Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

iska bace bale yace yana sona"

Ta k'are maganar tare da murgud'awa Duduwa Baki, Duduwa ta zaro Ido tace

"Yo in dai har haka kawai don yace da ke yana sonki shine iskancin to Innarki Hasiya da Baffanki sun dad'e da iskancewa"

Dije ta dafe kirji Bakinta a bud'e ta ce,. "WALLAHI ALLAH ya sakawa su INNA don kinci da zalinsu Kuma akan mummunar fahimtar da kika yi masu idan Baki rokesu suka yafe maki ba da wuya in hakkinsu zai barki ki shiga aljanna"

Duduwa ta ce,. "Ki je ki sanar dasu idan suna da abun Kare kansu su Kare kansu in gani in har su d'in ba Yan iskan bane kamar yanda kike tunani, to ma wai ke tayaya aka sameki in ba ta hanyar abunda kike kira iskanci ba?, To bari kiji hanyar da aka sameki itace Bala yake so yabi shima ya yi auren ya samo nashi rabon 'ya'yan, shima in banda rashin hankali irin nashi me zai yi dake masifaffiya bak'ar mafadaciya dake, shiyasa ma in bandashi kaf garin nan babu wanda na tab'a jin yace yana sonki to me za'a tsinta jikinki in banda jidali"

Dije ta zumburo Baki tace,. "WALLAHI kinci sa'a Ina ganin kimarki a idona da tuni na shikka maki rashin mutunci akan wannan k'azafin da kika yi man Ni da su Baffah, to Ni ALLAH na tuba ma wani tsautsayi zai sa har in yarda wani yace yana sona? Ai duk Wanda kika ga yana soyayya WALLAHI mugun ma dan iska ne na fad'a na k'ara fad'a Duduwa Bala Dan iska ne tunda har baiji kunyar kallon tsabar idanuwana ba ya bud'a Bakinshi yace wai yana sona ba"

Ta kalli Balan ta murgud'a Baki ta buga masa wata jar harara tace,. " kuma Bari kaji narantse da ALLAH duk kasa nayi ciki da kai zan kuka tunda kai baka da imani"

Tana k'are maganar ta fashe da kuka saboda tuno labarin da Inna ta Bata akan cewa duk ta yarda wani ya tab'a hannunta ko kuma yace yana sonta ta amince ciki zai fito jikinta yayi katoto ta haifo macizai.

Tana k'are maganar ta fita rangai rangai ta bare Baki iya k'arfinta tana ta kuka tana fad'in wayyo ita yau ta shiga uku tsautsayi ya hau kanta, kowa ya ganta tana kukan sai dai ya bita da kallo yana tunanin yau me yasa Dije kuka haka, saboda kowa yasan takadirancinta don abunda duk zai sakata irin wannan kukan ba abune kad'an ba, wasu ko dad'i kawai suke ji don tunaninsu ko wani ta samu wanda yafi k'arfinta ya darza mata shegen kashi.

Dije kam ko gabanta bata gani saboda tashin hankalin da ta fad'a, don ita a ganinta tata ta k'are shikenan tunda bala yace yana sonta cikinta zai yi katoto ta haifo macizai.

Aiko tun daga nesa Inna ta fara jiyo sautin kukanta cike da mamakin abunda ya saka Dije kuka yasa ta yi kasake tana jiran shigowarta, sai ko gata buguzum buguzum ta fad'o Gidan sai da ta yi tsalle ta fad'i k'asa tana ta kururuwar wayyo ita cikinta macizai sun fara taruwa, Inna ta bita da kallo cike da mamaki tace da ita,

"Wai ke lafiyarki kike cikawa mutane kunnuwa da kuka haka?"

Dije ta tsagaita da kukanta tace,. "Ba Balan Duduwa bane yace wai yana sona ba, Kinga fa har macizan sun fara taruwa cikin cikina suna cizar mani hanjina"

Inna ta so ta yi dariya amman ta mazge tace,. "Ni dad'ina dake hauka to bari kiji idan dai kika yarda ya tab'a hannunki ne macizan zasu fara taruwa ko kin manta labarin da na baki?"

