Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake yi fa"

Inna ta yi saurin faɗin,"Ni kaina da na haifeki ai idan kika kaini bango watarana ina dukanki ko kin manta ne?, To shikenan don kinyi laifi na dokeki sai ace ban sonki? Saboda haka idan kina son ki ƙwato ƴancinki gareshi to ki zama mace kamar sauran matan garinsu kafin ya dawo, in da hali ma har ki fisu natsuwa da kamun kai har ma da gayun gaba ɗaya, ke ko ki ga yanda zai dawo yana lallaɓaki don gaban kowa baya shayin nunaki matuƙar kika zama yanda yake so, sannan kika zamo dai dai da yanda na lissafo maki, amman idan kina wannan shirmen me zai hana ya jibgeki ko?, tunda ke kanki kinsan kunnuwanki ba jin magana suke yi ba"

Haka Inna ta yi ta cusawa Dije ra'ayin son abunda zai sa ta ƙwato yancinta wajen Safwan, saboda a matsayinta na Uwa ta fahimci cewa har yanzu ba wani abu da ya shiga tsakaninsu na auratayya, kuma har ga ALLAH tana son su Hajiyar su ji daɗin zama da Dijen, kamar yanda ta ga ita Dijen hankalinta ya fara kwantawa da su, saboda kyawawan dabi'unta da zata nuna masu su zai sa ta samu matsayi fiye da yanda ta samu yanzu garesu, musamman shi uban tafiyar wanda take so ta zamo tauraruwa a wajenshi fiye da duk wasu mata da zai aura bayanta.


Suna cikin firar ne suka jiyo sallamar Ladiyo, Dije ta yi saurin washe fuskarta da fara'a tace

"Ladiyooo!"

Ladiyo ta zauna kusa da Dijen tana gayar da Inna, sannan ta kalli Dije ta ɓata fuska tace

"Yanzu Dije ki zo garin nan ki kasa zuwa wurina?"

Dije tana dariya tace, "na so zuwa fa Inna ce ta hanani wai......"

Kallon da taga Inna tana yi mata ne yasa ta yi shiru ba shiri, Ladiyo ta zubo da wasu hawayen takaici tace,. "Banga laifin Inna ba tunda har Bala bai ji kunyar karɓar kuɗi a madadinki ba, WALLAHI ki godewa ALLAH ma da bai zamo Mijinki ba, don yanzu haka ba yanda banyi da shi ba akan ya barni in zo in ganki yaƙi baki, yanzu haka ma bai san na fito ba saboda Duduwa bata gidan yana fita nima ta fito abuna"





To fa🙀🤣🤣😂





Akafta😝






D/AUTA Ce✍🏻


*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Ku yi haƙuri da rashin mayar da reply akan comments ɗinku wani lkc amman duk wanda ya yi ina group ɗin na gani duka kuma na gode sosai ALLAH ya bar ƙauna.*




*Lamba ta 41*


Inna ta yi saurin faɗin

"Haba Ladiyo wannan hali ba halin macen da tasan haƙƙin aure bane, don na tabbata ke ma kin san cewa abunda kika yi ba kyautawa bace, saboda haka sawunki a likkafa ki tashi ki koma gidan Mijinki, kuma ki yi haƙuri tunda har bai amince da ki zo ba, insha ALLAHu Dije zata zo har gidan naku sai ku gaisa"

Ladiyo ta miƙe tana matsar ƙwallah tace, "Don Allah Inna ki barta ta zo taje gidan kowa fa ni kaɗai ce bata zo wurina ba"

Inna tace,. "Yi sauri ki je kada ya dawo ya taradda baki nan insha ALLAHu zata zo tunda nace maki zata zo"

Ladiyo ta fice da sauri tana faɗin,. "Sai kin zo Dije ina jiranki kinji?"

Dije ta ce "kar kiji komi tunda har Inna ta bari ai zaki ganni, daman cen don ta ce kada in je ne shiyasa......"

