Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sallah sannan akwai masu saida ruwa a wurin."



Kai ya jinjina yace "Nagode" kafin ya juya yabi hanƴar da mutumin ya nuna masa.



Wuri ya samu ya zauna sai a sannan ya buɗe jakar da Sadeeq ya basa, kaya ne kala biyu a ciki, sai su bread da biscuits sai kuma ruwan gora, ruwa ɗaya ya ciro kafin ya maida zip ɗin jakar ya rufe.



Wurin da aka ware kamar banɗaki ya gani nan yaje yayo tsarki kafin ya dawo ya ɗaura alwala sannan yayi sallah, Hannun sa ya ɗaga sama tare da kwararo addu'o'i sosai sannan ya miƙe ya ɗau jakar sa ya koma ciki inda ya fito.


Matashi yayi da jakar tasa ya kwanta, dan kuwa ba ƙaramin bacci yakeji ba, da tunanen da bai san ranar yankewar su ba bacci ta kwashe shi.


*************


..........Bai farka ba sai da rana tayi lokacin kuwa har jirgin ya tashi yayi nesa da fara tafiya, fita ya sakeyi yayi alwala yayi sallah.



Bai komo ciki ba sai ma samun ƙarafunan jirgin da yayi ya riƙe yana kallon ƙatuwar ruwan dama kuma yadda jirgin ke zuba uban gudu a kanta.



Ya jima sosai anan har akayi sallahr La'asar yayi, a takaice dai anan wurin ya wuni har dare kafin ya koma cikin ɗaki.



Kasancewar ya fara jin ƴunwa ya sashi buɗe jakar sa ya ɗauko biscuit guda ɗaya ya buɗe ta ya fara ci,sannan ya kora da ruwa a kai.



He was so very emotional and lonely hakan yasa wasu hawayen da bai san da zuwar su ba shiga sauƙo masa, kansa ya sunkuyar ba tare da ya iya controlling hawayen nasa ba, babu abinda yake tunawa sai mahaifiyar sa dama kuma irin rayuwar da sukayi a baya harda Abhi ɗinsa dake tsananin ƙaunar sa amma daga baya kuma shine wanda yafi tsana wanda har ganin sa baya son yi.



"Kai ɗan saurayi" yaji an faɗi hakan.


Ɗagowa yayi nan yaji ɗaya yace "Ka dame mu fah da shessheƙa bakaga bacci muke yi bane?."



"Kuyi haƙuri" kawai ya faɗa yana maida kansa.



Sati ɗaya ya wuce sai dai har yanzu basu iso inda zasu ɗin ba, inda kowa da ka gani a cikin wannan jirgi toh fah rayuwar sa yake cikin kwanciyar hankali sa6anin ZEEYAD da kullum yake cikin ƙunci tare da rashin walwala, ga kuma kayan abincin sa da ya fara ƙarewa inda sau ɗaya kawai yake ci a rana ba zai sake ci ba sai washe gari duk dan gudun kada ta ƙare ya rasa na ci wataran, ga kuma yanayin yadda yaga mutanen cikin jirgin kowa na harkar gaban sa ne, babu wanda yakeyi wa ɗan uwan sa tayin abin ci koh sha, kowa rayuwar sa yake.



A haka rayuwa ta cigaba wa ZEEYAD a cikin wannan jirgi, yau lafiya gobe babu lafiya har Allah yasa suka iso ƙasar Nigeria.



Mutane ne yaji sun fara shewar "an iso, an iso, kowa ya adana kayan sa sannan ya 6oye kuɗaɗen sa."



ZEEYAD da ya zamto ɗan kallo babu abinda ya fahimta, tafiya kaɗan jirgin tayi ta sauƙa a bakin ƙaton tekun ɗin.


Mintina goma da tsayuwar ta mutane suka fara kokuwar fitowa sai a sannan yaga adadin cunkoson mutanen dake cikin wannan jirgi.


"Kowa ya kula da dukiyar sa" yaji ana faɗa hakan yasa shi damƙe jakar sa a hammata.



