Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba" ta faɗa tana wurgawa Secretary muguwar harara.



Buɗe idanu ZEEDAN yayi lokacin da yaji ta ambaci ƙasƙantacce.



Tashi ZEEDAN yayi daga kan kujerar da yake tare da zuwa ya ɗauki coat ɗinsa akan hanger ɗin dake ajiye a office ɗin nasa ya sanƴa akan kayan sa tare da ficewa daga office ɗin.



Tashi tayi haɗi da wurgawa Secretary harara kafin taja doguwar tsuka ta fice tare da mara masa baya.



Tafiya take but koh ina na jikin ta na shaking, inda kuma kowa sai bin ta yake da kallo yana haɗiye ƴawu.



Lifter yake shirin shiga nan tayi saurin kiran sunan sa da ƙarfi "ZEEDAN?."



Cikin sauri ta ƙarasa wurin sa ta tsaya ta bayan sa tace "It's been a year kenan rabo na da Nigeria, but tunda na tafi outside dan gabatar da final exams ɗina koh ƙira na baka ta6a yi ba, a hakan kenan kake tunanin riƙe amanar da aka damƙa maka?."



Juyowa yayi gare ta yace "Babu wanda ya bar min amanar ki, stop deceiving yourself" ya faɗa cike da 6acin rai idanun sa na yin ja.



Hannu ta harɗe a ƙirji tace "Bakada ikon yi min tsawa ZEEDAN, yakamata ka girmama ni a matsayi na ta ƴa ga mai gidan ka."



Cize baki yayi yana kaɗa kai cike da muguwar taƙaici yayin da 6acin rai ke sake tsattsafo masa akan fuska dama kuma zuciya.



"Kada kuma ka manta da cewa we're getting ENGAGED next week, ZEEDAN koh kaƙi koh kaso ni Khairat sai nayi rayuwa da kai, kasan kuma maiyasa nace hakan?, sabida mahaifi na, ina da tabbacin ba zaka iya ja dashi ba sabida irin halarcin da yayi maka a rayuwa ya ciro ka daga tsumma ya maida ka cikakken mutum har ka zama abinda ka zama yau, ɗaya daga cikin manƴan Artist ɗin da akeji dasu a duniyar zane, ZEEDAN my love, ka daina 6atawa kanka lokaci sabida na tsani ganin wannan kyakkyawar fuskar taka cikin fushi dukda kuwa yana yi maka kyau sai dai ba ƙaramin tsorata ni yakeyi ba" ta faɗa tana kai hannu da niyyar shafo gefen fuskar sa.



Riƙe hannun nata yayi, sam dukan mace ba zai bada wani ma'ana koh armashi ba, idan ba haka ba babu abinda zai hana sa lakaɗawa Khairat duka a yanzun, sosai yaji daɗin nisan da tayi masa, but a yanzu da ta dawo dole ne ta zame masa ƙarfen ƙafa ta kuma hana sa sukuni, duk inda yaje tana biye dashi, duk macen da ta ra6e sa kuwa koh da ma'aikaciya ce babu abinda zai hana ta sanƴa guards ɗinta yi mata dukan cin mutunci, daɗi ɗaya zaiji na dawowar ta wato tayi maganin Surayya ma dake maƙale dashi kullum yawa chewing gum batason rabuwa dashi, but bayan wannan kuma babu wani abin so koh sha'awa tattare da Khairat, duk wani irin hatsabibanci Khairat ta san shi, da ta ga ZEEDAN tare da wata gara ace an zuba mata tafasasshen mai a jikinta sabida yadda zuciyar ta ke matuƙar ruruwa wuta na cin shi, yana ɗaga mata ƙafa ne kawai dan sabida mahaifin ta da ya kasance mutumin kirki dama kuma mahaifiyar ta Unlike Khairat da take rayuwa kamar ta ƴaƴan turawa, shiyasa ta wani 6angaren sam bai damu da takura masa da Surayya take yi ba, dan kuwa yasan da zarar Khairat ta dawo ita da ƙafafun ta zata gudu.




