Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yiwa iyayenta biyayya ko don dakon jiranta shekara da shekaru da Aminu ya yi saboda kawai yana son aureta"

Safwan ya yi saurin faɗin, "Eh nasan da zancen amman tunda ita bata sonshi ai sai a barta ta auri wanda take so"

Lawi yace "ka dai sowa ɗan uwanka abunda kake sowa kanka yafi abokina, hadisi ne ingantacce kuma ina da tabbacin kasan da shi, saboda haka Ni ina baka shawara ne a matsayina na Abokinka idan kaji ka taimaki kanka, idan kuma ka rufe ido ka ka kasa hango gaskiya to shikenan Ni dai na fita haƙƙinka"

Safwan ya yi wata dariyar gefen baki yace, "idan ka ga ban auri Zee ba to sai in itace da kanta ta ce ta fasa aurena, saboda na riga da na yi mata alƙawari akan zan auretan duk runtsi"

Kamal yace "ALLAH sarki Aminu WALLAHi na tausaya masa"

Safwan ya ɗaga kafaɗa yace, "ka ji da shi ni dai ba gudu ba ja da baya saboda nasan tana sona"

Haka suka yi ta fafatawa har aka gama walimar Safwan ya fito don ya yi sallama da su Zee, Kamal ya biyoshi saboda yana son ta ganshi don tasan yasan komi, aiko sai gata tsaye da Safwan ɗin suna sallama Fiddo ta riƙo masu kayan walimarsu da aka basu ta saka masu a mota, Zee tana yi wa Fiddo godiya suka yi ido biyu da Kamal, ta yi saurin riƙo ƙawarta tace

"Ruma kin ga Mituminki fa"

Ruma ta washe baki tace "laa! Kamal Rai kan ga rai?"

Kamar yana ɗan murmushin yace

"Rumasa'u kwana da yawa"

Tace "sai Alkhairi" ta ƙara da cewa "kai ma ka zo bikin kenan"

Yana dariya yace "Eh gamu munzo ta ya su Zee murna ALLAH ya sanya alkhairi"

Zee ta yi masa wani kallon tambaya sannan tace "Ameen" saboda mamakin ya aka yi yasan tsakaninta da Safwan ɗin, shi ko don ya tabbatar mata da yasan komi yace,.

"Ashe haka aka yi kenan Abokina ya yi wa wani Abokina ƙwace?"

Zee ta yi saurin kallon Safwan tace, "Abokin yaya Aminu ne fa"

Safwan ya ɗaga kafaɗa alamun ko a jikinshi yace, "ALLAH ya baiwa mai rabo sa'a idan Abokin nashi ne mijin ai sai ku daidaita kawai"

Zee ta zaro ido tare da ɓata fuska ta ce

"Haka ma zaka ce?"

Yace "eh to ai addu'a ce nayi ko?"

Ta turo baki tace, "to in fa Kuma addu'ar ta faɗa kanshi fa?"

Ya yi saurin faɗin "sai in ɗauki na annabawa ALLAH ya bani wata madadinki"

Kamal ya yi saurin faɗin, "ALLAH ai ya baka kuma sai dai in bazaka gode wa irin baiwar da ya yi maka ba"

Zee ta yi saurin kallonshi tace, "wa ya ba shi ɗin ?"

Kai tsaye kamal yace, " kyakkyawar Matarshi mana ko baki ganta ba"

Zee cikin firgici tace

"Tsaya Kamal don kana taya Aminu kishi kada ka ce zaka ɓata man rai, wace mata ka aura masa bayan ni da zai aura kwanan nan? A gaskiya bani son muguwar fata"

Ta ƙare maganar tana harararshi, Kamal ya yi yar dariya ya kalli Safwan da duk ya diririce alamun rashin gaskiya suka bayyana akan fuskarshi yace

"Kai Abokina to ka yi mata bayani da bakinka mana don naga kamar na shiga hurumin da ba nawa ba"

Safwan cike da jin haushinshi yace, "kai da ka yi mani waliccin auren ai sai ka yi mata bayani da bakinka don sai tafi saurin gamsuwa dai dai"

