Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi masa pointing da yatsar ta hakan ya sanƴa sa maida duban sa wurin.

"What, bangane ba" ya faɗa yana kallon ta.

Sake nuna masa wurin tayi har sau uku kafin kuma yace "Okay, okay" yana duba agogon dake saƙale a wrist ɗinsa kafin kuma yace "Alright, i guess daga nan wurin kika fito koh, get up then."

Kallon ta ya tsaya yi ganin ta zuba masa idanu tana kallo hakan yasa shi sake faɗin "Get up lady."

Ganin yayi mata alamu da hannu ya sanƴa ta yunƙurawa ta miƙe dakyar, kafin kuma yayi gaba yana faɗin "I wonder ta yadda kamar ki zata iya 6ata a cikin asibitin nan, i have alot to cover but kina neman 6ata min lokaci."

Duk shi kaɗai ke maganar shi not knowing DEENAH na chan tsaye inda ya baro ta.

"Why are you so quiet lady, kodai ke kur...." bai iya idda maganar ba sakamakon juyowa da yayi ya ganta chan tsaye inda ya baro ta ta zuba masa watery eyes ɗinta.

"Seems like she is looking for my trouble" ya faɗi hakan yana komowa inda take.

"Are you sure you're Okay?" ya faɗi hakan yana kallon ta.

Ƙafar ta t tayi mata nauyi ta taka da kyar cikin ɗingishi kafin ta tsaya.

Kallon ƙafar tata yayi yace "Ohh, you can't walk properly" kafin kuma ya ɗaura da faɗin "Aren't you thesame girl i saw the other day?."

Shiru tayi tana kallon sa hakan yasa shi faɗin "Alright, come on" ya faɗa yana miƙa mata hannun shi.

Ganin ya gane cewar ba zata iya tafiya ita kaɗai bane yasa ta basa hannun ta, kafin ya riƙo ta su fara tafiya.


Ciki suka koma kafin kuma ya fara tambayar duk wanda suka haɗu dashi koh sun santa.

A haka har suka haɗu da wata nurse tace "Ohh yeah sure, kamar na santa she is from Room 106 chan upstairs."

"Thank you" ya faɗa kafin yaja hannun DEENAH da ta zama ƴar kallo kawai sukayi.

Taimaka mata tayi ta haura stairs ɗin kafin kuma ya shiga bin lambobin ɗakunan yana duba number ɗin da Nurse ɗin ta faɗa masa.

"Got it" ya faɗa lokacin da ya hango room ɗin.

Ƙarasawa sukayi bakin ƙofar kafin kuma ya hau knocking a ƙofar.

Ba'a jima ba aka buɗe ƙofar, DEENAH ganin Umma yasa ta ƙarasawa da sauri tana faɗawa jikin ta ta ƙanƙame ta.

"Menene, meke faruwa?" faɗin Umma tana shafa kanta.

"Hello ma'am."

"Hi" ta amsa tana kallon sa.

"Is she your daughter?."

"Yeah, she is."

"Oh i see, actually i saw her outside crying..."

"What crying, mai ya same ta?" ta faɗa cikin katse shi tana ɗago DEENAH.

"Well actually, ina tunanin ta 6ata ne batasan hanƴar dawowa ba, so i decided nayi tambaya koh akwai wanda ya santa and i met one nurse on our way ita ce ta sanar dani cewar a ɗakin nan take."

"Oh Thank you so much, Allah yayi maka albarka."

"It's alright, take care" ya faɗa cike da girmamawa kafin kuma ya wuce ya tafi.

Rufo ƙofar Umma tayi tana janƴo hannun DEENAH ciki ta zaunar da ita tace "Ina su wadanda kuka fita tare dasu ɗin sukayi?."

Shiru tayi bata bata amsa ba, hakan ya sanƴa Umma ma yin shirun tana komawa da gefe ta zauna tare da rabka tagumi.


