Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai sun ɗanɗani guɗar su ne, yayi alƙawarin ba zai bar kowa ba, sannan kuma zaiyi mulkin da ba'a ta6a yin irin sa a ƙasar ba, bayason tunowa dasu shiyasa ya toshe dukkanin wata hanƴa da zai sanƴa sa yin kasuwanci da ƴan ƙasar kokuma yaji wani labari da ta shafi ƙasar, hakan yasa bayason kallon News dan gudun ma kada ya kalli wani abu game da ƙasar da zai sanƴa sa cikin damuwa ya hana shi sukuni, balle kuma ya tuna masa da cewa shi ɗin ɗan Sarki ne.

Hannun sa ya nausa akan steering ɗin idanun sa na matuƙar yin jaa sosai, fuskar sa ta canza launi zuwa jaa, sosai baƙin ciki da 6acin rai suka sake samun gurbin zama a cikin zuciyar sa.


Wacce yake tunanin zata zame masa waraka kuma wani daban takeso, wani chan daban da baikamata ace shi zata so ba, amma ta bar zuciyar ta ta rinjaye ta ta fara sonsa.

A haka yaja motar tasa ya bar cikin gidan zuwa gidan sa.


********************


Tsaye yayi a gaban ƙatuwar hoton ta da ya zana yanajin baƙin ciki sosai ganin ba shine zai mallaki DEENAH ba.

Zuciyar sa DEENAH takeso ba Khairat ba, sai dai sun kasa gane hakan, tayaya suke tunanin zai iya buɗar bakin sa yace musu wata daban yakeso ba ƴar su ba, bayan irin halarcin da sukayi masa a rayuwa?.


Sauƙe jajayen idanun sa yayi cikin nata yana kallo, maganganun da ta faɗa masa ne suka shiga dawo masa cikin kwakwalwa.

_"Am not lying, gaskiya nake faɗamaka, baka kai matsayin da zanyi maka ƙarya ba, idan ma kana tunanin inason ka ne yasa kullum kake bibiya ta then you're wrong, coz am inlove with someone else, and you know what?, yana da halaye masu kyau, sannan kuma ya tara dukkanin qualities ɗin da ake nema a wurin miji na gari, Unlike you da bakasan koh ɗaya daga cikin abubuwan nan ba, wanda bakada aiki sai kula matan banza sannan kuma kayi dukkanin abinda kaso dasu, kana tunanin ni irin matan nan ne da har zaka dinga bibiya ta dan kawai ka samu damar shawo kaina ka kuma yaudare ni da kalaman ka, ka cika mummunar manufar ka a kaina?"_


Zubewa yayi akan couch yana runtse idanun sa "Please don't do this to me" ya faɗa cikin rawar murya.


Wayarsa dake kan center table ce ta ɗau ringing ɗin da ya tsinkar masa da zuciya tare da faɗar masa da gaba.


Kallon wayar ya tsaya yi har ta tsinke bai iya ɗagawa ba.


Sosai yaji gaban sa na wani irin mummunar faɗuwa har wani kiran ya sake shigowa.

Hannu ya kai ya ɗau kiran yana kafawa a kunne.


Muryar Jafar yaji cikin kuka, hakan yasa shi miƙewa tsaye yace "Tell me."


Bansan mai Jafar ya faɗa masa ba, wanda ya sanƴa shi sakin wayar tasa a ƙasa glass ɗinta na tarwatse wa ba.


Sosai idanun sa sukayi jaa, kafin kuma jikin sa ya shiga rawa tsabar irin shock ɗin da ya shige sa.


Sosai ya girgiza da abinda kunnuwan sa suka jiye masa.


Da sauri ya maida duban sa kan ƙatuwar hoton DEENAH yana kallo, kafin kuma yayi hanƴar fita cikin tashin hankali ya fice daga cikin falon da gudu.


*************************


Tun da ZEEYAD ya tafi DEENAH ta kasa samun kwakwarar sukuni a zuciyar ta.

Sosai take tunanin sa haɗi da mafarkin sa a kullum.


Hankalin ta bai tashi ba sai da Jafar yace mata ZEEYAD is getting ENGAGED nan da 3days.


Sosai take rufe kanta a ɗaki ta sha kuka, ita kanta tasan ƙarya ne tace batason ZEEDAN.


Sosai soyayyar sa ke nuƙurƙusar mata da zuciya tana neman illatar da ita.


She can't believe mutumin da taso tun tana ƙarama turns out to be wata daban yake so ba ita ba.