Inna ta yi saurin buge mata baki da bayan hannunta tace,. "Shikenan ke ba za'a yi sirri da ke ba? To ni ba wai bana son ki je bane don wata manufa, tsoron nike ki je ki ɓallo muna wani aikin azo kuma ace ke ce mafari, amman yanzun ma ko da zaki je ban lamunta da inji wata mummunar maganar Bala ta shiga kunnuwan Ladiyo ba, ke shi kanshi ma ban amince da ki tankashi ba idan kin ganshi matuƙar ba gaidashi zaki yi ba"

Dije ta turo baki tace,. "Cabɗi ai WALLAHi Inna ban iya gaidashi lalle ma kam yaji daɗi nai"

Inna ta yi saurin kai mata wani mangari Dije ta miƙe cikin sauri ta bar wajen tana dariya tana faɗin,. "Wai ke Inna yanzu duk abunda Bala ya yi man baki ga laifinshi ba?"

Inna ta ce "ai mu godiya ma ya kamata mu yi masa ba muji haushinshi ba, don ke ma da kina da hankali da kin fahimci cewa hakan da ya yi taimakonki ne ya yi, don in banda shi da yanzu baki je makarantar da kike da gurin zama likitar ba"

Dije ta yi saurin faɗin

"Haka ne kuma Inna in don wannan kuma da wannan gaskiya, shege Bala shine ya ƙi yi man bayani tun farko in zo inyi masa godiya?"

Inna ta maka mata harara tace,. "Ke tafi cen sakarya sai aka ce dole shine zai yi maki bayani ba kece zaki hankalta da abun alkhairin da ya yi maki ba?, To yanzu dai gobe idan ALLAH ya kaimu kije gidan ki gayar da Duduwa har shi ma Balan ki gaisheshi ki yi masa godiya"

Dije ta washe baki tace, "aiko WALLAHi zan yi masa godiyar don na fahimci ba ƙaramin taimakona ya yi ba, yanzu ga shi ta sanadinshi na je birni na shiga makaranta idan ALLAH ya cika mani gurina shikenan sai in zama babbar Likita, kai Balan Duduwa dole ne inyi maka godiya yasin, Inna ko ma in je yanzu in dawo da wuri kafin ayi magriba?"

Inna tace,. "A'a ki dai bari sai goben yafi"

Haka ko aka yi goben tana yi bayan ta yi wankanta Inna ta ce ya saka tufafinta waɗanda suka fi kowane kyau cikin kayanta, sannan ta ɗauko kuɗi sababbi yan ɗari bibbiyu cikin waɗanda Hajiya Mama ta baiwa Dije wai ko da zata kasa idan ta buƙata, tace da ita ta je da su ta baiwa Inna Duduwa ɗari huɗu ta baiwa Jummala ɗari shida, ta ɗauko dubu ɗaya guda biyar ta ce idan ta ga Balan ta bashi ta ce ya yi cefane, sannan ta yi masa godiya, cikin hikima Inna ta dinga koya mata yanda zata yi da abunda zata faɗa, aiko Dije ta riƙe komi a kanta tana harda.

Sai ko ga Lanti da Mune sun zo suka taka mata suna ta yaba irin kyawon da ta yi, sai taɓa lesin da ke jikin Dijen suke yi suna jinjina kyawonshi, Mune ta kasa haƙuri sai da ta ce

"Lalle Dije ke kam kinji daɗi kin tako arziƙi wannan gayun haka ai ko birnin ma iyaka kenan"

Dije ta washe baki ta ce,. "Ai wannan ba komi bane idan kuka ga waɗanda aka saka man cikin kayan lefena"

Lanti da ta yi tagumi ta ce,. "Kinji daɗinki ke kam amman ko wannan ai ba ƙaramin kyau ne da shi ba"

Haka suka yi ta zuzuta Dije suna ƙara koɗata tana jin kanta a sama har da wani canza tafiya tana yanga kamar bata son taka ƙasa, har suka je gidan basu daina wasata ba.

Shigarsu gidan kai tsaye ɗakin Duduwa ta nufa, cike da fara'a Inna Duduwa ta fara tarbonta tana faɗin

"Lale marhabin da mutanen birni sannunku da zuwa, ashe muma zaki zo ganinmu? da har na fara yiwa Gambo ƙorafin rashin zuwanki ashe kina hanya?"