***************************



_________"Why are you like this Ummie, maiyasa a komai sai kin nuna son kai ne?, wane irin gata ne mai Martaba baya bani, but kullum kina cikin complain akan abu ɗaya wato ZEEYAD, you told me that ZEEYAD ya mutu da daɗewa, why then kuma kullum maganar ki bata wuce wa akan sa, i thought kin tsane sa ne kasancewar shi aka fara haifa and shine zai zamto sarki, why then yanzu da ya mutu ba zaki saurara da maganar sa haka nan ba?" ya ƙarashe cike da takaicin halin mahaifiyar tasa.

Cike da fusata ta fizgo shi yana fuskantar ta tace "You fool, ce maka nayi guduwa yayi da ƙafafuwan sa maybe yana mace koh a raye, muddin ina da yaƙinin ya mutu mai zai kai ni tada hankali na kullum akan sa, shekaru goma kenan da 6acewar sa, sai dai har yanzu na rasa dalilin da ya sanƴa hankali na ya kasa kwanciya akansa, dukda cewa boka na ya daɗe da sanar min da cewar ZEEYAD ya mutu sai dai har yanzu zuciya ta ta kasa yarda da hakan."

"Well then i have had enough of all this nonsense Ummie, maiyasa ke kullum zuciyar ki babu abinda ke cikin ta sai sharri, ZEEYAD bai tauye miki komai ba a cikin gidan nan but sai da kika bi dukkanin wata hanƴa da zaki bi na ganin kin raba shi da farin cikin shi, how then kike tunanin zaki kasance cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kullum bayan munanan abubuwan da kika aikata?, ina baƙin ciki sosai na ganin duk sabida ni kike wannan haukan dan ganin kawai na zamto shugaba a wannan yankin, tayaya dama kike tunanin zaki zauna cikin kwanciyar hankali bayan kin sanƴa wani ruhi cikin baƙar wahala...?"

Marin da ta tsinka masa ne yasa shi saurin haɗiye maganar sa bai iya ƙarasar wa ba "How dare you hun, how dare you a matsayi na ta mahaifiyar ka kake faɗa wa wannan maganar?."

"Well am even ashamed to call you my own mother, i wish i can change you" ya faɗa cikin ƙunar rai.

Sosai take mugun takaicin halin YAZEED, sam bataso halin sa ya kasance a haka ba, dah ace ana canza hallayyar mutum, dah babu abinda zai hana canza sa da Sooraj, taso ace YAZEED ne ke da muguwar zuciya irin ta Sooraj, sai dai kash akayi rashin sa'a yafi mai martabar ma kyawun zuciya.

"And babu tantama kece sanadiyyar 6acewar ZEEYAD, and i know that kinsan inda yake kuma kinsan cewa yana raye, tell me Ummie ina ɗan uwa na yake?."

"You're talking nonsense, i told you ZEEYAD ya daɗe da 6ata, am definitely sure zuwa yanzu dabbobin jeji sun daɗe da yin kaca-kaca dashi."

A tsawace yace "You're lying Mother, just tell me the truth, kinsan inda ZEEYAD yake don't you, indai har bakisan inda yake ba kuma baya raye, maiyasa kullum maganar ki akansa take farawa ta kuma ƙarewa indai har ba tsoron dawowar sa kike ba?."

"Don't you dare try to challenge me."

"Am not challeging you, i know that kinsan inda yake, you're just hiding the truth, aren't you?."

"Ka haukace ne komiye YAZEED?, i told you bansan inda ZEEYAD yake ba sannan bansan komai akan 6atar sa ba, why don't you trust me?."

"Trust, you want me to trust you, why should i trust someone like you?."

"Am your Mother."

"You are not my Mom, kin haife ni ne kawai but baki yi min tarbiyyar da zai sanƴa na kira ki Uwa ta ba, i just wish that *QUEEN MOTHER* tana raye har yanzu, itace uwata ba ke ba" ya faɗa cikin mummunar 6acin rai.

