Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abandoned Prince]```






*QUARTER FINAL*





*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*






*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*053...*




_Ku tanadi Hanky tukun kafin ku fara karatun😭_



________"Ni fah wannan mahaukacin Sooraj ɗin bai daki banza ba wallahi, sai na rama duk wani rauni da yayi min akan ƙanwar tasa na nuna masa cewa nima fah da tawa gatar, dan aure ya kawo ni wannan MASARAUTAR ba shi ke nufin koh banida gata bane sannan wani banza chan ya ta6a min lafiyar jiki kuma ya wanƴe lafiya, sai na tabbatar na ɗau fansa ta akan ƙanwar tasa idan yaso koh kashe ni zaiyi sai dai ya kashe ni" ta ƙarashe cike da fusatar da take ciki.

Rahinah ce tace "Ke ki raba kanki da Sooraj wallahi bayida hankali koh kaɗan ni kunga tattara inawa-inawa zanyi na koma London da zaran na ɗan ƙara jin sauƙi ban isa ya kashe ni a banza ba tare da na gama more rayuwa ta ba."

Shiru Hafeezah dake ta kai komo cikin É—akin tayi tana saurarar su.

Katse su tayi da faÉ—in "We must get rid of DEENAH's baby."

Wani irin kallo Sairah tayi mata kafin tace "Just look at our condition, koh nuna alamun kin damu bakiyi ba, kedai kawai akan burin ki hankalin ki ya karkata baki damu da kiyi mana jajen abinda ta6a66en nan yayi mana ba, and kinzo kina maganar wata banzar DEENAH chan daban."

Kallon ta Hafeezah tayi kafin tace "Kuma dan Sooraj yayi muku lahani sai hakan ya dakatar dani daga aiwatar da niyya ta komiye kike nufi, this is for your own good ke gaki nan koh cikin bakiyi ba and YAZEED ne zai zamto sarki nan ba da jimawa ba, muddin muka bari DEENAH ta haihu then komin daren daÉ—ewa sai abinda ta haifa ya gaji mulki muddin ya kasance namiji ne."

Shiru tayi tana tunani sai yanzu take ganin wautar ta tun farko da ta kada seducing YAZEED, nan ta miƙe tsaye tana kallon Hafeezah tare da faɗin "What do we do then?."

Murmushi Hafeezah tayi tare da faÉ—in "We kill the unborn child."

"But how, tayaya JALILAH is our only hope and mahaukacin yayan ta won't let us rest muddin muka sake yunƙurin yi mata wani abin."

Murmushi Hafeezah tayi kafin tace "Wayo zamuyi mata da daÉ—in baki mu janÆ´o ta cikin mu."

"That won't be easy, zuciyar ta gauraye take da imani, ba zata ta6a yarda damu ba har ta iya bamu haÉ—in kai, and besides kishiya ce a gareni there is no way zan haÉ—a inuwa É—aya da ita a matsayin team, we all want her dead sabida ya kasance ni kaÉ—ai na rage matar YAZEED why kuma zamu jawo ta cikin mu?."

"Kina tunanin koh nima kaina ina ƙaunar ta da YAZEED ne, ke kaɗai ce matar YAZEED sannan kece zaki zamto Sarauniya ga wannan ƙasa ba da wata ba, da zaran ta gama yi mana amfani sai kuma muga bayan ta."

Murmushi Sairah tayi kafin tace "Yanzu kikayi magana, ta ina yakamata mu fara yanzu?."


***********************


__________DEENAH ce tsaye bakin mirror ta ƙurawa cikin nata ido, hannu ta kai ta shafi cikin tanajin yadda yake yi mata motsi a ciki.

Murmushi tayi kafin tace "You're my only happiness now and i will do everything it takes dan ganin kazo duniyar nan da ranka, i can give my life dan ganin kai ka rayu, no enemy da ya isa yayi galaba akanka, this is my promise to you little ZEEYAD."

Rolling É—in gyalen hannun ta tayi akanta tana gyara dressing É—in jikin ta kafin kuma ta fice daga É—akin.

Tundaga sauƙowar ta kuyangu matan suke binta da ido har tsayawa sukayi suna kallon ta, DEENAH tamƙe fuska tayi tamkar bata ta6a yin dariya ba ganin yadda har wasun su sun fara ƙus-ƙus ƙasa-ƙasa.