Sakin hannun nata yayi, cikin kakkausar murya yace "I warned you, didn't i?."



Harɗe hannaye tayi s ƙirji tace "Sorry honey, but komin daren daɗewa you will be mine, from that day kuma babu wanda zai hana ni ta6a ka, not even you" ta faɗa cikin wani irin shu'umin murmushi dake nuna ita ɗin gogaggiyar ƴar iska ce.



Juyawa yayi a fusace tare da danna lifter ɗin ya buɗu kafin ya shige yana danna number ɗin flour ɗin da zashi.



Ganin yadda ya fito a matuƙar fusace 6acin rai ƙiri-ƙiri akan fuskar sa ya sanƴa guards ɗinsa saurin iyowa kansa.



Makullin mota kawai ya kar6a a hannun ɗaya daga cikin su kafin ya buɗe motar ya shiga tare da yi mata key ya tada ta ya bar cikin ƙatuwar company ɗin kamar zai tashi sama...............




***********************



.............Tsaye yake a gaban faskekiyar hoton ta dake manne a jikin wall ɗin ɗakin sa yana kallo.



Haɗuwa da tsaruwa irin na ɗakin kaɗai ya isa ya sanƴa ka ɗilalar ƴawu, abin sai wanda ya gani.



Sosai yaji komai ya fita a kansa bayan rabuwa da ita dama kuma sanƴa ta a idanu da baya yi, tun abin baya damun sa har yazo ya fara basa tsoro, baya ta6a samun sukuni a zuciyar sa muddin bai sanƴa idanun sa kan kyakkyawar hoton ta bane ba, ya ɗauka farin cikin sa zai gama cika ne a lokacin da yake tare da sarƙar sa, but a yanzu ya gane farin cikin sa ba zai ta6a cikewa ba muddin bata kusa dashi ne, and now rayuwar sa zata sake rugujewa ne kwata-kwata ya koma kamar marayan da bashida uwa kuma bashida uba sabida dawowar Khairat.



Hannun sa ya buga a jikin bangon yana fitar da wata iriyar zazzafar huci, sosai zuciyar sa ke mugun tafarfasa, he just wants to see DEENAH, ganin ta a hoto ba zai sanƴaƴa masa zuciya ba, he wants to see her in person koh zai samu sassauci a cikin zuciyar sa, ganin ta na sati biyu da baiyi ba kasancewar dawowa da yayi is like yayi shekaru goma ne bai ganta ba, he feels so empty without her, but dukda haka he can't tell actually abinda yakeji game da ita ba.................




*************************



..............Sanƴe take cikin farar uniform ɗinta wanda yayi matuƙar kar6ar ta.



Jujjuyawa takeyi a gaban mirror tana ganin yadda shape ɗin jikin ta ya fito a cikin kayan.



Umma ta shiga kwalawa kira cikin muryar kuka.



Da sauri Umma tazo ta same ta "lafiya, meke faruwa?."



Cikin kuka tace "Umma ki gani fah, kiga abinda uniform ɗinnan yayi min duk ya kwanta min a jiki ya fito min da shape ɗin jiki na, ni banaso gaskiya nikam ki canza min makaranta."



Baki kawai Umma ta saki tana kallon ta nan tace "Haba Auta, idan ya kwanta miki a jiki ba kina da wani ba, ki sanƴa sa mana."



"Umma suma duk haka suke yi min, nidai gaskiya banason su."



"Shikenan yanzu dai ki bari idan kinje kin dawo sai kije ki ɗinka wani."



"Aa Umma, nidai gaskiya ba zan iya fita dashi ba."




"Toh shikenan ai sai ki zauna a gidan tunda dama naga hakan kikeso" ta faɗa tana ficewa daga ɗakin.



Kallon jikin ta ta sake, kafin kuma ta ɗau farar safar ta ta sanƴa tare da farar half-cover shoe ɗinta.



