Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunani ya zo mata a rai tace da su

"Ku tsaya kuji wata shawara in kun amince mu ma mu dinga buga masa turancinmu na hauka ko da ba dai dai muka yi ba, ya fi dai da ace mu kai kararshi ya zo ya kara renamu"

Ladiyo ta rik'e hab'a tace,. "Ke Dije to in ke kin iya turancin mu ai bamu iya komi ba"

Dijen ta kyalkyale da wata dariya sannan tace,. "In kun amince Littafin da nake dubawa ina hardace sunayen abubuwa zan fara koya maku shi ku ma, ko don mu dinga haukatashi da turancinmu saboda if you had'a turanci da Hausa to no body kan k'ureka da shi"

Mune da ke cen rakub'e tana kallonsu ta yi wani tsalle tace,. "Yee! Su Dije anji dad'i an kware da turanci"

Dije ta galla mata harara tace,. "Ba nace kar ki sake shiga shirgina ba?? Ai Ni WALLAHI tun da kike da baki irin na aku kuturu bazan sake huldata da ke ba, ke kenan yawon gulma da tsegumi ko kin d'auka bansan kece kika fad'awa Malam nice na saka masa Beraye ba?, To bari kiji ko kusa dani na sake ganinki sai na shikka maki rashin mutunci mai matsayin monita a Makarantar nan"

Mune ta yi rau rau da Ido ta dunkule tana kuka, Dije ta ja su Ladiyo suka fita sunata shawarwarinsu akan baturen Malamin nasu.

Ai kuwa sai gashi cikin kwana biyu Dije ta fara koyawa su Ladiyo Littafin, cikin ikon ALLAH har sun fara ganewa suka watsar da karatun don daman cen ba wani son bokon suke yi ba, Dije Kam ta fita iskansu tana ta ci gaba da nacin bin kalmomin tana tantance su, don shi kanshi ganin ta fara catching d'in abubuwa ya fara rage nauyin tsanar da yake yi mata, wasa wasa sai gashi har lesson yake yi mata na daban ita kad'ai duk da a cikin class yake yi gaban sauran Yan ajin, amma kamar ita kadaice yake yiwa karatun, Sabida su iya kacinsu ido don basu fahimtar komi a darasin nashi.

Cikin ikon ALLAH sai ga Safwan da sakarwa Dije fuska wani zubin ma har da su murmushi idan ta buga masa wani kalar turancinta mai had'e da Hausa.

Lawi kam ganin yanda suke d'asawa ya fara jinshi yana kishin hakan, duk da dai bai tab'a nuna wani Abu da zai nuna matsayin da ya dauki Dijen ba, amman a zahirin gaskiya ba k'aramin so yake yiwa Dijen ba, yak'i furtawa ne don ya fahimci ita ba wannan ne a gabanta ba, don sai da ya bincika sosai ya tabbatar da Dije bata kula kowa sannan hankalinshi ya kwanta, to amman sai ga shi ya fara ganin canji a wurin Abokin nashi dangane da ita Dijen, cikin dabara ya shirya bugun cikinshi domin yaji gaskiyar lamarin.

Aiko ranar suna d'akinsu na gidan Maigarin don tuni Safwan d'in ya baro cen garin ya dawo nan d'in saboda wahalar go and come d'in da yake yi kullum tsakanin garin da kauyensu Dijen.

Lawi ya kalleshi yaga yanda yake ta marking d'in papers d'in Test d'in da yayiwa yaran Makarantar, ya yi gyaran murya yace

"Abokina wai fa kwanan nan naga sai wani kawance kuke yi da mutuniyar taka, ko dai ka rufta ne kai ma kamar Ni?"

Safwan bai daina marking papers d'in ba yace,. "Wace mutunniyar?"

