Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da take buƙata kaima kayi ƙoƙarin hakan amma mai ya ragu cikin halayyar ta?, babu, sai ma abin da yayi gaba, ya toh takeson ayi mata tunda ta kasa haƙuri ta rungumi jarabawar da Allah ya ɗaura mata, a hakan takeson samun sauƙi kullum itace cikin tunani da kuka, akanta aka fara rashin masoyi komiye, dah mutuwa kuma shi ZEEYAD ɗin yayi ya zatayi da ranta kenan, bata ga damar samawa kanta sauƙi ba Jafar, bata shirya rungumar ƙaddarar ta ba, kai kanka ka sani nayi dukkanin iya ƙoƙari na amma tayi ƙeƙe da kunne bataji, jiya a gaban ka ta gama yimin rashin kunƴa ta kuma ce na fita harkar ta, har cewa tayi ta tsane ni, ni Jafar upon all mutanen dake duniya sai ta rasa wa zata tsana sai ni, menene banyi muku ba a rayuwa?, wane irin farin ciki ne ban baku ba, ban ta6a bari kunyi kukan rashin mahaifi ba, baku ta6a neman abu a guna kun rasa ba koh na hana ku ba, koh da kuwa ace dukkanin kuɗin da ya rage min kenan indai kuka kawo buƙatar ku inayi muku Jafar, yau dan kawai DEENAH tayi rashin masoyi sanadiyya ta na zama maƙiyar ta, ta ɗau karar tsana ta ɗaura min har take ikirarin bana sonta, yanzu da abinda yakamata ta saka min kenan, ai gani nake inada iko wurin za6awa DEENAH mijin aure, yau dan na hana ta abu ɗaya a rayuwar ta sai na zame mata gagarumar mai laifi a wurin ta, har kaima kake goya mata baya kuke ganin rashin kyautatawa ta, dukkan ku da abinda zaku sakamin dashi kenan Jafar?, Bakomai" ta ƙarashe maganar cikin share hawayen fuskar ta tana samun bakin gado ta zauna, zuciyar ta nayi mata mugun zafin da ita kaɗai ta san abinda takeji.

Sosai jikin Jafar yayi sanƴi da maganganun Umma, sai yanzu yake gano rashin kyautatawar su a gareta, Umma mahaifiyar su ce, sannan babu farin cikin da bata basu a rayuwa ba, haka kuma she has the right ɗin yanke decision koh wani choice cikin rayuwar su, tabbas indai har kanason gamawa da duniya lafiya toh fah ya zama dole kabi maganar Mahaifiya, koh da kuwa ace bata wani bada gudunmawa sosai wurin gina rayuwar ka ba, but Umma babu abinda batayi musu ba, bata ta6a bari sunyi kukan rashin mahaifi ba kamar yadda ta faɗa, ta kan sadaukar da dukkanin wani farin ciki nata wurin ganin nasu farin cikin koh da kuwa it will cost her dukkanin abinda ta mallaka a wannan lokacin, ta tsaya wurin gina rayuwar su tare da basu tarbiyya mai kyau, tayi rayuwar ta ne wurin gina su tare da tafiyar dasu kan hanƴa madaidaiciya, tayi sacrifing alot akan su, and now dan tayi sanadiyyar barin ZEEYAD cikin rayuwar su suka ɗau laifi suka ɗaura mata, ba tare da sunyi nazarin cewa maybe Allah bai ƙaddara cewa zasuyi rayuwa ta har abada dashi ba, ba tare da sunyi nazarin mutane dayawa su kan zo su bar cikin rayuwar ka ba, wasu ma mutuwa sukeyi, wasu kuma zakuyi zaman mutunci dasu kamar ba za'a ta6a rabuwa ba sai dai kuma ka wayi gari babu su sunyi maka nisa wataƙil kuma shikenan ba zaku sake haɗuwa ba kuma sai a lahira, wataƙil hakan ce ta kasance tsakanin su da ZEEYAD ma maybe su sake ganin sa wataran maybe kuma ba zasu sake haɗuwa a duniya ba, Umma tayi sanadiyyar barin sa cikin rayuwar su ne, amma idan kayi dogon nazari dama chan haka Allah ya tsara rayuwar tasu zata zo ta kasance, basuda wani abin da ya wuce kawai suyi haƙuri, kowa na yin laifi kasancewar ɗan adam ajizi ne, amma su idanun su ya rufe sun ɗaurawa mahaifiyar su laifin abinda ba ita ta tsara ba kacokan akanta, ba tare da sunyi tunanin Allah ne ya tsara cewa rayuwar su zata kasance hakan ba, sannan kuma abinda yakamata suyi shine haƙuri musamman ma DEENAH da takejin itace tafi kowa rashi.