Zee ta washe baki ta ce "ƙyaleshi my cuddle bear nasan kishi ne yake taya Abokinshi bayan ni na riga da na yi masu nisa sai dai haƙuri"

Kamal ya yi mata wani kallo cike da jin haushin irin cin amanar da zata yi wa Abokinshi yace, "ita dai gaskiya idan ta tashi fita tafin hannu ya yi kaɗan da ya kareta, haka duk wanda ya ci amana to ya sani akwai lokacin da ranar sakamako zata ziyartoshi, ni kinga tafiyata fatana kawai ita Uwargidan ALLAH ya bata haƙurin sammakon da za'a yi mata"

Yana ƙare faɗar haka ya wuce abinshi, daga Safwan har ita Zee suka bishi da wani kallo mai ƙumshe da harara, ran Zee a jagule ta kalli Safwan ta ce"

"My hero Wai me yasa a ko'ina sai an samu yan adawa ne?, Ji don ALLAH yanda yake wani zaƙewa sai kace shine Aminun?"

Safwan ranshi a ɓace yace, "shareshi kawai hassada ce zo muje ki yi sallama da Hajiya mu je in raka ku gida tun kafin wannan magulmacin ya ɓata muna tsari"

Ya yi gaba Zee tare da janyo hannun ƙawarta amman sai Ruma ta ce da ita su je kawai ita zata jirasu, suna shigewa Ruma ta yi wurin Kamal zuciyarta cike da son jin gaskiyar abunda yake son sanar da Zee, ta nemi izinin ganinshi na ɗan lokaci suka keɓe gefe, Ruma ta zama serious bayan sun ƙare ɗan barkwancin da suka saba tace

"Kamal don ALLAH ka sanar da ni gaskiyar zance shin da gaske Man ɗin Zee yana da aure?"

Kamal ya yi yar gajeruwar dariya yace, "tunda kince ALLAH to ba wani kwana da zan tsaya yi maki, tabbas Safwan yana da Mata asali ma yanzu haka shekararshi biyu cikin ta uku da aurensu"

Ruma ta zaro ido waje tace, "Kamal kasan dai bamu irin wannan wasar da kai ko?, tsakaninka da ALLAH na roƙeka ka faɗa mani gaskiyar lamarin, saboda WALLAHi Zee ta mato sosai akan wannan guy ɗin idan har ta ji wannan magana nasan ba ƙaramin tashin hankali zata shiga ba"

Kamal ya karkace baki yana dariyar gefe idonshi suka kai ga Surayya da ke ta ɗaukar hotuna da Ƙawayenta ya yafitota da hannu, ta nufoshi tana dariya kasancewar tasanshi sosai saboda tare suka yi karatu da Safwan a garin, asali ma kamar gidan suke dukansu har da Lawi a lokacin da suka yi karatun jami'arsu.

Tana zuwa ta gayar da shi a mutunce bayan sun gaisa ya ce da ita, "Surayya ki yi mata bayanin gaskiya saboda ta ji da kunnuwanta, shin da gaske Safwan yana da aure ko kuwa?"

Surayya ta washe baki tace, "ALLAH sarki ƴar uwa da gaske kuwa Yayanmu yana da aure kuma yana bala'in son Matarshi, haka itama kuma tana sonshi sosai"

Diirim! dum! Shine abunda zuciyar Ruma ta yi saboda maganar ba ƙaramin bugun zuciyarta ta yi ba, nan take ta fara tausayin ƙawarta cikin canzawar yanayinta da ya koma kalar damuwa ta ce

"ALLAH sarki ko zaki iya nuna mani matar in ganta don ALLAH"

Surry tace, "bari in dubota don tun ɗazu ma ban ganta ba"

Surry ta yi cikin gidan zuciyarta cike da fatar ALLAH yasa ma auren ya wargaje kowa ma ya huta, sai dai duk bulayin neman Dijen da ta yi bata ganta ba, dole ta dawo da nufin sanar da ita cewa bata ganta ba, sai ga shi ma ta taradda su duka har da Safwan ɗin suna sallama da juna, saboda Ruma bata nuna komi ba nufinta sai sun je masaukinsu ta sanar wa da ƙawarta gaskiyar zancen.

