Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_




_*NOT EDITED*_




__________Motoci ne kusan huÉ—u a jere suka shigo cikin MASARAUTAR kowanne na samun gurbin parking.

Bai wuci da ƴan sakonni da tsayuwar su ba driver ɗin dake jan motar da ta kasan ce ta biyu a jerin huɗun ya fito da hanzarin sa yana zuwa ya buɗe murfin motar kamar zai kife ƙasa tsabar hanzari da yadda jikin sa ke rawa.

Tunkuɗe driver ɗin yayi da ƙafar sa yana mai fitowa daga cikin motar, kyakkyawan saurayi ne sosai wanda ba zai wuci 25yrs ba ya fito fuskar nan tasa a wani irin mugun tsuke, yana sanƴe cikin shigar ƙananun kaya irin ta ƴan gayun zama ni wanda sukayi matuƙar kar6ar sa tare da amsar fatar jikin sa, hannu ya sanƴa tare da cire baƙar shade ɗin idon sa yana mai sake bin farfajiyar MASARAUTAR da kallo, chan ƙasan maƙoshi ya "Wow" yana barin jikin ƙofar kafin driver ɗin ya maida ta ya rufe.

"OMG!, this place is so fucking hot" cewar wata ƴar matashiyar budurwa dake ƙarasowa kusa dashi cikin rangwaɗa tana fifita da hannun tana wani irin yatsine fuska, sosai na ƙare mata kallo, tundaga kan curly dyed gashin kanta har izuwa kan doguwar takalmin da take sanƴe dashi, kyakkyawa ce sosai ba laifi, inda itama ke sanƴe cikin shigar ƙananun kaya, doguwar riga irin ta turawa wacce bata wuce mata guiwa ba, ƴar matashiyar budurwa ce da ba zata gaza shekaru ashirin ba.

Kallon ta saurayin yayi kafin yace "Seems like mutanen nan basu wani damu da dawowar mu ba, nobody even cares da zuwa tar6ar mu."

Yatsine fuska tayi kafin tace "Damn them, let's find our way inside."

Kallo yake ƙarewa farfajiyar inda suke tsaye yana kallon yadda bayi maza da mata kowanne ke fice da shige.

Daga nesa macen ta hango mahaifiyar su tafe kuyangun ta na take mata baya, nan tace dashi "Seems like she is happy da ganin dawowar mu."

"She looks a bit kind of Old."

Ɗan dariya tayi tana ƙarasawa wurin mahaifiyar tata.

"What kind of beautiful Mom i have got" ta faÉ—a cike da jindaÉ—i tana rungume mahaifiyar tata.

Sosai Sarauniya Hafeezah tayi murnar da dawowan ƴaƴan nata, ɗago ta tayi tare da sumbatar ta a ƙunci tana sake rungume ta tace "Welcome home my beautiful princess."

Sun ɗan daɗe rungume da juna kafin su ɗago, nan Sarauniya Hafeezah tace "Rahila ku raka Rahinah izuwa masauƙin ta sannan ku samar mata da dukkanin wani abu da ta buƙata."

Duƙar da kai wacce aka kira da Rahila tayi tana faɗin "Angama ranki ya daɗe" ta faɗa tana riƙo Farha da niyyar janta su tafi.

Wani irin wawan mari ta É—auke baiwar dashi in a rude manner tace "Yuck!, what the hell do you think you're doing, touching me with your fucking dirty hands?."

Rolling idanu kawai Sarauniya Hafeezah tayi kafin tace "Calm down princess, she will be careful next time."

Sosai ran Rahinah É—in ya 6aci tana wiping inda baiwar ta ta6a ta kafin tace "I don't care, baki faÉ—a musu dukkanin rules É—ina bane, she must be punished for her misdeeds, i mean how could she touch me with this ugly, dirty and disgusting hands of her?."

"Apologised to her now" faÉ—in Sarauniya Hafeezah cikin tsawa.

Baiwar da ta sha rikitaccen mari duk ta rikice ne tayi saurin rissinawa tana faÉ—in "Ki gafarce ni ranki ya daÉ—e gimbiya, a bisa rashin sani na aikata miki hakan."

Kallon ta Sarauniya Hafeezah tayi tace "Listen princess, kiyi mata haƙuri kinji?."

