Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sanƴa ka 6oye irin ƙauna da kulawar da kake yi masa, dan kuwa yanzu sai ta fassara mutum tace ana ƙoƙarin kashe mata ɗa ne koh wani abin, hakan yasa Grandma take ɗan rage wasu abubuwan daga cikin ƙaunar da takeyi masa.

Grandma ce tace "Zanso kuwa naga wannan yarinƴar, dan tunda har ka iya faɗawa tsananin tarkon sonta haka i know ta tara dukkanin qualities ɗin da ake buƙata wurin mace ta gari, ya sunan ta dama kuma ƙasar da take, dan kuwa kasan babu abinda nake da buri a kullum da ya wuce naga ranar auren ku da kai da Boy" ta ƙarashe fuskar ta ɗauke da murmushi tana kallon YAZEED.

Ɗagowa YAZEED yayi yana murmushi yace "Her name is DEENAH and ita ɗin ƴar Nigeria ce."

"Masha Allah, nasha jin labarin matan Nigeria, tabbas ba za'a nuna musu komai wurin iya zaman aure da kulawa da miji ba, uwa uba akwai girmama baƙi da nuna musu tsantsar ƙauna, zanso naga wannan jikar tawa yadda naga kake ta rawar ƙafa akanta ɗinnan."

Murmushi YAZEED yayi cike da farim ciki kafin yace "Don't you worry Grandma, soon zan kawo ta ki ganta."

Murmushi Grandma tayi tace "Masha Allah, Allah ya kaimu lokacin."

Da "Aameen" ya amsa yana murmushi.

"Grandma?" cewar ZEEYAD dake tsaye kan stairs yana kallon ta cikin shagwa6e fuska.

"Au har ka tashi daga baccin?, toh ƙaraso mana" cewar Grandma tana kallon sa.

Sauƙowa ZEEYAD yayi yana zuwa ya rungume ta yace "Grandma, na fara missing naki."

"Ai duk kewar da zakayi ba zai kai wanda zanyi maka ba Habibi."

Ƙara rungume ta yayi yace "Grandma, why not ba zamuje tare dake ba?."

"A'a nikam ka ganni nan banga dalilin da zai sanƴa ni barin ƙasa ta ta haihuwa zuwa wata ba, ka ma bar yimin maganar tafiya tare dani, banga dalili ba."

"Where are you going?" cewar YAZEED.
Ɗagowa ZEEYAD yayi ya kallesa yace "Am going to found the love of my life."

Ɗan zaro idanu YAZEED yayi yana tasowa yazo kusa da ZEEYAD ɗin yace "Really?, tell me more about her."

"What about her?."
"I mean, everything about her, i want to know the lucky girl."

Murmushi ZEEYAD yayi kafin yace "Well you need to work alot before samun ganin ta."

"What, this is serious."

"Yeah it is" ya faɗa cikin murmushi.

Grandma ce tace "Nima fah na kasa kunne naji koh wacece wannan" ta faɗa tana kallon ZEEYAD.

Kallon ta ZEEYAD yayi tare da ɗan yin murmushi kafin yace "Duk kunason ganin ta then work hard."

"Work hard?" duk suka faɗa wurin haɗa baki.

"Yep" ya faɗa.

"Who is she da har sai munyi working hard zamu iya ganin ta?."

Murmushi yayi yana kallon su yace "What do you think she is other than Money?."

Duka Grandma ta kai masa yana kaucewa, inda YAZEED kuma yayi dariya tare da faɗin "But seriously am so eager to know the lucky girl."

"Wa kake tunanin will be the lucky girl other than Jalilah?" cewar Grandma.
Murmushi YAZEED yayi yace "Really?, the girl is cool yeah."

Duk kallon su yayi kafin yace "Grandma, stop it who told you cewa inason Jalilah?."

"Kenan dagaske ne kanason nata kenan, tunda babu wanda ya faɗamin ni na fahimci hakan da kaina."

Kallon ta ya tsaya yi kafin kuma ya 6ata fuska yana kauda kai.

"I know it ai, kaga yayi shiru koh, he loves her" cewar Grandma.