Kallon ta yayi yanajin zuciyar sa na mugun ƙuna kafin kuma ya fice daga wurin kamar zai tashi sama.

Da kallo ta bishi tanajin mugun taƙaicin hali irin na YAZEED, she wonders ma anƴa ba'a canza mata shi ba kuwa, sam ba haka taso hallayyar sa su kasance ba.



******************



*TWO WEEKS AFTER*



_________"Umma ni fah gaskiya nayi kewar ku sosai am coming over kawai naga DEENAH."

"Kai dai Jafar in banda abin ka kwata-kwata yaushe ne ya rage mu dawo ma, da zaran ƙanwar taka ta gama samun sauƙi zamu tattaro mu dawo mai kuma zamu tsaya jira?."

"Amma Umma..."

"Kaga ni banason wani dogon surutu dan Allah, tunda nace ba zaka zo ba ina nufin kada kazo ɗin."

"Shikenan toh Umma tunda kin faɗi haka, ina DEENAH fah?."

"Sun fita chan wurin motsa ƙafa basu dawo ba."

"Umma kince bata magana koh?."

"Kwarai hakane Jafar."

"Toh dan Allah Umma inaso na kasance mutum na farko da zai fara jin muryar ta idan ta fara magana."

"Insha Allah ɗan albarka."

"Ni zan ajiye waya Umma, anjima zan kira."

"Toh shikenan sai anjima, Allah yayi maka albarka."

Da "Ameen" ya amsa kafin ta yanke kiran.



******************


_________"Are you sure that your Mom isn't hiding something? Cewar ZEEYAD da ya gama daburcewa da rashin ganin DEENAH.

Kallon sa Jafar yayi yace "Am suspecting so, amma koma dai menene it wouldn't be something serious."

Shiru yayi yana karkaɗa ƙafa dan kuwa bayajin zai iya ƙara koh da kwana ɗaya ne ba tare da ya sanƴa DEENAH cikin idanun sa ba.

"Am sorry but i guess i can't continue living so empty like this, i need to see her."

"Mai kake shirin yi?."

"Am going there."

"What?."

"Yes" ya faɗa yana miƙewa tsaye.

"But ka manta da sharaɗin da Umma ta gindaya maka ne?."

Shiru yayi kafin kuma yace "Ban manta ba, but my mind would never be at ease without knowing halin da take ciki."

"No you can't do this, babu abinda hakan zai janƴo sai fushin Umma akan ka."

"Look am sorry but i can't do this anymore" ya faɗa kafin kuma ya fice daga office ɗin.

Baki sake Jafar ya bisa da kallo "He is madly inlove with DEENAH" ya faɗa kafin kuma shima ya tashi yana bin bayan sa.


*******************


_______Safa da marwa kawai yake yi a cikin ɗakin nasa, so boring haka yakejin komai, he can't find Happiness anywhere, jin sa yake so very empty all he wants and craves for shine ya sanƴa DEENAH a idanuwan sa, hakan yasa shi yanke shawarar zuwa Egypt a gobe sabida he can't wait any longer.

Sai dai his biggest fear shine sam bai shirya tunkarar wannan ƙasar da rabon sa da ita ten years ba, ji yake kamar ya fasa tafiyar sakamakon zuciyar sa da ta kasa samun sukuni a duk sadda ya tuno da cewa ƙasar sa ta haihuwa zashi, but idan ya tuno da cewa farin cikin sa na chan duk sai yaji babu abinda yake buƙata kamar ganin sa a ƙasar.

Kan couch ya zauna tare da janƴo Laptop ɗin sa yayi wasu ƴan danne-danne kafin kuma ya rufe ta ya ajiye.


Wasar sa dake kan center table ya ɗauka tare da yin typing message ya tura ya ajiye ta.


Runtse idanun sa yayi sakamakon jin sa da yake very remorsed.

Huci ya fesar tare da wiping face ɗin sa kafin a hankali ya furta "Yaa Rabb I need you."



