Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa ta koh ina, sosai sukayi masa lilis kafin ya basu umarnin dakatawa.



ZEEYAD dake kwance duk yabi ya galabaita dakyar yake iya motsa ƴar yatsar sa ne ya ɗago dan ganin koh wanene.



Durƙushewa ɗan Saurayin yayi wanda ba zai wuce sa'ar sa ba yayi yace "Hello Bro, long time no see."



"You.." ya faɗa cikin maida numfashi.



Murmushi ɗan Saurayin nan yayi kafin kuma ya damƙo gashin ZEEYAD ɗin yana zaunar dashi tare da kallon saitin idanun sa yace "Kai har ka isa, who the fuck do you think you are da har mahaifina zaiyi maka kyautar kaya na ka ƙona right infront of him?."



Shiru ZEEYAD yayi bai iya tanka masa ba inda kuma yake ta fitar da numfashin wahala yana runtse idanun sa cike da azabar da yakeji a jikin sa.



"Sooraj let go of him" ta faɗa tana zuwa ta ture shi daga riƙon da yayiwa ZEEYAD ɗin, kafin kuma ta ɗago da ZEEYAD ɗin tana shafa fuskar sa cikin kuka.



Daddagewa yayi tare da kwashe ta da wani irin azababben marin da sai da ya sanƴa ta ganin wasu irin taurari masu tsananin haske yace "Dan Ubanki mai ya kawo ki nan?."



Riƙe da ƙunci cikin kuka tace "Ai dama nasan zaka zo nan wurin tunda naji abinda Abhi ya faɗa maka akan ZEEYAD nasan sai ka biyo sa kayi masa illa, maiyasa wai ku bakuda imani ne?."



Kallo ya ƙare mata sama da ƙasa kafin ya ɗago ta tsaye yace "Ni kike faɗawa haka akan wannan bolan?, how the hell ma aka barki kika fito bayan ɗakin ki a rufe?."



"Eh ɗin na faɗamaka ɗin, mugu kawai azzalumi kuma wallahi sai kunyi nadamar abinda kukeyi masa dukkan ku."



Wani marin ya sake ɗebe ta dashi wanda ya sanƴa ta zubewa a wurin, nan ya kalli dogaran da yake tafe dasu yace "Ku sake yi masa dukan da yafi wanda kukayi masa yanzu, dukan da zai sanƴa sa guduwa da ƙafafuwan sa da zaran yaga dosowar wani daga cikin Family ɗin mu."



Ai kuwa kamar jira suke nan suka ha bugun sa da ƙafafuwan su, ita kuwa yarinƴar nan babu abinda takeyi sai kuka da ihun su sake shi inda yayan nata kuma ya riƙe ta gam yanajin wani irin tululun baƙin ciki ya tokare masa zuci, babu abinda yake fitarwa sai huci.



Sai da suka tabbatar da ya daina motsawa kafin su kyale shi, tusa ta gaba yayi yana janta suka bar wurin.



Barin su wurin keda wuya bayi matan dake harkokin su a wurin suka zo suka zagaye shi kowa na magana ƙasa-ƙasa suna tofa albarkacin bakin su "Ya mutu fah", "baya motsi", "Uhm nikam kunga tafiya ta", "Allah ya kyauta,lallai akwai hisabi ranar ƙiyama" Shine abinda wasu daga cikin su ke ta faɗa kafin duk su fara watsewa ɗaɗɗaya kowace na kama gaban ta...........




***************



........."Abhi! Abhi!! Abhi!!?" yake ta ƙira da ƙarfi kamar zai kai wa na gaban sa duka hannun sa damƙe da na ƙanwar tasa da har yanzu bata bar kuka ba.



Wata kyakyawar mata ce ta fito daga wani lungu wacce da alama ita ɗin Mahaifiyar su ce tana faɗin "Lafiya kake kwalawa mahaifin ka kira haka kamar wanda zaka tashi sama?."



Tura ƙanwar tasa yayi tana faɗawa jikin mahaifiyar tasu yace "Wannan shashashar ƴar taki mana da take neman zubar mana da mutunci a idon bayi."