"No Grandma i don't."

"Toh ai sai kuma kayi koma dai menene ai gaskiya zatayi halin ta, mudai namu ido, koh ya kace YAZEED?."

"Ofcourse Granny, but do you really think dagaske yana son nata, i mean banga hakan tattare dashi ba."

"Kai ka kyale ja'iri mana, he is just trying to hide his feelings, bai san na gano komai ba."

Jinsu kawai ZEEYAD keyi bai tanka musu, dan kuwa shi baiga dalilin da zai sanƴa shi son Jalilah ba.

"Ya bani labarin komai daga cikin rayuwar sa amma ya 6oyemin labarin soyayyar sa sabida bayason na sani" cewar Grandma.

"Maybe then, the girl broked his heart" cewar YAZEED.

"Kai no way, i pretty know babu yarinƴar da zata yaudari Boy, wannan santalelen Saurayi ai duk wacce ta barshi ya ku6uce mata ta tafka babbar asara" cewar Grandma cikin koɗa jikan nata.

"Exactly Grandma, then maybe da akwai abinda shi ya barwa kansa sani."

"Koma dai menene ai in tayi tsami zamuji."

Tashi ZEEYAD yayi ya bar musu cikin falon, inda duk suka bisa da kallon mamaki, ganin yadda mood ɗinsa ya canza fiye da kullum.

Part ɗinsa ya koma yana zuwa ya zauna bakin bed tare da kafe wuri ɗaya da ido yana mai damƙe hannun sa ɗaya, sosai yanayin fuskar sa ya canza zuwa 6acin rai dan kuwa ba zai ta6a manta yadda Umma taci masa mutunci akan dan yaso ƴarta ba, bai so DEENAH bane sabida wani abu nata, haka kuma bai ƙi ta sabida wani naƙasu da ta samu lokacin da take kwance babu lafiya ba, hasalima ya sha haɗuwa da mata iri-iri a rayuwar sa sai dai haɗuwar sa da DEENAH na ɗaya daga cikin tarihin rayuwar sa ne hakan yasa ba zai ta6a manta ta ba, but aduk sadda yayi nisa da cire ta daga cikin kwakwalwar sa sai Grandma koh YAZEED sun ɗauko masa maganar da zai sanƴa shi tunawa da ita, ba ƙaramin fama yasha ba wurin cire soyayyar DEENAH a ransa shi kaɗai yasan halin da ya shiga, koh shi a yanzu yanajin daɗin rayuwar sa without her but baisan maiyasa aduk sadda aka tuno masa da ita yakan ji ƙunci da 6acin rai tattare dashi ba, yasan tayi masa nisa yanzu haka shima yayi mata nisa tunda har ya yanke dukkanin wata alaƙar sa da family ɗinta sabida gudun sake tunato ta, he wants to live a new life ba tare da DEENAH ba, but da wata daban?...

Dakatawa yayi da tunanin da yakeyi, tabbas he wants to live a new life tunda gashi nan cikin new world ɗin da babu DEENAH or any of her family, but koh da yace zaiyi sabuwar rayuwa ya mance da ta baya, baya tunanin zaiji soyayyar wata mace daban kamar DEENAH.

Tashi tsaye yayi tare da zuba hannaye cikin aljihu ya hau yin safa da marwa cikin ɗakin nasa, yana mai tunanin yadda yakamata ya tafiyar da rayuwar sa.

Knocking ɗin da yaji a bakin ƙofar sa ne ya sashi dakatawa da tunanin da yakeyi, kafin ya taka zuwa bakin ƙofar yana buɗewa tare da leƙa kansa.

Wata kuyanga ya gani tsaye kanta a ƙasa kafin cikin girmamawa ta fara faɗin "Afuwan babban Yarima, nasan ka haramta mana zuwa koh da kusa da bakin ƙofar ɗakin ka ne."

Kallon tsaf ya ƙare mata kamar ba zaiyi magana ba, kafin kuma yace "Uhum?."

"Dama Jalilah ce tace nayi mata iso zuwa gunka, nace mata hakan ba zaiyiwu ba..."

