Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take yaji ransa ya 6aci,juyar da kansa yayi tare da buɗe tray ɗin breakfast ɗin dake gaban sa tare da ɗaukar fork da wuƙar da aka ajiye dan cin abincin,kafin yayi bismillah ya fara ci.



Ganin haka ya sanƴa kowacce buɗe nata abincin ta shiga ci,sa6anin ZEEYAD da bai buɗe nasa ba kuma har yanzu bai ɗago ba.



"ZEEYAD my dear,eat your food" faɗin Sarauniya Naseeba tana kallon sa.


Kallon ta Sarauniya Hafeezah tayi ta ƙasan ido kafin kuma ta kalli ZEEYAD ɗin shima a zuciyar ta tace _"What on earth is going on between them, she seems very nice to him, koma dai menene i must find it out very very soon"_ ta ƙarashe tana kallon ZEEYAD.



Kai ya jinjina tare da ɗaga murfin da aka rufe tray ɗin dashi,ƙurawa abincin dake kan tray ɗinsa idanu yayi yana jin wani abu na taso masa daga chan ƙasan zuciya.



Slice ɗin bread ne kwaya biyu sai kuma wata fale-falen soyayyiyar kwai da bata wuce yayi mata loma ɗaya koh rabi ba, kasa ɗagowa yayi ya kalle su dan kuwa yasan kowa shi yake kallo,dukda baya cin kwai haka nan ya daure ya sanƴa hannun sa tare da ɗaukar bread guda ɗaya ya haɗa da kwai ɗin tare da yin basmala ya kai bakin sa.



Kallon sa kawai Sarauniya Hafeezah keyi dan ganin reaction ɗinsa,dan kuwa itace wacce tasa akayi masa serving ɗin wulaƙancin nan.


Idanun mai Martaba ne ya faɗa kan tray ɗinsa,magana zaiyi sai dai yaji bakin sa tayi nauyi ya kasa buɗe ta,hakan ya sanƴa sa maida hankalin sa kan abincin da yake ci.


_"Mai kuma wannan yaron ke son nunawa,kamata yayi ya tada husuma anan wurin ta yadda zai fusata mai Martaba a yi masa hukunci mai tsanani,sai dai ya fuske yana cin abincin cikin kwanciyar hankali ba tare da wata damuwa ba,what is he actually up to?"_ cewar Sarauniya Hafeezah tana kallon sa har yanzun.


Bai iya cinƴe koh rabin wanda ya ɗauka ɗin ba sakamakon kwai ɗin da ya haɗa ta da ita yaji zuciyar sa na tashi,ga kuma jiri da ya fara ji duka a lokaci ɗaya.


Murmushi Sarauniya Hafeezah ta saki a cikin zuciyar ta tace _"Wow"_



Tashi yayi tsaye da kyar sakamakon kansa da yakejin tana juya masa,runtse idanun sa yayi yana sake ware ta tare da jijjiga kansa koh zai dawo saiti.



Ya san ba zai ta6a dawowa saiti yanzun ba indai har ba wai ya samu hutu da bacci bane,komawa yayi zaune kan kujerar tare da ɗaukar fork ɗin dake kan tray ɗin abincin sa yana damƙe ta a hannun sa inda yake trying so very hard ganin ya dawo nutsuwar sa,dan kuwa har dishi-dishi yake gani.



Miƙewa mai Martaba yayi bayan ya gama cin abincin sa tare da barin dining area ɗin ya haura sama.



Tashi Sarauniya Nazeerah tayi ba tare da ta tanka ba itama ta fice zuwa part ɗinta inda ya saura Sarauniya Hafeezah da kuma Naseeba.



Murmushi Sarauniya Hafeezah tayi tare da miƙewa itama ta fice ta zuwa nata part ɗin.



Kallon sa Sarauniya Naseeba tayi kafin kuma ta hau duba arear wurin dan ganin babu hankalin wanda ke kansu, tasowa tayi ta ƙaraso wurin sa tana shirin kai hannu jikin sa ne yace "Don't you dare...don't you dare touch me" ya faɗa cikin muryar dake nuna alamun yana jin jiki.


Murmushi tayi tare da ɗago fuskar sa tana kallo tace "I can see that you are so allergic to Egg, come on zo muje part ɗina nikuma zan kula da kai yadda yakamata, irin kulawar da koh a wurin Mahaifiyar ka baka same sa ba."