Kamar ba zata yi magana ba tace "Dan kawai kince hakan ne, am tired of standing here a nunamin masauƙi na mana, are they going to keep staring at me like this?."

"Show her to her room, and make sure kunyi avoiding duk wani abu da zai sanĆ´a ta 6acin rai."

"Insha Allah ranki ya daÉ—e" suka amsa cikin girmamawa.

Biyu ne suka shiga gaba biyu kuma suna take mata baya inda suka sanĆ´a ta a tsakiya "ughh they stink" ta faÉ—a cikin doÉ—e hancin ta tana korewa da hannayen ta suka wuce.

Sarauniya Hafeezah maida duban ta tayi gun saurayin dake tsaye ya wani 6ata fuska haɗi da naɗo baki wanda daga gani ƙiris yake ya fashe tace "Ayaan my boy" ta faɗa tana ƙarasowa kusa dashi tana rungumar sa.

"I guess am not your favorite anymore how could you ignore me kamar baki ganni ba kinje kina kula wata Rahinah chan daban?" ya faɗa cikin ɗagowa yana aika mata da wani irin kallo ƙasa-ƙasa.

"Am sorry Sweetheart, kasan bama haka da kai koh, come on na sanĆ´a an girka maka favorite É—inka am sure you will enjoy it."

Sai a sannan ya É—an saki fuska yace "Really?."

"Kai dai kazo muje" ta faɗa tana riƙo sa suyi gaba.

Da kallo yabi wata baiwa da tazo wuce su tana gaida su cikin girmamawa yana wani irin cize baki.

"Control yourself Ayaan, wadannan matan are like your servants dan haka ka É—auke idanun ka daga kansu."

"Sorry Ummie" ya faÉ—a suna cigaba da tafiya a haka har suka iso part nata.

Da wasu bayi ta haÉ—a shi inda shima akayi masa iso zuwa nashi part É—in.


****************

_______Sosai taci kwalliya cikin baƙar doguwar gown ɗin ta, kasancewa shine Favorite color nata.

Sosai ta dami Anty Khadija dake yi mata É—aurin head-tie akan tayi sauri.
"Anty Khadija yana ta jira fah, fisabilillah."

"Lallai ma DEENAH da ake kwalliya baki ce nayi sauri ba sai yanzu, toh wallahi ki zauna ki natsu kinsan dai banason abu da gaggawa, yanzu idan ban natsu na fidda ki mai kyau ba ai sai kije yace bakiyi kyau ba koh ma yaƙi yaba kwalliyar taki."

ĆŠan turo baki tayi tana kallon fuskar ta cikin mirror É—in.

Ameerah ce ta shigo É—akin tana faÉ—in "Miye nake ganin kamar duk kun shirya?."

Kallon ta Anty Khadija tayi tace "Toh da É—in mai kikeso muyi idan ba shirin ba?."

"Malamai ban fah gane ba, wai kuna nufin kuce har tafiya zakuyi yanzu?."

"Tsaya anan."

Jafar ne ya leƙo cikin ɗakin shima cikin shigar sa mai kyau yana faɗin "He is here."

Kallon sa Amirah tayi baki sake tace "Bangane he is here ba, wallahi ba zaiyiwu ba, tayaya zakuyi ku tafi ku bar ni bayan nasa rai" ta faÉ—a idanun ta na tara hawaye.

"Toh kuma laifin waye, ina zuwa kikayi kika kafa TV a gaba kina kallo yawa baƙauyiyar da ta fito daga karkara, kuma da nayi ta kiran ki kizo ɗin ba manna min kikayi ba, kyaji dashi ai dan mu kam ba jiran ki zamuyi ba" cewar Anty Khadija.

Cikin kuka Amirah tace "Wallahi in ta yiwu na zama albasa, wallahi baku isa ba" ta faÉ—a tana ficewa tayi É—akin Umma.

Kallon su Jafar yayi yace "Ya zakuyi mata haka?."

"Kyale ta nasan koh taje inbanda ƙauyanci babu abinda zata nuna, gara tayi zaman ta da akan ta kunƴatar damu."

"Anty Khadija, make it quick please."

"Ke ni dallah mai nakeyi ne yanzun, sai kisa na fasa na bar miki abin ki haka."

"Yi haƙuri" ta faɗa cikin sanƴi tare da tsuƙe bakin ta tayi shiru.

