Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wuce ita, koh da tsabar da yayiwa family ɗinsa bai kai wanda yake yiwa DEENAH ba.



Ta shigo rayuwar sa ta ƙarfi da yaji dan kawai ta ruguza masa ita, yanzu dole yayi wasting rabin shekara anan cikin ƙunci da baƙin ciki, bashida komi, bashida kowa, asarar wata shida a cikin rayuwar sa ta kama shi wanda yakamata ace da shi ne zai fara gina kanshi, tunda har Jafar yace dashi zai iya making kuɗi a drawing ɗin da yayi musu.............



******************



........"Nikam dan girman Allah ba zaki daina kukan nan bane, wallahi zan naɗa miki na jaki sai ki dinga yin kukan kawai da dalili, haba tsawon wata ɗaya ace mutum bashida aiki kullum sai kuka, ai koh mutuwar ubanki bakiyi kuka haka nan ba. toh wallahi ki fita daga ido na na rufe na gayamiki" Faɗin Umma cikin tsananin 6acin rai tare da jin haushin DEENAH.


Ta6e baki Rabi'atu dake zaune tayi tana habaice-habaicen ta "Ya mutum ba zaiyi kuka ba, an maida sa fanko, dama gado aka ci, sabida an saba da yawa-yawacen bin maza tun iyaye da kakanni, Allah sarki."


Sosai Umma taji zafin maganar Rabi'atu sai dai bata kula ta ba kasancewar bata iya rigima ba kwata-kwata, haka ma tasan ita ce ta kwashe mata abubuwa a ɗaki sai dai koh a fuska bata nuna hakan ba.



Jafar ne ya dawo daga aiken da Umma tayi masa ya miƙa mata yayi ciki abin shi ba tare da ya kalli inda DEENAH take ba.


Tashi tayi tabi bayan shi tana kuka ta kira sunan shi.

"Yaya."


"Nace ki daina yi min magana muddin baki shirya faɗar gaskiya ba."


"Yaya dan Allah kayi haƙuri."


"Ni kika yi wa laifi ne da zaki bani haƙuri, ai ba ni kika wa laifi ba Balarabe kika yiwa laifi." (Kasancewar basu san sunan ZEEYAD ba yasa suke kiran shi da Balarabe).


"Yaya wallahi zan faɗa, zan faɗi dukkanin abinda ya faru amma ina tsoron kada Kawu ya kashe ka kai da Umma."


Da sauri ya sauƙo zuwa inda take ya riƙo hannun ta, cikin kwantar da murya yace "DEENAH Kawu ne yasa kiyi hakan koh?."



Da sauri ta jinjina masa kai, hakan yasa shi fara kiran Ummar su.


"Menene dan Allah, banason damuwa fah."


Fita yayi yaje ya sameta yana kamo hannun ta yace "Umma kizo kiji."


Ajiye tray ɗin hannun ta tayi tana bin bayan shi zuwa falon nasu.


Baki Rabi'atu ta ta6e tana faɗin "Mtssww wai su gasu masu soyayyar uwa da ɗa."


Zama tayi kan kujera nan yace "Umma ai dama na faɗa miki Balarabe ba shida laifi kuma ba zai ta6a aikata abinda ake zargin sa dashi ba."


"Akan wannan maganar ka kira ni, idan ba shida laifi maiyasa tun farko ta buɗi baki tace shine, kaga fah Jafar ka fita idona na rufe."


"Umma gata nan ki tambaye ta da kanki, ita ta faɗa min."


Kallon DEENAH dake matsar kwalla tayi tace "Zo nan."


Zuwa tayi kusada Umma kafin Umma tace "Faɗamin gaskiya tsakanin ki da Allah, kinga dai Allah yana ganin ki kuma yana hukunta masu ƙarya koh?."



Kai ta jinjina mata, nan ta cigaba da faɗin "Kuma kinga Allah bayason masu ƙarya koh?."


Nan ma jinjina mata kai tayi sannan tace "Kuma duk wanda ya zalunci wani koh da kuwa wanda aka zalunta ɗin ya kasance mai aikata sa6o ne, indai ya kai kukan sa ga Allah yana bi masa haƙƙin sa koh bajima koh ba daɗe koh?."