Baƙar ƴar ƙaramar jaka ta goyo ta ɗauka tare da saƙala shi a kafaɗar ta, kafin kuma ta nufi ƙaton closet ɗin ta ta ciro baƙar After-dress ta ɗaura akan uniform ɗin nata.



Sosai ta sake gyaggyarawa kafin ta fice daga cikin ɗakin.


"Au kajimin Ja'irar yarinƴa, ke dama kinsan da wannan dabarar kuma kikayi ta tada hankalin ki?" cewar Umma tana kallon ta.


Ƙarasowa tayi ta zauna tace "Umma ba fah a bari ana ɗaura wani kayan akai, nidai dan Allah kawai ki canza min school, wanda zan iya sanƴa duk wani irin kayan da nakeso."


"Amma Auta ai idan akace za'a canza miki makaranta yanzu sai kin sake zana wata jarabawar Waec da Neco ɗin, ga kuma Jamb duka."



"Eh nidai Umma na yarda."



"Toh ya na iya tunda ke zakiyiwa kanki karatun, naji toh."


Cike da farin ciki ta rungume Umma tare da bata peck a kumatu tace "Ina matuƙar Ƙaunar ki Umma ta."


Murmushi Umma tayi tace "Naga dai ranar da zakiyi aure mu rabu yadda zakiyi."


Rau-rau tayi da idanu kafin ta sake rungume Umma tace "Nidai kam Allah babu wanda zai raba ni dake Umma ta."



"Ke kinga ni sake ni hakanan ki kama hanƴa ki tafi, koh so kike kiyi latti, sarkin kuka kawai" cewar Umma ganin tana shirin yi mata kuka.



Dubu biyu ta ciro a purse ɗinta ta bata tace "Gashi nan kiyi kuɗin mota da na break."



"A'a Umma akwai kuɗi a wuri na Yaya ya bani, ki riƙe abin ki."



"Toh shikenan Allah yayi masa albarka."



"Aameen, nikuma fah?" ta faɗa cikin shagwa6a.


"Kema Allah yayi miki albarka, Allah ya albarkaci rayuwar ku dukkanin ku, ya nuna min ranar auren ku har naga jikoki na."



"Aameen Yaa Hayyu Yaa Qayyum, Umma na, toh Umma ni na tafi."



"Allah ya kiyaye ya tsare hanƴa, Allah ya bada sa'ar karatu."


"Aameen Umma na" ta faɗa tana ficewa, da kallo Umma ta bi ta tana share hawayen idanun ta.............




**************************



............Koh da taje school ɗin sai da ta shiga class ta zauna kafin ta cire rigar sama ɗin da ta ɗaura tana ajiye shi kusada ita.



2hours lectures sukayi kafin su fito break.


Masallaci ta nufa tayi sallar azahar kafin ta idar ta fito.



Cafeteria ta nufa ta sayo Burger da drink sai ruwan gora kawai ta iyo gindin wani bishiya inda babu kowa ta samu bench ta zauna.



A hankali ta shiga ci kamar bataso har ta kammala, kasnacewar hutun 1hour kaɗai suke dashi yasa ta yin sauri ta kammala ta koma class.



Sosai suka sha lectures ɗin 2hours, inda sai da La'asar kafin lecturer ɗin ya fita.



Sallama kawai ta yiwa ƴan class ɗin nasu kasancewar ba wani shiga harkar su take ba, dan kuwa tafijin daɗin rayuwa ita kaɗai babu ƙawaye.



Kasancewar sunyi da Jafar zai zo ya ɗauke ta ne yasa ta yin masallaci tayi sallar La'asar, bayan ta idar ne kuma ta shiga zaman jirar sa.



Wayar ta ta ciro daga cikin jaka ta hau buga game.



Tana cikin yi ne kuma kira ya shigo wayar ta, kasancewar sabuwar lamba ce kuma shiyasa bata ɗaga ba dan kuwa bata cika ɗaukar kiran sabbin numbers ba.



Sau biyu kawai aka kira aka haƙura, nan kuma kiran Abdul ya shigo wayar ta.



