Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da rayuwar nan sai ni, sun kwace komai daga gareni, but dukda haka nayi ƙoƙarin kula da sarƙar da Ummie ta bani na ganin banyi missing nashi ba, na fara rayuwa kamar ta almajirai ne a cikin gidan uba na tun inada shekaru goma sha ɗaya, no one cares about me sannan kuma babu wanda ya ta6a yunƙurin kawomin ɗauki, after family ɗin mahaifiya ta sunji labarin halin da nake ciki sun yanke shawarar ɗauka na su tafi dani, but that selfish and disgusting Man ya hana su yin hakan sannan kuma ya yanke duk wata alaƙar dake tsakani na dasu, he took everything away from me, ya nesan ta ni da dukkanin wani abin da zai sanƴa ni jin farin ciki a rayuwa, hakan yasa nayi deciding barin masa ƙasar, am sure yana chan yana rayuwar sa happily da mutanen da yafi so, he wants me out of his sight, and i decided to stay out of his life for good, ba zan iya cigaba da baka labari ba sabida hakan bakomai yake ƙaramin ba sai tsanar sa, i just hate him like hell" ya faɗa cikin zafin zuciya fuskar sa na yin jawur jijiyoyin nan duk sun bayyano raɗo-raɗo a jikin shi wanda da alamu dai ba ƙaramin tsanar mahaifin nasa yayi ba.


Wata iriyar nannauyar ajiyar zuciya Daddy ya sauƙe cike da tausayin ZEEYAD, dan kuwa shi tunda yake bai ta6a jin wai Sarkin da yaƙi jinin sa ba, he can't believe irin rayuwar da ya tarar da ZEEYAD a ciki ya zamto ɗan sarki ne hakan, Sarkin ma ba na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya ba, na chan ƙasar Cairo, dukda dai yana zargin da akwai sa hannu a cikin wannan lamari sai dai ZEEYAD ɗin baisan da hakan ba, duba da yadda tun yana ƙarami mahaifin nasa ya taso dashi cikin wannan halin.

"ZEEYAD haƙiƙa ka bani tausayi, but tell me one thing yaushe ne ka yanke zaka koma ƙasar ka u haihuwa?."

Shiru yayi kafin kuma yace "Ba yanzu ba tukun, ba zan iya tafiya na bar MADEENAH cikin halin nan ba."

"Amma ZEEYAD baka ganin lokaci yayi da yakamata ace ka koma, kasan fah da zafi-zafi ake dukan ƙarfe, yakamata ace ka koma yanzu ka san wane irin hali mahaifin ka ke ciki dama kuma abokin ka da family ɗinsa."

"Who even cares about that Man, i don't care if he dies, abu ɗaya ne zai maida ni Egypt shi ne Family ɗin Sadeeq, and koh da zan koma wurin su ba mulki ne zai kai ni ba, i just wants to show them how far i have made it in life."


"ZEEYAD yaci ace yanzu zuciyar ka tayi sanƴi game da tsanar mahaifin ka da kayi..."

"No, zuciya ta ba zata ta6a yin sanƴi ba until na ɗau fansar abinda yayi min."

"ZEEYAD..."

"Am sorry to said this father but babu abinda zaka faɗa da zaiyi conviencing ɗina koh ya sanƴaƴa min zuciya akan wancan mutumin" ya faɗa yana miƙewa tsaye.


Miƙewa tsaye shima Daddy ɗin yayi yana takowa wurin ZEEYAD ya dafa kafaɗar shi yace "ZEEYAD nasan ba zan iya hana ka aiwatar da abinda kakeso ba muddin hakan ne zai sanƴaƴa maka zuciya, but kada ka manta cewa Uba komin laifin da zai aikata a rayuwa ba zaka iya canza shi daga matsayin mahaifin ka ba, koh da kuwa shi ya kawo ta'addanci da mugunta duniya babu yadda za'a yi ka iya canza shi daga matsayin Uban da ya haife ka, koh da kuwa ya kasance shi ɗin Mahaukaci ne he still remains your father, koh bakomai kai ya soka lokacin da mahaifiyar ka ke raye, dan haka kayi tunani tare da binciken abinda ya sanƴa shi canza hallayyar sa akanka na komawa mutumin da yafi kowa tsanar ka, Think about it ZEEYAD" yana faɗin haka ya fice daga cikin falon ya bar ZEEYAD tsaye.

