Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da DEENAH yaƙi 6ace masa a idanu har yanzun, sai dai baya tunanin yana da lokacin da zai tsaya kula sa yanzun.

Kallon sa yayi kafin kuma kamar wanda bayason yin maganar yace "DEENAH."

"DEENAH?" saurayin ya maimaita.

Kallon sa ZEEYAD yayi ganin yana neman raina masa hankali da kuma 6ata masa lokaci ne yasa shi ra6a wa ya wuce ciki.

Da kallon mamaki saurayin ya bisa kafin kuma a hankali ya furta "He seems so arrogant" ganin kamar shi ɗin baƙo ne a gare su yasa shi bar musu ɗakin yana ficewa.


Tsaye yayi yana kallon yadda Umma ke bata abincin tana amsa, zuciyar sa na wani irin forming farin ciki ganin ta dawo hayyacin ta har tana iya zama taci abinci, abinda ya daɗe yana jira kenan.

Cikin calm voice ɗinsa yace "MADEENAH?."

Tsayawa tayi baki buɗe ba tare da ta kai ga kar6ar abincin da Umma ke bata ɗin ba.

Duk juyowa sukayi daga ita har Umma suna kallon shi.

Kallon juna suka shiga yi da ita ba tare da kowannen su ya iya janƴe idanun sa daga cikin na ɗan uwan sa ba.

Yadda take kallon sa da manƴan idanun ta kaɗai ya sanƴa sa jin wani irin mugun kewar ta wanda baisan har haka yayi missing ɗin nata ba.

Umma ganin duk sun mace a kallon juna ya sata faɗin "I have had enough of this."

Saurin juyowa DEENAH tayi tana kallon ta hakan ya sanƴa ZEEYAD ma ɗauke duban sa yana dawo dashi kan Umma.

Kafin ya kai ga cewa komai Umma ta riga shi da faɗin "What do you think you are doing here?."

Shiru yayi kafin kuma daga bisani yace "Am sorry, i.."

"Sorry for yourself" ta faɗa cikin katse shi, kafin kuma tace "So ka kasa idda bin dokar da na sanƴa maka shine ka ɗauko ƙafa ka biyo ta har nan?."

"Am sorry, but na kasa daurewa ne."

"Ka kasa daurewa, what do you mean by ka kasa daurewa?, kana nufin ban isa na sanƴa doka kuma kabi bane komiye?."

Saurin girgiza mata kai yayi yace "Ba haka bane, it's just that..."


"It's just what?" ta faɗa cikin katse shi.

Shiru ZEEYAD yayi ba tare da ya sake ce mata komai ba yana sadda kansa ƙasa.

"Indai har ba zaka iya bin ƴar dokar nan da na gindaya maka ba, why then kake tunanin zan iya baka amanar ƴata kuma ka riƙe da kyau?."

Ɗagowa yayi yana kallon ta jin abinda ta faɗa, zaiyi magana tayi saurin katse shi da faɗin "Babu abinda zaka faɗa min, DEENAH kazo gani koh ba haka ba, sabida ita ka watsar da komai naka a chan ka taho nan saboda rashin haƙuri irin taka koh ba haka ba, alright then gata nan ai a gaban ka ka ganta, tunda har ka ɗauko ƙafar ka kazo nan dukkanin wasu sauye-sauye da zaka gani daga gare ta blame yourself for that, tunda har ba zaka iya haƙurin dawowar ta gida ba" ta ƙarashe cikin 6acin rai kafin kuma ta fice daga cikin ɗakin kamar zata tashi sama.

Maida duban sa yayi kan DEENAH da ta zama ƴar kallo tunɗazu a tsakanin su.

Sosai yake mamakin yadda tayi kamar wacce bata san shi koh wannan ne karon farko da ta fara ganin sa, dan kuwa bata wani nuna alamun hakan ba.