Dije ta yi girgiza Kai, Inna tace "ya tab'a maki hannun ne?" Tayi saurin girgiza Kai tace,

"A'a"

Inna tace, "to kwantar da hankalinki ba abunda zai sameki ai tunda ke baki ce kina sonshi ba har hakan ya janyo ki bashi fuskar da zai tab'a maki hannu, amman da ace kin bari ya tab'a maki hannun kam to da yau macizan zasu fara taruwa a cikin naki, amman yanzu tunda har kin tabbata bai tab'aki ba to Alhmdllh tashi kije ki ajiye allonki ki zo kiji wani labarin"

Dije ta share hawayenta hankalinta ya dan kwanta ta je ta ajiye allon ta dawo Inna ta shimfida masu tabarma ta ci gaba da bata labarai masu sakata tsantseni da halayen maza marasa mutunci masu lalata yara, Aiko daram darasin Inna ya shige kwanyarta don daman cen ita rayuwar maza ba damunta ta yi ba, don in banda Bala ma kaf garin ba Wanda ya tab'a taronta da wannan mummunar maganar.

Suna cikin firar ne aka fara buga masu sallama a k'ofar Gida, Inna ta kalli Dije tace

"Je ki gani wa yake sallama idan Baffanku ake nema ki sanar bai dawo ba"

Dije ta tashi tana yar wakarta ta nufi k'ofar Gidan, aiko sai gashi taga wani yaron Maigari ta kalleshi da kyau ta yatsina fuska tace,. ,"Baya gida kaje ka sanar"

Yaron ya kalleta kamar ya shaketa yace, "ai tunda ke kina nan muje Maigari yana nemanki daman dake da Baffan aka ce ku zo to tunda shi baya nan ke ki zo ki wakilceshi"

Dije ta murgud'a masa Baki tace, ,"wani munafukin ne ya Kai karata kuma? Ni me ma nayi da za'a nemeni?"

Yaron ya juya ya fara tafiya yace, "Wannan kuma sai ki baiwa kanki amsa Ni Kinga tafiyata sai kin k'araso"

Dije ta bi bayanshi da harara aiko sai ga Kira Inna ta kwala mata, ta amsa da k'arfi ta koma cikin gidan tace

"Inna Maigari ne ya aiko yace inje in karb'o dussata da ciyawar da yayi alk'awali zai dinga baiwa Akuyata"

Inna ta yi mata wani kallo tace, "wace dusa bayan waccen wadda ya aiko maki?"

Dije ta Sosa kai tace,

"To ko dai ciyawarce yake nufi Dan sak'on ne bai ji sak'on dai dai ba? Bari inje in karb'o in dawo INNA kar yaga na dad'e"

Ta fice da sauri Inna ta bita da kallo tace, "ALLAH ya shirya"

Dije kam tana fita ta nufi gidansu Hansai da sauran kawayenta sannan suka rankaya Gidan Maigarin, don zuciyarta ta tabbatar mata cewa Tambari ne ya kaita k'ara wajen Maigarin.

Aikuwa sai ko gashi tana zuwa ta ga Tambari da Mahaifinshi, sai dai kuma bakin fuskokin da ta gani da bakuwar motar da ke ajiye k'ofar Gidan Maigarin, wadda ko Babu tambaya zaa gano tasu ce duba da yanda ta hangosu yan gayu da wasu tufafi da suke sanye dasu iri d'aya da hula wadda a tashi d'aya za'a banbancesu da wayayyun yan boko, saboda kayan bautar K'asar da ke sanye a jikinsu dukansu su biyun da d'aya ya kasance fari yayin da d'ayan kuma yake baki-baki don ba za'a kirashi da wulik ba.



