Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rubbing bayan sa gently, ɗago da fuskar sa da tayi jaa sosai tayi tana kallon sa, haɗe bakin su tayi tana basa cool kiss kafin ta ɗago tana sake rungume shi a jikin ta, a hankali ta shiga faɗin "It's alright" tana ɗan bubbuga bayan shi.


*****************************


*THE NEXT DAY........*







*Yawan Comment, Yawan Typing*






*MHIZZ JIDDHERR.................✍🏽*
[9/10, 2:30 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *FINALE🤸🏽‍♀️*
*(FINAL)*




*Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```





*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*






*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*


*055*


_______Kai da komowa mai Martaba keyi cikin ɗakin sa, kansa a matuƙar ƙulle yake, ya rasa ta ina zai fara 6ullowa wannan lamari na Hafeezah, babu wanda yafi tausayawa kamar YAZEED ɗan albarka, tayaya zai fara yankewa mahaifiyar da hukuncin kisa a gaban sa, sai dai kuma wani 6angaren na zuciyar sa na umartar sa da ya shashashantar da lamarin YAZEED ya yanke mata hukunci a bisa dokar Allah (SWT), ya sauƙe mata dokar MASARAUTA koh dan albarkacin YAZEED ma, nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe yana maida duban sa kan hoton QUEEN MOTHER, ya jima yana kallon hoton nata kafin kuma ya sauƙe numfashi tare da ɗaukar sandar tafiyar sa a hankali cikin takun ƙasaita ya bar cikin ɗakin nashi.

A fadar sa ya yaɗa zango inda ministocin sa ke zaune suna jiran fitowar sa, tattaunawa sukayi sosai kafin kuma duk su miƙe su nufi filin da aka ware dan yankewa masu laifi hukunci.

Sosai mutane suka hallara tsofi da manƴa dama kuma ƙananun dan shaidawa idanun su irin hukuncin da za'a yankewa matar sarki Hafeezah.

Inda aka ware na zaman mai Martaba ya nufa ya zauna sai dai ya gama wulla idanun sa bai hango ZEEYAD da YAZEED ba anan wurin.

Bafaden dake tsaye a kansa yayi wa magana kan ya dubo masa su, cike da girmamawa ya amsa masa kafin ya bar wurin kafin wani yayi saurin replacing wurin tsayuwar sa yana ƙamewa.

***************

_______Zaune YAZEED ɗin yake yayi jugum dashi, kwakwalwar sa cunkushe take da tunanika kala-kala, he can't believe wai uwar da ta haife sa za'a yankewa hukuncin kisa a gaban ɗumbin mutanen gari, sosai yakejin wani iri a ransa, baya tunanin zai iya fita zuwa wurin taron nan, dan kuwa ba zai iya shaida irin hukuncin da za'a yi mata ba, sosai zuciyar sa ke rawa tana karyewa, shi kaɗai ya san abinda yakeji.

Knocking yaji daga bakin ƙofar ɗakin nasa ba tare da ya bada izinin shigowa ba JALILAH ta buɗe ƙofar ɗakin ta shigo, tsaye tayi tana kallon sa cike da tausayawa, ɗagowa yayi ya kalleta kafin kuma ya kauda kansa ƙasa.