Sosai ya zama soko a wannan wuri inda kowa sai bangaje shi yake yana ficewar sa.


A haka shima ya samu ya kutsa kansa cikin mutanen dukda kuwa irin ture sa da akeyi, a hankali yaji kamar ana jan jakar hannun sa ta baya, mamaki ne ya cika shi nan ya sake damƙe ta a hannu.


Ihun wata tsohuwa ya jiyo tana faɗin an kwace mata jakar kuɗin ta, babu wanda ya kula ta sai ma baki da kowa ke turowa yana yin gaba abinsa.



Ratsawa yayi cikin mutane zuwa gun wannan tsohuwa ganin mutane sun jefar ta sai tattaka ta akeyi.


Hannu ya kai da shirin ɗagota, aikuwa caraff ta kamo hannun nasa tana ihun "Ga shi nan ga 6arawon da ya ɗauke min jakar kuɗi ta, yau Allah ya kama ka, dama kune masu yiwa mutane sata ai, Allah ya kama ka yau" ta ƙarashe cikin kuka.



ZEEYAD ba ƙaramin mamaki yaci ba ganin tsohuwar nan na neman ɗaura masa sharri alhalin babu abinda ya aikata.



Fuzge hannun sa yayi daga riƙon da tayi masa ɗin, ganin kowa na wucewa cikin sauri bai saurare ta ba yasa shi shima jan baya da ita yana kallon ta, ƙarshe dai nan ya baro ta sai kukan 6atan kuɗin ta take yayi gaba.



Fitowa yayi daga cikin jirgin inda wani iska mai daɗi ya huro shi wanda ya sanƴa sa lumshe idanun sa, yayin da kuma tsikar jikin sa ya shiga tashi yana feeling so nervous wanda da kyar ya iya taka ƙafarsa ya fara tafiya yana bin mutanen wannan wuri da kallo kamar ɗan ƙauye.



Bakin tekun ɗin haka yake kamar wani kasuwa mutane kala-kala, ga kuma wasu yellow ɗin Vans zuzzube dayawa duk sunji jiki sunji duniya inda kuma suke ta ihun neman passengers ɗinda zasuyi cikin gari dasu.



"Central Market, Central Market, Central Market" shine yaji wani baƙin mutumi yana faɗa, inda ya zamto mummuna a idanun ZEEYAD ya tsaya yana ƙarewa wagegen bakin mutumin dake ta nanata" Central market" kallo dan kuwa karon sa na farko kenan da ya kalli baƙar fata sai dai fah dukda haka yaga na wannan mutumin ya bambamta da na saura, hakan yasa kansa ƙullewa ganin dai gasu nan dukkanin su baƙaƙe za'a kira su amma kowane da kallar baƙin sa masu haske ɗaɗɗaya yake gani.



Kallon ZEEYAD da ya saki idanu yana kallon sa yayi yace "White Broda how far na, where u wan go?."



Kai kawai ZEEYAD ya Jinjina masa dan kuwa idan ba "How far?" ba babu abinda ya gane cikin maganar sa sauran duk baiji ba kasancewar yadda yayi maganar cikin muryar ƴan shaye-shaye.



Gaba yayi yana ta kalle-kalle ba tare da ya san inda yake sanƴa ƙafafuwan sa ba, in banda kallon mutane babu abinda yakeyi.



Ji yayi an bangaje shi ya faɗi, nan ya juya ya kalli lukutar matar da ɗuwawun ta kamar wadanda aka hura musu iska tana sanƴe cikin Mini skirt ɗinda ya tsaya mata a guiwa sai harɗe ƙafafu take tana tafiya, idanu ya zaro waje wondering koh ita ma mutum ce, dan kuwa bai ta6a ganin ƙatuwa irinta ba.



Haka nan ya miƙe tsaye tare da karkaɗe jikin sa yana kallon matar da tayi nisa sai dai bai bar kallon ta ba har yanzun dan kuwa mamaki yadda take iya tafiya ma yakeyi.



Haka nan ya cigaba da tafiya duk inda ya samu ya jefa ƙafarsa haka ya fito daga cikin mutane.



