Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa kamar kuma mai tsoro ya kai hannu tare da ɗaukar jaririn yana kallon sa.

Shiru yaron yayi tare da ƙure fuskar wanda ya ɗauke shi ɗin da idanu yana kallo.

Sosai suke kallon juna shi da jaririn, cikin wasa yaron ya kai hannu ya shiga jan doguwar gemun fuskar sa da tayi buzu-buzu da ita.

Murmushin kan le6e ya saki ganin yadda ɗan jaririn keyi masa wasa.

Rungume shi yayi a ƙirjin shi yana lumshe idanun sa.

Dai-dai lokacin DEENAH da taji shirun ɗan nata yayi yawa ta fito dan ganin meke faruwa, turus tayi taja tana kallon bayan mutumin da jikin sa ke rufe da bargo har zuwa kansa.

Batayi wata-wata ba ta hau dube-duben abin duka ganin 6arawo ya shigo yana neman satar mata ɗanta.

Idanun ta ne suka faɗa kan flower-vase dake ajiye a dan haka da sauri ta kai hannu tana ɗauko shi kafin ta shiga takawa a hankali zuwa bayan mutumin, a hankali tace "Stay away from my child."

Saurin buɗe idanun sa dake a lumshe yayi yayin da zuciyar sa ta shiga running very faster.

Ganin bai juyo ba kuma bai motsa bane ya sanƴa ta sanƴa hannu tana yaye rufin da yayiwa kansa, idanun ta kan doguwar gashin kansa da ya sauƙo har baya tace "Surrender yourself... now."

Ganin har yanzun bai motsa bane ya sake sanƴa ta faɗin "Please ka ajiye min ɗana, i will give you everything you want, just don't hurt my child please" ta faɗa dan so take ya ajiye mata ɗanta kafin ita kuma tayi maganin shi.

Ganin ya motsa yana shirin juyowa ne ya sanƴa ta saurin ja da baya tana bada gap tsakanin su idanun ta akansa.

A hankali ya shiga juyowa still yaron rungume dashi yana sauƙe idanun sa cikin nata, kallon ta yake kafin kuma in a calm voice ɗinsa ya kira sunan ta "MADEENAH."




*Yawan Comment, Yawan Typing*





*MHIZZ JIDDHERR.............✍🏽*
[9/8, 5:11 PM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```






*SEMI__FINAL*



*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*




*054...*



_________A razane taja da baya tana yada vase ɗin hannun ta take ya tarwatse a ƙasa.

Manƴan idanun ta da ta waro tamkar zasu faɗi ƙasa ne ta kafa masa tana kallo cike da ɗimuwa da tashin hankali.

She can't believe her eyes, she can't believe mutumin da ya mutu kusan shekara ɗaya kenan shine tsaye a gaban ta, no inaa tayaya za'ayi hakan?, bayan kowa ya tabbatae da mutuwar sa har ma aka kai shi aka binne a idon ɗumbin jama'a, shine za'ace tsaye a gaban ta, toh kodai fatalwar sa ce?

Tasan tabbas ba shi bane ba, jikin ta ne ya kama rawa haka ma bakin ta da takeson buɗewa tayi magana sai dai ta kasa, a hankali kuma cike da tashin hankali ta shiga lalumar jikin bangon ɗakin still idanun ta akansa wanda shi ɗinma bai bar kallon nata ba har ta kai bakin ƙofar fita.

"DEENAH?" ya sake kiran ta.

Sake firgicewa DEENAH tayi jikin ta inbanda kyarma ba binda yakeyi, babban damuwar ta shine little ZEEYAD dake riƙe a hannun sa.

"DEENAH?" ya sake kiran ta yana taka ƙafarsa.

Ihun da ta saki ne ya sanƴa shi dakatawa daga tunkarar ta "Stay away from me, ka ajiye min ɗana ka tafi na roƙeka dan girman Allah kada ka cutar min da ɗana" ta faɗa cikin kuka dama kuma tsoron da ya cika mata ruhi.

Sake rungume yaron yayi a jikin sa yana mamakin abinda ya sanƴa DEENAH ke gudun sa, kodai bata gane sa bane ba, shine tambayar da yake wa kansa.

