Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata kuwa sai ta ɗauke shi tana faɗin ai itace yakamata ace tana sanƴa irin su.


A haka ta gama ɗaukar wadanda sukayi mata kafin ta fito zuwa part ɗinta.


Anan ta tadda DEENAH har ta gama gyara mata falon ta koma gyara ɗaki.


Ɗakin ta shigo anan ta dire abubuwan da ta ɗebo nan ta shiga gwadawa, kama daga kan su kaya, ɗan kunnaye da sarƙa dasu awarwaro da ma kuma dayawa na ado.



Idanun DEENAH ne suka sauƙa kan wani sarƙa da ɗan kunnen GOLD na Ummar ta nan taje ta ɗauke shi tana faɗin "Anty wannan shine kyauta na ƙarshe da Abban mu yayi wa Ummar mu kafin ya rasu baikamata ki ɗauke shi ba."



Hannu tasa ta fuzge tare da tsinka mata mari tace "Na ɗauke ɗin munafuka, idan Ummar taki ta dawo kice mata ni Rabi'atu ce ta ɗebe mata kaya, wadannan tsadaddun kayan ni yakamata na dinga sanƴa su ba Ummar ku ba, dalla wuce ki bani wuri koh na ham6are ki yanzun nan."


Ficewa tayi daga cikin ɗakin idanun ta na tara hawaye.


Sosai ta gyara mata koh ina sai tada ƙamshi yake, bayan ta gama yi mata gyaran ne kuma ta sake loda mata uban wanke-wanke da wankin kayan ta da basu wuci kala huɗu ba ta wanke.



Sosai DEENAH ta gaji wanda har tana yin aikin tana kuka, sosai jikin ta keyi mata ciwo.


Tana cikin yin wanke-wanken Kawu ya dawo da cefanen da yaje iyowa.



Sai a sannan ne Rabi'atu ta ta6uka abu wurin yin aikin gidan nata, sai dai dukda haka bata bar DEENAH da ɗaukomin wancan ɗaukomin wannan ba.



A haka ta gama girkin ta sai dai koh ta6i bata baiwa DEENAH ba dukda kuwa uban aiki da gajiyar da tayi, ga kuma ƴunwa da takeji.


Part ɗinsu ta koma tayi wanka ta shirya cikin atamfa ɗinkin riga da skirt kafin ta samu wuri ta kwanta.



Cikin bacci taji ana shafa ta, kafin taji an fara ɗaga mata skirt ɗin dake jikin ta.



A razane ta buɗe idanun ta tana sauƙe su cikin na Kawu dake shirin zare igiyar wandon sa.



Ihu tasa nan yayi saurin rufe mata baki yana zare mata jajayen idanun sa yace "Idan kika kuskura kika yi ihu, sai na ɗauke ki na maida ki ƙauye, sannan kuma duk wani aiki na Rabi'atu ke zaki dinga yinsa, kuma makarantar boko da ta islamiyya babu ke babu zuwa har abada."



Sosai jikin DEENAH ya kama rawa kuka kuwa harda majina, nan fah kawu ya fara kiciniyar ware mata ƙafafu inda ita kuma take matse wa.



Wani uban rankwashi ya zuba mata a tsakiyar kai yace "Ba zakiyi shiru ba sai kin tona min asiri?."


"Dan Allah Kawu kayi haƙuri, mai kake son yi min dan Allah kayi haƙuri wallahi banyi maka laifin komai ba, kada ka dake ni."



Sosai Kawu ya haɗa uban gumi fuskar nan tasa yawa an naushi fura, idanun sa wuri-wuri yake lashe baki yace "Ba dukan ki zanyi ba, ƙafafun ki kawai zaki buɗe min, wani abu mai daɗi zanyi miki, sannan kuma kada ki faɗa wa kowa kinji" ya faɗa yana ciro naira ashirin a cikin aljihun sa yace "Sannan kuma idan kika yarda nayi miki ,zan baki wannan kuɗin ki sayi minti, ai kinaso koh?."



"Dan Allah Kawu ka sake ni, ai Umma tana saya mana mintin da yafi na ishirin ma, dan Allah Kawu kayi haƙuri."