"Mai kuma ta aikata wannan karon?."



Nan ya kwashe abinda ya faru ya faɗa mata, ai kuwa batayi wata-wata ba ta kwashe ta da mari tare da ture ta daga jikin ta tace "Ni zaki jawowa abin kunƴa da zubar mutunci a idanun matan gidan nan, miye akayi akayi wancan banzan ZEEYAD ɗin da har zaki dinga tada hankali a kansa, kin kuwa san mai kike neman jawo mana?, Mutuniyar banza da wofi wacce batasan mai takeyi ba."


"Ummie, ya akayi ma kika barta ta fita waje?, i swear idan na sake kama yarinƴar nan ta kira sunan wancen ƙasƙantaccen koh da da wasa ne nothing would Stop me from killing her."



A razane Mahaifiyar ta ɗago tana kallon Sooraj ɗin dan kuwa yadda yayi maganar ya nuna tabbatuwar zai iya aikata hakan dagaske, dan kuwa sam yaron bai san wani abu wai shi imani koh Tausayi ba, tun yana ƙarami yake da wani irin baƙin mugunta koh da yake girma sake ƙaruwa yakeyi, ga kuma baƙin ciki da hassada dan kuwa a cewar sa sune yakamata su zamto masu mulkar ƙasar Cairo ba Sarki Abbas ba, burin sa a kullum shine sarki Abbas ya mutu mulki ya dawo 6angaren su.



Kallon Yarinƴar tayi tare da jan hannun ta tayi ciki da ita, zaunar da ita tayi tare da nuna ta da yatsa tace "Jalilah kin dai san yayan ki baisan tausayi ba koh?, sannan kullum ƙara girma yake muguntar sa na daɗa ƙaruwa, ina mai gargaɗin ki da ki fitar da wannan yaron ZEEYAD a zuciyar ki idan ba haka ba ni babu ruwa na da dukkanin abinda zai same ki."



Cikin kuka tace "Amma Ummie laifin mai ya aikata haka da sai ayi ta muzguna masa kullum?, kuma ai shine ɗan sarki babba amma aka tauye masa wannan hakkin..."



Saurin rufe mata baki tayi tace "Shhh, koh da wasa kada ki kuskura ki bar wannan zancen ya sake fitowa daga bakin ki, idan ba haka ba daga ni har ke mun mutu kenan ranar, ki share hawayen ki yanzu haka nan kinji, sannan ki bar tunanin yaron chan kin dai san halin mahaifin ku" ta faɗa tana goge mata hawaye.



"Ki tashi yanzu zan turomiki kuyangun ki suzo suyi miki wanka sannan su kawo miki abinci kici."



Kai ta jinjina kawai kafin mahaifiyar tasu ta fice.



"Ina fatan dai kin gargaɗi ƴarki?" cewar Abdulhakeem dake zaune kan wata doguwar kujera yayi naƙe-naƙe a kai inda kuma Sooraj ke zaune ta gefen sa sai hura hanci yake.



Kai ta jinjina masa cike da girmamawa tayi wucewar ta, da kallo yabi ta kafin yace "Yarinƴar nan sam bata ɗebo halina ba shiyasa take tausayin wancan yaron, amma nan ba da daɗewa ba zanyi maganin ta."



Murmushi Sooraj yayi yace "Abhi indai kana dani nikuma nayi alƙawarin yin dukkanin yadda zanyi dan ganin mulkin nan ta dawo hannun mu."



Dariya Abdulhakeem ya kwashe dashi cike da alfaharin halin irin na ɗan nasa yace "Shiyasa nake matuƙar ƙaunar ka fiye da kowa.".............




*********



.......Haka nan yake yashe anan wurin ba tare da ya sake motsi ba har hadari baƙiƙirin ya haɗu ruwa mai ƙarfi ya sauƙo.



A kansa aka ƙare ruwan tass har mutane suka fara fitowa dan cigaba da harkokin gaban su ZEEYAD bai farka ba.



Sai dai kuma ganin babu wanda ya damu dashi ya sanƴa kowace jan bakin ta tayi shiru ba tare da sun iya kai ƙarar abinda ya faru ba, dan kuwa sun san babu wani mataki da za'a ɗauka a kai.