Har ta fice daga part ɗin Grandma basu daina binta da kallo ba, tana fita kai tsaye hanƴar fadar mai Martaba ta nufa sam bata damu da kallon da kowa ke bin ta dashi ba duk inda ta ratsa, a haka har ta iso ƙofar fadar.

"What a beautiful being" ta tsinkayo murya daga bayan ta hakan ya sanÆ´a ta dakatawa ba tare da ta juyo ba.

Ayaan dake binta da tsinannen kallo ƙarasowa wurin yayi kafin ya shiga zagaye ta yana binta da kallo, dakatawa yayi a gaban ta kafin yayi murmushi yace "You look more beautiful fiye da yadda ake kwatancen ki."

Bata kallesa ba haka ma kuma bata kulasa ba.

Baki ya lashe yana sake matsowa kusa da ita kafin yace "Sai dai koh kaÉ—an baki dace da ciki a jikin ki ba, i mean ZEEYAD is already dead why keeping abinda ya bari har yanzu cikin mahaifar ki, you deserve a better life like this carrying a dead persons heir in your womb..."

Kallon da tayi masa ne ya sanÆ´a shi haÉ—iye sauran maganar, sosai maganar da yayi yayi mata zafi har wani irin huci ta shiga fitarwa cike da 6acin rai.

Hannaye ya ɗaga sama tare da faɗin "Oops those that hurt you?" kafin kuma ya sauƙe hannun cikin murmushin ƙeta yace "Seriously DEENAH you're much younger than your age and more beautiful than your expectation ZEEYAD is dead... why don't you give me a chance?" ya faɗa cikin ɗaga mata gira ɗaya.

Hannu ta ɗaga tare da wanke fuskar sa da mari, dafe ƙunci yayi yana juyowa ya kalleta cikin tsananin 6acin rai idanun sa na canza launi.

"How dare you?" ya faɗa yana ture ta da ƙarfi.

Tangal-tangal ta tafi zata faɗi kafin tayi saurin riƙe wani ƙarfe dake bayan ta yanw tsaida ta, wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya ta sauƙe tana riƙe cikin ta kafin kuma ta sauƙe numfashi ganin tana runtse idanun ta.

Ƙarasowa yayi inda take tare da fizgo ta tana kallon sa, murmushi yayi kafin yace "You think ana ta6a lafiyar jiki na kuma a wanƴe lafiya ne?" ya faɗa yana shafa kafaɗun ta cikin salon iskanci.

Su dai guards ɗin koh motsawa basuyi ba bale su tanka abin dake faruwa haka suka ƙame a wurin tamkar gumaka.

Ganin yadda yake shafa mata jiki ne ya sanÆ´a ta tattarar dukkanin karfin ta tana tura shi.

Baya yayi yana ja ya tsaya, dariya ya saki yana sake binta da wani irin kallo.

Saurin nufar ƙofar fadar tayi nan taga ya sake ɗaura mata hannu a kafaɗa wurin tsaida ta.

Idanun ta ne suka sauƙa kan wani ɗan guntun takobin dake maƙale gefen wandon ɗaya daga cikin guards ɗin, ai kuwa batayi wata-wata ba tayi saurin kai hannu tana zaro kafin ta juyo a fusace tana fille masa hannu da wannan takobin har jini na 6ata mata fuska.

Wani irin ƙara Ayaan ya saki cike da mugun firgita yana ja da baya tare da faɗi ƙasa ganin damtsen hannun sa guntule a ƙasa ga kuma yadda jini ke ta bulala tamkar an buɗe shower.

Ihu kawai yakeyi sai a sannan ne guards É—in suka iyo kansa, kan kace miye kuma har mutane sun fara taruwa kowa na zuwa ganewa idanun sa abin dake faruwa ganin yadda Ayaan É—in ke ta ihu har yanzu tamkar zai zauce.

"Arrest her" ɗaya daga cikin guards ɗin ya faɗa da ƙarfi yana nuna DEENAH dake tsaye tana ta faman sakin huci tamkar ranta zai fito.

