Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ubangiji."

Jinjina masa kai kawai sukayi kafin ya tattari kayan aikin sa ya fice daga ɗakin.

Sadeeq ne yace "You're right, canza shi zamuyi, kai ka zauna nikuma zan fita na sallame shi daga nan na wuce gida na sanarwa da Abhi abin dake faruwa."

"Alright" kawai ya faɗa yana samun wuri ya zauna kafin Sadeeq kuma ya fice.


************************


_________Mahaifin Sadeeq ne tsaye akan ZEEYAD ɗin yana kallon sa cike da tsantsar tausayin sa, juyowa yayi ga su Sadeeq yace "Kuna tare dashi cikin wannan larurar tsawon lokacin nan amma baku ta6a gigin sanar dani ba, wannan ba ƙaramin ganganci bane, dan kuwa banga alamun ana yi masa magani ba anan wurin."

Shiru duk sukayi, nan ya numfasa yace "Wannan lamari ya wuce tunanin mu duka, da akwai wani babban malami da na sani sai dai yana zaune ne a wani ƙauye chan, ya kware wurin dealing da ire-iren wadannan abubuwa, ku shirya zuwa gobe a ɗauke sa a kai shi."

"Insha Allah" duk suka amsa.

Washe gari da sassafe YAZEED yaje ya sanarwa mai Martaba kan cewa zaiyi tafiya sannan zai iya jimawa bai dawo ba.

Ɗagowa mai Martaba yayi ya kallesa wanda kallo ɗaya zakayi kasan bayida wata isasshiyar lafiya yace "Ina kake tunanin zakaje ka YAZEED?, kai kaɗai ne ɗan da nake gani a yanzu naji zuciya ta tayi sanƴi, ba zan so kayi nisa dani ba sabida kai ne wanda zai zamto magaji na sabida kai kaɗai ne wanda zai riƙe wannan kujerar mulkin cikin imani."

Numfasawa YAZEED yayi tace "Your Highness zan iya dawowa muddin aikin da naje yi ya kammala akan lokaci, taro ne na likitoci zamuyi, da zaran mun gama kuma zan dawo insha Allah."

Ba dan mai Martaba yaso ba ya yarje masa tare da yi masa fatan alkhairi, kai tsaye part ɗinsa ya koma ya ɗau dukkanin wasu abubuwan buƙatun sa ya fito, tarar da JALILAH dake jera breakfast a dining yayi a falon.

Da sauri ta ƙaraso wurin sa tare da faɗin "Zaka fita kuma bakayi breakfast ba" kallon suitcase ɗin dake riƙe a hannun sa tayi cikin sanƴi tace "Tafiya zakayi ne?."

Kai ya jinjina mata, sosai yake son koyawa zuciyar sa sabawa da ita sannan ya kasance yana kyautata mata a kullum, sabida sam batada naƙasu cikin halayen ta, murmushi yayi kafin yace "Yeah, zan ɗanyi tafiya ne na ɗan kwana biyu, anjima za'a kawo miki ƙarin food stuffs, and na bar miki kuɗi cikin bedside drawer ɗinki in case zaki buƙata kiyi wasu uzurin ki dashi."

Gaba yayi kafin ya sake dawowa yana kallon idanun ta da ya ɗan tara hawaye nan yace "I will miss you" kafin kuma ya bata light hug yana ɗagowa tare da bata peck a goshi sannan yaja suitcase ɗinsa yayi gaba.

Da kallo ta bisa har ga Allah taji daɗin yadda yayi mata, koh bakomai taji damuwar ta ya ɗan ragu hakan ya sake bata hope akan cewar komin badaɗe zai zo ya fara nuna mata kulawa, murmushi tayi kafin kuma ta nufi dining tana jan kujera ta zauna.

****************

Wani ƙauye ne suka iso wanda tsakanin sa da MASARAUTAR su akwai nisan kilomitoti kai tsaye gidan wannan malamin nan suka tambaya, kasancewar shi ɗin ba 6oyayye bane a ƙauye yasa akayi musu iso har izuwa ƙofar gidan sa.

Tsaye suka same sa a bakin ƙofar gidan sa da wasu samari biyu, Abhi ɗin Sadeeq ne ya fito daga motar kai tsaye wurin malamin ya nufa nan suka shiga gaisawa cikin mutunci da alama dai su ɗin tsoffin abokai ne.

