Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ALLAH ki dauko mani kaina, tun kafin a fara dafuwarshi a bangon duniya"

Ganin mutane da yawa sun watse sai Yan gani kasheni ciki kuwa har da Maigari da Liman sannan da Baffanta da ke nesa da su yana haki, ta k'ara keta kuwwa tace

"Ku saurareni zamu tafi amman ko harara aka yiwa god'iyarmu Dije sai mun dawo tare da gayyar rundunar Yan uwana aljanu, mun tafi Sarkin fadawa ga kanka Nan gobe ka k'ara dan gidan marasa tausayi amman ka sani za mu zo mu tafi da kai da ka kuskura ka fito fitsarin dare, mun tafi zo muje ke kuma sarkin bacci"

Sai kawai aka ga Dije ta fad'i yaraf tana fisge fisge tana wani Abu da kai ta gwalo Ido sai cen ta yi luf kamar Mai bacci.

Liman ya sake tofa mata addu'ar ya fara Kiran sunanta, Dije ta yi wukil da Ido d'aya suna had'a Ido da Liman ta zabura ta mike zaune tace

"Don Allah ka yi hak'uri WALLAHI da gaske naga Kura Ni da su Ladiyo, a tambayesu aji ai ko su zasu fadi gaskiya don ba Ni kad'ai na ganta ba har dasu, a gaban idona taci mutum biyar a farkon gari"

Maigarin yayi shiru yana nazari sannan yace,. "Ai kinci sa'a komi ya wuce tunda an wankeki tashi kije gida amman kar ki sake zuwa daji debo ciyawa"

Dije ta zaro Ido tace

"Na shiga Uku ita akuyar tawa me zata ci idan na daina fita daji?"

Maigarin ya yi Yar dariya yace

"Ni Zan sa akawo maki Ciyawar kullum ki dinga bata saboda baki da isashiyar lafiya tashi kije gida ki kwanta ki huta ALLAH ya baki lafiya"

Dije ta washe baki tace,. " Harda dussa?"

Yace "har da ita tafi gidan kawai"

Dije ta Mik'e tana tsallen jin dad'i tace

"Na gode Maigari ALLAH ya ja da nisan bacci kuma ya baka lafiya ya tsare gaba kuma yasa kar ka mance watarana kaki aikowa"

Maigari sai Ameeen yake fad'i don a matse yake da ta bar wurin tun kafin shima yayi sanadin abunda zai janyo ta k'ara kassarashi.

Dije ta nufi wajen Baffahnta tana dariya tace, "Na huta da zuwa Daji akuyata zata sami ciyawa kullum"

Baffah ya fisgo hannunta suka nufi gida, Mutane da sun hangota su yi ta darewa suna gudu Dije kam sai tsallen cin nasara take yi, Liman kam binta yayi da kallo yayi dariya don shi tsaf ya gano ba wani aljani da ke kanta tsabar iya shege ne ke damunta, amman ko ba komi ya jinjina mata tunda har ta samowa kanta hanyar kwatar kai, daga wannan gangamin jidalin data hadowa mutane a cikin gari.




Akafta😅






D/AUTA CE✍🏻

*💣DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*WAI! WAI! WAI RIGIJI GABJI WANI KAYA SAI AMALI LALLE DIJE K'ARANGIYA TAYI FARIN JINI BA KAD'AN BA INA GODIYA SOSAI MASOYA BOOK D'IN ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU A DUK INDA KUKE👍🏻*



*Lamba ta 4*



Ko da suka je gida suka taradda Inna tana tankaden garin masara tana yi tana sharar hawaye, Dije da gudu ta isa wurinta ta fad'a jikinta har sai da tiren garin yayi tsalle rabi ya zube rabi ciki, Inna ta saka hannu ta Kai mata wani mugun dunku a baya har sai da ta gantsara, a zabure Dije ta mike tana sosa wajen tana zunburo Baki alamar taji haushin dukan, Inna ta nunata da dan yatsa tace