Kanta wasu guards ɗin sukayi suna sanƴa mata handcuff a hannu, sam koh kaɗan bataji wani tsoro koh fargaba cikin ranta ba sai ma ji take da tayi dai-dai, sannan duk wani wanda yayi yunƙurin shiga gonar ta a shirye take da ta fuskanci wannan mutumin, yanke hannun Ayaan da tayi a yanzu ji tayi wani irin jarumta tazo mata, da mugun kallo take binsa har suka wuce shi kafin ta saki wani irin murmushin gefen baki.

Kaita akayi aka rufe cikin cell sam bata damu ba dan kuwa tasan komin daren daÉ—ewa dai sai ta fita dan ba zata dauwama cikin nan ba.

Wuri ta samu ta zauna tanajin zuciyar sa fes koh bakomai ta É—au fansar ta6a mata jiki da yayi.

********************

________Sosai Hafeezah ke wani irin mugun kuka a gaban ɗan nata ganin hannun sa a yanke, musamman da taji wacce ta aikata masa hakan ba ƙaramin fusata tayi ba, ji take zata iya kashe DEENAH muddin ta haɗa idanu da ita, sai ta ɗau fansar cire mata hannun yaro da tayi sai dai uwarta ta haifo wata amma ba dai ita ba.

Ganin mai Martaba baiyi magana bane ya sanÆ´a ta nufar sa a mugun fusace tana faÉ—in "Kaga abinda matar wancan mataccen É—an naka tayi wa É—ana amma har yanzu ka kasa cewa komai, banji ka bada umarnin aje a yanke mata hukunci dai-dai da abinda ta aikata ba, ta cire min hannun yaro amma kayi shiru tamkar wanda ba É—anka bane shi É—in, maiyasa ba zaka É—au mataki akanta ba?."

A tsawace mai Martaba yace da ita "DEENAH have done the right thing, your son here tries to humiliate her ba tare da yayi tunanin ita ɗin matar wansa bane ba, koh a dokar ƙasa laifi ɗaya ta aikata shine na ɗaukar mataki da hannun ta..."

Cikin kuka ta katse shi da faɗin "Ni zaka dubi idanu na kacemin ta aikata dai-dai, kasan ciwon da nakeji cikin zuciya ta na ganin yaro na babu hannu ɗaya?, ta maida min yaro miskini cikin ƙanƙanin lokaci dan haka nima ba zanyi ƙasa a guiwa wurin ɗaukar fansa wa yaro na ba, muddin kai ba zaka ɗauki mataki ba ni nan zan ɗauka" ta faɗa a haukace tana nufar hanƴar ficewa, kwala mata kira mai Martaba keyi sai dai inaa koh ta juyo ta kallesa balle yasa ran zata amsa har ma ta tsaya.

Bata tsaya koh ina ba sai part ɗin Grandma saurin miƙewa tsaye duk sukayi ganin yadda Hafeezah ta faɗo cikin falon nasu hannun ta ɗauke da takobi tamkar zata tashi sama.

Kai tsaye kan DEENAH ta iyo cike da fusata ba tare da tunanin komai ba idanun ta sunyi matuƙar rufewa da tsanar DEENAH ta ɗaga takobin, DEENAH saurin runtse idanun ta tayi tana jiran shigar takobin cikin cikin ta sai dai taji shiru, ihun JALILAH da taji ne ya sanƴa ta saurin ware idanun ta tana sauƙe su a bayan sa.

Duk mutanen cikin wurin idanu suka zaro cike da mugun tashin hankali ganin wanda wuƙar ya soka.

Da sauri Hafeezah ta saki takobin tana ja da baya a mugun razane tare da sakin wani irin ƙara tana ware idanun ta kan wanda takobin ke jikin shi.

Ɗago da idanun sa da sukayi matuƙar kaɗawa YAZEED yayi daga kan takobin yana kallon mahaifiyar tasa, zuciyar sa cike da tsantsar baƙin ciki, baƙin cikin da ba zai ta6a gushewa daga ransa ba har izuwa ranar da za'a busa ƙaho.

A hankali ya furta "Um... mie..." yana zubewa kan guiwowin sa wasu irin hawaye na biyowa ƙuncin sa.