"Ke kinga ki barni nayi abinda nazo yi cikin kwanciyar hankali, kinga babu kowa a cikin gidan nan, daga ni sai ke dan kuwa Rabi'atu ma ta fice ungwa, kuma kinga koh sha biyun rana batayi ba balle a taso su yayan ki daga makaranta, babu mai kwatar ki dan koh kinyi ihu ba wanda zai jiyo ki" ya faɗa yana kai hannun sa cikin skirt ɗinsa.



A razane tasa ihu tare da gantsara masa cizo a kunne kafin ta fito a guje.


A razane ya tashi cike da firgice wa ya ɗau hular sa ya bi bayan ta, sai haɗa uban zufa yake.



DEENAH kuwa tuni ta fice a gidan sai falfala gudu take da dagaggen skirt a hanƴa tana ihu da kuka, sai dai kamar haɗin baki babu kowa anan hanƴan kasnacewar ungwa ce da kowa na cikin gidan sa musamman ma da yau ranar aiki dayawa sun fice zuwa wurin aiki da makaranta.



Tuntu6e taci ta faɗa kan wani tsohon langa-langa inda ya yanke ta a ƙafar ta sosai take kuma jini ya 6alle ya fara zuba.


Hango Kawu da tayi a bayan ta ne yasa ta tashi ta ƙara ƙaimin gudun ta.



Tundaga inda yake zaune jugum dashi ya hango ta da gudu tana kuka.



Miƙewa tsaye yayi yana taro ta cike da tashin hankali ganin yadda take ta zuba kuka.


"Hey, mai ya sameki, mai yasa kike kuka, waye ya dake ki?" ya faɗa cikin jero mata tambayar.



Turus Kawu yayi yana kallon su cike da tashin hankali ganin DEENAH na nuna shi da hannu.


"That Monster, mai yayi miki?."


"Shine yace wai na buɗe masa skirt ɗina" ta faɗa cikin kuka sosai.


Jin ta ambaci skirt ne yasa shi maida duban sa kan skirt ɗin, nan yaga jini na biyo mata ƙafa ya 6ata mata skirt ɗin.


Sosai zuciyar sa ta hau bugu, gashi bata bar kuka da maimaita "Shine yace wai na buɗe masa skirt ɗina."



ZEEYAD da bai fahimci mai take cewa bane yasa shi nufar Kawu tare da cakumo wuyar rigar sa yace "Mai kayi mata?."


Cike da hargowa Kawu ya fara ihun "Jama'a a kawo ɗauki zai yiwa yarinƴar mutane faɗe, zumu zumu na kama sa yana shirin ƙetawa ƴata haddi, jama'a a kawo ɗauki" yadda Kawu yake ihu ne kuma yasa mutane suka fara taruwa, da kuma wadanda suke kan hanƴar wucewa duka, kan kace miye kuma wurin ya cika da jama'a gashi har yanzu Kawu bai bar faɗin cewa "ZEEYAD zaiyi wa DEENAH fyaɗe ba."


Wani dattijo ne yace "Haba malam Sale ka dawo nutsuwar ka mana haka nan kayi mana bayanin abin dake faruwa."


"Ya kake nayi, tayaya za'ayi na dawo cikin nutsuwa ta yana shirin lalata rayuwar marainiyar Allah, bamu san shi ba, bamu san daga wace nahiyar ya faɗo ba, yau rana tsaka na kama sa da wannan mummunar laifi."


"Mai kake son faɗa ne haka?."


"Gashi nan, wannan balaraben shi na kama yana shirin yiwa yarinƴa ta fyaɗe yau."



"Inalillahi wa inna ilaihi raji'un" duka ƴan wurin suka faɗa kafin kuma duk su rirriƙe ZEEYAD da baisan mai ke faruwa ba, bai kuma san abinda suke faɗa ba.



"Kai ku tsaya, ku tsaya, bari muji komai daga bakin ita yarinƴar tukun" faɗin dattijon nan kafin su nufi wurin DEENAH dake tsaye har yanzu tana kuka da alama bata cikin hayyacin ta sabida tsorata da tayi, ga kuma cinƴar ta da ta matse guri guda tana cigaba da kuka.



Wannan dattijon ne ya nufi wurin ta yace "Ke yarinƴa kinsan wannan?" ya faɗa yana nuna mata ZEEYAD.