Hannun ta ya buge yana miƙewa tsaye ya fara tafiya cikin tangaɗi.



Fizgo sa tayi ta baya tare da riƙe sa gamm idanun ta na yin jaa tace "Babu inda zaka ZEEYAD, dan kana ganin ina nuna maka kulawa a gaban sauran mutane ba hakan na nufin na baka umarni kuma kaƙi bi bane ba, ya zama dole ne ka biya min buƙata ta idan kuwa ba haka ba sai na tabbatar da na ya6a maka baƙin fentin da har ka mutu ba zaka ta6a zama fari a idanun jama'a ba."



"You are such a Monster" ya faɗa yana fuzge hannun sa daga riƙon da tayi masa.



Murmushi mai ciwo tayi tace "Ka dube ni da kyau ZEEYAD, har yanzu ni sabuwar jini ce wannan tsohon uban naka babu abinda zai iya yimin,wanda kafin na gansa ma wataran na kan shafe watanni, a haka kake tunanin zan zauna ba tare da namiji ba a matsayi na ta lafiyayyar mace?".



Kai ya girgiza kafin kuma ya shiga tafiya inda tabi sa da kallo a zuciyar ta tana faɗin

_"You could avoid me as hard as you can, but i will make sure that i get what i have been craving for from you."_



A hanƴar sa ta fita yaci karo da sarkin Dakaru,ganin halin da ZEEYAD ɗin yake ciki ne yasa shi saurin riƙo sa tare da faɗin "Yau ɗinma kwai aka sake baka kaci?, what a cruel world."



Dakarun dake jeka ka dawo daga wurin ya sanƴa su kama ZEEYAD ɗin su kai sa ɗakin sa,ba tare da musu ba suka zo suka kama sa dan aiwatar da abinda ya umarce su.



Har ɗakin sa suka kaisa suka kwantar kan motsatsiyar katifar sa, kafin su fito suna mai ja masa ƙofar.



"She just wants to see me dead" ya faɗa chan ƙasan muryar sa yana sauƙe nannauyar numfashi.



Ya sha fama kafin ya samu wani irin wahalallen bacci ya ɗauke shi........



****************



.............A hankali ya shiga buɗe idanun sa da sukayi masa nauyi yana ware su kan 6antararriyar ceiling ɗin ɗakin nasa da idan akayi ruwa mai ƙarfi da iska zata iya faɗowa kafin kuma ya miƙe zaune yana jinsa dama-dama.



Tashi yayi ya fito waje tare da ɗaukar wata motsatsiyar bokitin ƙarfe ya nufi wurin tuƙa-tuƙar da aka ware wurin wankin bayi mata ya ɗebi ruwa inda duk ta 6u66ule ruwan na tsiyayewa.



Haka nan ya kawo ta zuwa banɗakin da yake wanka,Wankan yayi da kyau kafin ya fito ya koma ɗakin sa.



Koɗaɗɗiyar Ghana-Must go ɗinsa da duk ta yayyage kamar wanda aka kwato daga bakin kura ya janƴo kafin ya shiga bincika kayan da zai sanƴa a ciki.



wata jallabiya mai hula a baya brown colour wacce itace mai ɗan kyau a cikin kayan nasa ya ciro duk da itama wasu wuraren sun 6ule kwari sun cinƴe amma haka nan ya sanƴa abarsa.



Wata ƴar ƙaramar drawer ya buɗe ya ciro wata sarƙa,sai sheƙi take da ɗaukar ido, jujjuya ta yayi a hannun sa tare da buɗe abin dake jikin sarƙar inda hoton wata Kyakkyawar mace ta bayyana fuskar ta ɗauke da murmushi, murmushin shima yayi kafin yace "You are the only treasure i have left."



maida abin yayi ya rufe kafin kuma ya sanƴa sarƙar a wuyar sa yana cusa ta cikin rigar sa.



Baƙar sumar kansa dake ta taruwa kullum bata samun isasshen aski da gyara ya taje inda ta bazu masa har kan kafaɗa,kafin ya shafa mai da jikin sa ya fito.



Hanƴar barin fadar ya kama har ya fice bai tanka wa kowa ba dukda kuwa kallon da bayi da dakaru dayawa ke binsa dashi suna gulmar sa hakan sam bai sanƴa sa yaji haushi ya tanka musu ba, dan kuwa koh kaɗan hakan baya basa haushi face ma gani yake wata daraja ce da Allah ya bashi tunda har ana iya nuna sa idan yana tafiya koh ayi maganar sa a bayan idanun sa.