Da kallo ZEEYAD ya bishi dan kuwa koh kaɗan maganar da Daddy yayi bata ta6a sa ba, ficewa yayi shima dan kuwa har ya fara kewar DEENAH.


******************


Asibitin ya dawo Umma da Jafar ne kaɗai ɗakin.

Gaida Umma yayi ta amsa ba yabo ba fallasa kafin ya sami wuri kusa da Jafar ya zauna.

Kallon sa Jafar yayi cikin ƙasa da murya yace "Har ka dawo?."

Kai ya jinjina masa, nan ya sake cewa "Am sorry to say, amma dai ba wannan mahaukaciyar yarinƴar zaka aura ba koh?."


Kallon DEENAH ZEEYAD yayi kafin yace "Are you trying to call your own sister Mad?."


"No, thats not what i mean, that rude girl da tazo nan da mutumin da kuka fita tare."

"Ohh" ya faɗa cikin yatsina fuska.

"Ita ce?."

"Yeah" ya faɗa kai tsaye.

"Na taya ka murna da mahaifin nata yace ya fasa auren ka da ita, sabida the girl doesn't seem normal to me."

Murmushin kan le6e yayi kawai ba tare da yace komai ba.

Muryar Umma suka tsinkayo tana faɗin "Jafar ni zan wuce gida ɗauro girkin dare, ka kula da ƙanwar taka koh?."


"Toh Umma bakomai, sai kin dawo."

Jakar ta ta ɗauka kawai ta fice daga ɗakin cikin sanƴin jiki.


Tashi Jafar yayi ya koma kusada da DEENAH ya zauna yana kallon ta.

"DEENAH, why don't you just try very hard ganin kin motsa koh da idanun ki ne, though nasan kullum kina iya ƙoƙarin ki na ganin kinyi hakan amma yaci tura, but you have to try very harder DEENAH, am just sick of seeing you in this condition" ya faɗa yana kamo hannun ta.


Kallon su kawai ZEEYAD keyi, but shima ganin DEENAH a hakan ba ƙaramin takurawa zuciyar sa yake ba, ita ba statue ba then atleast yakamata ace ta motsa koh da idanun ta ne.


Kallon cikin idanun ta dake saitin sa yayi yanajin zuciyar sa na yi masa zafi sosai.

Kauda idanun sa yayi daga kallon ta kafin kuma ya tashi ya fice daga ɗakin.


Three Months kenan DEENAH bata warke ba har yanzun, sai ma abinda ya ƙara gaba akan ciwon nata.

Zaune yake a office ɗin Doctor ɗin dake yi masa bayani akan rashin lafiyar DEENAH.

"The best solution is a fitar da ita waje kamar yadda na faɗa maka, coz her condition is getting more worse day after day, inda kuma zan tura ku yanzu sun fi mu kayayyakin aiki, and suna da expert doctors da suka kware ta wannan fannin sosai."


Kai ya jinjina masa kafin yace "Tell me, where is that place?."


"Cairo(Egypt), da akwai wani kwararren likita da zan haɗa ka dashi, am definitely sure indai kukaje chan then cikin ikon Allah zata samu lafiya."


Tunda ya ambaci Cairo zuciyar ZEEYAD ya hau bugu, No way babu ta yadda zai ɗauki DEENAH ya kaita Cairo ne, a wannan ƙasar yayi losing farin cikin sa, ba zai kuma iyayin risking rayuwar abar ƙaunar sa a chan ba, zai iya kaita kowane ƙasa ne a duniyar nan but banda that fucking Egypt country.