Dije ta yi ɗan murmushi tace, "eh daman ina da ƙudurin zuwa mu gaisa, yanzu kuma ga shi na zo na wanke laifina"

Duduwa zata yi magana sai ga Ladiyo aguje ta shigo tana wasar baki tana faɗin

"Sannu da zuwa Dije ashe da gaske kece kika zo?"

Dije tana dariya ta ce

"Nice kuwa ba wata ba to ya kika ganni"

Ta yi wani rawa da ido tana kallon kanta Ladiyo tace,. "Ai Dije ko kamshinki kawai aka ji ai ansan ke ɗin mai tsada ce balantana anyi arba da kyakkyawar fuskarki, ke ma da kanki kinsan kinyi kyau masha ALLAH da ke, ki godewa ALLAH birni ya karɓeki WALLAHi"

Duduwa ta miƙowa Dije kwanon faraufaraun da ta haɗo mata tace,. "Karɓi ki jiƙa maƙoshinki kar ki biye wannan uwar surutun"

Dije ta karɓa tana dariya ta ɗan kurɓa kaɗan ta miƙawa Lanti kwanon, tana goge bakinta da hankacif ta buɗe zif ɗin jakarta ta ciro ɗari biyu guda biyun ta miƙawa Duduwa tace,

"Gashi a siye goro Duduwa"

Duduwa jikinta yana rawa saboda tsabar farin ciki ta karɓa, sai zubawa Dije godiya take yi tare addu'a ba ƙaƙƙautawa, ƙarshe ma sai gata da ɓugewa da yiwa Dije kirari sai kace wata mabanya.

Dije ta riƙo hannun Ladiyo da ke ta wasar baki tace, "muje ke kuma inga ɗakin naki Ƙawata"

Ladiyo cike tsakanin jin daɗi ta ƙanƙame Dijen tana tsalle suka shiga sashen nata da aka keɓe da katangar da ta raba tsakaninta da Duduwar.

Dije tana zama Ladiyo ta fara jero mata kayan ƙurasa kala kala waɗanda suka haɗa da danginsu, Fara, kwai da kwai, ƙamƙam, ɗantamatsitsi, hanjinligidi, da soyayyiyar aya, saboda su ne sana'arta da take saidawa, Dije kam duk da kwaɗayinta gaba ɗaya ba abunda ta ci saboda jan kunnen da Inna ta yi mata, ganin haka yasa Ladiyon ta zuzzuba mata kowane a leda ta baiwa Lanti ta riƙa mata, sannan suka ci gaba da fira na ɗan lokaci kafin ta fiddo kuɗinta itama ta bata, Ladiyo cike da jin daɗi take ta yi mata godiya, sannan ta miƙe tana yi mata sallama Ladiyon ta rakota bakinta bai daina yi mata godiyar ba, Duduwa ma ta biyota sai godiya take yi mata sai gashi ko suka yi kiciɓis da Balan, yana ƙoƙarin zagayeta ya wuce don yi yayi kamar ma bai ganeta ba, Dije ta faɗaɗa fuskarta da fara'a tace

"A'a Malam Bala abun ba ko magana?, Ai sai ka tsaya mu gaisa ko?"

Bala ya fara sosa kai yana faɗin, "a'ah Dije ce? ai ban ganeki ba naga kin zama wata babbar Hajiya shi yasa"

Dije ta yi masa wani kallo tace, "ai dole in zama Hajiya Bala saboda ina tare da alhazawan, nan gaba kaɗan ma zan zo yi maku sallama idan zamu ta fi Saudiyya, ai dole ne in yi maka godiya akan abun alkhairin da ka yi mani, na gode sosai ALLAH ya ƙara lafiyar aljihu"

Ta saka hannu ta ciro kuɗin a jaka tace,. "Ga wannan ba yawa a ƙara ayi cefane"

Bala da gaba ɗaya kunya ta kasheshi cikin muzanta yace, "Da kin barsu kawai ai don har yanzu da sauran na cefanen"

