Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni ka bani hanya inga Jummalar tun kafin ka kasheta ka raba ganawar tamu"

Garbati ya yi maka mata wata harara tare da riƙe ƙofar yace,. "Sannu uwar Jummala to bari kiji WALLAHI da kin kawo iskanci har ki bar garin nan bazan taɓa barinki ki ga matata ba, don na sanki sarai da baƙin halinki tsaf zaki hure mata kunne ta bijire mani, bayan namijin ƙoƙarin da aka yi akan shawo kan matsalarta, don haka ki sani kika kuskura naji wani abu daga baya to ki sani duk garin nan ba mai hanani yin ƙasa ƙasa da ke idan na tashi gwada maki haukata"

Dije ta riƙe ƙugu tana maka masa wata harara sama da ƙasa tace,. "A tsammaninka share shayen da ka fara zai tsoratani ne?? To ka yi kuskure don kuwa Dijen Baffah tana nan yanda ka santa har ma da ƙarin wani ilimin baƙin halin da na ƙaro, zaka bani hanya in gano Ƙawata ko sai na fara nuna maka kalar baƙaƙen halayen nawa??"

Garbati ba shiri ya tuntsure da wata arniyar dariya yace,. "Ana iya shege a duniya yasin to ke Dije halan ance maki ni lusari ne kamar Tambari da kika renawa hankali?, To ni......"

Fitowar Jummalar ne ya sa shi yin shiru saboda turenshi da tayi da hannu biyu ta fito tana share hawaye ta janyo hannun Dijen suka shiga cikin ɗakin, Garbati ya bita da kallo yace

"Yanzu Jummala ni kika yi wa haka akan Dije?? Lalle kam yau sai kin nemi mai ƙwatarki hannuna"

Dije ta ɗaga murya tace, "ALLAH ya fika Garbati"

Jummala kam juyowa ta yi ta murguɗa masa baki wanda hakan da ta yi ba ƙaramar dariya ta bashi ba, ya sosa kanshi ya fice sannan su Mune suka shigo ɗakin su ma kowane da abunda zuciyarshi take ƙissima mashi.

Dije ta zauna kan gadon Jummala tana ƙare mata kallon mamakin yanda duk ta bi ta firgice ta rame saboda zalamar Garbati, ta riƙo hannunta tace

"Ƙawata baki da lafiya ne halan? Naga duk kin canza ba yanda na sanki ba"

Jummala ta kalli Mune da Lanti ta share hawayenta sannab tace,. "Ba komi"

Dije fahimtar tana son ta sanar da ita amman bata son su Mune su sani yasa ta ce da su Munen, "Don Allah Lanti ku jirani a waje zamu yi magana da Jummala kunji?, Kar fa kuji haushi kunsan komi yana buƙatar sirri"

Lanti kasancewar tasan saboda Mune ne yasa Jummala bata son fayyace sirrinta yasa ta miƙe ta fice, Mune ta taɓe baki ta miƙe ta fice tana gungunin faɗin

"To ALLAH na tuba mu miye ma ne bamu sani ba?"

Suna fita Jummala ta fashe da kuka Dije ta fara lallashinta tana faɗin,. "Ki yi haƙuri Jummala ki sanar dani matsalarki da kaina zan je wajen Maigari in sanar da shi aka maki haƙƙinki"

Jummala ta share hawayenta tace,. "Ai ba abunda za'a iya yi akan matsalata Dije saboda Garbati ya riga da ya sami ɗaurin gindinsu Babana, don asali ma sune suka bashi damar da har ya dinga yi man abunda yake man"

Kan Dije ya ƙulle da zancen Jummala cikin rashin fahimtar inda ta dosa tace,. "Wace dama ce suka bashi halan?? Gaske dai naga yana wata gadara ashe wuri ya samu"