Har kamar ba zata ɗaga ba sai kuma ta ɗaga, dan kuwa tasan ba ƙaramin cika ta da surutu zaiyi ba.



Sallama yayi mata ta amsa ba yabo babu fallasa, kafin su shiga gaisawa.



Nan dai suka hau yin hira duk da kuwa rabin da kwatar hirar shi yakeyi, ita dai nata bai wuce eh koh a'a ba.



Sun ɗau almost 15mins suna waya kafin yayi mata sallama ya katse kiran.



Time ta duba taga biyar saura dan haka ta latso lambar wayar Jafar tare da buga masa kira.



Ringing biyu ya ɗaga tare da ce mata "Am on my way" yana ajiye wayar.




Turo baki tayi dan kuwa ba ƙaramin gajiya tayi ba, a haka har ya ƙaraso yace da ita yazo.



Ficewa tayi taje ta same sa a inda yayi parking motar kafin ta shiga yaja sukayi gida............




*************************




.............Kwance take cikin shirin baccin ta, Abdul ya kira ta.



Sun ɗan daɗe suna waya kafin suyi sallama.



Numbern da yayi ta kiran ta bayan lokacin da suke waya da Abdul ta gani kafin kuma ta share tana gyara kwanciyar ta.



A haka har bacci ya ɗauke ta............




*************



.............Washe gari 12pm suka gama lectures ɗinsu na ranar duka, dan haka kai tsaye gida kawai ta dawo.



Wanka ta sake sannan ta shirya cikin kaya marasa nauyi, sai da tayi sallah kafin ta ɗebi abinci ta fara ci.



Wayar ta da ta ɗau ringing ta kalla, kamar ba zata ɗaga ba sai kuma ta ɗaga tana kaiwa kunnen ta.



Shiru taji anyi hakan ya sanƴa ta furta "Assalamu Alaikum."



Nan ma shiru akayi babu amsa.



"Hello" ta sake cewa.



Katse kiran tayi tana ɗan jan ƙaramin tsaki kafin ta cigaba da cin abincin ta............



*****************



............6angaren ZEEDAN kuwa ba ƙaramin rashin walwala yake ciki sakamakon rashin ɗaukar kiran sa da DEENAH bata yi ba.



Haka nan ya haƙura har zuwa dare ya sake buga mata sai dai jinta tana waya a wannan lokacin ba ƙaramin ɗaga masa hankali yayi ba, musamman da ya kai kusan 10mins yana bugawa but sai dai yaji ance tana waya, haka kurum yaji hankalin sa ya kasa kwanciya da wayar da takeyi ɗin.



Zaune yake a office ɗinsa, kallo ɗaya zakayi masa kaga damuwa akan fuskar sa.



Wayar sa ya ɗauka tare da sake dialing numbern ta, dukda yasa ran ba zata ɗaga ba kuwa.



Sai dai bisa ga mamakin sa yaga an ɗaga kiran tare da kuma yin sallama, he can't help it but yayi shiru yana saurarar zazzaƙar muryar ta.



Bai ta6a zaton zata amsa kiran nasa nan kusa ba, jin ta yanke kuwa duk yaji wani farin cikin da yake ciki ta yanke.



Sauƙe wayar yayi a kunnen sa yana damƙe hannayen sa tare da runtse idanu.



Jin muryar ta babu abinda ya ƙara masa sai kewar ta, ji yake idan bai sanƴa ta cikin idanun sa ba, ba zai iyayin bacci ba yau.



Wayarsa ya ɗauka tare da yin wasu ƴan danne-danne kafin ya ajiye ta...........



**********************


*THE NEXT DAY*



..........Zaune take ita da Abdul da ta ɗan fara sakin jikin ta dashi, dan kuwa ta lura shi ɗin mutumin kirki ne sosai, hakan ya sanƴa ta fara sakin jiki dashi.



Hira kawai suke ba yabo ba fallasa take amsa masa, idan yayi abin dariya tayi murmushi, amsar ta a gare shi bai wuci eh koh aa ba, sai kuma murmushi.