Duduwa ta yi masa wani mere tace, "da dai ka karɓa don kada ta tafi ka dawo kana cizon yatsa"

Bala ya sosa ƙeya yace, "Ayi haka? "

Dije ta mazge tace

"Karɓi kawai ai an zama ɗaya Bala idan basu isa ba ka faɗa kawai sai a ƙaro maka ai, don insha ALLAHu zakkar da za'a badawa idan an tashi ka tsimayi zuwanta, ko don saboda Ladiyo ai ba'a rabu ba ana tare"

Bala ya zura hannu cike da jin nauyi ya karɓe kuɗin, ya fara godiya Dije ta ce

"Ai Ni ce da godiya WALLAHi na gode sosai ALLAH ya biyaka ya saka maka dai dai da taimakon da ka yi"

Duka suka rakota har bakin gida sai godiya suke zubawa, har ta yi nisa Bala ya biyota cike da ladabi ya rusuna yace

"Afuwa nake nema nasan nayi maki laifi ki yi haƙuri ki yafe man don ALLAH"

Dije ta waigo tace da shi

"Zan yafe maka kuma zan ci gaba da kyautata maka matuƙar ka riƙe Ladiyo amana, ka kyautata zamanka tare da ita kuma ka gyara halayyarka ta son kuɗi ka daina kiranta ɓarauniya, sannan ka gyara duk wata mu'amalarka da ita, to da ka yi hakan ka ɗauka cewa tamkar ka sami alkhairina da na Maigidana ne, amman muddin na ji cewa baka zama da ita yanda ya da ce to ka ɗauka tamkar ka datse igiyar alkhairanka garemu ne, saboda haka idan ka gyara ka ga da kyau a aljihunka, idan kuma ka ɓata to shikenan ka lalace komi, ni ka ga tafiyata kuma ka sani zan saka masu kula da komi, don kada ka ga bana nan to ina da idanuwa ta ko'ina a garin nan"

Bala baki washe ya ce

"Ai Insha ALLAHu alkhairi ma zaki ji amman itama zan turo ta wajenki ki ja kunnenta akan abubuwan da take yi mani, da ta gyara shikenan matsala ta kau gareni da yardar Allah"

Dije tace, "tace wannan ba damuwa bace sai ta zo kawai ALLAH ya sa mu dace dai gaba ɗayanmu ya bamu zaman lafiya"

Yace "Ameen Ameen ranki ya daɗe ai ke kin haye saura mu kawai"

Dije ta so ta yi dariya ta mazge tace, "kai m ka kusa hayewar matuƙar na dawo garin nan na ji labari mai daɗi"

Bala sai duƙe ɗuke yake yi yan faɗin, "kar ki ji komi insha ALLAHu komi zai daidaita"

Haka suka rabu Dije sai ƙumshe dariyar da take cinta take yi, su Lantin ma sai da ta basu ɗari biyu tace su raba, suka tafi gida suna ta jin daɗi.



Hannuna ya yi sanyi yasin😩





Akafta😆




D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*INA YINKU ALL MY FAN'S INA GODIYA🙏🏻 DA ADDU'ARKU GARENI KU DAƊE KU YI LASTING MUTANENA👍🏻*



*Lamba ta 42*


Dije kam tana cin kayan ƙwalam ɗin tana kyalkyatar dariya, tana baiwa Inna labarin abunda ya faru don ko da su Baffah suka dawo gidan ranar labarin ne kawai take ta basu ana dariya.

Haka Dijen ta ci gaba da ziyarar yan uwa da abokan arziƙi don har wani ƙauye suka je da Inna inda ainahin tushen iyayenta suke, kowa ya yi sambarka da auren Dijen don kuwa su ma sun sheda ta sanadiyyar tsarabar Dijen da Inna ta kai masu.