"WALLAHI ki fita idona in rufe Dije na fara gajiya da rashin hankalinki, ke kenan kullum janyowa kanki abunda za'a saka ki a bakin duniya muma ki ja muna zagi a gari, to bari kiji WALLAHI kwanan nan zan sa Delu ta tafi dake birni kamar yanda kullum take rokata akan in bata ke ta kaiki aikatau, kije cen ki had'u da masu horaki da kyau tunda Ni kin renani"

Dije ta fara dire diren kafa tana kuka tana fadin, "ai WALLAHI Inna ko an kaini sai na dawo don ban zuwa birni a yanke mani Kai, Ni dai kiyi hak'uri don ALLAH na yi maki rantsuwa idan na sake ki dakeni"

Inna ta yi banza da ita ta makure jikin gina tana zunburar Baki tana mui mui da Baki tana sharar hawaye, sai ga Baffah ya fito bayi yana fad'in

"Wai ke Hasiya me yasa kullum kike tsangwamar yarinyar nan, to WALLAHI ahir dinki wannan karon don kuwa Dije dan sarkin aljanu ne a saman kanta, yanzu haka shi ya zo ya hana a d'auki mataki kanta Kan abunda ta aikata, kuma yayi gargadin ko harara wani yayi mata za su dawo su sake hargitsa garin nan, idan ke kinga ke zaki iya taron aradu da ka to karki fasa"

Ya kalli Dije yace

"Tafi ki dibi ruwa ki yi wanka ko da zakiji dad'in jikinki akan wannan sukuwar hawan dokin da aljanu suka yi akanki"

INNA Hasiya ta rik'e baki tace, "yanzu Kai Malam har ka yarda da shirmen Dije? Lalle kam, to Ni dai ina baka shawara WALLAHI ka daina goya mata baya tana k'ara zama girtsatstsa, don wannan shirmen nata ba zai hanani jibgarta ba idan tayi laifi ko da ko tsamiya ce akanta Ni babu ruwana"

Baffah zai shiga dakinshi ya waigo yace, "Kurar da kike tsoron zuwanta garin nan to ko nan gidan ma zata dira idan ta zo wannan karon, sai ki je kiyi gaggawar yin rame a karkashin gadonki kinga idan ta zo sai ki shige kawai, don kuwa ba fashi zaki janyo fushin Dan Sarkin aljanu"

Yana K'are maganar ya shige d'aki abunshi domin a matse yake da yada hakarkarinshi ya huta ya samu natsuwarshi ta dawo.

Dije ta dibi ruwa cike fam da farin bokin fenti ta kinkimeshi tana nishi ta yi bayi tana ta gunguni, don taci alwashin sai ta debe haushinta da ruwan gidan don kuwa sai ta yi wacakarta son ranta dasu tunda Innar ta yi mata fad'a.

Gashi sai sun zagaya bayan gidan suka debo ruwan ga wata rijiyar k'ofar gidansu Ladiyo kawarta, ta yi wankanta mai cike da barna sannan ta fito tana rawar sanyi daga ita sai siket a k'irji tana tsallen sanyi, Inna ta kalleta tace

"In dai takamarki mugunta kanki zaki yiwa in mura ta kamaki sai ki bidi mai ce maki sannu, sannan ruwa ma idan sun k'are ai kece zaki debosu don kinfi kowa sanin halin yayanki"

Dije ta zunburo Baki tace,. "WALLAHI Inna kar ki janyo fushin murkustus barakus bn muruddika, yanzu ya sanar dani in fad'a maki suna jin nauyinki don ke kika haifeni sunce in sanar dake daga yau kar ki koma yiman fad'a, da kyar na basu hakuri suka ce sun yafe amman kar a k'ara "

INNA ta rik'e baki tace

"Au abun har ya kai cen? To ki fad'a masu ba k'ari ba har da k'are k'are sai na yi idan sun tashi su yi kuli kulin kubura dani"

Kafin Dije ta yi magana sai ga Usmanu ya shigo Dije tana ganinshi ta yi sum sum ta sassada ta shige dakin Inna kudum, Usmanu ya bita da harara yace

"Wai Inna yaushe yarinyar zata yi hankali ne? Yanzu abunda ta janyo kenan a garin nan? WALLAHI taci sa'a bani nan da sai na kakkaryata bak'ar jidalalla, sannan wannan siket d'in da na hanata sakawa ta fito tsakar gida dashi hakanan shi kad'ai bata bari, to duk abunda na yi wa yarinyar cen Inna kar ki ga laifina tunda ta nuna cewa ban isa ba, to Ni sai na nuna mata na fita kangarewa"

INNA tace "Halin Dije sai ita abita da addu'a kawai ko za'a ci nasarar abun, amman duka yau aka Saba?"