Sake takawa yayi zai tunkare ta ta sake sanƴa masa wani ihun tana ja da baya, bai tsaya ba ya cigaba da tunkarar tata, cikin kiɗima ta fice daga ɗakin cikin gudu, ZEEYAD baiyi ƙasa a guiwa ba ya mara mata baya shima.

Dai-dai tazo sauƙa daga stairs wani irin sul6i ya kwashe ta bata kai ga faɗuwa ba ya taddo ta yana riƙo hannun tare da fizgo ta tana faɗawa jikin sa.

Ƙara ta saki tana rufe fuskar ta da tafukan hannun ta ganin fatalwa ya riƙo ta.

Kamar wacce kuma wani abin ya gitta mata a kwakwalwa ta tsagaita da kukan nata cak na kusan seconds kafin kuma ta shiga buɗe fuskar ta da ta rufe da tafukan hannayen ta tana ware su akan shi.

Da hannu ta shiga tatta6a ƙirjin sa ganin tana iya ta6a sa ne ya sanƴa ta ɗago da kanta da sauri tana kallon sa.

"DEENAH?" ya sake kiran ta cikin calm voice ɗinsa.

Shiru tayi tana kallon sa da idanun ta dake tsiyayar da hawaye, kallon juna duk suke na kusan 2mins kafin cikin rawar murya tace "A... Ab... Abyad?."

"Baby" ya kira ta.

Kanta ta shiga girgizawa cikin kuka tana riƙo fuskarsa dake cike da gashi ta sake kiran sa "Abyad."

Kuka ta fashe dashi tana rungume sa take faɗin "I know it, i know it... nasan baka mutu ba ban ta6a yarda cewa ka mutu ba, wayyo Allah na nagode maka."

Da hannun sa ɗaya shima ya rungume ta ɗayan hannun nasa rungume da little ZEEYAD.

Sosai DEENAH ke kuka kamar zata shiɗe, bai iya hana ta ba sabida yasan mai takeji da shima zai sami damar kukan da babu abinda zai hana shi yin kukan, lumshe gajiyayyun idanun sa yayi yanajin wani irin kewa haɗi da so da ƙaunar ta na huda dukkanin wani sassa na jikin sa.

Sun daɗe a haka zuciyar su cike da kewar juna, ƙishi-ƙishin ɗin kukan little ZEEYAD ne ya fargar dasu, ɗagowa tayi tana kallon sa kafin ta dubi yaron hannun sa inda shima ya ɗago yaron yana kallon sa.

Murmushi DEENAH tayi tana amsar sa shi dai ZEEYAD da kallo kawai yake binta dan kuwa ya rasa ɗan waye wannan ɗin.

Kallon idanun sa dake cike taf da alamun tambaya DEENAH tayi, kamo hannun sa tayi suka koma cikin ɗakin dan kuwa ta lura da akwai tarin stress da gajiyawa tattare dashi.

Rufe ƙofar tayi tana kwantar da little ZEEYAD kan bed kafin ta tunkaro ZEEYAD dake tsaye tana kallon sa.

Ganin tana sake shirin wani kukan ne ya sanƴa shi janƴo ta jikin sa yana bata tight hug mai kyau, sai dai har izuwa wannan lokacin babu koh burbuɗin murmushi akan fuskar sa, runtse jajayen idanun sa dake yi masa yaji yayi kamar wanda zai maida ta cikin sa ya huta da kewar ta dama kuma ƙaunar ta dake sake ninkuwa kullum cikin zuciyar sa, shi kaɗai yasan halin da ya shiga a wannan kwanciya ciwon da yayi na kusan shekara ɗaya.

DEENAH jin abinda take duka tamkar a mafarki, ta rasa da wasu irin kalamai zata kwatanta yadda takeji cikin zuciyar ta, she can't believe it, ta rasa ya akayi hakan ya kasance a raye bayan kowa ya shaida mutuwar sa, jana'izar sa dama kuma binnewar sa, ya kuma za'ayi ya dawo, sai anan ne kuma tunanin abinda YAZEED ke son faɗa mata lokacin da mahaifiyar sa tayi masa aika-aika ya shiga dawo mata kwanƴa, da alama sunan ZEEYAD yakeson kama mata a lokacin sai dai aka katse sa, kenan ya san wani abu ne dangane da hakan komiye?.