Tofa ga wata sabuwar cakwakiya🤣




Akafta😅







D/Auta CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*BAK'ON YANAYI BOOK NE MAI ZAFI HAR KUNA YAKE YI A HANNU SABODA TSABAR TSANANIN ZAK'INSHI BOOK D'IN BAK'ON YANAYI SALONSHI DABAN NE DA KOWANE BOOK DA KA TAB'A KARANTAWA A DUNIYAR LITTAFAI, ZAKU SAMESHI A ARHA DA FARASHIN NERA D'ARI UKU KACAL KUMA ZAKU SAMESHI A COMPLETE DINSHI CIKAKKE MAI B'UKATA TA NEMENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 SAYEN NA GARI MAYAR DA KUD'I GIDA SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI👍🏻 DOMIN KUWA BAK'ON YANAYI DAUKE YAKE DA NASHI KALAR SALO KALA KALA KUMA MABANBANTA MASU BURGE MAI KARATU DA SAKASHI SHIGA CIKIN SHAUKI YAYIN KARANTAWA💃🏻*


*Lamba ta 9*



Dije garin kallonsu har da su tuntub'e sannan ta sami gefe ta rakub'e kamar wata ta ALLAH tana yafito su Hansai da suka saki Baki suna kallon bak'in Yan bokon, Maigarin ya karb'i wata farar takarda daga hannun wannan farin mutumen, sannan ya bud'a takardar sai kace daman cen shi d'in wani jan wuya ne a bokon, gano ko harafi d'aya bai gano maanarshi ba yasa ya mik'awa Liman takardar, shima ya duba yaga bai san komi a ciki ba ya kalli Dije yayi wata dariya yace

"Karb'i takardar nan karanta muna ita Yar gidan Baffahnta"

Dije ta ji k'irjinta ya buga dam! da shiri cikin sanyin jiki ta karb'i takardar ta Kura mata Ido kurum!tana so ta gano abunda ke ciki, don ALLAH ya taimaka da harshen hausa aka yi rubutun sai dai kasancewar ba kullum ake zuwa Makaranta a garin ba yasa ba duka hausar ta sani ba, aiko kai tsaye wani tunani ya zo mata ta d'ago kanta ta kalli Yan bokon da suma ita suke kallo, sannan ta mayar da kanta tana k'ara tantance takardar ta mik'e cikin fara'a da wata jarumta ta kalli mai garin tace,

"Sak'o ne aka aiko daga birni akan a had'a duk wasu matasa na garin nan za'a daukesu aikin Soja a turasu Maiduguri domin a kwantar da tarzoma"

Maigarin da sauran masu ruwa da tsaki da ke garin har ma da su kansu bak'in suka zaro Ido, cikin firgici Tambari ya mike jikinshi yana rawa ya kalli Babanshi yace

"Muje Baba kasan bana jin k'arfin jikina idanuwana ma ko gani basuyi sosai, watakila ma shikenan Ni da lafiyar Ido haihata haihata"

Ba shiri dayan bakon wanda ba fari ba ya kumshe dariyarshi yayi saurin cewa,. "A'a ba haka bane mu an turo mu ne daga birnin akan zamu yiwa k'asa aiki mu zauna da ku anan Garin mu dinga koyawa yara karatu har na tsawon shekara d'aya, fatanmu kawai ku bamu had'in kai don ku sani tab'amu tamkar tab'a k'asa ne, don kuwa akanmu mutum zai iya k'are rayuwarshi gaba d'aya a prison in har ya kawowa hukuma ganganci"

Maigarin da sauran mutanen da ke garin suka zaro Ido alamun tsoro, Maigarin kam sai gyad'a kanshi yake yi alamun gamsuwa da zancenshi, Dije kam tana jin haka ta fara hararar dan farin saboda ganin yanda yake ta wani cin magani yana binsu da kallon kyama, Maigarin da kowa aka yi ta yi masu sannu da zuwa da fatar nasara akan aikinsu da suka baro gidajensu suka zo kauyen da nufin su tallafa masu.

Daga nan Maigarin yasa aka je aka gyara masu masaukin da zasu zauna sannan aka yi masu iso suka fito da jakunkunansu da suka zo da su aka shigar masu da su.

Dije ta bi dan farin da wata jar harara aranta tace,.

_"jishi don ALLAH sai kace baya tsugunnin Kashi, mu za'a nunawa fari?? farin banza da wani janbaki da ya gogawa lebenshi don kitifirin bala'i"_

Shi dai Kam bai ma san tana yi ba don hasali ma shi kwata kwata hankalinshi baya wurinsu yana cen tunanin ta yaya zai iya zama kauyen har ma yayi rayuwa a cikinta?.

