanda shi kanshi ya yi danasanin biye wa son zuciyarshi da ya yi, gashi zai janyowa kanshi baƙauyiyar yarinyar ta ga damarshi a banza a wofi, yaci alwashin ba zai sake kulata ba kuma zai yi ƙoƙarin auren Zainab kafin ma ya kammala karatun, sai suyi zamansu a cen kawai har sai sun gama karatunsu sun huta sannan ya dawo gida.




😝😝😝😝😝uhum






Akafta😍







D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*COMMENTERS ina matuƙar alfakhari da ku, saboda jajircewarku wajen daɗaɗan Comments naku ba dare ba rana,, Mmn Irfaan taki gaisuwa ta musamman ce,, ƴargata mmn Sultan ina yabawa ƙoƙarinki a kullum,, Hauwa Zubair ina yinki sosai tawajena,, Mun Sayyid sannu da ƙoƙari, Sa'ar Bukar Allah ja da kwananki,, Daughter Rufaida siffanta matsayinki a wurina abu ne mai girma, Maryam Omee bakina ba zai gaji wajen gode maki ba, saboda comments ɗinki yana ƙara mani ƙarfin gwiwa sosai, Ummu Afrah (Goribatyna) zumuncinmu daban ne,,,wai wai abun da da yawa fa aka ce mutuwa ta shigo kasuwa, Mutanen Dije idan nace zan ta lissafoku tabbas zan ƙare wannan page kaf ba tare da na gama zayyanoku ba, saboda haka mu haɗu a next Page's sannu a hnkl zamu game😉.*





*Lamba ta 45*



A ranar haka ya kwana yana ta murƙususunshi shi kaɗai cikin ɗaki ba wanda ma yasan me yake ciki, don kuwa yanda yaga dare haka ya ga safiya ko da safiya ta waye gaba ɗaya ya rafke ido sun faɗa sai karen hancishi da ya ƙara tsawo.

Ranar Alhamis ɗin itace ranar da ta kama za'a yi mother's day wanda za'a yi a wani katafaren hall da aka Ƙawata, don Hajiya Mama ma da ita za'a je wannan bikin, shiyasa shiri ake ta ko'ina su Dije sai kaiwa da komowa ake yi anata zirga zirga, Safwan da ke ɗaki yanata kuncinshi ganin Hajiya Mama tana ta sabgar bikinta ko damuwa da ta jishi ma bata yi ba, duk da kuma ta ji shiru bata ganshi ba tun safe har azahar, ko abun break ɗin da aka kai masa ko taɓawa bai yi ba yana nan yanda aka kawo shi ajiye, cike da takaici ya fito ɗakinshi yana wani muzurai ya yafito Fiddo zata wuce, cikin sauri ta ƙaraso wajenshi tana faɗin

"Big bros me ke damunka naga kamar ma baka da lafiya?"

Ya wani basar da zancen yace "kice da yarinyar nan ta kawo mani tea zan fita yanzu kafin in dawo, sannan kayan break ɗin da ke ɗakina a kwashe su duka a fito da su"

Yana ƙare faɗa ya juya Fiddo ta yi saurin faɗin

"Big bros ko dai in haɗo maka da kaina ne? WALLAHi wannan yarinyar ba abunda ta iya sai shirme"

Ba tare da ya juyo ba yace, "ki je ki sanar da ita"

Fiddo ta yi wani yatsine ta ce, "Ni na rasa me ma ya janyo ka kwasowa kanka wannan ƴar dajin, haka kawai ta zo ta janyo maka hawan jini da ƙurciyarka, duk matan duniyar nan ka rasa macen aure sai ita don bala'i, da class ɗinka ka lalace a kanta wannan abun kunyar da me ya yi kama?, Mitssss!"

