Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kowa ya hallara, za'ayi walimar da ba'a ta6a yin irin sa ba a wannan MASARAUTA."

Cike da jindaɗi da girmamawa shima ya amsa yana ficewa, mutane ne suka fara yiwa ZEEYAD jaje dama kuma murna kafin kuma kowa ya shiga watsewa.

Kallon Sadeeq ZEEYAD yayi yanajin ƙaunar aminin nasa sosai cikin zuciyar sa, ya wuce matsayin amini sai dai ɗan uwansa, murmushi Sadeeq ya sakar masa yana ƙarasowa gaban sa, rungume juna sukayi cike da farin ciki.

"Grandma ce tace, ya isa haka nan maza kuzo mu garzaya muje asibitin mai kuma muke jira?" ta faɗa cike da farin ciki da zumuɗin da take ciki.

Idanun ta ne suka sauƙa kan Ayaan dake ta maida numfashin wahala da kyar nan tace "Waye wannan ɗin?" lura da tayi da hannun sa ne ya sanƴa ta faɗin "Ayaan, hatsari yayi ne haka komiye?."

Ganin babu wanda ya bata amsa ne ya sanƴa ta faɗin "Toh ai shikenan, kai kuzo ku ɗauke sa ku kai shi wata asibiti dan mu sauri muke da mun taimaka masa, nama yi maka hakan ne sabida tausayi da ka ɗan bani."

Tana faɗin haka ta kaɗa kawunan su sukayi gaba.

Riƙo hannun ZEEYAD DEENAH tayi cikin nata, murmushi ya sakar mata itama tana maida masa martani.


*********************


________"Da kinsan abin dake faruwa cikin MASARAUTA da kin bar maganar cewa kin gama da ZEEYAD saura DEENAH da ɗanta."

"Mai kike nufi?."

Dariya Sairah tayi tana faɗin "ZEEYAD bai mutu ba yana nan da ransa..."

Katse ta tayi da faɗin "Maganar banza maganar wofi..."

"Kina nufin kice ƙarya nakeyi miki ne kokuwa?, ZEEYAD na nan da ransa bai mutu ba..."

"Maganar banza kike faɗi, Boka ya tabbatar min da cewa ya mutu sabida aljanin da ya tura masa Ƙaƙƙarfa ne dan kuwa da zaran ya shige jikin mutum koh shurawa baya sakeyi, sannan da idanun mu aka fitar da gawan sa akaje aka binne sa."

Murmushi tayi tace "Toh bara kiji ZEEYAD bai mutu ba, aikin bokan ki baiyi tasiri akansa ba, koh da aka binne shi wannan likitan abokin nasa dashi da YAZEED ne sukaje suka tono sa sabida sun san yana raye sannan suka 6oye sa a inda babu wanda ya sani tsawon wannan lokacin har izuwa yanzu da ya warke yake neman fansa ido rufe, inama jiye miki tsoron idan Ayaan bai mutu ba zuwa yanzu."

Zaburowa tayi tana waro manƴan idanun ta, gumi ne ke ƙeto mata yawa wacce ake yayyafa mata ruwa, cikin tashin hankali tace "Ayaan ɗana, mai yayi masa, a'ina Ayaan ɗin yake yanzu?."

Ta6e baki tayi tace "Rai a hannun Allah aka kaishi asibiti, waya sani ma koh ya mutu a hanƴa."

"Kada ki nemi ya6a min maganar banza mana, ina Rahinah fah?."

"Hmm, Rahinah ai tuni ta zame hannun ta dan kuwa kinsan matsoraciya ce, nice keta ƙoƙarin ganin naga bayan DEENAH da abinda ta haifa amma hakan yaci tura, yanzu kuma da ZEEYAD ya dawo na tabbata kashin ki ya bushe sabida ni koh sake ganin fuskata ba zakiyi ba daga yau, dama nazo ne na sanar miki da abin dake faruwa kuma dama cin arziki ya kawoni kuma na tara iya rabo na, ina fah godiya da bani access akan dukkanin wasu dukiyoyin ki, ni yanzu kinga tafiya zanyi koh bakomai kwalliya ta biya kuɗin sabulu."

Kamar zata 6alla ƙofar cell ɗin take faɗin "Mai kikayi min da dukiya Sairah?."

