Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka tace

"Tab! Kace dai shi d'in katon kafuri ne ya zo muna cikin gari? To sai ka barshi ta k'arfin tsiya tunda mu babu irinka marar sallah cikinmu"

Lawi yayi saurin Kai kallonshi ga Dije don yaga yanda take murgud'a Baki sai makawa Safwan harara take yi tana mui mui duk da baisan me take fad'a ba amman ya gano bakinta ba alkhairi yake fad'a ba, cikin wayancewa ya d'aga murya yace

"Magana kike yi ne?"

Dije ta yi saurin Shan jinin jikinta tace,. "Me kaji nace?"

Lawi yayi Yar dariya yace, "na zaci akwai wata tambaya dangane da abunda ya shige maki duhu akanmu ne"

Dije ta wani mere tace

"Ba komi wancen din ne kawai nake ta ganinshi Kamar ba musulmi ba"

Safwan yayi saurin Kai kallonshi gareta Aiko sai gashi ya gano fuskarta da idanuwanta da ya kasa mantasu tun lokacin da ta zuro kanta wajen lekenshi sukayi four eyes, aiko sai gashi da jin wani sabon b'acin Rai ya ziyartoshi, saboda daman cen da takaicinta da garin nasu duka ya kwana yana tsinewa wanda yayi tsanin postoshi garin, inda abokinshi Lawi yayi ta yi masa dariya don waya ma har sai da suka tambayi Maigarin yasa aka kaisu wani wuri nesa kad'an da cikin garin inda ake samun service, sannan ya yi waya da Yan gidansu ya sanar dasu halin da garin yake ciki don kada su kirashi suji basu sameshi ba su d'aga hankalinsu.

Shima Lawi yayi waya gidan nasu da abokan arzik'i sannan suka dawo zuciyar Safwan kamar ta fashe saboda takaicin garinsu Dije, da yake yiwa 'yan garin kallon bagidajai tamkar wasu mahaukata saboda kyankyaminsu da yake yi, don ko abincin da aka basu baici ba fiddo rishonsu yayi ya kunna ya dafa indomin da suka yo guzurinta kwali kwali, sannan ya kwankwadi ruwan gorarshi da ya zo dasu catoon catoon yasha ya jefar da gora sannan yaji hankalinshi ya dan kwanta.

Lawi kam sakin jikinshi yayi ya ci abincinshi kuma cikin dace yaji dad'in abincin don ba laifi basu da wata shahararriyar kazanta sukam.

Idonshi akanta yana jin tamkar ya shaketa a wurin, inda itama shi d'in take kallo tana yi tana harararshi tana murgud'a masa Baki tana mui mui.

Ranshi a matuk'ar bace ya mike ya koma d'akin da aka basu zuciyarshi cike da kuna tamkar yasa bindiga ya bindige kowa ma na garin yake ji saboda takaicinsu da abunda Dije ta yi masa yanzu.

Dije kam binshi ta yi da kallo tana yi masa hararar gefen Ido har ya bar wajen, sannan ta cije lebe tana wassafa irin matakin da zata d'auka a kanshi don ta ga kanshi yana rawa.

Har aka gama jawaban aka watse tunaninta baya wajensu tafe take zuwa hanyar Gidansu tana tunanin abunyi har taje Gida, aiko tun da sassafe Dije ta shirya cikin uniform d'inta da sukasha wanki tun jiya da marece, ta linkesu ta saka a karkashin filonta suka kwanta luf tamkar anyi guga, sannan ta baje ta zuba kwalliyarta da digo digon kwalli a fuska ta ranbada janbakinta ram a Baki taja Jakarta tana yiwa Inna da Baffah sallama.

Inna ta bita da kallo tace,. "Lalle wad'annan bak'in turawa da Sa'a suke, irin wannan kwalliya haka sai kace ranar JUMU'A??"

Dije ta rufe fuskarta tace,. "So nike yi abani shugabar Makarantar Inna naji wani Malami ranar yana cewa duk wadda kayanta suka fi haske itace za'a baiwa, don naji ma ranar yana magana da wani Malamin wai Ni yakeso a saka"

Inna ta rik'e baki tace

"To kenan ba ta k'ok'ari ake bi ba??"