Cikin tsoro Surry ta yi saurin komawa cikin gidan ta laɓe, har suka fita Gate ɗin gida Safwan ya bi su a baya sannan ta fito tana sauke ajiyar zuciya.

To sai dai abu kamar wasa har dare anata neman Dijen Baffah ammsn ba'a ganta ba, tun ana ɗaukar abun wasa har kowa hankalinshi ya fara tashi don kuwa anyi nemanta ko'ina gidan kaf ba'a ganta ba, Hajiya ta firgice sosai sai kiran Safwan take yi akan ta ji shin yana tare da Dijen ko kuwa, amman bai ɗauka ba saboda bai ma san ta kirashi ba don wayar a silen take, sai bayan ya gama firarshi da Zee ne Suka yi sallama yana kan hanya ya ga tarin miss calls na Hajiyar da su Surry da wasu ƴan uwansu duka, cikin tashin hankali ya dannawa Hajiyar kira sai ko ta yi caraf ta ɗauka, ba tare da ta jira jin abinda zai faɗa ba ta ce

"Ina khadija kuna tare da ita ne?"

Safwan a firgice yace "A'a WALLAHi Ni tun ɗazu rabon da na ganta"

Hajiyar ta yi saurin faɗin ka yi gaggawar nemota duk inda take, saboda an duba kaf gidan nan ba'a ganta ba, kuma jikina yana bani kai ne ka yi mata abunda ya janyo ta bar gidan, WALLAHi ka ji na rantse matuƙar baka nemo man ita ba to ko kada ka kuskura ka tako ƙafarka cikin gidan nan".

Kitt! Ta kashe wayar zuciyarshi cike da tashin hankali ya furta "Innalilahi wa'Inna ilairraji'un"

Cikin ruɗewa ya nufi tasha saboda cen zuciyarshi ta hasko masa zata nufa, saboda cewar da ta yi masa bata son karatun ita garinsu zata koma, sai dai kuma duk iya binciken da aka yi tashar babu sunan Khadija Umar a cikin jerin list ɗin mutanen da Motarsu ta tashi ranar a tashar, ya fito a gigice ya nufi wata ƙaramar tashar da ake shiga Mota nan ma ba wani alamun ta je cen, haka ya yi ta zagayen wuri wuri amman ko mai kama da ita bai gani ba, dole ya yi parking ya fito dafe da kanshi da ke yi masa mugun sara gashi dare ya fara yi da ke yi, saboda tsabar tashin hankalin da yake ciki sai waige waige yake yi a tunaninshi ko zai hangota, yana cikin hakan ne ya ji wayarshi ta yi Virbration cikin sauri ya ɗaukota tsammanin Hajiya ce zata sanar da shi cewa ya dawo an ganta, sai kawai ya ji Muryar Zee tana kuka tana faɗin

"Munafukin banza baƙin mayaudari ashe daman kai maƙaryaci ne ban sani ba? To asirinka ya tonu yau gaskiya ta fito labarin aurenka ya zo kunnuwana, ashe daman cen kana da Mata shine ka ɓoye man, to ka sani na tsaneka na tsaneka tsana mafi muni a rayuwata"

Ƙitttt ta kashe wayar, cikin wani sabon tashin hankalin da ya ƙara ziyartoshi ba shiri ya kai zaune daɓas ƙasa dafe da kai yace

"Kai wannan bala'in da me ya yi kama wayyo ALLAHna khadija ina zan ganki WALLAHi ina sonki don ALLAH ki dawo gareni plss!"



