Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cike da mamaki yace "Did i really ate it all alone?" ya tambayi kansa.

Sam baiji daɗin cinƴe chips ɗin da yayi a zama ɗaya ba, dan kuwa ba ƙaramin daɗi yayi masa ba, haka nan yayi ta kora zallar coffee ɗinsa yana 6ata fuska.

Bayan ya kammala dukkanin aikin da zaiyi cikin System ɗin tasa ne kuma ya ɗau wayar sa ya shiga kiran Grandma.

Kamar jira take tana ɗauka tace "Assalamu Alaikum Habiby."

Murmushi ZEEYAD yayi yace "Wa'alaikumusalam Grandma, ya kika san cewa nine?."

"Ya ba zan san cewa kai bane, bayan sunan ƙasar da kaje ya fito jikin lambar taka."
Ɗan murmusawa yayi yace "I miss you so much Grandma."

"Nima gani nan ka barni da kewar ka, shima YAZEED ɗin dake ɗan tayani hirar yayi tafiyar sa yin uzurin gaban sa, ni kaɗai yaushe zaka dawo ne?."

Murmushi yayi yace "Grandma, koh kwana ɗaya banyi ba amma har kin fara tambayar yaushe zan dawo?."

"Toh ai ka barni ne da kewar ka Habibi."

Murmushi kawai yayi yana mai son tambayar Jalilah sai dai yasan yana kama sunan ta yanzu Grandma ba zata barsa da tsokana ba.

"Ka kira mai Martaba kuwa Boy?" ya tsinkayo muryar Grandma.

Idanu ya ɗan lumshe ya buɗe kafin yace "No Grandma?."

"Maiyasa?" ta faɗa.
"Actually Grandma, i was busy all this while and have to cover abubuwan da banyi scheduled ɗinsu cikin ayyukan da zanyi yau ba, i was very tired and need to rest a bit so i take a Nap, daga nan kuma i had my lunch sannan nayi ƴan wasu ayyuka a system ɗina, so i decided to call you first kafin wani abin ya sake shige min gaba, banma wani samu hutun da zan tsaya kiran mutane ba."

"Um um Boy, mahaifin naka ne mutane?, yanzu ka kira ni kaji lafiya ta am totally fine sai dai kawai kewar ka, you should call your father now sabida nasan shima yana chan yana ta tunanin ka, i know he must be so worried about you."

"Alright Grandma" ya faɗa a hankali.

"Good Boy, toh yanzu sai yaushe kenan?."

"Maybe later, maybe tomorrow Morning" ya faɗa.

"Toh shikenan, sai na sake jinka koh?."

"Yes Grandma take care."
Yanke kiran tayi, ajiyar zuciya ya sauƙe kafin ya shiga lalu6o lambar mai Martaba ɗin cikin wayar sa.

Ta6e baki yayi ganin bashida contact nasa kafin kuma ya nemo landline ɗin cikin fadar dan kira koh zai same shi.


********************


Duk zaune suke suna yin Dinner kasancewar dare ne a wurin su.

Ƙarar Telephone ɗin da ya kauraɗe ilahirin Babban falon ne ya sanƴa su maida duban su gun da Telephone ɗin ke ajiye.

Ɗaya daga cikin guards ɗin cikin falon ne ya ƙaraso yana ɗaukar ƙiran tare da karawa a kunnen sa.

"Hello" ya faɗa.
Kallon inda mai Martaba ke zaune yayi kafin kuma yace "Yes, Who are you?."

6angaren ZEEYAD jin yace masa wanene shi ba ƙaramin haushi yaji ba, dakewa yayi yace chan ƙasan maƙoshi yace "ZEEYAD."

Rissinar da kai dogaran yayi kamar wanda yake gaban ZEEYAD ɗin yace "Afuwan Prince, hold on zan kai masa wayar yanzu" ya faɗa yana ɗaukar Telephone ɗin yayi wurin mai Martaba dashi yayin da duk ƴan dining ɗin suka biyo shi da kallo su Naseeba da Hafeezah kamar idanun su zai faɗo ƙasa.

Rissinar da kai yayi cike da girmamawa yace "Your Highness Prince ZEEYAD wants to talk to you."