Kallon Umma dake ta kuka yayi bayan dogon nazarin da yayi, nan kuma duk yaji tausayin ta ya kama shi yanajin babu daɗin dukkanin abinda sukayi mata a ransa, kunƴa ce ta lullu6e shi wai yau sune suka sanƴa mahaifiyar su mai son ganin farin cikin su a kullum kuka.

Zuwa yayi ya rungume ta yana patting nata a baya ba tare da ya iya furta komai ba.

DEENAH dake tsaye bakin ƙofar ɗakin tun bayan barin ƙofar ɗakin ta da Jafar yayi ta buɗe ta fito tana sauraren su saurin komawa ɗakin ta tayi tana rufo ƙofar tare da zuwa bakin bed ta zauna tana fashewa da wani irin matsanancin kuka.

Kuka take sosai harda shessheƙa kamar zata shiɗe zuciyar ta nayi mata zafi sosai.

Wato kenan ta rasa ZEEYAD har abada kenan?, dan kuwa taga har yanzu Umma na kan bakar ta bata ga alamun zata sauƙo nan kusa ba, ita kuma maybe ta mutu zuwa lokacin da zata sauƙo ɗin.





*Yawan Comment, Yawan Typing*







*MHIZZ JIDDHERR...............✍🏽*
[8/7, 1:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```






*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*






*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*







*037...*




_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_



_*Masha Allah ZEEYAD FANS CLUB, Gaskiya Comments naku ba ƙaramin burgeni tare da sanƴa ni farin ciki yake ba, haƙiƙa kuna matuƙar ƙoƙari wurin faranta min, babu abinda zance daku sai Allah Ubangiji ya bar Kauna, ya faranta muku kamar yadda kuke faranta min, yayi wa rayuwar ku data iyayen ku, ƴaƴan ku dama kuma mazajen ku da ƴan uwanku albarka🤲🏽🥰, Nagode sosai da iriyar ƙaunar da kuke nunamin , Allah Ubangiji ya bar zumunci*_





*LONG PAGE🤸🏽‍♀️*





_________Jafar ne zaune yake ta rarrashin Umma da har yanzu bata sauƙo ba, sakamakon zuciyar ta dake mugun zafi da halin DEENAH.

"Menene banyi wa DEENAH ba a rayuwa, mai ta nema ta rasa daga gareni, wai akan ɗa namiji DEENAH ke furta min kalmar tsana har take ikirarin kada nazo kusa da ita bata buƙatar gani na, take gani na a matsayin mai son zuciya."

"Umma dan Allah kiyi haƙuri haka nan, DEENAH tana cikin mawuyacin hali and am definitely sure ita kanta tayi nadamar abubuwan da ta faɗa miki, Umma she is depressed am sure batasan tayi wasu abubuwan ba, dan Allah ki bar kukan nan haka hakan zai iya jawo fushin Ubangiji akan mu, ace mun sanƴa mahaifiyar mu zubda hawaye, please i beg you ki bar kukan nan haka" ya faɗa cikin rarrashin ta.