Ni ma dai tashin hankalin yasa alkalamina ya faɗi ba shiri🙀





Akafta🤪







D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*Kar kuji komai allurar ƙarfi aka yi man😂😂😂😂😂shiyasa na zauce hannuna ya HAUKACE yana ta suburbuɗo maku typing, ku sha sha'aninku kawai kafin Nima in sha nawa idan allurar ta sakeni yasin😝*



*Lamba ta 49*



Dijen Baffah kam tunda ta fito ɗakinshi ta nufi ɗakinsu cikin dubarar rufe fuskarta da ɗankwalin doguwar rigar da ke jikinta, ta ɗauko jakarta da kuɗin liƙinta suke ciki ta rataya, ta fito kamar wacce zata shiga wurin walimar ta fice gidan cikin sauri ta tare Napep ta haye sai babbar tasha, ta ce motar garinsu take nema aka ce da ita sai dai ta Gombe idan taje sai ta shiga motar Kano, daga cen sai ta shiga motar da zata kaita babban birnin garinsu, cikin rashin tsoro ta faɗa motar jikinta yana rawa ta tambayi kuɗin motar aka faɗa mata ta biya, da aka zo wajen rubuta suna da numbar waya kamar tasan za'a nemeta ta rubuta sunan ƙarya da numbobin banza, tunda ita ko wayar ma bata da bale ta yi number, zuwanta bai wuce minti goma ba motar ta cika suka tafi don ko da tara na dare ta buga tana garin Gombe, sai da aka je cen ne wani tsoro ya shigeta saboda batasan inda zata je ta kwana ba, ta rakuɓe gefen wata mota tana ta sharar ƙwallah saboda motar da taga za'a hau a lokacin kuma a ce wai tafiya za'a yi cikin daren, tana nan tsaye sai ga wani ɗan union ya zo yana faɗin

"Ina zaki je ne Kano ko Kaduna ko Bauchi Sokoto ko Zamfara?"

Dije ta yi saurin goge ƙwallarta tace "kano"

Yace "to zo mu je ga motocin Kano cen ina kayanki?"

Tace "babu"

Ya yi saurin waigowa yace, "bangane babu ba an sace kayan ne ko yaya?"

Ta ce "bani da kaya"

Ya ce ",to ai sai ki yi bayani yanda zan gane zo mu je kar motar ta tashi don ta kusa cika"

Dije ta bi bayanshi har inda motar take aka yi mata mazauni ta yi tsalle ta shige saboda ƙatuwar mota ce, ta sami wuri ta rakuɓe tana muzurai saboda tsoron yanda za'a bi hanyar zuwa wani gari cikin daren, zamanta ba wuya aka tada motar suka kama hanya, tafe take tana addu'ar ALLAH ya kaisu lafiya har bacci ya yi awon gaba da ita, ga masifar yunwar da ta addabeta don rabonta da abinci tun Yola.

Cikin ikon Allah Asubar farin suna isa Kano, bayan an saukesu mutane da yawa suka fara arwallah domin su yi SALLAH, itama ta bi sahun mutanen ta siyi ruwan ta yi arwallah ta yi SALLAH duk da masifar ciyon da kanta take ji, sannan ta tambayi wani ina ake shiga motar Katsina, ya yi mata jagora har zuwa inda motocin suke ta ƙara ce da shi "don ALLAH Malam ina zan samu abinci inci WALLAHi yunwa nike ji sosai" ya ce ta zo su je ya nuna mata wani shagon sayar da abinci, aiko ta bishi har zuwa wani ƙaramin shagon, yace da ita ta shiga ta zauna ta jirashi ya kawo mata abincin, ba wani tunani ta shige shagon ta zauna tana kallon mutanen da ke wulgawa ta Kofar shagon, ƴan mintuna a sai gashi ya dawo yana wata dariyar rashin gaskiya, yana zuwa ba wani jinkiri ya rufe shagon, cikin tsoro Dije ta ce

"Ina abincin ?"

Ya sosa kanshi yace

"Ki fara bani naki abincin sannan sai in je in kawo maki nawa kafin lokacin ma mai abincin ta kammala"

Dije cikin mamaki tace

"Ni ina naga abincin da zan baka?da ina da shi ai bazan tambayeka ba"

Ya yi sake yin wata dariyar shakiyanci yace

"Ke ko kike da abincin ci ki natsu kawai mu gama komi cikin lokaci kafin mutane su fara cika tashar"

Dije ta zaro ido cikin tsoro tace, "WALLAHi ko ka bani hanya in fita ko yanzun nan in yi maka sanadin barin duniya"