Idda shigowa tayi tana zama kusa dashi tare da dafa kafaɗun sa tace "Inaso ka sani cewa, Allah ya ɗaura maka wannan ƙaddarar ne ba dan bayason ka koh baya ƙaunar ka ba, koh wane bawa mai imani Allah na jarabtar sa ta fanni daban-daban dan ganin ƙarfin imanin sa, haƙiƙa kai mai imani ne hakan yasa ka iya tsallake duk wani tuggu da mahaifiyar tayi ƙoƙarin cusa maka a baya haka kuma Allah na son ka da rahama hakan ya sanƴa shaiɗan baiyi galaba akanka ka biye mata ba dukda cewa ita ɗin mahaifiya ce mai iya umarta ayi ba tare da musawa ba, Allah na sonka da rahama YAZEED kada ka ta6a manta wannan, dah ace bayason ka na tabbata da kai za'a yankewa wannan hukunci ba iya mahaifiyar ka kaɗai ba, ka godewa Allah da ya sanƴa ka zamtowa mai tsarkakakkiyar zuciya, irin ƙaddarar mahaifiyar ka kenan babu wanda ya isa ya gujewa hakan koh ya canza shi, kayi haƙuri, kayi haƙuri YAZEED ka rungumi jarabawa, ba zaka ta6a iya canza ran sarki ba akan hukuncin da zai aiwatar, koh ka manta faɗin Allah ne na cewa duk wanda ya kashe shima a kashe shi, da akwai mutane da dama da suka shuɗe da tasu jarabawar tafi taka tsarkakiya da wahala amma sunyi haƙuri sun jure gashi komai ya zamto labari su kansu sun zamto labari, inaso ka sani cewa ZEEYAD ma bayida mahaifiya amma yana da mata, Kaka, mahaifi dama kuma ɗa, kaima kuma hakan take a wurin ka, kana da mahaifi, Grandma ta ɗauke ka tamkar ZEEYAD ne, kanada mata sannan kada ka cire ran zaka samu ɗa wataran kaima, mai yafi samun wadannan abubuwa farin ciki a rayuwa?, har yanzu kana da family ZEEYAD, Grandma, Mai Martaba, DEENAH, Rahinah, little ZEEYAD, Ayaan dama kuma ni, na tabbata wadannan sun isa su samar maka da farin cikin da kakeso na har abada, kayi haƙuri haka nan, ka sani rayuwar da ZEEYAD yayi fama da ita a baya ta wuce ƙuncin da kake ciki a yanzu, yanzu kuma da ya gano mahaifiyar ka ce tayi sanadiyyar mutuwar tasa mahaifiyar ya kuma ganka cikin halin ƙunci sabida za'a yankewa mahaifiyar ka hukunci mai kake tunanin zaiji cikin ransa cewar bakason a ɗaukar wa mahaifiyar sa haƙƙin ranta komiye?."

Ɗago da jajayen idanun sa yayi yana sanƴawa cikin nata da take kallon sa, murmushin kan le6e ta saki tana riƙo hannun sa cikin nata kafin ta cigaba da faɗin "Nasan ba zaka so yaji wani abu game da hakan ba, ka ɗauki QUEEN MOTHER tamkar mahaifiyar ka ne, dan haka ka ɗauka cewa mahaifiyar ka ta daɗe da mutuwa kaima tamkar ZEEYAD, sannan ka sanƴa a ranka cewar fansar ranta za'a ɗauka yanzu tamkar yadda Ubangiji ya halatta, kada ka kuskura ka bari ɗan uwanka ya gano kanajin ƙunci game da wannan lamari, nasan it will be hard for you, sabida har yanzu jinin ta ne ke yawo a jikin ka amma daurewa zakayi, daurewa zakayi YAZEED ka maida komai ba komai ba, ka toshe idanuwan ka da kunnuwan ka ka cire damuwar hakan tattare da kai idan kayi hakan then with time zakaji komai ya zamto tarihi cikin rayuwar ka lokacin da ka buɗi ido ka ganka zagaye da family ɗinka masu sonka kuma kullum suke ƙoƙarin ganin sun sanƴa ka farin ciki, bin hukuncin Allah shi kaɗai zai haifar da zaman lafiya cikin zuri'a dama kuma ƙasa baki ɗaya, ƙuncin da zakaji na lokaci ƙanƙani ne nayi maka alƙawarin hakan da zaran kaga kowa cike da farin ciki da walwala ba zaka san sadda kaima zaka warware al'amura su cigaba da tafiya dai-dai tare da kai ba, i know it's hard YAZEED but na ƙanƙanin lokaci ne bi-iznillah" ta ƙarashe tana kallon sa kamar yadda yake kallon nata.

Sosai yaji kalaman ta sunyi matuƙar tasiri tare da sanƴaƴa masa zuciyar sa, ya ɗauka ba zai ta6a samun sanƴi cikin zuciyar sa nan kusa ba, sai dai kuma cikin ƙanƙanin lokaci kalaman JALILAH suka sanƴaƴa masa zuciya tare da bashi hope ɗin tabbas watarana komai zai zamto tarihi tamkar ba'ayi ba haka kuma farin ciki marar yankewa zata darsu cikin wannan family nasu, gusar da gur6atattun mutane kamar mahaifiyar sa daga cikin ahali dama kuma ƙasa baki ɗaya shi kaɗai ne hanƴar wanzar da farin ciki marar yankewa, shima damƙe hannun ta yayi cikin nashi yana jinjina mata kai yayin da murmushi ke wanzuwa kan fuskar sa.