Hawayen ta ta shiga gogewa yana taya ta kafin tace "Insha Allah, Allah ba zaiyi fushi daku ba banyi kukan nan dan jawo muku fushin Ubangiji ba, sai dai ina yinsa ne kawai dan tausayin DEENAH bakomai ba."

Ajiyar zuciya Jafar ya sauƙe kafin yace "Umma nasan abunda DEENAH tace miki ne ya ƙona miki zuciya haka, dan Allah Umma kiyi haƙuri ki yafe mata, nima kuma ina neman gafararki, sannan ki cigaba da yiwa DEENAH addu'a har Allah yasa ta dawo dai-dai, na tabbata ita kanta ba zataji daɗin abinda tayi miki ba."

"Bakomai Jafar, komai ya wuce, insha Allah zan cigaba da yi mata addu'a sannan kaima inason kayi hakan, Allah yayi muku albarka duka."

"Aameen Umma, insha Allah zanyi yadda kika ce, kuma Umma yakamata ita ma kanta DEENAH ɗin ta tashi tsaye da addu'a, sannan ta yawaita karatun Alƙur'ani sabida rage shiga ƙunci, am sure idan ta riƙe wadannan abubuwan Allah zai kawo mata ɗauki tare da gusar mata da dukkanin wani damuwa da ƙuncin ta."

"Ai sai dai kai kayi mata magana, koh bakaji abinda tace min bane?."

"Umma ba zaki biye mata ba, am sure a yanzu babu abinda tafi buƙata kamar ke, it's just that kawai halin ƙunci da baƙin cikin da take ciki ne zai sa ba zata bar ki ki ra6e ta ba, Umma baikamata ki biye mata akan wannan furucin da tayi ba, DEENAH tafi buƙatar ki fiye da kowa a yanzu i know kinyi dukkanin ƙoƙarin ki, but indai har kika cigaba da janta a jiki am sure zata warware ta kuma manta komai."

Shiru Umma tayi kafin tace "Toh shikenan Jafar zanyi hakan."

"Yauwa Umma, zanje na sake confronting ɗinta naga koh zata buɗe ɗakin."

Bata ce komai ba ya tashi ya fice zuwa ɗakin DEENAH, ganin ƙofar a buɗe ya sanƴa shi turawa yana leƙa kansa.

Zaune ya ganta tsakiyar bed ɗin tayi crossing ƙafar ta tana zane da hannun ta jikin bedsheet ɗin.

Sallamar da taji yayi ne yasa ta ɗago kanta tana kallon sa.

Idda shigowa ɗakin yayi yana maida ƙofar ya rufe, DEENAH maida kanta ƙasa tayi tana cigaba da abinda takeyi.

"DEENAH?" ya kira ta calmly.

Bata ɗago ba haka ma bata amsa masa ba, zama yayi bakin bed ɗin yana facing nata, bai ce da ita komai ba sai kallon ta kawai da yakeyi, kafin kuma daga bisani yace "Do you mind us going on an outing?."

Tsayawa tayi kafin kuma ta ɗago kanta tana kallon shi, kai ya jinjina mata yace "Maybe zaki ɗan ji sassaucin abinda kikeji."

Maida kanta tayi tace "No."
"Why?" ya tambaye ta.
Shiru tayi kamar ba zata amsa ba kafin kuma tace "I don't feel like going out."

Shiru Jafar yayi kafin yace "What of idan mukaje Cinema anjima?."

"No" ta amsa.
"Ice-cream?."

Kai ta jinjina masa tace "No."
"Burger?."

Ɗagowa tayi tana kallon sa, kallon ta yayi yace "You want Burger right?, i will get it for you."

"I...i don't want anything" ta faɗa tana sadda kai ƙasa.

Kallon ta yake kafin yace "Look DEENAH, lets talk serious Okay, why are you doing this to yourself?."

"You need to move on DEENAH, ZEEYAD ba zai dawo ba, he is gone forever kenan DEENAH, ki bar yawan sanƴa kanki cikin ƙunci da tunanin sa haka, i know yanzu shima yayi moving on da rayuwar sa..."