"Ya kayi shiru?" ya tsinkayo muryar likitan.

Ɗagowa yayi ya kalli Doctor yace "Maybe you should prescribe another Country, but not Egypt."


"A chan ne kaɗai na san Likita kwararre ta fannin rashin lafiyar ta, da akwai kwararrun likitoci a wannan ƙasar that can take a very good care of her har ta samu lafiya i promise you."


"Alright" kawai ya faɗa kafin ya baiwa likitan hannu su gaisa yana tashi tsaye.

"Mr ZEEYAD, don't forget that guarantee ɗin kwana biyar ne kawai muke dashi akanta, she need to be admitted soon."

Kai kawai ya jinjina masa yana ficewa daga cikin office ɗin.

Ɗakin ya koma nan ya sami DEENAH kaɗai ce a cikin ɗakin, tana nan as usual kamar yadda take, sai dai wannan karon ba akan bed take ba, tana zaune ne akan wheel-chair


Ƙarasawa yayi yaja kujera ya zauna yana kallon ta cike da tausayin ta.

Murmushi ya ɗanyi kafin yace "Maybe we should go out on a date today" ya faɗa yana kallon ta.

Tashi yayi yaja wheel-chair ɗin ya karkata kansa zuwa hanƴar waje.

Chan cikin garden ɗin asibitin ya kaita inda babu kowa, baka jin kukan komai sai na tsuntsaye suna shawagi, ga kuma wani irin sanƴin iska mai cike da ni'ima dake kaɗawa.


Zagayowa yayi gaban ta yana kneeling akan guiwowin sa, idanun sa cikin nata.

Ɗan murmusawa yayi yace "I know you can feel me around you and even heard me, but i don't know why you still can't react to it, MADEENAH babu abinda nake buri da kuma fata a duniyar nan face samun lafiyar ki, you really mean the world to me ganin ki a cikin halin nan makes me very sad, i just need the real you back, i don't care if you shout or disgrace me infront of your boyfriend, all i want is for you to be back to your normal health, i can't afford to lose someone so important to me again, na riga da na rasa Ummie na, so please ki tausaya min and never leave me, ke kaɗai ce farin ciki na yanzu idan na rasak ki then my life would be useless forever DEENAH" ya ƙarashe cikin rawar murya zuciyar sa cike da tsoro dama kuma fargabar kada ya rasa DEENAH.


Goge ɗan hawayen da ya zubo masa ta gefen ido yayi yana jin zuciyar sa nayi masa wata iriyar rawa.


Baisan sadda DEENAH zata warware daga rashin lafiyar ta ba, dukda baya cire tsanmanin samun lafiyar tata komin daren daɗewa, yasan Allah zai amsa masa addu'ar sa da yakeyi kullum cikin dare akan DEENAH, sai dai zaiyi haƙuri ya cigaba har zuwa ranar da Allah zai amshi addu'ar sa ta samu lafiya ba tare da ya nuna wata gajiyawa ba.

On the other hand kuma dole ne ya yarda da maganar likita na kai DEENAH Egypt ƙarƙashin kulawar kwararrun likitoci, zaiyi hakan ne kawai dan samun lafiyar ta, but sam ba yanzu ne ya shiryawa zuwa Egypt ba.

Wayar sa ce ta ɗau ƙara, dan haka ciro ta yayi daga aljihu, nan yaga dai ita ɗin ce, sam bata gajiyawa da kiran shi, tunda mahaifin ta yace babu labarin auren su ta kama wata iriyar hauka akan shi, ya rasa gane Khairat wace iriyar yarinƴa ce nacacciya marar aji da kamun kai, sam bayason yana yi mata wulaƙanci shiyasa ma idan ta kira baya takurawa kansa wurin amsa kiran tata.

Maida wayar yayi aljihu yana sanƴa ta a silent, kafin kuma ya kalli DEENAH, murmushi ya ɗan sakar mata yana miƙewa daga kneeling ɗin da yayi.