Nan kuma yaga ƴan acha6a birjik a gefe suma da alamun passengers suke nema.



Ji yayi an riƙo jakar sa ta baya nan yaga ana jansa ana faɗin "Where u wan go?, pay 500 naira i will take you everywhere you want in Lagos." yaji mutumin ya faɗa tare da amsar jakarsa yana Ɗaurawa kan mashin ɗin nasa.


Mamaki ne ya kama ZEEYAD nan yace "No, actually i don't have any money with me."



"Ahh bro u must be joking nah, keep joke aside na, as fine boy as u are, u no get money?" an european boy" ya faɗa yana washe haƙora.


"No am not from Europe" ya faɗa cikin sanƴi yana ƙoƙarin amsar jakar sa.



"Are u waiting for someone to pick u up?, this one that ur body dey fresh like dis i know u must be from a wealthy Family" ya faɗa cikin washe masa haƙora yana maida masa jakar sa.



Shiru kawai ZEEYAD yayi ya amshi abinsa tare da yin gaba, dan kuwa sam baya fahimtar turancin ɗan acha6ar nan.



Tafiya ya cigaba da yi nan yaji ana yi masa horn a bayan sa, ɗan acha6ar nan ne dai ya sake biyo sa,nan yace dashi "Are u a lost, where u wan go?, make i take u for free."



"For Free?" ZEEYAD ya tambaya yana kallon sa.



"Ehen na, oya be fast oo before dis stupid cops arrived."



Zuwa ZEEYAD yayi inda dakyar ya iya hawa machine ɗin dan kuwa bai saba ba, Hannun sa ya ɗaura a kafaɗar ɗan acha6ar gudun kada ya su6ule ya faɗi, nan ya tada ta suka hau tafiya.


"Broda, where u wan go na?."


"You mean, where i want to go?."


"Yes."


"Actually, i don't know."


Slowing down ɗan acha6ar yayi yace "U don't know?."



"Yes" ya basa amsa.



"Where are you from, which country are you from?."



Shiru yayi kafin kuma a hankali yace "Egypt."



"Ehnn, no wonder u look so handsome and fresh like fresh tomato" ya faɗa cikin dariya.



"So bro where should i take u now?" ɗan acha6ar ya sake faɗa.


"Anywhere" ya faɗa.



Kara gudun mashin ɗin yayi, tafiya mai nisan gaske sukayi kafin su fara shigowa cikin gari, da kallo ZEEYAD ke bin wuraren da kallo, ganin duk tsofaffin gine-gine sunfi yawa ga kuma saman langa-langar su da duk a kokkoɗe sunyi tsatsa, ga kuma wani uban traffic jam da aka haɗa akan hanƴa.


Sosai ɗan acha6ar nan ya cika shi da surutu, har suka iso inda zasuje yayi parking.



"Yauwa kaga nan garage ne na kawo ka, ba zaka rasa wurin kwana ba."


Rungume jakar sa yayi yace "Thank you so very much."


"Don't mind na, it's my pleasure to meet such a handsome guy like u and even have a Conversation with."


Ɗan murmusawa ZEEYAD yayi ba tare da yace dashi komai ba.


"Alright bro, good luck i pray we met somewhere again" ya faɗa cikin dariya yana jan Babur ɗinsa yayi gaba.



Da kallo ZEEYAD ya bi shi yana mamakin dama akwai mutanen kirki har haka, ya ɗauko shi daga wuri mai nisa sai dai koh biyar bai caje sa ba, inama ya ƙarashe guntun rayuwar sa cikin haɗuwa da ire-iren wannan ɗan acha6ar.



Kallo ya ƙarewa tashar motar , kafin kuma ya samu wuri daga gefe ya zauna yana bin mutane da kallo.



Kowa na harkar gaban sa, yayin da masu sayar da abinci da toye-toye suma na yin nasu.


Hango table ɗin wata inƴamura yayi plate ɗauke a hannun ta tana ɗebo farin shinkafa daga cikin kula sai fitar da tururi yake, ƴawu ya haɗiya lokacin da yaji cikin sa tayi wani irin ƙarar ƴunwa.