Murmushi tayi cike da mugunta kafin tace "Ai yanzu duk wasu dukiyar ki na hannu na, kama daga kan gwalagwalan ki, azurfa, zinare, diamond kuɗaɗe da dai sauran su dan haka ni nayi gaba ba sai na tsaya ganin irin hukuncin da za'a yi miki ba, kinga koh dukan da Sooraj yayi mana ya isa hukunci a gareni, dan haka ni yanzu tafiya zanyi banida wani sauran lokaci, a mutu lafiya Hafeezah" tana faɗin haka ta juya tana yi mata waving da yatsu.

Cike da tashin hankali Hafeezah ke jijjiga ƙofar kurkukun tana kiran sunan Sairah amma koh amsa ta bata yi ba.

Sosai ta shiga tsananin tashin hankalin da bata ta6a tsintsar kanta a ciki ba, ji take kamar ta 6ace har abada kada ta sake dawowa MASARAUTAR.


***********************


______Koh da isar su asibiti kai tsaye ɗakin da mai Martaba yake suka nufa, Grandma ce ta fara shiga sai DEENAH sai kuma Sadeeq dake biye dasu.

Fargawa mai Martaba yayi dasu, murmushi ya saki ganin DEENAH nan yace "A'ina kuma aka baro min yaron nawa?."

Murmushi DEENAH tayi tana sadda kai ƙasa tace "Yana gida tare da JALILAH."

Kai ya jinjina kafin ya gaida Grandma cikin Girmamawa, amsa masa tayi tana sake yi masa ya jiki.

Duba shi Sadeeq yayi kafin yace "Insha Allah damuwar ka tazo ƙarshe."

Kallon sa mai Martaba yayi yace "Insha Allah, ai na faɗamaka da izinin Allah YAZEED zai rayu."

Murmushi Sadeeq yayi yace "Am sure abin da zaka gani yanzu sai ya zama silar warkewar ka."

Shi dai mai Martaba murmushi yayi kawai.

Zama Sadeeq yayi kafin yace "Da akwai abubuwa dayawa da suka faru wanda bakada masaniya akai, daga ni sai Abhi ɗina sai kuma Sadeeq ne muka san da wannan abu sai Ubangijin da baya koh da gyangyaɗi ne bale bacci."

"Mai kake son faɗamin?" cewar mai Martaba.

Gyara zama Sadeeq yayi kafin ya shiga koro masa bayanin dukkanin abinda ya faru.

Sosai mai Martaba ya cika da mamaki, bai gama mamakin nasa ba ZEEYAD ya shigo ɗakin.

Miƙewa yayi daga zaunen da yake ya shiga nuna shi da yatsa, murmushi ZEEYAD yayi tare da kiran sa "Abhi."

"He is real" cewar Sadeeq.

Kallon Grandma da DEENAH yayi kafin ya sake maida duban sa kan ZEEYAD ɗin.

Rungume sa ZEEYAD yayi sosai yanajin ƙaunar mahaifin nasa na ratsa cikin dukkanin zuciyar sa.

Sosai mai Martaba yayi mamaki dama kuma farin cikin dawowar ɗan nasa.

Ɗago shi yayi yana kallon shi yace "I can't believe this" yana sake rungume shi tsam.

Sun jima rungume da juna kafin su ɗago, sharewa mahaifin nasa hawaye yayi tare da faɗin "Cry no more Abhi."

Grandma ce tace "Yakamata dai yanzu ace munje mun sami YAZEED ma shima mu duba ya jikin shi."

Duk dugunzuma sukayi izuwa ɗakin da YAZEED ke kwance.

Na'urori jojjone a jikin shi, ZEEYAD ne ya ƙarasa bakin bed ɗin yana kallon ɗan uwan nasa cike da tausayin sa yana riƙo hannun sa, yaso yayi sacrificing rayuwar sa na ganin ya ceci DEENAH da abin dake cikin ta, baisan iya adadin ƙaunar da yake yiwa ɗan uwan nasa ba.

Sosai yake tausayin sa na iriyar mahaifiyar da Allah ya jarabce shi dashi, baisan ya ƙarshen Hafeezah zai kasance ba.

Hannun YAZEED dake cikin nasa ne ya fara motsi nan yayi saurin maida duban sa yana sauƙe idanun sa cikin na YAZEED ɗin da ya ɗan buɗe yana kallon sa.

ZEEYAD baisan sadda ya saki murmushi ba yana kiran sunan YAZEED ɗin "He is awake" ya faɗa nan duk suma suka ƙaraso bakin bed ɗin suna kallon sa.