Tafiya mai nisa yayi kafin ya iso gidan su abokin sa Sadeeq, kasancewar gidan ba baƙon sa bane ya sanƴa sa shiga har ciki bakin sa ɗauke da sallama


Sadeeq ɗin ya tadda da iyayen sa da ƙannen sa zaune suna cin abinci, hakan ya sanƴa shi saurin komawa.



"Abhi...ZEEYAD ne" cewar Sadeeq ɗin da ya miƙe tsaye dan kiran ZEEYAD ɗin, sakamakon kallon da mahaifin sa ke binsa dashi ne yasa shi dakatawa.



"Daga yau nayi maka iyaka tsakanin ka da yaron nan, kai ba ɗan kowa bane dan haka ka tsaya a matsayin da Allah ya ajiye ka na ɗan talaka mai ƙoƙarin neman na kansa tun kafin a kwace wannan matsayin daga gare ni, kana sane da irin kashedin da mahaifin sa Sarki Abbas yayimin akanka da ɗansa, ba zan iya ja da Adalin sarki mai nagarta irinsa ba koh da kuwa ina da ikon yin hakan balle kuma da banida shi, kai kanka kasan Sarki Abbas baya magana sau biyu, dan haka rabuwar ka da yaron sa shine alkhairi a tsakanin mu baki ɗaya sannan kuma shine zaman lafiyar mu."



"Amma Abhi indai har sarki Abbas adali ne kamar yadda ka faɗa maiyasa yake muzgunawa ZEEYAD kamar wanda ba ɗan cikin sa ba?, koh da ƴan waje baya yi musu abinda yakeyi masa."



"Wannan ba damuwar ka bace Sadeeq, wannan tsakanin su ne, bakasan komai ba dan haka ka bar komai a yadda yake kai dai naka idanu ne, sannan koh da da wasa kada ka kuskura makamancin wannan maganar ta fito daga bakin ka a wani wurin, zaka iya zuwa ka sallame sa ya tafi idan kuma ba zaka iya ba ni zan fita da kaina na faɗa masa."



Shiru Sadeeq yayi yana kallon mahaifin nasa kafin kuma daga bisani yayi hanƴar waje dan aiwatar da abinda mahaifin nasa ya umarcesa, tsinkayo muryar sa yayi yana faɗin "Sannan kuma kada ka manta da faɗa masa cewar ya fita daga hanƴar ka, koh da a hanƴa kukayi kici6us dashi ku nuna bakusan juna ba."



Juyowa yayi ya kalli mahaifin nasa kafin kuma ya jinjina masa kai ya fice.



A bakin dakalin gidan su ya sami ZEEYAD ɗin zaune yana jiran shi.



Cikin sanƴi ya ƙaraso wurin sa, ɗagowa ZEEYAD yayi ya kallesa tare da yin murmushi yace "Ka gama?."



Kai Sadeeq ɗin ya jinjina masa zuciyar sa a cunkushe dan baisan mai zai cewa ZEEYAD ɗin ba.



"Alright, shall we?" ya faɗa yana miƙewa tsaye.



"ZEEYAD" Sadeeq ɗin ya kiraye shi.



Kallon sa ZEEYAD yayi nan yaga damuwa fal fuskar Sadeeq ɗin ba kamar yadda ya saba ganin sa kullum cikin walwala da nishaɗi ba idan suna tare.



"ZEEYAD, inason faɗamaka wani abu amma fah ka sani babu yadda na iya ne, Umarnin mahaifi na kawai zan bi, inaso daga yau...." shiru yayi yana kallon ZEEYAD ɗin da ya zuba masa idanu yana kallo dan son jin abinda zai faɗa.



"Ba zaka iya faɗa masa bane?" ya tsinkayo muryar Mahaifin nasa ta bayan sa.