Rabon sa da ya sanƴa abinci a bakin sa kwana biyu kenan, miƙewa yayi daga inda yake zaune ya nufi wurin wannan mata.


Hango sa da tayi ne yasa ta washe haƙora tace "Ah ah Customer, welcome, u too fine oo ehnn,welcome" ta faɗa tana kallon sa.



"Hi" yace da ita.



"Hi, have a seat na, what do you want to buy?."



Murmushi yayi yace "Nothing...i...i am hungry pls help me with...."



Ai bai idda ba yaji ta daka masa wani irin tsawar da bai ta6a jinta ba tunda yake a rayuwar sa, hakan yasa shi jan baya da sauri.


"Help?, help my foot, help u with what?, abeg my friend get lost from here, are you the one that gave me the profit to start this business, idiot, abeg move ur dirty body away from here don't come and infect my food,broke white guy mtssswww," ta ƙarashe cikin jan doguwar tsaki kamar bakin ta zai faɗi ƙasa sai masifa take ta zubawa cikin yaren da baya fahimta.



Da sauri ya bar wurin yana danasanin sa na zuwa gashi a banza tayi disgracing ɗinsa gaban mutane kowa ya gane barar abinci yaje yi abinda bai ta6a ba, sosai yaji ciwon hakan, wuri ya samu ya zauna kawai yana cigaba da aikin kalle-kallen sa..............



*******************



.........."Your Highness, we have searched everywhere but the Prince is nowhere to be found" ya faɗa cike da girmamawa kansa duƙe a ƙasa.


Sosai Ran mai Martaba yayi mummunar 6aci jin labarin da ake kawo masa kullum tsawon sati biyu da 6acewar ZEEYAD.



"It's been two weeks now, sai dai har yanzu no one knows his whereabout, mun samu bayanan cewa tun lokacin da Sooraj ɗan wurin Abdulhakeem yazo da dakarun sa sukayi wa Yarima ZEEYAD dukan mutuwa tundaga ranar kuma ba'a sake ganin sa ba" ya sake faɗa cikin girmamawa.



Tashi tsaye mai Martaba yayi yace "Ku kawomin Abdulhakeem dama kuma Sooraj nan wurin, bama su kaɗai ba da dukkanin wasu dangi ku aika musu da cewa ina buƙatar su a fada yanzun nan, include the QUEEN'S" Ya ƙarashe cikin kakkausar murya idanun sa na yin jaa.



Duƙawa yayi cike da girmamawa sannan ya fice dan zuwa aiwatar da umarnin mai Martaba.



Mintina ashirin mai kyau fada ta cika Family kowanne zaune da iyalan sa a gefe wanda aƙalla zasu kai su biyar.



Da kallo mai Martaba ya bisu dukkanin su kafin kuma yace "Ɗa na Yarima ZEEYAD, yau sati biyu kenan da 6atar sa ba'a gansa ba, sannan rahoto yazo min cewa Sooraj ɗa ga Abdulhakeem shine wanda aka gansu tare ƙarshe ya sanƴa bayi sunyi masa duka, Sooraj" ya kiraye sa da ƙarfi yana aika masa da mugun kallo.


A razane Sooraj ya miƙe tsaye cike da girmamawa ya duƙa yace "Yes your Highness."


Shiru mai Martaba yayi kafin yace "A'ina ka kai min ɗa na?."


Kame-kame ya fara kafin yace "Wallahi ranka shi daɗe, tun lokacin da muka samu sa6ani dashi ban kuma sake sanƴa sa a idanu na ba, sabida na dai san lafiya ƙalau na...na taho na bar sa a wannan wurin" ya ƙarashe yana kallon Mahaifin sa.



Mai Martaba ne yace "Kada ka nemi ka raina min hankali mana, Abdulhakeem koh kasan da abinda ɗan ka ya aikatawa Yarima ZEEYAD?."