"You're alive?" cewar YAZEED yana kallon ZEEYAD ɗin.

Murmushi kawai ZEEYAD yayi yana sake damƙe hannun sa cikin nashi.

Da ido ya bisu farin ciki na cika zuciyar sa na ganin family ɗinsa akansa, murmushin da yakeyi ne ya ɗan gushe yace "Where is my wife?."

Murmushi DEENAH tayi tace "At home nursing our Baby" ta faɗa tana dafa kafaɗun ZEEYAD.

Kallo YAZEED ya ƙare mata kafin yace "Yaushe kika haihu, i mean jiya-jiyan nan na ganki da ciki, how then..."

Sadeeq ne yace "Banza, you've spent almost 6months a kwance anan."

Ɗago da kai yayi yana ɗan waro idanu yace "6 months?."

"And our baby is almost 2months now."

Kallon ZEEYAD yayi yace "Yaushe ka dawo?."

"Just a while ago" ya bashi amsa.

Maida kanshi yayi yace "Nayi shiru."

Duk dariya sukayi, nan Sadeeq ya sake duba lafiyar jikin sa, sun yini sosai a asibitin suna ɗebe wa YAZEED ɗin kewa.


***********************


*BAYAN KWANA UKU*


_______Sosai farin ciki kwanciyar hankali ya wanzu cikin wannan ahali a ƴan kwanaki ukun nan, sake ɗaura auren DEENAH da ZEEYAD akayi dan kuwa ana zaton wancan na farkon ya warware sakamakon nesa da yayi da ita na tsawon lokaci har ma tayi masa takaba *(Allahu A'alamu)*.


Kwance tayi kan faffaɗar ƙirjin sa, sosai suka luma cikin duniyar masoyan da sukayi kewar junan su na tsawon lokaci.

Kukan little YAZEED ne ya katse musu abinda sukeyi, nan ZEEYAD ya tsuke fuskar sa tamkar zaiyi kuka.

Dariyar ta DEENAH ta danne tana miƙewa zaune ta ɗauki yaron ta shiga jijjiga shi.

Kallon ZEEYAD tayi kafin tace "Maybe bayason ka dinga zuwa kusa dani ne shiyasa yake kuka."

Cikin marairaicewa yace "Ki kai shi gun Grandma ya kwana achan please."

Waro idanu DEENAH tayi kafin tace "Wannan ɗan mitsitsilin abun zan kai gun Grandma ya kwana?, he is just 2months."

Sosa ƙeya yayi yana kallon ta, nan tace "Alright then, idan yayi bacci yanzu sai ka ɗauke sa ka kai sa."

"Why me?."

"Daga nan sai ka yiwa Grandma bayanin abinda yasa ka kaishi ya kwana a gun ta."

Murmushi yayi yana miƙewa zaune yana ganin yadda DEENAH ke yiwa yaron wasa, peck ta bashi a lips tana goga hancin ta da nashi.

"Why will you kiss him?" cewar ZEEYAD yana kallon ta.

Kallon sa tayi ganin yadda ya haɗe girar sama da ta ƙasa, ɗan dariya tayi tace "Are you jealous of your own Son?, i didn't even kissed him it was just a peck."

Shiru yayi yana hura hanci, rolling idanu tayi kafin ta miƙe ta koma closet room, da kallo ZEEYAD ya bita yana murmushi dan kuwa kullum haka take idan zata shayar da yaron sai ta tashi a wurin ita a dole kunƴar shi takeji.

Fitowa tayi lokacin har yaron yayi bacci, shimfiɗe shi tayi cikin gadon sa kafin ta kalli ZEEYAD tace "Abyad kayi masa addu'a please" ta faɗa tana nufar bathroom.

Da kallo ya bita kafin ya nufi gun bed ɗin yaron yana kallon shi, murmushi yayi ganin how cute he is, addu'a ya tofe shi dashi yana ɗan rufa masa bargon jarirai.

Fitowa DEENAH tayi kafin ta canzo kayan ta zuwa na bacci, gaban mirror ta nufa ta shafe jikin ta da turaren jiki masu daɗin ƙamshi kafin ta dawo kan bed ɗin ta kwanta.

Kallon ZEEYAD dake kallon ta tayi tare da lumshe idanu tana faɗin "ka kashe mana wutar Abyad."