Baffah ya fito yana saka talkaminshi yace

"Ka dai yi a hankali in har ba so kake yi garin nan ya dawo toka ba, don kuwa Dije ba ita kad'ai bace idan ka janyo aka maidaka dan duk'usurun bak'in jakki ko bunsuru shikenan Kai ka janyowa kanka"

Ya fice abinshi Usmanu yaso yayi dariya ya mazge ya nufi randar ruwa Yana lek'awa ya hango ba komi duka tukanen duk ta kwashe ta yi wanka, aiko ya fara kwalla mata kira sai gata da kwandon kayan kwalliyarta tana shafa jar hodarta, cike da bacin ran da ke kwance akan fuskarshi yace

"Uban mi kike cikin Gidan da ba zaki je ki debo ruwa ba?"

Dije ta zunburo Baki tace,. "Yanzu na fito wanka fa Yaya sannan ace inje in debo ruwa? lalle ma!"

Usmanu yayo kanta zai daketa ta yi bayan Inna ta b'oye, cikin gargadi yace da ita WALLAHI muddin bata debo ruwan nan ba sai jikinta ya gaya mata yau.

A gurguje ta gama dige digen bak'in kwallinta ta danbara janbakinta ja fam da Baki sannan ta fisgi bokitin karfensu ta fita tana gunguni.

Ko da taje rijiyar makil take da mutane wad'anda wasu da yawa duka tsararta ne, tun daga nesa suna hangota wata ta yafito wata da ke kusa da ita tace

"Ga fa K'arangiya Nan Wai ashe aljanu ne da ita shiyasa ma masifarta kullum take gaba gaba"

Kafin Yar uwar ta bada amsa Dije ta k'araso ta ajiye bokitinta ta rik'e kugu, Kai tsaye ta matsa jikin rijiyar ta ce da wata mai suna Bintalo ta bata guga ta cika bokitinta, Bintalo ta yi mata kallon banza tace

"Kina so ki cika da wuri me ya hana ki zo da taki gugar?"

Dije tace,. "Taki nike ra'ayin dibar ruwan da ita zaki bani ko sai na janyo maki asara?"

Bintalo ta dafe gugarta da k'afa ta rik'e kugu tace,. "Me zaki iya yi ko an Gaya maki Ni ina tsoronki ne kamar kowa? To WALLAHI kika kawon wasa sai na maki danbanzan duka a wurinn...."

Kafin ta Kai k'arshe sai ko taji saukar mari akan fuskarta, Bintalo ta zabura zata rama gugarta ta sub'uce ta fad'a rijiyar, cike da takaici taci kwalar Dije ta shaketa saboda tafi Dije girma nesa, kafin kace me idon DIJE sun yi ja cikin tsananin fushi tace

"Sakeni Bintalo"

Bintalo ta zakalkalo tace,. "Anki a sakeki ba za'a sake kin ba kiyi abunda zaki iya"

Dije tace "nace ki sakeni Bintalo"

Bintalo ta k'ara shaketa cikin masifa tace, "Sai kin fiddo man gugata da kika sa ta fad'a ko ina sakinki, WALLAHI yau sai na ga k'arshen rashin kunyarki ba aljanu ba ko iccen kuka ne akanki sai na ci Ubanki..... "

Karaf! Sai jin k'arar saukar bokitin k'arfe aka yi a goshin Bintalo Dije ta kwad'a mata kasan bokitin, Aiko Bintalo ta fasa k'ara kafin kace me jini ya fara wanke mata fuska.