Tashi Abdulhakeem yayi yace "Kwarai kuwa ranka ya daɗe, dan kuwa nayi masa faɗa sosai akan hakan kuma yayi nadama yace ba zai sake ba, har ma nace ya koma yaje ya baiwa Yarima ZEEYAD haƙuri amma kuma sai ya dawomin da labarin cewa bai gansa ba ya bar wurin."



"Tayaya zaka yarda da ɗanka bayan kasan muguwar zuciya irin tasa, koh ka sani shine wanda yayi sanadiyyar 6acewar Yarima ZEEYAD sannan kuma ya 6oye maka gaskiya."



Cikin ruɗewa Sooraj ya fara faɗin "Abhi wallahi bansan komai kan 6acewar Yarima ZEEYAD ba, nidai nasan kawai nasa dogarai sunyi masa duka ne amma bayan nan kuma babu abinda ya sake shiga tsakani na dashi."



"Hafeezah!" cewar mai Martaba a tsawace.


Sarauniya Hafeezah da duk hankalin ta yayi gaba jin mai Martaba na kiran ZEEYAD da sunan ɗansa har ma da kiran sa Yarima yasa hankalin ta mugun tashi, a razane kuma ta ɗago tana kallon sa sabida yadda ya kira sunan nata.



"Ina ɗana?" ya faɗa yana kallon ta.


Cikin in-ina take faɗin "Bansaniba, bansan inda yake ba nayi maka rantsuwa da Allah babu abinda na sani game da 6atar sa."



Tsaye ya miƙe yana sarƙe hannaye a baya yace "Na baku nan da kwana ɗaya ku nemo inda ya shige, idan kuma baku aiwatar da hakan ba toh ina mai tabbatar muku da cewa sai kun fuskanci hukunci mai tsananin gaske" yana faɗin haka ya wuce fuuu tare da haurawa sama ya bar su nan zaune kowa da abinda ke gudana cikin zuciyar sa.



Murmushi Sarauniya Nazeerah ta saki dan kuwa ita babu abinda yafi burgeta face taga ana rigima,dan kuwa ita bata tsani kowa ba amma burin ta shine kullum ace rigima bata ƙarewa.


Sarauniya Hafeezah kuwa idanun ta yayi zuru-zuru,inda kuma take tunanin komawa wurin bokan ta dan kuwa taga kamar asirin ta na shirin tonuwa.



Sarauniya Naseeba kuwa ba ƙaramin tashin hankali da baƙin cikin 6acewar ZEEYAD ɗin take ba, dan kuwa bata samu ta aiwatar da burin ta akansa ba, sai dai fah bata cire rai ba komin daren daɗewa sai ta aiwatar da abinda tayi niya akansa.



Duka sauran miƙewa sukayi suna ficewa da Family ɗinsu ɗaya bayan ɗaya, kafin Abdulhakeem ma ya tashi suka fice da nasa iyalan.


Kallon Sarauniya Hafeezah Nazeerah tayi tace "Uhm, idanu sun raina fata yau Hafeezah, da alamu kamar muguwar ƙullin ki na shirin warware wa koh?."



Tsaki taja tana miƙewa tsaye ta fice kamar zata tashi sama.


Da kallo ta bita tana murmushi kafin kuma ta dawo da idanun ta kan Naseeba, murmushi ta sakar mata tace "Ke kuma fah, kina kewar masoyin naki ne?, sai ki bada himma wurin gano inda ya shige."


Kamar zatayi kuka haka nan ta tashi itama tana ficewa ba tare da ta tanka Nazeerah ba.


"Wow! Wow!! Wow!!!, inajin daɗin wannan drama sosai da sosai, dukkanin su sun ɗaurawa kansu babban aiki, basu san da cewa dukkanin abinda suke aikatawa mai Martaba na sane ba kawai kyale su yake yaga iya gudun ruwan su, mahaukatan banza da wofi, yanzu kuma da suka kai sa maƙura bari muga mai zai aiwatar akai dan kuwa da alamun yanzu aka fara wasan, yayin da nikuma zan zama ƴar kallo" ta ƙarashe cikin murmushi mai cike da jindaɗi.............



**********


.........."Tsaye yake gaban tafkeken hoton ta yana kallo inda kuma hawaye suka shiga yi masa zarya a kan fuska.