Dije ta yi saurin fad'in

"To ai nafi kowa k'ok'ari ke Inna shiyasa ma da bak'in suka zo Ni aka baiwa takarda na karanta, baki ga yanda na burge kowa ba saboda turancin da nayi ta karantawa kamar ba Ni ba"

Sai jin Suka yi ance "Kika iya karanta shirme dai, ai an fad'a mani komi bale ki zo ki dinga yiwa mutane bak'ar k'arya"

Usman da ke shigowa cikin Gidan ya katse masu firar, Dije ta zunburo Baki ta yi d'akin Baffah tace

"Baffah na tafi sai na dawo kayi man addu'a"

Baffah ya fito yana yi mata adawo lafiya ta fice cikin sauri don gudun Usman ya ci gaba da fallasa gaskiyar karyar da ta yiwa Innar.

Tun daga nesa ta hango Mutanenta da ke zaune bakin doguwar barandar ajijuwan hudu da ke Makarantar, wad'anda su kadai ne a duk fad'in Makarantar saboda rashin Muhimmancin da basa baiwa bokon bale har su nemi gudunmuwar gwamnati akan ta k'ara masu wasu ajujuwan domin k'ara fadada Makarantar.

Dije kam tana hangosu ta had'e Rai fuska murtuk'e alamun ba wasa tana tafe tana wasa da Karen da ke hannunta har ta zo ta gabansu zata wuce ko kallo basu isheta ba, Lawi ya bita da kallo yana dariya Safwan kam a hasale ya ce

"Hey you come here"

Dije ta waigo ta murgud'a masa Baki taci gaba da tafiyarta, aiko ya kara d'aga murya yace

"Stupid girl I say come here"

Dije ta waigo ta sake murgud'a Baki ta yi gaba, Lawi da dariyar da yake makalewa taso fitowa yayi saurin fad'in

"Da ke ake magana fa ko baki ji bane??"

Dije ta waigo cikin dan guntun ladabinta tace,. "Ai ni to bansan me yake cewa ba"

Lawi ya had'e fuska yace,. "Ki zo aka ce"

Dije ta dawo tana cin magani tace,. "Ai Naga banyi latti ba shiyasa"

Ta zo ta tsaya kansu kikam tare da rik'e kugu tana yiwa Safwan wani mugun kallo sannan ta kalli Lawi tace,. "Gani Malam"

Lawi yana kumshe dariyarshi yace,. "Kinga wanda ya kiraki nan ko shi ba Malamin bane?"

Dije ta kawar da kanta a gefe ba tare da tace kanzil ba, cikin fushi Safwan ya ce da ita

"Stupid girl kneel down!"

Cikin tsawa yayi maganar ya taso Kamar zai daketa, Dije ta yi saurin durkusawa k'asa cikin gunguni tana fad'in,

"Kaci sa'a nasan wannan da WALLAHI bazan durk'usa ba"

Aiko cikin fushi Safwan ya cira hannu ya gaura mata wani azababben mari, tare da nunata da yatsa cikin harshen turanci yace

"Zaki fad'i abunda kika ce ko sai na kifar da ke a k'asa??"

Dije dafe da gefen da tasha marin ta fara zubar da hawayen takaicin tozarcin da yayi mata a gaban sauran yaran garinsu masu jin tsoronta, aiko cikin takaicinta Safwan ya sake katsa matavwatw tsawar cikin turancin yace

"Ba zaki fad'a ba??"

