Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dake ni a maimakon ta" cewar Jafar yana riƙo ta tare da miƙawa kawun nasu hannun shi.


"Kai ni zaka yiwa rashin kunƴa koh?, toh bari ka gani" ya faɗa yana ɗaukar bulalar da niyyar zuga mata ne yaji an riƙe bulalar taƙi yin gaba taƙi yin baya.


Maido duban sa kan ZEEYAD dake tsaye hannun sa riƙe da bulalar yayi yace "Eh tabbas babu shakka, kaga zan dake ta nayi mata lahani ina zaka samu damar shafa jiki mai laushi, ai dole ka riƙemin bulala."


"What is he saying and who is he?" ya faɗa yana kallon Jafar.


"Kawun mu ne, yayan Baban mu ne shi."


"Yeah, naga alama" ya faɗa yana maida duban sa ga kawu dake sake da baki yana kallon su.


"Leave the Kid's alone, and don't you dare try to raise your hands on them again"ya faɗa yana fuzge bulalar hannun kawun.


"Bakomai, bakomai zamu gamu ne a gida, ai idan kun samu mai tare muku anan waje, ita uwarku ta gida bata isa ta hana ni dukan ku ba, shaiɗanun banza da wofi" ya faɗa cikin borin kunƴa yana yin gaba.


Duk da kallo suka bisa kafin Jafar yayi murmushi yana kallon ZEEYAD yace "You scared him away."



"Did i?" ya faɗa cikin ɗan waro idanu.


"Yeah, idanun ka suna cike da kwarjini ne, inaga shiyasa ya tsorata ya gudu" ya faɗa yana ɗan dariya.


Murmushi ZEEYAD yayi sannan yace "Yakamata ku tafi gida haka nan, sai gobe kuma."


Kai ya jinjina masa kafin yace "Toh sai gobe, DEENAH zo mu tafi" ya faɗa yana sanƴa hannun sa kan kafaɗun ta suka wuce.



Da Kallo ya bisu, wondering wane irin rayuwa sukeyi a cikin gidan su tare da wannan shaiɗanin mutumin...........


**************************


.........."Ke zo nan" ta faɗa dai-dai lokacin da su DEENAH suka shigo cikin gidan.



Cikin sanƴin jiki ta ƙarasa wurin ta, nan tace "shiga ciki ki gyara min ɗaki da falo banajin daɗin jiki na."


Kallon ta kawai DEENAH ta tsaya yi, hakan yasa ta daka mata uban tsawa tace "Dan Uwarki ba dake nake magana bane, kin wani sanƴa ni a gaba kina kallo haba ku kaɗai yara a cikin gidan nan amma sai kubi kuyi ta sawa mutum ciwon kai kuna sashi ihun da baiyi niyya ba, zaki wuce ne koh sai na ham6are ki?" ta faɗa cike da masifa da hargowa tana aikawa da DEENAH muguwar kallo.



Jafar ne yace "Yanzu fah dawowar mu daga islamiyya koh hutawa bamuyi munci abinci ba, kuma kice zaki sata aiki?."


"Toh ɗan masu iya yi, ai dah kawai duka ka kawomin nasan dagaske kake jin haushin abinda nakeyi wa ƙanwar taka, marar kunƴar banza da wofi kawai, tsabar baƙin halin ka da rashin kunƴa baka isa a sanƴa ka aiki a gidan nan kayi ba, kuma dan tsabar rashin mutunci yaushe rabon ku da ku ganni a cikin gidan nan amma koh sannu da zuwa baku iya yimin ba koh?, yayi kyau ba laifin ku bane."



A fusace ya juya ya buɗe 6angaren su ya shige.



Maida duban ta tayi kan DEENAH tace "Wai ba zaki wuce bane banza."



"Toh ai Anty kin tare ƙofar shigan" ta faɗa cikin sanƴi kamar zatayi kuka.



Tsaki taja tace "Wuce, kuma wallahi kika buge ni na haɗa kanki da bango" ta faɗa tana ɗan matsawa kaɗan.



Ƙafa DEENAH tasa tare da ƙoƙarin wucewa a rashin sa'a ta taka mata Hijabi.