Jummala ta saka gefen ɗankwalinta ta shafe fuskarta ta ce,. "Tun ranar da aka kawoni gidan nan ya fara bijiro mani da wani sabon iskanci, ganin da gaske yake yi yasa na ƙwaci kaina da ƙarfin tsiya na gudu gidanmu, amman tun cikin daren aka dawo masa dani, ke in taƙaice maki labari na jera sati ɗaya ina guduwa cikin dare ana dawo dani, a ranar da na cika kwana takwas a gidan nan ne Baba Ɗanliti ya zo da ƙatuwar igiyar ya ɗaureni kan gadon nan ta ko'ina, yanda ko motsin kirki bana iya yi bayan ya gama dukana yanata zagina, haka ya fice ya ce da Garbati duk abunda yake so ya yi dani kar ya ji tausayina, Garbati ganin wannan damar da ya samu yasa bai ji kunyar ALLAH ba ya yi ta cin zalina, ina kuka ina ihu amman bai ji tausayina ba ko kaɗan asali ma haka na kwana ɗauren, sai da safe ya kwance ni haka kullum dare Baba Ɗanliti yake zuwa yana ɗaureni har tsawon kwana uku sannan aka daina ɗaureni, shi kuma Garbati baya jin kunyar ALLAH baya tsoron aradu ta faɗo masa har yanzu bai fasa abunda ya ke yi ba"

Dije tace

"Ni Jummala har kinsa jikina ya yi sanyi WALLAHi, saboda nasan Baba Ɗanliti mutum ne shi mai kirki banyi tsammanin haka daga wajenshi ba, amman ki yi haƙuri tunda har kika ga anata dawo dake idan kin gudu to ana son ki zauna ne, don haka don Allah ki daina ihun da kike yi kina tonawa Mijinki asiri tunda har baya barin cin zalinki, insha ALLAHu watarana ko ance ya yi ma ba zai yi ba tunda har nasan yana sonki Jummala, ki ɗauka cewa ko yanzu sharrin sheɗan ne da kuma shaye shayen da ya fara"

Jummala ta yi saurin kallonta tace,. "Wa ya gaya maki yana shaye shaye ne?!"

Dije tace,. "Ke baki ga idonshi bane yanda suka koma jajjaye??"

Jummala ta yi saurin faɗin,. "WALLAHI Garbati baya shaye shaye don ko taba ma ban taɓa ganin yana busawa ba, wani lokaci dai ne nake ganin idanuwan suna komawa hakan ɗin, amman kuma daga baya sai su koma dai dai"

Dije tace "to ki yi haƙuri ni dai don ALLAH Jummala tunda dai ke ma fa kina son Garbati"

Jummala ta ce "in don so kam ina sonshi Dije amman abunda yake yi man ne bana so, sai inga kamar da mun mutu wuta ALLAH zai jefamu"

Dije ta miƙe tsaye tace,. "Ni dai haƙuri nike baki kuma ina baki shawarar ki daina ihu da kuwwar da kike yi ki barshi da ALLAH shi zai saka maki, don WALLAHI har an fara gulmarki a garin nan namu akan gudun da kike yi kina iface iface"

Jummala ta zaro ido waje tace,. "Na shiga uku Dije da gaske kike yi? Ashe ana jina wai ni ALLAH, gaske naga watarana yara suna zuwa gidan nan da sun kalleni suyi ta dariya"

Dije tace,. "Kaɗan ma kenan idan baki daina ba har sai kin fita kinji ana faɗin ga Jummala mai ihu cikin dare"

Jummala ta rufe baki tace,. "Aiko idan zai kasheni a gidan nan ba zan sake ihu har ajiyoni ba"

Dije tana saka talkaminta tace,. "Yafi maki dai ko don gudun gori watarana, tare da ƙananan gulmar masu yawan surutu"

Su Lanti da Mune suka taso ran Mune a jagule saboda ranta ya bata cewa da ita Dijen take, shiyasa ta yi saurin nufar hanyar fita tana faɗin

"Ni dai kunga tafiyata daman aikena aka yi na biyeku"