Lawi ya yi masa hararar gefe yace,. "Wace fa bayan Dije abokiyar rigimarka"

Safwan ya d'aga kafada yace,. "No ba wani abun kawai dai don naga tana da jajircewa akan karatun ne shiyasa"

Lawi ya k'ura masa Ido saboda son tabbatar da gaskiyar zancen, sannan ya sauke ajiyar zuciya yace,

"Da dai ka sanar dani gaskiya Abokina don bana son mu zo mu mato a soyayyarta daga Ni har kai"

Ba shiri Safwan ya d'ago kanshi ya kai kallonshi ga Lawin baki a bud'e zuciyarshi sai bugawa take yi da sauri da sauri, cikin b'acin Rai yace

"Kai ko ance maka zan so black cat zaka amince? Me Zan yi da karamar Yarinya irinta kuma don rashin mafadi Yar k'auye"

Lawi ya yi saurin fad'in

"Me zai hana ita din ba mace bace halan?"

Safwan cikin zafin Rai ya ajiye takardun ya mike ranshi a b'ace yace,. "Kai dai da kaga zaka iya to ka je ka yi ta yi, amman Ni kam matsayina ya girmi in lalace Kan duk wata ''ya da ke Cikin kauyen nan, musamman dai ita d'in da baka banbance komi a fuskarta sai hak'oranta da kwayar idanuwanta saboda tsabar bak'in da take dashi, cab! ALLAH ya rabani WALLAHI ku je cen ku k'arata"

Cike da jin dad'i Lawi ya bi bayan abokin na shi da kallo har ya fice, sannan ya mike tsaye cikin wani tsantsar farin ciki yace

"Gareka Lawi lokaci yayi da zaka fara farauto soyayyarka"

Aiko a gurguje ya shirya ya nufi wurin Maigari bayan sun gaisa ne ya dan sosa kanshi yana so yayi magana yana tunanin ta ina ma zai fara?, Maigarin ya kalli yanda bakinshi yake rawa alamun akwai maganar da yake so su yi amman nauyi ya hanashi fad'a, shiyasa ya sallami sauran mutanen da ke wajen sannan ya kalli Lawi yana murmushi yace,

"Lafiya yarona na ganka haka? Ga dukkan alamu dai akwai zancen da ka zo man da shi, to kar ka ji komi nasha gaya maka ka d'auka tamkar cewa Ni din Mahaifinka ne, don haka kar ka ji shakkun tunkarata da kowace irin magana ce "

Lawi ya kara sunne kanshi yace,. "Wata yarinya ce na gani Ina so a garin nan, to shine nike jin tsoron bayyana kaina gareta gashi bansan al'adar garin ba"

Maigarin ya washe bakinshi yace

"A'ah to Masha ALLAHU ita ko wace mai sa'a ce wannan ???"

Lawi cikin zumudinshi yace,. "Wata yarinya ce naji ana kiranta Dije"

Ba Maigarin ba harta Liman da ke zaune da carbinshi yana ja sai da ya zaro Ido, cikin fargaba Maigarin yace

"Wace Dijen ba dai ta gidan Malam Sanda ba?"

Lawi cikin jin nauyi yace "Eh ita ranka ya dad'e"

Maigarin ya sauke ajiyar zuciya yace,. "To dai lamarin aure bincike ake so a fara yi kafin a tsunduma kan lamarin, yana da kyau ka fara binciken halinta kafin ka fito da bukatarka gareta"

Lawi ya yi shiru sannan yace, "To Baba a matsayinka na mahaifinmu anan garin na baka wuk'a da nama akan lamarin"

Maigarin kam sai faman girgiza Kai yake yi cikin damuwa yace,. "Kana da masaniyar itace ta yi wa Abokinka turaren mayu har ya yi kwanciya Asibiti a sanadin hakan?, To bari in sanar da kai gaskiya tun wuri ka canza neman aurenka zuwa wani Gida, don wannan yarinyar mai Ido a tsakiyar kai ta shiga birni to ba'a san iya abunda zata aikata ba don......"