Bayan sun shige ne Maigarin ya dawo da hankalinshi garesu ya Kai kallonshi ga Dijen yace,. "Wai ke me yasa ba kya jin kunyar yin k'arya? Idan baki gane abunda takardar ta kunsa ba ai sai ki bari wad'anda suka sani suyi bayani yafi da ki tayarwa da mutane hankali a banza"

Dije ta muskuta ta kalli Tambari ta mere masa baki tace,. "Ai Ni na zaci sak'on da ke ciki kenan don na gansu da kayan sojoji"

Maigari zai sake yin magana Liman yayi saurin fad'in,. "ALLAH ya kyauta yanzu ayi abunda yasa aka taraku dai ba wani zakale zakalen magana aka ce ki zo wa mutane ba da su ba"

Ya katse abun ne don gudun kuma wata b'araka ta kunno Kai ganin sababbin bak'in da suka zo kar su fara cin karo da abunda zai saka su fara jin dama basu zo kauyen ba.

Maigarin ya gyara zamanshi yayi gyaran murya yace,. ,"Miye hadinki da Tambari har kika watsa masa k'asa a Ido kikasa yaji ciyo a hannu ya buge goshinshi?"

Dije ta makawa Tambari harara tace,. "WALLAHI Ni ba dashi nike fad'ana ba don Ni har ma muka gama fad'an ban ma ganshi a wurin ba, sai zan bar wajen ne ma na hangoshi yana mukususu"

Liman yakalli Dije da kyau yace,. "Kiji tsoron ALLAH ki fad'i me ya hadaki da shi?"

Dije ta Sosa kanta tace, "Eh to tunda kace tsakanina da ALLAH WALLAHI ba dashi nike fad'a ba shine ya shigarwa Kanwarshi ya zo zai dakeni Ni Kuma na watsa masa k'asa a ido yaje ya buge da icce ya jiwa kanshi ciyo, idan kuma ba'a yarda ba a tambayi su Hansai gasu nan ai"

Maigarin ya kurawa Dije Ido yana karantar yanayinta sannan yace,. "To munji wannan shi kuma Kiran Mahaifiyarshi da kika yi barauniya fa wa ta tab'a yiwa sata a gabanki"

Dije ta zabura tsaye tace,. "Ai WALLAHI ko a gabanta zan fad'a don tasan naganta lokacin da ta yiwa Innarsu Ladiyo sata har ma na fad'awa Innar Ladiyon sai ko gashi da aka binciketa anga kud'in saboda cikin dankwalinta ta b'oyesu, har ma ........."

Sunne Kan da Babansu Tambari yayi yana girgizar kai yasa Maigarin saurin dakatar da ita yace,. "To munji baki abun magana amman kisani ko da wasa kika sake cewa da ita barauniya sai kin karb'i hukunci, don Kinga wad'annan bak'in to su zan baiwa ke su kaiki birni asakaki gidan kaso a rufe ayi ta gana maki azaba, kinga shikenan bazaki sake ganin Innarki da Baffahnki ba, muma mu huta da bari barin da kike sakamu kullum safiya, haka fa kika fasawa yarinyar cen Bintalo goshi suka kawo kararki anan na basu hakuri dakyar suka hak'ura, yanzu haka ma Uwar d'akina tana cen tana fama da k'afa tun lokacin da kika zo muna da zancen Kura, to kiji ki k'ara ji kika yarda kika sake wani laifi a wannan karon ba zaki sha ta dad'i ba"

Dije ta yi fiki fiki da Ido alamun tsoro ya shigeta fuskarta a kumbure tace,. "To ai sune suke tsokalo fad'an ko banso muyi fad'a ba sai sun janyo anyi, suma a ja masu kunne su daina shiga sabgata"

Maigari yayiwa Tambari da Dijen iyaka haka ma su Hansai duka sai da ya ja masu kunne sosai akan kada su koma janyo abunda zai had'asu fad'a da kowa a garin bale ita kanta Dijen.