Fizgo ta tayi waje tare da shimfiɗa mata mari a fuska ta zungure ta har kamar zata faɗi tace "Duk girman idanun nan naki baki gani ba sai da kika taka min Hijabi da wannan takalmin naki da kika ɗebo uban najasa da datti a waje?, toh jeki gama gyara ɗakin ki fito ki wanke min shi dan dashi zanyi sallah akanki kuma ba zan ciro wani sabon Hijabin ba, kuma ki cire takalmin nan yanzu anan wurin, ba zaki shigar min dashi ciki ba."



Da sauri ta cire takalmin nata tana shigewa haɗi da matsar kwalla.



Koh da ta shiga kaca-kaca falon yake, ga kuma wani uban datti kamar bola kwanukan da akaci abinci dasu wanda da alama sun daɗe a wurin sakamakon abincin da duk ya bubbushe a jiki duk ta tattara su wuri ɗaya ta fito dasu baranda ta ajiye.



Tsintsiya ta shiga nema bata gani ba, hakan yasa ta faɗin "Anty ina tsintsiyar sharan?."


"Banidashi, jeki ɗauko na uwarki,kiyi amfani dashi" ta faɗa cikin yatsina fuska.


Wucewa tazo tayi taje part ɗinsu ta ɗauko tsintsiyar shara da mopper da abubuwan gyaran ɗaki duka ta fito.


Da kallo ta bita nan tace "Duk wadannan abubuwan na Ummar ku ce koh arowa tayi?."


"Na Ummar mu ce" ta bata amsa.


Baki ta ta6e tace "Wuce."


Wucewa tayi ta shiga kafin kuma ta hau gyaran cikin falon, kafin ta gama kuwa har an kira Magrib, gashi koh rabin gyaran bata yi ba.



Sosai ta fara sauri dan kuwa yau tasan ta shiga uku a hannun Rabi'atu ga kuma ɗaku na uku ne a cikin part ɗin nasu wanda duk sai tabi ta gyara su, gashi tunda ta dawo bataji muryar Ummar su ba, da alama dai bata dawo daga wurin aiki ba yau ɗin dawuri.



"Kutumar kan Uban chan" ta faɗa tsaye daga bakin ƙofar falon.


"Dan Allah Anty kiyi haƙuri, ƴunwa nakeji shiyasa banyi sauri a aikin ba" ta faɗa kamar zatayi kuka.


"Au bakici abinci ba koh?, zakiga bakici abinci ba dan Ubanki" ta faɗa tana bata mari a fuska sannan ta ɗaura da faɗin "Na baki minti goma ki gama tattara min cikin falon nan kiyi mopping ɗinsa mai kyau,kije ki ɗauko turaren uwarki ki sanƴa min."


"Toh" kawai ta faɗa tana cigaba da aikin nata da sauri.


Zama Rabi'atu tayi akan cushion tana aika mata da mugun kallo.


Itace bata gama aikin ba dawuri har sai da bakwai ɗin dare ya gifta kaɗan duk ta haɗa gumi sai kuka take sakamakon gajiya da kuma ƴunwa da takeji.


"Maida abubuwan ki ɗauko turaren wutar ki sanƴa min, gobe tunda bakuda makarantar safe kizo ki ƙarasar min da aikin."


"Muna da makarantar Boko fah gobe da safe."


"An biya muku kuɗin makarantar ne?."


Kai kawai ta jinjina mata hakan yasa ta daka mata tsawa tace "Da kai nayi miki magana?."


"Eh, an biya mana."


"Wuce dalla ki bani wuri."


Da sauri ta tattara kayan aikin ta fice daga part ɗin.


A komai part ɗin su Rabi'atu yafi nasu DEENAH kyau da tsaruwa dama kuma girma wanda shine ya kasance nasu DEENAH ɗin tun lokacin da Mahaifin su yake raye, amma tunda kawu ya auro amaryar sa Rabi'atu yasa ta a ciki Part ɗin ta daina samun isashhiyar gyara, ga kuma shegen ƙazanta a cikin ta, Rabi'atu irin matan nan ne da basu damu da gyara ba, ga kuma shegen hassada da baƙin ciki dama kuma sa ido a cikin ta, duk irin kayan da ta gani a jikin Ummar su DEENAH sai ta tada jaraba an siya mata irin sa idan kuwa ba haka ba tayi ta tada masifa da jarabawar tsiya kenan a cikin gidan, sosai ta ɗauki Ummar su DEENAH a matsayin kishiyar ta, dan kuwa ba ƙaramin kishi take da cigaban ta ba dukda mijin ta baya raye,amma bata zauna ba kasancewar tayi karatu sosai kuma har kwalin degree ne da ita, gashi kuma a yanzu tana shirin samun aikin Lawyer kasancewar abinda ta karanta kenan sai dai Rabi'atu batasan da hakan ba, da irin baƙin ciki da hassadar da zatayi mata ba kaɗan ba.