😳na yi nan🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️wlh Babu ruwana kar ace Ina nan aka yi 🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️



Akafta🤣🙌🏻






D/AUTA ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*




*COMMENTERS INA MAKU JINJINAR BAN GIRMA🤣👍🏻*




*Lamba ta 5*




Bintalo tana shafo goshinta ta ga jini ta fad'i k'asa tana kururuwa, gaba d'aya mutanen da ke wurin hankali a tashe suka fara salati, a cikin matasan 'yanmatan da ke wurin wata ta zo da gudu ta cire dankwalin Bintalon ta d'aure mata goshin jabau! Bintalo Kam sai ihu take wasu suka rikata zuwa gidansu.

DIJE kam ganin an bar gugunan d'ibar ruwa an nufi wajen Bintalo ana sallallami yasa ta cika bokitinta dam! Ta d'ora akai har ta fara tafiya, hankalin mutanen da ke wajen ya dawo kanta aiko wasu da yawa suka fara jifarta da miyagun kalamai suna aibatata, ita kam ko juyowa bata yi ba ta ci gaba da tafiyarta don ita kanta ganin jinin da ke fita a goshin Bintalon ya tsoratata, sai dai ta mazge kawai don kada a gano taji tsoro ace za'a ci zarafinta a banza.

Ko da ta shigo gidan da sanyin jiki ta juye ruwan ta ajiye bokitin zata shige d'aki, Inna Hasiya ta bita da kallo tace

"Ke lafiyarki na ganki wata sukuku haka? Ko karyar ciyon ne ya tashi don ba kyason komawa debo ruwan?"

Dije ta zumburo Baki tace,. "Ba Bintalo ba ce ta jani muka yi fad'a, kuma WALLAHI sai da nace ta kyaleni ta kyaleni taki to ai gashi nan yanzu ta janyo goshinta ya fashe jini sai tsiyaya yake yi"

INNA ta zaro Ido waje dafe da kirji tace,. "Goshinta ya fashe ko dai kin fasa mata? Na shiga Ukuna Ni Hasiya wai Dije kasheni kike so kiyi ne? kulluma da sabuwar masifar da zaki jajibo muna kisa mutane su yi ta ganin kamar bama tsawatar maki, to bari kiji WALLAHI Wannan karon sai dai in kasheki za'ayi a kasheki amman Ni Kam ba hannuna ba k'afata tunda ke kunnuwan Kashi ne da ke"

Tana k'are maganar cikin k'unar Rai tayi madafi inda taci gaba da tuka tuwon masararta, tana yi tana fad'a Dije ta shige d'aki sum sum tana matsar kwallah.

Aiko minti biyar a tsakani sai ga tashin muryar Iya Mero Uwar Bintalo, tun daga farkon shigowa Gidan take zazzaga ruwan bala'i har ta shigo Gidan rik'e da hannun Bintalo tare da wasu Yan bani na'iya masu zuwa ganin k'wam.

Iya Mero tana shigowa ta fara fad'in,

"Ina Hasiya fito kiga abunda tsinanniyar 'yarki ta yiwa Bintalo, WALLAHI Ni Kam bazan tab'a lamunta da rashin mutuncin da take yiwa mutane ba, don in kowa ya kyaleta Ni bazan kyaleta ba Dole ne sai na ramawa Bintalo itama in fasa mata goshin ta ji inda dad'i"

INNA ta fito daga madafi tana sharce majina saboda hayakin da ya turnuke d'akin madafin yasa idonta sunyi jawur, ta goge fuskarta da gefen zanenta ta k'araso wajen tace

"Don ALLAH Mero kiyi hakuri WALLAHI d'a ne ka haifeshi baka haifi halinshi ba, don da ta Ni Dije take bi to ko hannu aka saka mata a baki bazata ciza ba"

Ta nufo wurin Bintalo ta rik'ota da nufin taga yanayin raunin, aiko Iya Mero ta tureta da k'arfi ta shiga gaban Bintalo tare da cire mayafinta ta sha d'amara a masifance tace

"Ba wani dad'in bakinki da zai yi tasiri a wurina don yau dole ne sai na ramawa Bintalo abunda 'yarki ta yi mata don d'a baifi d'a ba da zaki wani kalallameni da dad'in baki to bazan hak'ura din ba sai na rama mata"