Ta buga wani uban tsaki ta yi cikin gidan ranta a ɓace, maimakon ta sanarwa da Dijen saƙonshi ta yi wajen Hajiya Mama ta ce

"Yau fa bros baya jin daɗi Hajiyarmu, yanzu haka break ɗin safe da aka kai masa yace a fito da shi bai taɓa ba, yanzu haka tea kawai yace a haɗo masa kafin ya dawo"

Hajiya ta yi shiru sannan tace "to ki je ki cewa Khadijah ta haɗa masa ta kai masa ALLAH ya bashi lafiya"

Tana ƙare faɗar hakan ta ci gaba da sabgoginta Fiddo ta fito cike da jin haushi ta nufi wurin Dijen tana sanar da ita, wai don ta cusa mata haushi ta ce da Surayya

"Aunty Surry yau fa muna da babbar baƙuwa daga Gombe Amaryar yaya Safwan zata zo"

Surayya ta kalli Dije da ke ƙoƙarin fita ɗakin ta janyo kunnen Fiddo tace,. "WALLAHi Hajiya Mama ta ji ki sai kin san baki ragawa kanki ba, ko ranar ba naji tana yi maki kashedi akan hakan ba?"

Fiddo ta ɓata fuska tace, "to ni miye laifina a ciki don na taya yayana son abunda yake so?, Shikenan sai ace kowa baya son zaɓinshi sai wannan bagidajiyar?, Ku kanku ai kunsan cewa ba ajinshi bace amman kuka rufe gaskiya kuna goya mata baya"

Surayya ta yi mata wani mere tace, "Ni rashin hankalinki Fiddo mamaki yake bani WALLAHi, shin da mu da shi wa ya kawo Khadijah gidan nan? Hajiya ko Ni? To ki buɗe kunnuwanki da kyau kiji da ace yaya Safwan baya sonta WALLAHi da ba zai taɓa amincewa ya aureta ba, saboda haka ki ajiye haukarki a gefe ki bar Mata da Mijinta su huta, saboda ke da kanki watarana zaki bada labarin irin son da yake yi mata WALLAHi, don ko wannan auren da yace zai yi, zai yi shi ne kawai amman ba wai don baya son khadija ba, kuma ma yanzu idan ba makiyin ALLAH ba wa zai ga khadija a yanzu yace bata dace da shi ba?"

Fiddo ta yi saurin faɗin, "sai kuma ni nan don WALLAHi ko kaɗan ma ba mahaɗa don kinsan ya yi mata zarra sosai"

Surry ta watsa mata wata harara tace, "to ai ki je kiyi ta yi kar ki fasa"

Haka suka yi ta sa'insa a tsakaninsu har abun ya so ya zamar masu faɗa sai da ƴanmatan da ke ɗakin suka shiga tsakaninsu, Dije kam cike da faɗuwar gaba ta kammala haɗa masa komi a wani ƙaramin tire, ta nufi ɗakinshi gabanta sai faɗuwa yake yi sai dai ganin ɗakin ba kowa ne yasa hankalinta ya kwanta, ta yi saurin ajiyewa ta zo zata fita kenan ta ji ƙarar buɗewar toilet ɗinshi, ta yi saurin ficewa ya ɗaga murya a hankali yace

"wannan kayan fa wa kika barwa su?"

Dije ta dawo jikinta yana rawa ta ɗauki ƙaton tiren ta zo zata fita yace

"Ki je ki dawo ina jiranki"

Ta fice ko waigowa bata yi ba saboda tsananin tsoronshi da take ji, ya bi bayanta da kallo jiki a mace ya zauna ya yi tagumi yana nazarin abubuwan da suka sha masa kai a zuciya, yana nan zaune har ta dawo ya yi saurin cire tagumin ya kalleta sama da ƙasa ya maka mata harara tare da zaro ido yace

"Ni kike so in zuba da kaina ko kuwa?"

Dije da ke tsaye tana wasa da yatsunta ta yi saurin duƙawa ta ɗauki ƙaramin flaks ɗin ta fara tsiyaya masa tea ɗin cikin cup, ta miƙo masa ba tare da ta kalleshi ba jin shiru bai karɓa ba yasa ta ɗago kanta ta kalleshi, sai ko caraf ta yi arba da kallon da yake yiwa ƙirjinta da ya fito cikin wuyan rigarta ba tare da ta sani ba wajen ƙoƙarin zuba masa tea ɗin, ta yi saurin ajiye tean cikin firgici ta miƙe tsaye tana gyara zaman rigarta zata fice, caraf ya riƙo hannunta da jajayen idanuwanshi ya yi jarumtar faɗin

"Magana zan yi da ke fa"

Dije ta waigo cike da mamakin jin muryarshi a tausashe ta ƙwace hannunta tare da gyara tsayuwarta ta rungume hannuwa tana wani cin magani, cikin ko in kula ya ɗauki kofin tean ya kurɓa sannan ya ajiye ya kalleta yace

"Zama zaki yi ba tsaye zaki yi man a kai ba"

Dije ta zauna kan kujerar nesa kaɗan da shi ba tare da tace ƙanzil ba, ya maka mata wata harara yace

"Au tsaranki ne ni kenan da zan zauna kan kujera ke ma ki zauna?"