Tashi yayi yaje ya kashe wutar ya dawo yana jawo ta jikin sa.

Shiru duk sukayi kafin kuma ya kira ta "Baby?."

Amsa masa tayi nan yace "Let's do it again."

"Do what?" ta faɗa cikin ɗan waro idanu.

"Please baby" ya faɗa cikin marairaice murya.

Turo baki DEENAH tayi kafin tace "Abyad is just 2months what if ka sake yimin wani cikin fah?."

Murmushi yayi jin yadda tayi maganar, nan yace "No i won't."

"Nidai wallahi kawai so kake kayimin wayo" ta faɗa kamar zatayi kuka.

"Baby please."

"Ai bakasan zafin haihuwar bane shiyasa kake faɗan haka."

"But that isn't a big deal."

"Haihuwar?."

Hancin sa ya manna kan gashin ta yace "Yeah."

Shiru tayi masa tana turo baki gaba.

"Baby please" ya sake faɗa kamar wanda zaiyi kuka.

Juyowa tayi tana fuskantar sa har numfashin su na gauruwa tace "But be easy on me please."

Murmushi yayi cike da farin ciki yace "I will Babe."

Labari ne ya shiga canzawa tsakanin su, nan naja yam legs ɗina na baro musu ɗakin bayan na yiwa little ZEEYAD good night tare da gargaɗin sa kada ya farka daga baccin da yake ɗin.


********************

______Zaune duk suke a dining ɗin mai Martaba suna breakfast wanda DEENAH da JALILAH ne suka girka shi na musamman harda YAZEED ɗin da yaƙi zaman asibitin a cewar sa yafison ya gansa cikin family ɗinsa, hatta Nazeerah ba'a barta a baya ba.

Fuskar kowa ka gani a cikin su ɗauke yake da farin cikin da baki ba zai iya misalta shi ba.

Duk motsin da DEENAH tayi idanun ZEEYAD na yawo akanta, tamkar ya ɗauke ta ya cinƴe koh irin abin da yakeji game da ita zai ragu haka yakeji.

Serving abincin suka gama yiwa kowa kafin duk su sami wuri su zauna.

Riƙo hannun ta ZEEYAD yayi cikin nashi nan tayi saurin janƴewa tana ƙirƙiro murmushin yaƙe.

Sake kai hannu yayi yana riƙo ta gam, ɗan satar kallon sa tayi taga ma hankalin sa baya kanta, ita tsoron ta a gaban mai Martaba suke ga kuma Grandma da sauran mutane idan wani ya gansu fah.

Take ƴan yatsun ƙafar sa tayi da ƙarfi, nan ya cika ta yana faɗin "Ouch."

Duk kallon sa sukayi nan ya ƙirƙiro murmushin yaƙe yace "Abincin ne da zafi."

Kujerar sa yaja daf kusa da DEENAH, yana sanƴa hannayen sa round her waist.

Cire hannun nasa tayi tana buge hannun.

Ganin yadda suke ta mutsu-mutsu ne ya sanƴa Grandma cewar "DEENAH, i need more sausages please."

Da sauri DEENAH ta miƙe tace "Yeah sure, bari na ƙaro miki" ta faɗa tana yin hanƴar kitchen ɗin.

Kallon abincin gaban sa da bai fara ci ba yayi yace "Ahm... i guess i need more salad on this" ya faɗa yana ɗaukar plate ɗin ya mara mata baya da sauri dan kar ma wani daga cikin su ya tsaida shi.

Da kallo Grandma ta bisa kafin ta girgiza kanta.

Tsaye ya ganta a kitchen ɗin wanda bata ma san da shigowar sa ba, tiptoeing ya fara kamar wani 6arawo dan kar ma tasan ya biyo ta.

DEENAH ƙamshin turaren sa da taji ne ya tabbatar mata da cewar ya biyo ta ne, kafin tayi wani yunƙuri kuwa sai ji tayi ya rungumo ta ta baya yana saƙala kansa ta wuyar ta.

Serving spoon ɗin hannun ta ya kar6a ya ajiye kafin ya juyo da ita yana kallon ta, sunkuyar da kansa yayi kafin ya shiga bata wani irin cool kiss a lips.

Dukan bayan sa DEENAH ta shiga yi tana son kwacewa amma yaƙi sake ta, tsoron ta kada wani yazo ya same su a haka tasan ita zai tarawa abin kunƴa shi kuma koh a kwalar rigar sa.