INNA cikin b'acin Rai ta shiga d'aki ta janyo Dije da ke makure Kan gadon bonon Innar suka fito d'akin, Inna janye da ita har sai da ta Kai Dije gaban Iya Meron ta saketa, sannan ta d'auko bokitin karfen ta ajiye gabanta tace,

"Ga ki gata nan Mero don ALLAH ki kasheta kar ki barta da ranta"

Cikin borin kunya Mero ta d'aga hannu ta zabgawa Dije wani Uban mari har sai da ta hantsila, aiko dukawar da Dije zata yi bata taso ba sai da kafafuwan Iya Mero sai gata ko tim! A k'asa tana salati zane ya wancakale gefe, sai fad'in take yi

"Ku ke ganinmu ba mu muke ganinKu ba...."

DIJE sai harararta take tana wani ciccika tana kumbura saboda tsananin b'acin Rai.

Yara kam da ke tsaye suna kallo sai ihu suke yi suna dariyar wallen da Iya Mero ta yi, aiko suka fara fad'in

" Ku zo ku ga Dije ta yasar da Innar Bintalo k'asa"

Bintalo tana ganin abunda Dije ta yiwa Innarta ta yo kan DIJE cikin zafin nama ta fara kai mata duka, Dije ta yi tsalle kamar wata zakanya ta sakarwa Bintalo duka a saman goshin, aiko Bintalon ta fasa wata arniyar k'ara ta durk'ushe tana ihu dafe da goshinta da ya sake fashewa da jini daga kanikancin da aka yi mata a shagon sai da maganin da ke kauyen, Iya Mero ta mik'e cike da jin kunyar abunda Dije ta yi mata gaban yara ta rik'o Bintalo da ke ihun wayyo goshinta tace

"Zo muje wurin Maigari tunda ita Uwarta ta kasa ALLAH wadaran wata haifuwa, WALLAHI Allah ya'isa tsakaninmu da ku Hasiya, kin haifo muna jaraba kin kawo muna cikin gari ta zame muna karfen k'afa"

Aiko ta ja Bintalon tana kuka tana ihu suka fita yaran suka bi su buuu! A baya suna dariya, Inna da ke kitchen tana ta sabgarta suna fita ya fito ta rufe Dije da duka ta ko'ina saboda haushinta da ya rufeta, sai ga Baffah ya shigo cikin tashin hankali saboda labari ya je masa irin aika aikar da Dije ta yiwa Bintalo, Yana kan hanyar zuwa gidansu Iya Meron ne aka ce dashi sunyi gidanshi takakka, shine ya nufo gidan da sauri don tsoron abunda zai je ya dawo don yasan halin Dije sarai ba za'a kwashe da ita ta dad'i ba.

Sai ko gashi ya taradda INNA Hasiya tana dukanta, aiko dakyar ya kwaceta a hannunta saboda zuciyar INNA ta Kai wuya da halin Dijen shiyasa ta yi ta jibgarta kamar ba gobe.

Dije Kam sai ihu take yi tana Kiran sunan Baffa tana fad'in

"Wayyo ALLAH ta karyani ta karya man hannu Baffa"

Baffah ya jata ya zaunar da ita akan tabarmar da Inna ta shinfida masa wadda ta zama ka'ida kullum sai an shimfidata saboda cin abincin dare.

Ya Fara lallashinta yana bata baki da kyar ya ciyo kanta ta daina kukan sai dai kam bata daina sauke ajiyar zuciya ba tana ciccika, don kam ta jibgu iya jibga a hannun INNA.

Har sai da aka kira sallahr Magrib sannan ya daina lallashin da yake yi mata, yace taje ta yi sallah kafin ya dawo ya siyo mata tsiren da take so mai shegen dad'i, Dije ta mik'e tana gunguni ta yi arwallah ko d'akin Innar kin shiga tayi anan waje ta shinfida tabarmarta ta yi sallahr tana kumbure kumburen fuska.