Fitar ta daga part ɗin ta hango Ummar su a tana girki akan Gas, da sauri ta ƙarasa tace "Ummah dama kin dawo?."


Kallon ta tayi tace "Na dawo, sai dai ban daɗe da shigowa ba, kinga yanzu ma na ɗaura girki."


"Amma Umma maiyasa baki dawo dawuri ba yau ɗin, kuma baki neme ni ba?."


"Aiki ne yayimin yawa a office shiyasa ban samu na kammala dawuri ba, ga kuma na wuce kasuwa yi mana siyayya, ban samu abin hawa dawuri ba, kuma ai na hango takalmin ki a bakin ƙofar Rabi'atu shiyasa ban damu da na neme ki ba, tunda yayanki yace min kina chan kina yi mata aiki, ashe ta dawo?."


"Toh Umma sannu da dawowa."


"Yauwa ƴar albarka jeki ajiye abubuwan hannun naki kizo kinji."


Da "Toh" ta amsa kafin ta shige ciki.


Ajiye abubuwan tayi a mazaunin su sannan ta shiga ɗaki ta ɗauko kaskon wuta da turaren wuta ta fito.


"Ina zaki dasu?."


"Anty ce tace na kawo mata nasa mata a ɗaki."


Shiru Ummar su tayi bata ce komai ba, hakan yasa ta wucewa.


Da sallama ta shiga nan ta sameta gaban TV tana kallo koh amsa sallamar ta batayi ba.


"Anty gashi nan."


"Ina wutar da za'a sanƴa turaren a ciki?."


Tsuru-tsuru tayi da idanu kafin tace "Babu wutar."


"Kamarya babu wutar?, ba yanzun nan naji muryar Ummar ku ba, bata hura wuta bane?."


"Eh, ba na mukubur ta hura ba yau ɗin."


"Tohh, a miye ta hura?."


"A Gas ne?."


Ta6e baki tayi tace "Manƴa, jeki anso min kaskon wutar ta na electric ɗinnan kizo ki samun a shi."


"Ai ya 6aci" ta faɗa tana kallon ta.


"Ya 6aci, kamarya ya 6aci, wa ya 6ata?."


"Tun rannan ne da kika ce na kawo miki, har ya faɗi a hannun ki ne bai sake kawo wuta ba."


Ta6e baki tayi tace "Bani turaren."


Miƙa mata tayi nan ta buɗe tare da kaiwa hancin ta, sosai yake da ƙamshi maimakon ta yaba sai tace "Ina wannan ɗinnan da nakejin ƙamshin sa har nan idan tasa ɗinnan?."


"Shi ɗin ya ƙare kuma bata sayi sabo ba."


"Mttssww, jeki kar6o min jafaran ki samin shi a haka nayi maneji" ta faɗa cikin yatsina tana ajiye turaren a gefen ta.


Ficewa tayi dan kuwa tasan shikenan kuma turaren ba zai sake dawowa wurin su ba.


Jafaran ta ɗauko ta kunna mata a falon harda cikin ɗaku nan part ɗin duka, inda duk datti ya cika su babu gyara tayi ficewar ta.


Koh da ta koma ta samu Ummar ta tasa mata ruwan wanka a kettle nan tayi wankar ta shirya cikin riga da wandon baccin ta, tayi sallahn Magrib ɗin da batayi ba, sannan ta zauna akan sallayar tana jiran a ƙira Isha'i tayi.


Bayan duk sunyi sallahr Isha ne kuma duk suna zaune a falon nasu suna kallo kasancewar girkin daren bai ƙarasa bane Jafar yace "Umma bari kiga wani abin mamaki" ya faɗa yana zuwa ya ɗauko jakar Islamiyyar sa.



Da kallo ta bisa nan DEENAH tace "Yaya, ka tsaya nima bari na ɗauko nawa" ta faɗa tana fita da gudu taje ɗaki ta ɗauko ta dawo fuskar ta ɗauke da murmushi.



"Umma kinsan mene?."



"Ina zan sani, ku faɗamiki meke saku farin ciki haka nima na tayaku."



"Zamu nuna miki amma sai kin rufe idanun ki."