Dije kam ganin zai sake dukanta ne yasa ta tashi ta yi tsalle ta fad'i k'asa dabas tare da kwallah wata Uwar k'ara tace

"Ayihuhu maza bisa kanku"



Akafta😛








D/AUTA CE


*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*Jinjinar ban girma gareki HAJIYA DUDUWA mai abun mamaki🤣*

*BAK'ON YANAYI littafine mai tafe da nashi kalar salo Wanda yasha banbam da sauran littafan da kuka tab'a karantawa a duniyar littafai, kar ku Bari ayi babu ku Naira 300 kacal zata baku damar tantance gaskiyar abunda na fad'a ma ku, mai bukatar littafin ta tuntubeni ta wannan number 09032685442 sai kun zo sayen nagari mayar da kud'i gida👍🏻*


*Lamba ta 11*


Ido sama ta fara sambatunta da ta saba kullum tana fad'in,. "Ya kai dan Sarkin aljanun yankin barakutusa, ya kai yariman sunbulowa ya kai dan gidan wargaza gumurzun jadduniya, ku garzayo duka anan yau ga ranarku ta zo mu taka rawa mu juyawa bikin cin dafuwar kan mai wankan injin, ku had'a wuta ku zuba ruwa a tukunya yanzu zan tsige maku Kan in baku kuje dashi bakin ruwan tekun bangon duniya, acen zamu yi shagalinmu na yau"

Tana k'are surutan ta mik'e tsaye tana wani juya idanuwa ta zo gaban Safwan tana wani kyarmar jiki tana dalalo da miyau tana wassafa irin shakar da zata yi masa tana shakku, aikuwa dai ta yi jarumtar yin kundunbalar keta wata arniyar kuwwar tace

"Gareeeeeeeki Lugudaniya"

Aikuwa ta cafko wuyanshi iya k'arfinta ta fara yakuce masa wuyan da fuskar duka, cikin azama ya saka hannu d'aya ya fisgota ta fad'i k'asa Tim! Kai tsaya ya d'aga hannu ya kara sharara mata wani marin, Dije ta mik'e ta sake yin cikinshi da yakushi ganin zata ji masa rauni ne yasa ya nufi wani iccen dalbejiya yayi tsalle ya katso wata k'atuwar bulala, Dije kam bata daina biyarshi tana yakucinshi ba don ma da abun yayi mata dad'i har da su cizonta take Kai masa hari dashi, yana samun sa'ar saita bulalar ya ware iya karfinshi ya dinga lafta mata bulalar, tun tana juriya itama tana yin cikinshi da yakushin da cizon har ta Kai ta fasa wata k'arar dole saboda zafin bulolin da ya ke sauke mata a jiki, ba shiri ta fara fad'in cewa

"Sai mun kasheka sai mun tsige maka idanuwa, sai mun nakasa maka k'afafuwa sai mun cire maka halshe"

Safwan kam bai daina dukanta ba har sai da yaji ta fara fad'in

"Nice Dije su sun wuce ni ce na iso yanzu WALLAHI nice Dijengalar Baffah da Inna Hasiya, kanwar Usmanu mijin Hansai, abokiyar Ladiyo da jummala"

Gano da gaske ita d'in ce ba aljanun ba yasa ya daina dukanta ko shi sai da Lawi ya zo ya rik'e bulalar, tare da wasu malamai biyu da suka zo suna bashi hak'uri, saboda zafin kan Safwan ba mai sauk'i bane don da ace Dije tasan koshi d'in wanene da bata yi wannan wautar gareshi ba, don kam iya gaskiya Dije ta daku iya dakuwa a hannunshi, don haka ta baje k'asa tana ta tumurmusau tana kuwwar wayyo ita ALLAH ya cire mata zuciya ya karya mata hannu da k'afa saboda tsananin azabar da tasha.

Lawi ya kalleshi ganin yanda yake ta wani sauke numfashi mai cike da tsagwaron fushi da b'acin ran da ya bayyana akan fuskarshi cikin harshen turanci yace dashi,.

"Cool Dawn my man wannan fa ba Sury bace bale ka yi ta dukanta haka, idan wani abin ya sami Yar mutane zaka sakamu shiga Uku fa"

Cikin fushi tare da d'aga murya Safwan ya yi magana cikin turancinshi da ya zame masa jiki yace,.