Ɗagowa tayi tana kallon sa, ɗan ɗagyal tayi tana manna masa long kiss a goshi kafin tace "I miss you" hawaye na biyo mata ƙunci.

Shi dai kawai da kallo yake bin ta yanajin wani irin ɗaci a zuciyar sa da maƙoshin sa, bakomai ke sanƴa shi jin hakan ba sai tsanar Hafeezah dama kuma wadanda take aiki tare dasu.

Cire masa bargon jikin sa tayi tana ajiyewa a gefe, kafin ta shiga rage masa kayan jikin sa, Bathroom ta nufa ta haɗa masa ruwan wanka mai zafi yadda zaiji daɗin wankan.

Fitowa tayi da towel riƙe a hannun ta kafin ta nufe sa tana miƙa masa, amsa yayi daga hannun ta yana bin ta da kallo duk inda tayi, ji yake tamkar ya fashe da kuka sabida irin baƙin cikin da yake ciki, he can't believe kusan 1year baya tare da Family ɗinsa all because of Hafeezah da son zuciyar ta, sadda kai ƙasa yayi yana cize la6an sa sosai da sosai zuciyar sa ke wani irin bombing shi kaɗai yasan abinda yakeji dama kuma Iriyar abinda zaiyi mata.

Muryar DEENAH da ya tsinkayo tana yi masa magana tunɗazu ne ya sanƴa shi ɗago da kansa a hankali kafin ya tashi ya nufi bakin bathroom ɗin inda take tsaye.

Saurin tura shi ciki tayi lokacin da tajiyo muryar JALILAH a bakin ƙofa tana rufo shi cikin bathroom ɗin.

Juyowa tayi ga JALILAH da ta shigo tana sakin mata murmushin yaƙe.

Murmushi JALILAH tayi mata kafin tace "Grandma tace na dubo ki na taya ki haɗa kayan taga kin daɗe ne."

Murmushi DEENAH tayi kafin tace "A'a ki barshi nima zan ƙarasar, amma ga Abyad nan ki tafi dashi nima yanzun nan zan fito" ta faɗa tana ɗaukar little ZEEYAD.

Amsar sa JALILAH tayi cikin murmushi tace "Are you sure you don't need a hand?."

Kai ta girgiza mata tace "Yeah, yanzun nan zan ƙarasar nazo ni."

Juyawa tayi zata tafi idanun ta suka faɗa kan tsohon bargo da kayan da ZEEYAD ya dawo dasu a ajiye, kallon DEENAH tayi nan tayi mata murmushi tace "Inaga tsoffin kayan Abyad ne."

Murmushi JALILAH tayi kawai tana ficewa daga ɗakin.

Da sauri DEENAH ta sanƴa masa key kafin ta koma bathroom ɗin, tsaye ta ganshi dafe da sink ɗin ƙaton mirror ɗin bathroom ɗin ƙugun sa ɗaure da towel.

Motsin shigowar ta ne ya sanƴa shi ɗagowa yana kallon ta, murmushi ta sakar masa kafin kuma tayi inda su cream da sabulan wanka ke jere tana lodo su ta zuba gaban mirror ɗin.

Stool taja masa ya zauna kafin ta buɗe drawer ta ɗauko scissors, clipper da dai dangin kayan aski da gyara suma tana zuba su gaban mirror ɗin.

Kallon sa take kamar yadda yake kallon ta, ba tare da tace dashi komai ba ta tattari dogon gashin kansa tare da sanƴa scissors ta shiga yanke shi, she can't believe cikin shekara ɗaya ya tara uban gashin da ya zarce nata.

Shaving cream ta mulka masa a fuska, sai da ta gama yi masa gyaran gashin kan nasa ya koma kamar na dah kafin kuma ta shiga gyara masa na fuskar sa, take kuma asalin kyawun sa da kamannin sa suka shiga bayyano wa.

Murmushi tayi tana jinta so very emotional kamar tayi kuka takeji haka kuma wani 6angare na zuciyar ta ke cike da farin cikin da ta kasa bambamce wane iri ne.