"Tohh" ta faɗa cikin ɗan zaro idanu.



"Umma ki rufe" cewar DEENAH tana zagayawa ta bayan ta ta rufe mata fuska.



Dariya tayi tace "Toh na rufe, ku nuna min."



Ciro takardar da ZEEYAD yayi zanen su a jiki yayi ya buɗe page ɗin tsakiya inda Zanen hoton Ummar su yake ya buɗe yace "Umma kada ki buɗe sai na ƙirga uku."


Nan ya gyara takardar yana nuna wa a saitin ta kafin ya shiga ƙirga "One, Two, There....Surprise" ya faɗa da ƙarfi lokacin da DEENAH ta buɗe mata idanun nata.


Baki ta buɗe kawai cike da ɗumbin mamaki tana ƙarewa hoton kallo, hannu tasa ta amsa tana cigaba da kallo cike da mamakin da take ciki tace "Who drew this, did you?" ta faɗa cike da farin ciki tana kallon sa.



"Noo" duk suka haɗa baki wurin faɗa kafin yace "Abokin mu ne yayi."



"What really?, he is so very talented, wannan ne hobby ɗinshi, ya sanni ne?" ta
tambaya.



"Bamu saniba, kawai ya zana ne, bayan munyi masa kwatancen kamannin ki, bari kiga nawa da na DEENAH" ya faɗa tare da buɗe page ɗin baya take hoton sa ya bayyana.


"Wowww" ta faɗa.


"Umma kiga nawa, har biyu ya zana ni" ta faɗa tana kawowa kamar zata shigar da takardar fuskar Ummar ta.



Amsa tayi cikin farin ciki ta shiga ƙarewa DEENAH dake manne a jikin takardar kallo.


"Wowww, look at my cute gorgeous daughter" ta faɗa cikin murmushi tana kallon DEENAH.


"Umma kinga wanda ya zana mu, mu biyu nida DEENAH."


Amsa tayi ta shiga dubawa tace "Masha Allah, abokin ku yaro ne ya zana wannan abin i can't believe my eyes, lallai wannan yaron nada baiwa ta musamman, toh kuma nawa kuka bashi?" ta faɗa cikin murmushi tana kallon su.



"Bamu basa koh biyar ba?."


Baki ta buɗe tana kallon su kafin tace "Lala baku kyauta ba ƴaƴan nan, mutum yayi muku zanen nan kuma baku basa komai ba, lallai yanada kirki sosai."


"Umma ana bada kuɗi ne idan anyi?."


"Ehmana, kuɗi sosai ma kuwa, ki ganki fah ke sak ya zana babu bambamci, kuma kice baki basa komai ba."


"Kenan Umma kina nufin zai iya yin na kuɗi, idan yayi zanen mutane su basa kuɗi?."


"Yeah it's a good ambition ai, just take a Look masu baiwa ta musamman ne zasu iyayin wannan zanen, sannan kuma su iya neman kuɗi dashi, da akwai wadanda aikin su kenan kuma ba ƙaramin kuɗi suke samu ba, musamman ma ace a ƙasashen turai yake, suma girmama irin masu wannan baiwar sosai da sosai and with this he can make alot of billions idan Allah yasa masa albarka a ciki."


Kallon juna shida DEENAH sukayi suna waro idanu cike da mamaki kafin kuma su tsinkayo muryar Ummar su na faɗin "Wanene abokin naka, sannan a wane gida yake?."


Kallon juna sukayi yayin da fara'ar fuskar su ke ɗaukewa..............





*Dan Allah ku dinga yimin sharing mana saboda Allah👏🏽😩*





*MHIZZ JIDDHERR...........✍🏽*



[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





_Kada wacce tayimin Kuka a page ɗinnan😩_





*011...*





_*Banida lafiya ku sani a addu'oin ku, banyi editing ba*_




...............Da kallo suke bin juna wondering wane irin amsa yakamata su bawa Mahaifiyar tasu, Jafar ne yace "Umma ai basuda gida, shi kaɗai ne yake rayuwa."


"Um!, bangane ba, kamarya shi kaɗai yake rayuwa?."


"Umma Balarabe ne fah, ba ɗan nan ƙasar bane, kuma bashida wurin kwana da zama sai gindin ƙatuwar bishiyar dake hanƴar islamiyyar mu."


"Balarabe, then toh a'ina ya san ku har kuka zama abokai dashi?."