"WALLAHI I can't tolerate any stupid nonsense from this villagers people, more especially that black cat, WALLAHI I will teach her lessons"

yana k'are fadar maganar ya bar wajen cikin k'unar rai ya nufi wani office d'in da yake da tabbacin nan ne d'akin Malamai, Lawi ya bishi da kallo ya girgiza kai sannan ya nufi inda Dije take ya ce da kawayenta su Mune su rikata ta tashi, sai dai kowacensu tsoro ya hana su yi abunda ya sakasu saboda sanin wacecen Dijen, Lanti ce ta yi jarumtar zuwa ta rik'o hannunta tace

"Yi hakuri Dije ALLAH zai saka maki tashi muje aji za'a fara yimuna karatun"

Dije da ke kuka har lokacin iya k'arfinta ta yi banza da ita, Lawi ya k'araso wurinta yace

"Ki yi hakuri ki tashi kije class dinku za'a fara yi maku karatu"

Dije ta yi wata zabura Lanti da su Mune duka suka yi baya da sauri cikin tsoronta, ita kam tana tashi ko ta kan talkaminta bata bi ba ta nufi hanyar gida tana tafe tanata rera kukanta har ta isa Gida, tana zuwa ta fad'a d'akin Inna ta dunkule saman gado sai gurzar kuka take yi, cike da mamaki Inna take ta tambayarta lafiya? Me aka yi mata? Amman kuka yaci k'arfinta, dakyar Inna ta samu ta yi shiru sai ajiyar zuciya take yi wata bayan wata tana ciccika, Inna tabi jikinta da kallo da duk shatin bulalar ya fito rad'am a jikinta duk da kasancewarta bak'a, cikin sanyin jiki tace da ita

"Wa kika jangalo yau wanda yafi karfinki yayi maki irin wannan dukan hakan?"

Dije kam tambayar Inna tasata fashewa da wani sabon kuka tana sauke ajiyar zuciya cikin kukan tace,.

"WALLAHI Inna sai na kasheshi"

Inna ta zaro Ido waje tace, "ke Dije ki kiyayeni kar ki janyo in k'ara yi maki wani dukan a yanzu, WALLAHI ahir dinki kada in sake jin irin wannan kalami ya fito a bakinki, ke da wa halan? me kika yi masa ya yi maki wannan dukan gashi duk ya farfasa maki jiki haka?"

Dije ta saka bayan hannu ta share hawayenta tace,

"Wani bak'in kafuri ne cikin malaman da aka kawo Garin nan"

INNA ta zaro Ido waje tace, " cikin bak'in Yan birnin??"

Dije ta d'aga kai tare da saukowar wasu hawayen, Inna tace

"Me kika yi masa"

Dije tace "banyi masa komi ba don kawai zan wuce naga Yana hararata na rama shikenan ya kamani yanata jibga kamar ya samu jaka, har da cewa wai Kuma har ku zai had'e ya daka yaga uban da zai hanashi a garin nan"

Inna ta yi mata wani kallon rashin yarda tace, "ki fadi gaskiya Dije don nasan da Baffanki ya dawo sai ya nemi jin ba'asin mafarin abun, kada kije ki sakashi jin kunya a gaban mutane"

Dije ta Fara rantsuwa tace, "WALLAHI ALLAH har cewa yayi sai ya turo mota daga birni an rushe gidanmu, kuma ni yasa a saceni a tafi Dani birni a sayar da kaina yayi kud'i"

Inna ta zabura cikin tsoro tace,. "To gashi Kuma kince baki yi masa komi ba, to haka kawai don kinfi kowa bak'in jini zai ce ya dakeki ke kad'ai? Akwai dai bari Baffanku ya dawo shi zai je yaji komi ai tunda ke kink'i fad'in gaskiya"

Inna ta fita ranta a b'ace da ganin dukan da aka yiwa yarta duk da zuciyarta ta bata cewa da walakin goro cikin miya, don kuwa tabbas banza bazata kai zomo kasuwa ba, dole dai akwai abunda tayi masa ya daketan.