Liman yayi saurin katseshi ta hanyar fad'in,. "Ayi mata fatan shiriya watak'ila ma sanadin shigarta birnin a samu matsalolinta su kau"




Hmmmm😕




Akafta😅





D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA A KOWACE NAHIYA KUKE CIKIN DUNIYA ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU, HADIZA D/AUTA TANA GODIYA SOSAI👍🏻*


*Lamba ta 16*



Maigari ya yi wani mere ya mayar da kai gefe alamun rashin gamsuwa da zancen Liman, ganin haka yasa Liman d'in ya gyara zamanshi yace

"Ni a tawa shawara abunda naga yafi a kira MALAM Sanda a sanar dashi zancen, ka ga duk abunda ya fad'a shikenan da shi za muyi aiki"

Maigarin ya yi shiru na d'an lokaci sannan yace,. "To za mu kirashin duk yanda muka yi zaka ji yarona, amman ina son ka yi nazarin maganata kafin ka yi nutso cikin abunda zaka zo daga baya kana cizon yatsa, Sabida a zahirin gaskiya yarinyar nan kirin jijiya ce, bata jin magana ko kad'an ina ji maka tsoron ka je da ita cikin danginka ta wargaza maka zumunci da Yan uwanka"

Lawi ya kara sunne kanshi cikin sanyi murya yace,. "Ai yanzu kurciya ce Baba jikina yana bani zata natsu matuk'ar ta ga bata gaban Iyayenta"

Maigarin ya d'age kanshi a sama yace,. "Uhm lalle kam akwai k'urciya to ALLAh ya baka k'arfin gwiwar tunkarar matsalolinta"

Lawi ya washe Baki fuska a sake yace,. "Ameen Baba na gode ALLAH ya rufa asiri kuma ya ja da nisan kwana"

Maigarin da Liman suka ce "Ameen" Lawi ya mike tsaye yace

"Ni zan dan fita babban birni in yo muna siyayya"

Maigarin yace "a dawo lafiya ALLAH ya tsare"

Suka yi sallama Lawi ya tafi zuciyarshi cike da farin cikin ganin cewa tamkar ma Dijen ta zamo Matarshi, bayan tafiyarshi ne Liman ya yi ta fahimtar da Maigarin akan fa'idar auren Dije birni, amman Maigarin kam sanin wacece Dijen yasa sam yak'i gano abunda Liman yake son nusar dashi, sai dai ya aika a Kira masa Baffahn Dijen don ya ji ta bakinshi saboda shi ya sa a ranshi ba zai tab'a yarda ya yi tsanin abunda za'a zo daga baya ayi kuka dashi ba.

Aiko dan sak'on yana sanar da Baffah'n Dije bai yi k'asa a gwiwa ba ya garzayo cikin fad'uwar gaba domin ya ji kiran me ne Maigarin ya ke masa kuma yanzu, duk da wani gefe na zuciyarshi yana sanar dashi cewa Dijen ce ta sake aikata wani abin bayan sakawa D'anbirni turaren mayu da ta yi, don duk iya b'oyon da yayi akan kada a gano Dijen ce sai da Maigarin ya gano itace, don kai tsaye ya kira Baffah'n ya yi masa Kamar daman cen ya san itace d'in, ta sigar bugun ciki yace da shi,

"Sanda mai yasa 'yarka bata bari a zauna lafiya ne wai? abun ya wuce kanmu ga shi yanzu har ta fara tab'a bak'inmu, to WALLAHI wannan karon za ta janyo maka zama gidan kaso matuk'ar baka tsawatar da ita ta ajiye shirmenta da rashin hankalin da take yi a garin nan ba"

Baffah jikinshi ya d'auki rawa ya fara cewa,. "Don ALLAH ayi hak'uri WALLAHI na yi mata fad'a sosai akan wannan abun da ta aikata, kuma yanzu haka ma an samu ta rage duk wani k'irin ji da take yi, insha ALLAHu hakan ba zata sake faruwa ba"

Maigarin ya yi shiru sannan yace, "au! Ashe dai da gaske itace d'in ce ta aikata? Um lalle rashin mutuncinta sai hauhawa yake yi, to WALLAHI bari kaji ta sake kwatanta wannan shirmen a gaban kowa zan saka Bafade ya yi mata d"an banzan duka a garin nan sai ya farfasa mata jikinta duka WALLAHI ka ji na rantse kuwa "

Cikin fushi ya mike ya shige cikin gida sai Liman ne ya dinga fahimtar da Baffah'n akan abun da Dijen ta yi bata kyauta ba, Baffah sai hak'uri kawai yake ta badawa cikin sanyin jiki ya baro k'ofar Gidan Maigarin.