Umarni ya baiwa wadannan samarin da su ɗau ZEEYAD su shiga dashi daga ciki, gidan nasa babba ne sosai kai tsaye wani ɗaki aka kai ZEEYAD tare da shimfiɗe sa kan gado.

Iso malamin yayi musu izuwa cikin ɗakin da yake babba ne sosai nan suma suka sami wuri suka zauna kan shimfiɗaɗɗiyar carpet ɗin ɗakin.

Gaisawa duk suka sakeyi kafin Abhi ya sake yi masa bayanin abin dake tafe dasu.

Kai malamin ya jinjina yace "Tabbas kunyi dabarar kawo sa nan wurin sabida nan ne dai-dai da irin shaiɗanin aljanin dake jikin sa, sai dai ina tsoron zai iya ɗaukan tsawon lokaci anan kafin ya warke."

Duk kallon juna sukayi kafin Abhi yace dashi "Allah ya gafarta malam, baka fah duba shi ba tukun."

"Bai zamto lallai sai na duba shi ba, sabida kallo ɗaya nayi masa na fahimci iriyar lalurar dake tattare dashi, koma wanene yayi masa wannan aika-aikar lallai ba ƙaramin maƙiyi bane a gareshi, baƙaƙen shaiɗanun Aljani ne a jikin sa, garawa dasu ba ƙaramin aiki bane, dan haka dole ne sai kun bada tsawon lokaci har izuwa samun lafiyar sa baki ɗaya, sannan idan kun koma gida ku cigaba da yi masa addu'o'i dama kuma sadaka a kullum hakan ne kaɗai zamu iya samun nasara kan wannan Aljani."

"Insha Allah" Abhi ya amsa.

YAZEED ne yace "Kenan tafiya zamuyi mu barsa anan?."

"Kwarai kuwa?" cewar Abhi.

"Toh amma har tsawon wane lokaci zai ɗauka kafin ya warke?" cewar Sadeeq.

Malamin ne ya numfasa yace "Ya danganta da iya lokacin da Allah ya tsara masa na samun lafiyar sa, wasu kan ɗau shekaru da dama kafin su warke mafi ƙarancin lokacin da ake ɗauka kafin a warke shine shekara ɗaya zuwa biyu, da akwai wadanda ke ɗaukar tsawon shekaru goma ya danganta da irin ciwon da aljanin zai sanƴa musu kafin ya bar jikin su."

Duk cikin tashin hankali suke kallon sa, murmushi malamin yayi da alama dai ba yau ya saba dealing da harkar aljanu ba kafin yace "Ku kwantar da hankalin ku, addu'a da yawaitar sadaka itace kaɗai abinda zaku dage da yi masa a yanzu."

Abhi ne ya sami ƙarfin guiwar basa amsa da "Insha Allah."

Ɗaya daga cikin yaran sa ya kira nan yace dasu yayi wa su Abhi ɗin rakiya zuwa ɗakin da zasu kwana.

Kamar yadda ya umarce sa ɗin ɗakin da zasu kwana ya kai su, kafin kuma a kawo musu abinci da sha, bayan duk sun huta ne kuma kowannen su ya samu wuri ya kwanta bayan sun yanke shawarar tashi sallar dare dan neman wa ZEEYAD ɗin addu'ar samun lafiya.


*************************


_________Kallon JALILAH Hafeezah keyi kafin tace "YAZEED yace miki zaiyi tafiya amma baki damu da ki sanar dani mahaifiyar sa ba, maiyasa?."

Kanta a ƙasa take faɗin "Kiyi haƙuri bansan da cewa bai sanar miki bane ba shiyasa ban faɗa miki ba."

Wanke fuskar ta tayi da mari kafin ta ɗaura da faɗin "Na tabbata kinyi masa wani abin ne ya sanƴa shi fara nuna miki kulawa, koh kin manta da cewa keda kwanciyar hankali kunyi hannun riga tunda har kika auri ɗana."

Cikin kuka take faɗin "Wallahi banyi masa komai ba, tadda ni kawai yayi a falo lokacin da zai tafi shine yake sanar dani."

Mugun kallo ta watsa mata nan tace "Ba wannan ba ma tukun, tun bayan mutuwar ZEEYAD ban sanƴa matar sa a idanu na ba, naji labarin cewa dake da ita akwai jituwa tsakanin ku, hakan yasa nake son yi miki wasu tambayoyi akanta tare da baki wani aiki."