Zuciyar ta koh kaɗan batason Abdul sai ZEEYAD, gashi rana guda yana neman su6uce mata.

Ganin da takeyi masa ne kaɗai yake sata jin nutsuwa a ranta, amma kuma batasan maiyasa take tsintar kanta da gayamasa maganganu marasa daɗi ba, sosai takejin zafi da haushin kanta a duk sadda ta faɗa masa magana marar daɗi.


Bakomai bane ya jawo hakan sai ganin sa da Surayya da tayi, shi ya 6ata komai, but koh da ace shi ɗin ya kasance mutumin banza kamar yadda take hasashe bata ta6a tunanin zuciyar ta zata daina son sa.


Tsaye take a gaban mirror tana ganin yadda ta faɗa sosai.

Jakar makarantar ta ta ɗauka, tana jin kamar ta fasa zuwa makarantar dan kuwa wani iri takejin ta yau ɗin, ga kuma zuciyar ta da bai bar tsinkewa ba wanda takejin hakan tun cikin dare.


Falo ta fito ta samu Umma zaune tana breakfast.


"Umma na tafi" ta faɗa.


Kallon ta Umma tayi tace "Ba zakiyi breakfast ɗin ba?."


"Na ƙoshi Umma, bana jin ƴunwa."


"Kin sha maganin ciwon kan kuwa?."


"Na sha Umma, ni zanyi latti bari na tafi."


"Toh shikenan,a dawo lafiya, Allah ya tsare hanƴa, ki tabbatar fah kinci abinci a makaranta."


"Insha Allah Umma" ta faɗa tana ficewa.


Adaidaita ta tara ya kaita makaranta ya sauƙe.


Lectures sukayi but duk hankalin ta baya kai har lecturer ɗin ya fice.


Ƙawayen ta da ta ɗan saba dasu cikin kwana biyun nan ne suka fita tare, sai da suka je sukayi sallah sai dai banda ita kafin su fito suje cafteria su sayi abinci.


Gida kawai takeson komawa sakamakon jin ta da take very nervous, tsikar jikin ta na tashi, tanajin wani irin strange feeling tattare da ita.


Bata bisu sun koma class ba ta kama hanƴar gida.


A hankali take tafiya har ta fice daga cikin school ɗin.


Idanun ta ne suka hango mata mai saida agwaluma ta chan tsallaken titi sai feshe ta yake da ruwa a cikin gora, gasu fresh dasu.


Murmushi tayi tare da jiran motocin dake kan kwaltar su ragu.


DEENAH nada tsoron tsallake kwalta musamman ma wannan dayake high way, shiyasa duk tsoro ya kama ta takejin kamar ta fasa sayan agwalumar.


Hango sa da tayi yana shirin jan kuskus ɗin sa ya bar wurin ne yasa ta sanƴa ƙafar ta kan kwaltar tana shirin tsallakawa da gudu.


Horn ɗin wani mota da batasan da zuwar sa bane ya gigitar da ita, kamar kuma wacce aka ɗaurewa ƙafafu haka ta kasa motsa ƙafar ta ta tsaya tana kallon ƙatuwar motar.

Within a blink of an eye kafin kuma tace zata sake motsa ƙafar ta motar nan har ta iso ta tare kwashe ta yayi sama da ita.


Burki motar taja da ƙarfin tsiya kafin kuma ya sake jin ƙarar sauƙar abu a gaban glass ɗin motar tasa, inda jini ya wanke masa shi.


Take kuma ta sake gangarowa ta faɗo ƙasa.


Babu abinda kakeji sai muryar mutane na nanata kalmar "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un."


A matuƙar firgice mai tuƙin motar ya fito hannayen sa akai shima yana nanata "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un."


Kan kace miye kuma mutane sun taru akanta, babu abinda kake ji sai salallami da hayaniya.

Ɗaukar ta akayi fuskar ta da aka rufe da farar Hijabin ta yayi matuƙar 6aci da jini, haka ma kayan jikin ta.


Mota aka samu aka sanƴa ta sannan kuma akayi asibiti da ita, inda wasu suka wuce nearest police station dake wurin dan sanar da faruwar lamarin.


Koh da aka kaita asibiti kasancewar akwai ƴan sanda tare dasu yasa akayi saurin admitting ɗinta.


ICU shine abinda aka rubuta a samar ɗakin da aka shigar da ita.

Jakar makarantar ta aka bincika koh za'a samo wani clue ɗin inda take da zama.