Almost hour ɗaya da rabi suka ɗauka kafin ta maida shi ainihin ZEEYAD ɗinsa, sai tada wani irin ƙamshi na musamman yake, sosai yaji wani irin iska na ratsa dukkanin ƙofofin gashin jikin sa, sai a yanzu yaji dama-dama haka kuma yaji kusan 50% na 6acin ransa ya gushe ganin yadda matar sa ta zage ta gyara shi ya dawo ainihin shi cikin ƙanƙanin lokaci.

Kallon sa take ganin yadda yayi kyau sosai, sai dai idanun sa da suka faɗa dama kuma ɗan ramewa da yayi sakamakon tsawon lokaci da ya ɗauka a kwance.

Sai dai ta rasa dalilin da yasa har yanzu babu fara'a kan fuskar sa dukda kuwa taga ya saki fuskar ba kamar ɗazun ba.

"You should get some rest" ta faɗa tana kallon sa.

"Only with you" ya bata amsa yana kallon ta.

Riƙo hannun ta yayi tare da sumbata, runtse idanun sa yayi yana sauƙe wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya, sosai abubuwa dayawa ke ci masa rai, sau tari an so aga bayan sa sai dai Allah na kareshi baya nasu nasara, but wannan karon a matuƙar fusace yake fiye da tunanin mai tunani, ji yake zai iya aikata komai idan yace komai yana nufin komai dan ganin bayan masu son ganin bayan sa, wannan karon karankatakaf zai maida hankalin sa ne ga fansar da zai ɗauka, ba zai ji kunƴar idon kowa ba koh da kuwa na ɗan uwan sa YAZEED ne, an kai sa maƙura wanda yakejin ba zai iya saurarawa koh tausayawa ba, all he needs and craves for shine yaga bayan Hafeezah muddin bai ga bayan ta da na ire-iren ta ba toh tabbas hankalin sa ba zai ta6a kwanciya ba, ba zai ta6a samun nutsuwa cikin zuciyar sa ba.

Cikin tsananin fushin da yake yayi magana wanda har muryar sa bata iya 6oye hakan ba yace "The Baby..."

Kallon sa DEENAH tayi kafin tace "He is... our Baby."

Ɗago da jajayen idanun sa yayi yana zuba su cikin nata "Our Baby?" ya faɗa 6acin ransa na gushewa.

Kai ta jinjina masa tana sadda kai ƙasa.

Ɗago da ha6ar ta yayi yana kallon ta kafin kuma yace "Kin raini cikin babyn mu all on your own?" ya faɗa kamar wanda zaiyi kuka ransa na daɗa 6aci kafin kuma ya ɗaura da faɗin "Am sorry i wasn't there with you."

"But it's not your fault" ta faɗa tana kallon sa da idanun ta dake tara hawaye.

Cize baki yayi tare da jinjina kai, sosai yake baƙin ciki baƙin cikin yadda Hafeezah tayi nasarar nesanta shi da family ɗinsa, DEENAHr sa dama kuma baƙin cikin rashin kasancewar sa lokacin da ta sami ciki ta raine shi ita kaɗai har ta haife shi, kenan dah ace Hafeezah tayi nasarar kashe sa then DEENAH will remain a single Mom har izuwa tsawon lokacin da zata sake samun wani wanda zai maye gurbin sa sannan ɗansa zai taso ba tare da soyayyar uba koh ganin mahaifin sa ba, ji yayi ransa ya sake 6aci fiye da dah, wuri ya samu ya zauna bakin bed ɗin, shi kaɗai yasan abinda yakeji cikin zuciyar sa, bayida wani buri da ya wuce na ganin bayan Hafeezah.

Dunƙule hannayen sa yayi yana runtse idanun sa da suka canza launi.