"Kai ta jinjina nan Umma tace "Toh ki faɗamin tsakanin ki da Allah, wane ne yayi miki haka indai ba balarabe bane?."


Cikin kuka tace "Wallahi Umma zan faɗa miki banaso Allah ya kama ni da laifi."



"Toh faɗamin ina jin ki."


"Umma wallahi Kawu ne..."


"Kawu?" ta faɗa cikin katse ta.


Kai ta jinjina mata kafin ta kwashe dukkanin abinda ya faru ta faɗawa Umma tare da ɗaura da faɗin "Umma wallahi Balarabe bai ta6a yi min komai ba, da naje wurin sa ina kuka ne shine Kawu ya ɗaura masa sharri sannan yace min zai kashe ki keda Yaya indai har ban ce balarabe bane, Umma dan Allah kije ki ciro shi kuma ki bashi haƙuri wallahi ba zan sake ba, ga kuma Kawu zai kashe ku."



Umma tsabar baƙin ciki da taƙaici batasan sadda ta hau jibgar DEENAH da duka ba.


"Dan Ubanki kawun mala'ika ne, da har zakiji tsoron abinda ya faɗamiki ki ɗaurawa bawan Allah sharri baiji ba bai gani ba, haka na koya miki ɗaurawa mutane sharri,koh haka aka koya miki a makaranta?, wawuyar banza da wofi marar wayo" ta faɗa tana tunkuɗa ta daga jikin ta ta faɗi.



Kuka Umma ta fashe dashi, dan kuwa DEENAH ta gama zubar da ita, yanzu da wane ido zata kalli Balarabe ta bashi haƙurin abinda ya faru,yaro yana zaman zaman shi DEENAH ta ja masa masifa da bala'i, ashe yana da gaskiya da yayi ta cewa ba shi bane, ashe ƴar ta ce mai ƙaryar.



A fusace ta tashi ta fice tana kwala kiran Kawu "Sale!, Sale!!."



Miƙewa tsaye Rabi'atu tayi cike da tsiwa tace "Toh yana bacci, lafiya kike kwala..."


Bata ƙarasa ba taji wani irin mari a fuskar ta,kafin Umma ta tunkuɗa ta gefe ta shige, muciyar da ta gani a bakin ƙofa ta ɗauka tare da shigewa cikin ɗakin.



Naƙe-naƙe ta sami Kawu sai baza bacci yana munshari bakin nan a wage.


Bata yi wata-wata ba ta zuba masa muciyar a baki take ya rufe ta yana tashi a zabure, kafin yayi wani abin kuma tuni Umma ta hau moɗa masa muciya tana faɗin "Wallahi kayi asara.mafi muni a rayuwar ka, insha Allah sai kayi nadamar abinda kayi kafin ka mutu, sai ka sha wahalar rayuwa ka rasa mai taimakon ka kafin ka mutu, abin naka bai tsaya a iya cin dukiyar marayu da muzguna musu ba, har ya kai ga kayi yunƙurin yiwa ƴar cikin ka fyaɗe, fyaɗe fah wallahi kaji kunƴa kuma insha Allahu sai kaga sakayya akan ƴaƴan ka ba kaima ka haifa ba?, kamar yadda kake lalata rayuwar ƴaƴan mutane kaima sai an samu mai lalata naka ƴaƴan, mazinacin banza da wofi, ƙaramin mutum asararre kawai" har suka fito waje bata daina bugun sa ba, Kawu kuwa sai ihu yake zubawa a taimake sa Fatima zata kashe shi, sai zagaye cikin gidan suke kasancewar Jafar ya rufe ƙofar fita da makulli babu damar Kawu ya fita sannan babu wanda zai kawo masa taimako.


Sosai Jafar ke farin cikin yadda yau Ummar su ke jibgan Kawu dariya kuwa yayi ta harda riƙe ciki ganin yadda Kawu ke ihu yana bawa Ummar su haƙuri kamar ƙaramin yaro.


Rabi'atu kuwa miƙit tayi idanun ta zuru-zuru tana ganin yadda Umma ke jibgan mijin ta Sale.


Sai da Umma tayi wa Kawu lilis kafin ta kyale sa nan ta cewa "Jafar ɗauko min mayafi na kuzo muj."


