Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zuwa ƙarshen wata insha Allahu da zaran an biya albashi zan tabbatar da na baka kuɗin ka a cike, ai ba sai ka tona min asiri a gaban yara ba, kuma dan Allah ka daina aibata min ƴaƴa dan kuwa bakasan wahalar da nasha wurin tarbiyantar dasu ba, indai kuɗin ka ne insha Allah nayimaka alƙawarin biyan ka zuwa nan da ƙarshen wata."



"Oho dai koma dai menene ki tabbatar da kin tanadi kuɗin nan dubu goma sha biyar cir tun kafin na haɗa ki da hukuma wallahi, haka kurum kaida haƙƙin ka ka riƙe a hana ka" ya faɗa yana buɗe ƙofar ɗayan part ɗin ya shige.



Nan tace "Haƙƙin marayu dai, koh ka manta ne?."



Nan ya dawo da wuri yace "Mai kika ce?."


Bata kula sa ba ta haɗa kan ƴaƴan ta tace "Muje."



Nan suka shige part ɗinsu suna rufo ƙofa,kwafa yayi yace "Zamu gamu ne" yana komawa ciki.



"Umma wa maiyasa kawu Sale yake yi miki haka ne, koh dama ba Abban mu bane ya gina gidan nan?."



"Toh nikam ya na iya ne dashi dan Allah Jafar, ai dama idan mutum yafi ƙarfin ka kawai ka kai kukan ga Allah shi zaiyi maganin azzalumai, idan ni banida yadda zanyi na kwato muku haƙƙin ku da dukiyar ku da ya cinƴe ai akwai Allah kuma yana ganin komai, shine wanda zai kwatar muku sabida babu wanda yafi ƙarfin sa, kuje ku ɗau abincin ku kuci" ta faɗa tana ficewa zuwa ɗaki ta barsu nan falon idanun ta na tara hawaye.



Da kallo duk suka bita suna mai jin tausayin Mahaifiyar tasu matuƙa a zuciyar su, dan kuwa ba ƙaramin ƙoƙari takeyi akansu ba na ganin ta inganta rayuwar su, tana iya sadaukar da komai nata akansu burin ta shine rayuwar su ta inganta tayi kyau, bata ta6a barin su sunyi kukan rashin uba ba, itace ta zame musu Uwa sannan kuma Uba, duk wani abu da Uba yakamata yayi itace keyi musu dukda kuwa ɗan uwan mahaifin su na raye sai dai babu abinda yakeyi musu, dukiyar da Mahaifin su ya bari ma yayi nake-nake akai a cewar sa zai kula da rayuwar ƴaƴan da ya bari, wanda hatta gidan da suke ciki na mahaifin su ne ya gina ta sai dai dukda haka wai sai sun biya kuɗin haya, sannan daidai da Naira biyar bai ta6a kashe musu cikin wannan kuɗin ba, komai Mahaifiyar su ce keyi musu kasancewar tana aikin gwamnati kuma albashin ta babu laifi, dashi takeyi musu dukkanin buƙatun su kafin tayi na kanta, shiyasa suma suke burin wataran su girma su sanƴa mahaifiyar su farin ciki fiye da wanda ta basu.



Jafar ne yabi ta ɗaki dan kuwa yasan kuka takeyi, DEENAH kuwa kula ta ɗauka ta ɗebi abinci a ciki tayi ficewar ta.



Kwance ta same sa idanun sa na kallon sama,motsin da yaji ne yasa shi ɗago da kansa ganin itace yasa shi runtse idanu yanajin kamar ya tashi ya faffale fuskar ta da mari tsabar takaici.


Ya rasa mai take nema daga garesa, kowa.gudun sa yakeyi sai dai shi yayin da yake gudun ta shine ita take son shigowa rayuwar sa, sam bayason hakan musamman ma da bai san ta ba, bai san daga ina take ba, gata kuma yarinƴa ƙarama hakan yasa sam bayaso ta dinga kusanto shi koh dan kar tasa mutanen ungwa su fara zargin sa da wani abin suyi masa korar cin mutunci, dan kuwa ba zai so barin arear nan ba coz he feels safe there.