Dije tace,. "ALLAH ya kiyaye Mune sai mun haɗu gidanmu ko? ko shikenan daga nan munyi sallamar har in bar garin"

Mune ta washe baki tace,. "Rufani ki saya anjima kaɗan ma zan sameki gidan Gambon, bari dai in je inda aka aikeni in dawo"

Ta fice Jummala da Lanti suka ƙyalƙyale da dariya, Dije ma tana dariyar tace

"Mune mutunniyata ALLAH ya nuna mani ta daina halinta da naji daɗi"

Sannan Jummala ta rakosu har bakin gidan tana ƙarewa Dije kallo tace,. "Ashe gani duhu na yi maki ƙawallita, kinga yanda kika yi kyawonki masha ALLAH har da wasu kumatu kika fara yi, lalle birni ta karɓeki WALLAHi watarana ma ko ganeki nasan ba zamu yi ba"




Ke kika ce haka Jummala balle ni Dijen😝😂







Akafta🤣




D/AUTA Ce✍🏻




*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*AM BACK MY FAN'S albishirinku Littafina na BAƘON YANAYI na sakeshi free ga kowa, duk mai buƙata ya nemeni insha ALLAHu zan bashi kyauta ba sai ka biya ƙwandala ba, fatana kawai ku bini da ruwan addu'oinku kamar yanda kuka saba, ina yinku sosai alkhairin ALLAH ya kai maku duk inda kuke masoyana👍🏻*



*Lamba ta 39*


Dije ta ƙyalƙyale da dariya tace,. "Haba Jummala ai duk inda na shiga ba zaki ce ki kasa ganeni ba, ballantana ma ai fuskata ba canzawa zata yi ba, ita ɗin dai ce wadda kika sani don haka ki ma daina wannan zancen, insha ALLAHu ni da ku mutu ka raba ƙawayena don kar ku ga wai don na je birni ku zaci watarana zan manta da ku, saboda komi na zama ai bazan taɓa mance Asalina ba, kuma muddin na tuno gida dole ne ku ma in tuno da ku, ni dai yanzu fatana kawai ki riƙe abunda na faɗa maki duk runtsi kada ki bari wani ya ji sirrin Mijinki, ALLAH ya baku zaman lafiya"

Jummala da Lanti suka ce "Ameen" ta rakosu har ƙofar gida tana ɗagawa Dije hannu tace

"Amman dai zaki dawo kafin ki koma ko?"

Dije tana shirin yin magana kenan suka jiyo muryar Garbati yana faɗin,. "Ta dawo ina? Ai ko wannan don kawai na so ne da WALLAHi ba zatan bata damar yin magana da ke ba, wannan ziyarar ma da aka kawo mun gode da ita, ina fatar ALLAH ya sa ba'a jangwalo man abunda zai fi ƙarfina ba"

Dije ta kalleshi sama da ƙasa tace,,,, "ka ma godewa ALLAH da har na zo na gyara abunda ka kasa gyarawa da kanka, idan ka ji tsoron Allah ka rage cin zalinta shikenan ka taimaki kanka, ni ka ga tafiyata don nasan darajar aurena bazan biyeka muna sa'insa ba"

Tana ƙare faɗar haka ta buga masa tsaki ta wuce abinta,Jummala ta ɗaga murya tace,

"Na gode Dije ALLAH ya biya sai kin dawo ai mun yi sallama ko?"

Dije ta ci gaba da tafiyarta ba tare da ta juyo ba ta ɗago mata hannu tace,

"Eh" Lanti ce kawai ta ce,, "to ya yi sai mun dawo jummala"

Suna tafe Lanti tana bata haƙuri akan abinda Garbatin ya yi mata, Dije saboda haushinshi ƙanzil ma kasa cewa ta yi har suka isa gidan Inna Gambo.

Yanayin yanda Gambon ta ganta yasa ta yi saurin faɗin,. "Wa ya taɓo mani Dijengalata ne? Daga zuwanta za'a fara ɗaga mata hankali"

Dije ta janyo tabarma ta zauna ta ce da Lanti itama ta zauna, bayan sun gaisa ne tace

"Wai ni kam Gambo yaushe Garbati ya koma haka ne??"