Dije ta yi kamar ba zata sauka ba cikin fushi ya ce "ba da ke nake magana ba ne?"

Ta sauko da sauri tana gunguni ƙasa ƙasa ya bi bakinta da kallo tare da ƙara haɗe fuska yace,. "Ni kike zagi?"

Ta yi saurin kallonshi ta murguɗa masa baki tace,. "Idan ba zaka faɗi maganarka ba ni tafiya zanyi"

Ya yi mata wani kallo yace, "Ok to ko zaki gwada tafiyar ne?"

Dije ta yi masa wani kallon reni duk da tana jin tsoronshi haka ta miƙe da nufin fitar, ya yi saurin miƙewa ya sawa ɗakin key ya zare ya ƙaraso gabanta ya tsaya yana zuƙar shayin yana kallonta har ya gama ya miƙa mata kofin ta ƙi karɓa, ya saka ƙafarshi ya take ƙafarta da ƙarfi tare da rungumota da hannu ɗaya ya matse mata gefen ciki da ƙarfi, sai gata da fasa wata ƙara saboda azabar da ta ziyarceta ba shiri, ta yi saurin karɓar kofin amman yaƙi bata damar ta ajiye kamar yanda yake so, cikin sigar mugunta ya saka ɗayan hannunshi ya ɗago fuskarta daf da tashi, yana ƙare mata kallon ido cikin ido sannan ya yi wani shu'umin murmushi yace

"Ni zaki kawowa ƙananun rashin kunyar da kika saba yi ko? To wannan karon da kanki zaki gano cewa ni ba sa'ar wasarki bane, idan kin ajiye rashin mutuncin kin tsira don zaki taimaki kanki, idan kuma kika ce zaki yi jayayya da ni to ke ce a wahale"

Dije ta yi saurin fisge kanta tana yi masa wani kallo ranta a matuƙar ɓace tace, "ba nace kada ka sake taɓa jikina ba ne? to WALLAHi wannan karon sai na faɗawa Hajiya duk abunda kake yi man"

Safwan ya bita da wani guntun mere sannan ya fashe da wata munafukar dariya ya ce "to bari in baki saƙon idan kin je sai ki sanar da ita"

Cikin mugunta ya fisgo kanta har ɗankwalinta ya faɗi gashinta da ke cikin ribom ya fito saboda faɗuwar da ribom ɗin ya yi, Safwan cikin fitar hayyaci ya damƙo gashin ya ɗago fuskarta tare da kai bakinshi cikin nata kamar wani maye, haka ya dinga tsotse leɓenta yana wata irin tsotsar fitar hankali tamkar wanda aka baiwa umurnin ya rabata da leɓunan duka, Dije tana zubar hawayen azaba tana dukanshi iya ƙarfinta amman hakan bai hanashi yin abunda yake yi ba, tun tana ɗaukar abun wasa har ta fara sarewa da lamarinshi,cikin zafin nana ta yi jarumtar turashi baya kasancewar gaba ɗaya a kasalance yake, hakan ya bata damar ƙwatar kanta tana kuka tana shafa leben da take tsammanin ma ya yi jini.

Ganin babu jinin yasa ta kalleshi kallo mai cike da tsana tace, "WALLAHi wannan karon sai kasan ni kake ciwa amana"

Cikin fushi ta nufi ƙofar ɗakin da nufin buɗewa ta tuno da cewa rufe yake, ta dawo gabanshi ta tsaya tana faɗin "ka buɗe man in fita tun kafin in tara maka jama'a WALLAHi"

Safwan ya ɗago da jajayen idanuwanshi da suka so baiwa Dije tsoro cikin dakiya tace

"Zaka buɗe ko kuwa har sai na yi maka abunda za'a kaika asibiti yanzun nan?"