Hannu na rawa mai Martaba ya kar6i Telephone ɗin yana karawa a kunnen sa tare da yin sallama.

Ajiyar zuciya ZEEYAD ya sauƙe daga ɗayan 6angaren yana amsa sallamar mai Martaba.

"How are you Son?."

"Am good and you?."

"Alhamdulillah" cewar mai Martaba cike da farin ciki sannan yace "Ina fatan ka sauƙa lafiya?."

"Lafiya, Alhamdulillah" ya amsa.

"Masha Allah."

Shiru ZEEYAD yayi kafin yace "Are you Okay i mean ya ƙarfin jikin ka?."

Farin ciki ne ya cika mai Martaba nan yace "Alhamdulillah."

"And kasha maganin ka?."

Kai ya jinjina kamar yana gaban sa yace "Yanzu mukeyin dinner, da zaran munyi kuma zan sha maganin."

"Okay, Good" cewar ZEEYAD.

YAZEED ne ya taso daga inda yake yana amsar wayar a kunnen mai Martaba yace "Sorry Abhi" kafin yace "Hey bro."

Murmushi ZEEYAD yayi jin muryar YAZEED yace "Hey dude, what's up?."
"Yane, ka sauƙa lafiya?."

"Yeah Alhamdulillah, how is Grandma kaje wurin ta right?."

"Yeah, ban daɗe da barin wurin ta ba, but zan koma when i finished having my supper."

"Alright good, take care of her please, and...and make sure mai Martaba yasha maganin shi."

Juyawa YAZEED yayi yana kallon mai Martaba dake kallon sa yace "Yeah insha Allah, i will" ya faɗa cikin murmushi.

Sallama ZEEYAD yayi masa kafin ya katse kiran.

Juyowa YAZEED yayi nan duk yaga suna binsa da kallo, wani irin haɗe fuska yayi musamman yadda yaga Ummien sa ke wurga masa mugun kallo, ɗaga gira ɗaya yayi yace "What, why are you all staring?" ya faɗa yana miƙawa guard Telephone ɗin hannun nasa.

Duk kauda kai sukayi suna maida duban su kan abincin da suke ci.

Kujerar sa yaja ya zauna yana mugun haɗe rai ganin har yanzu mahaifiyar tasa bata daina kallon sa ba.

Miƙewa tayi tace "YAZEED?."

Ɗagowa yayi yana kallon ta, nan tace "I need to talk to you" tana faɗin haka ta bar wurin a fusace.

Da wani irin kallo ya bita kafin ya tashi yana mai mara mata baya.

Sarauniya Nazeerah murmushi ta saki, yayin da gefe guda kuma takejin haushin missing ɗin drama da zatayi.

Part ɗinta ya bita tana mai rufo ƙofar ɗakin, kallon sa tayi tsaf kafin tace "How many times do you want me to warn to stay away from that boy..."

"Oh hold it please, dama abinda ya sanƴa ki kira na nan kenan, i thought it was something important da kikeson discussing" ya faɗa yana niyyar barin ɗakin.

"Wait right there" ta faɗa cikin kakkausar muryar dake nuna alamun ranta ya 6aci sosai.

Tsayawa YAZEED yayi ba tare da ya juyo ya kalleta ba.

Ƙarasowa gaban sa tayi, kafin ta nuna shi da yatsa cikin fushi tace "You just listen to me Okay?, i want you to separate all ties with that boy, you think cewar yana ƙaunar ka kamar yadda kake ƙaunar sa ne, he is supposed to be your enemy, someone da zakayi kishi dashi sakamakon abubuwan da ya mallaka, after all dukiyar da ya tara kuma shi ne wannan zai zamto heir ɗin family ɗinnan, amma duk da haka kullum kana maƙale dashi sabida rashin zuciya irin taka sannan kuma bakasan abinda kakeyi ba, he is more successful than you, you're supposed to be envy of him, baikamata ku dinga haɗa inuwa ɗaya dashi ba, koh bakaga yadda Sooraj yakeyi bane maiyasa ba zakayi koyi dashi ba..."