Aiko sai gashi kafin kace me zazzab'i ya rufe Dije saboda kukan da tasha da zugin da bulolin suke yi mata, Koda lokacin tashi Makarantar yayi Lawi dakanshi yasa su Mune suka kawoshi gidansu Dijen, domin ya zo ya baiwa Iyayenta hak'uri duk da yasan itama bata da gaskiya, amman don a Sami zaman lafiya ya zo sai dai Baffah da Usman duk basu gidan Dole sak'o ya baiwa su Lanti su fad'awa Inna Hasiya, Ladiyo da su Jummala sunata yi masa godiya da kirkinshi da ya nuna masu a cen Makarantar, cike da jin dad'i suka shiga Gidan sai dai ganin Dije lullube tana rawar d'ari yasa duka jikinsu yayi sanyi k'alau, Inna ta washe baki tace dasu

"Yawwa Jummala ku fad'a mani me ya had'a Dije da Bakon dan birni??"

Lanti ta bayyanawa Inna komi da ya faru, sannan suka bada Jakarta da talkaminta da ta baro a aje mata, suka dubo Dijen da ke ta ta bacci sharkaf tana nishin ciyo, kowacensu cikin tausayi ta nufi gida, Inna kam sai cisgar fad'a take yi ita kad'ai saboda ganin ashe ma Dijen ce ta janyo aka lakad'a mata irin Wannan shegen dukan gashi ta janyowa kanta ciyo.



An fara wasar fa😹



Akafta🤾🏻‍♂️






D/AUTA CE✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*





*MUTANEN DIJE K'ARANGIYA INA GAIDA KOWA Team Dije da team Safwan ALKHAIRIN ALLAH YA KAI MAKU HAR GADON BACCINKU DUKA👍🏻*


*Lamba ta 12*


Ko da Baffah ya dawo shiru shiru bai ji duriyar Dije ba tun yana zura idon ganin ta inda zata bullo har ya gaji dai ya tambaya, don ita kanta Innar ganinta da yayi sai a hankali yasa ya zargi ko sun k'ara kwatawa ne da Dijen shiyasa yaji Gidan shiru alamun bata nan, Inna kam bata so sanar dashi ba har sai ya ci abinci don tasan muddin yaji ba k'aramin d'aga hankalinshi zai yi ba, sai dai dole ba yanda ta iya saboda yanda ya matsa mata da tambayar ina Dijen taje har lokacin bata dawo Gidan ba?.

Kai tsaye ta ce dashi tana ciki bata da lafiya, hankalin Baffah a tashe ya garzaya d'akin Innar inda Dije take kwance cikin zazzab'i sharkaf sai nishin marasa lafiya takeyi, aiko tana ganinshi ta fashe da sabon kuka gwanin ban tausayi, cike da fad'uwar gaba Baffah ya zauna bakin gadon ya rik'o hannunta yace

"Meke maki ciyo?"

Dije ta share hawayenta cikin rawar murya tace, "jikina gaba d'aya ciyo yake yi man ga raunukan sai zafi suke yi man Baffah, WALLAHI saura kad'an a kashe maka ni yau da baka zo ka sameni ba"

Baffahn ya zaro Ido waje yace,. "Wanene da wannan danyen aikin gareki halan?, Ashe ko yau ba zan saurarawa kowa a gidan nan ba tunda har abun ya zo da cin zarafi irin haka, ki yi gaggawar sanar dani wa ya dake? tashi zaune ki fad'a man don in san irin matakin da zan d'auka kan mutum ko ma wanene"

Dije ta yunkura dakyar ya rikata ta tashi zaune cikin kuka ta fara nuna masa raunukan da Safwan ya ji mata ciyo, Baffah kam ganin jikin Dije duk shatin bulalar yasa ya fara zuba ruwan fad'a bakinshi har kumfa yake yi saboda tsabar b'acin rai, Inna kam ganin yanda ya hau da yawa yasa ta fayyaace masa komi da aka fad'a mata ta sanar dashi, akan wanda ya dake tan tare da dalilin da ya janyo ya yi mata dukan.