Yatsar sa ce ta fara motsawa kafin kuma yaja wani irin dogon numfashi yana ware idanun sa da sukayi matuƙar yin jaa sosai.



Yunƙurawa yayi ya miƙe zaune kamar kuma wanda aka tsikara ya tashi tsaye cikin tangaɗi ya ƙarasa bakin ɗakin sa da ruwa ya shiga yayi masa gyara, zubewa yayi tsugunne kan guiwowin sa wasu irin zafafan hawaye suka shiga kwaranƴo masa, kafin kuma ya sanƴa wani irin ihu da ƙarfin gaske ya shiga buga kansa da hannayen sa.



Sai da yayi mai isarsa kafin ya tsagaita, nan ya wuce cikin ɗakin nasa ya hau dube-dube, hannu ya kai wuyar sa nan yaji sarƙar tana nan, wata nannauyar ajiyar zuciya ya sauƙe yana sumbatar ta kafin kuma ya fito ya kama bin hanƴar ficewa daga Masarautar kamar ba shine wanda yasha jinƴa cikin dare kuma akayi masa dukan mutuwa ba dan kuwa da ƙarfin sa yake tafiya.



Duk inda yabi kuwa da kallo ake binsa ganin yadda yayi jina-jina kamar wanda yayi faɗa da kura, babu inda ya nufa sai gidan su abokin sa Sadeeq, tundaga nesa ya hango sa yana zuwa hakan ya sanƴa shi zuwa ya taro sa da sauri ganin jikin sa.



"ZEEYAD, mai ya sameka haka, waye yayi maka wannan aika-aikar?."



"Ina Abhi?" kawai ya faɗa yana janƴe jikin sa daga riƙon da Sadeeq ɗin yayi masa.



"Abhi yana cikin gida, lafiya, mai ya sameka ne haka ina tambayar ka?."



Bai kula Sadeeq ba ya nufi cikin gidan nasu, Abhi dake zaune baisan sadda ya miƙe tsaye ba sakamakon ganin ZEEYAD da kuma halin da yake ciki da yayi.



Zuwa ZEEYAD yayi wurin sa yace "Abhi ina buƙatar Takardun gama makaranta ta dake wurin ka."



"ZEEYAD...Maiyasame ka haka?."



"Babu, ina buƙatar takardu da na baka ajiya ne."



Kallon sa kawai Abhi ɗin ya tsaya yi na wasu daƙiƙu kafin kuma ya shiga wani ɗaki ya ɗan daɗe a ciki kafin ya fito ɗauke da wata jaka a hannun sa "Gasu nan" ya faɗa yana miƙawa ZEEYAD ɗin.



Amsa yayi ya buɗe ta nan yaga komai ya cika kafin ya rufe ta yana rataya ta a kafaɗar sa.


Duk idanu suke binsa dashi kafin yace "Am living, zan bar musu ƙasar su tun kafin suga baya na na rasa damar ɗaukar fansar abinda sukayi min, i will never give up in this life, dole ne nima na zamto mutum mai daraja ba kamar yadda suka ɗauke ni ba..." kafin ya ƙarasa Abhi yayi saurin faɗin "Ina kake tunanin zakaje, wa kake tunanin zai kar6e ka ya mutunta ka a wani yanki chan daban da babu wanda ya san ka?."


"I don't care whether za'a mutunta ni a kar6e ni, all i know is that dama chan babu mai ganin daraja ta, ba zai dame ni ba dan wasu daban da bansaniba basu mutunta ni ba sabida bansan hakan ba tun farko sabida, ba'a koyamin ba, please Abhi ina roƙon ka kada ka hana ni yin tafiyar nan sabida shine kaɗai kwanciyar hankali na."