"You just shut up and reserve your words please" ya faɗa cikin 6acin rai yana wurga mata mugun kallo kafin ya ɗaura da faɗin "Kada ki sake kwatanta ni da that fool called Sooraj, i wonder ke wace iriyar mahaifiya ce mai yiwa ɗanta mummunar huɗuba, koh dayake duk a banza kikeyi sabida ba zan ta6a ɗaukar koh ɗaya daga cikin abubuwan da kike faɗamin ba, think about it koh da nake ɗan ƙanƙani ban biyewa gurguwar shawarar ki ba, sai yanzu kike tunanin zanyi obeying ɗinki after nasan ciwon kaina na kuma gane abinda yake dai-dai dama kuma wanda yake ba dai-dai ba?, idan halayen Sooraj na birgeki why not then kawai ki zamar dashi ɗan ki nikuma kiyi watsi dani, listen mother indai dani kikeson amfani wurin cimma mummunar manufar ki then you made the wrong choice, who even cares about wani mulki, as far as inada hanƴar samun kuɗi na wanda zan iya kula da family ɗina ba tare da sun nemi wani abu sun rasa ba then am good with it, but maganar wani mulki ki ajiye shi a gefe, sabida bani da ra'ayin sa, Okay?" ya ƙarashe yana mai watsa mata mugun kallo cike da haushi dama kuma baƙin cikin kasancewar ta mahaifiyar sa.

Murmushi mai ciwo tayi tace "Hmm, Wow YAZEED ni kake faɗawa magana son ranka kamar wanda ba nice na sha wahalar haihuwar ka ba, na sha wahalar goyon cikin ka tsawon watanni tara sannan na shayar da kai for good 2years, amma wai yau nice nake sanƴa ka abu kana ƙi har ma kake gayamin magana iya son ranka?, Wow YAZEED lallai wuyar ka ta kai yanka, ni Hafeezah mahaifiyar ka zaka kalla ido cikin ido sannan ka gayamin baƙar magana yadda kaso dan kawai ina neman maka abunda zai fice ka a rayuwa."

"No, no, no wait please" ya faɗa cikin ɗaga mata hannu kafin yace "upon all abinda kika lissafo banji inda kika ce kin zaunar dani kin koyamin tarbiyya ta hanƴa madaidaiciya ba, you're not a good Mom Ummie, har abada ba zan ta6a regretting kasancewar ki mahaifiya ta ba muddin baki canza halin ki ba, although nasan Allah ne ya ƙaddara cewar zan zamto ɗanki but...but sam ban ta6a ƙaunar ki ba, ZEEYAD's Mom itace Mahaifiya ta not you."

A matuƙar fusace cikin tsawa tace "Enough of this YAZEED, Queen Mother, Queen Mother, Queen Mother, Queen Mother my foot, bakada wani magana kullum da ya wuce ace itace uwarka, koh ka daina yimin maganar matacciyar nan kokuma ranka yayi mugun 6aci a cikin gidan nan, babu wanda ya ta6a ja da magana ta, kai ɗan da na haifa baka isa ka bijire min kuma na kyale ka hakanan ba, ya zama dole ne kabi umarni na YAZEED sannan ka rabu da ɗan wancan matacciyar tunda ba ciki ɗaya aka haife ka dashi, haka kuma kada na kuskura na sakejin labarin ka taka ƙafa zuwa wurin mahaifiyar matacciyar matar nan, that old hag nasan duk itace ke hure maka kunne kana sake bijirewa umarni ne, i have had enough of you da halayen ka YAZEED, whether you like it or not dole ne ka rabu dasu muddin ba so kake na ɗau mummunar mataki akanka ba, kai wane irin wawa ne marar wayon yaro?, ana nema maka arziki kana ta tsiya, kasancewar ka a successful Doctor\Surgeon ba shine zai sanƴa ni haƙura da ƙudiri na ba, why don't you understand YAZEED kasancewar ka Sarki is all i have dreamt of, so i would never allow you to ruin my plans, na daɗe da ɗaukar wannan alwashin a zuciya ta YAZEED, ya zama dole kayimin biyayya sannan kayi dukkanin abinda na sanƴa ka or else" ta ƙarashe cikin fiddo idanun ta da sukayi jaa sabida 6acin rai tana nuna sa da yatsa tace "Or else you will regret it" ta ƙarashe in a serious tone ɗin dake nuna zata iya aikata komai.