Da sauri ya ƙarasa wurin ta yana kiran sunan ta, ja yayi ya tsaya ganin tayi baya da sauri tana kya6e baki kamar zatayi kuka.

Mamaki ne fal ya cika zuciyar ZEEYAD yana mai bin ta da kallo.


Pillow ta ɗauka tare da rungume wa a ƙirjin ta tana kallon shi.

"What..what are you doing?" ya faɗa cike da mamaki yana ƙara step ɗaya kuwa tasa ƙara tare da cusa kanta cikin pillow ɗin.

Dakatawa ZEEYAD yayi yanajin zuciyar sa na running so very fast wanda ke sanƴa sa feeling uncomfortable.

"Actually she had a memory loss" yaji an faɗi hakan daga bayan shi, kafin kuma ya sake jin "Besides, who are you?."

Zuciyar sa ce tayi wani irin mugun harbawa jin an ambaci memory loss, inda kuma wani irin jiri da zazzafar ciwon kai suka darsu masa lokaci guda hakan ya sanƴa sa saurin dafe ƙarfen gadon yana runtse idanun shi.

Ɗagowa yayi yana kallon DEENAH da har yanzu bata ciro kanta daga pillow ɗin ba zuciyar sa na karyewa.

Da sauri ya ƙarasa wurin ta tare da janƴe pillow ɗin yana ɗago da fuskarta yayi cupping a hannun sa.

Cikin rawar harshe yace "You..you...you doesn't remember anything?."

DEENAH da ta zaro manƴan idanun ta cike da tsoron wanda bata sani ba yayi mata hakan ne, yasa ta sakin ƙara cike da firgici tana ƙoƙarin kwace fuskar ta.

"Stop" ya faɗa a hankali yana ƙoƙarin saita nutsuwar sa.

ZEEYAD sam bai yarda DEENAH tayi losing memory ɗin ta ba, dan kuwa ganin yake kamar shi ɗin ne kawai bataso ba wani abin ba hakan yasa ta faking cewar tayi losing memory ɗinta.

"Stop it" ya sake faɗa.

"I said Stop it" ya faɗa a tsawace yana tsare ta da jajayen idanun sa.

Cak ta tsaya tana kallon shi.

Wani abu mai ɗaci ya haɗiya yace "why...how could you loss your memory, i know you're faking it right?, just tell me that baki manta koh ni wanene ba, please" ya faɗa idanun sa cikin nata.

Shiru tayi tana kallon sa ba tare da tace komai ba.


"Please" ya sake faɗa cikin raunanniyar muryar sa.


"Please DEENAH" ya sake faɗa.

"Just tell me that baki manta dani ba, idan kika ce kin manta ni then bakiyi min adalci koh kaɗan ba."

Yatsun hannayen ta ya kamo tare da kallon zoben da ya sanƴa mata lokacin da take kwance a asibiti yace "See this, i gifted you this, remember?" ya faɗa yana kallon ta.

Zoben ta ƙurawa idanu tana kallo wanda bata ta6a lura dashi a hannun nata ba sai yanzun.

A tsorace kuma ta hau kokuwar cire shi daga yatsar hannun ta.

Riƙe hannun nata yayi yace "What are you doing, wannan ma baki tuna shi ba, oh yeah ba zaki tuna shi ba, then what about my face?" ya faɗa yana nuna mata fuskar sa.


"She can't remember anything" yaji an sake faɗa ta bayan shi.


Ba tare da ya juya ya kalli wanda yayi maganar ba yace "And i would make her remember it."


"You can't do that."


"Of course i can" ya faɗa cike da fusata yanajin zuciyar sa na zafi.

"I am an expert Doctor and when i said ba zata tuna komai yanzu ba, then so be it."

Share mai maganar yayi yana tattaro hankalin sa da nutsuwar sa kan DEENAH yace "Look MADEENAH, i know atleast yanzu kin tuno wani abin da kika sani, you can't do this to me, please talk to me please."