DEENAH ji tayi zuciyar ta na breaking into tiny-tiny pieces sakamakon ganin YAZEED da tayi cikin sa soke da takobin da mahaifiyar sa tayi niyyar kashe ta dashi.

Bata koh iya motsa koh da ƴar yatsar ta bane wasu irin zafafan hawaye na biyo mata ƙunci.

Grandma kuwa zubewa tayi kan kujera itama tamkar wacce aka zarewa ruhin ta daga jikin ta.

Cikin maganar sa da bata fitowa mai kyau yake kallon mahaifiyar tasa yace "Are... you... happy now?."

Kai kawai Hafeezah ke girgizawa cike da tashin hankali hawaye na biyo mata ƙunci.

Babu wanda ya iya tunkarar YAZEED sakamakon wani irin shock da ya ziyarci kowannen su, cikin kuka ya sake faÉ—in "Are you happy now... Ummie?" yana zubewa kwance a wurin inda kuma jini ya shiga wanke wurin.

Da gudu Hafeezah ta iyo kanshi mai Martaba ya daka mata wani irin tsawa "Don't you dare go near my Son Hafeezah."

Amma inaa bata saurare sa ba tayi kan YAZEED É—in sai gurzar kuka take tamkar ranta zai fita.

"Oh no!, no... my lovely son YAZEED, i killed you, i killed my own Son, na shiga uku na lalace na kashe YAZEED É—ana..."

"Sieze her" cewar mai Martaba ɗin ai basuyi wata-wata ba guards ɗin suka iyo kanta suna ɗagota, hannun YAZEED ɗin ta riƙo gam babu abinda take sai kuka shikenan ta kashe ɗanta da kanta a garin son zuciya da baƙar zuciya irin tata.

Dakyar suka iya kwace YAZEED daga hannun ta, da gudu JALILAH ta iyo kansa bata ma damu da ciwon ƙafarta ba dan kuwa tama daina jinsa baki ɗaya ne a jikin ta tana ɗagoshi, sosai take kuka tana girgiza masa kai.

Murmushi yayi mata kafin yace "Don't... cry."

Kai kawai take girgiza masa tana kuka.
"Please...please i beg you kada ka mutu ka barni, ba zaka mutu yanzu ba baikamata ace ka mutu ba, no... no please, please" ta faɗa da ƙarfi cikin kuka tana ɗan bubbuga fuskar sa ganin idanun sa na neman rufewa.

Riƙo hannayen ta yayi yana kallon fuskar ta kafin yace "Am sorry..."

"No...ba zaka mutu ba, ba zaiyiwu kaima mu rasa ka ba, dan Allah kada ka mutu na roƙeka, dan Allah..."

Shafa fuskar ta yayi yana share mata hawayen dake biyo mata fuskar, "Please forgive me..." ya faÉ—a cikin rarrabewar harshe.

Kallon DEENAH dake tsaye akansu tana hawaye yayi kafin yace "Z...EE...ZEE..." bai ƙarasar da zancen nasa ba jami'an dake aiki da emergency Ambulance suka zo suka ɗauke shi.

Cakumo É—aya sarki yayi yace "Save him... Save my son please shi kaÉ—ai ne ya rage min..."

Kwacewa mutumin yayi daga riƙon da yayi masa kafin yayi saurin marawa ƴan uwan sa baya.

Tari mai ƙarfin gaske ne ya sarƙe mai Martaba ɗin, take shima cikin gaggawa aka ɗauke sa suka fice.

Sosai JALILAH ke kuka tamkar zata shiÉ—e tana kallon hannun ta da yake kaca-kaca da jinin YAZEED haka ma kayan jikin ta.

Tashin hankalin da DEENAH da Grandma ke a ciki baya misaltuwa, dukkanin su kuka suke an rasa mai rarrashin wani, jikin DEENAH har rawa yake, tasan itace tayi sanadiyyar mutuwar YAZEED da ace bata tankawa Ayaan ba dah Hafeezah bata haukace tazo da niyyar kashe ta abin ya faÉ—a kan YAZEED ba.