Ficewa Jafar yayi yana faÉ—in "We're waiting."

Ba'a daÉ—e ba Amirah ta dawo da Umma a bayan ta tana matsar kwalla lokacin har an gama É—aurawa DEENAH É—ankwalin.

Daga bakin ƙofar Umma ta tsaya tana kallon su tace "Amirah tace kunje ba zaku tafi da ita ba, maiyasa?."

Anty Khadija ce tace "Anty tunɗazu fah nake ce mata tazo ta shirya amma taƙi kula ni taje ta ƙura TV a gaba wai ita nan tana kallon favorite series ɗinta."

"Wallahi ba haka bane, ni babu wacce ta kira ni a cikin su, kawai dai basa son zuwa ne dani kuma sai naje" ta faÉ—a cikin kuka.

"Toh ya isa haka nan jeki shirya da wuri, ku kuma ku jira ta."

"Amma Umma Abyad fah yana ta jira" cewar DEENAH É—in cikin 6ata fuska.

"Kuyi mata haƙuri yanzun nan zata shirya ku tafi, abu na lokaci ɗaya kam menene dalilin ku na ware ta, wuce kije ki shirya."

Daɗi ne ya cika Amirah dan haka saurin wucewa tayi zuwa bathroom tana dariya ƙasa-ƙasa ganin yadda Anty Khadija da DEENAH suka 6ata fuska.

Ficewa Umma tayi daga É—akin cikin É—agun murya yadda Amirah É—in zataji Anty Khadija tace "Kuma wallahi minti biyu ki idda wankan nan ki fito, minti uku ki shirya kinga dai 5mins kenan koh, idan kika wuce haka kuma kya same mu a chan."

Sanin halin Anty Khadija ya sanĆ´a Amirah saurin fitowa daga wankan tana tsuke baki.

Da sauri ta É—au kayan ta mai kyau ita ma tasa kafin ta shiga shirin nata cikin sauri ganin yadda duk suke bin ta da harara yawa idanun su zai fito.

"Inbanda ma Ć´ar wahala iriyar ki kowa nan da kika gani da saurayin sa zashi ke koh da uwar wa zaki oho" cewar Anty Khadija tana aika mata da harara.

"Hmm Anty Khadija kenan nima fah saurayin nan ba rasa shi nayi ba..."

"Dallah ki rufewa mutane baki kiyi sauri, da wani ƙazamin saurayin naki a wurin hammata duk gumi idan yazo yawa wanda yayi gudun tsere kafin ya ƙaraso, ke har kina iya zama dashi a hakan ba tare da kinji komai ba mtssww."

"Oho dai, koma dai menene ba za dai ace banida saurayin ba."

"Da wannan abin ai gara babu, ke DEENAH kin ganshi kuwa, ni wallahi ina tantama ma idan ba irin samari ƴan ghetto masu yiwa ƴan mata ƙarƴar nan bane, who even knows koh baban bola mai ajakuta ne, dan kamar na ta6a ganin mai kama dashi yara na bin sa da gwangwan a baya."

"Nasan fah duk dan naji haushi nace na fasa bin ku kike faÉ—amin haka, kuma wallahi ahir É—inki kin dai san bana fushi da wuri."

"Toh dama mutum marar zuciya ina shi ina fushi komin É—acin a da za'a faÉ—a masa, kina ganin wannan Amirah É—in koh kaÉ—an batada zuciya wallahi, ka gama faÉ—a mata magana iya son ranka amma koh a jikin ta, dallah kiyi sauri da wani rigar ki yawa wacce zata wasan Ć´an bori koh kyau."

Ita dai Amirah bata kula ta ba, haka Anty Khadija tayi ta gaggasa mata magana duk dan taji haushi amma ita koh a jikin ta sai ma waƙar ta da take tana dariya.

A haka Jafar ya sake dawo ya same su nan yace "It's already 8:30 fah."

Miƙewa DEENAH tayi tana gyara zaman rigar jikin ta tace "Muje Yaya, ku same mu a waje."

Miƙewa Anty Khadija ma tayi tace "Toh su Amirah sai a iske mu a waje koh."

Tsaye Amirah tayi da kwalliyar da take tace "Dan Allah Yaya Jafar ka jira ni, wallahi na kusa kammalawa dan Allah."