Lumshe idanu ZEEYAD yayi ya sake buɗewa cike da ƙosawa yace "Let her in" yana faɗin haka ya koma ciki ba tare da ya jirayi cewar ta ba.

"What does she want again, i thought she fractured her leg" ya faɗi hakan yana mai zama bakin bed ɗinsa.

Bayan kamar mintina biyar ya sake jiyo ƙarar knocking, lumshe idanu yayi cike da ƙosawa kafin kuma ya tashi yaje ya buɗe.

Idanu ya ɗan waro ganin ta tsaye tana yi masa murmushi.

Kallo ya bita dashi tundaga ƙasa, tana sanƴe ne cikin light-blue ɗin gown, fuskar ta ɗauke da light make-up ɗin da yayi matuƙar amsar cute face nata, inda kuma dogon gashin kanta da babu koh da ɗankwali kamar kullum yasha style da gyara mai kyau wanda ya sake taimaka wa wurin fito da tsantsar kyawun ta.

Da kyar ya iya ɗauke idanu akanta yana wani irin murtuƙe fuska ganin yana neman bada kansa a gaban ta.

Barin bakin ƙofar yayi yana komawa cikin ɗakin ya zauna kan couch.

Da ɗingishin ta ta idda shigowa cikin ɗakin tana maida ƙofar ta rufe.

Ɗagowa yayi yana kallon ta ba tare da yace mata komai ba.
Ganin kallon da yakeyi mata ne yasa ta faɗin "I...am sorry i know baka tsanmaci zuwa na ba, but ƙafar tawa ta ɗanji sauƙi ina iya taka ta, shine nace bari nazo na sake yi maka godiya, Nagode sosai Akhi."

Kallon tsaf ya ƙare mata kafin kuma ya miƙe tsaye yace "Thank you for what?" ya faɗa yana kallon ta.

Sunkuyar da kai tayi ganin yadda yake kallon ta, tana wasa da yatsun hannun ta tace "Dah ba dan kai ba then Allah ne kaɗai yasan abinda Sooraj zaiyi min yau, sabida nasan babu abinda zai hana shi aikata abinda ya faɗa koh fiye da hakan ma."

Tausayi ta basa nan yace "You don't have to worry Okay?, i promise Sooraj ba zai sake yi miki wani mummunan abu ba kuma, uhm?."

Kai ta jinjina cikin murmushi kanta a ƙasa.

"I should be going now" ta faɗa.

Kallon ta yayi kafin kuma ya jinjina mata kai.

"Naji Grandma tace zakayi tafiya gobe, would you mind idan na haɗa maka chips-cracker, i know you will love it, zaka iya ajiyewa kana ci kullum ba zai 6aci ba."

Ɗan waro idanu yayi yace "Really?."

Kai ta jinjina masa nan yace "Ofcourse i will love it."

Ɗagowa tana yi masa murmushi kafin tace "Alright, zan haɗo maka shi zuwa anjima koh gobe."

Kai ya jinjina mata kawai kafin tace "Ni zan wuce."

"Bye" kawai yace kafin kuma ta fice daga cikin ɗakin yana binta da kallo.

Idanu ya lumshe yana komawa ya zauna kan couch ɗin yana cize baki.

Ɗan ƙaramin tsaki yaja dan kuwa yaga ta fara shigewa gonar sa dayawa, dole ne ya taka mata burki tun kafin ta zaci shima sonta yake yasa yake barin take ra6ar sa, alhalin shi kawai tausayin ta yakeji haka kurum.



************************



___________Da dare bayan ya gama hirar sa da Grandma ya koma part nasa, idda shirya kayayyakin sa yayi kafin kuma yabi lafiyar gado.


************************

__________Washe gari ƙarfe takwas na safe ya gama shirin sa, dan haka part ɗin Grandma kawai ya wuce dan yi mata sallama.

Sosai Grandma tasha kuka ganin fah dagaske tafiyar zaiyi ya sanƴa ta cewa ta canza ra'ayin ta kan cewar babu inda zaije shi.

Sai da ya rarrashe ta sosai tukun kafin ta kwantar da hankalin ta.