Gambo ta ce "tooh! Ke kuma Dije me ya haɗaki da Garbati ne?, Ko kin manta cewa da da yanzu ba ɗaya bane?"

Dije ta taɓe baki tace,

"Ai ni Gambo ba ruwana da sabgarshi shine dai yake son shige mani hanci, don Ni WALLAHI in Banda Jummala da ba abunda zai sa ma in ganshi in yi masa magana, saboda baƙar muguntar da yake yi wa Jummala don ya ga ita ba zata iya ramawa ba, don WALLAHI ALLAH in nice a dare ɗaya zan ji masa rauni"

Ta ƙare maganar tare da bubbuga hannunta tana dukan tabarma alamun da gaske take zancenta, Gambo ta yi mata wani kallo tana mere Baki tace

" To ko ke ɗin ce me zaki iya yi? Ballantana ma ni ina maki addu'ar ALLAH ya rabaki da wannan mugun hali irin na Jummala, Ai babu sakaryar yarinya irin wannan yarinya da bata da aiki sai tonawa kai asiri, saboda a garin nan ma mu yaushe rabonmu da wannan abun kunyar da haukar da take yi ne?, Ai ni WALLAHi ya biyani ma da ya ke koya mata hankali tunda har ita ta zama mara rufin asiri"

Dije ta bi Gambo da kallon baki san dawan garin ba ne, duk da wani gefe na zuciyarta kuma tana son ƙarin bayani akan zancen nata, ta sauke ajiyar zuciya tace,. "Ke dai Gambo don baki san irin cutar da yake yi mata bane, don ke kanki kinsan Jummala ba ruwanta abun ne ya yi mata yawa shiyasa ta kasa haƙuri"

Gambo ta yi mata wani kallo tace, "To karkaɗe kunnuwanki da kyau kiji Jummala sam bata kyautawa kanta ba, saboda halinta na rashin haƙuri ne ya janyo komi, ina laifin Garbati don ya nemi yin kwanan aure da ita?, Mitssss! Ni bari inje in kawo maku fura ku sha ya fi man wannan magana mai cike da abun haushi"

Dije ta yi tagumi tanata nanata kalmar kwanan Aure a ranta don kawai ta gano ma'anarshi, amman ta kasa cikin zuciyarta tace

_"To ni kam wane kwanan Aure ne haka wanda har ake cin zalin mutum a kanshi?, wai ko dai Gambo bata gano abinda nake nufi ba ne shiyasa....."_

Hushin numfashin Gambon ne da taji a kusa da ita yasa ta yi saurin cire tagumin da tayi tana faɗin,. "Ni fa Gambo bana shan furar nan a ƙoshe nake"

Gambo ta maka mata harara tace,. "Ita furar ce yau bazaki sha ba Dije? Tab! Lalle birni ya sa kin fara canzawa, yanzu furar da har kokawa muke yi da ke akan sai kinsha ina ba zaki sha ba itace yau na baki a arha kike gwasaleni? To ai in ke ba zaki sha ba ke Lanti karɓi ki sha tunda dai nasan ba zaki ƙi cimarmu ba ke"

Gambo tana ƙoƙarin miƙawa Lanti furar Dije ta yi saurin riƙe kwanon tana turo baki tace,. "Ni dai bani in sha don naga kina ƙoƙarin ki canza man manufata"

Gambo ta buge hannunta Dije ta sake riƙe kwanon tana dariya tace,. "Sai fa na sha Gambo kafin ki bata tunda har ni kika fara yi wa tayi tun farko"

Gambo ta sakar mata tana faɗin,. "In banda ina tsoron ki janyo man asarar furar da ko lasata ba zaki yi ba, wai ma me ya janyo shi mijin naki da zai tafi ƙasar wajen bai je da ke ba??"