Zama DEENAH tayi akan sofa tana yin matashi da laps ɗinsa kafin ta shiga faɗin "Ranar da suka cemin ka mutu Allah ne kaɗai yasan irin halin da na tsinci kaina, i was shattered and alone, ban ta6a yarda da cewa ka mutu ba amma babu wanda ya saurare ni they all believed cewa ka mutu sannan ba zaka ta6a dawowa ba, it was the next day after your false death aka gano ina da cikin 2weeks, nayi kukan da ban ta6a yin irin sa ba a wannan ranar sabida ni kaɗai ce zan raini yaron mu sannan zai taso a maraya babu uba, but luckily for me Grandma was always there for me na ganin ta kwantar min da hankali tare da bani baki, a haka na raini ciki na cikin kariyar Ubangiji sabida irin hare-haren da akayi ta kawo masa, a haka na raine shi har izuwa ranar da na haife shi sai sannan ne na yarda da cewa ka tafi dagaske sannan ba zaka ta6a dawowa garemu ba, nayi kewar ka fiye da tunanin mai tunani, babu ranar da bana zubar da hawaye tare da yi maka addu'a, Hafeezah tayi dukkanin iya bakin ƙoƙarin ta na ganin taga baya na da abin dake ciki na sai dai hakan ya gagara hakan ya sanƴa ta ɗaukar ƙarar tsana ta ɗaura min..." shiru tayi sakamakon kukan da yaci ƙarfin ta nan ta shiga rera shi.

Zamewa yayi ya sauƙo kafin ya rungume ta a jikin sa tare da lumshe idanun sa, wani irin abu mai ɗaci ya haɗiya yana cigaba da patting bayan ta.

"Am here now, insha Allah komai yazo ƙarshe, no harm will come to you or our Baby, i promise you this" ya ƙarashe yana buɗe jajayen idanun shi.

Cikin kuka DEENAH tace "Hafeezah is in jail right now, she... she tried to kill me but..." shiru tayi ta kasa iddawa sakamakon kukan da yazo mata.

"Tell me" ya faɗa yana cigaba da shafa bayan ta.

Labarin dukkanin abubuwan da ya faru ta basa ba tare da ta rage komai ba.

Iska mai ƙarfi yaja tare da furzar wa tamkar wanda yaci abu mai yaji sosai, sosai idanun sa suka sake kaɗawa tsabar 6acin ran da yake ciki jikin sa har rawa ya shiga yi yayin da jijiyoyin jikin sa suka mimmiƙe ruɗu-ruɗu kamar ka zaro su daga jikin nasa.

Dukda baiyi magana ba ita kanta DEENAH ta tsorata da yanayin sa, miƙewa yayi itama tana miƙewa da sauri, safa da marwa ya kama yi cikin ɗakin hakan ya sanƴa DEENAH riƙo shi tana faɗin "Kabi komai a hankali Abyad."

Furzar da hannun ta yayi daga riƙon da tayi masa ɗin har tana kamar zata faɗi.

"Abyad" ta kira shi, hanƴar ficewa yayi daga ɗakin a fusace tana mara masa baya ta riƙo ƙofar tana faɗin "Ina zakaje, you can't go out like this."

"Get out of my way..." ya faɗa cikin huci.

"Ina kake tunanin zakaje, atleast you should get some rest first?."

"Rest, you want me to get some rest DEENAH?."

Shiru tayi kawai tana kallon sa.

"Out, out of my way" ya sake faɗa yana tsare ta da jajayen idanun sa.

"Abyad ka..."

"Out of my way?" ya katse ta cikin tsawa.

Sosai ta tsorata har batasan sadda ta basa hanƴa ba, buɗe ƙofar yayi ya fice a fusace kafin tayi saurin mara masa baya.

Sosai yake tafiya tamkar zai tashi sama, kallo ɗaya zakayi masa ka gano tsantsar 6acin ran dake cikin zuciyar sa.

DEENAH haɗa tafiyar tata take da ɗan gudu dan kuwa ta kasa taddo shi, duk inda suka ratsa kuwa sai dai ayi ta basu hanƴa wasu na ihun fatalwa yayin da wasu kuwa na kare kawai suke arta wa ƙafar su.

A haka suka ƙarasa cikin fadar sam bai jira an buɗe masa ƙofar shiga ba ya bangaje ta ya shige, sosai idanun sa suka rufe baya tunanin zai kyale duk wani rashin ɗa'a da akayiwa matar sa, duk sai kowa ya girbi abinda ya shuka ɗaya bayan ɗaya.