Wayar ta suka ciro nan dai suka ga babu security, kai tsaye kuma Contacts suka shiga.


*BLOOD🩸💦❤️* shine abinda suka ga anyi saving numbern da akayi last kira dashi, kafin kuma su danna dialing numbern.


Bugu biyu Jafar ya ɗaga tare da yin sallama yace "Sis?."


"Assalamu Alaikum" cewar police.

"Wa'alaikumusalam" Jafar ya amsa muryar sa na nuna alamun ɗan mamaki.


"Kai ɗan uwan mai wannan wayar ne?."


"Eh ɗan uwanta ne, maiyafaru ta jefar da wayar ne?."


"A'a ba jefar da wayar tayi ba, ta samu hatsari ne a hanƴar ta ta zuwa makaranta, she was knocked down by a truck."


"Inalillahi wa inna ilaihi raji'un, DEENAH, wane hali take ciki yanzu, tana ina yanzu?" ya faɗa cikin tashin hankali.


"Zaka iya zuwa nan general hospital..."

Tun bai idda ba Jafar ya katse kiran, kafin kuma cike da tashin hankali ya baro office dan zuwa asibitin.


A hanƴa ya kira Umma akan ta same shi a asibiti sai dai bai faɗa mata abin dake faruwa ba, hakan yasa ita ma hankalin ta yayi mummunar tashi ta baro wurin aikin ta.


*******************


Safa da marwa kawai sukeyi a gaban ƙofar ICU ɗin, Umma inbanda kuka babu abinda takeyi, shi kansa Jafar kawai daurewa yakeyi amma ya kasa rarrashin Ummar tasu.


Gashi tunda suka zo kusan awanni uku kenan ba'a bar su sun shiga ba, likitocin ma basu bari sunyi musu magana ba.


Waya ya ɗauka ya kira ZEEDAN tare da shaida masa abin dake faruwa ba tare da ya iya controlling kukan da yazo masa ba.


******************

Su Umma na zaune jugum har dare sallah ne kaɗai ke tada su, kamar daga sama suka ga ZEEYAD ya faɗo.


Da sauri Jafar ya nufe shi nan ya riƙo Jafar yace "How is she, tana ina yanzu?."


Ƙofar ICU ɗin kawai yayi masa nuni, ba tare da kuma ya jira cewar sa ba ya nufi ƙofar ya buɗe ta tare da shigewa ciki.


Duk da kallo su Umma da Jafar suka bisa Umma na tashi tsaye.


Turus yaja ya tsaya ƙafafuwan sa na neman gaza ɗaukar sa.


DEENAH ce kwance bata numfashi kanta ya sha ɗauri da farin Bandage an sanƴa mata irin abinda ake sawa patience ɗinda suka samu karaya a wuyar su, ga kuma abin shaƙar numfashi dake manne a hancin ta, injinan dake zagaye da ita suna taimaka mata wurin inganta lafiyar ta kuwa ba'a magana.


"Ma..MADEENAH?" ya kira sunan ta a hankali.


Takawa ya fara zuwa wurin ta likitocin sukayi saurin riƙe shi.


Cike da 6acin rai yace "Let go of me" yana fuzgewa.


Cakumo wuyar ɗaya daga cikin su yayi yace "Don't...don't let her die..."

"Koma miye matsayin ka a wurin ta yakamata ka fita yanzu bamu gama aikin da mukeyi akanta ba tukun, we can't save her life muddin bamu samu nutsuwar yin hakan ba" cewar ɗaya daga cikin su.


Cika wanda ya cakume ɗin yayi yace "Yes...go on save her please, don't let her die, idan ta mutu nima mutuwa zanyi, please don't let her die" ya faɗa.pleadingly yana haɗa hannayen sa wuri ɗaya.


"Zamu yi iya ƙoƙarin mu na ganin mun ceto rayuwar ta, but please ka fita waje tukun."


Tsayawa yayi yana kallon DEENAH idanun sa na kawo ruwa, kafin kuma yayi saurin kauda kansa yana jinjina musu kai ya fice a hankali cikin mutuwar jiki.


Ganin yadda ya fito ne yasa su Umma tunkarar sa cike da tashin hankali.


"How is she, ka ganta, miye likitocin suka faɗa?" cewar Jafar yana kallon sa.


Kallon Umma da ta sha kuka ta godewa Allah ZEEDAN yayi, nan duk tausayin ta ya kama shi nan yace "She would be fine."


"We have waited for so long now, but har yanzu basu bari mun ganta ba almost 8hrs now."