Ƙarar horn ɗin motar da sukaji ne ya sanƴa su maida duban su gun gate ɗin, musamman ma DEENAH da ta san wannan ba horn ɗin motar Jafar bane, Umma kuma bata fita koh ina yau da tata motar ba _"Who could it be?"_ shine abinda ta faɗa a ranta tana maida hankalin ta kan Abdul dake yi mata magana.



Buɗe ƙofar akayi take wata zazzafar mota ta kunno kai cikin gidan, kafin ya nufi parking space ɗin gidan yana parking motar.



Hango su yayi ta cikin tinted glass ɗin motar tashi, wani irin abu yaji ya tsaya masa a zuciya.



Hannu yasa ya buɗe murfin motar ya fito tare da tunkaro su kamar zai tashi sama.



DEENAH ba ƙaramin mamakin ganin balarabe tayi a gidan su ba.
_"What is he doing here?"_ shine abinda ta faɗa a ranta tana zazzare ido.




Saurin daidaita nutsuwar ta tayi tana sake ƙirƙirar murmushin ta mai ƙara mata kyau akan fuskar ta tana kallon Abdul.



Fuskewa ZEEDAN yayi yana controlling mugun kishin dake taso masa a zuci ya ƙarasa wurin su murmushi akan fuskar sa.



Dafa table ɗin dake tsakanin su yayi tare da furta "Hi."



Ɗagowa Abdul yayi ya kallesa kafin shima yace "Hi" yana miƙa masa hannu alamun su gaisa.



Cike da mugun basarwa ZEEDAN ya juyar da kansa zuwa ga DEENAH yace "Is your Mom around?."



Kai ta jinjina masa tana kauda idon ta daga kallon sa.




"Zaki iya yi min jagora zuwa wurin ta?" ya sake faɗa.



"Sure" kawai ta faɗa, kafin ta miƙe daga kan kujerar da take.



Kallon Abdul tayi tare da sakar masa murmushi tace "Yi haƙuri dear, bara nayi masa iso zuwa wurin Umma."



Murmushi shima Abdul da yaji haushin basar dashi da ZEEDAN yayi ya maida mata kafin yace "Bakomai."



Wucewa tayi kawai nan ya mara mata baya, zuciyar sa na matuƙar yin suya sosai.
_"Dear! Dear!! Dear!!!"_ yake ta maimaitawa a zuciyar sa.



Falon nasu suka shigo wanda ke ta tada ƙamshi na musamman kafin tace dashi "Ka zauna, bari na kira Umma" ta faɗa tana shigewa wani lungu.




Ɗakin Umma taje ta sanar da ita da cewa tayi baƙo, nan ta sako Hijabin ta suka fito tare.




ZEEDAN ganin Umma ba ƙaramin kunƴa ce yaji ta kama sa ba, sunkuyar da kai yayi kawai, yayin da Umma kuma ke ta bin sa da kallon mamaki.



"Wa nake gani kamar Balarabe?" faɗin Umma dake shirin zama kan kujera.



Wucewa DEENAH tayi kitchen ta haɗo masa abin ci da sha akan tray ta fito.



Zaune ta gansa kusada ƙafar Umma, dan haka zuwa tayi ta ajiye masa a gaban sa kafin tace "Umma ni na wuce Abdul yana ta jira na babu daɗi na bar sa."



"Aikuwa dai kam yakamata ace kinje kada ki barsa yayi ta jira."



Ficewa tayi inda ya bita da kallo ta ƙasan idanu.
_"Is she going back to that frog?"_ ya faɗi hakan a zuciyar sa yana jin kamar ya tashi ya mara mata baya.



Sosai zuciyar sa ke mugun yi masa zafi................






*Yawan Comment, Yawan Typing*





*MHIZZ JIDDHERR...............✍🏽*



[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```





*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*






*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*021...*




_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_





............Sun ɗan daɗe da Umma kafin ya tashi ya fito.