Shiru Abhi yayi yana kallon sa kafin kuma ya numfasa yace "ZEEYAD ɗa na, ba zan hana ka yin tafiyar nan ba tunda haka kakeso, sai dai inaso ka sani kada ka ta6a manta cewa kana cikin jarabawar Ubangiji ne, sannan kuma kada ka ta6a tunanin Allah baya sonka shiyasa ya sanƴa ka cikin wannan hali, kada ka manta da cewa Allah yana jarabtar bayin sa da yakeso ne ta hanƴa daban-daban, sannan kuma bakomai zai sanƴa ka cin wannan jarabawa ba face haƙuri, kayi haƙuri ZEEYAD, kayi haƙuri da yadda rayuwa tazo maka, babu tantama watarana zaka ci ribar sa" ya faɗa yana shigewa cikin ɗakin sa kafin kuma ya fito hannun sa ɗauke da kuɗi yace "Ungo wannan kuɗin ka sashi a jikin ka, zaka iya cin abinci dashi a hanƴa."



Kai ya girgiza yace "No Abhi, ba zan amshi kuɗin ka ba, sabida i don't need anyone's support to build myself up, ni da kaina zan gina kaina da gumi na bana buƙatar taimakon kowa, kuma ƴunwa ai na saba da ita koh ka manta ne nakan shafe kusan kwanaki uku ba tare da na sanƴa abinci a baki na ba face ruwa?, ƴunwa ba damuwata bace ba dan kuwa na saba da ita."



Shiru kawai Abhi yayi yana kallon sa ba tare da ya iya cewa komai ba.



"ZEEYAD, ina goyon bayan ka, na san kai mutum ne mai ƙoƙari da nagarta nasan zakayi dukkanin yadda zakayi dan ganin ka inganta rayuwar ka ba tare da taimakon kowa ba, amma dan Allah ZEEYAD inaso kayi min wani alƙawari."



"Tell me" ya faɗa yana kallon Sadeeq ɗin.



"Inaso kayimin alƙawarin ba zaka canza amini ba, sannan kuma inaso kayimin alƙawarin komin daren daɗewa zaka dawo ƙasar ka ta haihuwa."



"Nayi maka alƙawarin ba zan canza amini ba, tayaya ma zan iya canza ka Sadeeq? idan nayi hakan na zama butulu, kai ne kaɗai baka guje ni ba lokacin da nake buƙatar aboki kuma ɗan uwa a rayuwa ta, ba zan ta6a mantawa da Family ɗinku ba sabida kunyi min gata, a gidan ku nake samu nakecin abinci wataran koh da banso hakan ba sai ka tilasta ni na ci, bakomai zai sanƴa ni dawowa nan ƙasar ba sai dan ku,kune babban dalilin da zai sanƴa na dawo."


Rungume juna sukayi shida Sadeeq ɗin na ƴan mintina kafin kuma su rabu kowanne na ƙoƙarin maida hawayen da yazo masa.



Abhi ne yace "ZEEYAD ɗa na inaso kayimin wannan alfarmar, mai zai hana ka bar tafiyar nan har sai gari yayi duhu sawun mutane sun fara ɗaukewa, kafin nan kuma ni zan je wurin wani tsohon aboki na wanda ya san inda ake ficewa daga ƙasar nan ta 6oyayyiyar hanƴa, zan sanƴa sa yayi maka jagora har zuwa inda zaka ba tare da an sami wata matsala ba."



Shiru ZEEYAD yayi bai ce komai ba alamun yana tunani,nan Sadeeq yace "Abhi yayi gaskiya ZEEYAD, fitar ka a yanzu ba ƙaramin haɗari bane dan kuwa idon kowa a kanka yake sannan da zaran an ganka da jaka dole ne a kai ƙarar an ganka zuwa MASARAUTA, daga nan kuma kaga komai ya kwa6e."



Kai ya jinjina alamun ya yarda nan duk suka saki murmushin farin ciki kafin Abhi yace "Sadeeq ka kar6i jakar sa, nikuma zanje wurin Abdulsalam na dawo kafin dare ya rufta" yana faɗin haka yaje ya hau keken sa mai bayan napep yana yi musu sallama ya fice.



Amsar jakar sa Sadeeq yayi yace "Ka zauna anan nikuma zan shiga wurin Ummie ta ɗaura maka ruwan zafin da zakayi wanka dashi, sannan na baka kaya na ka sa ka cire wannan na jikin naka, zan kawo maka magani ma sabida naga kamar akwai zazza6i a jikin ka."