Satinta biyu dam a ƙiriu Direban da ya kawota ya zo ɗaukarta da uwar tsarabar ƙauyensu niƙi niƙi suka lula yola, bayan tasha kukan rabuwa da Inna da sauran ƙawayenta da yan uwa da abokan arziƙi, kowa da kalar tsarabar da ya bata ta kaiwa surukarta Hajiya Mama, don Maigarin kanshi galan ɗin manshanu lafiyayyen suya ya bada akai masu, Baffah da Inna kam babu ce kawai basu bayar ba don tsakanin tsintsiyar laushi, kuka, daddawa, guro, kayan yaji maburki, busasshiyar rama, gero, dawa, wake, niƙaƙƙen garin waken na ɗanwake lafiyayye, manja, manƙuli, soyayyar gyaɗa, kai kayan ƙwalam na Ladiyo ma ba'a barsu a baya ba, don kuwa kaf maƙulashenta sai da ta yo wa Dije tsarabarsu saboda takanas Bala ya bada kuɗi aka haɗa mata kayan.

Tafiyar wuni biyu ce ta kai Dije Yola cikin tsananin galabaita saboda rashin sabo da tafiyar, Ba Surry da Hajiya Mama ba har Fiddo kanta sai da ta nuna jin daɗin dawowar Dijen, saboda himilin kayan tsarabar da ta zo masu da su, Hajiya Mama baki har kunne sai godiya take zubawa saboda tsananin jin daɗin karamcin da su Baffah'n suka yi masu.

Kasancewar hutunsu Dijen ya ƙare kwananta biyu a gidan aka yi mata provision ta koma makaranta, ita kanta cike take da ɗokin ganin mutanenta sis Aysha da kuma ƙawarta Hannatu, saboda sunyi kewar juna ba kaɗan ba.

Kwanci tashi asarar mai rai sai ga Dijen Baffah ta shiga jerin sahun kowace mace a duniya, don kuwa ranar farko da ta fara ganin baƙon watanta duk house ɗinsu sai da kowa ya sani, saboda uban kuka da ta ci akan ita bata taɓa iskanci ba amman jini sai fitowa yake yi a jikinta, Wayyo ita ALLAH a taimaketa wani yaci amanarta ya iskanceta bata sani ba, Sis Aysha itace ta janyota zuwa toilet saboda uwar dariyar da taga anael yi mata, cikin natsuwa ta fahimtar da ita komi ta nuna mata ga yanda zata yi ta kimtsa kanta, sannan hankalin Dije ya kwanta amman fa tasha tsokana a wajen mutane ba kaɗan ba, lokacin da ta gama kwanakinta ma Sis Aysha itace ta yi mata gwari gwari akan yanda zata tsallake jikinta.


*Shin wai ina baƙin Turai ne?*


Malam Safwan kam tunda ya tafi Ƙasar ya yi ƙoƙarin danne damuwar da ya tafi da ita domin ya fuskanci karatunshi, sai dai wani gefe na zuciyarshi yana tunano masa Dijen Baffah da shirmenta, wani zubin ya yi dariya wani lokaci kuma ya ɓata fuska musamman idan ya tuno abunda Hajiya Mama take yi masa akanta.

Masha ALLAH kasancewarshi mutum mai tsattsauran ra'ayi yasa baya da wasu abokan kirki sai tsirara ko su just for mutunci kawai don shi miskili ne na gasken sosai, baya shiga shirgin kowa sai wanda ya dace ace ya shiga.

Wannan halin na shi ne ya janyo mata da yawa suka mato a kanshi, inda ko wace ƙoƙarin take yi ace itace ta yi sa'ar ƙulla alaƙa da shi, musamman ma da ya kasance gifted akan karatunshi ko kaɗan baya wasa, don daman cen shi tun asali yana baiwa karatu muhimmanci ko lokacin da ya yi karatun a gida Nigeria bale yanzu da ya shigo cikin fararen fata.

Matan turawan ma da yawa wasu sun ƙyasa ballantana na mu matan na baƙar fata masu zuwa cen karatu, sai dai rashin fuskarshi yasa kowace take ɗar ɗar da shiga sabgarshi don tsoron kada ya yanƙwanasu su ji kunya, amman a hakan sai da wasu turawa suka sami kanshi suka fara mutunci da shi, a cikin baƙaƙen fatarmu namu ma akwai mace ɗaya Zainab wacce ake kira da Zee bab da Namiji ɗaya Auwal da suka sami sa'ar shiga rayuwarshi, waɗanda su kansu yan asalin Nigeria ne sai dai kowane daga cikinsu suna garuruwa mabanbanta, zee Bab yar Gombe ce yayin da Auwal yake ɗan asalin Kano, wasa wasa sai gasu sun zamo aminanshi waɗanda komi zasu yi dole ne sai sun nemi junansu.