Ɗago da idanu tayi tana kallon Hafeezah da ta tsare ta da idanu "aikin da nakeson kiyimin kuma bana buƙatar a sami wata matsala koh da ƴar ƙanƙanuwa ce, sannan banason kiyimin ƙarya akan tambayar da zanyi miki, yin hakan daidai yake da barin ki fadar nan kokuma wani naƙasu tattare da rayuwar ki."

Saurin sadda kai ƙasa JALILAH tayi hawaye na biyo ƙuncin ta kafin ta tsinkayo muryar Hafeezah tana faɗin "Inason ki faɗamin dalilin rashin fitowar ta fada koh gaida mai Martaba dukda cewa ta gama takabar ta."

Shiru JALILAH tayi zuciyar ta na dukan tara-tara.

"Ke nake saurara sannan kada ki kuskura kiyi gigin yimin ƙarya."

Cikin rawar murya tace "Babu komai, bata fitowa ne kawai sabida batada lafiya."

Murmushi Hafeezah tayi kafin tace "Zan baki dama ta ƙarshe muddin kika kuskura kikayi min ƙarya sai kinyi nadamar kasancewar ki cikin MASARAUTAR nan."

Shiru tayi kafin cikin kuka tace "Gaskiya nake faɗamiki, har yanzu tunanin mutuwar sa bai bar jikin ta ba, hakan ne ya haddasa mata rashin lafiya sannan bata kuma son fita koh ina."

"Inaji a jiki na ƙarya kike yimin."

Saurin ɗagowa tayi tana girgiza mata kai tace "Ki yarda dani Allah yana gani ba ƙarya nakeyi miki ba."

"Sairah ki kama ta ki shiga ciki da ita kiyi mata duk wani irin hukuncin da kikeso har sai ta buɗi baki ta faɗi gaskiyar abinda ta sane game da wancan yarinƴar da kullum ake 6oye ta ba'a barin fitowar ta."

Yatsine fuska tayi kafin tace "Miye na baiwa kaina wahala ke daga ganin idanun ta kinsan ƙarya takeyi da akwai abinda take 6oyewa kyanta shine mu tilasta mata ta faɗi gaskiyar abinda ta sani kokuma jikin ta ya gayamata."

Rahinah ce tace "Mai kuwa kuke tunanin zai sanƴa a dinga 6oye ta, cikin ɗaya ne koh biyu it's either dagaske batada lafiyar ne kokuma ciki gareta shiyasa ake 6oye ta ba'a son fitowar ta."

Duk shiru sukayi tare da zubawa JALILAH da kanta ke sadde a ƙasa ta runtse idanun ta ido.

Fizgo hannun ta Hafeezah tayi tana aika mata da wani irin mugun kallo tace "Ciki ne da ita koh ba haka ba?."

Da sauri ta shiga girgiza mata kai ba tare da ta iya buɗar bakin ta ba.

"Answer me" ta faɗa cikin daka mata tsawa.

"Ba zatayi magana ba, we should force her ta hanƴar koya mata hankali."

Jawo hannun ta Hafeezah tayi zuwa cikin wani ɗaki tana rufe ta a ciki tace "A cikin nan zaki dawwama koh da mutuwa zakiyi ba zaki fito ba, muddin ba wai kin shirya faɗar gaskiya bane ba."

Kallon ta Sairah tayi kafin tace "Har yaushe ne zamu jira ta faɗi gaskiyar?, samu zamuyi wata daga cikin bayin dake aiki a 6angaren su nemo mana bayanin abin dake faruwa."

"Bana tunanin koh su ana barin su su ganta, sabida na ta6a tunkarar wasu daga cikin su suma sunce rabon da su sanƴa ta a ido ya kai watanni uku."

"Toh ya zamuyi kenan?" cewar Rahinah.

"Wannan banzar JALILAR zamu matsawa ta faɗa mana gaskiya nasan tana 6oye mana ne, amma muddin ya zamto dagaske DEENAH tana da ciki..."

"Ba zamu bar abin cikin nata da rai ba" cewar Hafeezah cikin ƙarar da maganar Sairah ɗin.