Kallon ta yayi yace "Amirah, kafin mu wuce yanzu zan biya na ɗau Ruqayyah da siblings nata, and kafin mu ƙarasa dare zai iya yi, kin dai san kuma bama son dare yayi sosai mu dawo koh?."

"Shikenan bakomai kuje" ta faÉ—a cikin sanĆ´i tana barin bakin mirror É—in.

"Alright, 5mins ya isheki ki gama shiryawa?" ya faÉ—a.

Kai ta jinjina masa tace "Eh wallahi yanzu zan idda na fito."

"Alright, make it fast."

"Kashh wallahi na É—auka kinyi zuciya ne, ashe dai duk burga ce" faÉ—in Anty Khadija.

Hararar ta Amirah tayi tana komawa ta cigaba da kwalliyar ta.

DEENAH marawa Jafar baya sukayi zuwa É—akin Umma dan yi mata sallama.

"Jafar kada fah ku daÉ—e" cewar Umma.

"Insha Allah Umma."

Kallon Umma DEENAH tayi tace "Umma gift É—ina fah?."

"Ai dai kya je ki dawo tukun koh?."

Murmushi tayi tace "Toh shikenan" tana marawa Jafar baya.

Ficewa sukayi daga gidan, motar sa da ta hango ne yasa ta kallon Jafar tace "Tare dashi zamuje?."

"Yeah ke dasu Amirah ni zan wuce É—auko Antyn ki da siblings nata."

"Cha6 wannan yarinĆ´ar ce Anty na, na fah girme ta."

"Well she is your Aunt then tunda yayan ki na sonta."

"No case then" ta faÉ—a tana yin gaba.

Da kallo ya bita yana murmushi kafin shima ya wuce motar sa.

Knocking tayi jikin glasses ɗin window ɗin dake a zuge, ɗan buɗe murfin motar yayi kafin ta ƙarasa buɗewa tana kallon sa.

Sosai ya haɗe cikin shigar shadda baƙa mai ɗinkin armless wacce tayi matuƙar amsar farar fatar sa sai zuba ƙamshi yake.

Tsayawa tayi kallon sa ba tare da ta shiga cikin motar ba.

"Come in" kawai ya faÉ—a staring at her.

Shigewa tayi tana rufo ƙofar kanta a ƙasa tace "Sorry, i kept you waiting."

"It's alright babe, shall we?."

Kallon sa tayi kafin tace "Su Anty Khadija basu fito ba, yi haƙuri dan Allah ka sake jira."

"Okay" kawai ya faÉ—a idanun sa kan steering.

"Are you Okay?" ta faÉ—a tana kallon sa.

Kallon ta shima yayi yace "Mai kika gani?."

"You look somehow different, kodai kayi fushi ne mun 6ata maka lokaci?."

"Not at all, by the way you look so gorgeous" ya faÉ—a cikin murmushi yana kallon ta.

"Thank you, kaima kayi kyau, thats because you wore my favorite color."

Murmushi yayi yace "And you always look beautiful koh da baki sanĆ´a favorite color É—inki or wore make-up ba."

Kallon sa tayi cikin murmushi tace "You mean banyi kyau da make-up ba?."

Kallon ta yake yace "Of course kinyi kyau, but not as beautiful as your natural look."

Murmushi tayi kawai tana kauda kai tace "Gasu nan sun fito."

"Alright" ya faÉ—a yana tada motar.

Baya su Anty Khadija suka buÉ—e suka shiga tare da gaida shi ya amsa musu cikin sakin fuska.

Kallon DEENAH yayi yace "Shall we Ma'am?."

Kai ta jinjina masa cikin murmushi kafin yaja motar sukayi gaba.

Amirah dake ta rarraba idanu ne tace "Uhm kaga soyayya wai motar ma da zai ja sai ya tambaya ta, lallai DEENAH kin more."

Gwa6e bakin ta Anty Khadija tayi tana aika mata da harara.

Murmushi ZEEYAD yayi tare da kallon DEENAH yace "What's is she saying?."

"Don't mind her, ta É—an zauce ne."

Murmushi yayi yana maida hankalin sa kan tuƙin da yake.

Satar kallon Anty Khadija Amirah tayi kafin tace "DEENAH kice yasa mana É—an kiÉ—a mana, mota shiru haka biya."