Maida masa martanin murmushin JALILAH tayi tanajin daɗi sosai a ranta na yadda ta kwantar masa da hankali, sun daɗe suna kallon juna kafin kuma yayi saurin kauda kansa yana miƙewa tsaye.

Tsaye itama ta miƙe kafin tace "Nasan abu mai wuya ne kaje wurin taron nan, zaka iya kwanciya ka huta koh zaka sami ƙarfin jikin ka."

Kai kawai ya iya jinjina mata, murmushi tayi ta nufi hanƴar ficewa.

"JALILAH" ya kira sunan ta, tsayawa tayi tare da juyowa tana kallon sa "Thank you" yace da ita, murmushi tayi masa kawai kafin ta buɗe ƙofar ɗakin ta fice.


********************

_______Cikin mutane tayi ta ratsawa cike da tashin hankali har ta iso inda mahaifin nata ke zaune da gudu tazo zata isa garesa wani dogari yayi saurin tare mata hanƴa da takobin hannun sa.

A tsawace tace dashi "Get out of my sight you stinking being" ta ƙarashe cikin wulla masa mugun kallo da idanun ta da sukayi jazir alamun tasha kuka ta gaji ne.

Hankalin sarki ne ya dawo kansu, fuskar sa ya sake ɗinkewa ganin Rahinah ce tsaye tana yiwa dogarin rashin kunƴa.

Cikin tsukewar fuska wannan dogarin yace da ita "Mai Martaba baya buƙatar ganin kowa yanzu har sai bayan an aiwatar da abinda ya tara jama'a anan wurin."

Hannu ta ɗauke ta wanke fuskar sa da mari kafin ta nuna sa da yatsa tace "How dare you, uba na ne shi dan haka babu wanda ya isa ya hane ni daga zuwa ganin sa a duk lokacin da naso, ƙasƙantaccen bawa kamar ka bai isa ya taremin hanƴa da sunan tsare ni daga zuwa wani wuri ba musamman ma wurin mahaifi na, so get your ugly face out of my sight now."

Sosai dogarin yaji zafi cikin zuciyar sa, sa'ar ta ɗaya ita ɗin ƴa ce ga sarki dah kuwa babu abinda sai hana shi tattaka ƴar banza ƙaramar yarinƴa da ita.

Hanƴa ya buɗa mata nan tayi saurin wucewa tana aika masa da mugun kallo, kafin ta isa ga mahaifin nata tana zubewa a gaban shi tare da riƙo ƙafafun sa.

Cikin kuka take faɗin "Abhi dan Allah, dan Allah ka kyale Ummie kada ka yanke mata wannan tsattsauran hukuncin, ka tuna fah mahaifiyar mu ce tayaya zaka yanke mata hukunci gaban mu?, Abhi gashi Ayaan ma yana chan asibiti kwance rai a hannun Allah, hannun sa sai ƙara ciwo yake infection ya shiga likitoci sun ce zasu sake yanke masa hannun, dan Allah Abhi kayi haƙuri kada kayi mana haka, ina zamu sanƴa ranmu idan ka ɗauke mana Ummie, ita kaɗai ce gatan mu kuma ita kaɗai ce mai son mu, dan Allah kayi haƙuri ka janƴe maganar hukuncin nan" ta ƙarashe cikin fashewa da wani irin matsanancin kuka.

Sosai jikin mai Martaba yayi sanƴi, yana tausayin yaran nasa sai dai hakan ba zai hane shi daga aiwatar da abinda ya zamto wajibi a gareshi ba, dukkanin wani baƙin hali daga gun mahaifiyar su suka ɗauko shi, shiyasa kaf cikin ƴaƴan sa yafi ƙaunar ZEEYAD da YAZEED sai kuma ƴaƴan Nazeerah wadanda kowacce ya aurar da ita tun suna 18yrs kuma alhamdulillah suna nan zaune gidan mazajen su lafiya ba tare da sun ta6a kawo masa rahoton wata matsala ba dan kuwa yasan halin mahaifiyar su suka biyo wacce bata shiga sabgar da bata shafe ta ba take kuma ɗauke ido akan dukkanin wani abu da ta gani muddin ba wai ka tambaye ta bane ba, sa6anin Ayaan da Rahinah da koh kaɗan basu ɗauko hali mai kyau ba sai karatun da uwar su Hafeezah ta koyar dasu, yanajin tausayin wannan rayuwar tasu sai dai ya zama dole ya yankewa Hafeezah hukunci koh suma sa samu su gyara halayen su dan kada hakan ya faru a kansu nangaba.