Buɗe ƙofar da JALILAH take ta fiddo ta kafin ta sanƴa ta zama kan kujera, kallon ta tayi tsaf tace "Cikin lallama nake sake tambayar ki JALILAH ki faɗamin abubuwan da kika sani game da DEENAH, menene dalilin da ya sanƴa bata fitowa, muddin kuma kika kuskura kika sake yimin ƙarya wannan karon toh lallai zakiyi nadama, ke nake sauraro."

Cikin kuka JALILAH tace "Ummie maganar gaskiya nake faɗamiki, ban...bansan komai ba..."

Marin da Sairah ta ɗauke ta dashi ne ya sanƴa ta dafe ƙuncin ta cikin azaba kafin tace da ita "Farko kince rashin lafiya take, yanzu kuma kince bakisan komai ba, hakan ne ya sake tabbatar min da cewa ƙarya kikeyi sannan ke munafuka ce, koh ki faɗi gaskiya kokuma jikin ki ya gayamiki."

Kuka kawai take hannayen ta dafe da ƙunci, tasan muddin ta faɗa musu gaskiya they won't stop at nothing har sai sunga bayan DEENAH da abin dake cikin ta, muddin kuma ta buɗi baki ta faɗi gaskiya then taci amanar DEENAH kenan, ita kuma ba zata ta6a barin hakan ya faru ba.

Barin wurin Sairah tayi bata daɗe ba ta dawo riƙe da ƴar ƙaramar wuƙa tazo gaban JALILAH ta tsaya tare da nuna ta da wuƙar tace "Ki faɗi gaskiya koh kuma uwarki ta haifi wata."

Hafeezah ce tace "Koh ta faɗi gaskiya kokuma ki yanke mata maƙoshi idan yaso sai ta mutu kawai."

Rahinah ce tace "Ba haka zakuyi mata ba, sai wuƙar zakuyi a idanun ta muddin ta sake yin ƙarya ki da6a mata shi cikin ido, idan taƙi faɗar gaskiya ki sake soke ɗayan idon dashi, da kanta zata faɗi gaskiya."

Da shawarar Rahinah tayi amfani dan haka cakumo gashin kan JALILAH tayi tana lankwasar mata da wuya haɗi da saita wuƙar a idanun ta tace "Kin dai san dama tun chan ba sonki nake ba koh, ke kishiya ta ce kuma ni ban ɗau kishiya matsayin abokiyar zaman lafiya ba, zan iya yin komai idan nace komai ina nufin harda kisa muddin jini na bai ɗauki mutum ba, dan haka indai har bakya buƙatar rasa idanun ki inaso ki faɗamin gaskiya menene ke wakana da DEENAH a cikin wannan gidan da kullum take a killace?."

Shiru JALILAH tayi tana cigaba da kuka "Talk kokuma ki rasa idanun ki."

Kai ta shiga girgizawa tana faɗin "Gaskiya na faɗamuku."

Haushi ne ya kama Sairah dan haka da6a mata wuƙar take shirin yi a ido Rahinah tayi saurin tsaida ta.

"Dakata tukun, cire mata ido azabar ƙanƙanin lokaci ne, ni na san mai zanyi mata ku bani minti biyar naje na dawo yanzu" tana faɗin haka ta fice daga ɗakin.

"For the last time JALILAH ki faɗi gaskiya kokuma ki shiga uku."

Shiru tayi da ka ganta kasan tana cikin gagarumin tashin hankali, Rahinah ce ta dawo ɗakin hannun ta riƙe da ƙaton kaskon wutar gaushi.

Murmushi tayi tare da kallon su tace "Da wannan zaku horar da ita da ba zatasan lokacin da zata buɗi baki tayi magana ba" ta faɗa tana dire kaskon.

Murmushi Sairah tayi tace "Tabbas kinyi dabara" tana ƙarasowa ta ɗau kaskon kafin tace ku kama min ita ku ɗaure."

Cike da mugunta suka ɗaure JALILAH jikin chair yadda ba zata iya motsi ba tare da liƙe mata baki.

Ƙarasowa gaban ta Sairah tayi haɗi da sakin murmushin mugunta kafin ta ajiye gaushin wutar a ƙasan ƙafar JALILAH yadda raɗaɗin zai dinga dukan tafin ƙafarta kafin su koma gefe su tsaya suna kallon ta.