Hango su yayi har yanzu suna nan, ganin yadda Abdul ke zuba murmushi ne ya sanƴa ZEEDAN jin kamar yaje ya shaƙo wuyar sa ya murɗe tsabar haushi da takaici.



_"He seems so very happy with her, ita kuma da yake sokuwa ce tana biye masa"_
Ya faɗi hakan a zuciyar sa yana jin kamar ya tunkare su ya tarwatsa wannan wurin nan, but ba zaiyi hakan ba koh dan ajin da yake dashi kada ya zube.



Hannaye ya zuba cikin aljihu kafin ya fara tafiya a hankali kamar wanda bayaso kan shi a sama ya wani haɗe fuska da rai kai kace guna yaci.



Ganin ya kusa kawowa wurin su ne yasa shi yin slowing tafiyar sa yana kallon su ta gefen ido ta yadda ba zasu gane hakan ba.


Zuwa yayi ya wuce su, sai dai ganin yayi gaba DEENAH bata kula sa ba ba ƙaramin sake 6ata masa rai hakan yayi ba.


Tsayawa yayi yana jin zuciyar sa na mugun tafarfasa, musamman dan ita ya taso tundaga inda yake dan ya samu sukuni a zuciyar sa, but instead of hakan sai ma wani ƙarin baƙin cikin da ya sake kwasa akan na dah.


Ganin ta da wani daban is like ana sossoka masa wuƙa ne a cikin zuciyar sa.


He can't help it but yayi tafiyar sa, hakan ne kaɗai zai sanƴa sa jin nutsuwa a ransa, dan kuwa ba zai iya ganin ta da wani tana sakar masa tsadaddar murmushin ta ba, wanda shi yakamata ace yana ganin hakan kullum ba wani daban.


Juyowa yayi yana kallon su _I wonder what he looks like, there is nothing interesting about this guy, why take 6ata lokacin ta akan shi?"_ ya faɗi hakan a zuciyar sa kafin kuma ya furzar da huci ya wuce ya shige motar sa.



Tada ta yayi tare da danna horn da ƙarfi still idanun sa akansu, but DEENAH yi tayi kamar ma batasan da akwai mota a cikin gidan ya dame su da ƙara ba.


Steering ɗin ya nausa yace "Why isn't she responding?."


Buɗe gate ɗin da mai gadin yayi ne yasa shi jan motar a zafafe ya fice daga cikin gidan.


Motar Abdul da ya gani ne ya sanƴa shi slowing yana ƙare mata kallo.


Yatsine fuska yayi yace "The Guy is a little bit rich, tunda yana iya hawa motar miliyan 12" ya ƙarashe yana tsuke fuskar sa kafin ya sake jan motar a tsiyace yana harba ta kan kwalta.................




***********************



.................Cikin sauri take shiri kasancewar tayi latti yau, yasa duk ta kasa samun kwakkwarar sukuni.


Ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta cikin makarantar.


Da sauri ta fito kasancewar Umma ta fita wurin aiki haka ma Jafar ya sanƴa ta rufo ƙofar da key tana baiwa mai gadi ajiya kafin ta fice.


Tsaye tayi a bakin kwaltar tana jiran adaidaita, inda da kyar ta samu wani ya ɗauke ta.


Zuwa yayi ya sauƙe ta a school kafin ta biya sa tana saurin shigewa cikin makarantar kasancewar bai shiga da ita ciki ba.


Zuwa tayi ta tarar har an shiga musu an fara lectures ga kuma ƴan latti nan a waje da alama lecturer ɗin baya kar6ar masu latti.


Ba tare da ta 6ata lokacin ta ba ta nufi inda ta saba zama babu kowa ta zauna.


Earphone ta ciro a cikin jakar ta tana sanƴawa akan kunnen ta, kafin ta ciro Book ɗinta ta shiga bitar karatun da sukayi a baya.


Ji tayi sam karatun baya shiga kwakwalwar ta dan haka ajiye takardar tayi tana folding hannayen ta a ƙirji.