Ƙarasowa yayi wurin su kafin ya kalli ZEEYAD yace "Kayi haƙuri ɗa na ZEEYAD, amma abinda zan faɗamaka a yanzu ƙila kaji babu daɗi, inason daga yau ka rabu da Sadeeq sannan kuma kada ka sake nunawa ka sanshi a wani wurin koh da kuwa haɗuwa kukayi a hanƴa, ZEEYAD ka tsaya a matsayin ka na ɗa ga shugaban wannan ƙasa, shima Sadeeq zai tsaya a matsayin sa na ɗa ga sarkin manoman wannan gari, ina tsoron faɗamaka cewa alaƙar ka da Sadeeq ɗana daga yau babu ita..."



"Alright" ya katse shi cikin rawar murya kafin kuma ya ɗaura da faɗin "Duk dan nine abinnan yake faruwa, kowa bayason alaƙa ta tsakanin sa da ɗansa, kowa gudu na yakeyi, ba sabon abu bane a wuri na, am already used to it, so why should i feel bad dan Mahaifina ya yanke alaƙa ta da Sadeeq?, koh bakomai yanada wasu abokan ai, dama ni kaɗai akeson muzgunawa kuma kullum suna samun nasarar hakan, i won't put the blame on anyone of you coz i guess i was born to suffer, ƙaddara ta ce hakan dan haka kada ku wani damu kanku, kuma zanyi duk abinda kakeso sabida ai kaima ka ɗauke ni ne tamkar ɗanka...Unlike my Father, so why should i said No to what you ask?, nima ba zan so wani abu ya sami kyakkyawar Family ɗinku ba, koh bakomai kunyi min gata a rayuwa, and now....ba zanyi musu da duk abinda kace ba, zanyi yadda duk kace dani kuma zan rabu da Sadeeq" ya ƙarashe cikin jinjina kai.



"ZEEYAD..."



"Sadeeq, in dai har ni zanji maganar mahaifin ka, maiyasa kai ba zaka ɗau abinda zai faɗamaka ba, you know what?, na daɗe ina fatan wannan ranar tazo ta, ranar da za'a raba ni da kai, ba dan komai ba sai dan kawai rayuwar ka ta inganta, dan kuwa rayuwa tare dani dai-dai take da rugujewar duk wani farin ciki naka kaima, am Glad Sadeeq, so very Glad" yana faɗin haka ya juya yayi tafiyar sa trying so very hard to control his tears.



Da kallo Sadeeq da mahaifin sa suka bi ZEEYAD dashi dukkanin su zuciyoyin su cike da tausayin sa har ya 6acewa ganin su.



Dafa kafaɗun Sadeeq yayi yace "Kayi haƙuri Sadeeq, nasan kanajin zafin rabuwa da aminin ka a zuciyar ka."



Saurin goge hawayen da suka kawo masa yayi kafin yace "No...inaga hakan shine dai-dai" kafin kuma ya ɗaura da faɗin "Abhi kace yau zamuje Gona, zamu iya tafiya yanzu?."



Kai mahaifin nasa ya jinjina masa kafin kuma ya dafa kafaɗun sa,suka koma cikin gidan...............





_Yauwa nace ƴan ZEEYAD fans group kodai kurame na tara ne ni bansaniba🤔, kun iya karanta littafi mai read more biyu zuwa uku amma sharhi ya gagare ku?, toh gaskiya bana kar6an ƴan la6e a cikin group ɗina, almost 300+ participants amma bai wuce mutane biyar bane masu comment, lallai daɗi ne yayi muku yawa toh tsaf yau ɗinnan zanyi aiki a kanku insha Allah😑da ba zan kar6i hakan ba yauwa_




*Share Fisabillah*






*MHIZZ JIDDHERR...........✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```(The Abandoned Prince)```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*
*(MHIZZ JIDDHERR)*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





_Bismillahi_Rahmanin_Rahim_




*003...*




......"ZEEYAD, mai ka aikata ne haka, maiyasa suke bin ka, mai kayi musu?" cewar Sadeeq da har yanzu basu bar gudun ba cikin huci.



Tuntu6e yaci ya faɗi a ƙasa, Juyowa ZEEYAD yayi nan yaga ƙafar Sadeeq ɗin na fitar da jini, alamun ciwon da yaji ba kaɗan bane.




Kallon tawagar su Mulah da suka kusan isko su yayi kafin kuma yaje da sauri ya kamo Sadeeq ɗin tsaye suka cigaba da gudu.



"ZEEYAD, just go ba zamuyi sauri ba, zasu iya taddo mu" faɗin Sadeeq dake ɗingisa ƙafar sa.