"Wai ke miye haka ne?" faɗin Anty Khadija ƙasa-ƙasa kamar ta make ta, kafin kuma tayi kwafa tana kauda kanta.

Ta6e baki Amirah tayi haÉ—i da yin shiru sai rarraba idanu take har suka isa inda zasu.

Babban Event center ne mai kyau da tsaruwa, koh ina gauraye yake da hasken wutar lantarki kasancewar dare ne.

Wuri ya samu yayi parking motar, nan duk suka buÉ—e suka fito.

Amirah ce tace "Uhm lallai rabon da nazo wuri irin wannan ai tun auren Anty Salma."

Tsaki Anty Khadija taja dan kuwa ba ƙaramin haushi Amirah ɗin ta bata ba.

"Shall we?" ya faÉ—a nan duk suka juyo suna kallon sa, nuni yayi musu da hanĆ´ar da zasu bi kafin ya shige gaba suna take masa baya.

Amirah ce tazo kusa da DEENAH tace "Ke DEENAH anĆ´a ba asirce wannan bawan Allahn kikayi ba kuwa?, wallahi ya haÉ—u Kafci."

Harara DEENAH ta zuba mata dan kuwa itama ba ƙaramin haushi Amirah ɗin ta bata ba, ta 6ata musu lokaci gata bakin ta baya iya yin shiru indai taga abu.

"Allah ya huci zuciyar ki, ni da ba dan nazo bama wallahi da sai na koma tunda naga sai wani gani-gani kuke yimin dake da Anty masifatu É—in chan."

DEENAH dai bata kula ta ba har suka iso entrance ɗin hall ɗin da aka kama musu ɗin, yadda aka ƙawata wurin ba ƙaramin kyau yayi ba, style akayi wa wurin da balloons baƙaƙe ga kuma dim lights da suka sake ƙawata cikin wurin abin sai wanda ya gani.

Wow duk sukayi exclaiming bale ma Amirah da ta saki baki tana sake bin wurin da kallo.

Juyowa yayi ya kalli DEENAH yace "You have a seat, i will be back in a moment."

Kai ta jinjina masa tare da zama cikin kujerun da aka zuba a wurin tana sake bin É—an daidaikun mutanen dake jeka ka dawo a wurin da kallo.

Fitar sa keda wuya Anty Khadija ta hau Amirah da faɗa "Ke wace iriyar banza ce Amirah, ke shikenan kwata-kwata ba zaki ta6a hankali ba, miye amfanin abinda kikayi yanzu ke koh kunƴa bakiji ba, shikenan ke baki baya iya yin shiru a komai, ai dama abinda yasa nace ba zaki bimu ba kenan sabida kwata-kwata bakida hankali ne amma sai ake ganin kamar banason ki ra6e mu ne, ke shikenan ba zaki ta6a wayewa ba kenan a rayuwa, kina komai kamar baƙauyiya, haba yaci ace kin gyara yanzun babu abinda kika nema kika rasa a gidan ku amma duk inda kikaje sai kin nuna ƙauyanci har inda mutanen ba zasu nuna miki komai bama, toh wallahi koh ki gyara koh mu yi ta samun matsala dake, wannan ai daƙiƙanci ne."

Shiru Amirah tayi kamar ba ita ce mai bakin surutu É—azun nan ba.

Wuri Anty Khadija ta samu ta zauna ranta fal a 6ace.

Basu fi 5mins da zama sai ga Jafar ne tafe da wata kyakkyawar yarinĆ´a da ba zata wuci 17-18yrs ba, bayan su kuma wasu yara ne da ba zasu wuci 10yrs ba mace da namiji, da alama dai Ć´an biyu ne yaran sabida yadda suke É—an kama da juna.

Murmushi DEENAH da ta hango su tayi tana miƙewa ta nufe su zuciyar ta fal farin ciki tace "Yaya itace?."

"Yeah" ya amsa mata cikin murmushi.

"Wow tafi kyau a zahiri akan a cikin hoto" ta faÉ—a tana kallon yarinĆ´ar.

Murmushi itama yarinĆ´ar tayi tace "Ina wuni?."

Kallon Jafar DEENAH tayi kafin ta amsa mata gaisuwar cikin ɗan dariya, kafin kuma ta riƙo hannun ta tana nuna mata seat ta zauna da ita da ƙannen nata.