Da sauri ya shige ɗaki farin ciki kamar yayi yaya ya ɗauko mata mayafin ta nan ta yafa ta rufe side ɗin ta ta kaɗa kan Ƴaƴan ta suka fice.



Mutane dayawa ne a bakin ƙofar gidan babu wanda ta kula ta ratsa ta cikin su suka wuce.


Abin hawa suka tara inda ya kai su har Police HEADQUATER, luckily wannan wanda ya kar6i case ɗin shine a duty yau dan haka iso akayi musu zuwa ofishin sa.



"Dan Allah yallabai yaron da ka kama nakeso ka sake sa, bashida laifin komai bai aikata komai ba, dan Allah a sake sa haka nan."



Gyara zama yayi ya kalle ta yace "Bangane a sake sa ba, case ɗinnan ya riga da yayi nisa kuma har an yanke masa hukunci, mai kuma kuke buƙatar proving anan?."


Jawo DEENAH tayi tace "Ƴata ce ta amsa cewa yayi laifi toh ba gaskiya ta faɗa ba, ba kowa bane mai laifin face Kawun su."


Kallon DEENAH yayi yace "Kinason kice min wanda aka kama da laifi ,he is not the one at fault kenan?."


"Kwarai kuwa abinda nake nufi Kenan."


"Amma maiyasa, sai yanzu ne zaku zo da wannan maganar?."


"Gata nan ita da kanta, kayi mata dukkanin tambayar da zakayi mata, ita kuma zata faɗa maka gaskiyar abinda ya faru."



Kallon DEENAH yayi yace mata "Zo."


Zuwa tayi nan yace da ita "Ki saki jikin ki, ki faɗamin abinda ya faru a wannan ranar."



Goge hawayen fuskar ta tayi kafin ta shiga koro masa bayanan dukkanin abinda ya faru.


Sosai ɗan sanda yayi mamaki, nan yace "Babu shakka that Man sounds guilty."



"Dan Allah ina shi yaron yake yanzu?, a sako shi dole ne mu nemi yafiyar sa."


"Sergeant" ya kwala masa kira.


Shigowa wanda aka kira da sergeant yayi tare da sara masa cikin girmamawa nan yace "Kuje ku taho da wannan Balaraben nan."


"Yes sir" ya faɗa cikin sarawa yana ficewa.



Sosai zuciyar DEENAH ke tsinkewa haka kurum ta rasa dalilin maiyasa.



Zuwa akayi aka taho da ZEEYAD, sosai yayi baƙi ya rame, nan duk suka maida duban sa zuwa garesa.



Sosai fuskar sa ta sake ɗaurewa lokacin da ya haɗa idanu da DEENAH.


Umma ce ta durƙusa har ƙasa ta shiga baiwa ZEEYAD haƙurin sharrin da akayi masa.


Koh kaɗan bai ga laifin Umma ba sabida ai ita ɗin Uwa ce, kuma duk Uwar da taji an yiwa ƴar ta fyaɗe dole ne ta fice cikin hayyacin ta idanun ta su rufe musamman idan ya kasance ta tarbiyan tar da ƴaƴan ta.



"Stop begging me please, banga laifin ki ba, i just want you to know that ni bani bane nayi wa ƴarki fyaɗe."


"Na san da hakan, wannan ne dalilin da yasa nazo da kaina dan na baka haƙuri, dan Allah kayi haƙuri haƙiƙa an zalunce ka dukda nasan ba lallai bane ka iya yafe mana, Kawun ta shi ke da laifi" ta faɗa cikin harɗe hannayen ta.



Sunkuyar da kai ZEEYAD yayi dan baya son tsayuwar sa a nan he can't stand this DEENAH girl, sosai yakejin ta fita a kansa, sam bayason ta baya son ganin ta.



"It's alright" kawai ya faɗa kansa a ƙasa.


"Nagode, Nagode Allah yayi maka albarka, ban ta6a zaton zaka yafe mu cikin ƙanƙanin lokaci ba."


"Take him away" cewar Ogan nan aka fita dashi, kafin ta juyo zuwa gareshi tace "Dan Allah ku sake shi, ba shi bane mai laifin, mai laifin na chan gida mun baro shi, shi zaku kama ba wannan bawan Allahn ba."