"You just shut up now, idan ba so kake suyi maka dukan mutuwa ba" faɗin ZEEYAD ɗin.



Wani ƙaton ƙarfe suka wullo nan ya same shi a kai, take kuma duk suka zube a wurin,nan kuwa akayi nasarar cafke su.



"Kai ɗan iska ƙasƙantacce, har kai ka isa ka aikata wannan mummunar laifin kuma kace zaka gudu?, ba dai a cikin wannan masarautar ba" cewar wani dogari yana ɗago sa tsaye.



ZEEYAD kansa ne ke mugun juya masa dan kuwa bibbiyu ma yake ganin su sakamakon abinda suka buga masa a kai, nan aka tusa su gaba daga shi har Sadeeq ɗin zuwa fadar sarki..........



************



............Durƙushe suke a gaban mai Martaba da kallo ɗaya zakayi masa ka gano 6acin rai ɗauke akan fuskar sa.



Duban sa ya maida kan ZEEYAD da har yanzu baijin kansa dai-dai kafin kuma ya Kalli Sadeeq yace "Ku saki abokin nasa, shi kuma da ya aikata laifin ku tabbatar da kun yi masa hukunci mai tsanani ta hanƴar horar dashi."



Kallon sarkin Dakaru yayi yace "Wannan aikin naka ne Najeeb, ka tabbatar ya fuskanci hukunci dai dai da abinda ya aikata."



Kai wanda aka kira da Najeeb ya sunkuyar alamun amsa maganar sarkin, kafin kuma ya bada Umarnin fitar da ZEEYAD ɗin.



Bayan Fadar ta watse ne ya saura daga mai Martaba sai kuma Uwargidar sa *Sarauniya Nazeerah*.



Cike da tsantsar makircin da tayi course akai ta kalle shi tare da faɗin "Allah yaja ran Sarki, amma nace kana ganin wannan hukunci da kakeyi wa ZEEYAD baya yin tsanani kuwa, ka tuna fah ɗanka ne kuma...."



"Ya ishe ki haka Nazeerah" ya faɗa cikin ɗaga mata hannu kafin kuma yace "Ina buƙatar ke6ancewa ni kaɗai."



Sum-sum ta tashi daga kishingiɗen da take ta fice, nan dakarun ta suka take mata baya zuwa Side ɗinta.



Ajiyar zuciya sarki ya sauƙe kafin kuma ya tashi daga kan Throne ɗinsa ya fara yin safa da marwa a cikin fadar.



Sosai da sosai har chan cikin ƙololuwar zuciyar sa yake Ƙaunar ZEEYAD wanda ya samo asali ne daga ƙaunar da yakeyi wa Mahaifiyar sa.



Lokacin da Mahaifiyar ZEEYAD keda rai babu abinda yafi so da Ƙauna bayan su,sai dai yanzu ganin ZEEYAD ɗin da yake ba ƙaramin baƙan ta masa rai da sanƴa shi fushin da baiyi niyya ba yake.



Tsanar da yakeyi wa ZEEYAD ɗin koh maƙiyin sa baya yi masa shi wanda har cikin zuciyar sa ba haka bane ba,sai dai kawai ba zai iya controlling anger ɗinsa bane aduk sadda ya ɗaura idanu akansa.



Yayin da ya kasance baya kusa dashi kuma babu abinda yake muraɗi da kwaɗayin gani kamar sa.



Ajiyar zuciya ya sauƙe inda kuma wasu irin zafafan hawaye suka zubo masa akan ƙunci,kai ya jinjina kafin kuma ya bar cikin fadar zuwa ɗakin sa.......




**********



.........."Stop being nice to me General, kayi abinda aka umarce ka a kaina, coz that won't change things."



Kallon sa sarkin Dakaru yayi kafin ya furzar da iska yace "ZEEYAD, kaci abincin nan tukun, koh da zan hukunta ka ɗin ya zamto da ƙarfin ka."



Kallon tray ɗin abincin da akayi serving ɗinsa yayi kamar wani ɗan gidan yari, kafin kuma ya ture yace "Am not eating it, just let me be" ya faɗa cikin rawar murya.