Zee Bab kam gurinta na shiga rayuwar Safwan ya cika don kuwa sannu a hankali ta fara nuna masa irin yanda ta damu da shi, kasancewar ba directly ta fito masa ba shiyasa bai hantareta kamar yanda ya saba yiwa sauran mata ba, cikin dabara ta ƙulla alaƙar soyayya da shi mai ƙarfi, wadda ta kai basa shayin nunawa duniya irin yanda suke son junansu ko a gaban ma waye, har suna iƙirarin zasu auri junansu duk runtsi duk da cewa itama Zee ɗin tana da mijinta da zata aura acen gida Nigeria.

Sai dai akasin da aka samu shine ranar da Safwan ya sanarwa da Hajiya Mama labarinta rufe ido ta yi fata fata da shi, akan cewa bata lamunta da ya auri kowace mace ba har sai ya mutunta auren Dije tukunna, shi ko ya nuna mata shi fa ba sonta yake yi ba yanzu ya sami matar aure kuma ita yake so ya aura, don hasali ma ita kanta Zee ɗin bai sanar da ita cewa yana da wata mata ba, saboda rena auren Dijen da ya yi a tunaninshi da ya auri Zee zai korata ta koma ƙauyensu, idan kuma Hajiya ta bashi dama zai cikawa amininshi Lawi alƙawalin da ya yi wa kanshi na duk runtsi sai ya mayar masa da ita ya aureta tunda har ya fishi sonta.

Sai dai kuma gashi Hajiya Mama tana son dakushe masa karsashi, don shi kam sun riga da sun daidaita da Zee akan da ya kammala karatunshi zasu dawo gida Nigeria ayi aurensu kawai.

Akan haka ne ma rashin fahimta ya shiga tsakaninshi da Hajiyar, idan ya kira wayarta ta ƙi ɗauka ya galabaita sosai da mugun fushin ta yi da shi sosai, saboda duk Iyayenshi maza ya yayunshi biyu mata da suke aure duk sunyi ta bata haƙuri akan ta barshi ya yi auren amman ta yi biris da kowa, tace in dai har akan ta goya masa baya ne ya yi wani auren ya ci amanar yarinyar mutane to bazata taɓa lamuncewa da auren ba, jin wannan kalaman nata masu tsauri yasa ya ajiye komi ya nufo Nigeria ba shiri, sai dai yanayin da ya taradda ita ya sa ya ƙara gasgata zancenta dole marairecewa akan neman biyan buƙatarshi, tare yi mata bayanin cewa shi ba zai ci amanar Dijen ba, asali ma so yake yi ya haɗata da masoyinta na asali tunda har ya sami matar da yake so.

ganin ta ƙi amince cewa ne yasa ya kwaso mata mutane suka zo suna bata baki kowa da abunda yake cewa dangane da ALLAH ya ce Annabi yace, ana roƙonta akan ta barshi ya yi aurenshi kafin ita Dijen ta mallaki hankalinta tasan minene auren, da ƙyar aka shawo kanta amman da sharaɗin duk ranar da Amaryar ta tare itama Dijen a ranar za'a kaita gidanshi a matsayinta na uwargida, hankalinshi ya ƙara tashi ya ruɗe gaba ɗaya saboda tsoron Zee taga kamar ya munafunceta tunda bai ce da ita yana da wata matar ba, aikam ba kalar magiyar da bai yi mata ba akan ta janye zancen tariyar Dijen sai daga baya idan Zee ta zo, amman Hajiya Mama tace sam! Bata san da wannan zance ba, dole ba kuzari ya harhaɗa kayanshi da nufin komawa, saboda yanda ita Zee ɗin ta dameshi akan ya dawo ya dawo.