Abinda take nanatawa ta sake faɗa "Shine yace wai na buɗe masa skirt ɗina."



"Inalillahi wa inna ilaihi raji'un" duk ƴan wurin suka hau nanatawa.


"Kun gani koh ai na faɗa muku, wannan dama daga ganin sa ba shida aiki sai lalata yaran mutane, na daɗe da fara zargin sa, toh wallahi ba zan yarda ba, dole ne a kirawo hukuma suyi gaba dashi, dole ne a samarwa ƴata ƴancin ta wallahi, dan kuwa ba zaiyiwu ya lalata mata rayuwa bane ba kuma na kyale shi."


Kan kace miye kuma har an kirawo ƴan sanda, ZEEYAD da sai yanzu ya fahimci abinda ke faruwa ne yace "Babu abinda nayi mata, mai zai sa nayi mata haka, itace tazo wuri na wannan mutumin na biye da ita" ya faɗa yana nuna Kawu.


Ɗaya daga cikin mutanen ne yace "Ƙarya kake yaro, na daɗe da sanin irin ku, yau Allah ya toni asirin ka, kanaso kayi wa yarinƴa fyaɗe sai kuma Allah ya kama ka, dole ne ƴan sanda su zo su tafi da kai wallahi" cewar wannan mutumin cikin muryar turanci, sai a sannan ZEEYAD ya fahimci Kawu sharrin yiwa DEENAH fyaɗe ya ɗaura masa.



"What, fyaɗe?, bani bane i would never do such thing, shine yayi mata fyaɗe, and she came running to me for help, you can asked her again bani bane nayi mata fyaɗe."



"Karya kake ita ma ai yarinƴar an tambaye ta kuma tace kai ne kayi mata fyaɗen, yanzu dai an ƙira Uwar Yarinƴa da ƴan sanda suna kan hanƴar zuwa dole ne kayi bayani wallahi" nan suka sake ƙanƙame sa yayin da wasu kuwa har sun fara kai masa duka.


Kawu kuwa babu abinda yake cewa sai "yauwa ku ƙara masa, shine, shine wallahi sai hukuma sun hukunta ka, macucin banza da wofi" ya faɗa yana yin wurin DEENAH tare da kamo ta, kafin ya sunkuya ta saitin kunnen ta ganin hankalin mutane ya koma ga ZEEYAD ya raɗa mata "Kina jina wallahi kika kuskura kika ce nina nayi miki abinnan sai na kashe Mamar ki da Yayan ki, sannan kuma na maida ki ƙauye ba zaki sake dawowa nan ba ,idan Ummar ki tazo kice mata shine yayi miki hakan idan kika kuskura kika ce nine sai na yanka ki na binne ki, kinji?" ya faɗa yana muskular ta.



Kai kawai ta jinjina masa jin abinda ya faɗa, kafin kuma ya cigaba da faɗin "Ku ƙara masa, koh ku kashe sa ma shine daidai."



Motar ƴan sanda ne suka iso wurin tare da Ummar su DEENAH, babu abinda take faɗi sai kiran sunan DEENAH cikin kuka, jin abinda aka faɗa mata a waya an yiwa DEENAH fyaɗe.



Da sauri ta nufi wurin DEENAH dake tsaye tana ta kuka tare da rungumo ta tace "Inalillahi wa inna ilaihi raji'un, Wane azzalumin ne ya aikata miki haka?, mai kikayi masa da zai nemi 6ata miki rayuwa...?"


"Gashi nan, gashi nan shine wanda yayi mata fyaɗe" cewar Kawu yana nuna ze da ya sha bugu a hannun jama'a, inda dakyar ƴan sanda suka kwace shi.



Da sauri ta miƙe tana kallon ZEEYAD ɗin zuciyar ta na yi mata zafi kamar zai fito waje, cukumo sa tayi tace "Kai ne, kai ne kayi mata fyaɗe, kai ne kayiwa DEENAH ta fyaɗe, mai tayi maka da zaka saka mata da wannan mugun aikin, maiyasa, har kai wanene da zaka ta6a jikin ƴata kayi mata fyaɗe?" ta ƙarashe tana zuba masa mari a ƙunci tana jijjiga shi.