Kai kawai ya jinjina masa yana zama kan tabarmar kabar dake shimfiɗe a wurin.



Ruwan zafi dayawa aka dafa masa wanda zai gasa ciwon jikin sa dashi dama kuma wanda zaiyi wanka dashi.



Wanka yayi Sadeeq ya basa kayan sa sabo ya sanƴa, sannan ya amso masa abinci da ruwan sha a wurin Ummie, tare da maganin zazza6i.



Sosai ZEEYAD yaji daɗin jikin sa dan kuwa har bacci sai da yayi, sallah ce kawai ke tada shi, har Abhi ya dawo daga wurin abokin nasa.



Da misalin ƙarfe sha ɗayan dare bayan sawun mutane ya fara ɗaukewa ne suka fito da Abhi, ZEEYAD da kuma Sadeeq inda hannun Sadeeq ɗin ke riƙe da wata ƴar madaidaiciyar jaka.



Tafiya mai nisan gaske sukayi kafin su iso inda zasu ɗin, kai tsaye suka shige gidan inda yake kama da garage.



Mutane ne birjik Zazzaune kowanne da jakar kayan sa a gaban sa.


Abokin Abhi ne ya taho nan sukayi sallama kafin Abhi ya gabatar masa da ZEEYAD a matsayin wanda zaiyi tafiyar.



"Masha Allah naji daɗi da kukazo akan lokaci dan kuwa ƙarfe ɗaya motar mu ke tashi."


Murmushi Abhi yayi yace "Nagode sosai abokina Abdulsalam, Allah ya biyaka da alkhairin sa."



"Babu komai abokina Mas'ud duk yiwa kaine, nima bansaniba koh watarana zan iya zuwa neman wani taimako daga gareka ba, ai ka taimaki wani kai ma Allah zai taimake ka, gashi chan yaje yabi layin chan kafin mu fara shirin tafiya" ya faɗa yana nuna musu gefen da wasu matasa dama kuma manƴan mutane ke zaune.


"Insha Allah" cewar Abhi kafin ya juya ga Sadeeq yace "Sadeeq ka bashi jakar, ZEEYAD wannan jakar abinci ne na leda wanda baya 6aci dama kuma ruwa wanda abokin ka ya tanada maka shi, dukda banida tabbacin zai isheka kafin ku ƙarasa inda zaku amma nasan zai rage maka wani abin, dan Allah kada ka ƙi amsa kaji?."



"ZEEYAD, dan Allah ka amsa kyauta ce daga gareni a matsayi na na aminin ka."



Kai ya jinjina tare da amsar jakar ya goya a bayan sa yace "Nagode muku, Allah ya bani ikon da zan biya ku da abinda kukayi min na alkhairi a rayuwa" ya faɗa tare da goge hawayen da suka zubo masa.



Announcing aka fara kan kowa ya fara shirin shiga mota, nan fah duk suka miƙe kowa ya fara kokuwar shiga maza da mata da kayayyakin su, wasu da iyalan su wasu kuma su kaɗai inda mafi yawa masu kasuwanci sunfi yawa, sai dai tsabar son banza irin tasu ba zasu iya biyan kuɗin jirgi suyi tafiyar su cikin kwanciyar hankali ba sai sun bi ta 6oyayyiyar hanƴa.



Abokin Abhi ne ya dawo yace "Aboki na Mas'ud, na tanadar wa ɗanka wurin zama mai kyau inda zai sake dashi da kayan sa, ku biyo ni muje mu."



Motoci ne trailers manƴa irin na kwasar shanaye guda huɗu inda kuma saman su yake rufe da tent, ɗaya daga cikin motocin ya kai su inda ZEEYAD ya shiga ya samu wurin zama mai kyau da kayan sa, dukda kuwa babu shimfiɗa sai dai hakan ba damuwar sa bace tunda baya cikin matsi kuma bai saba kwanciya kan abu mai laushi ba.



Hannu suka shiga yiwa juna waving dukkanin su kafin a maida tent ɗin a rufe, kafin a ɗauko sandar busassun karan dawa a lafta a kai ta yadda babu wanda zai san da cewa mutane aka ɗebo a ciki.