*THE NEXT DAY*


_______Ƙafar sa da ya sanƴa cikin ƙasar ne ya sanƴa dukkanin wata tsika ta jikin sa tashi.

For the first time after 10yrs, he is now temporary back to his Birth country.

Wata iriyar iska mai haɗi da sanƴi ce yaji ta huro shi, hakan ya sanƴa shi shaƙar iska haɗi da furzar da ita yana lumshe idanu.

Baƙar shade ɗinsa ya ciro ya maka a face ɗinsa tare da gyara zaman coat ɗin jikin sa yana sake tamƙe fuska kai kace wani babban maƙiyin sa ya hango tafe.

Wasu mutane ne suka tunkaro su cike da girmamawa kowanne cikin shigar baƙar suit fuskar su manne da baƙar shade.

Iso sukayi masa izuwa wasu tsala-tsalan motoci masu masifar ɗaukar hankali tare da buɗe masa ya shiga suka rufe.

Duk shigewa cikin motar sukayi kafin kuma su jata tare da barin cikin airport ɗin.


Wata katafariyar hotel mai matuƙar tsada da kyau aka kai sa tare da yi masa iso zuwa ciki cike da girmamawa kai kace zasu kife ƙasa ne, kafin kuma ayi masa iso har izuwa masauƙin sa.

Sai da yayi wanka ya huta sosai kasancewar dare ne ya sanƴa shi fitowa Balcony ɗin apartment ɗin nasa yana dafa ƙarafunan.

Sosai yake ƙarewa yanayin city ɗin kallo daga inda yake tsaye, tabbas ba ƙaramar cigaba aka samu a ƙasar nan ba, daga ganin yanayin wannan city ɗin kasan suna samun nasarori sosai.

Ɗan ta6e baki yayi kafin yace "So haka mutumin nan yake aiki?."
Kafin kuma ya yatsine fuska yana cize baki.

Iska ya shaƙa ya fesar kafin kuma ya koma cikin ɗaki.

Sosai ya sake yin danne-dannen sa cikin Laptop kafin kuma ya nemi lafiyar gado, zuciyar sa cike fal da tunani dama kuma murnar zai ga farin cikin sa gobe.


***********************


__________Da sassafe ya shirya, inda ya haɗe cikin baƙar shadda mai ɗinkin armless, wanda yayi matuƙar amsar jar fatar sa tare da yi masa bala'in kyau, fuskar sa dama kuma baƙar sumar kansa da ta sha gyara sai sheƙi suke, kasancewar Jafar ya turo masa address ɗin asibitin yasa ba tare da 6ata lokaci ba ya fice daga ɗakin sai tada ƙamshi yake.

Sabuwar motar da ya saya wanda already an riga da an kawo masa ita ya shiga tare da yi mata key ya bar cikin hotel ɗin.


Tracing location ɗin da Jafar ya tura masa yayi wanda ya kai sa har cikin asibitin, kafin ya nemi parking space yayi parking.

Jinsa yake wani iri sosai, Face-Mask ɗinsa ya sanƴa tare da ɗaukar glass ɗin sa ya maka a fuska, kafin ya sanƴa hannu ya buɗe murfin motar ya fito yana sake shan ƙamshi.

Tsayawa yayi tare da ƙarewa farfajiyar asibitin kallo kafin kuma cikin tafiyar sa mai haɗi da muguwar ƙasaita ya nufi ciki fuskar nan tasa tamau.

Wani Nurse ya tsaida kafin kuma cikin muryar larabci ya tambaye sa ward ɗin da akayi admitting ɗin DEENAH.

Kwatance yayi masa kafin kuma yayi masa godiya tare da bin hanƴar da ya nuna masa.

Tafiyar 10mins ce ta ɗauke sa zuwa wurin dan haka kutsa kai yayi kawai ciki yana wani cika haɗi da batsewa ganin kowa na bin sa da kallo.