"I...i didn't do it, i swear i didn't do it, bani bane, ba zan ta6a yin hakan ba, ki yarda dani."


"Na yarda da kai, bakada hankali ne?, wallahi sai ka fuskanci hukunci mai tsanani sai kayi nadama aikatawa ƴata haka, koh dan saboda kai sai nayi dukkanin yadda zanyi na cika buri na na zama Lawyer, sai na tabbatar da anyi maka hukuncin da ba zaka ta6a fitowa daga gidan yari ba muddin ka tafi."



Da kyar ƴan Sanda suka raba riƙon da tayi wa ZEEYAD, nan kuma aka karkata ƙeyar su dukkanin su zuwa police HEADQUATER dan ɗaukar bayanai.



Isar su keda wuya dukkanin su aka kai su wani office harda ZEEYAD da aka garƙama wa handcuff a hannu.



Kujera aka bawa Ummar su DEENAH da har yanzu bata bar kuka ba, kamar wacce ake sarar naman jikin ta, sosai takejin zuciyar ta kamar ta fito waje.


Kawu ma samun wuri yayi ya zauna sai zazzare idanu yakeyi, yawa tsohon munafiki.


Nan fah aka fara ɗaukar Statement ɗin kowa daga cikin su.


Kawu ne ya fara da faɗin "Na aike ta shago akan ta sayo min ruwan sanƴi sabida matata Rabi'atu bata nan bansan inda ta sanƴa makullin firijin mu ba, ta kai kusan awanni biyu bata dawo ba, hakan yasa ni yanke shawarar bin bayan ta, anan ne kuma na tarar da wannan mai jan kunnen yana aika mata mummuna" ya faɗa cikin fashewa da kukan munafurci.


Nan aka dawo kan ZEEYAD aka tambaye sa koh gaskiya ne abinda kawu ya faɗa nan yace "Bani bane, bani bane nayi mata hakan, zaku iya tambayar ta, bani bane."



"Sau nawa kakeson a tambaye ta, bayan kuma ita yarinƴar ta shaida cewa kai ne kayi mata hakan."


"Ku sake tambayar ta, little DEENAH nine nayi miki hakan?."


Shiru kawai tayi tana bin kowa da manƴan idanun ta da suka kumbura da kuka,kafin ya sake faɗin "Tell them, ba ni bane koh?" ya faɗa yana kallon ta.


Ɗan sandar nan ne ya tambayi DEENAH yace "Kada kiji tsoro kinji, babu wanda zai iya ta6a ki anan, ki saki jikin ki kinji?."


Kai ta jinjina nan yace "Good girl, yanzu faɗa mana wanene yayi miki abinnan?."


Shiru tayi tana binsu dukkanin su da idanu, inda Kawu kuwa babu abinda jikin sa da zuciyar sa keyi sai rawa.



Maida duban ta tayi kan ZEEYAD tana kallon cikin kwayan idanun sa kamar yadda shima yake kallon nata.



Maganar da kawu ya faɗa mata ne ya shiga dawo mata kai


_"Idan kika kuskura kika yi ihu, sai na ɗauke ki na maida ki ƙauye, sannan kuma duk wani aiki na Rabi'atu ke zaki dinga yinsa, kuma makarantar boko da ta islamiyya babu ke babu zuwa har abada."_


Kafin kuma ta sake tuna

_"Kina jina wallahi kika kuskura kika ce nina nayi miki abinnan sai na kashe Mamar ki da Yayan ki, sannan kuma na maida ki ƙauye ba zaki sake dawowa nan ba ,idan Ummar ki tazo kice mata shine yayi miki hakan idan kika kuskura kika ce nine sai na yanka ki na binne ki, kinji?"_



Hawaye ne suka shiga kwaranƴo mata daga idanu, batason rasa Mahaifiyar ta sannan batason rasa ɗan uwanta mafi soyuwa a gareta, dukkanin su su biyun nan sunada muhimmanci a rayuwar ta.


Idan ta ɗaurawa balarabe sharri bata kyauta masa ba, sabida yana da kirki sannan kuma yayi mata zanen hoton ta dama kuma na yayan ta da Ummar ta, idan tayi masa sharri bata kyauta masa ba sannan kuma ba zai ta6a yafe mata ba.