Light scoff YAZEED yayi yana tsuke fuska yace "You know what Ummie?, do your worst then" yana faɗin haka ya fice a fusace ya bar mata ɗakin nata.

Da mugun kallo ta bisa tanajin zuciyar ta nayi mata mugun tafarfasa yawa zai wantsalo waje tace "Kada ka kuskura ka kaini bango YAZEED, zan iya yi maka abinda baka ta6a tsanmani ba, but ya na iya i really need you to fulfill my dreams, thats the only reason kepting me away from doing something bad to you Son, but sooner or later haƙuri na zai iya ƙarewa daga nan kuma zan iya aikata koma menene, koh da kai baka cika min buri na ba then ni zan cika wa kaina da kaina" ta ƙarashe cike da muguwar ƙulin dake take ƙullawa cikin ranta ƙirjin ta na yin up and down tsabar fushin da take ciki.


**********************

_______B'angaren ZEEYAD kuwa tunda ya gama waya dasu ya kira Sadeeq suka gaisa.
Sallar La'asar yayi kafin ya sake ficewa, shine bai dawo ba har saida akayi isha yayi kafin ya dawo ya kwanta.

Washe gari ƙarfe takwas ya gama shirin fita, sai da yayi waya da Grandma tukun kafin ya fice zuwa Company ɗinshi.

Bayan yayi clearing dukkanin wasu abubuwan da zaiyi ne kuma ya wuce gym, kasancewar kwana biyu bai motsa jiki ba yasa duk yake jinsa wani iri.

Anan ya shafe rabin day ɗinsa kafin ya wuce gida ya huta.

Washe gari ma hakan ce ta kasance bayan yaje ya gama komai da komai nasa ya wuce gym sannan ya dawo gida, kasancewar gobe zai wuce wata ƙasar, daga nan kuwa ya wuco Nigeria dan kuwa so yake yaje ya gaida iyayen Khairat, dan kuwa mahaifin ta ba ƙaramin halacci yayi masa a rayuwa ba.


********************



_________Zaune suke da YAZEED da Grandma suna hira, inda duk ta lura YAZEED ɗin kamar da akwai abin dake damunsa.

"Ya dai Habibi meke damunka ne, kamar da akwai abin dake damunka dan kuwa ban saba ganin ka cikin halin ƙunci haka ba."

Ajiyar zuciya YAZEED ya sauƙe, zuciyar sa na mugun ƙuna yace "Grandma, are you sure cewar Ummie na ce ta haife ni?."

"Mai kake faɗa ne haka YAZEED, mahaifiyar ka ce fah dukkanin wani abu da zatayi maka baikamata ka ɗauke shi da tsanani ba dole ne kayi haƙuri ka dinga kauda kai muddin kanason gamawa da duniya lafiya."

"But Grandma matar nan batason na gama da duniya lafiya haka ma itama batason gamawa da duniya lafiya, batada wani buri a kullum da ya wuce ta dinga aikata munanan abubuwa take kuma son ɗaura ni akan hakan, Grandma that woman is nothing but a big mess to my life, ta sanƴa ni a gaba all she wanted shine na rabu da ɗan uwana haka ma kema na bar zuwa wurin ki, bansan menene abinda ZEEYAD ya tauye mata ba da tabi ta ɗau karar tsana ta ɗaura masa, i doubt idan ba uwa ɗaya bace ta haifeni da ZEEYAD kawai an ɗauke ni ne an baiwa matar nan just dan kawai bata samu haihuwa, but ba ita ce ta haife ni ba, ban ta6a ganin uwar da take neman buɗewa ɗanta hanƴar faɗawa halaka ba sai wannan matar, she is totally disgusting Grandma, idan nace miki ban tsane ta ba then nayi miki ƙarya" ya ƙarashe maganar kamar zai haɗiyi zuciya dan baƙin ciki, sosai fuskar sa ke nuna alamar tsantsar 6acin rai.