Zubewa tayi akan kujerar dake bayan ta tana shessheƙa mai cin rai, sosai take cikin shock ɗin ganin mutuwar YAZEED a gaban ta, shikenan JALILAH ta zama ƙaramar bazawar kamar ita though ita tana da magajin da zata dinga tuna mijin ta dashi but JALILAH fah yanzu ne ma sabo ya soma shiga tsakanin ta da YAZEED gashi kuma ya tafi ya bar ta, this is very shocking, sam bata tsanmaci zuwan wannan incident ba, sosai zuciyar ta ke rawa, sosai take baiwa kanta laifin afkuwar wannan lamari, tasan YAZEED ba zai rayu ba shikenan shima ya tafi tamkar yadda ZEEYAD ya yafi tsawon watanni biyar kenan bata ga ya dawo ba, haka shima YAZEED ɗin zai tafi ba zai dawo ba har abada dan kuwa bata tunanin zai rayu, sosai takejin tausayin mai Martaba ma ace ya rasa ƴaƴan sa matasa wadanda zasuyi gadon mulkin sa, bashida wani magaji na kirki kuma da har za'a iya bashi mulkin ƙasar ya riƙe, gashi shima dama bai gama farfaɗowa daga shock ɗin da ya shiga na mutuwar ZEEYAD ba ga kuma na YAZEED "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un" take ta nanatawa a ranta.


************************

_________Sosai likitoci suka rufu akan YAZEED suna iya bakin ƙoƙarin su na ganin sun ceto rayuwar shi.

Mai Martaba gabaki ɗaya ya rikice ya zangwame lokaci guda, hankalin sa a matuƙar tashe yake, Abhi ɗin Sadeeq ne ke ta ganin ya kwantar masa da hankali amma kamar sake ƙara masa damuwa yake, ya kasa zaune ya kasa tsaye, damuwa da fargaba sunyi masa ƙatutu a cikin zuciya bai ma damu da tasa lafiyar ba, burin sa shine YAZEED ya samu lafiya nan ne kaɗai hankalin sa zai kwanta.

Fitowar wani likita daga ɗakin tiyatar ne ya sanƴa mai Martaba iyo masa wani irin riƙo yana faɗin "How is he, how is my Son?."

"Calm down your Highness, muna iya bakin ƙoƙarin mu ne na ganin mun ceto shi, zai fi kyau ka sarara haka muyi aikin mu cikin kwanciyar hankali" yana faɗin haka yayi gaba da sauri.

A takaice dai sun É—au awanni da dama akan YAZEED kafin su fito daga É—akin tiyatar kusan likitoci shida ciki harda Sadeeq.

Duban idanun Sadeeq Abhi yayi kafin ya kalli mai Martaba da shima shi yake kallo.

"How is YAZEED?, sannan zuwa yaushe zai samu lafiya mu tafi dashi gida?."

Kallon Abhi É—insa Sadeeq yayi cikin sanÆ´i yace "I'm sorry..."

Kallon da mai Martaba yayi masa ne ya sanÆ´a sa kasa idda maganar tasa.

"Yes, tell me."

"YAZEED have only 30% chance of survival munyi nasarar cire takobin daga cikin sa wanda yayi nasarar huda small intestine ɗinsa, so munyi masa dukkanin wani ƙoƙarin ma na likitoci but..."

"Kana nufin kacemin kana tantama zai rayu koh ba zai rayu ba kenan?" cewar mai Martaba É—in.

Kai Sadeeq ya jinjina masa, nan mai Martaba ya sake faɗin "Zancen banza ne wannan likita, ran YAZEED ba a hannun ka yake ba, you have no gut to tell me ba zai rayu ba, ni nasan insha Allah ɗana zai rayu na rasa na farko ba zan iya jurar rasa wannan ba, our kingdom needs someone very trusthworthy da zai mulke ta, YAZEED is the only person da nake sa ran zai cika min buri na, this kingdom will fall apart muddin YAZEED ya mutu..." hawayen da suka zubo masa ne ya sanƴa maganar tasa ƙaƙarewa.

Ido Abhi yayi wa Sadeeq akan ya wuce yaje kafin kuma shi ya shiga baiwa mai Martaba É—in baki.

Sadeeq Office ɗinsa ya koma, kifa kansa yayi akan table ɗin ofishin nasa, wasu hawaye masu zafi na wanko masa fuska, he can't believe iriyar ƙaddarar wannan MASARAUTAR yana tsoron rasa YAZEED tabbas idan YAZEED ya mutu then komai lalacewa zaiyi, and ZEEYAD kuma har yanzu babu wani labarin cigaba a fannin lafiyar shi.