Gajiya tayi da dukan bayan nasa ganin yaƙi ɗagowa, sai da ya gama sanƴaƴa mata jiki kafin ya ɗago yana kallon ta, gira ɗaya ya ɗaga mata yana yi mata murmushi.

Tsuke baki tayi tana barin wurin ta shiga haɗa Sausage ɗin da Grandma tace ta kawo mata akan plate.

Bin ta yayi yana sake riƙo ta, "Abyad please, what if aka ga mun daɗe fah?."

Ɗan ta6e baki yayi yace "Sai nace musu i was just romancing you."

Kai ta girgiza tana zuba sausage ɗin akan plate, sake riƙo ta yayi yana bata wani kiss ɗin, da kyar ta iya kwacewa cikin sanƴin jiki tana ture shi gefe.

Saita nutsuwar ta tayi kafin ta ɗau plate ɗin tayi saurin ficewa.

Da kallo yabi ta yana cize lips ɗinsa, huci ya fesar kafin ya ɗau plate ɗin abincin sa yana mara mata baya, sam bai ƙi su dauwama har abada a wannan yanayin ba.

Fuska ba walwala yazo ya zauna, kallon sa Grandma tayi kafin tace "And where is the salad?."

Kame-kame ya fara yana kallon abincin gaban nasa, nan Grandma tace "Ba ga Salad ɗin a gaban ka kuma kaje kitchen neman sa."

Haɗa ido yayi da YAZEED dake yi masa kallon tuhuma nan ya saki murmushi yana buɗe silver bowl ɗin salad ɗin, dukda kuwa akwai akan abin nasa haka nan ya sake loda wani, DEENAH kuwa dariya take ƙasa-ƙasa ganin yadda yake loda salad ɗin.

"Ya isa haka nan mana kodai kai kaɗai ne zaka cinƴe duka?" cewar Grandma.

"Ohh" ya faɗa yana rage ta a ciki kafin ya maida bowl ɗin ya rufe.

Tusa abincin kawai yake amma ba wai dan yanajin ƴunwar sosai bane ba.

Hayaniya da ifface-ifface suka fara jiyowa daga bakin ƙofa nan duk suka saurara kan kace miye kuma ta bangajo ƙofar ta shigo.

Duk miƙewa tsaye sukayi, cike da mugun 6acin rai sarki yace "Wane mai ganganci da aikin sa ne ya bar wannan matar ta shigo min cikin fada?."

Da gudu guards ɗin suka ƙaraso suna rissinawa, ɗaya ne yace "Ka gafarce mu ranka ya daɗe, ba a son ranmu ta shigo ba."

Kallon Hafeezah dake tsaye ta saki baki da hanci tana kallon ZEEYAD da YAZEED yayi kafin cikin 6acin rai yace "Mai ya kawo ki nan, get her out of my sight."

Kai ta shiga girgizawa idanun ta akan ZEEYAD take faɗin "No... no... how could this be, how could you be alive... i killed you... na kashe ka baikamata ace kana raye ba bayan na tabbatar da cewa ka mutu, you can't be alive" ta faɗa cike da tashin hankali tana kallon sa idanun ta kamar zasu zubo.

Duk ja kowa yayi yana kallon ta jin abinda take faɗi, kallon inda YAZEED ke tsaye da sandar dake taimaka masa wurin tafiya tayi kafin ta nufi wurin sa da sauri tana kamo fuskar sa "Oh my lovely Boy, ka gafarce ni dan Allah, ka gafarci mahaifiyar ka am glad you're still alive, thank GOD."

Idanun YAZEED ne ke fidda tsantsar 6acin rai wanda kana gani kasan daga ƙasan zuciyar sa take fitowa tunda yaji abinda mahaifiyar tasa ta ambata.

Kamar wacce aka tsikara kuma ta shiga waige-waige tana faɗin "Ayaan, ina Ayaan ɗina?."

Bata ankara ba taji an fizgo ta tare da ɗauke ta da wani irin azababben marin da ya sanƴa ganin ta ɗaukewa na wucin gadi.

Dafe ƙunci tayi tana kallon mai Martaba dake tsaye ransa tayi mummunar 6acin rai, cikin kakkausar murya yake faɗin "So you're the one Hafeezah?, kece kike bibiyar rayuwar yaron nan..."