Ya yi guntun murmushi cikin wata siriryar murya yace

"To ki jira inyi abunda ko da kin yi nasarar kaini Asibitin ba zan ji haushin jinyar ba saboda na fanshe haushina"

Ya nufo kanta ta yi baya cikin tsananin tsoro amman bai fasa nufota ba ganin da gaske yake yi wata cutar zai sake yi mata yasa ta maƙe jikin bango tana faɗin

"Don Allah Malam ka yi haƙuri WALLAHi bana son abunda kake yi man ka ji tsoron ALLAh kada ya kamaka da laifin cin amanar iyayena da kake son yi"

Safwan bai fasa zuwa wurinta ba asali ma hannunshi duka biyu ya saka ya rungumota tare da shafo dukiyar fulaninta, a ɗimauce ya zuge mata zif ya dinga wasa da su son ranshi, Dije kam gaba ɗaya wani masifar tsoro ne ya sake ziyartarta tare da azabar da take ji, Malam Safwanu kam ganin tsoro akan fuskarta yasa ya daina ƙawata son zuciyarshi da laushin fatarta, ya shafo himilin gashinta ya ɗora kanshi saman kanta ya shaƙo ƙamshin mayukan da aka shafe gashin da shi, ba shiri ya lumshe idonshi tare da ƙara ƙankameta jikinshi ya sauke wata ajiyar zuciya, Dije kam saboda kukan da ya ci ƙarfinta kasa ƙwatar kanta ta yi, ƙarshe ma sulalewa ta yi ƙasa ta durƙushe tana wani irin kuka gwanin ban tausayi, saboda ganin take yi ba ƙaramin saɓon Allah bane Safwan yake aikatawa, ya yi saurin durƙusowa gabanta yana ƙare mata kallo zuciyarshi cike da jin haushin kanshi, amman cikin dakiya ya haɗe fuska yace

"Zaki yi wa mutane shiru ko kuwa sai kin janyo na lallasaki yanzun nan?, To bari kiji kinga wannan abun da na yi maki WALLAHI ubanshi zanyi matuƙar Matar da zan aure ta zo gidan nan kika yi mata rashin kunya, ko kuma kika nuna cewa ma wai kin sanni a gabanta, don ko da wasa kika nuna cewa akwai wata alaƙa tsakanina da ke sai kinsan kin aikata hakan, ke ko da ma ace kinji an faɗa a gabanki to kiyi gaggawar ƙaryata hakan gareta, idan ba haka ba WALLAHi abunda zan yi maki sai ya fi wannan muni, idan kuma kina ganin zancena faɗa ne kawai to ki fallasa wannan sirrin ina jiranki"

Yana ƙare faɗar maganar ya buɗe ɗakin ya fice zuciyarshi fes yake ji tamkar an sauke masa wani ƙaton ɗutsi a saman kai, don yasan tsoron da ya baiwa Dijen ba zai bari ta yi masa wani shirme ba idan Zee ta zo, don daman fargabarshi ɗaya ita don yasanta sarai da salon rashin kunyarta tsaf zata yanyo kwaɓarshi ta yi ruwa.

Tsabar takaicin abunda ya yi mata ne yasa ta kasa barin ɗakin, ta ci gaba da kukanta sannan daga baya ta lallashi kanta ta yi ƙoƙarin saita kanta ta kimtsa jikinta ta fito ɗakin, tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki ta yi sashen masu aiki don bata so Hajiya ko wani ya tambayeta me ta yi wa kuka, don bata san da wane ido zata kallesu ta sanar da su irin cin mutuncin da Safwan ɗin ya yi wa addini ba.

Ko da ƙarfe huɗu tayi mutane da yawa sun fara shirin zuwa mother's day, don Safwan kanshi ma ya shirye tsaf sai tashin ƙamshi yake yi saboda murnar zuwan Zee da ke kan hanyar gidan ita da ƙawarta Ruma, da kanshi ya je ya sanarwa Hajiya zai je ya taro su Zee kada ta fita zai je ya kawosu gidan su gaisa kafin su wuce wajen event ɗin, cike da walwala ta nuna masa farin cikinta don ta nuna masa bata da mu ba, duk da cikin zuciyarta cike take fam da takaicin rashin sanin ciyon kanshi da bai yi ba, sai dai kuma idan ta tuna yanda yanzu yake ta nuna kulawarshi akan Dijen sai ta gode wa ALLAH saboda ganin addu'arta ta fara karɓuwa.