Shiru tayi kawai tana kallon sa dan kuwa babu abinda ta tuna game dashi, infact a takure ma take sabida tsoron sa takeji sakamakon tsawar da ya daka mata, hakan yasa duk ta kasa sake jikin ta.


"MADEENAH?" ya faɗa.

"What is going on here?" ya jiyo muryar Umma.


Cike da 6acin rai Umma ta ƙaraso wurin, ganin yadda ya damƙe hannun DEENAH cikin nashi ba ƙaramin 6aci ranta yayi ba.

Hannun DEENAH ta kama tana fuzgewa daga cikin nasa cikin 6acin rai tace "How dare you, ka fara wuce gona da iri."

Shiru yayi bai ce komai ba dan kuwa baya tunanin zai iya sake tankawa Umma idan tana magana.

DEENAH saurin 6oyewa tayi a bayan Umma.

Kallon sa Umma tayi tace "I warned you didn't i?, dah ace zaman ka kayi achan da baka zo ka tadda 6acin rai da damuwa ba, abinda nake gudu kenan hakan yasa ban sanar da Jafar halin da take ciki ba, had he know nasan babu abinda zai hana shi zuwa nan, duk ƙaunar da kakeyi mata kana tunanin yafi wanda ɗan uwanta keyi mata ne?, amma shi yabi doka ta ya zauna inda na umarce shi, but look at you sai da kayi dukkanin yadda kayi ka kasa controlling zuciyar ka ka biyo ta nan, kana tunanin zuwa tarar da farin ciki sai dai ya tadda akasin hakan, tunda yanzu ka samu abinda kake nema zaka iya tafiya, duk ranar da muka dawo zaka iya zuwa ka duba ta."

"Please don't send me away, i care so much about your daughter."

"Kana nufin mu bamu isa mu bata isasshiyar kulawa bane komiye, dukkanin halin da DEENAH ke ciki baka kai ni jin zafin hakan ba, so now stay beyond your limits, DEENAH bata buƙatar ka yanzu a rayuwar ta dan kuwa wahalar da kanka kawai zakayi, i guess kaima ba zaka rasa family ɗin da zaka kula dasu ba, so from now on...nayi maka tsakani da DEENAH babu kai babu ita, i want you to stay out of her life for good, kaje ka nemi wacce kuka fito daga ƙabila ɗaya tare, dan kuwa a matsayi ta ta Hausa-Fulani bana tunanin zan iya baka auren ƴata" ta ƙarashe in a serious tone.

ZEEYAD jin maganganun Umma yake kamar ana watsa masa ruwan zafi a jiki, kai ya fara girgizawa yana faɗin "No...no i can't do it, i can't leave without DEENAH..."

"Of course zaka iya rayuwa babu DEENAH tunda ba tare aka haifo ku ba, sannan kuma ka iyayin rayuwa tun kafin ka haɗu da ita."

Kai ya girgiza yace "That was a different thing, but DEENAH...i just couldn't imagine my life without her."

"Bana buƙatar ja in ja da kai, i have said my mind and i won't take back my words."


"I have suffered enough in my life, but please kada ki sake nesanta ni da DEENAH i beg you Aunt" ya faɗa yana zubewa kan guiwowin sa.

Ɗauke kai Umma tayi kafin tace "Bana magana sau biyu, sannan ba ƙoƙarin nesanta ka da DEENAH nake ba, ina nufin ka rabu da ita ne har abada."

"Please Aunt, i can't live without DEENAH, i promise zan koma inda na fito indai har ba zaki raba ni da ita ba."

"You don't have to do that, as i told you earlier i would repeat myself again, as from now on babu kai babu DEENAH, don't let me repeat myself for the third time, stay away from my daughter, Forever."