"Take her away" kawai ya iya faɗa, sake riƙo ƙafar sa tayi tana kuka tare da kiran sunan sa amma yayi mata biris har aka fitar da ita daga wannan wurin.

Taro ne ya sake cika mutane sai halarta suke, ganin ƴaƴan nasa basuda niyyar fitowa ya sanƴa shi bada umarnin a fito da Hafeezah dan yanke mata hukunci.

Ba'a jima ba aka kawo ta hannayen ta ɗaure da chain, kallo ɗaya zakayi mata ka hango tsantsar tashin hankali da firgici akan fuskarta, ganin yawan mutanen da suka hallara ne ya sake darsar mata da tsoro tare da gasgata mata cewar dagaske fah yau tata zata ƙare a duniyar.

Wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga yi mata zarya akan kumatu, wani irin nadama, tsoro dama kuma fargaba na sake darsar mata cikin zuciya, sosai take nadamar abubuwan da ta aikata wanda daga ƙarshe bata ci kyakkyawar ribar komai daga cikin sharrin da ta aikata ribar ta kuwa shine hukuncin kisa a gaban ɗumbin jama'ar gari idon kowa na kallo, sosai ta shiga yin kuka tana ta shiga uku ta lalace a yafe mata ba zata ƙara ba.

Biris guards ɗin dake biye da ita sukayi har suka rakata zuwa inda zata hau a rataye ta ɗin.

Zubewa tayi a wannan wurin tana cigaba da kukan da ba zata amfanar da ita komai ba, babu abinda take tunani sai iriyar rayuwar da tayi a baya kamar ba zata mutu ba, tayi ta cutar da bayin Allahn da basuji ba basu gani ba dukda sunan ita mai mulki ce, ta kashe innocent baiwar Allah LATEEFAT duk dan son zuciyar, ta kuma wulaƙantar da rayuwar ZEEYAD sabida bata tsoron Allah bata tuna ranar ƙin dillanci, bata tuna cewar zata mutu fah wataran, gashi mai mulkin da babu irin sa a yau ya nuna mata iyakar ta, ya nuna mata cewa babu wani sarki koh mai mulki sai shi, ya nuna mata cewar duniyar a hannun sa yake, ya nuna mata cewa baya gyangyaɗi bale bacci, ya nuna mata cewa shi mai ji ne jin da babu wani mahaluƙi da ya isa ya kwatanta ya yake, ya nuna mata cewa kowane ɗan adam nada iyakar sa a rayuwa sannan ya nuna mata cewa lokaci kowane ɗan Adam ke jira, lokacin da ya tanadar masa na ranar girbar abinda ya shuka walau alkhairi ne koh sharri.

Sosai take kuka kamar ranta zai fita, koh kaɗan babu wanda yaji tausayin ta a wannan wurin sai ma shewa da mutane ke tayi kan cewar _A kashe ta_, sosai wannan kalma da suke ambata ke sake firgitar da ruhin Hafeezah, ji take kamar ta nutse a wurin saboda kunƴa, sosai zuciyar ta ke mugun bada sauti mai cike da tsoro da firgici ganin dai tsakanin ta da mutuwa bai wuci taku ɗaya ba, mutuwa na jiran ta a gefe, babu damar tuba koh neman yafiyar Ubangiji, sabida bakin alƙalami ya riga ya bushe, sauƙin ta ɗaya a kashe ta kamar yadda ta kashe ta haka ne kaɗai zata ji sassauci cikin kabarin ta, though ta riga da yanke wa kanta cewar makomar ta ba mai kyau bace, sannan wannan hukunci da za'a yi mata yanzu ba hukunci bane hukunci sai taje cikin kabarin ta inda zata tadda babu kowa sai ita sai kuma halayen ta be it masu kyau ne koh munana.