Sam baya ƙaunar alaƙar sa da wasu kuma yanzu, yafison yayi rayuwar sa shi kaɗai ba tare da takurar wani koh wata ba, amma wannan yarinƴar na neman takura masa.



Ajiye kular tayi kawai ta juya tayi tafiyar ta inda kuma ya bita da kallo yana mamakin abinda ya hana ta tsayawa kallon nasa yau, gashi kuma yaga kamar ranta a 6ace yake fuskar ta a ɗaure.




Koh da ta koma gida a bakin ƙofar shiga taci karo da Kawun nasu yana shirin fita, nan yayi wuff yace "Ahaf, an fita yawon gantalin koh?, yarinƴa koh kayan makaranta bata cire ba amma ta ɗau shegun ƙafafuwan nan nata ta fice sabida ba'ayi mata tarbiyya ba, kinje inda aka saba kwakule ki a baki kuɗin koh tunda haka uwarki ta koya miki, zaki daina kallo na ne da wadannan idanun naki kamar na mujiya koh sai na sanƴa hannu na kwakwule su, munafukar banza da wofi, zaki wuce ne koh sai na haɗa wannan kan naki da bango tukun?, tsinanniya."



Da sauri ta shige ciki tana haɗawa da ɗan gudu, dan kuwa sam bata ƙaunar abinda zai haɗa ta da kawun nata sabida ba mutumin kirki bane shi, baya ganin mutuncin mahaifiyar ta shiyasa ta tsane sa daga shi har matar sa Rabi'atu sam basu san miye tausayi ba, shiyasa takejin tsanar su a ranta sosai.



6angaren ZEEYAD kuwa abincin ya buɗe ya gani, shinkafa ce da wake da mai da yaji, maida ta yayi ya rufe dan kuwa shi fah ba wai ya iya cin irin abincin nan bane bashida yadda zaiyi ne kawai.



Sati ɗaya kenan DEENAH na kawo wa ZEEYAD abinci, sai dai taurin rai da rashin yarda irin nasa ya hana sa ci, ga kuma wulaƙanta ta da yakeyi dukda baya so amma yaga alamun kamar yarinƴar batada zuciya komai yayi mata zata nuna tayi fushi sai dai kuma washe gari zai sake ganin ta da wani kular abincin kuma.



Yau kuma Through out bai ganta ba bai ga wulgawar ta koh na yayan ta ba, hakan yasa shi jindaɗi sosai dan kuwa a cewar sa sun gaji dashi ne shiyasa suka haƙura basu samu abinda suke so ba.


Shiru shiru kwanaki huɗu sun wuce baya ganin DEENAH sai yayanta da yake ganin gilmawar sa kullum idan zashi islamiyya koh makaranta.



Tun yana jin daɗin hakan har kuma yaji zuciyar sa ta daina jindaɗin hakan, yau dai ya yanke shawarar tarar Jafar ɗin dan tambayar sa koh lafiya baya ganin ƙanwar sa.



Bayan an tashi ne daga islamiyyar kamar kullum Jafar yazo wucewa nan yace dashi "Hey."


Tsayawa Jafar yayi kafin kuma ZEEYAD ɗin ya ƙarasa wurin sa yace "How are you?."


"Fine" ya basa amsa a takaice.


Kamar kuma ba zaiyi magana ba ya buɗi baki yace "Ina ƙanwar ka, maiyasa bana ganin ta ta daina zuwa islamiyya?."



Shiru Jafar yayi kamar zaiyi kuka nan yace "DEENAH?."



"What's wrong with her, is she Okay?" ya faɗa cikin ɗan damuwa.


Kai ya girgiza masa alamun A'a kafin kuma yace "Nima bansaniba, bansan wane hali ƙanwata take ciki ba, bansaniba koh tana lafiya kokuma sunyi mata wani mugun abun ba."



"Mai kake nufi, su waye sukayi mata mugun abu?."



Kallon ZEEYAD ɗin yayi kafin kuma yayi gaba ba tare da ya basa amsa ba.



Saurin binsa yayi yace "Tell me."


"Kawu ne ya ɗauke ta ya kai ta ƙauye, yace ba zata dawo ba har sai Ummar mu ta biya sa kuɗin hayar sa, idan ba haka ba kuma ba zai dawo da ita ba kuma zai aurar da ita ga ɗan sarkin Ƙauyen."