"Zamu sake shi tunda har aka gano yanzu bashida wani laifi, sai dai ba zamuyi hakan ba har sai mun sami saƙo daga kotu an wanke shi daga laifin da ya aikata."



Kai ta jinjina tace "Wannan zai zo da sauƙi tunda har an gano wanda yayi laifin, buri na shine ku kama sa sannan kuma ku hukunta shi."


"Insha Allah, muje."



Nan duk suka miƙe kafin su ɗau motar Police guda ɗaya da polisawa guda biyu suka fice, basu tsaya a koh ina ba sai bakin ƙofar gidan su.


Ratsa ɗan ɗaiɗaikun mutanen da suka rage sukayi suka shiga cikin gidan, nan fah suka tadda Kawu kan tabarma Rabi'atu nayi masa fifita.


Ganin ƴan Sanda yasa hankalin sa matuƙar tashi ba tare da wata wata ba aka garƙame sa aka tafi dashi, ba tare da damuwa da ciwon dake jikin sa ba.



Bayan wata ɗaya akayi zaman Kotu, inda dakyar Kawu ya amsa laifin shi, bayan an kuma kama sa da laifin tauye haƙƙin Marayu dama kuma case ɗin laifin fyaɗe daga ƙauye.


Haƙƙin marayu aka kwatar musu, wanda kuɗi ne dayawa a hakan ma ba kaɗan Kawu ya cinƴe ba, sannan kuma aka wanke ZEEYAD daga laifin da ake tuhumar sa na aikata fyaɗe.



Koh kaɗan baiji farin cikin hakan ba, dan kuwa baya tunanin zai iya yafewa DEENAH, ta sa shi yayi spending watanni biyu a gidan yari, Uwa Uba ya rasa abu mafi muhimmanci a gareshi duk domin ita.



Sosai Umma ta cika da farin cikin wanke ZEEYAD da akayi, ga kuma farin cikin dukiyar marayu da aka kwato musu abin su, Kawu kuma yayi gidan yari har ƙarshen rayuwar shi.



Gida suka wuco harda ZEEYAD ba dan yaso ba, dan kuwa sosai yake so yayi musu nisa, bama su kaɗai ba da kowa ma yakeson yin nisa.



A bakin ƙofar gidan suka tsaya sabida ZEEYAD yaƙi ya shiga yace shi tafiyar sa zaiyi.



"Dan Allah kar muyi haka dakai mana, kayi min halacci wurin yafe mana laifin da mukayi maka...."


"Na yafe muku, sai dai banda ita" ya faɗa yana kallon DEENAH da ita ma ke kallon sa.



Sosai zuciyar Umma ya buga jin abinda yace "mai....mai kake nufi?."


"Ta ruguza min rayuwa, i spend two months in jail all because of her, tasan ba ni na aikata laifin ba amma tayi shiru bata ce komai ba, and just because of her nayi losing abu mafi muhimmanci da soyuwa a wuri na, how do you expect me to forgive her then?."



Shiru Umma tayi bata iya cewa komai ba, dan kuwa ta hango tsantsar 6acin rai dama kuma gaskiyar abinda yake faɗa a idanun sa na cewa ba zai yafewa DEENAH ba.


"She is just a little girl..."


"No she is not, she knows exactly what she is doing, am sorry to say this to you as a mother, but nothing would make me forgive her for ruining my whole life, am living and don't try to Stop me please, coz i need to move on with my life, ta koya min hankali sannan ta koyamin kada na sake yarda da kowa komin irin kirkin da suke nunawa maka kuwa, i just hate and despised her."



Sosai Umma taji zafi dama kuma rashin jindaɗin maganganun sa akan DEENAH nan tace "Alright then, i won't stop you from leaving but let me make one thing clear to you, my daughter has a clean heart and she is pious, dan ta aikata kuskure ba shi ke nufin ba zaka yafe mata ba, koh da baka yafe mata ba Allah ba zai kama ta da laifi ba dan kuwa ita ɗin tana cikin ƙaddarar ka ne, nayi niyyar taimakon ka ne amma sai dai ba zan iya jurar irin kalmomin da kake jifar ƴata dashi ba, you should get going then, i won't stop you."