Shiru ZEEYAD yayi yanajin dukkanin wani sungun farin cikin sa na gushewa, zuciyar sa yakejin kamar zata fito waje da maganganun Umma, wani irin abu yaji ya tokare masa maƙoshi zuciyar sa na mugun suya sosai, baisan dalilin da ya sanƴa Umma bata ƙaunar sa ba, baisan laifin da ya aikata mata ba, DEENAH itace farin cikin sa amma gashi yau guda tana neman yanke alaƙar dake tsakanin su, yanason DEENAH da dukkanin zuciyar shi, da dukkanin jinin jikin shi, yana jinta tamkar numfashin sa ne, bai ta6a kyashin ta ba, soyayya yakeyi mata na gaskiya, ba tare da duban cewa ya fita wani abin ba, babu abinda yayi lacking a rayuwa except farin ciki sai dai a duk sadda wani abin farin cikin ke neman kusanto shi, a lokacin ne kuma za'ayi dukkanin yadda za'ayi na ganin an raba shi dashi, baisan yaushe ne zai sake samun farin cikin da zaiyi lasting kwana ɗaya a cikin ta ba, kullum zuciyar sa a cunkushe take, kullum zuciyar sa cikin kewa da begen ta yake, da ita yake kwana kuma ya tashi, and now Umma na ƙoƙarin raba sa da ita, and ita kuma ba zata iya hana hakan ba sabida matsalar mantuwa da ta samu, runtse jajayen idanun sa yayi yanajin yadda zuciyar sa ke racing da ƙarfi.

"Doctor, why don't you just led him away from here, koh haka zaku zuba ido kuna ganin abin dake faruwa, my sick daughter need to rest domin samun lafiyar ta" cewar Umma.

Maido duban sa kan ZEEYAD dake durƙushe tunɗazu bai juyo yaga fuskar sa ba, but haka kurum yakejin wani irin strange feeling akansa, idan ma shi ɗin ɗan uwa ne a garesu ai baiyi kama dasu ba koh kaɗan, sannan baya tunanin ɗan asalin cikin Nigeria akwai mai irin farin nan, daga ganin sa kaga balarabe koh ba indiye, kallon bayan sa kawai Sadeeq keyi dukda baisan asalin kan zancen nasu ba sai dai ya tausayawa bawan Allahn sosai, sabida rabo da masoyi sam babu daɗi.

Umma ganin Sadeeq ɗin yaƙi kula ta sai ma tsayuwa da yayi yana kallon ZEEYAD ya sanƴa ta fizgo hannun DEENAH da niyyar su fice waje.

Saurin riƙe DEENAH ZEEYAD yayi ransa na mugun 6aci.

Tsayawa Umma tayi tare da juyowa ganin DEENAH taƙi biyo ta ta tsaya.


Ganin ZEEYAD riƙe da hannun ta ba ƙaramin 6ata mata rai yayi ba.

"You can try as hard as you can to separate me with DEENAH, but that won't work" ya faɗa yana tashi tsaye tare da juyowa.

Kallon sa kawai Umma keyi cikin 6acin rai.

Wayar dake hannun Sadeeq ne ya su6uce ya faɗi sakamakon arba da idanun sa sukayi akan fuskar ZEEYAD.

"Let go of her...now" cewar Umma.

Bai motsa ba haka kuma bai saki hannun DEENAH ba, dan kuwa ya ƙudurta a ransa cewar muddin ya saki hannun DEENAH ba tare da Umma ta tausaya masa ba then...ya barta kenan har abada kamar yadda mahaifiyar ta ta buƙata.

"So you won't let go um, alright" ta faɗa tana sakin hannun DEENAH kafin tace "Let's see idan ita DEENAH ɗin choose to be with you or prefer to walk away" ta faɗa tana kallon sa.


Cize bakin sa yayi trying so hard to control his emotions.

Juyowa DEENAH tayi tana kallon shi, kafin kuma tayi saurin juyawa ga Umma tana miƙa mata hannu.

Kallon su kawai Umma keyi ba tare da ta baiwa DEENAH hannu ba.

Sadeeq da sauran nurses ɗinma ƴan kallo suka zama a wurin.