_"Toh wannan idan na cire mask ɗina suma zakuyi kenan?"_ ya faɗi hakan a ransa kafin kuma ya ɗan ja ƴar ƙaramar tsaki.


"Fifth flour, Room 106" ya faɗa a hankali yana bin matattakalar benin.


Isowar sa flour ɗin yaja ya tsaya kafin kuma a hankali ya shiga takawa yana bin numbern kowane room da kallo.

Ja yayi ya tsaya, Room 105 ya gani a rubuce a ta hannun damar sa, zazzafar iska ya fesar yace "That is the room on my left hand side" ya faɗa yana juyawa ya kalli saitin room ɗin.

So, yau Finally zai sake sanƴa MADEENAHn sa a idanun sa.

Murmushin da bai san da zuwan ta ba yayi kafin ya tunkari ƙofar yana kai hannu da niyyar murɗa handle ɗin.


"Careful" yaji an faɗa ana tunkaro inda yake tsaye.

Kallo ɗaya yayi musu ya ɗauke idanun sa, kafin kuma yayi saurin sake maida duban sa kansu idanun sa na sauƙa a kanta.


He became speechless for some moments, ganin ta tare da wani hannayen sa riƙe a kafaɗun ta da alamu dai taimaka mata yake wurin tafiya.

Kauda kai yayi tare da runtse idanun sa, sabida he can't believe abubuwan da idanun sa ke gane masa, No wannan ba MADEENAHn sa bace, ba zata ta6a bari wani ya ta6a jikin ta ba, koh da kuwa da sunan taimaka mata yake sonyi ɗin.


Bai san da ƙarasowar su ba sai ji yayi ana yi masa magana "Excuse us please" yaji wannan saurayin ya faɗa.


Juyowa yayi yana sauƙe idanun sa cikin na saurayin, wanda dukkanin su wata iriyar shock ta ziyarce su lokaci guda, ZEEYAD ne yayi saurin ɗauke idanun sa yana sauƙe su cikin manƴan idanun ta da ta kafe sa dashi tana kallo.

Saurin basu hanƴa yayi kafin wannan Saurayin ya sake ta tare da buɗe mata ƙofar.

Kallon sa tayi tare da sakar masa murmushin da ya kusa tarwatsa zuciyar ZEEYAD kafin kuma ta shige ciki.


Kallon ZEEYAD saurayin yayi yace "Nan kakeson shiga?."

ZEEYAD da zuciyar sa ke mugun yi masa zafi idanun sa sun fara canza launi ba tare da ya kula shi ba ya bar nan wurin yana tafiya kamar zai tashi sama yanajin wani irin abu mai ɗaci a maƙoshin sa.





*Yawan Comment, Yawan Typing*





*_ZEEYAD FANS GROUP, kunga kwana biyu na lafa koh😌?, dan bana removing yasa kuka koma turomin stickers daga nan kuma kuyi miƙit wai ku ga masu wayo, Toh tsaf nake sane daku harda masu karantawa suyi shiru duk kun kusa jin ku a waje insha Allah_*









*MHIZZ JIDDHERR................✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*030...*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_




_*BANYI EDITING BA*_





_____________"Abhi am serious i saw him, he was standing right infront of me, i just don't know how i lose sight of him, Abhi ka yarda dani naga ZEEYAD with my own eyes."

Kallon Sadeeq Abhi yayi kafin yace "Ya kake tunanin zan yarda cewa ZEEYAD ka gani?, indai har shi ne wanda ka gani mai zai hana sa zuwa garemu bayan dawowar sa daga inda yaje?."

"Abhi believe me, ka yarda dani i really do saw him, fuskar sa ba zata ta6a 6acemin ba, he is ZEEYAD."

Shiru Abhi yayi yana jeka ka dawo a cikin falon yana jin maganar Sadeeq ɗin kamar almara, koh shi kan shi Abhi ya cire ran idan ZEEYAD na raye har yanzun ganin har izuwa wannan lokacin bai bayyana ba.