"Lateefat, Haƙiƙa naci amanar ki, ban kula da amanar da kika barmin ba, na gaza kula da ɗa kwaya ɗayan da kika bari,na ruguza masa rayuwar sa dama kuma mafarkin sa, bana ta6a tunanin zai iya yafemin, Hafeezah tayi nasarar raba ni dashi, Haƙiƙa ina matuƙar ƙaunar ZEEYAD fiye da kowa, sai dai nazo na wayi gari babu shi babu labarin sa, sai a sannan ne kuma hankali na ya dawo, bayan ɗa mafi soyuwa a gareni yayi nisa dani, bayan sunyi nasarar cusa masa tsana ta a zuciyar sa, bana tunanin zan yafewa ɗaya daga cikin su akan abinda suka aikata.".............



*Idan kin karanta kiyi sharing sabida ƙaunar Allah da Manzon sa👏🏽*





*MHIZZ JIDDHERR...........✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*





*008...*




_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._




..........Haka nan yayi ta zama a wannan wuri shi kaɗai inda kuma yake bin kowanne mahaluƙi da yazo wucewa da idanu.


Sosai ya jigata da ƴunwa wannan karon dan kuwa ga abinci nan na saidawa yana gani amma babu damar ci, dan kuwa ya lura ma da cewa mutanen wannan tasha kamar ɗabi'ar su ce masifa da faɗa, dan kuwa a ɗan zaman san nan anyi faɗa a gaban shi ya kai sau shida, ga kuma ƴan shaye-shaye da bushe-bushe nan birjik abin ba'a cewa komai.


Tashi yayi da jakar sa a hannu ya fice daga tashar.


Tafiya mai nisan gaske yayi kafin ya samu gindin wata ƙatuwar bishiya ya zauna.


Jakarsa ya ajiye anan tare da ɗaura kansa akai kan kace miye kuma baccin wahala ta kwashe shi.


Sosai ya sha bacci kafin ya farka, dube-dube ya hau yi ganin babu jakar sa babu alamun ta.


Tashi yayi tsaye yana duddubawa har bayan bishiyar ya zaga babu an sace.


"It was Stolen" ya faɗa kamar zaiyi kuka.


Da sauri kuma ya kai Hannu kan wuyar sa nan dai yaji sarƙar tasa na nan, wata iriyar ajiyar zuciya ya sauƙe tare da furta "Alhamdulillah" yana maida ta cikin rigar sa, kafin kuma ya hau tafiya yana barin wurin...........



*THREE WEEKS LATER*


........Rayuwa a haka tayi ta tafiyar wa ZEEYAD cike da wahala da ƙunci.


Dakyar yake samun na ci da sha balle kuma na wankan tsaftace jikin shi.


Duk inda ya shiga kowa tsangwamar sa da hantarar sa yake, musamman yarbawa da inƴamuran nan masu shegen masifa kamar saci kai.


Da kyar da ikon Allah ya samu wani local Restaurant inda wata mata ke saida abinci yana yi mata wanke-wanke inda ita kuma take biyan sa da abinci, a takaice dai ya zama ɗan aiken ta dan kuwa shi ke serving customers abinci ma yana kai musu idan sun zo saya koh ci.


Yau ma zaune yake yana wanke plates ɗinda akaci abinci dashi sabida sunyi ƙaranci sai an wanke kafin a samu na sanƴawa wasu abinci.


Bayan ya wanke ne ya ɗauka ya kai yana miƙa mata cike da girmamawa.


Amsa tayi cike da masifar baya sauri sai ya kora mata customers ta fara zuba abincin kan ta miƙa masa ya kai.


Cikin ɗan ɗakin da aka ware na zaman customers ya shiga tare da nufar teburin wanda akace ya kaiwa abincin.


Samun mutumin yayi zaune yana waya inda kuma yake ta kyakyata dariya da alamun dai wani abin ake faɗa masa a wayar.