Juyowa DEENAH tayi kafin ta sanƴa ɗayan hannun ta tare da fara kiciniyar cire hannun ta cikin nasa.

Riƙon da yayi mata ne ya sanƴa ta kasa kwacewa.

Sosai tayi trying wurin ganin ta kwace hannun ta sai dai ta kasa hakan ya sanƴa ta fara yi masa kuka.

Runtse idanun sa yayi zuciyar sa na matuƙar zafi sosai yanajin zafin kukan ta sosai a cikin zuciyar sa.

Fara sassauta riƙon da yayi mata yayi hakan ya sanƴa ta saurin fuzge hannun ta sai dai kafin ta kai ga cirewa baki ɗaya yayi saurin riƙo ƴar yatsar ta dake sanƴe da ring ɗin da ya bata.

Wani kukan ta sake sanƴawa hakan yasa shi saurin sassauta riƙon inda tayi saurin fuzge yatsar ta ring ɗin na ficewa cikin hannun sa.

Kallon ring ɗin ya tsaya yi kafin ya damƙe shi cikin tafin hannun shi yana ɗagowa ya kalli DEENAH da ta rungume Umma tana kuka.

"So now DEENAH da kanta ta guje ka, are you still going to force yourself into her life again, kokuwa ka haƙura?."


Duban sa ya maida kan hannun sa dake damƙe da zoben yace "No, i would do as you said, i won't force myself into your daughters life again..am...am living her for good not just because she doesn't like me, but because you forced me to, and i will make sure ban sake shigowa rayuwar ƴar ki ba, i will make sure i stay far away from you guys, i will make sure i became exactly who you wants me to be, Thank you for all you've done to me and i really appreciate it, banyi fushi dake just because kin raba ni da DEENAH ba, but nayi fushi ne da kaina for spending years loving someone that can never be mine, you're a mother and am sure you make the right decision for your daughter, which she will never regret, and yes duk sadda DEENAH ta dawo hayyacin ta don't tell her that kece wacce kika raba mu but i chose to leave her on my own, sabida banason rusa farin cikin happy family like you, just tell her that nine nace ba zan rayu da ita ba, idan kikayi hakan then i know that she would hate me forever sannan kuma ta cire ni daga zuciyar ta dukda kuwa bana tunanin idan ina ciki tuntuni, daga nan kuma zatayi ƙoƙarin ganin ta mance dani kamar yadda nima zanyi yanzun, am sorry idan na ta6a 6ata miki...am living" ya ƙarashe yana maida duban sa kan DEENAH da har yanzun bata ɗago ba, kauda idanun sa yayi daga kanta kafin kuma ya ɗaga ƙafa dakyar ya fice yana buge Sadeeq da ya saki baki da hanci yana kallon shi, ba tare da ya koh kalli fuskokin wadanda ke tsaye cikin ɗakin ba.

Da kallo Umma da itama jikin ta ya gama yin sanƴi tayi sai dai ta dake tana shafa kan DEENAH dake rungume da ita.

Cikin gudu Sadeeq ya fice dan mara masa baya sai dai koh alamun sa bai gani ba, kamar wanda iska ya ɗauke.

"Yanzun nan ya fita, where could he be?" ya faɗa cikin gigicewa yana yin hanƴar waje da gudu tare da bangaje dukkanin wanda ke gaban sa ya wuce.

Har farfajiyar asibitin Sadeeq ya fice sai dai baiga ZEEYAD ba baiga alamun sa ba.

"Ohh no" ya faɗa kamar wanda zaiyi kuka yana riƙe kai cikin mugun takaicin wautar da yayi har ya bari ya fice daga ɗakin.


Office ɗinsa ya dawo tare da ɗaukar makullin motar sa yaja ta tare da barin asibitin.

Dai-dai lokacin ZEEYAD dake tafiya yanajin kamar ruhin sa ta bar jikin sa ya fito, kai tsaye motar sa ya nufa tare da buɗe ta ya shiga.