Duka ƴan fadar miƙewa sukayi cike da mugun kiɗima suke bin ZEEYAD da kallo tayaya mutumin da suka binne sa suka rufe masa fuska da ƙasa zai faɗo musu cikin fada tamkar wanda aka koro shi.

Kai tsaye kan Ayaan dake zaune daga gefe yayi kamar yasan zai same shi anan ɗin kuwa, baiyi wata-wata ba ya cakumo kwalar rigar sa kafin kuma ya shiga basa kyawawan mari ba tare da yama damu da rashin hannu ɗaya da bayida shi ba, sosai yake laftawa Ayaan marin da yake sanƴasa wuntsilawa har yake ji da ganin sa suke ɗaukewa na wucin gadi kafin ya farfaɗo kuwa ya sake jin sauƙar wata marin, ɗaga sa ZEEYAD yayi yana basa wasu irin kyawawan blow a fuska yana haɗa shi da bango, ihu kawai Ayaan keyi gashi babu wani wanda yayi kuskuren takowa inda yake bale yasa ran za'a cece shi daga hannun mai bugun nashi dan kuwa koh fuskar sa bai samu ya gani ba, sosai yayiwa Ayaan jina-jina har kamannin sa sai da suka sauya ya koma mummuna dashi fuskar nan tasa tayi luhu-luhu yawa kwa6a66en flour ɗinda yaji yeast, sosai ZEEYAD ya haɗa masa jini da majina a fuska, haƙoran sa da suka zube kuwa sun kai huɗu tsabar bugun da yasha, dukda irin wannan bugun ZEEYAD bai ji ya sami nutsuwa a ransa ba, inda ake rataye takobi ya nufa yana zaro guda ɗaya tare da nufar kan Ayaan ɗin da ya kasa motsa koh da ƴar yatsar sa ne, ɗaga takobin yayi yana shirin sara masa DEENAH tazo da gudu tana riƙe hannun sa ta baya, cikin kuka take faɗin "Control yourself Abyad, zaka kashe shi fah."

Sai a sannan ya dawo hayyacin sa yana sauƙe takobin, rungume sa tayi ganin yadda jikin sa ke rawa cike da 6acin rai tana kuka.

Yasar da takobin yayi shima yana rufa mata hannayen sa, a hankali yake faɗin "Are you satisfied now?."

Kai kawai take jinjina masa tana cigaba da shessheƙa, kiss ya manna mata a kai cike da ƙaunar ta yana shafa kan nata.

Sun jima a hakan sosai basu ma lura da mutanen dake tare a wurin kowa na kallon su cike da mamaki ba.

"Boy?" Grandma ta kira sa.

Buɗe jajayen idanun sa yayi lokacin da yaji sauƙar muryar Granny ɗinsa cikin kunnuwan sa.

Zame jikin sa yayi daga na DEENAH yana juyowa ya kalleta, sosai ta sake waro idanun ta tana dafe ƙirji cike da kiɗima dan kuwa da aka kai mata gulmar da ya gama maye gari sam bata yarda ba, sai yanzu da idanuwan ta suka sauƙa akansa.

DEENAH ce tayi saurin faɗin "Ba na faɗamuku ba, nacemuku Abyad bai mutu ba amma babu wanda ya yarda dani, and here he is now, kowa ya ganewa idanun sa sannan kuma nasan zaku daina ɗaukata matsayin zautacciya yanzu."

"Grandma" ya faɗa yana iyowa kanta.

A ɗan tsorace taja da baya still idanun ta akansa.

Kamar wanda zaiyi kuka ya miƙa mata hannayen sa, sai da ta tsaya tana sake ƙare masa kallo kafin kuma ta shiga takowa gareshi, hannayen nasa ta fara ta6awa cikin tsoro.

Waro idanu tayi ganin dai dagaske ba fatalwa ta ta6a ba, ɗago da idanun ta tayi tana kallon sa ta sake kiran sa "Boy."

"Grandma" ya faɗa yana rungume ta.