Kallon su Anty Khadija yarinĆ´ar tayi ta gaida su cike da girmamawa suka amsa mata.

Kallon DEENAH Jafar yayi yace "Where is he?."

"Ahm, yace min zai dawo yanzu."

Kai ya jinjina yace "Okay, you wait here i will be right back, Okay?."

"Okay" ta amsa masa kafin shima ya bar wurin.

Jafar bai daɗe da barin wurin ba ZEEYAD ya dawo, duk zuba masa ido sukayi suna kallo har ya wuce wurin DEENAH ɗin, ɗan duƙawa yayi yana yi mata magana a kunne kafin ya ɗago yana kallon fuskar ta.

Kai ta jinjina masa tana miƙewa tsaye, kallon Anty Khadija tayi tace "Dan Allah Anty Khadija zamuje mu dawo yanzu, ki kular min da baƙin nawa."

"Okay toh, bakomai" ta faÉ—a.

Kallon sa tayi tace "Muje."

Mara mata baya yayi suka wuce, yayin da duk suka bisu da kallo, Amirah magana ne fal a bakin ta sai dai ganin kada Anty Khadija ta sake dizga ta a gaban budurwar Jafar ne ya sanĆ´a ta tsuke bakin ta tayi shiru.

Waje suka fito nan ya kalle ta yace "Actually, i have nothing to said."

"What?" ta faÉ—a tana kallon sa.

Shafo lallausar sumar kansa yayi cikin murmushi yace "I just wanna spend some time with you alone."

"You're unbelievable" ta faÉ—a.

"Am i?."

"Without a doubt."

"Alright, muje chan na saya miki sweet-cotton" ya faÉ—a yana nuna mata wurin wani mai saida sweet-cotton a farfajiyar wurin.

"It's my birthday, we should be celebrating, dare yana yi fah."

"Yeah we will celebrate, but atleast we should have a little date here."

Folding hannaye tayi tana kallon sa ba tare da tace komai ba.

"Shall we?" ya faÉ—a yana kallon ta.

"Yeah, but muyi sauri kar mu 6ata musu lokaci."

"Alright" ya faɗa yana miƙa mata hannun sa, da kallo tabi hannun nasa kafin kuma ta miƙa masa nata hannun yana riƙewa cikin nasa suka fara tafiya.

Isowa wurin sukayi nan ya kalleta yace "Tsinke nawa kike so?."

"Kasan ni ba wani shan sa nake sosai ba, koh da muna yara ma idan baban-bola yazo ni ban cika amsar sweet-cotton ba, tsinke É—aya ya ishe ni."

"Really?, ba shida auki fah" ya faÉ—a yana kallon ta.

"Yeah ni ba dayawa nakeso ba."

"Alright" ya faɗa yana ciro wallet ɗinsa, wayar sa da tayi ƙarar shigowar message ya ciro yana miƙa mata wallet ɗin yace "Pay him" yana yin gaba.

"Nawa ne kuÉ—in?" ta tambayi mai saida abin.

"ĆŠari biyar ne Hajiya" ya amsa mata.

Baki sake take kallon sa tana sake maida duban ta kan tsinken sweet-cotton É—in.

Shiru tayi kawai tana ciro 1k ta miƙa masa tace "Toh ka kawo biyu."

Tsinke biyu ya ɗauko yana miƙa mata ta amsa kafin tace "Nagode" tana juyawa ta tayi inda yake tsaye.

Wallet ɗinsa ta miƙa masa ya amsa tana bashi tsinke ɗaya.

"No bana shan zaƙi" ya faɗa.

"What, why?."

"I just don't like ire-iren abubuwan nan, it's for kids like you."

Kallon sa take kafin tace "Kids, you mean am a kid?."

"Yeah, i can't believe sai yau kike cika 20yrs."

"Kids are children's below 10, and am 20."

"Well then that doesn't make any difference, believe it or not you're still a Kid."

"No am not."

"What are you then, a teenager?."

Something similar to that" ta basa amsa.

Murmushi yayi kawai ba tare da ya sake cewa komai ba har suka iso inda suka bar su Anty Khadija zaune.

"Where are they?" ta faɗa tana ƙarewa wurin kallo ganin babu su.