Da kanta ta raka sa part ɗin mai Martaba dan yi masa sallama, a cikin fada ya same shi zaune akan Throne nasa kamar kullum da manƴan mutane suma Zazzaune.

Hango Grandma da ZEEYAD ne yasa shi miƙewa tsaye daga kan Throne ɗinsa yana tako ƴar matattakalar da akayiwa wurin ya sauƙo.

Gaisuwar mutunci sukayi da Grandma kafin ya maida duban sa kan ZEEYAD dake kallon sa yana yi masa murmushi.

Ɗan murmusawa shima ZEEYAD yayi yana kuma harɗe fuska lokaci guda.

"Boy yazo yayi maka sallamar tafiyar tasa ta yau ne."

Da mamaki mai Martaba ke kallon su kafin yace "Tafiya?."

"Kwarai kuwa, bai sanar da kai bane?" cewar Grandma.

Kallon sa sarki yayi kafin yace "Tabbas ya sanar dani."

Ɗagowa ZEEYAD yayi yana kallon sa, kafin Grandma tace "Ai yau ce tafiyar tasa, watanni biyu kawai zaiyi ya dawo, nasan kaima ba ƙaramin tashin hankali ka shiga da ya sanar da kai hakan ba, amma ya muka iya tunda harkar kasuwancin sa ce zata kaishi."

Sosai yanayin fuskar mai Martaba ya canza da jin abinda Grandma ke faɗi cewar ZEEYAD zaiyi tafiya har ma yayi watanni biyu, alhalin bai sanar dashi hakan ba, murmushi mai Martaba ya ƙaƙalo yace "Hakane" kallon ZEEYAD yayi yace "Allah ya kaika lafiya ya dawo da kai lafiya, inaso ka manta da dukkanin abinda ya faru a baya ka ɗauka nan ɗin gidan ka ne sannan bakada inda ya fishi, ka dawo lafiya ɗana" cewar mai Martaba yana ɗaura hannaye kan kafaɗun ZEEYAD ɗin.

Karo na farko kenan da yaji mahaifin nasa ya bashi tausayi dan haka murmushi kawai yayi tare da jinjina kai kafin kuma ya rungume shi.

Sosai mai Martaba ya cika da farin ciki dan kuwa bai tsanmaci zuwan wannan runguma ba, bubbuga bayan ZEEYAD yayi yana murmushi kafin yace "Allah yayi maka albarka."

Ɗagowa ZEEYAD yayi yace "I promise you zan dawo."

Duk murmushi sukayi kafin kuma ya kama hannun Grandma yace "Grandma, jirgi na ƙarfe goma zai ɗaga, i should be going."

Kai ta jinjina masa tana rungume kafin ta ɗago tana bashi kiss a forehead tace "Muje."

Kallon mahaifin nasa ya sake yi, ɗan murmusa masa yayi kafin kuma ya kama hannun Grandma su fice daga fadar.

Da kallo mai Martaba ya bisu har suka fice, kafin ya sanƴa hannu ya goge ƴar siririyar hawayen da ta zubo masa, yana juyawa ya koma kan Throne ɗinsa.


************************

__________YAZEED, Sadeeq, Grandma dama kuma ZEEYAD ɗinne tsaye a gaban wasu danƙara-danƙaran motoci na azo a gani da alama duk rakiya zasuyi masa.

"What are we waiting for, ba cewa kayi 10 jirgin ka zai tashi ba?" cewar Sadeeq.

Kallon agogon hannun sa ZEEYAD yayi yace "She must be on her way."

"Who?" duk suka haɗa baki wurin faɗa.

Hango ta da yayi tana zuwa ne yasa shi faɗin "There she is."
Duk maida duban su sukayi gun Jalilah dake zuwa tana ɗan sauri hannun ta riƙe da silver lunch box tana ƙarasowa wurin.

"Ku gafarce ni, nayi latti."

"Oh come on, muje kada mu sashi ya rasa jirgin" cewar Grandma.

Duk buɗe ƙofar akayi musu suka shige, ZEEYAD da bai shiga bane ya juyo yana kallon Jalilah dake tsaye tana kallon sa yace "Aren't you going?."