Murya taji an bada umarnin a aiwatar da hukunci, nan fah ta sake ruɗewa har dasu sakin fitsari mai zafi da zawo a wando tsabar tsoron mutuwa da tsoron abinda zata tarar a rayuwar da zatayi har abada babu mutuwa nangaba, bata ankare ba taji a ɗaure mata hannaye ta baya an rufa mata baƙar hula akan fuska tare da saƙala mata igiya a wuya.

Kalmar shahada malamin dake kusa da ita ke bata amma inaaa Hafeezah koh jinsa bata yi tsabar fargaba da tsoron da ya rufe ta ga kuma harshen ta da yayi mugun nauyi, babu abinda take sai ihu kamar zata shiɗe tana kiran sunan mai Martaba da ƴaƴan ta musamman YAZEED akan ya taimake ta gasu nan zasu kashe ta, haka wannan malamin ya kyale ta yaja gefe, matse mata igiyar akayi a wuya, tare da ɗaura ta kan wani dogon abu, hankalin kowa da kowa ne ya dawo filin ya ɗau tsit babu abinda kakeji sai ihu da shewar Hafeezah, bata ankare ba kuwa aka ja igiyar dake rataye da wuyar ta sama kafin a tunkuɗe abinda ƙafafun ta ke kai, take filin ya ɗauki sautin *ALLAHU AKBAR* babu ƙaƙƙautawa, shure-shure Hafeezah tayi tayi tana ciccila ƙafafu a haka har ta gama ƙafafun suka saki haka ma jikin ta da alamu dai rai yayi halin sa.

Wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya sarki ya saki yana sadda kai ƙasa, wasu 6oyayyun hawaye ne suka zubo masa jikin sa yayi bala'in sanƴi, da kyar ya iya miƙewa ya tashi ya bar wurin a sanƴaƴe fadawan sa na mara masa baya.

B'angaren YAZEED kuwa jin ƙuwa da tashin sautin *Allahu Akbar* ya tabbatar masa da cewa an yankewa mahaifiyar sa hukunci.

Zamewa yayi ya zauna daga tsayen da yake wasu irin hawaye masu zafi na tsiyayo masa, riƙe kansa dake barazanar 6allewa yayi da hannu bibbiyu yana tsoron irin makomar da mahaifiyar sa zata tarar, a haka ya wuni cikin ɗakin ba tare da ya fita koh da jana'izarta bane ba.


*BAYAN SATI ƊAYA*


________Har izuwa wannan lokaci basu gama fita daga cikin shock ba dukda kuwa Hafeezah mai laifi ce a wurin su amma hakan bai hana jikin su gabaɗaya yin sanƴi ba da rashin ganin ta cikin su ba.

Sosai YAZEED ke ƙoƙarin yakice abinda ya faru da ita daga cikin zuciyar sa, koh kaɗan baya son tunano ta sai dai kuma a kullum baya gajiya da yi mata addu'a da kuma nema mata sassauci wurin Ubangiji.

ZEEYAD ma hakan take a wurin sa, gabaɗaya ya rasa meke yi masa daɗi, zuciyar sa cike take da jimamin mutuwar Hafeezah ga kuma tausayin ɗan uwansa da ya cika masa zuciya, though a kullum DEENAH na iya ƙoƙarin ta na ganin ta kwantar masa da hankali, sai dai hankalin nasa yaƙi kwanciya dan kuwa tun bayan yankewa Hafeezah hukunci bai sake sanƴa YAZEED ɗin a idanu ba, he just do hope yana cikin ƙoshin lafiya ga kuma dama bai gama warkewa har chan ba.

A haka rayuwa ta cigaba da tafiya, cikin watanni biyu kowa ya mance da wata Hafeezah inda suka tsiro da sabuwar rayuwa mai cike da so da ƙaunar juna abin gwanin ban sha'awa.

Rahinah yafiyar JALILAH da kowa ta nema cikin fadar akan gur6atattun halayen ta a garesu, nan kuwa duk kowa ya kar6e ta tare da nuna mata babu komai.

Ayaan kuwa sake yanke hannun sa likitoci sukayi inda akayi masa aiki aka sanƴa masa ta roba, shima yayi nadamar halayen sa sannan ya nemi yafiyar kowa da kowa musamman ma DEENAH da ZEEYAD.