Baffah ya dawo rik'e da bak'ar ledar ya zo har gabanta ya ajiye yace, "gashi kici ko tsoka bance ki baiwa kowa ba, kici ke kad'ai abunki gobe ma zan siyo maki wani in har naga kin saki fuskarki kin daina fushi"

Dije ta karb'i ledar ta ajiye gabanta ciki ciki tayi godiya ta dunk'ule cikin kafafuwanta tana turo Baki, ko da ma aka gama abinci kin ci ta yi don daman wannan halinta ne duk lokacin da take fushi bata cin abinci sai kowa yayi kwana, in taji yunwa ta matsa mata sannan ne take fitowa a sace ta ci ta koma.

To haka abun yake ko yau don kuwa ko Naman da Baffah ya siyo matan bata ci ba har sai da taga kowa yayi bacci, sannan ta canyeshi tas amman bata daina jin yunwa ba don rabonta da abinci tun safe kafin su je daji yin ciyawa, aiko ta fito Sadaf Sadaf ta nufi madafi, ta debo abincin tana ci tana tunanin abunda zata yi ta soshe dukan da Inna ta yi mata, aiko tana gama cin abincin ta sha ruwa ta yi gyatsa sanna fara d'auko tabarya ta bud'e turmin da ke kife ta fara daka iya k'arfinta tana lugude tana tana kad'a turmin tana waka sama sama.

Aiko cikin Bacci INNA ta jiyo sautin daka tsakar dare ta waiga taga Baffa kwananshi kawai yake har da minshari, ta yi saurin dunkulewa cikin tsoro sai dai ta kasa kunne tana jiyo sautin kad'a turmin da wakar da ake yi sama sama, kafin kace me INNA ta fara jib'i don ko numfashi dakyar take bari ya fito don tsoro, sai cen ta ji an koma dukan langa langar da aka yi rufin madafinsu da shi, sai waka ake yi inda cikin wakar taji muryar Dije tana fad'in

" Gamu yau munzo a gidan nan!, zamu tsolale idon matar gidan nan!, don nasan tana saurarenmu a gidan nan!, gamu nan gamu nan zuwa wajenki ki fito Nan! ko mu zo da kanmu a nan wurin nan!, murkutus barakus matso nan! d'an jugumuna matso nan!, ku matso ku matso ku kamota a cen din!, don mu had'u mu tsigale idon nan!"

INNA ta zabura da k'arfi sai gata k'asa ta fad'o tim!, Har ta fasa k'ara ta yi saurin toshe bakinta, saboda har izuwa lokacin ba'a daina wakar ba sai ma maimaitawa da ake yi, INNA cikin rawar jiki da kyarmar tsoro ta fara bubbuga filon Baffah, har ta yi nasarar tashinshi cikin rufe baki alamun tsoro tana zaro Ido tana yi masa nuni da k'ofar d'aki, Baffah cikin firgici yace

"lafiya? Me aka yi ne na ganki haka"

Inna ta yi mashi alamu da ya sassafta murya cikin tsananin tsoro bakinta yana rawa tace,.

"Saurara ka ji"

Aiko Baffah ya taso ya tsaya jikin k'ofar ya kasa kunne yana sauraren wakar da Dije take yi, cikin fad'uwar gaba yace

"Innahu min Sulaimanu......"

Ya dawo cikin tsoro ya fara tofe Inna da addu'a shima ya tofe kanshi sannan ya nufi k'ofar da nufin ya bud'e, INNA ta zaro Ido tace

"Don girman Allah Kar ka bud'e"

Baffah ya juyo cikin rada yace,. "Ke a ganinKi don mun rufe d'aki bazasu iya zuwa su cire maki idon ba? To kinyi kuskure don haka Ni fita zanyi in basu hakuri in kuma Ni sun cire nawa idon a madadinki shikenan, sai da nace maki kar ki matsawa yarinyar nan ai gashi kin janyo muna jangwam!"

Ya nufi k'ofar cikin fushi ya fara kiciniyar bud'e d'akin aiko sai jin Suka yi garam! A guje dukansu suka nufi karkashin gado kowa yana turin Dan uwanshi domin ya samu ma b'oya.