Kai ta girgiza masa kafin kuma ta miƙa masa box ɗin tace "Here, abinda nayi maka alƙawari ne, i just hope zakaji daɗin shi."

Kallon ta yake kafin kuma ya sanƴa hannu ya amsa yace "I appreciate it."

Ɗan murmusawa kawai tayi tana controlling hawayen dake son kawo mata.

"Are you going to cry?" ya faɗa yana kallon ta.

Saurin girgiza masa kai tayi tana sunkuyar da kai ƙasa.

"Mai zai hana a ƙarasa tattauna dukkanin abinda ake son faɗa a waya?" cewar Grandma cikin ɗagun murya.

Duk dariya su Sadeeq sukayi.

Kallon ta Jalilah ZEEYAD yayi yace "Bye."

Ɗagowa tayi tana kallon sa da Idanun ta da suka cika taf da kwalla, shigewa motar yayi inda aka maida murfin aka rufe.

Sai da motar taga ficewar motar daga arear wurin kafin ta juya cikin sanƴin jiki ta koma.


**********************


_________"What do you mean na ƙara trying?, that boy almost got me killed a wannan ranar, i wonder maiyasa na kasa samun nasarar ganin bayan sa har yanzu, abinda yafi bani mamaki yake kuma ɗaure min bai wuce yadda akayi ya fahimci nice wannan magen ba."

Dariya bokan nata ya sanƴa kafin ya tsagaita yace "I warned you didn't i?, muddin kika takurawa kanki na cewar sai kinga bayan Yarima ZEEYAD toh tabbas zaki iya aikata babban kuskuren da zai kai ki ga kashe Yarima YAZEED maimakon shi, amma kece kika tilasta nikuma banida wata hanƴar da ta wuce wannan da na faɗa miki, muddin kika samu kika cize sa toh tabbas gubar dake jikin haƙorin kuliyar zata yaɗu zuwa chan cikin zuciyar sa ne, a haka zaiyi ta fama har lokacin sa yayi, amma kin kasa hakan, kaɗan daga cikin alamun ba zaki ta6a yin nasara akansa ba kenan."

Sosai zuciyar Sarauniya Hafeezah ya cika da mugun 6acin rai nan tace "Tabbas sai nayi nasara akansa tamkar yadda nayi akan Uwar sa, ni Hafeezah banta6a cin burin aiwatar da abu kuma abin yazo ya gagare ni ba, tabbas sai na baka kunƴa wurin aiwatar da ƙudiri na tare da cimma buri na akan ZEEYAD, wannan alƙawari ne na ɗauka" ta faɗi hakan in a serious tone tana zaro idanu cike da muguwar ƙiyayya.

Dariya boka ya fashe dashi yace "Kada kice ban gargaɗe ki ba yake Sarauniya ta."

Mugun kallo ta wurga masa kafin tace "Ka iya bakin ka, kai kanka kasan gaban wacce kake, bana ɗaukar rainin hankali da zancen banza."

Shiru bokan yayi yana mai zazzare idanun shi.

"Ka jira ka gani, zaka ga yadda akeyin ta."


***********************


_______"Ya bar ƙasar yau?, how on earth then zan samu damar cika burina akansa, who knows yaushe zai dawo koma ba zai sake dawowa ba."

Murmushi gayen yayi yace "Aunt miye na wani damuwa dan ZEEYAD ya bar ƙasar?, i mean ba gani ba, miye ba zan iya yi miki ba wanda shi zaiyi miki?."

Wani irin mugun kallo ta watsa masa tace "Kai ka kalli kanka da kyau ragon banza yi ɗaya sai kace ka gaji, har miye abin sha'awa a jikin ka da, manage Kawai nakeyi da kai sabida babu yadda na iya ne, but ZEEYAD kai kanka kasan dole he must be different from all men, surar jikin sa kaɗai ya isa ya zautar da mace bale kuma aje ga how good he tastes in bed."