Sosai tururin wutar ke ƙona tafin ƙafarta, babu abinda takeyi sai gumi da take haɗawa ga kuma hawaye dake tayi mata parate a kumatu, sam babu damar ihu.

Sai da suka ga ta fita hayyacin ta sosai tukun kafin Sairah ta janƴe wutar inda Rahinah kuma ta kwara mata ruwa a fuska tare da ɗaye abin bakin ta cike da mugunta.

Wani irin azababbiyar ajiyar zuciya JALILAH ta saki kanta dake lilo Sairah ta riƙo kafin tace "Faɗamin yanzu."

Shiru tayi mata tana cigaba da sauƙe ajiyar zuciya sosai dukkanin ilahirin jikin ta keyi mata zugi da raɗaɗi musamman tafin ƙafar ta.

Wanka mata mari Sairah tayi a tsawace tace "Kina mugun 6ata min rai, tell me now."

Rahinah ce ta ɗauki gaushin wutar tare da tsunbula ƙafar JALILAH a ciki kafin Sairah tayi saurin sanƴa hannu tana toshe mata baki daga ihun da takeyi ɗin "Faɗamin yanzu."

Tsabar azaba batasan sadda ta shiga jinjina kanta ba.

"Ciki ne da ita?."

Nanma jjinjina mata kai tayi kafin kuma tayi murmushi tana ɗauke hannun ta daga rufe mata baki da tayi inda Rahinah kuma ta cire mata ƙafar daga kan gaushin.

Sunce ta sukayi kafin Sairah ta tura ta tana faɗin "Amfanin ki ya ƙare."

Murmushi Hafeezah tayi tace "Am so proud of you girls" ta faɗa tana basu kyakkyawar runguma.

Kiran kuyangun ta tayi kafin tace dasu "Show her the way out."

Kallon JALILAH dake kwance a galabaice sukayi kafin su nufe ta tare da ɗaga ta suka fice da ita.

Wheel-chair suka nema suka ɗaura ta akai kafin su shiga tura ta dan maida ta part ɗinta, sosai take a matuƙar galabaice har dishi-dishi take gani.

Hango Yayan ta Sooraj dake tafe kamar zai tashi sama tayi kullum shi kam a ƙufule yake da cikin tsananin fushi ta san muddin ya ganta a haka babu abinda zai nuna mata sai ma yayi mata Allah ya shi ƙara yayi wucewar sa, saurin sadda kanta tayi har sun wuce shi kafin kuma yayi saurin dakatar dasu.

Tsayawa sukayi daga tura ta ɗin, tana jan rigar ta ya rufe mata ƙafafun ta, ƙarasowa wurin yayi yana kallon ta ganin kanta a sadde ya sanƴa shi faɗin "Mai kikeyi akan wannan keken guragun?."

Cikin rawar harshe tace dashi babu komai.

Kallo ya ƙare mata kafin ya kalli kuyangun da suma kansu sadde a ƙasa kafin ya sake maido duban sa kan JALILAH yace "Ƙarya kike yi."

Shiru tayi bata ce dashi komai ba, zagayowa yayi ya tsaya a gaban ta yana sake ƙare mata kallo, ƙafarta da yaga tana ta kiciniya dashi ta cikin rigar ta ya duba ba tare da yace da ita komai ba ya sunkuyo yana ɗaga rigar tata, a matuƙar hasale ya ɗago yana duban ta tuni kuma ya fara sakin huci yana ɗago ƙafar ta tare da ƙure tafin da ido ganin yadda ya kwakkwaile, cikin hucin 6acin rai yace "Wane ɗan kasadan ne yayi miki wannan aika-aikar?."

Shiru tayi tana fashewa da kuka, tsawa ya daka mata cike da 6acin rai yace "Shut the fuck up and tell me who did this to you."

Cikin kuka take faɗin "Sairah, Rahinah da Ummie ne..."

"Uban mai kikayi musu?" ya faɗa a tsawace.

Kai ta girgiza masa alamun babu komai.

Sosai ransa ya 6aci babu abinda yake sai huci, miƙewa tsaye yayi yace "Ku kaita gida" kafin kuma ya wuce fuu kamar wanda iska zai tashi sama dashi.

Bai tsaya koh ina ba sai faɗowa da yayi cikin falon Hafeezah ya hau kwala kiran sunan ta "Hafeezaaahhh" kamar zai tashi ginin gidan yana bangaje duk wani abu da ya shige masa gaba.