Shiru ZEEDAN yayi yana sunkuyar da kai kafin kuma ya wuce ba tare da ya sake tanka musu ba, dan kuwa shi kaɗai yasan irin abinda yakeji a cikin zuciyar sa.


*******************

Around 2am na dare har yanzu babu wanda ya rintsa a cikin su.


Kallo ɗaya zakayi musu kaga irin tashin hankalin da suke ciki.

Buɗe ƙofar ICU ɗin akayi, kafin wata nurse ta fito cikin gudu, nan duk suka bita da kallo tsoro da fargaba na ƙara ƙaruwa musu a zuciya.


Ba'a jima ba ta dawo da wani abu a hannun ta tana shigewa ciki.


Bin bayan ta duk sukayi suka shige dan ganin abin dake faruwa.


Abin da nurse ɗin ta kawo ne aka shiga manna mata shi a ƙirji yana ɗago ta da ƙarfi da alamu dai numfashin ta da yayi ƙasa sosai ake son dawo dashi.


Kusan sau biyar akayi mata hakan, suna kaiwa na shida kuma shiru kakeji abin bai ɗago ta ba.


Sake manna mata shi sukayi nanma shiru kakeji.


Kallon juna doctors ɗin sukayi kafin ɗaya ya girgiza kai.


Numfashi duk suka sauƙe da ƙarfi, kafin kuma su shiga cire mata life saving machines ɗin da suka sanƴa mata ɗin.


"What's going on?" cewar Jafar yana kallon su.


Duk juyowa sukayi suna kallon su kafin ɗaya yace "Am sorry, she is..."


"Oh really, you are trying to tell us that she is gone, isn't it?" faɗin ZEEYAD yana kallon sa.


Takowa yayi bakin bed ɗin tare da jan kujera ya zauna yace "Look at her, just look at her face, tayi maka kama da wanda ya mutu?."


Murmushi yayi kafin yace "I know she is not dead, she is alive you need to check her again" ya faɗa a tsawace yana miƙewa tsaye.


Umma kam tuni ta sume anan wurin nan nurses biyu sukayi kanta.


Jafar kuwa sumar tsaye yayi yana kallon fuskar ƙanwar tasa.

ZEEDAN kan DEENAH ya nufa ya shiga marin fuskar ta a hankali yana faɗin "Hey wake up, wake up, everyone is here for you, your family are here, all of us are here, you can't just die easily like this, MADEENAH wake up, i know baki mutu ba, just wake up please" ya faɗa yana cigaba da bubbuga fuskar tata.


Dafa shi doctor ɗaya yayi yace "Ba abin mamaki bane idan ta mutu, koh ka manta da cewa dama dukkanin mai rai mamaci ne?."


A fusace ya juyo cikin tsawa yace "Ban manta ba, but MADEENAH ba zata mutu yanzu ba, she is supposed to be my wife, i know she is not dead you're jusr making this up, MADEENAH wake up please" ya faɗa cikin hawaye yana rungumo ta jikin shi.


"Please you can't do this to me babe, you can't leave me so soon, i know you're not dead."


Shiru yaji baiji motsin komai a jikin sa ba, but dukda haka ya kasa yarda da cewa DEENAH ta mutu.


Sakin ta yayi yana ɗan janƴe jikin sa, nan yaga ta koma ta faɗa kan bed ɗin jikin ta a sake.


Durƙushewa yayi a wurin yana kamo hannun ta ya damƙe cikin nashi yace "Please MADEENAH kar kiyi min haka, ke kaɗai ce farin ciki na da ta rage, ke kaɗai ce kike sani farin ciki, i know you don't like me, kuma bakya sona, but please kar ki mutu nikuma nayi miki alƙawarin ba zan sake shigowa rayuwar ki na takura miki ba, i promise you this, just wake up please."


"She is not waking up" cewar Jafar.

Kallon sa ZEEDAN yake, nan ya sake cewa "She is dead for sure."


"No she is not, i know she is not dead."


Ƙarasowa Jafar yayi wurin yana kamo hannun DEENAH ya sanƴa cikin nasa, cikin kuka yace "Bata motsi, bata numfashi, look nima ba zan yarda da cewa ta mutu ɗin ba, amma tun da muka rasa Abban mu kuma har yau bai dawo ba, then na yarda da cewa na rasa ƙanwata ma, yes it really hurts to believe this but we can't change the fact, DEENAH..." ba tare da ya ƙarasar ba ya tashi ya fice daga cikin ɗakin da sauri sakamakon kukan da yazo masa.