To shiyasa yanzu ya ji tsoron wannan kiran kuma da Maigarin ya sake yi masa, a sukwane ya isa ya zauna cikin d'ar d'ar ya fara mik'a masu hannu suka gaisa, sannan cike fargaba ya ce

"Gani ranka ya dad'e ALLAH dai yasa lafiya??"

Maigarin ya gyara zamanshi ya yi shiru na d'an lokaci sannan yace, "to Sanda wannan kiran daban ya ke da sauran kiran da aka sha yi maka a baya, saboda haka ka natsu ka fahimci abun da zai fishsheka ya sama maka zaman lafiya Kai da 'yarka da iyalan gidanka duka"

Baffah ya gyara zamanshi ya ce "Ina sauraronka ranka ya dad'e"

Maigarin ya fesar da iska a bakinshi kai tsaye ya ce

"D'aya daga cikin bak'in yan birnin nan to mai wankan darzar ne ya ga 'yarka Dije yana sonta da aure, kai me ka gani zaka iya surukuta da mutanen birni ko kuwa?don shi dai wannan yaron dan Gombe ne, abokin tafiyarshi ne dan YOLA"

Baffah kam dirim! dum! yaji a cikin zuciyarshi don kuwa maimakon ya ji dad'in maganar amman sai dakan lugude zuciyarshi take yi, ya yi shiru na yan mintuna Maigarin yana ta yi masa kallon gefe yana girgiza k'afafuwa, sai cen Baffah'n ya yi jarumtar fad'in

"ALLAH ya taimake ka ni dai gaskiya bazan tab'a yin nisa da Dije ba, nafi son ALLAh ya bata Mijinta a garin nan in auradda ita kusa da ni, don haka Ina mai baku hak'uri akan ya samu wata kawai su daidaita amman Ni kam ba zan yi wa Dije aure a birni ba"

Maigarin ya gyad'a Kai yace, "kayi kyaun kai Malam Sanda Ni ma dai abunda na hango kenan tun kafin ka zo da naji maganar, insha ALLAHu zan sanar dashi sakonka ALLAH ya zab'a musu abunda ya fi alkhairi dukansu da mu gaba d'aya"

Baffahn ya ce "Ameen" har zai mike Liman ya yi saurin dakatar da shi yace,. "Malam Sanda ka je dai ka yi shawara kafin akai karshen maganar saboda shi fa aure nufin ALLAH ne, Kuma duk inda ya nufa cen za'a Kai Yarinya to mutum bai isa ya canza tsarin ALLAH ba don lamarin ALLAH ba'a yi masa shishigi, don haka ka da ka yi jayayya da hukuncin Ubangiji a cikin lamarin aure, ka je ka nemi zabin ALLAH kafin ka yanke hukuncinka na k'arshe akan maganar"

Baffah ya dan yi Murmushin yak'e yace,. "Na gode liman amman Ni Kam iya gaskiyata ce na sanar da ku, don kam Ni bazan yi wa Dije aure a birni ba, musamman ma dai gari irin wannan na nesa ka ga tafiyata na barku lafiya"

Baffah sai fad'a yake yi cikin zuciyarshi har ya isa gida in da kai tsaye ya zayyanawa Inna duk abunda ke faruwa Inna ta zaro ido waje tace

"Oh ni d'iyar mutum biyu yanzu ita Dije me ya had'ata da wad'annan Yan gayu da har zasu ce suna sonta? Ko dai basu dube yanayinta da kyau bane?"

Baffah ya galla mata wata jar harara yace,. "Fad'a man aibin da ke jikinta da har wani ba zai ganta yace yana sonta ba??"