Wani irin bugu ZEEYAD yaji zuciyar sa tayi lokacin da Jafar ya idda maganar sa wanda bai san ma da cewa Jafar ɗin ya wuce yayi tafiyar sa ba.


He was shocked for a moment jin abinda ya fito daga bakin Jafar ɗin, he can't believe how cruel people can be.


Duniyar nan ta cika da azzalumai dayawa,he feel so sorry for little DEENAH, how comes za'a aurar da yarinƴa mai ƙarancin shekaru kamar wannan?, he couldn't believe it.



Addu'a yayi Allah yasa mahaifiyar su ta samu kuɗin ta biya sa ya dawo da DEENAH.



Samun wuri yayi ya zauna zuciyar sa cunkushe yanajin babu daɗi sosai.



Haushin kansa ne yake kama sa idan ya tuna irin wulaƙancin da yakeyi mata idan ta kawo masa abinci, amma haka nan zai rufe ido ya gasa mata magana son ransa duk dan taji haushi amma hakan baya tasiri.



Haka nan ya kwana da tunanin DEENAH da halin da take ciki ya tashi dashi.


So yake ya sake ganin ta koh da sau ɗaya ne ya bata haƙurin abinda yayi mata, sannan kuma yayi mata alƙawarin ba zai sake yi mata hakan ba.


Yarinƴa ce ƙarama amma kuma zuciyar manƴa gareta.



"Am so sorry" ya faɗa cikin rauni zuciyar sa nayi masa zafi tare da jin haushin kansa sosai, da yasan hakan zata kasance da ba zai ta6a 6ata mata ba a rayuwa.


Wani satin ya sake wucewa amma babu DEENAH babu labarin ta sai Jafar kaɗai da yake ta gani yana wucewa kullum shima fuskar sa babu walwala da alamun dai ba ƙaramin kewa yaji na rashin ƴar uwar tashi kusada shi yayi ba...............



****************************



.............It's been two months kenan da 6atan Yarima ZEEYAD, tun mutane na ɗaukar abin wasa har yazo ya wuce tunanin su sabida ganin yadda ran sarki yake ta ƙara 6aci a kullum, yayin da kuma ya sanƴa aka garƙame duk wani bawa koh dogari da ya ta6a ƙuntata wa ZEEYAD a rayuwa, ba zasu fito ba har sai Yarima ZEEYAD ya dawo koh kuma an sami labarin inda yake, koh da kuwa za'a ɗau shekaru masu yawa ne.



Hukunci mai tsanani aka haɗa su dashi kama daga kan Mulah, Hakim dama kuma duk wani wanda ya ta6a muzguna masa.



Haka ma yake a 6angaren Abdulhakeem da ɗansa Sooraj, hukuncin da sarki yayi musu shine ya kar6e duk wani abu da za'a gani a danganta su da wadanda suka fito daga gidan mulki ya kwace hatta haɗaɗɗen gidan da suke zama suke kuma taƙama dashi ya kwace shi daga garesu inda suka koma rayuwa kamar ta talakawa har sai Yarima ZEEYAD ya bayyana.


"That Asshole, yaushe ne zai bayyanar da kansa?, mu fita daga cikin wannan ƙazamar rayuwar, just take a look at me kamar ni the great Sooraj ace ina rayuwa a wannan kangon, abokai na duk sun gama raina ni, wallahi Abhi duk kai kaja mana dah baka kira ni na dawo ba da yanzu ina chan school abuna ina holewa ta, duk girman school ɗinmu dama kuma squad ɗin mu ni ake ganin nafi girma sabida irin 6arin kuɗin da nakeyi, amma kaga inda nake rayuwa yanzu, imagine idan friends ɗina suka gano ya kake tunanin zanji, wane irin kunƴa kake tunanin zanji, it's been two months now amma ji nake kamar nayi shekaru ɗari a cikin nan just take a look at this rusted place please mtssww" ya ƙarashe cikin ƙunar rai kamar zaiyi kuka.



Ta6e baki Abdulhakeem yayi yace "Koma dai mai zaka ce ka faɗe sa anan wurin, kada ka kuskura kayi su6utar baki a gaban kowane dogari, idan kuwa ba haka ba kai kanka sai ka raina wayon ka, ka godewa Allah ma ana baka ci da sha amma a hakan kake complaining."