Da kallo ya bisu dukkanin su kafin kuma ya juya ya fara tafiya.


"Umma ina zai je?" faɗin DEENAH.


"Bar shi ya tafi shi ya za6i hakan."


Da gudu ta mara masa baya tana riƙo rigar sa ta baya tace "Ina zaka je?."



Runtse idanu yayi kafin kuma ya cire hannun ta daga riƙon da tayi masa.


Sake ruƙo shi tayi tace "Dan Allah kayi haƙuri."


"Stay away from me, you're nothing but a problem to me, i just hate seeing your face for good" ya faɗa yana tunkuɗe ta ta faɗi ya cigaba da tafiyar sa ba tare da ya waiwaye ta ba jin Kukan da take.


Da sauri ta koma wurin Ummar ta tace "Umma dan Allah kice ya tsaya, Umma ki basa haƙuri kada ya tafi, dan Allah Umma."



"Shi ya za6i ya tafi DEENAH, ba zan iya hana sa ba, kiyi haƙuri."



"Nidai dan Allah Umma kice kada ya tafi, shikenan ba zan sake ganin sa har na kai masa abinci ba kenan, Umma kice ya tsaya" ta faɗa tana kallon ZEEYAD ɗin da yayi nisa.


Riƙo ta Umma tayi ta shigar cikin gidan kafin Jafar da jikin sa yayi mugun sanƴi shima yana kallon ZEEYAD ɗin ya shige cikin gidan.



Bayan sati biyu Umma ta nemi transfer ɗin aikin ta zuwa Sokoto kasancewar chan zasu koma da zama yanzu, sabida anan Babbar Yayar su take aure, shiyasa ta za6i ta koma chan ɗin da zama kusada ƴar uwarta.



Shirye-shiryen tafiya kawai suke inda DEENAH kuwa sam batason tafiyar, kullum sai taje inda ZEEYAD yake zama bata ganin sa, kenan hakan na nufin yayi mata nisa.


Buɗe tafin hannun ta tayi tana kallon sarƙar da batasan koh na mecece ba, iya tsawon kwanakin nan babu wanda yasan tana tare da sarƙar nan.



"DEENAH?" ta jiyo an kira sunan ta, saurin 6oye sarƙar tayi tana amsa kiran da Umma tayi mata ta fito.


"Zo kici abinci mu wuce haka nan."


"Umma na ƙoshi" tana faɗin haka tayi wucewar ta ɗaki tana ciro sarƙar da ta 6oye ɗin tasa a jikin ta.



Da kallo kawai Umma ta bita dan kuwa har yanzu bata bar tunanin ZEEYAD ba, inbanda ma yarinta irin ta DEENAH.



Cikin ƙanƙanin lokaci duk suka gama shiryawa, kafin su fito bayan Jafar ya kira musu adaidaita sahu har zuwa ƙofar gida.



Kayayyakin su suka sanƴa kafin duk su shiga, inda daga baya kuma za'a zo a kwashe manƴan kayan ɗakin.



A tashar mota ya sauƙe su suna zuwa kuwa motar Sokoto ta cika ba tare da 6ata lokaci ba kuma motar ta tashi suka kama hanƴa.........TOH SU DEENAH SAI DAI MUCE ALLAH YA KIYAYE.



*10 YEARS AFTER.............*




*********************




*TOH, Ance idan ansan farkon rikici ba'a san Ƙarshen ta ba, bayan shekaru goma shin yaya kuma rayuwar wadannan mutane zata kasance dai Oho, waya sani koh zasu sake haɗuwa ko kuma dai shikenan rabuwar kenan har abada?, toh dai Allah ne masanin wannan mu haɗu a page na gaba dan ganin yadda rayuwar kowanne daga cikin su ke tafiya*




*MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*






*013...*







*10 YEARS LATER*






...............Tafiya take cikin sauri tana haɗa wa da ɗan gudu ta shige cikin ƙatuwar mall ɗin.



Wani abu ta danna, nan take Ƙofar mall ɗin ya buɗu ta shiga.



Da kallo ta fara bin mall ɗin tana hange-hangen ta inda zata nemo sa yayin da hannun ta ke ɗauke da roses flower a cikin ledar sa.