Dije ta kai ludayin fura bakinta tana faɗin, "sha kuruminki ko yanzu idan ya dawo tare zamu koma sai kinyi shekara biyar baki ganni ba, balle har ki yi man kora da hali, don haka ki rubuta ki ajiye sai kin nemi ganina da kuɗinki baki ganni ba, don ma ko da zan dawo na koma baturiya bazaki gane ni ba"

Gambo da Lanti suka fashe da dariya, cikin dariyar Gambo tace,. "sannu turawa masu jajayen kunnuwa sai dai kuma ke gashi naki baƙaƙe ne, to ko ya za'a zamo baturiyar da kunne baƙi Oho!?"

Haka suka ci gaba da firarsu mai cike da barkwanci suna dariya har aka aiko kiran Lanti daga gidansu, bayan tafiyarta ne Dije tana wasa da kare tana zane a ƙasa tace da Gambo,. "Wai ni kam Gambo in tambayeki? minene kwanan Aure da naji ɗazu kin faɗa?"

Gambo ta yi shiru na ɗan lokaci sannan tace,. "Yanzu ke baki san kwanan auren ba??"

Dije ta na dariya tace,. "Da na sani Gambo me zai sa in tambayeki? Ko yanzu abunda yasa na tambaya don bana son ya fito a jarabawarmu ta hausa ne ko wata rana wani ya tambayeni ya gano ban sani ba??"

Gambo tace,. "Hu'umm yanzu ke baki taɓa yin kwanan auren ba kike nufi ko yaya?"

Dije ta yi shiru sannan tace, "To ba bama sai in na sanshi ba sannan zanyi"

Gambo ta yi saurin cewa,. "Baki taɓa kwana ɗaki ɗaya da Mijinki ba?" Ta yi shiru tana nazari sannan tace "eh to na taɓa sau ɗaya lokacin da Hajiya ta matsa naje ɗakin Malaminmu na kwana, amman ni bansan me hakan yake nufi ba"

Gambo tace "To yanzu ki adana tambayarki kar ki yi ta da kowa sai Mijinki idan har ALLAH ya dawo da shi lafiya, kar ki mance ki tambayeshi ki ji menene kwanan Auren?, Insha ALLAHu da kanshi zai warware maki zare da abawa, don na tabbata shi yasan me hakan yake nufi, amman fa kar ki sake ki tambayi kowa sai shi kin ji ko?"

Dije ta ɗaga kai cikin rashin fahimtar inda ta dosa, amman har dare bata daina tunanin kalmar kwanan Auren ba, in ta canko wannan ta canko wancen har ta gaji ta jefar duka, duk da ta so ace ta tambayi Inna Hasiya amman da ta tuno da gargaɗin da Gambo ta yi mata sai ta fasa.

Tun cikin daren ranar Inna ta fara haɗa wainar farar shinkafar da Usmanu ya siyo daga birni, madadin Geron da Baffah ya ce ayi da shi.

Aiko tun da sassafe ta fara tuyar wainar Dije tana tayata har suka gama, aka bi gida gida da wainar ana rabawa mutane sai sambarka suke yi, don ko Maigarin sai da aka cika masa ƙaton kwano da waina da miya har da manshanu aka kai masa gida yana ta godiya.

Mutane sai shigowa suke yi ana yi wa Dije Barka da zuwa ana yi wa su Inna godiyar tsaraba, duk da wasu da yawa ma gulma ce take kawosu don su ganewa idonsu yanda Dijen ta koma, sai dai yanda take ta gayar da su ne a mutunce yasa suka fara ajiye gulmarsu, don mafi akasarin masu shigowar sun jinjina yanda Dijen take gayar da su cikin ladabin da basu santa da shi ba, uwa uba yanda suka ga jikinta ya murje kyawonta ya ƙara fitowa duk da take baƙar fata.