"I know yanzu kin sha iska right, so i guess we should go back for now" ya faɗa yana kama kan wheel-chair ɗin ya juya ta suka fara tafiya.


Ciki ya koma da ita, anan ya tadda Jafar tsaye, ganin su yasa shi nufar shi yana faɗin "Yanzun nan dawowa ta, shan iska kuka fita?."

Kai ya jinjina masa suna shigewa cikin ɗakin.


"Likita yace min za'a fitar da DEENAH waje hakane?."


Shiru yayi yana zama kafin kuma yace "Yeah."


"Bana tunanin Umma zata yarda."


"What, why?."


"Idan ma zata yarda sai dai idan da ita za'a tafi, ba zata ta6a yarda tayi nesa da DEENAH ba, Likewise me too" ya ƙarashe cikin ƙasa da murya.

Murmushi ZEEYAD yayi yace "Kace kawai zakayi kewar DEENAH, but Mom naku babu abinda tafi buri a yanzu face samun lafiyar MADEENAH why then zata ƙi a fitar da ita waje?."


Murmushi Jafar yayi yace "Kayi gaskiya, i would miss DEENAH, ina ma dani za'a yi tafiyar."

"Seriously, idan ka tafi kuma waye zai cigaba da kula min da business ɗina?."


"But Sir, baka tunanin lokaci yayi da zaka fara maida hankalin ka ga business ɗinka?, i mean kana samun Customers akan harkar zanen ka from ƙasashe daban-daban, but duk sabida ka damu da DEENAH ta samu lafiya you turned everything down, bakason yiwa kowa aiki yanzu, bana tunanin wannan as good."


"Who even cares about wani zane yanzu, ba zan ta6a yi musu aiki mai kyau ba a wannan halin so i decided to quit it for some time."

"For some time, how sure are you cewa DEENAH zata samu sauƙi nan ba da jimawa ba, you can't gave up on your career like that, kana nufin koda shekaru goma DEENAH zata ɗauka a haka then, kaima a hakan zaka cigaba da zama?."

"Look Jafar ba zaka gane ba, koh bakomai inada dukiyar da zanyi rayuwar nan da shekaru talatin da shi, so just stop disturbing me akan na koma bakin aiki na, idan companies ɗina ne inada masu running min su a ƙasashe daban-daban..."


"Amma ai gaskiya Jafar ke faɗa maka."


Duk ɗagowa sukayi suna kallon Umma dake shigowa.


"ZEEYAD, abinda Jafar ya faɗamaka gaskiya ne, yakamata ace yanzu ka kwantar da hankalin ka sannan ka koma bakin aikin ka, baka tunanin Career ɗinka zata iya faɗuwa warwas sabida aikin da ka daina yi wurin ƙin amsar tayi daga manƴan customers ɗinka, rashin lafiyar DEENAH baikamata ya sanƴa ka giving up akan aikin ka ba, tun kafin ka sake haɗuwa da DEENAH ka gina kanka har ka kawo matsayin nan, kai mutum ne da yakamata ya zamto mai wuyar samuwar gani, amma sabida DEENAH ka za6i kayi living simple life tare da kuma hulɗa da kowanne irin mutane, lokaci yayi yanzu da yakamata ka ajiye batun DEENAH a gefe haka nan, kasancewar ka kullum kusada ita ba shi ke nuna alamun mahaliccin ta zai iya kar6ar abar sa kokuma ya bata lafiya ba, lokaci yayi yanzu da yakamata ka ajiye sabgar DEENAH a gefe ka cigaba da ƙoƙarin gina kanka, ni zan ɗauki DEENAH na kaita chan Egypt ɗin kamar yadda likita ya faɗa, sannan ba zan amince ka biyo mu ba, yakamata kayi nesa da DEENAH haka nan, ba zan so ta zamto sanadiyyar rugujewar arzikin ba, Nagode da irin kulawar da ka nuna mata tsawon wannan lokaci, yakamata ace ka tafi yanzu haka nan."