Hajiya ta ce da shi kafin ya bar ƙasar ya je makarantarsu Dije ya ganota, amman don kada ma ta gano ba zuwan zai yi ba ya nuna mata cewa zai je har da cewa ta kawo saƙo, aikam sai ga shi saƙon ma da ta bada akaiwa Dijen aika mata ya yi shi ya fece, zuciyarshi cike da mugun jin haushinta saboda shiga rayuwarshi da ta yi, uwa uba yanzu da ta sanadinta aka hanashi yin abunda yake so, don shi bai ma san da wane kalar idon zai kalli Zee ya sanar da ita cewa wai yana da mata, kuma matar ma irin Dije ai wannan ma shi idan ta sani ya zubarwa da kanshi aji, shiyasa ya ci alwashin ba zai taɓa bari tasan da wannan mummunar maganar ba, har sai idan an ɗaura masu auren da ita idan ta zo ta gani da kanta ta ji da kunnuwanta, akan haka ya tsayu suka ci gaba da zuƙar soyayyarsu hankali kwance, duk da kuma wani gefen na zuciyarshi cike yake da fargabar Zee ta san da labarin kafin aurensu.

***

A cen ƙauyensu Dijen kuma anyi auren Usmanu da Hansai, Dijen ma ta je amman kwananta biyu ta dawo Yola saboda a lokaci ana cikin karatu ne excuse ne aka ɗaukar mata, ƙawayenta kuma su Jummala da Ladiyo ma masha ALLAH zamansu lafiya, sun ajiye shirmen yarinya sun fuskanci zaman aurensu, sai dai Balan Duduwa da kullum tsimayi yake yi zuwan ranar da Dijen zata aiko masa da zakkar, shiyasa lokacin da ma ta zo bikin Usmanu yake ta rawar jiki akan bata wani girma na musamman, ganin hakan yasa ta sake yi masa wata kyautar duk da cewa a lokacin itama buƙace take da kuɗin saboda guntayen matsalolin hidamar auren Usmanun, don ba ƙaramar hidima aka yi ba saboda ko ɗakin Hansai shafe yake fess da broking tyles, Mutane sai zuwa gani ake yi ana sontin sulɓinshi, don kaf garin ɗakinta ne kaɗai da tyles ɗin don Inna cewa ta yi ta haƙura bata so ita kam ta yafe.


*****

Kwanaki suna tafiya makonni su zo su wuce, wata ya wuce shekara ta zo wasa wasa sai ga shekara biyu an laƙumeta ba tare da an tantance ba, bikin Surayya ya zo sai hada hadar bikin ake yi bangaroran biyu, waton gidan ango da na Amarya saboda daman cen angon ne ake jira ya kammala ginin gidanshi, Alhmdllh kuma ya kammala masha ALLAH yanzu haka saura sati biyu ayi auren nasu, Safwan ma kanshi saura shekararshi ɗaya ya kammala karatun da ya je yi ya dawo gida, ayi aurenshi da masoyiyarshi Zainab wadda a yanzu yake jin akan sonta ba gudu ba ja da baya.

Dijen Baffah ma a lokacin tana J.a.s.s 3 zasu yi j.l.c su wuce s.s 1, a lokacin idan kika ga Dijen Baffah ba zaki ce itace ba, saboda yanda maƙerin ƴanmata ya fara ƙereta ta ko'ina ta cike masha ALLAH, kwanciyar hankalin da ta samu ya fito jikinta ya haskaka mata fatarta, don a duba ɗaya zaka gano tsantsar kyawon halittar da ALLAH ya yi mata, uwa uba ga kyawon fuskarta da ya fito ɗas cikin doguwar fuskarta, ga gashinta ya ƙara cika da tsawo saboda gyaran da yake samu sosai, Hajiya Mama kanta idan ta kalli Dije sai ta ji takaicin rashin sanin ciyon kan da Safwan ya nuna akan Dijen, saboda ganin yanda komai da ake so mace ta mallaka na siffar jikin Dije ALLAH ya wadata da abunta, sai dai kawai don ita ɗin tana baƙa amman kuma yanzu baƙin ba ƙaramin kyau ya

Please Login or Register in order to submit comment