Duk fitowa sukayi sakamakon yadda ya kira sunan nata, bai tsaya koh ina ba sai gaban ta yana nuna ta da yatsa yace "How dare you?."

"Kai mahaukacin ina ne...?."

Bata ƙarasar ba ya daka mata tsawa da faɗin "Shut up, so you're this merciless?, i will make sure na koya miki hankali dake da wadannan fitsararrun ƴaƴan naki for torturing my sister" ya ƙarashe kamar zai kifo kansu.

"Wannan mahaukacin kuma daga ina?" cewar Sairah tana kallon Sooraj ɗin.

Marin da ya kifa mata a ƙunci ne ya sanƴa ta saurin dafe wurin har kanta na wani irin juyawa.

Dorina ya gani rataye jikin wall baiyi ƙasa a guiwa ba ya shiga zuga mata a jiki "I will show you that ba hauka kaɗai ne dani ba, duka psychiatry ne a kaina."

Ihu kawai Sairah keyi kamar zata shiɗe, finciko Rahinah dake shirin guduwa yayi yana wani irin kwallo da ita kafin ita ma ya hau zuga mata dorinar ba ji ba gani, babu abinda duk sukeyi sai ihu suna kiran sunan Ummie ta taimake su, sosai Sooraj yayi musu jina jina ya haɗa musu majina da jini kafin ya shiga nuna su da yatsa yana faɗin "Dan mun aurarwa ƴar mu wa ɗanku ba hakan ke nufin mun sallamar da ita wa duniya kokuma batada gata bane ba, koh kun manta wanene Sooraj da abinda zai iya yi?, daga yau duk wani wanda ya ƙara yi mata koh da banzan kallo ne i will make sure i pluck the hell out of the bitch eyes out."

Sosai Sarauniya Hafeezah ta tsorata dashi har ya gama dukan su bata iya tankawa koh ta hana ba dan kada ma ya haɗa da ita dan kuwa sai yau ta sake tabbatarwa da bashida hankali koh kaɗan.

"And you" ya faɗa yana juyowa ga Hafeeza har sai da ta tsorata yadda ya zaburo mata ɗin yace da ita "Daga yau kulawar ƙanwata ya koma Ƙarƙashin ki, zanje na maido da ita yanzu na baki kwana biyu ki dawo mata da ƙafar ta mai kyau yadda yake, idan kuma ba haka ba sai na tabbatar da na haɗa ki da wadannan abubuwan da kike kira ƴaƴa na ƙona ku duka, idan yaso sai nima a kashe ni dan ban damu da rayuwar ba yanzu, tunda ZEEYAD ya mutu na fahimci cewa duniyar nan bakomai bane, sannan har yanzu ina baƙin ciki da rashin neman yafiyar sa da banyi ba, dan haka duk wani wanda yaso shiga gona ta kokuma ya kuskura ya sake ta6a min lafiyar ƙanwa sai na tabbatar da yayi nadamar hakan, kinji koh bakiji ba?" ya faɗa a tsawace yana kallon ta da rikitattun idanun sa.

Da sauri ta shiga jinjina masa kai tana faɗin "Naji."

Kallon Rahinah da Sairah dake zube a ƙasa jina-jina yayi kafin yace "Kaɗan daga cikin abinda zan iya aikatawa kenan, ku sake ta6a min ƙanwa na gani zan dawo da ita yanzun nan ku tabbatar kun rissina har ƙasa kun bata haƙuri sannan babu wanda zai kula da ita da lafiyar ta sai ku, kunji koh bakuji ba?."

Kai suka shiga gyaɗa masa, a tsawace cikin baiwa kowannen one-one lashes yace "Bakuda baki ne?."

"Munji wallahi munji" suka faɗa cike da tashin hankali.

Wiping fuskar sa yayi yace "Good, Good" kallon abubuwan da ya bibbirkita yayi kafin yace "Ku tashi ku tsaftace nan wurin yanzun nan, ku tabbatar da cewa babu datti koh kaɗan, sabida ƙanwata ba zata dawo cikin gidan nan ta tadda datti ba sabida ba ma'abociyar ƙazanta bace irin ku."

Tun kafin ya gama rufe baki suka yunƙura dakyar cikin ɗingishi da alama dai ba mugun rauni yaji musu ba, suka shiga aiwatar da abinda ya sanƴa su, wuri ya samu ya zauna kafin ya kalli Hafeezah dake tsaye yace "Har dake."