Cikin dariya ya nufota zai cafkota ta zille ya sake yunkurin kamota ta ɗaga jakarta ta buga masa ita iya ƙarfinta, aiko cike da jin haushi ya damƙota ta fasa wata uwar ƙara, shi ko ba kunya sai ƙoƙarin mannata da jikinshi yake yi, ganin da gaske keta mata haddi yake so ya yi ta fasa wata uwar kuwwa bakinta a sake sai ihu take yi, suna cikin kokawar ne aka banko Ƙofar shagon da ƙarfi ta buɗe ya yi saurin kallon ƙofar yana muzurai, Dije ta yi waje da gudu a firgice ko ɗankwali babu bale takalmi, jikinta sai rawa yake yi tana faɗin

"WALLAHi sai na kasheka azzalumi shegen banza ɗan'iska"

Mutane suka taru a kanta saboda ganin yanda take ta kuka tana tsine masa, sai tambayarta ake ba ɓata lokaci ta yi bayanin duk abunda ya haɗa su, aiko nan take mutane suka yi ta tsine masa suna aibatashi, wani ya shiga ya ɗauko mata jakarta da talkami da ɗankwalinta ya bata ta saka, sannan wasu matasa suka rufeshi da duka, cikin tausayinta wani bawan ALLAH ya je ya siyo mata tea da biredi ya kaita wani waje ta raɓa ta sha, sai dai tana gama sha amai ya biyo baya ba shiri ta fara rawar sanyi, mutumin ya siyo mata magani ta sha sannan ya sakata motar katsina sai da motar ta tashi sannan ya tafi yana jinjina halin wasu iyaye masu yiwa ƴaƴa riƙon sakainar kashi, su yi ta sakin ƴaƴansu duk inda suka ga dama.

A galabaice Dije ta isa babban birnin garinsu ta shiga motar da zata kaita ƙauyensu, har ƙofar gida Direban ya kaita saboda babu ko sisi a hannunta duk mota ta cenye kuɗin, asalima ko kuɗin zuwa katsinar ma sai da wata mata ta cika mata da nata basu kai ba, cikin tsananin galabaita ta faɗa gidansu yaran da suka biyo motar suka bita suna ihun ga Dije ga Dije amman ko ta kansu bata bi ba.

Tana shiga kai tsaye ɗakin Inna ta faɗa ta haye gado ta dunƙule cikin zane tana rawar sanyi, Inna daga bayi ta jiyo muryar yara suna ta kuwwar zuwan Dijen, jikinta yana rawa ta nufi ƙofar gidan inda suka ci karo da Hansai da itama ta fito daga sashenta aguje cikin murna da ɗokin ganin Dijen.

Amman basu ganta ba sai Direban da ya kawota kawai da ke ƙofar gidan yana bada saƙon a karɓo masa kuɗinshi tafiya zai yi, Inna ta tambayi yaran ina Dijen suka ce tana cikin gidan ta shige ɗaki, gaban Inna ya ƙire ya faɗi saboda jikinta ya bata cewa ba zuwan lafiya ne Dijen ta yo ba, cikin sauri ta kwance ƙullin da ke haɓar zanenta ta re da tambayar nawa ne kuɗin?

Direban ya faɗa ta bashi ta yi masa godiya cike da rawar jiki ta koma cikin gidan gabanta sai faɗuwa yake yi, sai dai tun kafin ta isa gadon ta jiyo sautin nishin Dijen, da ke ta rawar sanyi haƙoranta suna haɗuwa suna karkarwa, cikin sauri Inna ta zauna ta re da yaye rufar da ta yi ta taɓa wuyanta ta ji zafi zau!, Cikin faɗuwar gaba tace

"Dije lafiyarki ku wa?ina Hajiyar? Ya aka yi kika zo ke kaɗai bayan kuma nasan buki kuke yi?"

Dije cikin rawar baki hawaye suna zuba gefen idonta tace,. "Ni kaɗai nake ai"

Hansai ta shigo jiki a sanyaye ta zauna gefen Dijen tace, "Sannu Dije baki da lafiya ne?"