"Why ba zanyi complain ba?, dama ai haka zakace sabida duk laifin ka ne, kai ka jawo, har ZEEYAD ɗinne ba zaka iya tattaka sa da kanka ba sai ka kira ni, yanzu fisabillah ka dubi halin da ka jefa ni, duk wani ɗa dake cikin Masarautar nan is out there suna karatun su cikin kwanciyar hankali except me, the great me."



"Hafeezah tace min ta koma wurin bokan ta sannan kuma yace mata ZEEYAD na raye, sai dai fah ya kasa gano inda yaron yake dama kuma yaushe ne zai dawo."



A fusace ya miƙe tsaye yace "What, the rascal is alive, then toh Uwar miye yakeyi da ba zai dawo ba?, this is bad, i wish nasan inda yake" ya faɗa cike da muguwar takaici.



Kallon sa Abdulhakeem yayi kafin yace "Kana tunanin zai dawo ne?, idan ma kana tunanin hakan ne toh kayi gaggawar kauda shi a ranka, tayaya kake tunanin tunda ya samu ya tseratar da rayuwar sa zai kuma dawowa nan, bana tunanin zai dawo koh nan da shekaru ɗari ne..."



"Hell no!, bakin ka ya sari ɗanyen kashi Abhi, dole ne ya dawo koh kana tunanin zai yafe zaluncin da akayi masa ne?, ni nasan zai dawo sannan kuma da zaran ya dawo wasan zata fara tsakanin nida shi ne, dan kuwa duk dan shi ne nake cikin wannan halin na rantse sai na sashi yayi nadamar hakan" ya faɗa yana huci kamar wani tsohon maƴunwacin zaki...............




_*Am so Bored Today😩, dan Allah ku sanƴa ni farin ciki da zafafan comments ɗinku, kunji?, ba dan ni ba sai dan wanda yayi mu*_






*MHIZZ JIDDHERR............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*010..*





..........Haka rayuwa ta cigaba wa ZEEYAD cikin ƙunci kullum, a yanzu ƴan kuɗaɗen dake jikin sa ma sun kusa ƙarewa kasancewar kuɗin wanka da yake biya kullum Naira Hamsin, ga kuma sayan abinci dasu wanki da yakeyi duka.


Ga kuma zuciyar sa dake cike da damuwar rashin ganin DEENAH da baya yi yau sati uku kenan, kullum idan ya tambayi Jafar sai dai yace dashi bata dawo ba, hakan ba ƙaramin sake sanƴa shi cikin rashin sukuni yake ba, so yake kawai ya nemi yafiyar ta akan abunda yayi mata.



Yau ma zaune yake kamar Kullum jikin bishiyar da ya saba zama ya haɗa kai da guiwa, yana tunanin yadda zaiyi ya tafiyar da rayuwar sa dan kuwa ba zaiyiwu ya cigaba da zama anan ba kullum ba tare da abin yi ba, dole ne ya fita ya nemo wa kansa mafita zama haka kurum ba nasa bane indai har yana so ya zama very successful a rayuwar sa.


Tsayuwar mutum yaji a kansa sai dai sam bai damu da ya ɗago ba, dan kuwa da akwai wani mutum da ya sanƴa shi gaba ƴan kwanakin nan bashida wani aiki sai takura masa.


Dire masa kular abincin tayi a gaban sa kafin kuma ta juya da sauri tayi tafiyar ta kasancewar an fara shiga aji.


Ganin an ajiye masa kula yasa shi saurin ɗagowa yana kallon bayan ta, wani irin murmushin da bai san da zuwan sa bane ya su6uce masa yana faɗin "She is back."


Sosai zuciyar sa ta cika da farin cikin da baisan zai sake jinta nan kusa ba, har ta shige cikin class ɗin bai bar ganin ta ba.


Numfashi ya sauƙe kafin kuma ya maida duban sa ga kula ɗin, buɗe ta yayi nan yaga soyayyiyar indomie ce da ƙwai, saurin rufewa yayi lokacin da ƙamshin kwan ya bugo masa hanci har sai da yaji kansa ya ɗan juya masa.