Bai ƙarasar ba ta katse shi da faɗin "Eh nice, nice nake bibiyar rayuwar sa and i won't stop at nothing har sai naga bayan shi kamar yadda naga bayan mahaifiyar sa daga shi har matar sa da abinda ta haifa..." shiru tayi tana waro idanun ta da sukayi jaa ganin yadda ta saki layi a zancen nata tsabar baƙin zuciya irin tata.

"What?..." cewar Grandma da wani irin shock ya ziyarce ta lokaci guda bama ita kaɗai ba kowa na wannan wurin sai da ya tsinci kansa cikin wata iriyar shock da kiɗimewa wanda basu ta6a tsintar kansu ciki ba musamman ma YAZEED da yaji tamkar an raɗa masa wani irin makeken dutse akai, ZEEYAD kuwa jin sa da hankalin sa ne suka bar jikin sa na wucin gadi musamman yadda yake ganin ɗakin na mugun juya masa wani irin abu na dukan tsakar kansa, a takaice dai halin da ya tsinci kansa ciki ba zai misaltu ba.

Mai Martaba ma hakan take a wurin sa koh da ƴar yatsar sa ya kasa motsawa bale ya buɗi bakin sa yace zaiyi magana, sosai yakejin kansa dama kuma harshen sa sunyi masa mugun nauyi, nauyin da ya rasa yadda zai fara kwatanta wa.

A haukace ta iyo kan ZEEYAD da yayi tsaye tamkar gunki tana cakumo kwalar rigar sa take faɗin "Ka zame min ciwon ido tun kafin kazo duniya, dukkanin wani abu dake faruwa yanzu ba laifin kowa bane face na mahaifin ku wanda ya ɗauki so da ƙaunar duniya ya ɗaurawa LATEEFAT haka ma ya ɗau soyayyar sa ya ɗaura maka tun kafin kazo duniya, a kullum bashida magana da ya wuce na QUEEN MOTHER, duk wani ƙiyayya da ƙuncin rayuwar da ka tsinci kanka a ciki ya faru ne duka sanadiyyar mahaifin ka da ya fifita mata ɗaya cikin duka matan sa, wannan ne dalilin da ya sanƴa ni jin tsanar mahaifiyar ka har nake harin rayuwar ta ta mutu kowa ma ya huta, sai dai na sake wayar gari da wani mummunar labarin da ya sake hura min wutar tsanan ta dama kuma kai lokacin da naji tana ɗauke da cikin ka, nayi dukkanin iya ƙoƙari na na ganin baka zo duniyar ba dukda nima lokacin ina ɗauke da cikin amma hakan yaci tura, Yes nice nan na kashe mahaifiyar ka ta hanƴar sanƴa boka na ya ɗaura mata ciwon da koh da anyi magani ba zata warke ba sannan ba wanda zai zargi asiri ne akayi mata, yayin da kai kuma nayi dukkanin shige da ficen da zanyi na ganin na ɗaurawa mahaifin ka dama kuma dukkanin kowa dake wannan gidan tsanar ka sabida nayi-nayi ka mutu ka ƙi mutuwa hakan ya sanƴa ni ɗaukar alwashin sai na wulaƙantar da kai ka zamto koh da bayin gidan ku sun fika gata sannan nayi nasarar hakan, tafiyar ka ya sanƴa asirin da nayi karyewa har mahaifin ka ya shiga neman ka ruwa a jalo, raina ya sake 6aci ne bayan dawowar ka cikin MASARAUTA dama kuma yadda ka zamto mai kuɗin da ban ta6a tsanmani ba, nayi shige da fice dayawa akanka amma duk a banza, ina yi maka tsanar da ban ta6a yiwa wani mahaluƙi a wannan duniyar ba sannan har na mutu ba zan bar yi maka wannan ƙiyayyar ba, ya zama dole ne ka mutu daga kai har iyalan ka, dole ku mutu koh da kunƙi" ta faɗa tana jijjiga shi kamar wata zautacciya.

Tunda ta fara magana ZEEYAD bai iya koh da motsa ƴar yatsar sa bane ba balle tasa ran zai tanka, sosai shock ɗin da ya shige sa yayi tasiri a jikin sa, sosai idanun sa suka kaɗa sukayi jazir yayin da zuciyar sa yakejin tana wani irin bleeding.