Sosai ya baiwa Grandma tausayi, cikin kwantar da murya tace "Kayi haƙuri YAZEED kaji?, addu'a zaka cigaba da yiwa mahaifiyar ka Allah ya shirye ta yasa ta gane dai-dai, but kasan kowace Uwa na ganin abinda ta yankewa ɗanta shine dai-dai a wurin ta, Uwa nada son kai a duk sadda take nemar wa ɗanta wani abu wanda take tunanin zai amfane shi, kada kaga laifin ta na tabbata dah zaka zaunar da ita kayi mata nasiha a matsayin ka na ɗan da ta haifa zata saurare ka sannan ta rage yin wasu abubuwan, take heart dear and ka cigaba da addu'a kaji?" ta faɗa tana shafa sumar kanshi.

Kai ya jinjina mata kawai idanun sa na yin jaa, rungumo sa tayi tana cigaba da kwantar masa da hankali tare da basa baki.


************************


________Sati biyu ZEEYAD yayi a ƙasar Poland kafin ya wuco Nigeria.

Ji yayi dukkanin tsigar jikin sa na tashi da isowar sa garin Kano.

Kai tsaye motocin da aka tanada wanda zasu ɗauke sa zuwa masauƙin sa ya nufa kafin a buɗe masa ya shiga suka ja tare da barin airport ɗin.

Kai tsaye Guest House ɗinsa aka kaisa, wanka yayi ya shirya cikin kaya marar sa nauyi kafin ya sauƙo ƙasa.

Ƙarewa gidan kallo yake, tabbas sosai yayi missing gidan, duba da nan ne wurin zaman sa kullum.

Ordern abincin da yayi aka kawo masa, sai da yaci tukun kafin ya shiga zagay gidan.

Wani corridor yabi cikin jerin ɗakunan dake cikin farfajiyar falon kafin ya buɗe ɗakin farko ya shiga wanda ya kasance ɗakin zanen sa ne.

Kallo yake ƙarewa fararen board ɗin zanen nasa dake rufe da fararen kyalle duk sunyi ƙura kafin ya taka ƙafarsa yana idda shigewa ciki duka.

Sauƙe idanun sa yayi kan board ɗin da yasan zanen ta ne a jikin su kasancewar ya ware su daban a gefe guda kafin ya taka ƙafarsa zuwa wurin.

Hannu yasa ya yaye farar kyallen board ɗin farkon inda zanen fuskar ta lokacin da take yarinƴa ya bayyana.

Kallon zanen yakeyi, kafin kuma ya shiga yaye sauran kyallen jikin sauran boards ɗin inda duka zanen kyakkyawar fuskar ta suka bayyana akai, da ɗaɗɗaya yake bin kowane board da kallo yanajin wani abu na taso masa daga chan ƙasan zuciyar sa, yayin da kuma ta wani fannin zuciyar sa cike take fal da 6acin ran da mahaifiyar ta ta ƙunsa masa da irin cin mutuncin da yayi mata dan kawai ya haukace a son ƴar ta.

Idanun sa ya lumshe yanajin yadda zuciyar sa ke zafi sosai.

Ficewa yayi daga ɗakin ba'a daɗe ba kuma ya dawo da galan ɗin kero dama kuma Ashana a hannun sa.

Ciro hotunan zanen yayi ya haɗe kansu wuri ɗaya, kafin kuma ya shiga tsiyaya musu kerosene ɗin.

Ta rigada ta zama tarihi cikin rayuwar shi, dan haka baya tunanin ajiye wani abu game da ita as a good idea,

Kyarta ashanar yayi ya shiga kallon flame ɗin wutar har sai da ta kusa mutuwa kafin kuma ya jefa ta kan photunan drawing ɗin, nan duk suka kama da wuta.

Sam baiji daɗin ƙona su ba, but bashida wani option da ya wuce yayi hakan.

Ɗakin ya baro kafin ya fito harabar cikin gidan nasa, securities yayi wa maganar suje su kula da wutar idan ta gama cinƴe hotunan su kashe sannan su tsaftace ɗakin, kafin ya dawo ciki suna mara masa baya inda ya haura sama su kuma suka nufi ɗakin zanen dan zuwa aiwatar da abinda ya sanƴa su.

Satin ZEEYAD biyu ya gama abinda ya kawo sa, inda ya sayar da duk wata ƙadara tasa da yasan yana da ita a Nigeria.

Tsaye yake gaban mirror yana gyara dressing ɗin blue ɗin suit ɗin dake jikin shi, wanda ba ƙaramin kyau da sake fiddo hasken fatar sa yayi ba.