Yasan rai ba a hannun sa yake ba but zaiyi dukkanin ƙoƙarin sa tare da addu'ar ganin YAZEED ya rayu haka ma ZEEYAD, su ɗin abokai ne amana a gareshi dan haka it's a must for him ya dage da yi musu addu'a dukkanin su, kowa nasu tausayi suke basa DEENAH, JALILAH Grandma dama kuma Mai Martaba, ɗago da jajayen idanun sa yayi kafin kuma ya tashi ya fice daga office ɗin.


*************************


*6 MONTHS LATER*


_________Hafeezah na hango cikin Katuwar cell hannayen ta dama kuma duka ƙafafun ta ɗaure da chain, sosai tayi kaca-kaca tayi jina-jina da ita, sosai ta koma wata iriyar shiru-shiru tamkar ba Hafeezah marar imanin nan ba.

Sosai takejin baƙin cikin kashe YAZEED da tayi, sai dai ta dangana laifin ne akan DEENAH wanda har yanzu bata cire ran kashe ta ba da ita da abinda ta haifa ɗin bayan ta fito daga kurkuku, dukda batasan dalilin da ya sanƴa ba'a yanke mata hukunci har yanzu ba but batada wata damuwa tunda akwai Sairah da Rahinah su zasu ƙarasar mata da sauran aikin da batayi ba.

"Chill out DEENAH, soon dake da abin da kika haifa ɗin zaku baƙunci lahira, i don't care yadda makoma ta zata kasance all i want and need is your death, i won't stop at nothing until a avenge my Son's death dama kuma Ayaan da kikayi sanadiyyar naƙasar masa da halitta, i hate you DEENAH yadda ban ta6a tsanar wani mahaluƙi a duniya ba, ba zan ta6a samun Peace of mind ba har sai naga gawar ki da ta ɗan da kika haifa da idanu na, i have spent six months cikin wannan kurkukun duk saboda ke, i swear... i swear DEENAH dole ne ki mutu only then i can be happy" ta ƙarashe idanun ta na kaɗawa suyi jazir.


**********************

________Zaune DEENAH take akan dukda ba sallar takeyi ba sai dai bakin ta É—auke yake da tasbih dama kuma kiran sunan Allah tare da nemawa YAZEED dake kwance har yanzu lafiya, yayin da 6angare guda kuma take yiwa mijin ta addu'ar da kullum bata gajiya dayi masa.

Ƙananan kukan da Jaririn dake kan gado yayi ne ya sanƴa ta miƙewa tana zuwa kan gadon tare da ɗaukar sa, a hankali ta shiga jijjiga shi tana faɗin "It's Okay Baby, Momy is here banyi nisa da kai ba" ta faɗa tana rungume shi a ƙirjin ta.

Lumshe idanu tayi hawaye na sauƙo mata tace "You left us a lokacin da babu wanda ya ta6a tsanmani, a lokacin Allah ya ɗau ranka, but gashi Allah ya dawomin da photocopy ɗinka, wanda dashi ne zan dinga tuna ka sannan dashi ne nakejin present ɗinka a kusa dani, you may not be here with us but we were always with you and we will forever be Abyad" ta ƙarashe tana zama kan bed ɗin kafin ta kwantar da yaron da alamu dai ya koma bacci, yaye fuskar sa da tayi daga cikin towel ɗinne ya sanƴa wayar hannu na kusan su6ucewa da ganin kyakkyawar halittar yaron mai kama da mahaifin sa sak tamkar an tsaga kara.

Murmushi DEENAH tayi tana sake kallon fuskar yaron, kishingiÉ—a tayi kusa dashi tana a haka har Asuba tayi.

Kiran farko ta farka tana sauƙe idanun ta kan fuskar kyakkyawan Baby boy ɗin nata.

Murmushi tayi tana miƙewa tare da gyara masa kwanciya kafin ta tashi ta nufi bathroom, Alwala tayi ta fito kafin ta tada sallah, bayan ta idar ne kuma tayi azhkar da Tasbih ɗinta, ta daɗe akan sallayar tana addu'a kafin kuma tayi karatun Al'ƙurani mai girma, bayan ta idda ne ta miƙe tare da nannaɗe sallayar tana maida shi gurbin zaman sa.