Rufewa yayi ya maida gefe ya ajiye yana jin zuciyar sa na tashi.



Kifa kansa kawai yayi a guiwar sa yana lumshe idanu, ya daɗe sosai a haka kafin kuma ya tashi ya ɗau kular ya nufi inda ya saba zuwa yin wanka.


Ajiyar abincin ya bada sannan ya biya kuɗin wanka ya shiga yayi tare da sauya kayan sa ya fito.


Amsar kular yayi, aka lakuta masa man shafawa a hannu ya shafa, sannan kuma ya dawo inda ya saba zama lokacin har an tashe su a break.


Tsaye ya ganta a kusada bishiyar tana dube-dube da alamu dai neman sa take.


Takowa yayi ya ƙaraso wurin yace "Are you looking for me?" ya faɗa yana samun wuri ya zauna tare da ajiye kular.


Idanu ta zuba masa kawai tana kallo ba tare da tace komai ba.


Ɗan murmusawa yayi ya ɗau kular yana miƙa mata.


Amsa tayi jinsa da nauyi yasa fuskar ta matuƙar sauyawa, zama tayi tare da buɗe kular nan dai taga bai ta6a abincin ba.


Ɗagowa tayi da fuskar ta da ta ɗanyi fayau kamar ta ɗan rame inda kuma idanun nata suka ɗan ƙarayin girma tana kallon sa.


Kauda idanu yayi daga kallon ta yana wasa da sarƙar sa da ya ciro.


Idanu ta maida kan sarƙar tana kallo, tana kallon yadda yake lailaya ta a hannun sa.


Ɗagowa yayi nan suka haɗa ido, mamaki ne ya cika shi ganin kamar bata ta6a gajiya da kallon mutane, a yanzu ya gane ba mayya bace but naturally kawai haka Allah yayi ta da yawan kallo.


Baki ya buɗe yace "Don't cast an evil eye on my Necklace, this Necklace means the world to me, gara ma ki daina kallon sa" ya faɗa yana maidawa cikin aljihun rigar sa.


Barin kallon sa tayi dan yau ɗinma taga kamar zagin ta yayi dan haka kawai ta sauƙe jakar goyon ta ta ciro ɗan ƙaramin fork a ciki, sannan ta shiga cin abincin ta.


Kallon yadda take cin abincin yake kamar batason ci, bata iya cinƴewa ba ta rufe sauran ta maida kular cikin jakar makarantar ta.


Tana shirin tashi ta tafi ne yace "Hey."


Dakatawa tayi kawai tana kallon sa, nan yace "Wai ke bakya magana ne komiye?, anyways give me pencil and a Book."


Tsayawa tayi kallon sa dan bata fahimci abinda yake faɗa ba, ganin hakan yasa shi shiga yi mata gwari-gwari cikin gwada mata yace "Pencil and Book."


Sai a sannan ta gane abinda yake nufi dan haka kawai jakar ta ta buɗe ta ciro takarda da Pencil ɗin ta miƙa masa.


Kallon ta yayi kafin ya kalli ƙasan Pencil ɗin da duk a tattaune da alamu cinƴe sa takeyi _"Poor Pencil, shi ɗinma bata barsa ba tsabar maita, oh ashe ba mayya bace, and she didn't look like one"_ ya faɗa a zuciyar sa kafin kuma ya buɗe tsakiyar Book ɗin ya shiga zana Pencil a jiki wanda da alamu abu yake rubutawa, sai dai ya kan ɗago ya kalleta lokaci zuwa lokaci yana cigaba da rubutun da bata san na mene yakeyi ba, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kuma ya gama abinda yake rubutawan, ya hau kallon cikin takardar.



Murmushi yayi sannan kuma ya miƙa mata takardar tata, amsa tayi idanun ta akan fuskar sa da bata gajiya da kallo kullum, kafin kuma ta maida duban ta cikin takardar dan ganin abinda ya rubuta a ciki.


Sosai ta waro manƴan idanun ta dake nuna alamun mamaki tana ƙarewa kanta dake manne a jikin takardar kallo.


She can't believe her eyes, sak ita take kallo a jikin takardar nan, kamar wacce ke ganin reflection ɗinta a jikin madubi.