Makullin motar sa ya ɗauka tare da ficewa daga cikin ɗakin yana sauƙowa ƙasa tare da ficewa zuwa harabar gidan.

Inda motar sa ke ajiye ya nufa ya buɗe ta ya shiga, kasancewar an buɗe masa gate ya sanƴa shi jan motar tare da barin harabar gidan zuwa gidan su Khairat.


*******************

________Kasancewar securities ɗin gidan sun waye shi ya sanƴa su buɗe masa tafkekiyar gate ɗin gidan yana kutsa kai ciki.

Parking ɗinta yayi a parking space, kafin ya buɗe ta ya fito yana maƙala baƙar shade ɗinsa.

Bai wuci 5mins a tsaye ba ya hango Khairat ɗin da iyayen ta sun nufo shi.

Khairat ganin ZEEYAD ba ƙaramin sake losing control ɗin kanta tayi ba, wani irin ƙara tasa tana iyowa kanshi da gudu da niyyar rungume shi.

Cire baƙar shade ɗin fuskar sa da yayi haɗi da wulla mata wani irin mugun kallon da ya kusa kifar da ita a wurin ne ya sanƴa ta saurin jan burki tana jan reverse haɗi da shan dukkanin jinin jikin ta.

Kauda kansa yayi daga gareta yana wani irin tamƙe fuska yawa wanda aka aiko masa da tragic labari.

Khairat jiran iyayen ta tayi suka ƙaraso kafin ta mara musu baya.

Cike da sakin fuska da farin cikin ganin sa da sukayi suka tar6e sa.

ZEEYAD ɗan sakin fuskar sa yayi kafin ya shiga gaida su cike da girmamawa kamar yadda ya saba.

Sosai sukaji daɗin yadda yayi musu, ganin bai nuna musu wani girman kai koh makamancin hakan ba, inda sukayi masa iso zuwa cikin gidan.

Babu musu ya mara musu baya ba tare da ya koh dubi gefen Khairat dake ta aika masa kallo kamar ta ɗauke shi ta haɗiye ba, ganin yadda yaƙara kyau haɗi da sakeyin wani irin fresh, ga kuma tarin kwarjini da haibar dake tattare dashi yasa ta kasa yin magana sai kallo kawai da take ta binsa dashi har suka isa ƙayataccen falon cikin gidan.

Zama yayi cikin ɗaya daga cikin lallausan cushions ɗin falon, yana sake tamƙe fuskar sa.

"Welcome Son, ashe da baka manta mu ba?" cewar Momyn Khairat cikin farin cikin ganin sa da tayi.

Ɗan Murmusawa kawai yayi nan Dady yace "Nima i thought koh dagaske ya mance damu ɗin, sai kuma yau gashi ya kawo mana surprise visit."

Murmushi ZEEYAD yayi yace "Ba zan ta6a mantawa daku ba, no matter how rich and famous i become, ku ɗin tamkar iyaye ne a wuri na."

Murmushi duk sukayi kafin Daddy yace "Masha Allah, ya ka baro mutanen dama kuma mahaifin naka?."

"Alhamdulillah Sir" ya faɗa.

"Masha Allah, ke baki iya gaisuwa bane?" cewar Daddy yana kallon Khairat dake ta bin ZEEYAD da eyes yawa zata haɗiye shi.

A ɗan razane ta ɗago tana sosa wuya tace "Welcome."

Bai kalleta ba haka kuma bai amsa mata ba sai ma yi da yayi kamar bai jita ba, sosai zuciyar ta ta sosu da hakan sai dai maimakon ya bata haushi taji ya burgeta sosai, dan kuwa komai yayi mata a yanzu ya kai yayi ɗinne, ɗan babban sarki kamar sa kamata yayi yaja aji fiye da yadda yakeyi ma a yanzun.

Inviting ɗinsa sukayi zuwa dining sai dai fur ZEEYAD yaƙi amincewa a cewar sa zai wuce ne sabida akwai wuraren da zaije.

Basu tilasta masa ba tunda ra'ayin sa ne hakan, sai dai Khairat koh kaɗan bataji daɗi ba ganin zai tafi.