Kwanan Dije biyar a garin sai ga Abinci Garbati da kanshi ya yi sallama har ƙofar gidansu Dijen ya kawowa Dije inji Jummala, mamaki fal ranta daga ita har Inna saboda ta bata labarin abunda ya faru tsakaninsu, don ma tsabar renin hankali har da cewa wai don ALLAH ta je Jummala tana son ganinta, Dije tana ganin Inna ta shige bayi ta yi ficewa ta kira yaron da Garbati ya baiwa ya kawo mata abincin har ya yi nisa, ta miƙa masa tace ya je yace da shi bata so ai ita ba mayunwaciya ba ce.

Yaron ya karɓa ya tafi ta tsaya soron tana jiran dawowarshi don kada ma Inna ta ji ta yi faɗan me yasa ta mayar, aiko madadin ta ga yaron sai ga shi ta ji sallamar Garbati, ta yi saurin fitowa ta tsaya gaban Garbatin ta riƙe ƙugu tana girgiza ƙafa tace

"Yawwa daman ai kai nike jira abincin me ne ka kawo man? ance maka ina da yunwa ne ko kuwa??"

Garbati ya marairece fuska ya ce,. "Nasan nayi maki abunda bai kamata ba amman don ALLAH ki yi haƙuri, WALLAHi naji daɗin zuwanki wurin Jummala kin ga yanzu zamanmu muke yi lami lafiya, WALLAHi na gode sosai da ƙoƙarinki ALLAH ya biyaki da gidan Aljannah"

Dije dole ta ajiye makaman rashin kunyar da ta tanadar masa tace,. ,"Na yafe amman ku bar abincinku na gode"

Tana ƙare faɗar haka ta koma gida abunta, Garbati bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen sake nemo yaro ya ƙara aika mata da abincin sannan ya tafiyarshi, zuciyarshi cike da jin haushin mummunar fassarar da ya yi mata.







Dama ka bani idan bata so ni ina ci😔






Akafta😆







D/AUTA Ce✍🏻


*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*AM BACK MY FAN'S😉*



*Lamba ta 40*



Shigar yaron ya yi dai dai da fitowar Inna daga bayi, cike da mamaki ta bi Dije da kallo har yaron ya ajiye kwanon abincin ya fice, Inna zata yi magana Dije ta yi saurin faɗin

"Mayar masa da abincinsu na yi shine ya dawo da shi"

Inna ta ɓata fuska tace,. "Ba'a mayar da hannun kyauta baya ko baza ki ciki ba sai ki kyautar ya fi da ace ki maida"

Dije ta miƙe tsaye tana dariya tace,. "Bale ma zan ci ai abincin Jummala ne don haka zan ci inji in ta iya girkin"

Inna ta maka mata harara tace,. "Au kina ma so amman shine kika mayar? to ALLAH ya kyauta amman ko ba yanzu ki daina mayar da hannun kyauta don wannan yana daga cikin aikin sheɗan"

Dije tana wanke hannunta tace "insha ALLAHU Inna bazan sake ba, yanzun ma don ya gano naji haushin abunda ya yi mani ne"

Dije ta zauna ta fara cin abincin tana yi tana rawa da kai tace "Inna ko ashe da gaske Jummala ta iya girkin"

Inna ta yi banza da ita kamar bata ji ta ba har sai da ta gama sannan tace da ita, "Shin wai ke kin fara koyon abincin ƴan'birnin ko kuwa har yanzu irin namu ne kawai kika iya? "

Dije tana lashe hannunta tace, "Ni fa Inna Makaranta nike zuwa kuma a cen ma muke kwana har sai anyi hutu nake dawowa gidan, kuma idan na dawo Hajiya bata bari in yi wani aikin wahala, cewa take yi wai in huta kafin in ƙara girma sai a fara koya man girkin"


Inna ta yi shiru sannan tace,. "Idan kin koma ki dinga shiga cikin masu dafuwar abincin gidan kina kallon yanda suke girkinsu, ko da tace ki zauna ki huta ki ce da ita ke kina son ki iya kinji ko? Sannan ita kanta ki dinga share mata ɗakinta kina gyarashi tsaf tsaf yanda kika ga ana yi mata"