Tsinkayo muryar sa tayi yana faɗin "Do you like it?."


Kallon sa tayi har yanzu fuskar ta bai bar fitar da mamaki ba, kafin kuma ta saki murmushin da ya ƙara mata kyau sosai tana kallon cikin takardar tace "It's me."


_"She is beautiful"_ ya faɗa a zuciyar sa ba tare da ya iya ɗauke idanun sa daga kan fuskar ta dake murmushi ba.


"This is me" ta sake faɗa cike da jindaɗi tana kallon cikin takardar.


"DEENAH" ta jiyo muryar Jafar ta bayan ta.

Da sauri cike da jindaɗi tace "Yaya, yaya kazo kaga ni, ni ya zana a cikin takardar nan" ta faɗa tana nufar wurin sa ta shiga nuna masa.


Waro idanu shima Jafar yayi cike da ɗumbin mamaki kafin ya kar6i takardar daga hannun DEENAH ya shiga ƙare masa kallo yana kallon fuskar DEENAH ɗin.


"Wooww" ya faɗa cikin sakewar baki kafin yace "Waye yayi miki?."


Da hannu ta nuna ZEEYAD dake zaune kawai yana kallon su.


Zuwa yayi ya zauna kusada ZEEYAD ɗin yace "This is amazing, you're so talented, nima zaka zana min?" ya faɗa yana kallon ZEEYAD ɗin cikin murmushi.


Sai a sannan ZEEYAD ya saki fuska yayi murmushi yace "Yeah sure."


Da sauri ya buɗe jakarsa ya ciro takardar sa yace "Gashi nima ka zana min irin na DEENAH, nima ka zana ni ina dariya."


Zama DEENAH tayi kusada yayan nata tana kar6ar takardar ta a hannun sa tana sake kallo cike da farin ciki.


Cikin ƙanƙanin lokaci yayi zanen Jafar da DEENAH da takardar dake hannun su suna kallo suna murmushi.


"Done" ya faɗa yana miƙawa Jafar takardar.


"Wooww DEENAH ki kalla, mu biyu ya zana" ya faɗa yana nunawa DEENAH takardar.


Dariya ta saki nan tace "Kamar hoton mu ya ɗauka yasa a ciki."


Da sauri Jafar ya ɗago ya kallesa yace "Zaka iya zana Ummar mu?."


Murmushi ZEEYAD yayi yace "Bansan Ummar ku ba, sai dai idan zaka kwatanta min yadda take."


Da sauri ya sake miƙa masa takardar yace "Zan faɗamaka yadda take, da DEENAH take kama, sai dai ita fara ce kamar ni, idanun ta basu kai na DEENAH girma ba amma kuma yafi nawa da kaɗan, hancin ta dogo ne mai ɗan tudu da kauri, bakin ta kuma ƙarami ne irin na DEENAH, sai dai kasan ita Babba ce" ya ƙarashe faɗa yana kallon ZEEYAD dake ta zane a jikin Book ɗin.


"Is that all?" ya faɗa yana kallon Jafar.


Kai Jafar ya jinjina masa, murmushi ZEEYAD yayi yace "No baka ƙarasar da kammanin ta ba."

"Mene ya saura da ban faɗa ba?."


"Her eyebrows, her eyelashes, her cheeks komai yadda yake a fuskar ta."


Nan yace "Eh hakane" kafin kuma ya shiga sake yi masa bayani dalla-dalla yadda Ummar su take.


Miƙawa Jafar takardar yayi nan ya kar6a dawuri dukkan su shida DEENAH suna maida duban su ciki.


"Umma ce" dukkan su suka haɗa baki wurin faɗa suna dariya.



"Ya'akayi kasan haka Umma take?" faɗin DEENAH tana ɗagowa ta kalle shi.



"Ke dalla baya jin hausa dai" faɗin Jafar kafin yayi wa ZEEYAD bayanin abinda DEENAH ɗin tace


"You are so wonderful, ya akayi kayi haka, Ummar mu ce sak ka zana" cewar Jafar ɗin yana kallon sa.


"Kawai na sani ne, ba kai ka faɗamin yadda take ba."


"Kenan kana nufin, idan muka faɗa maka yadda komai yake zaka iya zana shi sak?."