Inna ta mik'e cikin sanyin jiki tace,. "Na ga dai ko Yan garin nan namu har yanzu babu Wanda ya tab'a cewa yana son Dije sai Bala,ko shi kuma har yanzu bai tab'a zuwa Gidan nan yace ya zo zance wajenta ba"

Baffah cike da fushi yace,. "Eh kam da yake tafi kowa muni kaf! kafatanin mutanen garin ba ai ko dole a k'ita kam, to ke Hasiya in tone tone kike so ayi sai in ce mace nawa aka aurar a garin nan wadda ko kafar Dije bata kamo ba? Ke kanki kinsan cewa rashin jinta ne kawai ya janyo ake jin shakkun zuwa neman aurenta, kuma insha ALLAHu da ta mallaki hankalinta zata dena ai"

Inna ta yi saurin fad'in "Da zaka bi shawarata Ni dai Malam da ka yi bincike akan asalin yaron, idan ka gamsu dashi shikenan sai a auradda ita a huta kaga ita hankalinta a kwance namu a kwance"

Baffah yayi saurin fad'in " nasha aradun ALLAH in za'a mayar da gabana gabas a yankani ba zan bashi auren Dije ba, kiji ki k'ara fad'a in dai har nine nake da ikon auradda ita to bazan kaita nesa da mu ba, auren nesa ko auren jaraba haka kawai in bada 'yata ayi ta cin zalinta bata da kowa a gari bale taje ta Kai masa kuka taji dad'i, Ina ai bazata sabu ba wai bindiga a ruwa"

Ya mike ya fice fuuu sai zabgar fad'a yake ta yi, mintuna kad'an da fitarshi sai ga Dije ta shigo da Yan wak'e wak'enta tana tsalle, Inna ta yafitota ta ce

"Ke zo nan"

Dije ta k'araso ta zauna nesa da ita cikin tsoron kada Inna tace ta yi wani abin kuma, Inna ta maka mata harara tace

"Ki matso nace"

Dije ta gurguso ta zauna tare da zunb'uro baki ta kumbure fuska, cikin k'ara had'e fuska Inna tace

"Miye hadinki da Abokin wanda kika yiwa turaren mayu??"

Dije ta washe Baki tace,. "ALLAH sarki ai yana da kirki Inna kinsan na ce maki shine ya aramani Littafin nan na koyon turanci, kuma WALLAHI kullum sai yaba kokarina yake yi har litrafan rubutu ya bani Inna ai na nuna maki su ko?"

Inna ta maka mata wata hararar tace,. "Au ashe ya dad'e yana sonki shine baki fad'a man ba??"

Dije ta zabura tare da zaro Ido waje tace,. "Kambala'innan Ni yake so?? Inna wa ya fad'a maki wannan bak'in kazafin? Haka kawai Ina zaman zamana a janyo man jarfa"

Aiko Dije ta fashe da wani mugun kuka tace,. "ai na rantse da ALLAH ban yafe wa duk wanda yayi man wannan bak'in sharrin ba, ALLAH yasa cikin mutum ya kumbura ya fashe kafin safiya ta waye "

Inna ta kume dariyarta tace,. "To mara hankali Baffahnki ne ya fad'a Kinga shikenan da adduarki ta karbu ko da safiya ke yi sai dai aga hanjinshi a watse cikinshi ya fashe"

Dije ta zaro Ido waje tace,. "Na shigesu WALLAHI na goge addu'ar kuma na yafe masa amman shi kuma sai na ji dadilin da yake son jangwalo man jangwam"

Tana k'are maganar ta yi hanyar fita, Inna tace,.

"Dawo ina zaki je?"

Dije bata fasa fitar ba tace,. "Inna don girman ALLAH ki yi hak'uri inje in dawo"

Ta fice da saurinta sai ciccika take yi ta nufi gidan Maigarin, aiko sai gashi tana kaiwa tana hango Lawi ya dawo yana ta d'auko ledodin siyayyar da ya yi masu Safwan yana taimaka masa da wasu, Dije tana zuwa ta tsaya gaban Maigarin ta rik'e k'ugu tace,

"Maigari na kawo k'arar bak'onka da yake son ya lalatani ya ci amanata ya yi man ciki don bashi da Imani"




😳🙆🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️





Akafta🤣







D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA ALL ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU👍🏻*


*Lamba ta 17*


Ba Lawi kawai ba harta Maigarin da sauran mutanen da ke wajen sai da suka furta "Innalilahi wa'Inna ilairraji'un raji'un"

Cikin rud'ewa Maigarin yace,. "Subhanllah! garin yaya hakan ta faru?"