Ajiye masa abincin ZEEYAD yayi sannan yaje ya ɗauko masa ruwan pure water guda ɗaya ya ajiye masa yana shirin ficewa ne wannan mutumin ya yafito shi da hannun sa kan ya tsaya.


Tsayuwa yayi jiran sa inda shi kuma ya cigaba da wayar sa yana kyakyata dariya ga kuma abinci da ya sanƴa a gaba yana ci.


Da kallo kawai ZEEYAD ke binsa ganin ya barsa tsaye shi bai ce masa komai ba, sannan kuma bai barsa ya tafi ba.


Har saida ya kusa idda cin abincin kafin uwargijiyar ZEEYAD ta shigo ciki kafin kuma ta hau balbale sa da masifar ya shanƴa ta a waje bai zo ya baiwa sauran customers abinci ba "So kake ka kora min customers su daina zuwa wuri na kalan ma suce ba'a kar6ar su yadda yakamata, ni banma san uwar miye da tsautsayin da ya kai ni ɗaukar ka aiki ba dallah wuce kaje ka wanke min plates mutane na jira" ta ƙarashe tana aika masa da muguwar kallo.


Wannan mutumin kuwa da kallo kawai yake bin su bai ce komai ba yana cigaba da wayar sa da cin abincin sa.

"But he asked me to wait" ya faɗa.


"Zaka wuce ne kokuwa sai raina ya 6aci?."


Wucewa yayi yana mamakin wai a hakan ma ranta bai 6aci ba kenan da wannan uban masifar da ta rufe shi.


Fitowa tayi kamar zata tashi sama dan masifa ta hau aikace-aikacen ta.


Da kallo yabi mutumin da ya fito yana biyan matar kuɗin ta kamar baya so sannan yayi gaba yana jin kamar ya bishi ya rufe shi da duka dan haushi.


A haka har dare kafin ta sallame sa da naira ɗari biyu tace "Yau ka 6ata min rai shiyasa ba zan baka ɗari uku ba, ina mai tabbatar maka idan ka sake ka kuma 6ata min rai zan daina ma baka abincin baki ɗaya da tukwuicin aikin" ta faɗa tana wani yayyatsina fuska.


Amsa yayi ba tare da ya raina ba yayi godiya yana sanƴawa cikin aljihun sa kafin yayi mata sai da safe ya wuce.


Tsinkayo muryar ta yayi tana faɗin "Ka tabbatar fah gobe ka fito dawuri sabida kasan akwai share-share da gyare-gyaren da zakayi koh?."


Kai ya jinjina mata yana wucewar sa.


Gidan wani wanka ya biya ya biya kuɗi yayi wanka da wasu ƴan buƙatun sa kafin ya wuce inda yake kwana.


Rumfar wani mai shayi ne yake zuwa ya kwana inda yake biyan sa naira ɗari kullum kuɗin kwana.


A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar masa a garin na Lagos wanda babu laifi ya ɗan tara kuɗaɗen sa, sannan kuma duk wani aiki idan ya samu na ƙarfi Wanda za'a biya sa yin abinsa yake, a haka har ya fara ganewa da yanayin rayuwar Lagos ɗin ya rage shan wahala kamar dah.


Cikin kuɗaɗen da ya ɗan tara ne yaje kasuwa ya ɗan sayi kayan sawa da ɗan abubuwan da ba'a rasa ba na amfanin shi.


Wata rana yana zaune Shi kaɗai kasance matar da yake mata aiki ta daɗe da korar sa hakan yasa yake shan wahalar samun wani aikin kuɗin.


Aljihun sa ya duba ya ciro ƴan kuɗaɗen sa dake ciki tare da ƙirga su, dubu ɗaya ce da ɗari uku da hamsin ta rage masa a hannu.


Tunani yake tayi dan kuwa indai bai sami wani aikin ba, babu inda zai dinga samun kuɗin biyar wurin kwana indai wadannan na hannun sa suka ƙare.


Miƙewa yayi dan kuwa yau yayi alƙawarin sai ya samu wani aikin yi ɗin.


Sosai yayi yawo sai dai babu abinda ya samu, wuri ya samu ya zauna

Please Login or Register in order to submit comment