Baffah cikin tsananin b'acin Rai ya ja talkamanshi sai Gidan Maigarin, inda kai tsaye ya fara nuna rashin dacewar abunda BAK'ON Malamin yayi wa 'yarshi, Maigari da sauran mutanen da ke wurin Suka dinga bashi hak'uri sannan cikin tattausan kalami Suka nuna masa aibun abunda Dijen ta yi masa wanda Sam Sam bai dace da tarbiyyar dalibi ga malaminshi ba, tun yana ganin laifin Safwan har ya kai ya gano ashe rabin laifin duk na Dijenshi ne, sannan Maigarin da mutanen Suka fahimtar dashi sosai akan ya tsawatarwa Dije akan sake faruwar wata hatsaniya tsakaninsu, daga k'arshe suka bashi hak'uri akan abunda aka yiwa Dijen , sannan ya baro wurin ya koma gida inda dakyar da jib'in goshi ya samu tasha yan farau faraun fura sannan tasha pracetamol ta koma ta kwanta, cikin dabara Baffah yayi ta kwantar mata da hankali akan muddin Safwan d'in ya sake dukanta ta zo ta sanar dashi don wannan karon shi da kanshi zai rama mata, ba ko Malami yake ba ko hukumar ce da kanta sai dai idan an rufeshi mabudin ya b'ace.

Sannan Dije ta rage bak'in cikin da ke cin zuciyarta, amman fa tasha alwashin sai yasan da ita yake zancen, haka ta kwana tanata wassafa irin muguntar da zata yi masa, cikin ikon ALLAH kwananta biyu ta warke Masha ALLAH,a rana ta uku da komawa Makaranta ne ta ci alwashin sai taje school d'in ko don labarin da su Jummala suke ta bata kullum akan yanda suke gane karatunsu, duk da dai shi Safwan d'in ba hausa yake yi masu ba amman dai ba laifi suna dan fahimta sama sama.

Aiko ranar Alhamis tun da sassafe ta shirya cikin uniform d'inta, ta yi sallama da su Baffah cikin natsuwa ta nufi Makarantar, don shi Baffah har so yayi ta daina zuwa Makarantar a cewarshi tunda ba ta ALLAH ba ce, don dai ita Dijen ta nace tana son karatun ne yasa ya amince amman ya ja kunnuwanta da kyau akan ko kallon Safwan d'in kada ta sake yi don gudun wata sabuwar fitinar, sai da ta yi masa alk'awali sannan ya barta akan zata koma d'in, don tun lokacin da tasha dukan ta zama wata so silent da ita ko rashin jin cikin Gida duk ta daina yi, saboda kwata kwata ko walwala daina yi ta yi a gidan kullum tana d'akin Inna dunkule kan gado, don duk masifar da take yiwa akuyarta idan ta zubar da abinci ko abinsha, a lokacin duk ta daina don acen baya har bulala take sakawa ta yi ta dukan akuyar tana yi mata fad'a da kashedi kala kala, har wani zubin sai Inna ta yi mata fad'a akan zalin d'in akuyar da take ci sannan take kyaleta, amman sai gashi Safwan yasata zama kurum kurum dolenta.

Aiko tafe take kanta a duk'e tun da ta hangosu daga nesa ta Sha mur tare da saita natsuwarta, don ko da ta zo ta gabansu sai da ta dan rankwafa sannan ta gayar dasu sai dai bata jira sun amsa ba tayi gaba abinta, Safwan ya bita da wata jar harara yayi kwafa yace

"Mumu kawai black cat"

Lawi ya kyalkyale da dariya yana dafe bakinshi don kada Dijen ta jiyo dariyarshi, amman duk da hakan bai hanawa kunnuwanta ji ba sai dai ko kad'an bata waigo ba har ta shige cikin class dinsu.