Dije ta ɗaya Kai Inna ta miƙe ta je ta ɗauko mata magunguna ta matsa mata sai da ta sha sannan ta koma ta dunƙule, Inna ta kalli Hansai tace

"A sami yaro a aikashi gidan Maigari ki ce ya zo gida ana nemanshi"

Hansai ta fita Inna ta dawo ta sassafta murya tace, "Dije faɗa man gaskiya kafin malam ya zo shin Mijinki rabuwa ya yi dake ne ko yaya?"

Dije ta yi saurin girgiza kai tace,

"A'ah Inna ba ma wanda yasan na tafo"

Inna ta sake jin wani sabon fargaba, ta tada ita zaune tace "Kallanni da kyau Dije bana son Baffahnki ya shigo baki sanar da Ni gaskiyar abunda yake faruwa ba"

Dije ta ja jikinta ta jingina da bango tace,

"Ba rabuwa ya yi dani ba Inna amman WALLAHi ni na gaji da aurenshi tunda yake son ya lalace mani rayuwa"

Inna ta zaro ido waje tace "bangane ya lalace maki rayuwa ba? ki yi man bayani dalla dalla yanda zan gane"

Dije ta share hawayenta tace

"Inna jikina yake taɓawa WALLAHi har kayana ya tuɓe yanata yi man wani iskanci a jiki........"

Ba shiri Inna ta kai mata wani bahagon mari a baki cikin fushi ta nunata da hannu tace, "au Wai daman akan wannan dalilin ne kika gudo tun daga Yola har zuwa garin nan? To buɗe kunnuwanki da kyau kiji WALLAHI matuƙar kika ce bazaki iya yiwa Mijinki biyayya akan duk abunda ya zo maki da shi ba, to Ni Ko ko kaɗan ba zamu shirya da ke ba"

Dije dafe da gefen da ta sha marin cike da mamaki tace, "Inna WALLAHi har ƙirjina yake taɓawa yana ƙoƙarin cire mani ɗan kamfai, kuma ma har dukana yake yi fa"

Inna ta wurga mata wata ƙatuwar harara tace, "abunda ya fi duka ma idan ya yi maki kin cancanta ai, to bari kiji duk abunda kika ga ya yi maki ko yana ƙoƙarin yi dake to tuni Baffahnki yayi hakan dani, kuma gani daram har yanzu kin ganni ba abunda ya sameni, don haka tun wuri WALLAHi ki shiga taitayinki miye amfanin karatun da kike yi?, Saboda haka tun kafin ki janyo wa kanki abun gori cikin mutane, sannan ki tsallake Hajiya ki nufo gidan nan ke kaɗai ko tsoron abunda zai sameki a hanyar baki ji ba, yanzu da wane ido kike so mu kalleta ace kin tsallaketa akan wannan guntuwar matsala kin nufo gida?. "

Dije ta zumɓuro Baki tace, "kedai Inna don baki san me yake yi mani bane shiyasa"

Inna ta buge mata baki tace "ina ko zan sani tunda ban taɓa yin auren ba, to bari kiji in baki sani ba ki sani shekarun baya akan wannan dalilin ne aka ɗaure Jummala, ke ma idan kina son ayi maki haka to WALLAHi ko a cikin ɗakin nan zamu iya ɗaure masa ke, ya yi duk abunda yake so da ke tunda ba zunubi ne zai aikata ba"

Dije ta zaro ido tace

"Inna yanzu daman akan haka ne aka ɗaure Jummalar? Cabɗi to WALLAHi gaskiya kam ba'a kyautawa rayuwarta ba, to ni dai WALLAHI bazan taɓa bari wani ƙaton banza ya yi iskanci da Ni ba ina kallo in ƙyaleshi ba"

Inna ta sake Kai mata wani marin wanda ya yi dai dai da shigowar Baffah tana faɗin

"Mu zaki tonawa asiri Dije?"