Kuka Grandma ta fashe dashi tana faɗin "Allah mai iko kenan" sake ɗagosa tayi tana tatta6a jikin sa kafin ta sake rungume shi tana faɗin "Ba Fatalwa bane ba, Boy ɗina ne Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah abin godiya, tabbas duk wanda bai yarda da akwai Allah ba ya ta6e duniya da lahira, ikon Allah ya wuce gaban tunanin ɗan Adam, babu abinda Allah baya iyayi, lallai Allah ba azzalumin bayin sa bane, duk kuwa wanda yace zaija da ikon Allah ya shiga uku."

"How is this possible" cewar wani daga cikin mutanen da suke wurin.

"The prince is dead, we all witnessed him being buried, how comes kuma za'a ce shine wannan, bayan koh lokacin dah bamu ta6a jin inda akayi mutuwa kuma aka dawo ba."

"Yeah ofcourse he isn't dead" cewar Sadeeq dake tsaye a wurin tunɗazu.

Duk juyowa sukayi suna kallon sa, ɗaya ne yace "How sure are you about this?."

"Sabida mune wadanda muka tono shi bayan an binne shi, bayan na gano cewa bai mutu ba he is alive."

Grandma ce ta ƙaraso gun Sadeeq tana kallon sa kafin kuma ta ɗau hannu tana wanke fuskar sa da mari tace "You know this since but you decide to keep the truth away from us, bayan kafi kowa sanin halin da DEENAH ta shiga bama ita kaɗai ba da mai Martaba ma kanshi, amma koh da wasa baka ta6a furta mana wani abu akan sa ba."

Sadda kai ƙasa YAZEED yayi yace "Am sorry Grandma..."

"Don't be sorry, am just mad at you sabida 6oye mana hakan da kayi amma yanzu na gano amfanin hakan ma sannan kayi abinda ya dace, come on give me a warm hug ɗan albarka."

Murmushi Sadeeq ɗin yayi yana rungume Grandma ɗin, Albarka ta sanƴa masa kafin ta ɗago tana kallon sa tace "Ya jikin YAZEED, har yanzu mai Martaba na chan wurin nasa ne?."

Kai ya jinjina mata kafin yace "Shima his health is improving."

Murmushi tayi cike da farin cikin jin hakan kafin ta kalli ZEEYAD dake riƙe da DEENAH tace "Yakamata a sanarwa da mahaifin ka wannan kyakkyawar labarin sabida ya samu hankalin sa ya kwanta, tunda YAZEED ya faɗa rashin lafiya da sakamakon mummunar abinda Hafeezah ta aikata ya kasa samun sukuni sabida gani yake zai rasa shi shima kamar yadda ya rasa ka, dama ance bayan wuya sai daɗi Allah ne kaɗai yasan dalilin shi na jarabtar wannan ahali ta wannan hanƴa gashi nan kuma mun fara ganin sakamako mai kyau. Shiyasa akace dukkanin wani tsanani da zaka tsinci kanka a ciki kada ka kuskura ka cire rai daga samun rahamar Ubangiji haka kuma kada ka gajiyawa da yawan addu'a, Allah na jarabtar bayin sa ne ta hanƴoƴi da dama sannan ba wai dan baya ƙaunar mu bane yake jarabtar mu hasalima yafi jarabtar bayin sa da yafi so, dan haka mu sake godewa Allah da wannan jarabawar da yayi mana domin kuwa gashi nan mun fara cin moriyar ta dukda kuwa ance wata hisabin sai a lahira, Allah ne kaɗai zaiyi mana maganin azzaluman cikin mu."

Kallon wata kuyanga tayi tace "Ke Marwa, kije ku ɗaura girki mai rai da lafiya wanda zai ishi kowa dake cikin MASARAUTAR nan ayi sadaka, abinci zaku dafa irin ta ƴan gayu sannan a fitar a rabawa mabarata da almajirai sannan akai masallatai kowa da kowa ya samu."

Cike da girmamawa wacce tayi wa maganar ta amsa.

"Kai kuma Najeeb kaje ka bada sanarwa wata sati a ranar ita yau akwai gagarumar Walima da za'a gabatar a cikin MASARAUTA sannan ana gayyatar kowa

Please Login or Register in order to submit comment