"No" ta katse shi kafin ta ɗaura da faɗin "Kai kacemin yana sona sosai and he is ready to sacrifice everything for my sake, and you expect him yayi moving on da rayuwar sa so soon haka bayan abinda Umma tayi masa, i know that he still loves me sannan zai iya dawowa gareni ko wane lokaci ne" ta ƙarashe wani irin siririn hawaye na biyo mata fuska.

"Look DEENAH Stop blaming Umma for all this, she is not at fault..."

"She is not at fault then laifin wanene kenan, she is responsible for everything thats happening to me."

"Stop it DEENAH" ya faɗa a tsawace, kallon idon ta yayi yace "Let me tell you maganar gaskiya, ZEEYAD ba zai ta6a dawowa ba sannan ba zai ta6a neman ki ba, haka ma ba zai ta6a dawowa ƙasar nan ba, stop deceiving yourself, ke kina nan believing cewa yana tunanin ki kamar yadda kika addabi kanki da nashi kullum ba tare da kin san meke faruwa chan tattare dashi ba, who even knows koh ya riga da ya manta ki, ke kina nan kina baiwa kanki wahala, people change DEENAH, and sometimes for the worse, you need to understand this."

Sosai zuciyar DEENAH ke zafi da maganganun Jafar, pillow ta janƴo tana wurga masa in a rude manner tace "You're lying, i know bai manta dani ba, and he still loves me sannan zai dawo anytime for me, he still loves me, Okay?."

Ran Jafar ne yayi mugun 6aci, sai dai ya dake tare da girgiza kai yace "You have changed alot DEENAH, ba haka kike dah ba, you need to get back to your old self tun kafin lokaci ya ƙure ki rasa rayuwar ki a banza, while shi kuma ya samu wacce yake so yayi auren sa, ke kuma ki tsaya tunanin sa ya kashe ki tunda shi kaɗai ke sonki mu baki ɗauke mu matsayin masoya ba, i can't believe how rude you've been to our Mom jiya na cewar kin tsane ta sannan bakyason ta kusa dake, kinsan how badly kika yi hurting nata kuwa?, instead of kiyi nadamar hakan kinzo nan kina tunanin abinda ba zai fice ki ba, look DEENAH daga yau nida Umma kowa ya fita harkar ki kije kiyi dukkanin abinda kike ganin shine dai-dai da rayuwar ki, babu wanda zai sake interfering a rayuwar ki bale ki faɗa masa babu daɗi, just do what you think is right for you" ya faɗa yana miƙewa tsaye.

Tashi tsaye tayi itama a fusace tace "Yes i would do what i think is right for me" tana faɗin haka ta nufi wurin closet ɗinta tare da buɗe shi ta ciro akwatin kayan ta, kafin ta buɗe sauran 6angare biyun ta shiga fiddo da kayayyakin ta tana wulla su kan bed.

Da kallon mamaki Jafar ke binta dashi har ta gama fiddo kayayyakin, kafin ta ɗago akwatin zuwa kan bed ta buɗe shi ta fara zuba kayayyakin nata a ciki.

"What...what are you doing DEENAH?."

Bata kula sa ba sai ma cigaba da jera kayayyakin nata da tayi a ciki.

"Am sorry DEENAH, i didn't mean to..." katse shi tayi da faɗin "Am doing what i think is right for me, koh ba kai bane ka bani go ahead ɗin yin hakan?."

"Yes nace kiyi dukkanin abinda kika ga dama but bance kiyi packing kayayyakin ki ba, where do you think you're going?."

"Zan tafi inda za'a nuna min so da ƙauna tare da kulawa ne" ta ƙarashe tana zipping akwatin bayan ta gama jera kayayyakin tare da sauƙo dashi ƙasa tana jan shi.

Da sauri Jafar yaje yana tare bakin ƙofar yana kallon ta yace "What has come all over you DEENAH?."