Cikin wannan shekarar duk suka jesu aikin Umarah dan sake roƙon zaman lafiya mai ɗorewa da farin ciki a wannan ahalin nasu.

Sosai suke gudanar da zaman lafiya mai cike da ƙauna a wannan family ɗin.

DEENAH da ZEEYAD kuwa Nigeria suka zo tare da kawowa su Umma ziyara, sosai da sosai Umma, Jafar, Mami, Anty Khadija wacce itama auren ta ya kusa dama kuma Amirah da mahaifin su sukaji daɗin wannan ziyara ganin yadda DEENAH ta zama wata fresh da ita gwanin ban sha'awa ga kuma little ZEEYAD mai kama da mahaifin sa wanda a halin yanzu yake da shekara ɗaya da ƴan watanni.

Sati biyu sukayi wa su Umma suka koma Egypt, inda kuma anan ne suka cigaba da gudanar da rayuwar farin ciki.

Cikin wata shekarar da ta zagayo mai Martaba ya sauƙa ya baiwa ZEEYAD mulki dan kuwa a cewar sa ya gaji da mulkin haka shima yana buƙatar hutu, ai kuwa an samu adalin sarki mai kwazo wanda kuma yafi mahaifin sa iya aiki da tafiyar da mulki, sosai jama'a ke jin daɗin mulkin sa, cikin shekaru biyu ya dawo da wannan ƙasa abar kwatance a ƙasashen duniya baki ɗaya.

Su DEENAH kuwa an sake murjewa an zama manƴan mata kuma Sarauniya, farin ciki gun wannan ahali ba'a cewa komai.

A yanzu su YAZEED ma na da ɗansu mai shekara ɗaya, Grandma kuwa ta sake tsufa amma har yanzu da sauran ƙarfin ta, sosai takejin farin cikin kasancewa cikin ahalin ta.


*5 YEARS LATER*

_____Abubuwa da dama sun faru cikin wannan shekaru, ciki kuwa harda mutuwar Grandma da mai Martaba, sosai sukayi baƙin ciki da mutuwar wadannan mutane biyu mafi soyuwa a garesu daga ƙarshe dai sun wallafa Allah komai inda suka cigaba da yi musu adduar samun rahamar Ubangiji a kullum.

Yau ma kamar kowacce ƙarshen wata su kan haɗa family re-union dan ganawa da dangi dama kuma abokan arziki.

Wurin hutu ne ƙato cikin MASARAUTA wanda daga gani kai kasan special ne wurin ba kowa ne ake bari yake ma ra6ar arear wurin ba, sosai tsari dama kuma gine-ginen cikin MASARAUTAR suka canza da alama dai ba ƙaramin cigaba ake samu kullum ba, ga kuma yadda Bodyguards ke zagaye da wurin kowanne hannun sa riƙe da bindiga.

Kyau da tsaruwar wurin hutun ba zai faɗu a baki ba, daga nesa daga ciki kuwa na hango su zazzaune kan manƴa-manƴan darduma masu kyau na alfarma, duba na na maida gun wasu dattijai dake zaune suma nasu wurin daban, kallo na ƙare musu tsaf Abdulhakeem, Abhi, mahaifiyar Sadeeq, mahaifiyar Jalilah dama kuma Sarauniya Nazeerah ne zaune gaban su kuwa abubuwan more rayuwa ne kala-kala suna ci suna ɗan ta6a hira cike da nishaɗi.

Maida duba na nayi kan dardumar dake tsakiya wanda ya kasance wasu irin kyawawan yara ne akai wanda aƙalla zasu kai su goma koh ɗan ƙasa da haka gwanin ban sha'awa kamar dai ka sace su ka arce, kundai san yaran larabawa da shegen shiga rai😝, sannan manƴan cikin su ba zasu wuci 13yrs ba, suma wasan su suke duk fuskokin su ɗauke da walwala except yaro ɗaya wanda duk ciki shine kyakkyawan cikin su fuskar nan tasa a matuƙar ɗinke yaja gefe ɗaya ya zauna yana gungunai tare da aikawa da sauran yaran kallo cike da haushin su.