"Abhi ka yarda dani."

Shiru yayi tare da kallon Sadeeq yace "Na yarda da kai, amma indai har shine wanda ka gani dagaske, maiyasa kayi gangancin barin sa ya tafi bayan kuma a wuri ɗaya kuke ba tare da kayi masa magana ba?."

"Abhi wannan shine kuskuren da nayi wanda har yanzu nakejin haushin kaina akan hakan, but duk inda ZEEYAD yake nayi alƙawarin nemo shi, sabida lokaci yayi da yakamata ya dawo ga mahaifar sa yanzu."



*************************


__________Zubewa yayi akan lallausar couch ɗin dake falon yana maida numfashi.

Idanu ya runtse yana komawa da baya ya kwanta inda maganganun Umma suka shiga yi masa yawo a kwakwalwa.

"No!" ya furta da ƙarfi yana watsar da dukkanin abubuwan dake kan center table ɗin gaban shi.

Sosai yake fidda huci mai zafi kamar ransa zai fito "Why, how could you do this to me, i love her with all my heart and soul, how could you" ya faɗa da ƙarfi yana buga hannun sa jikin table ɗin inda glass ɗin ta tsage tare da tarwatsewa.

Bai damu da hannun sa da ya yanke yana tsiyayar da jini ba, dan kuwa zafi da raɗaɗin da yakeji a cikin zuciyar sa ya zarce tunanin mai tunani, shi kaɗai yasan mai yakeji, shi kaɗai yasan iriyar wahalar da yake sha, ransa a mugun 6ace yake, ji yake komai ya sunce masa zuciyar sa a mugun cunkushe take duk sabida raba sa da abar ƙaunar sa da akayi, bai ta6a sanin menene so ba sai akan DEENAH, idan aka cire irin soyayyar iyaye toh itace first love ɗinshi, akanta ya fara son wata ɗiya mace, ya sha haɗuwa da mata iri-iri sai dai duk cikin su babu wacce ya kula, ya tanada wa DEENAH kanshi tsawon shekaru, bai ta6a kawo cewa zai iya rasa ta ba, gashi yau mutuwa bata raba su ba amma mahaifiyar ta ta raba su, mahaifiyar ta tayi breaking heart ɗinsa tasa shi cikin halin ƙunci da wahalar da bai ta6a shan ta ba, ji yake wahalar da yasha a baya bai kai wanda yake sha yanzu akan DEENAH ba, sabida ya kwallafa rai sosai akanta shiyasa yakejin zafin rashin ta fiye da komai da za'a iya kwatantawa, bai ta6a furta mata cewa yana sonta ba ganin kamar hankalin ta ba'a kansa yake ba, but yana sonta so dearly fiye da komai na rayuwar sa a yanzu, ba zai ji ciwon rasa dukiyar sa ba kamar yadda yakejin ciwon rasa DEENAH a yanzu, gani yake tarin dukiyar da ya tara bayida wani amfani dan kuwa sun kasa samar masa farin ciki, bai rasa komai na rayuwa ba sai dai ya rasa abar da zata kawo masa farin ciki.

Sosai idanun sa dama dukkanin jikin sa sukayi jaa tsabar 6acin rai, abin ka da jar fata.


Miƙewa yayi da kyar yana layi ya wuce cikin bedroom tare da faɗawa kan bed ɗin idanun sa na rufuwa.


************************


_______A hankali ya shiga buɗe nannauyar idanun sa da suke matuƙar zugi yawa wanda aka zuba masa barkono a ciki kafin kuma ya sake maida su ya rufe yanajin haushin farkawar sa daga baccin, baiƙi ya dawwama cikin barci ba har abada muddin hakan zai mantar dashi damuwar da yake ciki.

Ya ɗau almost ten mins a haka kafin kuma ya buɗe idanun sa yana mai miƙewa zaune.