Kukan Grandma ne ya cika wurin fizgo Hafeezah tayi kafin ta shiga bata mari "Allah ya isa tsakani na dake Hafeezah ashe kece kika kashe min ƴata, mai tayi miki mai ta tsare miki, son zuciya da hassada ya sanƴa kika kashe ta kuma kike farautar ɗan da ta haifa dama matar sa da ɗansa suma ki kashe toh insha Allah kin gama yawo a duniyar nan, ya zama dole ne ki girbi abinda kika daɗe kina shukawa, miye ribar ki yanzu, ribar mai kikaci a aikata sharri cikin rayuwar ki Hafeezah,gashi nan ke da kanki kinzo kina tonawa kanki asiri, ai dama Allah ba zai ta6a barin ki ba, mutuwa ta tabbata akanki Hafeezah, a rayuwa sharri kaɗai kika maida abinci da shan ki dama kuma suturar ki, kaicon ka YAZEED bawan Allah bakayi dacen uwa ba kaga abinda uwar ka ta janƴowa kanta, Allah ne kaɗai yasan dalilin sa na jarabtar ka da uwa kamar Hafeezah yaron kirki ɗan albarka" ta ƙarashe tana goge hawayen fuskar ta da bakin mayafin jikin ta.

YAZEED komawa yayi ya zauna tare da sadda kansa dake barazanar tarwatse wa, wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga yi masa zarya jin kayan kunƴar da mahaifiyar sa ta aikata, sosai yake ƙarajin tsanar ta na ninkuwa cikin zuciyar sa, da wane irin ido zai dubi ɗan uwan sa, shi kaɗai yasan mai yakeji cikin zuciyar shi, ji yake tamkar zuciyar sa zata tarwatse, wani irin ciwon kai mai tsanani ne yaji ya kama shi gashi dama yanzu yake farfaɗowa daga rashin lafiyar da yake.

Saurin riƙo sa JALILAH tayi tanajin wani irin tausayin sa na ratsa dukkanin zuciyar ta, tabbas Allah ya jarabce shi, Allah ne kaɗai yasan irin halin da yake ciki sannan mai yakeji a yanzu.

Runtse idanun sa dake yi masa zugi ZEEYAD yayi, maganganun Hafeezah jinsu yake tamkar ana feshe zuciyar sa da tafasasshen ruwan zafi.

Mai Martaba zubewa yayi kan kujerar da yake dan kuwa idan ya cigaba da tsayuwa toh tabbas zai iya zubewa anan koh a ɗauki gawar sa ma.

Guards ɗin dake tsaye ne suka zo suka tafi da Hafeezah, dukda iriyar ihun sai ta kashe ZEEYAD da iyalan sa da take tana neman kwacewa basu sake ta ba.

Fadar ce ta ɗau shiru sai shessheƙar Grandma kawai akeji, DEENAH rasa nayi tayi tama rasa wurin wa zata fara zuwa tayi comforting, tsaye ita ɗinma tayi hawaye sun gama wanke mata fuska.

Da kyar ZEEYAD ya iya motsa ƙafar sa yaa fara tafiya dan barin cikin fadar.

Kallon sauran tayi kafin tayi saurin mara masa baya.

Ja tayi ta tsaya bakin ƙofar ɗakin su durƙushe ta ganshi kan guiwowin sa bayan sa take kallo kafin ta shiga takawa a hankali dukda kuwa tsoron tunkarar tasa take.

Zagayowa tayi gaban sa tana ta6a shi tare da kiran shi a hankali "Abyad?."

Ɗago da jajayen idanun sa da suka ƙanƙance yayi yana zuba mata su kamar jira yake ta shigo ya rungume ta sosai yana runtse idanun sa, sosai takejin yadda zuciyar sa ke gudu da sauri-sauri kamar zata 6allo ƙirjin sa ta fito, sake ƙanƙame shi tayi a jikin ta wani irin tausayin sa na ratsa zuciyar ta, a hankali take hura masa iskan bakin ta a kunne tana patting bayan sa gently dan ganin ya sauƙo daga fushin da yake ciki.

Hawayen da yayi shekaru da shekaru yana jiran fitowar su ne suka shiga yi masa zarya a fuska yana sake ƙanƙame DEENAH, sosai jikin sa ke rawa zuciyar sa na sake yi masa zafi, sun jima a haka ƙanƙame da juna har izuwa lokacin da taji gudun zuciyar tasa ta sassauta.

Lumshe idanu tayi tana cigaba da

Please Login or Register in order to submit comment