A gaban su Abhi motocin suka tashi kafin su rakasu da ido kowanne na share hawayen da ta zubo masa na tausayi.



Dafa kafaɗun Sadeeq yayi cikin kwantar masa da hankali kafin su koma inda suka fito.



ZEEYAD kuwa very Umcomfortable yakejin sa, ji yake kamar ya baro wani abu mai muhimmanci wanda baikamata ya baro sa ba a baya, sai dai ya kasa gane koh menene, zuciyar sa a cunkushe take ya kasa samun sukuni.


_"Why should i worry myself about him?, he always wants me out of his sight"_ ya faɗa a zuciyar sa bayan ya tuna mahaifin sa mai Martaba.



Da kallo yabi ƴan cikin motar wanda sam basuyi kama da ƴan cikin gari ba sunfi kama da wadanda suka fito daga ƙauye yayi sakamakon akwai hasken fitila a ciki, kafin ya sunkuyar tare da kafa kansa kan guiwowin sa yana tunanin wace iriyar rayuwa zaiyi a inda bai san kowa ba, uwa uba kuma sam bai san wace ƙasar suka dosa ba.



"Kai yaro kayi hattara dai da jakar ka, dan kuwa akwai masu sata, na faɗamaka hakan ne dan naga kamar wannan ne farkon tafiyar ka."



Ɗagowa yayi ya kalli dattijuwar matar kafin yace "Nagode" yana janƴo jakar zuwa jikin sa.



Shiru yayi kawai yana maida kansa, yana saurarar yadda motar ke ta jigila akan hanƴa wanda da alama ba kwalta suke bi ba.



Tsinkayo muryar wani yaro yayi yace "Abhi wace ƙasa zamuje wannan karon?, kuma naga bamuda yawa a cikin nan maiyasa?."



"Ai wannan karon inaso muyi tafiya cikin kwanciyar hankali ne, shiyasa na za6i na biya kuɗi dayawa dan mu samu gurbin zama inda babu mutane dayawa, kaga zamu sake kuma mu wala."



Ɗagowa ZEEYAD yayi yana kallon su tare da tunanin dama kuɗi mai yawa Abhi ya cire ya bada dan kawai ya sami gurbin zama mai kyau?, muryar yaron yaji yana faɗin


"Eh, hakane toh ina zamuje?."



"Nigeria zamuje, dan kuwa naji ance ƙasa ce da Allah yayi musu arzikin kayan alatu da more rayuwa kala-kala, uwa uba kuma Kasuwanci da shine suka fi yi kuma muma shi zai kai mu chan, dan kuwa naji ance chan sunada kan kasuwanci sosai komai ka kasa na sayarwa zaka samu kasuwa sannan kuma basu cika raina kuɗi ba komin ƙanƙantar ta, wani abin ba sai na faɗa maka ba idan munje mu zaka gani da idanun ka."


Tunda ya fara magana ZEEYAD ya ɗago yana kallon sa, shi dai a iya ilimin da yake dashi kan ƙasashe yasan Nigeria tayi ƙaurin suna wurin kar6ar cin hancin da rashawa, uwa uba kuma insecurity da suke fama dashi ga kuma terrorist da suka sanƴa su gaba, kullum cikin kashe Al'ummar da basu ji ba basu gani ba ake, kenan wannan ƙasar za'a kai sa kenan yanzu?.



"Nigeria?" ya maimaita hakan..............