"Wane asiri zata tona bayan yanzun nan muka gama waya da Uwar mijinta an sanar da ita Dijen tana nan saboda ta ɗaga hankalinta sosai akan rashin ganinta, don haka ki bar yarinya ta huta da wahalar motar da ta kwaso sannan ki fara dukan nata tunda ke hannunki bai girma da bugunta"

Ya ƙaraso wajen Dijen ya shafo kanta yace, "Dijengalata me yasa kika baro cen ba tare da sanin Mijinki ba"

Dije ta fashe da wani sabon kuka, Inna ta ce da Baffahn ya zo ya ji suka fita tare har zuwa ɗakinshi, cikin ɓacin rai ta sanar da shi dalilin da ya dawo da Dijen, Baffah ya yi shiru yana nazari saboda shi tsammaninshi ma tuni an wuce wannan babin, ashe yanzu ake matsalar ya sauke ƙatuwar ajiyar zuciya yace

"A gaskiya yaron nan ya yi haƙuri da yawa WALLAHi, amman ita kuma a hankali zaki fahimtar da ita ba da duka ko faɗa ba, saboda yanzu haka mijinta yana kan hanyar zuwa garin nan, kuma da ya zo nike son ta bishi su koma don banga amfanin zaman da zata yi muna anan ba"

Inna ta sauke ajiyar zuciya tace, "ALLAH ya kawoshi lafiya amman kasan dai ko kaɗan bata kyautawa Hajiya ba ko?, Ace duk dawainiyar da take yi da ita amman ta tsallaketa ta zo wurinmu akan wannan guntuwar matsala"

Baffah yace

"Haƙuri za'a yi kuma yanzu tunda dai mai afkuwa ta riga da ta afku, sai a kira ita Hajiyar a bata haƙuri shi kuma idan yazo mu bashi haƙuri ya tafi da matarshi"

Inna sauke wata ajiyar zuciya tace "ALLAH ya kawoshi lafiya sai dai ni naso ace a barta ta yi kwana biyu anan, saboda in fahimtar da ita abubuwan da suka shige mata duhu"

Baffah ya ce "aganinki ba za'a ga munyi ƙaranta ba?"

Inna tace "izininshi zamu nema ai saboda duk abunda zai sa ta kamo hanya tun daga cen har nan to abun ba ƙarami bane, saboda haka don ALLAH idan ya zo ka nuna masa kana son a bar Dijen nan ta ɗan kwana biyu"

Baffah cike da mamakinta yace, "ke fa kika ce da ni ga dalilin da yasa ta gudo to kuma yanzu sai ya zo tafiya da ita kuma muce a barta ta yi kwana biyu?, Ni fa bana son abunda zai sa mutanen nan su ga rashin kyautawarmu, ko dai akwai wani abu bayan wannan ne?"

Cikin damuwa Inna tace, "babu wani abu amman kasani ko yanzu tsugunne bata ƙare ba, matuƙar ta koma ba tare da an fahimtar da ita minene auren ba da abunda ya ƙumsa, saboda ina jin tsoron tace zata sake biyo doguwar hanyar nan ita kaɗai ko don gudun wani abu mara kyau ya sameta"

Baffah ya yi shiru yana nazari sannan yace, "to kuma Hasiya kin yi nazari anan, to ALLAH yasa shi ma idan ya zo ya amince ya bar muna ita ɗin"

Inna tace "ai nuna masa ɓacin ranka zaka yi akan sakacin da ya yi har ta biyo wannan uwar hanyar ita kaɗai"

Baffah ya yi saurin faɗin, "kar fa ki janyo inji kunya wajen surukina?"

Inna tace "ba wani jin kunya hakan da zaka yi shine zai ƙwatowa Dije ƴancinta, saboda gobe ya ji tsoron ƙara yin sakaci da ita har ta biyo hanya ba tare da sananinshi ba"



Tofa Inna uhum da kinsan halin da mijin Dijen yake ciki da ba ki ce haka ba😔





Akafta😉





D/AUTA Ce✍🏻

*💣 DIJE K'ARANGIYA💣*



*NA HADIZA D/AUTA*




*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*



*DOMIN JIN DAƊINKU MASOYANA ku natsu tsaf ku ci gaba da kwasar ganima😂😝*



*Lamba ta 50*



Safwan kam firgicin da yake ciki ne yasa ya baje

Please Login or Register in order to submit comment