"Shine wanda DEENAH take kaiwa abinci kullum."


"Shine yayi wannan zanen?."


"Eh Umma kuma fah bayajin hausa ma, sai turanci kaɗai" cewar DEENAH tana kallon ta.


Tunani Ummar tasu ta shiga yi kafin ta rufe takardun tace "Ku maida cikin jakan ku, bari na dubo mana girkin" ta faɗa tana tashi ta fice zuwa waje.


Da kallo suka bita kafin Jafar ya kalli DEENAH yace "Ya naga fuskar Umma ya canza?."


"Koh ka sani zata ce kada mu sake kula shi tunda bamu sanshi ba" ta faɗa kamar zatayi kuka.



"Umma tana da kirki ba zata raba mu dashi ba."


Takardar ta sake ɗauka tana sake kallon hoton dake jiki fuskar ta na fitar da murmushi...........


******************


...........Washe gari bayan gari yayi haske tuni sunyi shirin makarantar su kowa ya sanƴa uniform ɗinsa inda Ummar su ma tayi shirin fita aiki.


Kallon Umma dake ta sauri tayi tace "Umma baki fah zuba min abincin ba."


"Wane abinci kuma DEENAH?" ta faɗa tana kallon ta.


"Abincin da zan kaiwa abokin Yaya."

"Ina shi yayan naki?."

"Yana waje."


"Kira shi yazo ya kai masa dawuri, kinga dai zanyi latti koh?."


Da sauri ta fice taje ta kira Jafar da har ya fice waje ta dawo.


Abincin Umma ta miƙa masa tace ya kaiwa abokin sa ya dawo da wuri su wuce.



Amsa yayi cike da farin ciki yace "DEENAH zo muje."


"A'a ba zata ba, kai kaje" cewar Ummar tasu hakan yasa farin cikin dake ɗauke kan fuskar DEENAH gushewa.


Ficewa yayi nan Ummar tasu ta kalli DEENAH da kanta ke ƙasa alamun tayi fushi kafin kuma tace "Kinason ganin sa kullum?."


Da sauri ta ɗago tana kallon Mahaifiyar tata jin abinda ta faɗa.


"Kinason ganin sa kullum?" ta sake tambayar ta.


Da sauri ta jinjina mata kai alamun eh, nan ta sake cewa "Daɗi kikeji a ranki idan kin ganshi?."


Shiru tayi tana kallon fuskar mahaifiyar tata kafin kuma tace "Umma idan yaƙi cin abincin da na kai masa ne nakejin babu daɗi."


"Maiyasa baya cin abincin da kike kai masa?."


"Nima ban sani ba, amma idan naje har korata yakeyi yace na daina zuwa kusada shi, kullum baya cin abincin da nake kai masa sai dai na baiwa almajirai a hanƴa."


"Bashida kowa, bashida wurin kwana kuma bayacin abincin da kika kai masa, strange" ta faɗa cikin ɗan nazarin abin kafin kuma ta numfasa tace "Okay muje."


Fitowa sukayi bakin ƙofar gidan suna jiran dawowar Jafar.


Suna tsaye suna jiran dawowar Jafar kawu ya fito daga cikin gidan, kallo ya ƙare musu sama da ƙasa kafin yace "Toh za'a fita harkar karuwancin da aka saba kenan?."


Ɗauke kai Umma tayi bata kulasa ba sai ma danne-dannen wayar da takeyi fuskar nan nata a murtuƙe.

Nan ya sake cewa "Ke, ki koma ba zaki makarantar ba, Rabi'atu bata jin daɗin jikin ta dan haka ki tsaya ki taya ta da ayyukan ta tukun."


"A wane dalilin?" cewar Umma dake kallon sa cikin mamaki tunda ya fara magana.


"A dalilin matata batada lafiya sannan kuma a matsayi na Na wan Mahaifin ta."


"Toh gaskiya kayi haƙuri, yanzu makaranta zata kuma ta riga da ta shirya, idan yaso idan ta dawo sai tayi mata aikin, amma yanzu kam gaskiya makaranta zata."


"Ni nace ba zata makarantar ba, Koh so kike dama ita Rabi'atu ɗin ta mutu koh, ke baki taimaka mata ba, ke kuma baki bar ƴar ki ta taimaka mata ba, kinayin haka ne duk dan kinsan batada ƴan uwa anan babu mai zuwa mata kullum taya ta aiki shiyasa kike haka, yanzu idan nayi magana nace ke kike 6ata ƴaƴanki da kanki sai ki hau ni da rashin kunƴa kina cewa ƴaƴan ki masu tarbiyya ne, ina tarbiyyar take bayan kina yi musu da hani da taimakon mutane."