_Littafin ZEEYAD na kuɗi ne, kan Naira ɗari biyar kacal (500), VIP group masu son posting sau biyu a rana kuma duba ɗaya ne (1000), zaki yi payment ɗinki Via 1489237499, Muhammad Hauwa Gana, Access Bank, sannan ki turo da shaidar biyan ki ta wannan number 07061979284, banda VTU please, ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali_


```Kun tsorata koh?😠, Toh yaceen haka zakuji na faɗa a next page indai baku shararo min zazzafan comment ba😏```



*Kiyi sharing sabida Ƙaunar Allah da Annabi👏🏽*






*MHIZZ JIDDHERR...........✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*




*007...*





_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._




..............Tafiya mai nisan gaske sukayi dan kuwa sun kai awanni huɗu akan hanƴa kafin su iso inda zasu.



Nan duk motocin sukayi Parking kafin a fara bada umarnin fitowa.


Duk mutane ne suka fara fitowa,sai da kowa ya fita kafin ZEEYAD ya fito.



Ƙaton bakin ruwa ne wanda ke ɗauke da manƴan jiragen ruwa dayawa wasu sun fara tafiya wasu kuwa suna zuzzube a bakin ruwan ba'a fara tafiya ba.



Wannan Abokin Abhi ɗinnan ne yayi wa ZEEYAD jagora zuwa wurin wani daban, gefe suka ja suka ɗanyi magana kafin ya haɗa sa da ZEEYAD da ya zamto ɗan kallo a wannan wuri.



"Yaro wannan mutumin shine zaiyi maka jagora har zuwa inda zaku, duk wata buƙata taka ka tambaye sa zai yi maka ita bakada wata damuwa kaji?, ni zan koma inda na fito yanzu ka kula Allah Ubangiji ya sauƙe ku lafiya."



Kai ZEEYAD ya jinjina tare da furta "Aameen" sannan yabi bayan wannan mutumin nan zuwa cikin wani jirgi.



Ciki chan ƙasa suka shiga inda ya kasance kamar gida ne da ɗakuna a cikin sa harda falo da abubuwan da ba'a rasa ba na cikin manƴan jiragen ruwa.



Wani ɗaki ya kai ZEEYAD yace "Tafiyar nan zata ɗauke mu tsawon makonni biyu, dan haka anan ne zaka dinga kwana sai dai ba kai kaɗai bane da akwai wasu ƴan kwanan ma, idan kana da abin shimfiɗa ka shimfiɗa shi ta gefen chan ka kwanta sannan kuma kayi takatsantsan da jakar ka, idan kana buƙatar wani abu koh ƙarin bayani zaka iya samu na a waje" yana faɗin haka ya juya ya fice.



Da kallo ZEEYAD yabi ɗakin dashi, ɗaki ne shi ba ƙarami ba kuma ba babba ba ɗan madaidaici ne dai, inda kuma akwai tabarmai shimfiɗe wanda da alama akwai masu wurin.



Gefe ɗaya ya samu ya zauna yana rungume jakar sa a jiki, kafin kuma ya shiga tunanin iriyar rayuwar da zaije ya tarar achan wani wurin da koh mafarki da tunanin zuwa bai ta6a ba.



Maganar wannan mutumin da ta ɗansa ne ya faɗo masa rai, nan ya furta "Business?."



Wasu ne suka shigo ɗakin nan ya maida hankalin sa kansu, duk da kallo suka bisa kafin su sami wuri kan wani tabarma su zauna.



Ɗaya daga cikin su ne yace "Wai kowa ma ya waye ya gane da barin ƙasar sa yanzu zuwa wata, kai kuwa ɗan Saurayi mai zakaje yi a Nigeria, kuma daga ina kake?."



Shiru ZEEYAD yayi bai iya tanka musu ba, nan ɗayan yace "Kai ina ruwan ka ne dashi, ka sani koh rayuwa ce tayi masa zafi ya gudo?."


Haka nan suka cigaba da firar su yana jinsu bai tanka musu ba, sai ma ɗaukar jakar sa da yayi ya fice.



Wannan mutumin da ya kawo sa ɗakin ya shiga nema kasancewar da akwai mutane dayawa ya sanƴa sa samun sa da kyar.



ZEEYAD ne yace "Dan Allah, a'ina ne zan sami ruwa da abin sallah?."



Kallon sa mutumin yayi yace "Kana nufin kace bakazo da komai ba?, ai komai na nan wurin na saidawa ne da akwai masu saida duk abinda kakeso har a sauƙa, idanma canjin kuɗaɗen ka kakeso ayi maka zuwa na Nigeria duk akwai wadanda zasuyi maka, kaje ta bayan chan nan ne inda aka ware wurin

Please Login or Register in order to submit comment