"What, are you trying to separate me with DEENAH?" ya faɗa yana kallon Umma.


"Ba ƙoƙarin raba ka nakeyi da ita ba, ina ƙoƙari ne na ganin bata zamto dalilin rugujewar arzikin ka dama kuma career ɗinka ba."


"You can't do this to me?."


"Jafar kaje ka fara yi mana dukkanin wasu shirye-shirye, gobe zamu bar ƙasar."


"Amma Umma..."

"Banason naji kace komai, kai dai kayi abinda na sanƴa ka, muma ba rasa arzikin kula da DEENAH mukayi ba."


Kallon ZEEYAD da duk jikin sa ya gama mutuwa ya gama sanƴi yayi yace "Sir kayi haƙuri but gaskiya Umma ta faɗa."


"Your Mom doesn't like me, tanason sake raba ni da DEENAH for the second time ne."


"Sir baka fahimce ta bane..."

"Ofcourse na fahimce ta, i can clearly see that tun farko bata ƙaunaci alaƙa ta daku ba, and tayimin proving hakan yau, but ba zan iya rabuwa da DEENAH ba, and nothing can Stop me from going with her" ya faɗa cikin 6acin rai.


"Jafar da kai nake magana har yanzu kana tsaye ɗin" cewar Umma da ranta ya soma 6aci.


Ficewa Jafar zaiyi ZEEYAD yayi saurin riƙo shi yace "I will take care of everything."


Shiru Jafar yayi kafin yace "Amma ai Umma tace a'a..."


"Let me take care of everything."


"ZEEYAD, taimakon da kayi mana a baya ma ya isa haka nan, sannan kuma mungode, amma yanzu lokaci yayi da zaka zame hannayen ka daga rashin lafiyar DEENAH, a matsayi na ta mahaifiyar ta zan ɗauki nauyin komai, ba sai ka kuma spending wani abu a cikin dukiyar ka akanta ba, ka bari duk sadda ta zamto mallakin ka ba zan hana ka kashe mata koh da dukiyar da ka mallaka duka bane, amma banda yanzu ni zan kula da ƴata, dan haka ka zame hannun ka daga ciki haka nan, Jafar wuce kaje."


Jafar ɗan kallo ya zama a tsakanin su, baisan dalilin Umma na son nesanta DEENAH da ZEEYAD ba, amma koh bakomai Umma nada gaskiya, baikamata ace ZEEYAD ya yasar da komai ya tattara dukkanin hankalin sa da nutsuwar sa kan DEENAH ba.

"Jafar?" Umma ta sake faɗa.


Saurin ficewa Jafar yayi daga ɗakin dan zuwa aiwatar da abinda Umma ta sanƴa shi.


Sosai ran ZEEYAD ya 6aci zuciyar sa nayi masa mugun zafi, tun ba yau ba ya lura sam Ummar su DEENAH bata ƙaunar sa, gashi yanzu tana yin dukkanin ƙoƙarin ta na ganin ta raba sa da DEENAH, sai dai sam ba zai bar hakan ta faru ba.


Ficewa yayi daga ɗakin kamar zai tashi sama.


*****************


A Airport Jafar ya sauƙe su kafin kuma su shige cikin reception kafin tashin jirgi yayi.


Sosai Jafar kejin kewar ƙanwar tasa tun basu tafi ba, duk tafiya zasuyi su bar shi shi kaɗai, ya san komai ya daina yi masa daɗi kenan.


"Umma dan Allah ku dawo immediately after DEENAH ta samu sauƙi, nima zan dinga kawo muku ziyara a duk sadda na ɗan samu hutun aiki."


Sosai Umma taji tausayin sa, dan kuwa ita ma ba ƙaramin kewar ɗan nata zatayi ba, haka kuma tasan ba ƙaramin kewa zasu bar sa a ciki ba.


"Kada ka damu Babban Yaya kaji, insha Allah ba zamu daɗe ba zata sami sauƙi mu dawo."