Dije Kam jin muryarsu da ta yi ne ta shige d'akin Innar ta rufo k'ofar da sauri har sautin yace garam! d'in, don tsabar sauri ko sakatar bata saka ba ta dunkule gado tana minsharin k'arya, don nufinta ko da sun zo su taradda ita tana bacci don su gasgata abun da gaske ne ba shirinta ba.





Akafta🤣






D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*BAK'ON YANAYI BOOK NE MAI ZAFI HAR KUNA YAKE YI A HANNU SABODA TSABAR TSANANIN ZAK'INSHI BOOK D'IN BAK'ON YANAYI SALONSHI DABAN NE DA KOWANE BOOK DA KA TAB'A KARANTAWA A DUNIYAR LITTAFAI, ZAKU SAMESHI A ARHA DA FARASHIN NERA D'ARI UKU KACAL KUMA ZAKU SAMESHI A COMPLETE DINSHI CIKAKKE MAI B'UKATA TA NEMENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 SAYEN NA GARI MAYAR DA KUD'I GIDA SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI👍🏻 DOMIN KUWA BAK'ON YANAYI DAUKE YAKE DA NASHI KALAR SALO KALA KALA KUMA MABANBANTA MASU BURGE MAI KARATU DA SAKASHI SHIGA CIKIN SHAUKI YAYIN KARANTAWA💃🏻*



*Lamba ta 6*



Aiko mai makon taji shigowar su Inna sai taji saukar duka a jikinta, da sauri ta zabura ta fara sosa inda dukan ya sauka tana muzurai saboda ganin Yaya Usman a tsaye da bulalarshi a hannu, cikin fushi ya fara magana yana cewa

"Don Ubanki buge bugen Uban mi kike yi muna cikin dare?"

Dije ta zaro Ido waje tace,. "Buge buge kuma? Yaushe?"

Ya d'aga bulalar ya sake kai mata wani dukan aiko ta fasa Kara, Inna da baffa da tunda Suka jiyo sautin tafiyar Usman suka sha jinin jikinsu suna addu'a k'asa k'asa tamkar wasu sababbin larabawa, ihun Dije yasa Suka kalli Juna ba shiri Inna ta dafe k'irji tace

"Wayyo Ni Uwata wayyo Ubana Dije ALLAH ya kawo maki d'auki"

Baffah ya yi saurin kallonta yace,. " Mi kike nufi? Ai dole muje mu dubo mu ga meke faruwa"

INNA ta zaro Ido tace

"Wa? Ni! WALLAHI ka je dai nikam ba inda zanje kana jin tana zuba irin wannan ihun haka kawai ace tarko ne suka had'a man inje su tsigale man idanuwa su barni da kwarmin ido wayam ba komi"

Baffah ya maka mata wata jar harara ya fara gungurowa yana fitowa karkashin gadon, musamman kuwwar da yaji Dije tana zubawa yasashi k'ara kid'imewa ya nufi k'ofar d'akin a sukwane zai bud'e, daga cen karkashin gadon Inna tace

"Ka rufeni ta baya da kwad'o Don Allah kar ka barni a bud'e"

Baffah yayi saurin bud'e d'akin yana tofa addu'a a gaggauce saboda ihun Dijen da yak'i k'arewa, Aiko yana fitowa ya fara jiyo sautin Dije tana magiya har ya Kai bakin k'ofar ya dawo da sauri saboda sautin saukar dukan da yaji ana yiwa Dije, sai murzar hannu yake yi yana muzurai yana sake tofa wata addu'ar, sannan yayi kundunbalar fad'awa d'akin aguje kamar an jefoshi sai gashi karaf ya hango Usman da bulalar dokinshi yanata laftar Dije, cikin tsananin b'acin Rai ya d'auke Usman da wani bahagon mari sannan ya fisge bulalar cikin fushi ya fara fad'in

"Wane rashin Imani ne ya sakaka dukanta cikin wannan talatainin dare? Me ta yi maka da bazaka bari har safiya ta waye ba ka horatan?"

Usman cikin k'unar zuciya yace,. "Yanzu Baffah duk wannan iya shegen da take yi a cikin gidannan baka ji ba?"

Baffah ya yi saurin fad'in,. " Don naji

Please Login or Register in order to submit comment