Daga ɗayan gefen kuwa su ZEEYAD, DEENAH, YAZEED, JALILAH, Sadeeq wanda Rahinah ce matar sa yanzu, Ayaan, Sooraj da wata budurwa a gefen sa wacce da alama dai matar sa ce, sai kuma ƴaƴan Nazeerah mata Layla, Raudat dama kuma mazajen su, sune duk zazzaune da ka gansu kasan kwanciyar hankali da jindaɗi ta zauna musu kowannen su fuskar su ɗauke da fara'a suna hira suna cin abubuwan dake jibge kaca-kaca a gaban su.

Ɗaya daga cikin yaran wanda ba zai wuci shekaru huɗu bane yayi masa gwalo hannun sa riƙe da wata kyakkyawar yarinƴa da ba zata wuci watanni bakwai da rabi ba sai lagwaigwaya ta yake wai shi a hakan riƙon ta yayi da kyau.

A fusace yaron farkon wanda ba zai wuci 7yrs ba ya iyo kansa kafin ya shiga jan yarinƴar a hannun sa, ihu ɗayan ya fara yana faɗin ya sake masa ƙanwar sa ai batason sa ne yasa bataje wurin sa ba.

Shi kuwa ɗayan in banda huci babu abinda yakeyi daga ƙarshe dai yayi nasarar kwace yarinƴar daga hannun sa yana rungume ta a jikin shi, Kuka ɗayan ya fashe dashi ganin yafi ƙarfin sa ya kwace masa ƙanwar sa.

Hankalin mutanen wurin ne ya dawo gun su, DEENAH da suma tasu wurin zaman daban miƙewa tayi a fusace tare da faɗin "Abyad."

Juyowa yaron yayi yana kallon ta bar yanzu yana nan rungume da yarinƴar sai huci yake da alama dai zuciya ne dashi.

Ƙarasawa wurin mai kukan tayi tana tayar dashi tsaye kafin ta shiga share masa hawaye tana bashi haƙuri.

"Ummie ai shine ya kwace Ummu-kulsum a wuri na" cewar yaron yana nuna inda Abyad ke tsaye.

"Shushh, kayi shiru haka kaji?, zanyi maganin sa itama yanzu zan kwace ta sai hankalin ka ya kwanta koh?."

Kai ya jinjina mata yanajin daɗi a zuciyar sa.

Ƙarasawa tayi gun Abyad kafin ta sanƴa hannu tana amsar Kulsum a hannun shi, da yatsa ta nuna sa kafin tace "I warned you several times akan yawan zuciyar ka amma baka ji, daga yau ba zaka sake ta6a kulsum ba, kana sonta amma kuma kullum kana cikin faɗa da yayan ta tayaya itama zata ji daɗi ta soka idan taga kullum kana cikin faɗa da yayan ta, eh?."

Shiru yayi yana kallon ta kafin ya buɗi baki kamar wanda bayason maganar yace "But he is hurting her bai iya riƙe ta ba."

"Just do as i asked you to."

"Ba zan ƙara faɗa dashi ba indai Kulsum zata soni akan hakan."

Murmushi tayi tana basa peck a kumatun sa tace "Good Boy maza kaje ka rungumi Zaid ku shirya yanzun nan."

Kamar yadda ta umarce sa ya ƙarasa gaban Zaid yace "Am so sorry Zaid, ka yafemin kaji?."

Kai Zaid ya jinjina masa kafin kuma su rungumi juna cike da farin ciki.

Murmushi duk mutanen wurin sukayi, juyawa tayi tana komawa wurin zaman ta, Kulsum hango Ummien ta ya sanƴa ta fara yayyarfa mata hannu alamun ta ɗauke ta, murmushi JALILAH tayi tana amsar ta daga wurin DEENAH.

Cikin raɗa ZEEYAD yace da DEENAH "I wonder why your Son yake da zuciya haka."

Murguɗa masa baki tayi tace "Kaji ka da wani magana, halin ka ya ɗauko, which means a gunka ya ɗauko komai ma."

Murmushi yayi yace "Do you think the Boy is in love?."

Wani irin kallo tayi masa kafin tace "Mai kake faɗa ne haka?, mai ma ya sani he is just fond of Kulsum shine kawai."

Ɗinke bakin sa yayi tare da yin shiru

Please Login or Register in order to submit comment