Kai kawai ya iya jinjinawa yana kallon DEENAH dake kan Wheel-chair.


"Ai Jafaru kam ba ƙaramin kewa zaiji ba, yanzu dai kawai sai ka dawo wurin mu da zama" cewar Mami.


Murmushi yayi kawai ba tare da yace komai ba.


Suna nan tsaye aka fara announcing tashin jirgin dan haka duk rakiya sukayi musu zuwa filin jirgin.

Sosai sukayi sallama da juna, inda Jafar ya rungume DEENAH kamar kada ya sake ta ya ɗago yana share hawayen shi.

Rungume Umma yayi sosai yana jin shi so empty kafin kuma yayi musu addu'a sosai suka kama hanƴa.

Tsaye suke a bakin ƙofar shiga jirgin, inda ana ƙoƙarin shigar da DEENAH ne kuma sukaji an riƙe wheelchair ɗin nata.


Da mamaki Umma ta ɗago ta kallesa fuskar nan tasa a matuƙar murtuƙe ya sha baƙar shade.


"What's this?" cewar Umma.

Cire glass ɗin idon sa yayi kafin kuma yace "Am sorry, ba zuwa nayi na hana ku tafiya ba, nazo ne muyi sallama."


Kai kawai Umma ta jinjina.


Kafin kuma ya sake cewa "Ba zan iya ja da abinda kika yanke ba, but am sorry to say this; i can't stay away from DEENAH, am going with her."


"Don't try to underestimate me ZEEYAD, idan ba haka ba zan iya raba ka da DEENAH kwata-kwata ka fice daga cikin rayuwar ta."


"You can't do that."


"Zan iya yin fiye da hakan ma, muddin hakan zai kawo wa ƴata zaman lafiya, raba ka da ita ba abu ne mai wuya a gareni ba, sannan kada ka manta na yiwa ƴaƴa na tarbiyyar da basa iya ja da magana ta, ka fara shige min hanci dayawa, ban saba hulɗa da wadanda ke ja da maganar manƴan su ba, a hakan kake tunanin zaka so DEENAH kuma na baka auren ta?."

Ɗagowa yayi ya kalle ta yace "Am sorry, i didn't mean to hurt you, it's just that na damu da DEENAH ne hakan yasa bana iya barin wurin ta for more than an hour, but please kada ki raba ni da DEENAH."

"Zamu tafi yanzu, jirgi ya kusa tashi."


Riƙo hannun DEENAH yayi a cikin nashi yana kallon ta.

"And what kind of Nonsense is that, let go of her hand now."


Sakin hannu DEENAH yayi nan Umma tace "Sannan koh da ziyara banason ka kawo wurin DEENAH, ka tsaya ka maida hankalin ka kan abinda yayi dalilin ka na zuwa ƙasar nan."


Kai kawai ya iya jinjinawa yanajin zuciyar sa na zafi sosai, kafin kuma ya juya ya bar su nan.

Zuwa yayi ya wuce su Jafar da suka saki baki suna kallon su tunɗazu ba tare da ya tankawa wani daga cikin su ba.


Sai da suka ga tashin jirgin su Umma kafin su baro Airport ɗin.




*Yawan Comment, Yawan Typing*






*MHIZZ JIDDHERR................✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```




*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*




*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*




*027...*



_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_





*CAIRO INTERNATIONAL AIRPORT,*
*HELIOPOLIS EGYPT*


_____________Ƙarfe takwas ɗin dare su Umma suka sauƙa a ƙasar Egypt, dan haka already akwai masu jiran su wadanda su zasu kai su masauƙin su kasancewar Jafar ya gama yi musu komai ta yadda ba zasu wani sha wahala ba idan sunje.


Hotel ne mai kyau da tsada aka kai su kafin ayi musu iso har zuwa masauƙin su.

Umma dai kallon garin take dan kuwa yanayin ƙasar da garin kaɗai zai tabbatar maka da akwai kwanciyar hankali da daɗin zama.