Haka aka gama aka baiwa Mahaifinsu Tambari hak'uri aka aje akan za'a ga Baffann Dije idan ya dawo shima a sanar dashi ya ja kunnuwan 'yarshi.

Har sun tashi zasu bar wajen Dije ta koma ta zauna tace,. "Nace ciyawar ita Kam har yanzu ba'a Kai ba"

Maigarin ya kawar da kanshi gefe yace,. "Kije Gida idan baki ganta ba ki dawo ki karb'a"

Dije ta mike cikin sanyin jiki tace,. "WALLAHI fa yau ban tafi Daji ba idan akuyata bata ci ciyawar ba hanamu baccin dare zata yi"

Maigarin ya waigo cikin b'acin Rai yace,. "To kunatau! Kije tana cen nace akai maki idan an yo"

Sannan Dije ta washe Baki tace,. "Yawwa Nagode ALLAH yasa kafi haka dussar ma ankai nagode duka amman har da gobe zaka aiko man ko?"

A kufule ya d'aga murya yace,. "Har jibi ma kije Gida shikenan"

Dije ta lak'ama kafad'ar su Ladiyo suka tafi suna ta firarsu suna dariya, har sunyi nisa Dije ta dafe Baki tace dasu

"Wai kun ga abunda na gani kuwa?"

Lanti Jummala da Ladiyo Hansai suka had'a baki wajen fad'in

"Bamu kanun labaran mu sha?"

Dije ta sassafta murya tace,. "Kunga wani fi'ili wai Namiji da shafa janbaki?"

Ladiyo ta kyakyalkyale da dariya tace,. "Ashe ba Ni kad'ai nagani ba?"

Hansai tace,. "Kuka sani ko haka Bakinshi yake?"

Lanti tace,. "Injiwa? Baki ganin yanda yake fari tass! Ai irinsu ance cikin injin ake sakasu ana wankesu, garin wankin nasu ne ma bakinsu yake yin ja irin haka"

Dije ta yi wani mere tace,. "Tirr ALLAH ya rabani da canza halittar da Ubangiji ya bani haka kawai garin wankan injin d'in a wanke da zuciyata ta fashe in mutu"

Hansai tace "Ameen to amman naji ance zasu dinga karantar da mu to me zasu karanta muna?"

Lanti tace,. "Wai Boko mu da ko Makarantar ma ba wani zuwanta ake yi ba za'a yi wahalar d'aukosu a kawosu garin nan"

Dije ta harareta tace,. "Kece dai bakya zuwa nikam duk ranar da nasan malamai zasu zo ai kinsan ina zuwa, ku ne dai ba kwa son karatun Shiyasa duk cikinku babu wadda ta iya abacada"
Hansai zata yi magana Ladiyo ta rufe mata Baki tace,. "Ni dai ku zo muje gida kar aga mun dad'e tunda an kashe rigimar"

Hansai tayi gaba Ladiyo tabi bayanta Suka tafi, Dije ta kalli Lanti da Jummala tace,. "Ni fa kunsan me?"

Suka ce "sai kin fad'a"

Dije ta janyo kansu ta yi masu kus kus d'in cewa,. "So nike muje mu ga wadancen bak'in Yan bokon muji shi wancen Mai wankan injin d'in ko ya iya hausar shi"

Lanti ta zaro Ido tace, "Bakiji kashedin da aka yi muna ba halan? Ni dai WALLAHI ban zuwa babu ruwana kunga tafiyata"

Dije ta kalli Jummala tace,. "Kema jeki abunki amman ku sani WALLAHI sai kunsan Ni kuka yiwa rashin nasiha"

Jummala ta kalli Lanti da ke ta sauri ta bar waen ta dawo da kallonta ga fuskar Dije take ta ciccika tana harararta cikin tsoron hukuncin da zata yi masu tace,. "Ni dai muje in raka kin"

Dije ta washe baki tace,. "Ko ke fa zo muje su Kuma ki barni da su zamu had'u ai"

Jummala cikin tsoro da kashedin da Maigarin yayi masu ta bi Dije Suka zagaya ta bayan gidan Maigarin har suka kai bakin k'ofar d'akin da aka ajiye bak'in cikin sanda Dije itace a gaba ta saka hannu ta yaye labulen kad'an ta leka kanta, aiko ta hango dan farin yana sauya tufafi ya zura dogon wandonshi kenan idonshi suka yi caraf da na Dije, aiko ba shiri ta saki labulen aguje ta falfala da gudunta saboda tsoron ganinshi da tayi daga shi sai guntun wando, saboda a rayuwarta kaf bata tab'a cin karo da wani a hakan ba sai ranar.