Kishi fal cike a zuciyar saurayin yace "Naji yana da kyawun fuska da na jiki, but how sure are you cewar zai iya biyawa mace buƙata bayan ba ta6a gwada shi kikayi ba."

Kallon sa tayi tace "Lafiyayyen namiji kallo ɗaya nakeyi masa na gane cewa shi ɗin lafiyayye ne, ka bar cika ni da surutun banza kayi tunanin yadda zamu samo mafita."

6ata fuska saurayin yayi kafin yace "Wai tukun kinma san wani abu kuwa?."

"Menene?."

"Yarinƴar nan Jalilah na fahimci son ZEEYAD take, sabida inda jiya sau biyu kenan ina ganin shigar ta part ɗinshi, and i saw him rungume da ita jiya seems like sun fara soyayyar ma dan kuwa yau da zai tafi har gifting ɗin abu tayi masa cikin lunch box."

Tunda ya fara magana Sarauniya Naseeba ke zaro manƴan idanun ta kamar zasu faɗo ƙasa "Kai wane irin mahaukaci ne daƙiƙi, maiyasa baka sanar dani wannan batun ba sai yau?."

Ɗaga kafaɗa yayi yace "Well ai gashi yanzu na faɗamiki, hope zaki bani tukwuici da wannan labari da na kawo miki?" ya faɗi hakan yana lashe baki.

Wani irin azababbiyar mari ta ɗauke shi dashi tace "A wannan mummunar labarin kake son na baka tukwuici, kayiwa kanka ka tashi ka fice ka bani wuri yanzun nan tun kafin raina ya idda 6aci, tashi yayi cike da muguwar fusata yana niyyar ficewa tace "Suhail?."
Dakatawa yayi ya juyo yana kallon ta kafin tace "Inason ka tabbatar min da gaskiyar zance Jalilah son ZEEYAD take kokuwa, idanma zai yiwuwu ka bibiyi YAZEED koh abokin sa Sadeeq kayi dukkanin yadda zakayi na samomin report ɗin cewa shi ZEEYAD ɗin na sonta kokuwa, idan kayimin hakan toh tabbas kanada tukwuici mai girma."

Murmushi yayi kafin ya jinjina kai yana ficewa.

"Oh Jalilah darling, mai kuma kike ƙoƙarin sanƴa kanki ciki yanzu, kika shiga gona ta then mai kike tunanin zai faru dake, why don't you just wait a matsayin that decent yarinƴar da na sani, ba zanso illatar da innocent ƙaramar yarinƴa kamar ki ba" ta faɗi hakan cikin harɗewar fuska.






*Yawan Comment, Yawan Typing*(kunga bansa hakan a post ɗin jiya ba shiyasa duk kuka karanta kukayi shiru bai wuci mutane biyar bane sukayi comment, ku kunji daɗi nikuma kun barni da takaici koh?, toh ku daiyi hattara😌)





*MHIZZ JIDDHER...................✍🏽*



[8/5, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*




*036...*


_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_




*LONDON, UNITED KINGDOM, (UK).*




___________ZEEYAD ne zaune a wani irin ƙayataccen office shi kaɗai babu abinda kakeji sai ƙarar sketching ɗin da yake da Pencil akan paper ɗin dake gaban sa.

Knocking ƙofar shigowa akayi inda ya bada izinin shigowa, wasu mutane ne biyu suka shigo mace da namiji, kallo ɗaya zakayi musu ka fahimci suɗin turawa ne.

Macen ajiye tray ɗin lunch ɗin da ta shigo dashi tayi daga chan gefe inda aka ware tare da ƙayata shi kamar falo, kafin kuma ta fice.

Wuri Namijin ya samu ya zauna, sai da ZEEYAD ya gama abinda zaiyi cikin zanen kafin ya tattaro wadanda ya zana baki ɗaya ya haɗa kansu cikin wata ƴar madaidaiciya folder yana ɗagowa ya kalli ɗan matashin saurayin dake gaban sa.

Hannu ya miƙawa ZEEYAD suka gaisa kafin ZEEYAD yace "Here, aikin su ya kammala, kamar yadda sukayi alƙawarin sai an kammala aikin zasu bada sauran 50% ɗin kuɗin then am waiting" ya ƙarashe yana tura folder ɗin gaban Saurayin.