ZEEDAN yana gani suka ƙarasa cire mata abubuwan da aka sa mata kafin su rufa mata farar kyalle a fuskar ta.




*Yawan Comment, Yawan Typing*







*MHIZZ JIDDHERR.............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*024...*



_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_




ZEEYAD na durƙushe a wannan wurin helplessly yana kallon DEENAH dake rufe da farin kyallin.

Rayuwar su ta baya ne ya shiga dawo masa kwakwalwa, how kind she is, the way she used to stare at him with her captivating wide eyes, and a lot of things, kawo izuwa ga ranar da ya fara ganin ta bayan haɗuwar su da shekaru goma.


"Noooo" ya faɗa da ƙarfi crying his heart out.

"Am sorry, am so sorry, don't leave me please i beg you DEENAH" ya faɗa yana kifa kansa kan bed ɗin hannun ta cikin nasa.


*****************

Ɗagowa yake a hankali da idanun sa dama kuma fuskar sa da yayi mugun jaa yana mai addu'ar Allah yasa dukkanin wannan mummunar abin a mafarki ya gansa.

Hannun ta dake cikin nasa ya kalla kafin kuma ya shiga bin ta da kallo har yanzu tana rufe da farar kyalle.

Baki ya cize yana runtse idanu, miƙewa yayi zaune tare da yaye farar kyallen yana kallon fuskar ta.

No!, he can't believe DEENAH is gone, he can't believe kyakkyawar fuskar nan is gone.

"May be she just fall asleep" ya faɗa trying to get rid of his sorrows.

"MADEENAH?, MADEENAH??" ya faɗa yana ɗan bubbuga kumatun ta.

"Look MADEENAH, bansan ki da irin wannan wasan ba, your family is all worried about you, those stupid doctors da basusan aikin su ba are saying that you are dead, but i know that you are still alive, i guess basu gwada ki dai-dai bane, you just wait here, dole ne na kira su suzo su sake gwada ki, just wait here please, i will be right back" ya faɗa kamar wani mai sumbatu yana miƙewa ya fice daga ɗakin.

Jafar ya gani zaune ya haɗa kai da guiwa, ba tare da ya kula sa ba ya wuce.

Wani doctor ya gani yana wucewa nan yayi saurin kiran sa yana faɗin "Hey you wait right there."


Ƙarasawa yayi gaban doctor ɗin kafin yace "Come with me, i want to show you something" ya faɗa yana riƙo hannun doctor ɗin zuwa ɗakin da take.


Kanta suka tsaya nan yace "Look those silly doctors said that she is dead, i want you to check her again, coz i know she must still be alive, come on."

Kallon sa Doctor ɗin yake cike da mamaki kafin yace "What are you saying?, she is already dead, mun riga munyi confirming hakan tun jiya, she is just a corpse...."

"No she is not a corpse, my DEENAH is not a corpse, MADEENAH sunan ta ba gawa ba, get it?" ya faɗa cike da 6acin rai yana kallon sa.

"Look why don't you get some rest?, you look so stressed, inaga shiyasa har yanzu you refused to accept the fact that she is dead, it's already 4am da zaran anyi sallar Asuba zamuyi discharging naku."

"Let's see who you discharge then" ya faɗa yana juyawa ga DEENAH.

Hannu yasa ya ɗago ta yana kallon fuskar ta yace "Inaji a jikina baki mutu ba, and i will make sure that i prove them all wrong na cewar kin mutu" ya faɗa yana ɗagowa ya kalli doctor ɗin.

Ficewa yayi daga ɗakin Doctor ɗin ya bisa da kallo cike da mamakin sa na dagewa cewa DEENAH bata mutu ba.

Jafar ne ya ɗago ya kalli ZEEYAD da ya fito da DEENAH riƙe a hannun sa, nan ya tashi cike da mamaki yace "Where are you taking her?."


Bai kula Jafar ba yayi gaba, hakan yasa Jafar saurin mara masa baya.

Ficewa sukayi zuwa farfajiyar asibitin kafin ya nufi parking space inda ya ajiye motar sa, Jafar ne ya buɗe masa bayan ya sanƴa DEENAH.


Kafin duk su zagaya su shige cikin motar.

"Where...where are we going?."


"Somewhere, that i can prove them all long" ya faɗa yana jan motar a tsiyace ya bar cikin asibitin.


Kai tsaye wani Babban private hospital mai kyau da tsada ya nufa.

Zuwan su kuwa aka kar6i DEENAH duk da kuwa basu ga alamun rai tattare da ita ba.