"Mai kuke so nayi muku a cikin gidan, no one values my feelings, babu wanda ya nuna kulawar sa akan abinda nakeji, bakuda abin cemin kullum da ya wuce na manta shi sannan nayi haƙuri, but kun ƙi ku gane cewa it's so hard for me, nikaɗai nasan mai nakeji ba zaku ta6a fahimta ba."

"Let her go Jafar?" ya tsinkayo muryar Umma a bayan shi.

Juyowa yayi yana kallon Umma yace "Let her go..., to where exactly?."

"To where ever i want" cewar DEENAH ɗin.

Juyowa yayi yana kallon ta kafin yace "No, you aren't going anywhere, not even nan da ƙofar falo."

"Alright then, try and stop me" ta faɗa tana shirin wucewa ta space ɗin da ya bari.

Saurin sanƴa hannun sa yayi yace "I told you babu inda zakije DEENAH."

Kallon sa tayi tace "Ka barni na wuce."

"Please DEENAH" ya faɗa.

"Kai kace nayi dukkanin abinda naga dama."

"Yeah, i said that but bance ki haɗa kayan ki ki tafi ba."

"Move out of the way" ta faɗa tana kallon sa cikin fushin da ya fara taso mata.

Kai ya girgiza yace "Maybe over my dead body."

A tsawace cikin sarƙewar numfashi ta sake cewa "Stay out of the way, now."

Idanu kawai ya zuba mata ba tare da ya ɗauke hannun nasa kuma ya motsa ba.

"Stay out" ta faɗa cikin azababbiyar fushin da tazo mata tana ɗauke fuskar sa da mari tana huci inda kuma numfashin ta ya shiga sarƙewa.

Umma kwalalo idanu tayi tana rufe baki da hannayen ta biyu lokacin da DEENAH ta mari Jafar.

Jafar ɗago da fuskar sa da tayi jaa yayi yana kallon DEENAH da itama shi take kallo.

Fashewa tayi da kukar nadamar da tazo mata tana zubewa kan guiwowin ta.

Sosai take dizgar kukan kamar ranta zai fita, inda duk suka tsaya kallon ta babu wanda ya iya tanka mata.

Shiɗewa ta farayi da kukan inda kuma numfashin ta ya shiga seizing kukan nata na yayyankewa, duk sake maida duban su kanta sukayi kafin suyi wani yunƙurin kuma tayi collapsing a wurin, Jafar ne yayi saurin taro ta yana kiran sunan ta "DEENAH?."

Umma da sauri itama ta shigo ɗakin tana riƙo ta tare da kiran sunan ta "DEENAH?."
Kallon Jafar da shima duk hankali tashe tayi tace "Ya dai...meke faruwa ne Jafar, Mai ya same ta?."

Kallon Umma Jafar yayi kafin ya miƙe tsaye yace "Umma bari na ɗauko key ɗin mota mu kaita asibiti" yana faɗin haka ya fice da sauri.

Jijjiga ta Umma ta shiga yi cike da tashin hankali tana kiran sunan ta.

Dawowa Jafar yayi riƙe da key ɗin mota a hannun sa yace "Let's go Umma."

Cicci6ar ta yayi tare da yin waje da ita, Umma ɗaki ta wuce ta ɗauko mayafin ta cike da tashin hankalin da take ciki ta mara masa baya.


************************


________Likitoci ne suka duƙufa kan DEENAH da numfashin ta yayi low sosai suna iya bakin ƙoƙarin su wurin ganin sun ceto rayuwar ta.

Umma dake ta kai kamo babu abinda take sai kukan halin da DEENAH ke ciki, tana tsoron kada ta rasa ƴar tata a wannan karon.

Jafar rarrashin ta kawai yake shima cikin dauriya, kallo ɗaya zakayi masa shima kaga tashin hankali ɗauke kan fuskar sa.

Da kyar da siɗin goshi likitoci suka samu numfashin ta ya ɗan daidaita, dan haka Oxygen suka sanƴa mata da wasu na'urorin su kafin su fice.