Kasancewar akwai komai na buƙata a Apartment ɗin hotel ɗin yasa abinci kaɗai aka kawo musu da abin sha.

Ɗan zazzagaye ɗakin Umma tayi Falo ne da ɗakuna guda biyu sai kitchen dama kuma Toilet a kowane ɗaki.

Sosai taji tsarin hotel ɗin yayi mata dan haka toilet ta kai DEENAH tare da yi mata wanka suka fito.

Canza mata kaya tayi zuwa masu ɗan nauyi kasancewar garin akwai ɗan sanƴi-sanƴi, kafin ita ma ta shiga ta watsawa jikin ta ruwa ta fito.

Sallolin ta ta rama kan kuma taci abinci tare da ɗaukar waya ta kira Jafar da sabon layin ta na chan.

Bugu biyu taji Jafar ya ɗaga daga ɗayan gefen tare da yin sallama.

"Wa'alaika Salam, ɗan albarka."

"Umma na, kun bar ni cikin kewa."

"Toh ya muka iya, haka Allah ya ƙaddara."

"Hakane Umma, dafatan kun sauƙa lafiya, Ya DEENAH fah?."

"Lafiya ƙalau alhamdulillah, yanzu ma zamu kwanta duk da dai ba wata gajiya na kwaso ba, kasan gobe da safe zamu wuce asibiti."

"Hakane Umma, yakamata kam ki huta, ya kikaji yanayin ƙasar?."

"Toh dai gashi nan dai, babu laifi zaiyi daɗin zama daga gani."

"Masha Allah, hakan yayi kyau, gobe da safe wanda zai kai ku asibitin ku haɗu da likitan zai zo shi insha Allah."

"Toh shikenan ai bakomai, Allah ya kaimu, ya wurin su Mami fah?."

"Lafiyan su ƙalau ban daɗe da barin wurin su ba ina gida yanzu."

"Toh masha Allah, zan kira su gobe, yanzu dai bari na kwanta."

"Toh Umma, sai da safe."

"Allah ya tashe mu lafiya."

"Aameen" ya amsa kafin ta datse kiran.


Keken da DEENAH ke kai ta tura zuwa ɗaya daga cikin ɗaku nan, kafin ta kwantar da ita akan bed, addu'a tayi mata tare da rufa mata bargo.

Wutar ɗakin ta kashe kafin ita ma ta sami wuri ta kwanta.


*********************


_________Da misalin takwas na safe wanda zai kaisu asibitin ya iso.

Dan haka shirya DEENAH tayi tare da ɗaukar dukkanin wasu abubuwan buƙata suka kama hanƴar asibitin.


*********************



*AS-SALAM INTERNATIONAL HOSPITAL*
*CAIRO, EGYPT*



Babban asibitin gwamanti ne wanda ya amsa sunan sa wurin kyawu da haɗuwa, haɗi da ƙwararrun likitoci dama kuma ingantattun kayan aiki.


Kai tsaye amsar DEENAH wasu Nurses sukayi daga hannun Umma aka tura ta zuwa wani ɗaki da ba zan iya fasalta koh wane irin ɗaki bane.

Ba'a bar Umma ta shiga ba sai ma iso da akayi mata zuwa wani ɗakin daban, wanda dai da alamu nan ne wurin zaman jiran patients.

Umma kam da kallo take bin koh ina, hankalin ta duk ya koma kan inda aka kai DEENAH.

Batayi awanni biyu masu kyau da zama ba wadannan nurses ɗin suka dawo.

Ganin su ya sanƴa Umma tashi daga zaunen da take tana tambayar su lafiyar DEENAH.

Cikin turanci suka ce da ita "Kece Mahaifiyar MADEENAH ABDULSALAM?."

Kai Umma ta jinjina tace "Eh, Nice."

"Alright, Likita na buƙatar ganawa dake, biyo ni muje."


Ficewa sukayi daga ɗakin zuwa ofishin likitan.

Kansa a

Please Login or Register in order to submit comment