Ummar su DEENAH sam batason surutu da hayaniya irin na Kawu gashi kuma akan hanƴa suke kowa na wucewa yana kallon su, ga kuma kawun baya magana a hankali, bai ƙi ya tara mata mutane ba yanzu sannan ya aibanta ta a gaban su tare da yi mata sharri, wannan ba damuwar sa bace, dan kuwa bashida mutunci koh kaɗan, hakan yasa Umma buɗe jakar ta ta ciro makullin part ɗin nasu ta bawa DEENAH tace "Yi haƙuri MADEENAT ƴar albarka, ki haƙura da makarantar yau ɗin ki taya antyn ki aiki,kinga batada lafiya koh?."


DEENAH da idanun ta suka tara hawaye ne tasa hannu ta kar6i makullin tace "Toh Umma bakomai zanyi mata aikin ai na kwana ɗaya ne kawai."


"Yauwa yarinƴa ta Allah yayi miki albarka" ta faɗa tana shafa kanta.


Tsaki kawu yaja sannan yace "Ni za'a nunawa tijaranci da munafurci?, ke kanki kinsan a matsayin ƴaƴa na suke sannan kuma ina da kowane irin iko akan su ke baki isa ki hana ni yin abinda nayi niyya game dasu ba, shima wannan jan ƙosan kwanan nan zan fara maganin ka kaima" ya faɗa yana nuna Jafar dake ƙarasowa wurin nasu yana aikawa da kawu da mugun kallo.


"Jeki kinji" ta faɗa tana share maganar Kawu ɗin.

"Umma ina kuma zata je?, sati uku fah bata je makaranta ba duk dan sabida Kawu da ya ɗauke ta ya kaita ƙauye ta sha wahala ta dawo dakyar kika samo kuɗin amso ta, shine kuma yanzu zai ce ba zata je makarantar boko ba, shi yake biya mana kuɗin makarantar ne?" ya faɗa cike da muguwar haushin kawun nasu dake cinsa.


"Kin gani koh, kina dai ganin irin maganganun da yaron nan ke faɗamin a gaban ki amma kin kasa hana sa, sabida kina jin daɗin yadda yake min magana kamar wanda shine na sama dani, toh koh mahaifin ka da yake raye baya yimin magana gatsai haka balle kai ɗan da ya haifa jiya-jiya, jeka makarantar ka dawo zaka dawo ne ka same ni anan gidan, ɗan iskan banza ɗan iskan wofi."


Hannun Jafar kawai Umma taja sukayi gaba ba tare da tabi kan maganar kawu ɗin ba.


Da kallo DEENAH ta bisu tana matsar kwalla, dan kuwa tasan ba ƙaramar baƙar wahala zata sha a hannun su ba yau.


Tsaki yaja sannan ya juyo ga DEENAH tare da daka mata tsawa yace "Zaki shiga ciki ne kokuwa sai nayi kwallo dake, shegen kanta yawa yawa tayan tifa."


Tusa ta gaba yayi har part ɗinsu sannan ya hau ƙwala kiran "Rabiya"

A ƙufule ta fito idanun nan duk a kumbure kwantsa ya cika da alama ma tashin ta kenan daga bacci nan tace "Haba dan Allah Mai-gida, wannan wace iriyar wulaƙanci ce?, ina cikin bacci na kayi ta kwala min kira haka sai kace wanda za'a tashi ƙiyama mtssww" ta faɗa tana tufar da ƴawu.


Haƙora ya washe yace "Allah ya huci zuciyar ki gimbiya ta, jeki kawai kiyi kwanciyar ki ga nan mai aiki na samo miki, ita zata yi miki dukkanin ayyukan cikin gidan nan, ni yanzu bari na fita naje nayo cefanen kayan miyar da za'a yi, ai kince kaza kike so koh?."


Yatsina fuska tayi tace "Eh kaza nakeso, sannan kuma ka haɗomin da gasasshiyar ta da 5Alive, na samu naci sabida ƴunwa nakeji yanzun."