Shiru tayi tana kalle-kalle kafin kuma ta shiga rero waƙa cikin zazzaƙar muryar ta

_I have been reading books of Old_
_The Legends and the Myths_
_Achilles and his gold_
_Hercules and his gifts_
_Spider-Man's Control_
_And Batman with his fists_
_And clearly i don't see myself upon that list_
_But she said, “where do you wanna go?”_
_How much you wanna risk?_
_Am not looking for somebody with some superhuman gifts,_
_Some superhero,_
_Some Fairy tale bliss_
_Just something i can turn to somebody i can kiss_
_I want something just like this_
_Tu-ru-ru, Tu-ru-ru_



"Woo bravo!" aka faɗa saitin kunnen ta.


Da sauri ta ɗago tana cire headphone ɗin kanta tare da binsa da kallo.


Zama yayi kusada ita, nan tayi saurin matsawa gefe.


Kallon ta yayi kafin kuma ya ɗan ta6e baki shima yana kauda kansa daga kallon ta yace "You're late today, why?."


Shiru tayi pretending tana duba takardar hannun ta.


Kallon ta yayi jin taƙi kulasa, hannu yasa ya kar6i takardar hannun nata ya shiga dubawa.


Ta6e baki yayi yace "Uhm this topic, sai yanzu kukeyin sa?, i have done it in my secondary school, but ku how comes sai yanzu kuke yin sa, strange" ya faɗa yana still idanun sa a cikin takardar.


Bata kula sa ba sai ma wayar ta da ta ciro ta hau daddanawa, ba tare da tabi ta kanshi ba.


Kallon ta yayi ta gefen ido bai ce komai ba sai ma maida duban sa da yayi cikin takardar yana kallo.


_"She is trying to show me attitude"_ ya faɗa a ransa yana kallon ta ta gefen ido.


Rufe takardar yayi kawai ya zauna tare da crossing legs ɗinsa yana neman ta hanƴar da zai jata da hira.


"Ahm..oh yeah tell me, ke mawaƙiya ce?, you have a sweet voice."


Bata ɗago ta kallesa ba sai kai kawai da ta girgiza masa alamun "a'a."


_"She should atleast fake a smile on her face koh da bata so, i can't believe ta zage tana yiwa wancan tiny thing ɗin murmushi but taƙi sakar min fuska"_ ya faɗa a ransa yana kallon ta.


Ɗagowa tayi ta kallesa nan yayi saurin sakar mata murmushi, kafin kuma ta sake sadda kai ƙasa tana cigaba da danne-dannen ta.


_"Oh GOD, did she just ignore my beautiful smile?"_



Takardar ta ta ɗauka ta shiga buɗewa tana bi a hankali.


Buɗe jakar ta tayi ta ciro farar glass tare da sanƴawa a idanun ta tana cigaba da duba takardar hannun nata.


Duk abin nan da take bata ɗago ta kallesa ba, sai shi da ya zama kamar soko yana ta bin ta da kallo.


A haka suke zaune babu wanda yace da wani uffan a cikin su har lokacin second period lecture ɗinta yayi.


Tattare komai tayi ta sanƴa a jaka kafin ta miƙe tana rataye jakar a kafaɗa.


Kafar uniform ɗinta da ta ɗanyi ƙura ta sunkuya to goge shi da handky ɗinta kafin ta jefa shi cikin jaka ta fara tafiya.


Sai da ta ɗanyi nisa kaɗan kafin ya ɗauke idanun sa da ya zuba akan coca-cola shape ɗinta yana mai mara mata baya.


Har cikin class ɗin ya biyo ta ta sami wuri ta zauna shima ya zauna, nan kuma hankalin ƴan class ɗin baki ɗaya ya dawo kansu.


Babu abinda kakeji sai maganar mutane ƙasa-ƙasa, da kaji kasan kowa tofa albarkacin bakin sa yake.


Shi kuwa koh kaɗan bai damu da kallon da ƴan mata da samarin class ɗin ke binsa dashi ba, sai ma sake tsuke fuska da yakeyi yana basarwa.


Ita kuwa

Please Login or Register in order to submit comment