"She will be fine, i know she will" ya faɗa yana kallon Jafar.


Sallar Asuba aka fara kira dan haka dukkan su masallaci sukayi.


Basu dawo ba sai da gari ya ɗan waye.

ZEEDAN ne yace "I know bata mutu ba, kafin mu isa yanzu she must be awake."


Jafar dai kawai jinsa yakev dan kuwa yaga alamun kamar ZEEYAD ɗin kwakwalwar sa ta ɗan ta6u ne, but shi ya san DEENAH ta mutu, amma shi sam babu alamun zai yarda da hakan nan kusa.

"Wait...don't tell me cewa kaima ka yarda cewa ta mutu?" ya faɗa yana kallon Jafar da yayi shiru yana saurarar sa.


Shiru Jafar yayi yana kallon sa ba tare da ya iya cewa komai ba, dan kuwa abinda yakeji a cikin zuciyar shi ba zai musaltu ba, dan kuwa DEENAH tamkar farin cikin sa haka take, ita ɗin ta kasance abar alfaharin sa ce, tabbas yayi rashin ƴar uwa, yarintar su kaɗai abar burgewa ce wanda idan ya tuna sai yaji wani irin kewar da yakejin har a abada ba zai daina ta ba, su kaɗai kawai iyayen su suka haifa, Mahaifin su tun DEENAH nada shekaru biyar ya rasu, inda ya saura daga shi sai Ummar su da DEENAH, su uku kaɗai, sun taso cikin so da ƙauna dama kuma kulawar juna, sai dai yau guda wannan ƙaunar ta yanke Saura shi da Umma kaɗai cikin family ɗinsu, bai san yaya rayuwar su zata kasance da rashin DEENAH ba, rayuwar su ba zata ta6a tafiya cikin farin ciki kamar ta dah ba, maiyasa DEENAH bata mutu tun a ƙaramar ta ba sai yanzu da ta zama budurwa wacce kowa ke so dama kuma ƙulla alaƙa da ita?.


Kuka Jafar yasa yana rufe fuskar sa da tafukan hannun sa, sosai zuciyar sa ke yi masa zafi, ganin gari ya waye kuma ya kusa rabuwa da ƴar uwar sa, rabuwa ta har abada, ba zai sake ganin ta ba, shi kaɗai yasan irin abinda yakeji a zuciyar sa, he can't believe it shima, sai dai babu yadda ya iya da lamarin Ubangiji, tunda dama duk Allah ne ya hallice mu sannan kuma wataran dole ne mu koma gareshi, koh ba jima koh ba daɗe, dan kuwa babu wanda zai dauwama a duniyar.

Sosai ya baiwa ZEEYAD tausayi inda shima har ya fara sanƴawa ransa cewa dagaske MADEENAH ɗin sa ta mutu ba, kafin kuma yayi saurin kawar da tunanin daga ransa yana girgiza kai.


A inda suke tsaye wata Nurse ta fito ta same su tare da sanar dasu cewar doctor na neman ganin su.


Mara mata baya sukayi zuwa office ɗin doctor ɗin, zuciyar su cike da zulumin abinda zai fito daga bakin sa.

Duk wuri suka samu suka zauna kowanne zuciyar sa cike da fargaba dama kuma tsoro musamman ZEEYAD da ya kasa zaune properly.


Kallon su likitan yayi yace "Menene matsayin ku a gare ta?."

Kallon juna sukayi kafin Jafar yace "Mu ɗin yayun ta ne."


Kallon ZEEYAD yayi alamun mamaki kafin kuma ya share yace "Well am sorry to said this, but...."


"Don't tell me please, please Doctor don't tell me that she is dead" cewar ZEEYAD kamar wanda zaiyi kuka.


Shiru doctor yayi yana kallon sa kafin kuma yace "Well am sorry..."


"Ta mutu right?, alright then zamu tafi da ita tun jiya da dare aka tabbatar mana da hakan a asibitin da muka fara zuwa, and gashi nan anan ma hakanne, I told you sir DEENAH is dead."


Sosai ZEEYAD ke jin wani irin abu mai ɗaci a maƙoshin shi, har yanzu bai yarda ba, babu ta yadda za'ayi ace DEENAH ɗinsa ta mutu ne, No it can't be.


Gyaran murya Doctor yayi yace "Well maybe ku tsaya ku saurari abinda zan faɗa tukun."


Duk maida duban su sukayi kansa dan jin abinda

Please Login or Register in order to submit comment