Har bakin motar sa suka rako sa, sosai ya lura da Khairat a matse take da son yi masa magana, sai dai koh kaɗan bai bata fuskar hakan ba, bale ma ta nemi kawo masa raini koh wani abin.

Ita kanta Khairat ta san ZEEYAD ba ajin ta bane dama chan ma karfin hali kawai takeyi na yi masa gori kala-kala dan kawai mahaifin ta ya taimake shi a wani fanni na rayuwar sa, amma tunda taji labarin asalin koh wanene shi taji tayi mugun raina kanta, musamman yanzu da ta sauƙe idanun ta a kansa ta ƙara gasgata lamarin cewar ZEEYAD yayi mata nisa kuma ba zai ta6a zama nata ba.

Sallama yayi da Momy da Daddy, kafin yaja murfin motar sa ya rufe yana tada ta.

Sosai idanun Khairat suka cika taf da kwalla zuciyar ta nayi mata mugun zafi, wai yau ita ZEEYAD ke ignoring kamar baisan da wanzuwar ta a duniyar ba.

Tana gani yaja motar sa ya bar cikin gidan, inda ta fashe da wani irin matsanancin kuka tana yin ciki da gudu.



**********************



___________Jafar ne tsaye bakin ƙofa yana ta rarrashin DEENAH da tun wayewar garin yau bata fito ba, gashi har ana neman ƙarfe biyun rana yanzu.

"DEENAH dan Allah ki buɗe ƙofar nan haka, why are you doing this?."

"DEENAH?" ya sake faɗa ba tare da nuna wani gajiyawa ba.

"DEENAH please i beg you ki buɗe ƙofar nan, i have been standing here for almost 30mins yanzu amma kinƙi buɗe ƙofa, are you sure you're alright?."

"DEENAH?" ya faɗa yana knocking door ɗin.

"Please Lil sis, open the door, i just wanna see how you're doing and i promise ba zan takura miki ba dan Allah DEENAH."

Tunda yazo bakin ƙofar ɗakin yake ta bugu tare da kiran sunan ta, amma koh kaɗan baiji motsin ta ba, hankalin sa ne ya fara tashi koh wani abin ya same ta ne, sake knocking ƙofar yayi da ɗan ƙarfi yana kiran sunan ta "DEENAH?."

Shiru ya sake ji hakan yasa shi barin bakin ƙofar zuwa ɗakin Umma.

Zaune ya same ta da Qur'an a hannu tana karantawa, cikin mugun fushin da yake ciki yace "Umma anƴa kin damu da ƴarki kuwa?."

Tsagaitawa tayi da karatun bayan ta kai ƙarshen aya kafin ta rufe tana ɗagowa ta kalle shi.

Kallon ta yakeyi shima kafin yace "You doesn't seem to care at all, DEENAH locked herself up tun jiya da dare har yanzu bata buɗe ƙofar ba i have been knocking on her door for almost 30mins now, amma koh motsin ta banji ba, amma ke banga wani damuwar rashin fitowar ta tun safe da batayi ba tattare dake, kuma koh takawa bakiyi kinje kin duba kinji koh tana lafiya ba, Umma what has come all over you ne wai?, you've changed alot ba kamar dah ba" ya faɗi hakan ne cikin fushin da yake ciki.

Miƙewa Umma tayi daga zaunen da take tana zuwa ta ajiye ƙur'anin wurin ajiyar sa, kafin ta cire Hijabin jikin ta tana hanging ɗinsa tace "Zaka iya ficemin daga ɗaki idan ka gama yimin faɗa na Uba na."

Mamaki ne ya cika Jafar ganin Umma koh nuna damuwa akan hakan batayi ba.

"Koh dai bakaji mai nace bane na maimaita?."

"Umma what's wrong with you?, DEENAH tana chan..."

Bai ƙarasar ba ta katse shi cikin faɗa da cewa "Ya kake so nayi mata Jafar, mai kakeso nayi, wane irin ƙoƙari ne banyi ba na ganin DEENAH ta bar wannan halin nata na ƙunshe kai a ɗaki?, wane irin ƙoƙari ne banyi ba na ganin na jawo ta jiki na tare da bata dukkanin kulawar

Please Login or Register in order to submit comment