Zama sarkin dakaru yayi a gaban shi yace "Look ZEEYAD, being always bored won't make things right, ka rigada ka saba da wannan rayuwar tun kana ɗan shekara goma, dan haka it's now high time da yakamata kayi accepting ƙaddarar ka, babu wani abu da zakayi dan canza ra'ayin mahaifin ka akanka, ba cewa nake ka cire rai da samun sauƙin rayuwa ba, amma yakamata ka kasance cikin farin ciki kullum koh da kuwa kana cikin bad mood ne, ganin ka kullum cikin ƙunci shike baiwa maƙiyan ka damar cigaba da munana maka dan kuwa shi maƙiyi babu abinda yafi tsana kamar ganin farin cikin wanda ya tsana ɗin, shawara ce ZEEYAD kada ka ta6a bari maƙiyan ka su gano weak point naka dan kuwa dashi ne zasu cigaba da muzanta maka kullum, try and change your way of life ZEEYAD and stop being bored always" ya faɗa yana buga kafaɗun sa kafin kuma ya tashi ya fice ba tare da ya jira cewar sa ba.



Da kallo ZEEYAD ɗin ya bishi kafin ya maida duban sa kan abincin dake gaban sa, tabbas yana jin ƴunwa sai dai ba zai ci abincin nan ba, dan kuwa ba yarda yayi da sarkin dakarun ba shima.



Bayan kamar mintina sha-biyar Sarkin Dakaru ya dawo ɗakin, murmushi yayi ganin koh ta6a abincin baiyi ba, lallai ba ƙaramin jinjinawa taurin rai irin na ZEEYAD yake ba.



"So, lokacin hukunta ka yayi ZEEYAD."



Ba tare da yace komai ba ya miƙe ,chain aka ɗaura masa a hannaye kafin a tusa ƙeyar sa zuwa waje.



Fili ne ƙato aka kawo shi, kafin kuma a kaisa kan wani abu kamar mumbari aka ɗaure masa hannaye a sama.



Mutane da dama sun halarci wannan wuri dan ganin wane irin hukunci za'a yiwa Yarima ZEEYAD da yayi faɗa da babban dakare kamar Mulah,a gaban mahaifin sa sarki.



Wata Ƙatuwar dorina mai baki uku aka ɗauko,wacce take da tsayi da kauri.



Kafin kuma aje ta bayan sa a shiga shauɗa masa ita bisa ga umarnin mahaifin sa.



Lafiyayyun bulala ɗaɗɗaya har zuwa Hamsin akayi masa, amma koh gezau baiyi ba balle idanun sa su tara hawaye, zuciyar sa ce kaɗai ke mugun yi masa tafarfasa, dan kuwa yayi alƙawarin ba zai sake yin kuka ba a duk hukuncin da za'a yi masa,dan idan da sabo ya saba.



Sunce sa akayi nan ya faɗi a wurin hannayen sa dafe da ƙasa, da idanun sa da sukayi mugun jaa ya ɗago ya kalli mahaifin nasa da shima shi yake kallo.



Saurin kauda kai yayi daga kallon da ZEEYAD ɗin keyi masa kafin kuma ya tashi dogaran sa suna mai gyara masa hanƴa tare da yi masa kirare-kirare ya bar wurin............




*TWO DAYS AFTER*




Zaune yake yana gasa bayan nasa da yaji shatin bulalar da akayi masa, kasancewar bashida wani mai taimaka masa.



Bayan ya gama ne yayi wanka sannan ya shirya cikin ƴar tsofaffiyar kayan sa, kafin ya kama hanƴar zuwa cikin gida, kasancewar ɗakin sa ma a chan bayan gidan yake wurin arean Bayi Mata.



A hanƴar sa ta zuwa ne ya haɗu da wata Dattijuwar mata, da kallo ta bisa har ya ɗan wuce kafin tace "Hmm,Yaro kana ganin Rayuwa kai da Masarautar Ubanka."



Tsayawa yayi ba tare da ya juyo ba, ita ɗinma tsayuwa tayi ganin koh zai kula ta, juyowa yayi tare da sake mata murmushin da ya sanƴa ta daskare wa a wurin tana kallon sa har ya 6acewa ganin ta.



Cike da mugun sauri ta nufi 6angaren *Sarauniya Hafeezah* dan shaida mata abinda idanuwan ta suka gani.



Zubewa tayi a gaban ta tana kwasar gaisuwa.


Wani irin Kallo ta watsa mata cike da ƙasƙanci kafin tace "Lafiyar ki kika faɗomin ɗaki haka kamar wacce aka jefo, bayan kinsan yanzu lokacin hutu na ne?" cewar Sarauniya Hafeezah.