Tare ɗaya su Umma sukayi bayan fitowar su yayin da sauran suka wuce uzurin gaban su.

Cike da muguwar 6acin rai Likitan ke kallon su kafin yace "Muje Office" yana faɗin haka yayi gaba inda suka mara masa baya.

Cire coat ɗinsa likitan yayi yana lanƙaya ta jikin hanger, kafin yaja kujerar sa ya zauna yana nunawa su Umma kujerar dake facing ɗinsa alamun su zauna.

Zama sukayi idanun su akan sa inda duk sun ƙagu suji abinda zai ce.

Wani file ya ɗauko ya ɗanyi rubuce-rubucen sa a jiki kafin ya ɗago yana kallon su yana mai harɗe yatsun sa yace "We did everything that we can na ganin mun ceto rayuwar ta and alhamdulillah munyi nasarar hakan, but inaso ku faɗamin abu ɗaya for how long ƴar ku ke fama da ciwon da ta tashi dashi and tun bayan samun sauƙin ta kun koma an sake duba lafiyar kwakwalwar ta kokuwa?."

"I guess ta kai kusan 5months a kwance babu lafiya, sannan maganar check-up wata uku likitan ya bamu mu dawo yanzu haka sati ɗaya ne ya rage mu sake komawa" cewar Umma.

Ajiyar zuciya doctor ɗin ya sauƙe kafin yace "Well kamar yadda kuka sani tun farko kwakwalwar ƴar ku ba ƙaramin buguwa yayi a accident ɗin da ta samu ba, baya ga haka tayi fama da cutar stroke in the other hand kuma memory loss, i mean tabbas abin yayi mata yawa but nayi mamakin ganin yadda rayuwar ƴar ku ke shirya faɗawa halaka a karo na biyu fiye da wanda tayi fama dashi dah amma baku wani ɗau abin serious ba kuka barta."

"Mai...mai kake nufi likita?."

Gyara zama likitan yayi yace "Tun bayan farfaɗowar ta da kuma dawowa hayyacin ta da tayi, baku ga wasu physical changes tattare da ita ba, be it wurin ɗabi'u, tafiya koh magana ba?."

Shiru Umma tayi tana kallon Jafar dake kallon likitan kafin tace "Tabbas mun gani..."

"Why then baku yi mata abinda takeso ba?, koh kun manta cewa brain nata bai gama warkewa completely ya dawo normal ba, kuka zo kuka ƙara mata stress ɗin da kwakwalwar ta ba zata iya ɗauka ba har ya kai ga jawo mata matsalar depression, wanda ba ƙaramin illa yake dashi ba haka ma kuma ba saurin warkewa ne dashi ba komin maganin da za'a baka kasha except indai ba na kusa da ita bane suka jawo ta jikin su tare da bata dukkanin kulawa dama kuma abinda zai sanƴa ta farin ciki, sannan su tabbatar tana shan magungunan ta kan lokaci haɗi da cin lafiyayyen abincin da zaiyi boosting brain nata, kunsan ƴarku bata gama fita daga haɗarin ciwon da tayi a baya ba, instead of ku jata jikin ku ku nuna mata tsantsar kulawa tare da bata dukkanin abinda zata buƙata taji daɗi, but No bakuyi hakan ba sai ma sake jefa rayuwar ta da kukayi at risk" ya ƙarashe cikin faɗa kamar zai ham6are su.

Tunda ya fara magana Umma ke ta hawayen da ta kasa controlling ɗinsu, shiru office ɗin ya ɗauka kafin kuma likitan ya sake cewa "Well i guess banida wani abu da zan iya yi muku yanzu wanda ya wuce nace muku ku maida ta wurin likitan da kuka gani farko tun kafin rayuwar ta ta gama faɗawa cikin illa ta koma gidan jiya or fiye da hakan ma."

"Yes Doctor, zuwa yaushe kake ganin yakamata ace an maida ta ɗin?."