Kansa ya ɗaura kan steering ɗin motar yanajin wani irin zazza6i mai zafi na neman rufe shi, sosai idanun sa sukayi jaa kansa na mugun sara masa.

Da kyar ya samu yaja motar ya bar cikin asibitin.






*Yawan Commen, Yawan Typing*






*MHIZZ JIDDHERR..............✍🏽*
[8/30, 9:32 AM] Mhizz Jiddherr❤️: *Z E E Y A D*
```[The Abandoned Prince]```





*NA*
*JIDDAH BINT MUHAMMAD*





*MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION*




*028...*



_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah. Please don Allah duk wacce ta san ba siyan maganin za tayi ba kada ta dauki number ko ta kira waya, kada mu 'batawa kai lokaci🙏🏻_

_*infection*_
_Muna da magungunan sanyi sadidan! wanda yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye! infection yana karya garkuwar jikin dan Adam yana dakusar da kowace irin mu'amula mussaman ga ma'aurata, sanyi ko wane iri kike/kake fama dashi da izinin Allah idan anyi amfanin da irin maganinmu za'a dace_ _*SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARAI*_
_07084653262_




___________Yau ma Ficewa sukayi dan kai DEENAH motsa ƙafafuwan ta a inda suka saba.

After so many attempts da tayi da kanta, ta samu tafiyar tata ta ɗan daidai ta sai dai tana yin kaɗan zata zauna alamun ta gaji.

"Wowww seems like tafiyar ki ya fara miƙewa, i can't believe it" cewar ɗaya daga cikin nurses ɗin.

Murmushi kawai DEENAH tayi Kasancewar shine abinda taga suna yi.

"So now mai kuma ya rage?" cewar ɗaya.

"Ummm, i think gudu."

"Gudu kuma?."

"Yep."

"No ba zata iya ba, ƙafar tata bata yi wani kwarin da zata iya yin gudu ba."

"Alright then, sai mu koma ciki."

Riƙo DEENAH sukayi suka koma ciki.

Zaune suka sami Umma na waya, dan haka zaunar da DEENAH sukayi kafin su tsaya jiran Umma ta gama wayar.

DEENAH idanu kawai ta zubawa Umma tana kallo har ta idda wayar ta ajiye.


Murmushi Umma tayi, kafin ta kalle su tace "Har kun gama?."

"Yes Ma'am, sai gobe kuma."

"Masha Allah, Nagode muku sosai, Allah ya biya ku."

"Kada ki damu Ma'am, ai aikin mu ne."

"Mu zamu wuce yanzu, sai gobe kuma."

"Alright thank you so much."

Murmushi sukayi kafin su juya da niyyar tafiya.

Tashi ita ma DEENAH tayi tana mara musu baya.

"A'a DEENAH?" cewar Umma.

Miƙewa Umma tayi daga inda take zaune tare da zuwa ta kamo DEENAH tace "Zo nan ki zauna, sai gobe kuma zasu dawo."

Hannun ta shiga kwacewa tana kya6e baki alamun zata yi kuka.

Ɗaya daga cikin nurses ɗin ce tace "DEENAH je ki zauna kinji, gobe zamu dawo mu sake fita."

"Come on" cewar Umma tana riƙo ta.

Ƙara tasa tana kwace hannun ta tare da maƙe kafaɗa, kafin kuma tayi bayan su tana 6oyewa.

Murmushi Umma ta ƙaƙalo kafin tace "Meke damun ta?."

"Ma'am ki kwantar da hankalin ki, damu ta saba yini kullum shiyasa batason mu tafi mu bar ta."


"DEENAH dear, zo nan gare ni kinji?" cewar Umma tana kai hannu ta kamo ta.

Sake 6oyewa tayi tana ƙanƙame su.

"Ma'am sai kinyi haƙuri, kinsan yanzu kwakwalwar ta ta koma tamkar irin ta yara ne, a hankali zata saba dake."