Kawu kuwa zai iya aikata abinda ya faɗa akanta muddin bata ce Balarabe bane yayi mata hakan.


Sake tsinkayo muryar Police yayi yace "Kada kiji tsoro ki faɗa mana wanene?."



Idanun ta a cikin na ZEEYAD dake kallon, kafin kuma ta ɗau hannu a hankali tana pointing ɗinsa tace "Shine."



"Kun gani koh, mai na faɗamuku, ai na faɗa muku cewa shine, munafukin banza da wofi" faɗin Kawu.


"What, me?" ya faɗa cikin rawar murya.



A hankali ya shiga girgiza mata kai yace "No, she is lying, bani bane, she is lying to me i would never do this" ya faɗa idanun sa na yin jaa sosai yana kallon DEENAH cikin 6acin rai.



"Tell them, tell them the truth, tell them that i didn't do it, tell them" ya faɗa mata a tsawace yana fitar da zazzafar huci.



Hannu Ummar DEENAH ta ɗauka ta wanke fuskar sa da mari tace "How dare you, how dare you raise your voice on my daughter, ba zata yi ƙarya ba, kai ne mana ka aikata mata hakan, idan ba kai bane ba zata ta6a nuna ka ba sabida yarinƴa ta bata ƙarya."



"DEENAH stop pointing and tell them the truth."


"What truth?" faɗin Police yana tashi tsaye cikin 6acin rai kafin kuma yasa azo a kama ZEEYAD ɗin a tafi dashi.



Rirriƙe sa sukeyi sai dai yaƙi tashi tsaye kamar ya kwace haka yake zaburowa yana kallon DEENAH da har yanzu bata sauƙe hannun ta kan pointing ɗinsa ba.



Abar wuyar sa ce ta tsinke ta faɗo bai saniba, sabida baya cikin hayyacin sa, burin sa kawai ta buɗi baki tace ba shi bane.



Da kallo tabi abin dashi har aka fice daga office ɗin da ZEEYAD yana kiran sunan ta.



Duk mara musu baya ƴan cikin office ɗin sukayi kafin kuma ta sunkuya ta ɗauki sarƙar tana kallo.


Police ɗinne ya dawo yace mata "zo" nan ta damƙe sarƙar a hannun ta tana binsa.


Jikin Ummar ta taje ta raku6e tana cigaba da kuka mai ƙarfi.


"Kada ki damu insha Allah sai anyi masa hukunci daidai da abinda ya aikata miki, muje" faɗin Ummar tata itama cikin kuka.



Sai a sannan kuma aka kaita asibiti dan yi mata gwaji dama kuma duba lafiyar ta.................







*MHIZZ JIDDHERR................✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```



*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





_Da yawan ku na cewa wahalar ZEEYAD tayi yawa a sassauta masa, sai dai fah ku sani ba zan canza koh da (A) bane daga cikin labari na, idan zaku karanta a yadda tsarin labarin yazo ku karanta, idan kuma baiyi muku ba na ajiye abina, dama dan ku karanta nakeyi idan kuma kunce bakwa so toh nima kun kawo min sauƙi, sai na ajiye shi kawai, dan haka ku bar ni na tafiyar da abuna yadda na tsara shi please👏🏽, babu abinda zan canza a ciki._





*012...*





...........Koh da sukaje asibiti gwaje-gwaje akayi mata sosai, nan dai aka gano babu wata matsala tattare da ita sannan kuma ba'a yi mata fyaɗe ba, illa ciwon da taji kawai da akayi mata dressing ɗin shi.



Sosai zuciyoyin kowa ya cika da mamaki jin ba'a yiwa DEENAH fyaɗe ba, nan kuma aka fara tuhumar ta akan mai ZEEYAD ɗin yayi mata.


Cikin kuka tace "Babu abinda yayi min, shine yace wai na ɗaga masa skirt ɗina" ta faɗa tana goge hawayen fuskar ta da hannu ganin Kawu na zare mata ido ta baya.


"Yayi attempting yin fyaɗen ne kenan, duk da haka yanada laifi sannan kuma sai hukuma ta hukunta shi da izinin Allah" cewar ɗan Sanda.