"Today, tomorrow, Next Tomorrow, but indai ya wuce sati koh kuka ɗau wani dogon time then the risk is yours to take."

"Alright, Thank you" ya faɗa kafin ya kalli Umma yace "Umma muje."

Kamata yayi ta tashi tsaye kafin su fice a office ɗin yana rarrashin ta.

Ɗakin da aka kwantar da DEENAH suka shiga, inda suka ganta kwance unconcious an laƙa mata abin shaƙar numfashi, ga kuma drip da aka jona mata da sauran abubuwa.

Kuka Umma ta fashe dashi tana faɗin "Kaico na!, ki yafe ni DEENAH nasan duk nice dalilin faɗawar ki wannan hali, kinyi gaskiya da kika ce bamusan abinda kike ji ba, ya Allah ka yafe ni."

Patting ɗinta Jafar keyi a baya yana faɗin "It's alright Umma, ki bar faɗin haka, dukkanin wani abu dake faruwa nada dalilin faruwar sa, stop blaming yourself for all this please, kin ta6a ganin inda uwa ke ƙoƙarin kai ƴar ta halaka ne, bale kuma ke da kullum kike fatan rayuwa mai inganci wa DEENAH?, dan Allah ki bar sawa kanki damuwa and DEENAH insha Allah zata tashi in good health har tafi dah ma, just keep praying."

Kai ta jinjina tana share hawayen fuskar ta kafin yace "Zanje na fara shirye-shiryen komawar ku Egypt, DEENAH will be fine insha Allah, yakamata ace zuwa jibi dai kuna chan."

Kai kawai ta iya jinjina masa, kafin yaja mata kujera ta zauna shi kuma yana ficewa.




************************



__________B'angaren ZEEYAD yau 3days da barin sa Nigeria zuwa wata ƙasar, ayyukan sa yake gudanar wa cikin kwanciyar hankali da nutsuwa.

Yayin da kullum kuma suna cikin waya da Grandma ɗinsa 24\7, inda sauran masa 1month ya ƙarashe abubuwan da suka kaisa ya dawo.

Yau ma zaune yake cikin wani ƙayataccen madaidaicin falo mai ɗan karen kyau, ƙafar sa ɗaya kan ɗaya yana mai daddana wayar sa.

After some seconds ya kai wayar kunnen sa, murmushi ya saki bayan an ɗau kiran yace "Grandma?."

"Habiby, ya kake?."

"Am food Grandma, and you?."

"Alhamdulillah, Alhamdulillah Habiby sai kewar ka kawai, ka duba fah yau watan ka ɗaya baka nan, kada kaso kaga yadda duk na rame."

Murmushi mai ɗan sauti yayi yace "Grandma kenan, kada ki damu maybe na gama abubuwan da suka kaini zuwa next two weeks, so bana tunanin zan cike sauran wata ɗayan."

"Toh alhamdulillah, naji daɗi sosai Boy, Allah yasa dai hakan ta yiwu."

"Insha Allah Grandma" ya faɗa cikin murmushi.

"Toh ga Jalilah nan na son magana da kai, tace tunda ka tafi baku gaisa ba."

"Yeah" ya ɗan faɗa.

"Assalamu Alaikum" yaji ta faɗa.

"Wa'alaiki Assalam" ya amsa mata.

"Ina wuni Akhi?."

"Lafiya, am good, and you?."

"Lafiya ƙalau alhamdulillah, ya ayyuka?."

"Alhamdulillah" ya amsa a takaice.

"Masha Allah, Allah ya taimaka, dama gaisuwa ce."

"Aameen, Thank you" ya faɗa kafin yace "Grandma?."

Muryar Grandma yaji a wayar tana faɗin "Masha Allah Boy, Allah ya taimaka yayi maka Albarka."

"Aameen Yaa Rabb Grandma."

"Toh sai anjima koh?."

"Yeah" ya faɗa kafin

Please Login or Register in order to submit comment