Mutumin kam cikin sauri ya saka wandon ya mayar da rigar ya fito d'akin da sauri sai dai ko kurar Dije bai hango ba sai Jummala da ke gudu itama a k'ok'arinta na son ganin ta taradda Dijen da ta samu tasha kwana sai balbala gudu take yi kamar wacce zata tashi sama.

Yayi kwafa ranshi a b'ace ya yi tsaye Yana nazarin mafita sannan ya koma d'akin inda ya taradda abokin tafiyarshi ya dawo da kwanon abincin da Maigarin ya Aiko masu.

Cikin tsananin b'acin Rai ya zauna yana huci cikin harshen turanci yace,. "Bazan iya zama a garin nan ba gaskiya , sai da na fad'awa Mama bazan zo ba ta matsa man in zo to ai gashi nan na fara cin karo da takaicin babbak'un kauyawan"

Abokin tafiyarshi yace ,. "Plss Safwan ka fahimci abunda ake so ka gane mana, yanzu miye aibin garin nan ne? gashi Maigarin da mutaneshi sai ina zasu sakamu suke yi sun karbemu hannu bibbiyu fa"

Wanda aka Kira da safwan d'in ya wani mere baki ya gallawa abokin tafiyar tashi harara ya buga wani uban tsaki yace,. "WALLAHI da naga abunda bazan iya ba Ni fecewata zanyi in barka kaji da su, don bazan zauna takaicinsu ya kar ni ba a banza, yanzun nan fa ina k'ok'arin canza kayana ne na hango idon wata bak'ar mage ta zuro Kai tana kallona"

Abokin tafiyarshi ya kyalkyale da wata arniyar dariya yace,. "Anan din ma ka sake had'uwa da wata magen kenan? To kasani ko ita wannan d'in itace Matar ba magen da ka baro a cen ba"

Safwan saboda tsabar takaici ko kallonshi bai sake yi ba yana kammala saka kayan yayi kwanciyarshi, tare da janyo wayarshi da nufin ya yi kira aiko sai gashi yaga gaba d'aya kaf layukanshi babu d'aya mai network duk sun d'auke.

Ba shiri ya Mik'e zaune cikin harshen turanci yace. "Oh sheet! Wannan wane irin bak'in gari ne haka? gaba d'aya basu da service fa ko d'aya"




🤣🤣🤣🤣wasa farin girki shin su waye su Kuma bak'in Yan bokon????.




Akafta😛








D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*Jinjinar ban girma gareki masoyiyata ta asali mai Sona da zuciya d'aya Yar kanawa d'iyar mutan Yola Alkharin ALLAH ya Kai maki har gadon baccinki, Ina alfakhari da samunki gareni AISHA YOLA kisani sonki cikin jinina yake ALLAH ya bar mu tare har aljannah gaba dai gaba dai tawajena makiyanki fadawanki😛*

*BAK'ON YANAYI COMPLETE ga Mai b'ukata 300 kacal Mai so ta tuntubeni ta wannan number 09032685442*



*Lamba ta 10*



Dije kam tana gudu tana haki har takai gindin wata bishiya ta fadi zaune k'asa tana sauke nishi a wahalce saboda Uban gudun da ta kwaso, Jummala ta k'araso itama tana haki ta fad'i kusa da ita tana hakin tana fad'in

"Haba Dije shine kika ki tsaya man in fa an kamani kice me?"