"Toh ai shikenan, mu godewa Allah da bai kai ga lalata mata rayuwa ba, ke kuma Fatima ki dinga kula, shiyasa nace zan ɗau yarinƴar nan na kai ta chan ƙauye wurin Uwar gida ta Rakiya amma kika ƙi, da achan take yanzu da babu abinda zai sameta" cewar Kawu.


Shiru kawai Umma tayi tana mai yin hamdala a ranta ganin ba'a lalatawa ƴar ta rayuwa ba.


Sallamar su akayi daga asibitin inda ɗan Sanda yace zasu cigaba da tuhumar ZEEYAD har sai sun gano wasu bayanan game dashi.


Gida suka dawo, abinci kawai Umma ta zuba mata ta bata magani ta sha sannan ta kwanta, har yanzun bata bar kuka ba, A haka bacci ya ɗebe ta anan wurin.



Bata farka ba sai bayan Azahar, dan haka sallah kawai tayi ta zauna ta sake dasa wani sabon kukan.



Zuwa Umma tayi ta zauna kusada ita tace "Menene kuma ƴar albarka, akwai inda keyi miki ciwo ne?."


Kai kawai ta girgiza mata tana cigaba da kuka.


"Toh maiyasa kike kuka?."


"Umma ni babu abinda yayi min ai baiyi min fyaɗen ba tukun kice a fito dashi dan Allah."


Shiru Umma tayi tana janƴo ta jikin ta ta share mata hawaye tace "Yi shiru toh haka nan ki daina kuka kar kisa wa kanki ciwon kai, ai koh bai kai ga yi miki wani abin ba ai yanada laifi tunda yana ƙoƙarin aikatawa ne aka kama shi, kinga dai da abinda ya saka miki koh?, da zuciya ɗaya kika ɗauke shi, kinyi masa halacci ba tare da sanin koh wanene shi ba, yanzu da ya kai ga lalata miki rayuwa fah?, dole ne a hukunta shi sabida gaba, yi shiru haka nan kinji?."



Jafar dai kawai da idanu yake bin su, amma sam bai yarda da abinda DEENAH ta faɗa ba, haka kuma bai yarda da Kawu ba, ganin yadda yake ta rawar ƙafa tunɗazu yana zuwa ya tambayi lafiyar DEENAH abinda bai ta6a yi ba kenan.


Rarrashin ta Umma tayi har saida tayi shiru kafin kuma ta fice zuwa ɗaki.


Sauƙowa Jafar yayi zuwa inda take zaune yace da ita "Kiyi haƙuri DEENAH ki daina kuka haka nan kinji, ai kince baiyi miki komai ba koh?."


Kai ta jinjina masa, nan yace toh "Idan baiyi miki komai ba, waye ne yayi miki, kuma mai ya kai ki wurin shi?."


Shiru tayi bata basa amsa ba tana cigaba da kuka.


Dube-dube ya hau yi kafin kuma cikin raɗa yace "Kawu ne koh?."


Da sauri ta hau girgiza masa kai tana faɗin "Ba shi bane Allah."


"Ƙarya kikeyi DEENAH, Kawu ne yayi miki haka, shine yace ki ɗaurawa balarabe sharri, ke kuma kika ɗaura masa dan kawai ya tsoratar dake da wani magana tasa, ke kuma kika yarda zai iya yin hakan, kika ɗaurawa balarabe sharri, kinsan miye Balarabe yace min ɗazu da safe da na kai masa abinci?."



Shiru tayi bata basa amsa ba, nan ya cigaba da faɗin "Cemin yayi kina da kirki, tunda ya shigo Nigeria bai ta6a haɗuwa da mutum ɗaya daya taimake sa dan Allah har yaji tausayin sa ba sai ke, yace na baki haƙuri da ce miki mayya da yayi a baya dama kuma wulaƙancin da yayi tayi miki idan kin kai masa abinci yaƙi ci, sannan kuma yace a shirye yake yayi miki wani zanen muddin zaki cigaba da farin ciki, yace min kece Mace ta farko da ya fara yarda da ita tun bayan mutuwar mahaifiyar sa, sai dai kuma a yau DEENAH kin ruguza yardar da yayi miki, shi mai son ganin ki ne kullum cikin farin ciki sabida kema kinyi iya ƙoƙarin ki na ganin ki sanƴa sa farin ciki, sai dai kuma a yau kece kika ruguza masa wannan farin cikin, ya bani labarin sa kuma shi ɗin abin tausayi ne sosai, sai gashi kuma yau rana tsaka kin sake kwa6e komai kin cusa masa ƙunci ta hanƴar yi masa sharrin yunƙurin yi miki fyaɗe bayan kuma bashida laifi sai ma ƙoƙarin sa na kare ki da yakeson yi, ke butulu ce DEENAH kuma nasan balarabe ba zai ta6a yafe miki ba akan wannan sharri da kikayi masa, sannan kuma ba zai sake yarda da kowa ba, sabida ya ɗauka ke ɗin mutuniyar kirki ce..."