Dan lokaci a tsakani sai gashi ya shigo ajin yana wani cin magani ya jefa mata chalk tare da nunata yace ta goge allo, ta mik'e ba tare da ta yi gardama ba ta goge black board d'in tass ta koma ta zauna, daga nan ya fara karatunshi mai cike da zallar turanci tsintsa don mugunta duk ya zo tambaya sai ya tambayeta saboda kawai ya kureta,
Wani lokaci ta bashi amsa dai dai wani kuma idan bata iya ba ya kirata jahila, haka ya k'are darasin nashi cikin isa da gadara ya koma tambayoyin cikin tambayoyin ne kawai sai ga wani bera tun daga cen saman rufin ajin ya fado tsakiyar class d'in saboda rufin ajin gaba d'aya duk ruwa sun canye rabin, aiko ba shiri yayi wani tsalle cikin tsoro yace

"Oh my gosh"

Bera ko kamar ya san tsoronshi yake yi garin gudun neman mafaka ne ya nufi wurinshi, aiko sai ga Malam Safwan da yin wani uban tsalle ya dale window yana sambatu irin na tsoro, ganin hakan yasa duka Yan ajin suka fara dariya k'asa k'asa, Dije kam fuskarta a had'e tamau tamau ba alamun ma zata yi dariya, bayan beran ya wuce ne a gurguje ya kammala karatun ya fice, Dije ta kalli Yar paper'r da ke hannunta ta fara karanto abubuwan da duk yayi ta fad'a mata kalmomi kanana na turanci kamar haka

Illiterate.
Black cat.
Urgly girl.
Village girl

Sai maimaitasu take yi amman ta kasa tantance fassararsu bale tasan ma'anarsu, a ranta ta kudurta zata tambayi abokinshi domin ya fassara mata su fillah fillah, Aiko kai tsaye ta fito ajin aka yi dace ta hangoshi cikin wani class yana karantarwa, aiko taje da sallamarta cikin ladabi tace dashi wurinshi ta zo, ya yi Yar guntuwar dariya ya d'auki excuse wurin Yan class d'in ya fito, cikin sakin fuska tace dashi don ALLAH wata tambaya take son yi masa in da Kai tsaye ta fara zayyano sunayen a kanta da ta samu ta hardace su cikin kanta.

Lawi yayi shiru yana tunanin amsar da zai Bata wadda ranta ba zai b'aci ba, don zuciyarshi ta bashi cewa duka kalmomin daga bakin Safwan suka fito zuwa gareta don yasan k'aramin aikin abokinshi ne wannan, aiko dai ya koma class ya dauko wani littafin kalmomin turanci da fassararsu cikin harshen hausa ya mika mata yace taje ta duba da kyau zata gano fassarar kalmomin duka a ciki, cike da jin dadi Dije ta karb'a tana murna har ta juya zata tafi ta waigo tace

"Don ALLAH ka ara man shi nan da kwana Uku zan maido maka"

Yana dariya yace,

"Na baki sati d'aya ma amman ki sani akwai tambayoyin da zanyi maki idan lokacin ya cika kin kawo"

Cike da jin dad'i tace ta amince ta koma class dinsu zuciyarta cike fal da murna, tare da tunanin hanya mafi sauk'i da ta gano wadda zata rama abunda Safwan d'in yayi mata cikin dan kankanin lokaci.

Har aka tashi Makarantar Dije bin littafin take yi d'aya bayan d'aya shafi bayan shafi har ta gano abunda duk yake nufi da miyagun kalmomin da ya yi ta jifarta da su kala kala.

Tsawon kwana biyu Dije tana kamun beraye tana sakawa kwali tana b'oyewa don har da abinci da ruwa take ajiye masu, don kuwa ta kama bera yafi ashirin irin bakake d'in nan manya manyan, kullum Inna da Baffah sai dariya suke yi mata suna fad'in

"Dije Kuma aikin kiyon beraye kika koma yi ??"

Sai dai tayi dariya amman bata nuna masu cewa wani nufi ne a ranta ba, sai ko gashi tun da sassafe zata je Makarantar Allo ta yi dubarar fita da k'aton kwalin berayen, bata zame ko'ina ba sai Gidan Maigarin cikin nasara ba kowa a wajen ta yi dubarar ajiye kwalin ta je k'ofar d'akinsu Safwan ta leka, sai ko gashi shi kad'ai a d'akin yanata baccinshi hankali kwance.

Dije ta d'auko kwalin ta shigo bakin d'akin a hankali ta kwantar da kwalin ta budeshi Aiko sai ga Beraye suna ta fitowa daga ciki suna shigewa cikin d'akin sai da

Please Login or Register in order to submit comment