Saurayin mai suna Ben ne yace "Yes sir, but ba'a yi musu painting ɗin da suka buƙata ba."

"What kuna nufin kuce bakuyi musu bane komiye?."

"No sir bamuyi ba."

"But why, na faɗamuku cewa kuyi musu didn't i?."

"Yeah, but sir sunce aikin ka suke so ba na wani ba, hakan yasa nayi deciding idan kazo kawai kayi musu."

"Mai dame suke so a zana musu?."

"Abubuwa goma ne kawai sabida akwai wani tsohon babban Museum da suke son sake ƙawata shi, and sunce suna son aikin ne cikin satin nan."

"This week?, but kasan dai ba zanyi sati ɗaya a ƙasar nan ba, but i will try na ganin na kammala musu in 2days da zan ƙara anan, su kuma sauran kuji dasu."

"Yes, Boss." ya faɗa.

"Anything else?" cewar ZEEYAD.

"Yeah Sir, da akwai wani Babban Engineer daga ƙasar Canada, yaga ayyukan ka and he was very impressed sunyi matuƙar tafiya dashi, shima yana buƙatar haɗuwa da kai dan tattauna wasu abubuwa, sannan yace da akwai contracts dayawa da yakeson baka, nayi masa alƙawarin idan kazo zan sanar masa shikuma zai taso tundaga chan yazo ya sameka."

Wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya ZEEYAD ya sauƙe yana lumshe idanu, numfasawa yayi yace "Fine then, but don't forget idan ya wuce jibi then ba zai samu gani na ba, anything else?."

"No, sir shikenan we will take care of the rest."

"Good" ya faɗa yana miƙewa tsaye.

Tsaye shima MANAGER ɗinsa Ben ya tashi, kafin ZEEYAD yayi gaba yana mara masa baya suka fice daga office ɗin ba tare da yabi ta kan abincin da aka kawo masa ba.

Bayan ya bar Company ɗin Guest House ɗinsa ya dawo, sai da ya sake yin wanka sannan yayi taking Nap, bayan ya farka ne kuma ya nemi abinda zai ci.

Hot chocolate coffee ya haɗa cikin ƴar madaidaiciyar mug kafin ya fito falo ya zauna ya hau sipping kaɗan-kaɗan.

Tunowa yayi da Chips-Cracker ɗin da Jalilah ta bashi, dan haka tashi yayi ya koma cikin ɗaki ya ɗauko ya dawo falon ya zauna.

Hawa biyu ne silver lunch box ɗin dan haka buɗe hawa na farko yayi inda yaci karo da farar paper a ciki.

Ɗan frowning face yayi cikin mamaki yana ɗauko farar paper ɗin a ciki ya hau jujjuya ta a hannun sa.

Buɗe ta yayi inda akayi rubutun ta larabci, kafin ya shiga karantawa.

Sai da ya kai ƙarshe kafin ya ɗanyi chuckling beneath his breath yana ajiye paper ɗin, kafin ya ɗau box ɗin ya buɗe ɗayan hawan, nan ne yaci karo da chips ɗin wanda akayi masa yankan chops.

Hannu yasa ya ɗauko ɗaya tare da jujjuya shi yana kallo kafin kuma a hankali ya kai bakin sa yana mai yin basmala.

Ƙurus-ƙurus haka ƙarar taunar da yayi mata ya bada "it's cracking indeed" ya faɗa yana sake ɗauko ɗaya ya kai bakin sa.
Mug ɗin Coffee ɗinsa ya ɗauka tare da kaiwa baki yayi sipping.
System ɗinsa da ya jona a chaji ya tashi ya ciro kafin ya hau danne-dannen sa yana cin chips ɗinsa yana haɗawa da sipping coffee.

Idanun sa kan system ɗin ya kai hannu cikin box ɗin a karo na ba adadi, nan yaji ta wayam.
Sake kai hannun yayi yana yawo da ita cikin kwanon kafin ya ɗago yana maida duban sa kai

Please Login or Register in order to submit comment