"Maybe in there" ya faɗa yana nuna mata wata ƙofa.

"Anan za'ayi taron?" ta tambaya tana kallon sa.

Kai ya jinjina mata yana yin gaba nan ta mara masa baya.

Buɗe ƙofar yayi ya shiga kafin ita ma ta mara masa baya.

Cak taja ta tsaya ganin wani irin duhu mamaye cikin É—akin gabaÉ—aya.

Idanu ta fara rarrabawa tare da yin lalume tana yin gaba "Abyad?" ta ƙira sunan nasa a hankali.

"Where are you, why is it so dark in here?."


"Abyad?" ta sake faÉ—a cikin É—an tsoron da ya fara darsar mata tana cigaba da laluma hannayen ta.

"Ab..." bata kai ga ƙarasar maganar tata ba taji an saki ihun _Happy Birthday to you_ dai-dai lokacin da wutar wurin ya kawo wasu flowers suka shiga zubo mata akai.

Sosai ta tsorata da yadda sukayi mata É—in dan haka hannaye tasa ta rufe fuskar ta ta fara kuka a hankali, inda kuma wurin ya cika da sautin flute É—in happy birthday.

Fuskar kowa washe yake da murmushi, Jafar ne ya fara tafa hannayen sa yana yi mata waƙar _Happy birthday to you_
_Happy birthday to you_
_Happy birthday dear DEENAH_
_Happy birthday to youuuuu_

Zuwa tayi da É—an gudu tana rungume shi cike da farin cikin da take ciki.

_How old are you now?_ cewar Anty Khadija cikin ɗan waƙa.
_She is 20yrs old now_ Amirah ta amsa.

Duk É—an dariya Ć´an wurin sukayi suna kallon Jafar da DEENAH É—in.

ĆŠagota yayi yana share mata hawayen yace "Why the cry?."

"Actually you guys scared me" ta faÉ—a cikin É—an dariya.

Kallon ZEEYAD da yayi folding hannaye a gefe tayi tana ƙarasawa wurin sa tace "Thank you."

Cike da É—an mamaki yace "For what?."

Wurin ta ƙarewa kallo wanda daga gani ba ƙaramin naira aka zuba masa ba tace "This is all your doing, isn't it?."

Murmushi yayi yace "Actually, you deserve anything, more than this."

Murmushi tayi tana sadda kai ƙasa.

"It's getting late, muyi abinda ya kawo mu mu tafi, let's cut the cake" faÉ—in Jafar.

Duk nufar inda ƙaton kyakkyawan cake ɗin yake sukayi, Jafar ne ya kallesu yace "Am eager naji cake ɗinnan cikin baki na."

Murmushi duk sukayi kafin tace "Muje."
Murmushi yayi ya mara mata baya, tsakiya duk suka sanĆ´a ta.

Anty Khadija ce ta ɗau ƴar ƙaramar knife ɗin yanka cake ɗin tana miƙawa DEENAH.

Amsa tayi cikin murmushi tana saita shi kan inda zata yanka, waƙar happy birthday ɗin suka cigaba da yi mata har ta yanka cake ɗin suna cigaba da tafa mata.

Slice ta É—auko tana sanĆ´awa Jafar a baki inda shima ya gutsuro da niyyar bata sai dai ya fuzge yana sanĆ´awa girlfriend É—insa tare da barin DEENAH da sakakken baki, juyowa yayi tare da É—aga mata gira yace "Wife first."

Turo baki tayi tana juyawa ta kalli ZEEYAD dake gefen ta.

Murmushi yayi yace "Don't mind him" ya faÉ—a yana É—aukar knife É—in ya yanka É—an madaidaicin slice, kallon ta yayi yace "Haa."
BuÉ—e baki tayi nan ya sanĆ´a mata cake É—in, yana goge cream É—in da ya É—an 6ata mata gefen baki da tissue, duk tafi suka sanĆ´a, DEENAH kuwa sosai zuciyar ta ke cike da tsantsar farin ciki marar misaltuwa.

Wani yanka ta sake iyowa tana baiwa Anty Khadija a baki, kafin duk Ć´an wurin ta bisu ta basu suma.

Amirah ce tace "Toh shi ba zaki bashi bane?."

Kallon ZEEYAD tayi duk sai taji babu daÉ—i, kafin

Please Login or Register in order to submit comment