Juye-juye ta fara tana kuma bin saman stairs ɗin dake cike da dandazon mutane da kallo.



Ƙaton mall ne sosai domin kuwa har lifter mai stairs akwai a cikin mall ɗinnan, tsayawa faɗin haɗuwa da tsaruwar mall ɗinnan 6ata lokaci ne, sai wanda ya gani kawai.



Ja ta fara yi da baya tana shirin juyawa ne taji ta bugu da mutum take tayi baya-baya ta faɗi yayin da flowers ɗin hannun ta suka tarwatse.



Baki ta saki tare da runtse idanu flowers ɗin na zubo wa kanta.



"Sorry" taji an faɗa cikin wata iriyar daddaɗar husky voice kafin kuma ya miƙo mata hannu da niyyar taimaka mata ta tashi.



Da kallo tabi farin hannun nasa ba tare da ta miƙa masa nata hannun ba.



Yunƙurawa tayi ta tashi tsaye kafin ta fara tattara flowers ɗinta da suka zube ba tare da tabi ta kanshi.



Kallo ɗaya ya sake yi mata yana damƙe hannun sa kafin kuma ya juya ya fara tafiya.



Ɗan ta6e baki tayi tana cigaba da kwashe flowers ɗinta ta miƙe tsaye.



Waige-waige ta fara bata gansa ba hakan yasa ta komawa wurin Reception ta sami wuri ta zauna.



"Hey" taji an faɗa ana ɗago mata hannu, wani kyakkyawan saurayi ne fari tass dashi.



Murmushi tayi tana miƙewa daga zaunen da takeyi ta nufe shi tare da rungume shi, murmushin shima yayi yana ɗago ta tare da ɗan jan kumatun ta yace "Sorry, i kept you waiting."



Turo baki tayi cikin sigar shagwa6a kafin ta saki fuska tace "Happy birthday" tana miƙa masa flower ɗin hannun ta.


"Oh thank you" ya faɗa cikin murmushi sosai yana amsa, nan yace "Kin biyo ni nan just to give me this?."



Kai ta jinjina masa tace "Yeah, yakamata muje mu sha ice-cream tunda yanzu kam nazo, sabida kullum sai dai kace aiki yana yi maka yawa, dakyar ma mutum zai sami ganin ka wataran balle kuma muyi spending time tare."



Kallon flowers ɗin yayi yace "Thanks for the flowers, muje mu sha ice-cream" ya faɗa yana ɗaura hannaye a kafaɗun ta kamar wata ƙawar sa suka fito.



Fitowa sukayi daga wurin kafin kuma su nufi wani building ɗin kuma daban, ice-cream suka saya kafin su fito kowannen su na sha suna tafe suna hira cike da Nishaɗi.



Baki take shirin kai ice-cream ɗin nan ta sake ji tayi banging mutum ice-cream nata ya karye ya faɗi ƙasa.



Da Kallo tabi bayan sa ganin bai koh tsaya bata haƙuri ba, sai ma waya da yakeyi tare da ɗago mata yatsu biyu alamun sorry kuma bai juyo ba.


Juyawa tayi ta kalli saurayin nan dake gefen ta tana 6ata fuska nan ya ɗaga mata kafaɗa yace "Muje mu sake yankan wani."



Murmushi tayi kafin kuma suje ya sake saya mata wani, cike da farin ciki suka gama sha, sannan sunyi spending time da juna sosai kafin kuma ta tafi..............




*************************



.........Wasu baƙaƙen Mercedes BMW ne wanda aƙalla zasu kai ashirin biye da juna, suna sharara uban gudu akan kwaltar kai kace na gidan uwar su ne koh su kaɗai ne motoci akan hanƴar.



Kai tsaye wata ƙatuwar gini wanda da alamu company ne da aka rubuta A&A ENTERPRISES, suka shiga inda kowanne ya samu gurbin parking.



Da sauri aka buɗo motar aka fito bodyguards ne guda biyu cikin baƙaƙen suits fuskar nan tasu murtuƙe babu alamun fara'a, ga wani uban black shade da suka manna wa idanun su suka nufi ɗaya daga cikin motocin tare da buɗe ta.