"Insha Allah" ya faɗa.


"Zaka zama abokin na?" cewar Jafar ɗin.


Murmushi ZEEYAD yayi jin yadda yayi maganar nan ya girgiza masa kai.


Cike da jindaɗi ya rungume DEENAH yace "Yace zai zama aboki na daga yau."


Murmushi tayi tana kallon sa, ƙarar bugun bell ɗinda sukaji ne ya sanƴa su tashi da sauri nan Jafar yace "Gashi zan bar maka takarda ta ka zana ni ni kaɗai, kaji?" ya faɗa yana ajiyewa ZEEYAD takardar tasa.


DEENAH ma ajiye nata tayi tana murmushi tana kallon sa.

"Mungode sosai, Allah yayiwa rayuwar ka albarka" cewar Jafar kafin yaja hannun DEENAH sukayi gaba.


Juyowa tayi tana kallon sa hakan yasa shi sakar mata murmushi kafin kuma ta juyar da kanta suna cigaba da tafiya.



Takardar DEENAH ya ɗauka ya shiga ƙarewa zanen hoton ta da yayi a jiki kallo kaifin yayi murmushi ya juya zuwa ga next page ya shiga yin wani zanen kuma.


Bayan an tashe su da yamma suka biyo ta wurin ZEEYAD fuskar su ɗauke da murmushi suka zauna a gaban sa, nan Jafar yace "Alhamdulillah, Mun tashi ka gama yi mana zanen?."


Takardar ya ɗauko ya basa kafin ya shiga buɗe nasa cikin farin ciki "Wooww" ya faɗa yana buga tsalle kafin ya shiga nunawa DEENAH, "Kinga ni ya zana da irin hular larabawa akaina, kiga yadda nayi kyau."


Murmushi DEENAH tayi tace "Ina nawa fah?."

Nata takardar suka buɗe Jafar, da har farin cikin da yake ciki yayi masa yawa yace "Ki ganki, kyakkyawa dake kiga har flower ya zana miki akanki kamar head-band kina murmushi."


Dariya tayi tana kallon cikin takardar tace "Muje gida mu nunawa Umma."


Kallon ZEEYAD Jafar yayi yace "Ya Sunan ka?."


Idanu DEENAH ta zuba masa jin koh mai zai ce, sai dai kafin ya buɗi baki yayi magana suka jiyo murya ta bayan su.
"Kan bantar Uba, mai kukeyi anan bayan kowa ya watse ya tafi gida?, ƴaƴan marar mutunci tsinannu" ya ƙarashe yana ɗaukar ƙatuwar bulala ya nufo su.


ZEEYAD ya gane shi, shine mutumin da yasa masa ido ƴan kwanaki biyun nan.


Hannun DEENAH Jafar ya ruƙo suna shirin rugawa ne a tsawace yace "Idan kuka kuskura kuka motsa koh da ƴar yatsar ku ne toh wallahi sai na lahira ya fiku jindaɗi a garin nan yau."


Duk tsayawa sukayi suna kallon sa had ya ƙaraso gaban su, nan ya shiga nuna su da bulalar yana faɗin "Ku gaku ƴaƴan tsinanniya kuma gantalalliya koh?, ita uwarku ta fice yawon karuwancin da ta saba ku kuma kuna nan wurin baƙon da baku san daga inda ya fito ba yana kwakule ku ya baku wani abin koh?."


"Mu ai Ummar mu ba yawon karuwanci take zuwa ba, aiki take zuwa ta samar mana abinda zamu ci kuma ta kula damu..." bai ƙarasar ba yaji wani irin bugu a bakin sa nan kawun nasu yace "Idan ba yawon karuwanci take zuwa ba, ina take samun kuɗin da har take iya ɗaukar ɗawainiyar ku duka, kuma wurin aikin nata ba duk maza ne suka cika ba, Allah ne kaɗai yasan 6arnar dake faruwa achan, kai kuma nan har ƙanwar ka shegiya mai idanun mujiyar nan kake kawo wa wani ƙato yana tatta6a ta koh?" ya faɗa yana shirin fizgo DEENAH da ta 6uya bayan Jafar.



"Ka sake ta, ka sake ta idan zaka dake ta ni ka

Please Login or Register in order to submit comment