Dije ta mayar da kallonta ga Lawi tace,. "Gashi nan ka tambayeshi ka ji ai Wanda ya mutu a ke yi wa k'arya"

Lawi ya k'araso gabanta cikin rud'ewa tare da kid'imewa bakinshi yana rawa yace,. "Dije ki fad'i tsakaninki da ALLAH yaushe muka yi haka da ke?"

Dije ta galla masa harara tace, "kai ma ka fad'i tsakani da ALLAH in ba cewa ka yi ka yi kana sona ba?"

Ta k'are maganar tare da murgud'a masa Baki tana yi masa wani kallon up and dawn, Safwan da ke tsaye yana kallonsu ba shiri ya tuntsure da wata arniyar dariya, sannan ya koma jikin motarsu ya jingina yana toshe dariyarshi da taki tsayawa.

Maigari yayi saurin fad'in, "Ina Dije"

Dije ta waigo da kallonta gareshi tace "gani"

Yace "zauna inji shin shi Lawi ta wace hanya ya bi domin ya lalataki kamar yanda kika fad'a yanzu??"

Dije ta zauna tare da lankwashe k'afafuwa tace,. "Cewa fa ya yi yana sona to Ni kuma WALLAHI billahillazi ban sonshi ku shaida don ni ban shiryawa yin ciki ba yanzu, to haka kawai ya janyo man bala'i ina zaman zamana yasa in haifo macizai su zo su kasheni a banza, to WALLAHI ban sonshi Ni kam ya ma sani tun yanzu"

Cikin k'umshe dariya Maigarin ya kalli Lawi da ke tsaye sororo ya kasa d'auke idonshi akanta saboda tsagwaron tsantsar mamakin da ta bashi, yace,. "Yarona ka zauna don inji ta yaya har hakan ta faru bayan tun farko sai da na sanar da kai gaskiya??"

Lawi ya janyo kafafunshi tamkar Wanda kwai ya fashewa a ciki ya zauna tare da sunne kanshi cikin jin nauyin su Maigarin, maigarin ya sake cewa

"Me ya hadaka da Dije?"

Lawi ya sauke ajiyar zuciya yace, "WALLAHI Ni ba abunda ya hadani da ita, hasali ma Ni ko maganar da na sanar da kai har yanzu ban tab'a yinta da ita ba, kawai dai ta jahilci abun ne shiyasa"

Dije ta maka masa wata harara tace, "Ai billahillazi ka yi kad'an da ka kirani jahila ko don ka bani littafai to ai ka jira ka ga in ban maido maka da kayanka ba"

Maigarin ya dake cikin bata fuska yace,. "Ke Dije ki fad'i tsakaninki da ALLAH ya tab'a cewa da ke yana sonki bakinshi da naki? Ko kuma ya tab'a nuna maki wani halin rashin da'a Wanda ya danganci k'ok'arinshi na son yi maki cikin kamar yanda kika fad'a??"

Dije ta yi shiru tana nazari sannan tace,. "Eh to tsakanina da ALLAH bai tab'a cewa dani yana sona ba, don ni WALLAHI ma mutuncinshi nike gani saboda naga yana da kirki, ba kamar Abokinshi da muka fara fad'a ba duk da ko shi d'in yanzu mun shirya har karatu yake koya man"

Lawi sai lokacin ya ji wani sanyi ya ratsa zuciyarshi, cikin tanbaba yace

"To ya aka yi kika ce Ina son in lalataki in yi maki ciki??"

Dije ta ce,. "To wa ya ce ka ce kana Sona??"

Yayi saurin fad'in "au! Don nace ina sonki shine zan yi maki ciki?"

Tace "Eh ai Kai ma kasan da na ce nima ina sonka dole ne inyi cikin, Ni ko don a shawo kan matsalar tun kafin faruwar hakan shine na kawoka kararka"

Cikin k'umshe dariya yace,. "Au yanzu da kince kina sona shikenan sai ki yi ciki.?"