Kansa dake yi masa mummunar ciwo kamar zata tsage ya riƙe yanajin duniyar na yi masa juyi.

Da kyar ya samu ya lallafa ya faɗa bathroom.

Wanka yayi ya tare da ɗaura alwala ya fito.

Shiryawa yayi cikin farar jallabiya sannan ya tada sallah.

Bayan ya idda tare da yin adhkar ne ya miƙe tare da komawa falon.

Inda Telephone ke ajiye ya nufa tare da danna yin kira ya dawo cikin falon.

Ba'a ɗau lokaci ba ma'aikatan cikin hotel ɗin suka shigo ɗaya ɗauke da tray ɗin abinci a hannun sa, ɗaya kuma ɗauke da kayan shara.

Amsar order sa yayi tare da komawa ɗaki.

Zama yayi akan sofa ɗin ɗakin tare da buɗe tray ɗin abincin.

Abincin ya zubawa idanu yana kallo, abinci ne na ƴan ƙasar su wanda bansan sunan sa ba.

Rabon sa da yaci irin abincin nan tun Ummin sa na da rai, it was his favorite meal, ganin abincin ya sanƴa shi tunawa da ita, itace take zaunar dashi ta bashi abincin a baki koh da kuwa baiso hakan ba zata tilasta masa yaci, sai dai kuma gashi yau shi zai ciyar da kansa.

Hannu ya kai ya ɗau spoon kafin ya kai cikin bowl ɗin dake ɗauke da wata miya wacce bansan ta mecece ba tare da ɗebo ta ya kai baki yana yin bismillah.

Ji yayi abincin salam babu taste a bakin shi dan haka cokali ɗaya kawai yaƙara yana maida ta ya rufe.

Juice ya tsiyaya a cikin cup ya sha kaɗan tare da barin sauran kafin kuma ya ɗau tray ɗin abincin yana fitarwa falo.

Ma'aikatan hotel ɗin ya kira suka zo suka fita da tray ɗin.

Zaune yake shiru idanun sa da sukayi masa nauyi a lumshe ya rasa meke yi masa daɗi.

Haka ya kai almost 15mins yana nazari, kafin kuma a zabure ya buɗe idanun sa yana miƙewa tsaye.
"Grandma?" ya furta, kafin kuma ya zuri makullin motar sa yana yin hanƴar ficewa da sauri.

********************


________A gaban wani tsohon gida yayi parking motar sa yana mai fitowa daga ciki.

Kallo tsaf ya ƙarewa gidan, wanda ya kasance babba ne sosai, tabbas gidan ne dan kuwa bai ta6a zatan zai iya gane hanƴar ta ba.

Ya kai 5mins yana kallon gidan da yake tunanin babu kowa ganin ta garƙame da ƙatuwar kwaɗo wacce har kamar ta fara yin tsatsa ma.

Wucewar wasu samari guda biyu ya gani dan haka saurin tarar su yayi, bayan sun gaisa ne kuma cikin harshen larabci yake tambayar su inda mutanen wannan gidan suka je.

Ɗaya daga cike ne yace "Mutanen gidan nan ai sun daɗe da tashi."

"Koh zaku iya faɗamin inda suka koma?."

"Ehto naji dai kamar ance mai Martaba Sarki Abbas ne yazo ya ɗauke su tare da maida su chan cikin fada."

Zuciyar ZEEYAD ne yayi wani irin mugun faɗuwa jin an ambaci sarki Abbas, inda kuma tsoron abinda ya sanƴa shi maida kakannin sa MASARAUTA ya darsu masa.

"But...zaku iya faɗamin tun yaushe ne barin su nan?."


"Ehto, zai iya kaiwa shekaru takwas zuwa bakwai haka."

Idanu ya zaro da jin abinda suka faɗa, kenan hakan na nufin 6atar sa ya sanƴa mai Martaba maida kakannin sa

Please Login or Register in order to submit comment