Dije kam ta shirya tsaf cikin ƴanmata sai tashin ƙamshi take yi duk da kasancewar zuciyarta ba daɗi, amman hakan bai hanata tsara shigarta irinta wayayyun ƴan boko ba, don kuwa takanas Surayya ta ce da mai mata kwalliya ta gyara Dijen tamkar yanda zata gyarata, saboda tana son Zee ɗin ta gano itama Dijen ba baya ba ce don kar ta Renata, cikin ikon Allah ko sai ga Dije ta fito ras da ita tamkar ka saceta ka tsere don kyau, ga doguwar rigar fitted gawn ce ta Kama jikinta sosai ko'ina ya fito tsantsan, musamman hips ɗinta da ƙirjinta da suka fito raɗam a cikin rigar, idan baka sani ba zaka ɗauka cewa ma itace Amaryar, don komi irin na Amare aka yi mata har ɗaurin head ɗin da aka yi mata ma wani style ne a saman kanta, aiko Dije sai jinta take yi wata higher class tamkar ba ƴar secondary ba, saboda a lokacin tana da shekara sha shida amman yanayinta zai sa ka ga tamkar tafi hakan saboda tsabar kauɗinta.

Hajiya Mama kanta da ta ganta ba ƙaramin daɗi ta ji ba a ranta ku ta yaba kwalliyar sosai.

Motocin suka fara kwasar mutane zuwa wajen da za'a yi bikin, manyan mata hamshaƙai haka suka yi ta shigowa gidan da motocinsu suna gaisawa da Hajiyar suna wucewa wajen da za'a yi taron, gidan ya rage ba wasu mutane da yawa sai Amarya da ƙawayenta a falo sunata shirinsu ana ƙara gyara amaryar.

Sai ga Safwan da Zee'nshi tare da ƙawarta sun yi sallama sun shigo, Fiddo ta yi wani tsallen jin daɗi ta nufesu tana faɗin

"Oyoyo Auntynmu"

Kasancewar tasanta a hoto yasa ta je wajenta ta rungumeta, Dije tana ganinsu wani faɗuwar gaba ya ziyarceta, kai tsaye wata dubara ta zo mata don ta tabbatar da lalle itace budurwarshi da yake yi mata kashedi akanta baya son tasan tsakaninsu, ta yi wani murmushin mai cike da ma'anoni ta taso tana wani taku cikin wani salo ta sha gabansu duka ta tsaya, tana yi wa Safwan wani shu'umin kallon cikin shagwaɓa tace

"Haba Husby Ina ta jiranka ka zo ka ga kwalliyata tun kafin ta goge shine sai yanzu ka dawo gidan"

Ta jujjuya gaba da baya sannan ta tako gabanshi ta ɗora hannunta ɗaya a kafaɗarshi duk da ya fita tsawo sosai, ta shafo fuskarshi da ɗaya hannun ta yi fari da ido tace,.

"To yanzu ya ka ganni na yi kyau ko kuwa da wani gyara in je in gyara?"

Cikin tashin hankali Zee ta kalleshi cikin hargitsewar tunani, nan take wani jiri ya kwasheta ta yi baya ba shiri ƙawarta ta yi saurin riƙota tare da yi mata kashedi da ido, amman duk da hakan ta kasa natsuwar da ƙawarta take so ta yi saboda masifar kishinshi da ya rufeta, don son Safwan da kishinshi a jininta yake ko da basu tare bale yanzu da aka janyo zuwanshi ta ƙarfin tsiya.



Ina team Zee ku zo ku riƙe Zee don kar ta faɗi yasin ni dai na yi nan babu ruwana🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️😝



*Hmmmm! Rashin COMMENTS zai janyo fushin Alƙalamina, da ya ɗauke yasin zaku jini ɗif kamar an ɗauke wuta😚, idan banga sauyi ba daga yau zan shiga hutun sabuwar Shekara😼*





Akafta🤣








D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*



*Lalle yau kwalliya ta biya kuɗin sabulu💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 yasin yau kun faranta man fiye da tunaninku🥰 don haka ga nawa tukuici nan gareku masoya Dije Ƙarangiya all, ku ma ku ji daɗi kamar yanda na ji, ku daɗe ku yi lasting mutanena gaba ɗayanku ina yinku sosai ba shakka👍🏻*