Dije tace "Eh in ma baka sani ba to ka sani yanzu don Ni na dad'e da sanin hakan"

Ta k'are maganar tare da murgud'a masa Baki ta kalli Maigarin tace,. "Don Allah ka yi man iyaka da shi tun kafin ya kassarani"

Maigarin gano inda ta dosa yace,. "Ai kuma tunda kince baki sonshi shikenan zance ya wuce, amman ki sani don yace yana sonki kin amince masa ba shi zai sa ki yi ciki ba, don haka kai yarona ka bata hakuri kuma a kiyaye faruwar hakan a gaba tunda dai ita tace bata sonka"

Lawi ya mike Dije ta yi saurin kallonshi tace,. "Ina zaka je kuma bayan baka bani hak'urin ba?"

Ya fuske yana saka talkamanshi yace,. "To ki taso mu je daga cen sai in baki hakurin in kina so"

Dije ta mike ta bi bayanshi har zuwa wani k'aton kututturen icce da ke gefen k'ofar gidan Maigarin ya zauna, Safwan ya bisu da kallo ya yi mere ya shige d'akinsu sai dariya yake kyakyatawa.

Dije ta yi tsaye kikam tana girgizar jiki tace,. "Bani hak'urin Ni dai in tafi inda zan je kar aga na dad'e"

Lawi ya kai kallonshi ga su Maigarin ganin basu kallonshi ya washe fuskarshi yace,. "Ai dai nasan kina son kije Makarantar gaba da primary ko?"

Dije ta saki baki sake tace, "Eh kai zaka kaini?"

Ya yi saurin fad'in

"Tabbas in har kin amince kin aureni to Ni na yi maki alk'awali Ni zan kaiki kiyi Makarantarki har ki yi degree ki zama likita kina yi wa marasa lafiya allura"

Dije ta zaro Ido cikin jin dad'i ta yi saurin zaunawa kan iccen tace, "Don Allah da gaske kake yi zaka kaini in yi likita ???"

Yace "me zai hana in har zaki aureni"

Dije ta yi shiru sannan ta ce "Ni ba Wai aurenka ne matsalata ba bana son ne ince ina sonka don WALLAHI na tsani in haifi macizai saboda tsoronsu nike ji sosai, akwai ranar da muka je daji muka ganshi WALLAHI har suma sai da na yi acen aka kwasoni aka kawoni gida"

Ta k'are maganar cikin zubowar wasu yanmatan kwallah, Lawi ya yi saurin fad'in

"To ya isa daina kuka Ni na hak'ura ko baki ce kina sona ba in dai har kin yarda zaki aureni shikenan Ni kin gama mani komi, Ni ko zan kaiki ki yi karatu har ki fito matsayin babbar likitar Mata"

Dije ta washe Baki cikin tsananin jin dad'i tace,. "Aiko WALLAHI na amince kai Ni gobe ma ayi auren muje in fara karatun Likitancin"

Lawi ya zaro Ido waje yana dariya yace,. "Masha ALLAh lalle Ni Lawi dangata ne"

Dije ta rufe fuska tace,. "WALLAHI ina son inga ina yiwa mutane allura nasan sai sunyi ta kuka"

Lawi ya tuntsure da dariya yace,. "Au to mugunta ma za ki yi ashe ba taimako ba??"

Dije tace "duka biyun ai Ni ina da tausayi wani zubin fa in naga ana kuka nima sai inji ina yi"

Lawi bakinshi a washe yace,. "ALLAHu Akbar ashe haka Dijen take da imani ban sani ba?"

Dije ta rufe fuska tace,. "Ni dai yaushe za'a yi auren in fara zuwa karatun likitar?"

Lawi ya sassauta murya yace, "to ai ke sai kin gama wannan da kike yi sai kije ta gaba sannan ki fara ta Likitar"

Dije ta zaro Ido tace,. "Cabd'i ashe abun da wahala? To yanzu ita ta gaban wannan da muke yi

Please Login or Register in order to submit comment