Dije ta ɓata fuska tace, "To ai tana da mai yi mata gyaran ɗaki, har ma da bayinta duk akwai masu wankewa kullum"

Inna tace,. "To idan kin koma ki karɓi komi ki dinga yi mata da kanki, girkin ma ki shiga cikin masu girkawa kuna yi tare don ki ga yanda ake yi"

Dije ta turo baki tace "Don Allah Inna ki bari kawai Surry ta koya man, tunda naga itama watarana tana shiga ta yi girkin idan saurayinta zai zo fira, sai dai kuma su fa da wata ƙatuwar akwati suke sanwa a kai, baki ganshi ba da murhun ɗora girki ya kai shida ko bakwai fa, to ni har yanzu ban ma san ta yanda ake kunna abun ba, saboda da wutar lantarki ma naga ana aiki da shi"

Inna tace "To ki dinga koya kinji kinga abincinsu daban da namu, idan baki iya ba sam ba zaki ji daɗin zama cikinsu ba, kuma kinga Mijinki ɗan gayu ne yana buƙatar ace komi kin iya irin nasu, idan kuma ya ga baki iya komi ba sai ya auro wata matar wadda ta iya abubuwa irin nasu, kin ga shikenan sai ta karɓe mijin ta barki sake da baki tunda baki iya komi ba"

Dije ta yi shiru sannan tace,. "Ai ni Inna ko don renin hankalinshi ma dole in koya kafin ya dawo, amman fa gaskiya in yace zai auro wata bayan ni yasin sai naci Uban ko ma wacece inna"

Inna ta zaro ido waje tace, "saboda mi? Ko ance maki ke kaɗai ce ALLAH ya halastawa ya zauna da ke? To kul kar in fara jin wannan shirmen gareki, don jikina yana bani yanda yake ɗan birnin nan ba zai zauna da ke ke kaɗai ba matuƙar ba kin iya komi na yan birnin ba, don haka idan har baki son ya ga wata ya sake aurowa to ki natsu da kyau ke ma ki zama yar gayu kamar su, ki dinga wanka kamar yanda suke yi, ki iya girki irin nasu, ki iya kwalliya irin ta su ke tafiya ma idan kin so zaki iya maidata irin tasu, saboda kawai ki zamo dai dai da mutanensu don kawai ki ƙwatowa kanki ƴanci, ki rage yawan surutu da faɗi ba'a tambayeki ba, ki zamo shiru shiru sannan ki dinga komi cikin natsuwa ba rawar jiki ko ƙiriniyar da kika saba yi anan ba, sannan kar ki yi wasa da ibada kamar yanda kika koya tun nan gidan, idan ma da hali ki dinga yin azuminki na Litinin da Alhamis don samun nutsuwar zuciya"

Dije ta yi shiru tana ta wassafa duk abubuwan da Inna ta faɗa a ranta, sai cen ta yi ajiyar zuciya tace

"Ai Inna na fara koyar wasu abubuwa, kinga ko kwalliyar garinmu da nake yi acen yanzu duk na daina yi, saboda Surry tace in ina yi mutane zasu gano cewa wai daga ƙauye na fito su rena ni"

Inna tace,. ,"To ki yi ƙoƙari ki yi ta koyar abubuwa irin nasu kafin Mijinki ya dawo, saboda kawai idan ya zo ki yi masa bazata don na tabbata ba ƙaramin so yake yi maki ba, tunda har ya aureki a yanda ya ganki bayan akwai ƴanmata da yawa a cen birnin, amman duk ya tsallake kowa ya aureki"

Dije ta cire tagumin da ta yi tace, "Ni WALLAHI sai in ga shi baya sona ma kamar Malam Lawi, don yafi sona da shi nesa ba kusa ba, don dai shi baki ga yanda yake ta hantarata ba komi na yi ya yi ta gwasaleni yana katsa man tsawa, watarana ma har dukana

Please Login or Register in order to submit comment