*Lamba ta 46*


Safwan mamaki da al'ajabin da ta bashi ne yasashi daskarewa ko motsi ya kasa yi bale ya yi wani yunƙurin kare kanshi, illah kallon Zee da yake yi yana girgiza kai, ganin hakan yasa Fiddo ta yi saurin riƙo hannun Zee tace

"Zo mu je ciki ku gaisa da Hajiyarmu Aunty, wannan da kike gani ba kowa ba ce face ƙaskantacciyar ƴar aikinmu, dubarta da kyau ki gani bagidajiya ce usuli ƴar ƙauyen ƙayau, ta nace akan dole sai yaya Safwan ya aureta bayan kuma shi ko kaɗan baya sonta"

Ta janyo hannun Zee ta yi wa Dije wani kallo ta buga mata ƙaton tsaki tace, " mtsss! Mayya kawai"

Zee tana yi tana waigenshi zuciyarta cike da ƙunar baƙin cikin da Dije ta sakar mata, sai wassafa yanda zata shaƙe Dijen take yi a ranta har sai ta ɗauke numfashi sannan ta saketa, har suka isa ɗakin Hajiyar suka zauna bata san ma sun je ba, sai da ta ji Fiddo tana gabatar da ita ga wata Auntynsu sannan ta dawo hankalinta ta fara sunne kai tana gayar da su.

Safwan kam shigewar su Zee ciki yayi dai dai da dawowar natsuwarshi, ya kai kallonshi ga inda yake tsammanin ganin Dijen sai dai kuma wayam bata nan, ya wara idanuwanshi a masifance domin ya hango ta ina zai ganta ya sauke fushinshi akanta, sai dai kuma bata ba dalilinta a falon duka, a harzuƙe ya yi wurin Surayya yace

"Ina magen yarinyar cen ta tafi???"

Sury cikin firgici tace

"WALLAHi Ni ma bansan inda ta je ba yayanmu"

Safwan ya kaiwa iska duka sannan ya bar wajen ya sake dawowa ya ce da ita, "to ki yi gaggawar dubo man ita yanzun nan idan ba haka ba WALLAHi yau daga ke har ita sai kun san dani kuke zance"

Cikin rawar jiki Surry ta miƙe ta yi ɗakinsu domin ta gani Dijen tana cen ko kuwa, sai dai ta duba ko'ina Dijen bata gidan take ta sanar da shi yana huci ya yi wurin Hajiya, sai dai tuno ɗakin da mutane yasa ya ja ribas dole tare da furzo iska mai zafi a bakinshi yana wani bubbuga kanshi alamun ta saka shi a tension da yawa.

Yana nan tsaye sai ga Fiddo ta fito tare da su Zee tana ganinshi ta yi saurin zuwa wurinshi tace, "big bros WALLAHi yau idan ka kama yarinyar nan ka ci ubanta da kyau da kyau, don ni kaina yau sai na tayaka mun ci uban shegiya......"

Kallon da Safwan ɗin ya yi mata ne yasa ta yi saurin cewa da su Zee "Aunty ku zo mu je ku ci abincin kafin mu je wajen da za'a yi event ɗin"

Zee ta yatsina fuska ta kalli Safwan tace,

"Barshi kawai Ƙanwata ni yanzu ma zamu koma gida"

Safwan ya yi saurin zaro ido cikin wani sabon tashin hankali ya marairece fuska yace, "Sorry Unique ke ma kinsan ke ce dream ɗina safe da rana, ke ce wadda nike mafalkin aure a kowane lokaci, wannan yarinyar ba kowa ba ce a wurinmu face ƴar aiki kamar yanda kika ji Fiddo ta sanar da ke tun farko"

Zee ta yi masa wani arnen kallo mai cike da ma'anoni sannan ta nufi hanyar fita ƙawarta ta riƙo hannunta, cikin wayancewa ta ce da Fiddo mu je ki kaimu wajen da za'a yi bikin, Fiddo cike da damuwa ta ce "to ku yi haƙuri ku ci abincin mana kunga kun kwaso tafiya ga shi ko ruwa ma baku sha ba"

Ƙawarta Ruma ta yi murmushi ta ce "ok to mu

Please Login or Register in order to submit comment