Yaron da taga idanun sa a buÉ—e ne ya sanÆ´a ta yin murmushi kafin ta É—auke sa tana yin É—akin Grandma dashi.

Akan sallaya ta tadda ta dan haka shimfiÉ—e shi tayi akan gadon Grandma kafin ita kuma ta fice.

Wanka ta iyo tayi shirin ta mai kyau tamkar kullum kafin ta dawo É—akin Grandma nan ta tadda har ta yiwa jaririn wanka, gaida Grandma tayi kafin DEENAH ta kar6i yaron tana dawowa É—aki dashi.

Tana cikin shirya shi JALILAH ta shigo É—akin fuskar ta É—auke da murmushi take faÉ—in "Mai raino tazo."

Murmushi DEENAH tayi tana miƙa sa wa JALILAH bayan ta shirya shi.

Kallon sa JALILAH take kafin tace "Har gobe ba zan daina cewa fuskar mahaifin sa nake gani tattare dashi ba."

Murmushin yaƙe kawai DEENAH ta iya yi, ita kaɗai tasan abinda takeji cikin zuciyar ta, abin akwai ciwo ciwon da babu wani mahaluƙi da ya isa ya kwatanta ya yake koh da kuwa ya ta6a shiga irin halin sai dai kawai yayi ta 6oye damuwar dake cikin zuciyar sa da murmushi, but tabon da hakan ke yiwa zuciyar mutum ba ƙarami bane.

Ganin yadda yanayin ta ya canza ne ya sanƴa JALILAH miƙewa tsaye tana faɗin "Toh mu mun wuce."

Kai kawai ta iya jinjina mata kafin kuma ta miƙe akan bed ta shiga kukan da batasan ranar dainawar ta ba.


***********************


*3 DAYS LATER*


________Zaune Sadeeq yake a ofishin shi kira ya shigo wayar sa, gaban sa ne ya faÉ—i ganin malamin nan ne mai kira.

ÆŠagawa yayi tare da yin sallama cikin sanÆ´i.

Shiru yayi yana saurarar abinda mutumin ke cewa, hankali tashe ya miƙe tsaye yana faɗin "What do you mean...?."

"He is under your care, and kayi alƙawarin bashi dukkanin kulawa how comes kuma zakace baka ganshi ba yanzu."

"This is Nonsense, kai kacemin bai sami lafiya ba har yanzu, ya kuma zakace min ba sace sa akayi ba."

"Hold up, i will be right there yanzun nan, duk inda yake ka tabbatar kun nemo shi before i arrived" yana faÉ—in haka ya ajiye wayar tare da ficewa cikin kiÉ—ima.

Sai da ya leƙa ya duba lafiyar YAZEED tukun kafin ya fice ba tare da ya sanarwa kowa ba.

*******************

______Daga cikin closet room É—insu take jin kishi-kishin É—in yaron yana surutan su irin na jarirai inda ita kuma take amsa masa, kayan su take haÉ—awa kasancewar gobe da sassafe zasu koma Nigeria dan kuwa taga sam wannan zaman MASARAUTAR ba zata ta6a yiwuwa a garesu ba, muddin tana son É—anta ya rayu ya zama dole ta tafi tayi nesa dasu dan kuwa kusan sau huÉ—u ana kawowa jaririn ta hari tana kamawa, hakan ya sanÆ´a ta zuwa part É—insa da ta mance yaushe rabon ta da ta shiga tana harhaÉ—a abubuwan ta.

A hankali yake tafiya har ya idda shigowa cikin É—akin, turus yaja ya tsaya yana bin É—akin da kallo kafin kuma ya shiga lalla6awa a hankali yana nufar jaririn da ya hango akan tsakiyar bed É—in É—akin.

Tsaye yaja yana ƙarewa kyakkyawar yaron kallon wanda ba zai wuci watanni biyu da haihuwa ba, wutsil-wutsil yaron keyi da ƙafarsa yana cigaba da surutun sa irin ta jariran.

Gyara rufar bargon jikin

Please Login or Register in order to submit comment