Dariya yayi yace "Kada ki damu bari naje ni yanzun nan na dawo, ke kuma ki tabbatar da kin kammala dukkanin ayyukan ki kafin na dawo cikin gidan nan idan ba haka ba yau sai jikin ki yayi tsami a gidan nan, kinji koh bakiji ba?."


"Naji" ta faɗa kanta a ƙasa.

Maida duban sa yayi ga Rabi'atu yace "Shalele ta bari naje ni yanzun nan na dawo."


"Toh" kawai tace koh ladar samun addu'ar dawowa lafiya bai samu ba haka nan ya fice kamar ya tashi sama dan sauri.


Kallon DEENAH dake tsaye tayi tace "Ke dan gaki isashhiya jiya ban ce miki akwai aikin da zaki ƙarasar min ba, amma dan munafurci shine kika shirya kika kama hanƴa da niyar ficewa zuwa makaranta?."

"Kiyi haƙuri mantawa nayi."


Rankwashi ta zuba mata a tsakiyar kai tace "Mantawa kikayi, ni zakiyi wa ƙarya toh dan Ubanki ki wuce kije ki ƙarasar min da aikin jiya."

Hannun ta dafe da kanta tayi hanƴar part ɗinsu tana matsar kwalla.


"Ina kuma zaki?."


"Canzo kaya na zanyi."

"Zo nan" ta faɗa.


Zuwa DEENAH tayi ta tsaya a gaban ta nan ta miƙa mata hannu tace "Bani makullin."


Makullin DEENAH ta bata nan kuma ta sake cewa "Ina abincin makarantar ki?."


"Yana cikin jaka na."


"Ciro shi" ta faɗa cikin tsuke fuska.


Sauƙe jakar makarantar tayi ta ciro lunch box ɗinta a ciki da ledar bredi ta miƙawa Rabi'atu.


Amsa tayi tare da buɗe kular nan ƙamshi ya bugo mata hanci harda su lumshe idanu, Farfesun Cow- tail ne sai shining yakeyi mata a idanu nan ta haɗiyi ƴawu tace "Cha6 ana bura uba a cikin gidan nan, wato ku nan har farfesu akeyi muku ku kai makaranta lallai daɗi yayi muku yawa, yanzu da ban tambaya ba haka nan zakije ki ajiye shi tsabar baƙar zuciya da mugunta irin taki bayan kinsan banida lafiya ga kuma ƴunwa dake nuƙurƙusar ƴan hanjin ciki na, lallai ƴar gata" ta faɗa tana tsamo nama ɗaya ta jefa a bakin ta tana tauna harda su lumshe idanu.


Suɗe hannu tayi tace "Wuce kije ki fara yi min aikin" ta faɗa tana amsar jakar makarantar ta.


Shigewa DEENAH tayi zuwa falon nan ta gansa kaca-kaca kamar ba jiya ta gyara sa ba, tattare ledojin da ta gani anci abu a ciki tayi ta fito ta sasu a dustbin kafin kuma ta kalli part ɗinsu da yake a buɗe da alamu Rabi'atu na ciki nan taje ta dan ɗauko tsintsiya.


Inda suke ajiye kayan shara ta nufa ta ɗauko, motsin da taji a ɗakin Ummar ta ne yasa ta zuwa ta leƙa, daidai lokacin kuma Rabi'atu ke ƙulle abu a bakin zanin ta.


Jin kamar tsayuwar mutum ne yasa ta juyowa a firgice tana kallon DEENAH dake tsaye tana kallon ta, Wata iriyar azababbiyar ashariya ta dumulmulo tare da sauƙe shi akan DEENAH tace "Dan bahun ubanki mai kikeyi anan, ba cewa nayi kije kiyi min aiki na ba?."


"Kayan shara nazo ɗauka fah."


"Kayan shara kika zo ɗauka shine zaki sanƴa ni gaba kina kallo da wadannan mayun idanun naki, shegiya mai suffar kafiran aljanu, algunguma kuma wallahi kika kuskura kika buɗi baki kika cewa Ummar ki na ɗau mata abu a ɗaki wallahi sai kin gane kurenki a gidan nan kin dai san hali na koh?, zaki ficemin ne koh sai nazo nayi wurgi dake anan shegiya mai kama da farar mayu."


Da sauri DEENAH ta fice ta juya ta bar ɗakin, nan kuma Rabi'atu ta cigaba da binciken ta har dasu sauƙe akwati tana cicciro abubuwan dake ciki, duk wanda taga yayi

Please Login or Register in order to submit comment