Sosai Umma taji babu daɗi a ranta wai yau DEENAH ce ke gudun ta sabida bata santa ba.

Wuri kawai ta samu ta zauna kafin tace "Shikenan kuje toh."

Ficewa sukayi still tana maƙale dasu.

Office ɗin su suka koma da ita kafin kowacce tayi wurin table ɗin ta.


DEENAH kuwa wurin kawai take bi da kallo, duk abinda ta gani kuwa sai ta ɗaga shi tana kallo tare da son tuno koh menene shi, idan ta kasa kuma sai ta ajiye shi ta kama wani.

Wata nurse ce ta shigo ɗakin tare da ƙiran sauran Emergency call, ba tare da 6ata lokaci ba dukkan su suka dunguma suka fice daga office ɗin cikin sauri.


Da kallo DEENAH da ta kya6e baki kamar zatayi kuka ta bi su, kafin ita ma ta fice daga ɗakin a hankali cikin tafiyar ta da bata gama warkewa ba.

Ficewar ta kuwa bata ga alamun su ba dan haka wani hanƴar da take tunanin nan suka bi tayi.

Tafiya take har ta sauƙo ƙasa tayi hanƴar waje amma bata gan su ba, dan haka wani hanƴar ta sake kamawa ta fara bi har ya kaita zuwa wani wurin da babu mutane sosai.

Waige-waige ta fara yi kafin kuma ta samu irin kujerun ƙarfe masu kyau da akeyi ɗinnan ana ajiye su a wajen asibiti ta zauna idanun ta na kawo hawaye.

Ɗilowa hawayen yayi dan haka ta kai hannu ta shafo shi tana kallo dan kuwa batasan menene shi ba, taga dai kamar irin abin nan ne da take gani a idanun matar nan wasu lokutan, ga kuma taga sai zubowa suke ta kasa controlling ɗin su, ga kuma wani irin yanayi da takejin ta wanda batasan koh na menene shi ba.


Kwanciya tayi akan kujerar tana cigaba da rera kukan ta a hankali.

Ta kai almost 10mins a haka kafin ta jiyo muryar a saman ta "Are you Okay?."

Tsaida kukan nata tayi tana buɗe idanun ta.

Jin tayi shiru bata ɗago ba ya sa shi sake faɗin "Do you maybe need some help?."

Shiru ta sake yi tana wuwwula idanu kafin kuma ta shiga ɗago da kanta a hankali tana sauƙe idanun ta cikin nasa.

Saurin maida kanta tayi tana runtse idanun ta.

Mamaki ne ya kama shi a ransa yace _"Is she normal?"_ yana mai tsugunnawa.

"Hey" ya sake faɗa.

A hankali ta miƙe zaune tana wuwwula idanun ta kanta a ƙasa.

"Are you Okay, why are you sitting here alone crying?."

Shiru tayi bata basa amsa ba sai ma idanu da ta kafa masa tana kallon idanun sa kasancewar fuskar sa ɗauke da facemask.

Waving hannayen sa yayi akan fuskar ta inda tabi hannun nasa da kallo, tana sake maido idanun ta kansa.

"What's your name?" ya faɗa.

Shiru tayi nan ma just staring at him.

_"Toh kodai kurma ce?"_ ya faɗi hakan a ransa kafin kuma yace "Are you lost?."

Nanma shiru tayi tana kallon sa, kafin kuma ya miƙe daga tsugunen da yake yana faɗin "Well, am living then tunda ba zakiyi magana ba" ya faɗa yana juyawa da niyyar tafiya.

Riƙo rigar sa tayi ta baya hakan ya sanƴa shi tsayawa tare da juyowa yana kallon ta.

A hankali yace "Seems like ta shirya magana" kafin kuma yayi magana yadda zata ji yace "So now tell, what are you doing here all alone?."

Ta inda ta 6ullo

Please Login or Register in order to submit comment