Almost 2mins wanda aka buɗewa motar ya ɗauka kafin kuma ya zuro farar ƙafar sa da tasha black shoe companyn GUCCI sai sheƙi takeyi yana sanƴe cikin black suit shima kamar bodyguards ɗinsa, fuskar nan murtuƙe babu alamun fara'a, jacket ɗin kan rigar sa ya gyara yayi gaba, nan duk suka mara masa baya yayin da biyu ke gaba dashi ta gefe da gefe, kowannen su na tafiya kamar zai tashi sama tsabar sauri kasancewar abinda suka ga Uban gidan nasu nayi kenan.



Kyakkyawa ne sosai, dogo mai murɗaɗɗen jiki wanda daga gani kasan baya rabuwa da Exercise kullum, dukda fuskar sa babu fara'a hakan bai 6oye irin tsantsar kyawun da Allah yayi masa ba.



Buɗe masa glass door ɗin akayi nan suka kutsa kai ciki kafin kuma kai tsaye su nufi wurin lifter inda biyu ne kawai biye dashi sauran kuma suka tsattsaya kowanne na patrol da bindigar sa a hannu.



Kai tsaye hawa na goma sha biyu kamar yadda suka danna numbern jikin lifter ɗin ya kai su.



Suna isa kuwa ya buɗe suka fito, inda kai tsaye kuma suka nufi ƙofar dake chan ƙarshen haɗaɗɗen corridor ɗin wanda tsaya faɗar tsaruwa da haɗuwar sa 6ata lokaci ne, buɗe masa ƙofa akayi nan ya shige inda kuma ƙatuwar hall ɗin mai ɗauke da wani dogon table da kuma seats ɗin da aƙalla zasu kai talatin kowanne da mutane akai, shigowar sa yasa hall ɗin ɗaukar tsit kafin kuma ya tako zuwa ga babban seat ɗin da yafi kowanne kyau da girma a cikin su inda kuma shine yake a center suna bin sa da kallo har ya zauna yana ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, kafin bodyguards ɗinsa su tsaya ta kansa ɗaya a gefen hagu ɗaya a na dama.



"You're late ZEEDAN" Cewar ɗaya daga cikin mutanen dake zaune akan table ɗin.



Kallon sa wanda aka kira da ZEEDAN yayi kafin kuma ya gyara zaman sa yana fuskantar su kafin kuma ya hau ticking ɗin yatsun sa akan table ɗin, cikin zazzaƙar husky muryar sa yace "Am born to be a king, No one orders me and no one dares to command me except GOD, i can arrive at anytime i wanttt" ya faɗa cikin jan kalmar ƙarshen.



Shiru mutumin yayi kafin kuma wani ya kar6i maganar da cewa "Let's get back to business then, as we all know My company is falling apart, i mean we are going bankrupt wannan ne dalilin da yasa nake neman taimakon ku kan ku taimaka kuyi investing a Company na domin farfaɗo dashi daga faɗawa halaka."



"Am not investing, but i can buy the company idan kaso" cewar wani daga cikin su.



"Yes, i don't think i can invest too, but if you're ready to sell the company out, zan iya saya" cewar wata daga cikin su.



Nan duk kowa ya fara kawo nasa ƙorafin akan ba zaiyi investing ba sai dai ya saya.



"Alright, alright am ready to sell it out, nawa zaku saya?."



Wata ce ta fara cewa "100million."


"150million" cewar wani.


"180million."


"200million."


"210million."



Haka kowa yayi ta faɗar kuɗin da zai saya wani yana ƙara yawan kuɗin akai duk dan su samu ya sayar musu da company ɗin.



"210million shikenan kuma babu mai ƙarawa akai?" cewar mai son sayar da company ɗin.



"1billion" suka jiyo ya faɗi hakan cikin calm voice ɗin sa, nan duk suka maida duban su gare shi, nan ɗaya yayi wuff yace "3billion."



Nan kuma kowa ya sake gyara zaman shi dan ganin ƙarshen karawa tsakanin wadannan biyu da basa son raini musamman wurin harkar business inda za'a sai da wani abu kowannen su burin sa shine ace ya fitar da kuɗi dayawa, shiyasa da yawa ke son gayyatar su su biyu aduk sadda suka tashi saida wata babbar kadara tasu.



"5billion" ya

Please Login or Register in order to submit comment