Kukan da ta fashe dashi ne yasa shi dakatawa da zancen sa bai idda ba, Umma ce ta fito daga ɗaki jin ta fashe da matsanancin kuka nan ta hau faɗin "Menene kuma, miye yasa ta kuka, Jafar kai ne koh, mai ka faɗamata?."



Tashi yayi tsaye yace "Umma ni babu abinda na faɗamata sai gaskiya."



"Jafar zan sa6ar maka fah, fice ka bani wuri kai da zaka kwantar mata da hankali kuma shine zaka sake sanƴa ta cikin damuwa, haka na koyar da kai halin yaya na kwarai?."


Ficewa Jafar yayi dan kuma sosai yaji haushin DEENAH dan ya gane cewa sharri ne tayi wa Balarabe.


Rarrashin ta Umma ta fara sai dai kamar sake zuga ta take, da kyar dai ta samu ta ɗan sarara da kukan bayan tayi mata alƙawarin zata sa a fito dashi..........



********************



........Yau sati biyu da faruwar wannan lamari, kuma har yanzu DEENAH bata bar kuka ba ga wata iriyar rama da tayi, sosai takejin wani abu a zuciyar ta da ta kasa gane koh menene shi, wanda yake yawan sata rashin sukuni, kullum jin zuciyar ta take a cunkushe, bata da wata walwala.



Tun Umma na lallashin ta kullum har ta gaji ta daina kula ta, ga Jafar ma yanzu ya daina sakar mata fuska yana kula ta kamar dah, Islamiyya ma ya daina zuwa tare da ita komai shi kaɗai ɗinsa yakeyi ya daina kula DEENAH muddin ba ta faɗi gaskiyar Kawu ne ya sanƴa ta aikata hakan ba.


Ita kuwa DEENAH sosai ta ɗau maganar Kawu da gaske dan kuwa babu ranar da zasu haɗu bai sake yi mata warning ɗin da yafi na dah firgitar wa ba, dan har wuƙa yana cire mata yace dashi zai kashe Umma da Jafar, wannan ne dalilin da yasa har yanzu ta kasa faɗar gaskiya sannan kuma take jin zuciyar ta a cunkushe.


6angaren ZEEYAD kuwa watanni shida aka yanke masa zama gidan yari, dukda an gano baya harƙallah da kowa kuma shi kaɗai ke rayuwa bai sanƴa an sake sa ba, sabida kawai laifin da aka ɗaura masa na yunƙurin aikata fyaɗe.


Sosai yakejin tsanar DEENAH a zuciyar sa, ta ruguza masa komai na rayuwa, sanadiyyar ta zai 6ata watanni shida a kurkuku, sanadiyyar ta yayi losing diamond Necklace ɗinsa that is worth billion of dollars, the last gift da Mahaifiyar sa tayi masa, dashi ne yake tuna Mahaifiyar ta and now yayi losing ɗin wannan Necklace ɗin yayi losing farin cikin sa har abada, ji yake ya tsani komai ya tsani kowa, sai dai tsanar da yayi wa DEENAH ya wuce gaban misali, da farko ya ɗauka ita ɗin mayya ce sai dai kuma a yanzu ya gano sharrin ta ya wuce gaban na maita, ita ɗin annoba ce sannan kuma shaiɗaniya kamar yadda ya ɗauke ta.



Koh wane bugun zuciyar sa na bugawa ne da tsanar DEENAH, a yanzu ji yake babu babbar maƙiyar sa a duniya da ya

Please Login or Register in order to submit comment