Dije ta kalleta Kai tsaye tace, "Zan ce Sabida kinje ganin Yan birni ne sun kamaki kina lekonsu"

Jummala ta zaro ido waje tace,. "To ai kece kika leka ba Ni ba don ni ban ma hangosu ba"

Dije tuno abunda ta gani yasa ta yi saurin rufe fuskarta tace,. "Ai nikam na ganowa kaina shiyasa Inna tace leke baya da amfani don garin leken sai ka ganowa kanka abunda ba shi ba ashe da gaskiyar Innata"

Jummala ta bi ta kallo mai cike da son karin bayani tace,. "Me kika gano halan?"

Dije ta runtse idonta da sauri cikin jin kunyar kanta tace,. "Kinga Jummala bazan iya tuna komi ba tashi muje gida tun kafin a gano mu ne muka lekasu idan har ya sanarwa da Maigari"

Jummala ta Mik'e jikinta yana rawa tace,. ,"Hakane fa to Ni dai Kinga na tafi ko banza tallah zan je ma yanzu"

Jummala ta yi hanyar Gidansu Dije ta yi Gida zuciyarta sai wassafa mata Yanayin da taga Safwan d'in take yi, inda take jin kunyar kanta da kanta saboda mugun ganin da idanuwanta suka yi.

Aiko haka ta kwana duk wani motsinta sai taga fuskar Safwan tana yi mata gizo yana harararta tare da yi mata kashedi da gargadi kala kala, don har Inna sai da ta gano akwai abunda yake damunta, amman da ta tambayeta tace, "wasu bak'in Yan boko suka zo garin nan zasu koya muna karatun Boko, shine na matsu Litinin ta zo mu fara zuwa Makarantar".

Inna kam sanin wacece Dije dangane da son karatun yasa ta amince, sai ko gashi ko da safiya ta waye aka yi gangami akan kowa ya taru k'ofar Gidan Maigari ana nemansu babba da yaro, aiko cikin kankanin lokaci aka hallara k'ofar gidan inda kai tsaye Maigarin yayi masu bayanin zuwansu Safwan da Lawi da dalilin da ya kawosu garin, inda yayi masu gargadi da jan kunne sosai akan tabasu da abunda zai biyo bayan hakan.

Aiko kowa jikinshi yayi sanyi duk da wasu da yawa cikin garin bokon ba damunsu yayi ba bale har su damu da wani zuwansu, don da yawa cikinsu yaransu ko Makarantar basu tab'a lek'awa ba, masu k'ok'arin zuwan ma irinsu Dije kasancewar Malamman daga wani babban garin da suke a karkashinshi ne ake turosu, saboda sun fahimci daliban kalilan ne yasa suke yin tsalle akan zuwan nasu garin kullum, don wani zubin ma sau biyu ko sau uku ne suke zuwa a sati har ta kai yaranma kansu basu zuwa Makarantar sai ranar da suka san malamman zasu zo,Dije ma tana cikin masu k'ok'arin zuwa Makarantar na sahun farko, don wani zubin ma a sanadinta wasu yara da yawa suke zuwa Makarantar don habaici da take yi masu tana yi masu gorin cewa su jahilai ne tunda har basu iya abacada ba, amman duk da hakan a class d'aya duka ba zasu wuce mutum biyar zuwa shida ba, yanzu haka aji biyar Dije take a Makarantar tare da su Jummala da su Hansai, yan ajin shida mata duka anyi masu aure mazan kuma daman cen karatun bai wani damunsu ba.

Haka Maigarin ya Kare yi masu bayanin ya gabatar da su Safwan garesu, Lawi dai kam ya saki jiki yayi masu bayani dai dai da saninsu amman Safwan kam iyakacinshi gyad'a kai yana dariyar yake, saboda shi warinsu ma yakeji yana damunshi a gundure yake da akai k'arshe ya bar wajen.

Da ma aka zo kanshi akan ya tofa albarkacin bakinshi don tsabar renin hankali irin nashi da harshen turanci yayi magana, dukansu ko sai zarar Ido sukeyi suna kallon Bakinshi don su ko zo in kasheka da turancin basu sani ba, bayan ya k'are bayanin ne Abokinshi Lawi ya fassara masu abunda ya fad'a tare da yi masu bayanin cewa Safwan bai iya hausa ba baya jin yaren sam, Dije kam tana jin

Please Login or Register in order to submit comment