Da sauri ita ma taje jiki na rawa ta shiga taya su.

Sawa yayi aka kawo masa lemo mai sanƴi ya naɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya yana korawa yana kallon su.

Sau uku sunayi yana ce dasu baiyi ba su sake gogewa su gyara, sosai da sosai suka jigata Rahinah da Sairah sai kuka suke ganin girman falon amma koh tausaya musu baiyi ba gashi kuma dama ba sabawa sukayi ba, sosai sukejin kamar bayan su zai 6alle ya faɗi.

Sai da yaga gidan ya fita tass kafin ya miƙe yace "Ku tabbatar kun gyara mata ɗakin da zata sauƙa idan tazo, muddin kuma naga koh da tsakuren datti ne kuyi kuka da kanku" yana faɗin haka ya fice a fusace.


**********************

_______Sosai hankalin DEENAH da na Grandma ya tashi ganin abinda su Hafeezah sukayi wa JALILAH.

DEENAH ce cikin kuka tace "Grandma they won't stop at nothing har sai sunga bayan babyn jiki na, sai dai ba zan ta6a bari hakan ya faru ba kafin su ga bayan mu ni sai na kawo ƙarshen su."

"DEENAH tayaya, just take a look akan abinda suka yiwa JALILAH think of abinda zasu yi miki ke da suke farauta, cikin ki watar sa biyar ne kawai da ƴan kai, am sure ba zasu sarara ba har sai sunga bayan shi."

Dafe cikin tayi lokacin da taji motsin sa, cikin kuka ta runtse idanun ta tana samun kujera ta zauna, kafin ta shiga girgiza kai tana faɗin "Sunga bayan mahaifin shi nikuma ba zan bari suga bayan shi ba, mai suke nema ne damu, ba dama mahaifin sa suke so ba kuma sun raba mu dashi, why kuma yanzu suke sake harin mu nida ɗana" ta faɗa cikin kuka tana rungume cikin nata.

Cike da tausayin ta Grandma ta zauna a gefen ta tana faɗin "DEENAH har abada kada ki gaji da neman addu'ar tsari daga wurin Ubangiji, ni inaji a jiki na ba zasu ta6a yin nasara akanku ba komin asiri da tsafin su Allah ba zai ta6a basu galaba akanku ba, ya kama ta ki zamto mai dauriya, jajiratacciya dama kuma jaruma koh dan saboda ɗan dake cikin ki ma, muddin kina son ɗaukar fansar ran mahaifin sa then yakamata ki rage rauni dama kuma yawan shiga wannan ƙuncin ki nuna musu cewa ke bakya tsoro sannan babu abinda zasu iya yi miki keda ɗan cikin ki."

"Grandma is right DEENAH, lokaci yayi da yakamata kema ki nuna musu cewa a shirye kike da ki kare kanki da ɗanki, ki kuma nuna musu cewa Allah yana tare daku and no harm can come to you, zamu goya miki baya akan dukkanin wani hukunci da zaki yanke" cewar JALILAH da har anyi mata dressing ɗin ƙafar tata.

Grandma ce tace "Kwarai kuwa DEENAH, idan suna taƙama su su uku ne zasu iya ja damu ai mu mun fisu yawa, kinga da ɗan cikin ki mu huɗu kenan, mu nuna musu cewa muma fah ƴan iskan kanmu ne sannan ba zamu sake kar6ar wani rashin mutunci koh nuna tsoron su a fili dama kuma zuciya ba, na tabbata ɗan cikin ki shima yana goyon bayan mu a wannan harkar dan nasan shima ba zai so ayi babu shi ba wurin ɗaukar fansar ran mahaifin sa."

Dariyar da batasan da zuwan sa ba tayi jin abinda Grandma ke faɗi, murmushi Grandma tayi ganin DEENAH ɗin tayi dariya nan tace "Ehmana ai gaskiya ne duk zamuyi maganin su ɗaya bayan ɗaya da izinin Allah."

Murmushi sukayi dukan su kafin kuma su rungume juna.






*Yawan Comment, Yawan Typing*







*MHIZZ JIDDHERR............✍🏽*
[9/6, 10:49 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The

Please Login or Register in order to submit comment