Cikin 6arin jiki da mugun gulmar dake cinta tace "Allah ya taimake ki Sarauniya ta,mata mafi soyuwa ga sarki *Abbas Ibn Qazeem*, nazo miki ne da wani babban labari yake Sarauniya ta.



Murmushi tayi tace "Shiyasa nake Ƙaunar ki Jakadiya Nadiya, domin kuwa a kullum kina kawomin labarin dake sanƴa ni cikin nishaɗi na tsawon kwanaki, ina jinki wane labari kuma kika zo min dashi yau?" ta ƙarashe tana 6antarar Apple ɗin dake hannun ta.



"Ai Sarauniya ta yau nazo miki da abun ban mamaki, yau idanu na sun ganemin abinda zai hana ni sukuni ya kuma hanaki kema, a yau dai da wadannan idanuwan nawa naga yaron nan Yarima ZEEYAD yana murmushi."



A matuƙar razane ta ɗago tana kallon Jakadiya kafin ta ɗau hannu ta wanke ta da wani irin azababben mari tace "Tashi ki bani wuri matsiyaciyar banza da wofi wacce bata gaji arziki ba, ni zaki zo wa da wannan mummunar labarin da koh a mafarki wani yazo min dashi toh tabbas sai naga bayan sa?, Useless old hag, wannan mummunar labari ce, how dare you ruined my happy mood?."



"Allah ya huci zuciyar ki, sarauniya ta, ba dan na ɓata miki rai na Kawo miki labarin nan ba, ina ganin Kamar zaki ɗau mataki akai ne tunda babu abinda kika fi tsana kamar farin cikin shi, Allah ya huci zuciyar ki yake Sarauniya ta" tana faɗin haka taja jikin ta ta baro wurin riƙe da ƙunci.




Nazarin maganar Jakadiya ta shiga yi kafin Kuma taja dogon tsaki tare da dakawa bayin nata tsawa take suka watse daga wurin.



Tashi tsaye tayi tana fidda wani irin huci mai zafi dake tasowa daga chan ƙasar zuciyar ta dake yi mata ƙuna tace "Baikamata ka kasance cikin farin ciki ba ZEEYAD, yakamata ka ƙare rayuwar ka ne cikin ƙunci,wahala dama kuma baƙin ciki, kamar yadda naga bayan Mahaifiyar ka kaima haka nakeson ganin bayan ka, sai dai taurin rai irin naka yasa har yanzu na kasa aiwatar da ƙudiri na akanka, kasancewa cikin farin ciki sam ba naka bane ZEEYAD ya zama dole nayi gaggawar yiwa wannan lamari tufkar hanci, tun kafin sirrin da nake 6oyewa shekaru da shekaru ya tone" ta faɗa tana tattare doguwar gown ɗin dake jikin ta tayi hanƴar ficewa da sauri..........



*************




............Tundaga inda take ta hango ZEEYAD ɗin tsaye a bakin ƙofar shiga fada, wanda da alama dakaru ne suka hana sa shiga, hakan ba ƙaramin faranta mata rai yayi ba dan kuwa burin ta shine a kullum ya kasance cikin ƙunci da wahala.



Ƙarasowa wurin tayi nan kuwa dakarun nan suka shiga kwasar gaisuwa kafin su buɗa mata, kallon ZEEYAD da koh da wanzuwar ta baisan dashi bane tayi kafin ta gyara tsayuwar ta tana juyowa gareshi tare da harɗe hannaye a ƙirji tace "ZEEYAD my Boy, shin ba zaka durƙusa a gaba na ka roƙe ni na sanƴa wadannan ƙasƙantattun bayin barin ka ka shiga izuwa wurin mahaifin ka ba?, au koh dayake ashe ma fah Mahaifin naka ya tsani ganin ka toh akan mai kuma kake son nuna masa fuskar ka?."



Hannu tasa ta ɗago ha6ar sa tace "Wannan kyakkyawar fuskar taka kamata yayi ace duk sadda akayi arba da ita mutum ya kasance cikin farin ciki ba baƙin ciki ba, amma abin mamaki kowa ya tsane ka a wannan nahiyar koh maiyasa hakan oho" ta faɗa tana ƙiƙƙifta idanu

Please Login or Register in order to submit comment